Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa " Okay Dama badon Allah kake Sona ba? Dama Ni tuntuni nasan da hakan , nayi maka laifi ba sai ka yafe mun ba?. Wani Irin kallo yayi mata tare da cewa " Anƙi A haƙuran Oya Out.! Yayi maganan yana ɗan Doka mata Tsawa ...cikin Sauri Aaliyah ta fice daga Falon Hawaye na bin Kuncin ta , Hannun ta tasa tana Goge Hawayen dake zubo ma Kuncin ta , kamin ta nufi Ɓangaren Ƴan Aikin gidan .

Tun da ta juya ta fita Aydaaan ya kasa Kauda idanun sa daga Hanyar da ta fice , Dafe zuciyar sa yayi dake Harba masa Da ƙarfi kamin ya furta a bayya ne da cewa " Me yasa zuciya ta zaki mun haka? Ina jin tausayin Ta , Ina kuma Son Jidderh , Humm Dan Gyada kafadan sa yayi tare da cewa " Ko meye dai nayi ma kaina Alƙawarin Auren su duka. Miƙewa yayi yana nufar Privacy don ya watsa Ruwa ko zaiji Sanyi a zuciyar sa .

Abun da ya faru da Hauwa kuwa bayan Sakin ta da Salisu yayi ,daƙyar ta iya barin gidan ,don har yamma ya fara sannan ta saka mayafi tana ficewa daga Gidan tare da nufar Layin su don ta koma gidan mahaifin nata don bata da inda zata je da ya fi mata nan .

***

Assalamu alaikum Ta yi Sallamar a sanyaya jikin ta a mace ganin Baba da tayi da Buta yana Alwala alamun zai tafi masallaci . Umma ne ta fito daga Madafi hannun ta Ɗauke da muciya alamun talge ta gama . Tsayawa cak tayi ganin Hauwa da tayi kaman kuma yanda shima Baba yayi mutuwar zaune . Don shi a kullum gani yake idan Hauwa ta Rasa Salisu to bazata taba samun mijin Aure ba , a cewan sa maza yanzu basa Aure sai lalata da mata a haka suke karar da Rayuwar su cikin aikin alfasha , Wanda Azaban shi na Wurin mahalicci tun a duniya zaka fara ganin abun da ka aikata ,zaka girbi Abun ka .


Wani irin ƙaƙari yayi kamar tari zai shake sa , cikin Wani irin murya ya ce " Hauwa? Me kika zo yi da Wannan yammacin Ana Kirar Sallah?. Eiyee.? Ya kuma maganan cike da Tsawa da kaguwa da yayi kan yaji lafiya.!

A hankali Hauwa ta sinne kanta ƙasa , hawaye na fara zubo mata , Baba Ƙaddara ce.!
Ƙaddara? Ya maimaita maganan yana ajiye butar hannun sa tare da miƙewa Tsaye ,me kike nufi ? Faɗa mun Sakin ki yayi ne shi Salisun?.


Eh Baba ". Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un , Shikenan dama kin fi so ki rinƙa kaikawa Tsakanin Ni da Mahaifiyar ki muna haɗa kafaɗa ,haka kike so to dawo ki zauna . Hauwa kin mawa kan ki sakiyar da babu Ruwa , Haba Hauwa Allah ya baki namiji kamar Salisu ....Umma ne tayi Saurin katse shi tare da cewa " A'a Malam ,Hauwa fa tana Hakuri da Salisu , ya nuna baya ra'ayin ta to ya zata yi , Ga Hauwa babu makusa ,amma ace Salisu ya sake ta , Kai Wannan yaro yaci mana mutunci , wallahi sai Allah yayi mana sakayya tsakanin mu da shi ....duk hawalar da ya ....ke Ya isa da Allah." Baba ya katse Umma cikin nuna ɓacin Rai .


Dama kema ai bakya ganin Laifin yar naki ko kuwa me zata yi ai ke bakya gani . Ban da dama ba Ƙaunar Salisu take yi ba , da ya sake ta ko ya fara banbami ba sai ta zube ƙasa ta basa Haƙuri ba?. hakuri malam? Hakuri fa kace? Umma tayi maganan tana kara jajanta wa kamin tace " Wallh malam Ni na fara zargar Wani Abu tsakani ka da Wannan yaron Salisu haba , me ya rage game da Hauwa? Bayan cutan yunwa , wallahi ina da tabbacin Hauwa har ciwon zuciya ta na dashi . Ke da Allah tashi bar kukan nan ki wuce Ɗaki ki cire Wannan mayafin , Ko kashe kan ki zakiyi akan Ɗa namiji? Wuce Ni da Allah , Allah ya baki mai ƙaunar ki ,cida sha da sutura kar ya yanke maku har Abada . A hankali Hauwa tasa ƙafa tana shigewa Ɗakin Umma , saboda Tsaban tashin hankali ko gaban ta bata gani dakyau . Juyawa Baba yayi yana cigaba da banbami da faɗa , yana cewa " Ai kuma Hauwa shikenan keda Aure sai dai kiga Anayi . Tun da kika rasa Salisu yaron kirki ɗan manyan mutane Wallh kin yi Asara . Aje Muciya Umma tayi tare da nufar Ɗakin ta don ta rarrashi Hauwa ,don ta lura sam ba a hayyacin ta take ba .

***
*Moddibo's Family*
Ɓangaren Aaliyah kuwa tun bayar ficewar ta daga Part Ɗin Yallaɓai Aydaan ,ta tattara kayan ta ba tare da kowa ya sani ba ta gudu daga Garin Lagos zuwa Yobe , Don garin su ta koma da Yammaci ta sauka a gida .

A soron Gidan su ta tsaya sam ta kasa shiga saboda Tsoron Inna Turai da kuma a yanzu ya zata amshe ta . A haka har Gari ya fara duhu magriba tana fara Wucewa . Motsin shigowa soron nasu da taji ne yasa ta zabura tana miƙewa daga Tsugunon da take a ƙasa . Abba ne da ya dawo daga masallaci ya dallara Haske n fitilan sa tare da cewa " Waye ne anan wurin?. Jin Muryar sa Inna Turai dake Tsakar gida tana Aikin abincin dare yasata Saurin ƙarikowa tare da cewa " me ya Faru ? , Tayi maganan dai dai Abba na Haske fuskar Aaliyah... Aaliyah Suka ambata Sunan.....!




#MMN TEDDY🧸
*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*


*🌐MMT'S*
*WRITERS ASSO.📚🖊️*
(MMTWA)
#We are here to educate, entertain and enlighten our Readers...

Ina masu zuwa mun hello maman teddy Ni marubuciya ce pls ki sani a ƙungiyar ki , ko kuma maman teddy ina Son na iya rubutu ban san ƙungiyar da zan shiga don suyi Guiding ɗina ba , So pls This is my new association .
Ga masu sha'awar fara Rubutu ko marubuta Wanda basa da ƙungiya , to dama gare ku ga Sabon association na Mamanteddy ,Zaki iya mun magana ta WhatsApp number na 08081202932 yauwa...

Albishirin ku masoya maman teddy , a yau min fara Ɗaura maku daya daga cikin Nobels din ta mai Suna ƳAR WAYE.? A YouTube channel namu , me kike jira maza garzaya don ki saurara , it's a Love caring and sympathetic story , ƳAR WAYE.! ga YouTube link namu zaku iya joining https://youtu.be/M0SeeufXge8
sannan kar ku manta Wurin yi mana Subscribe mun gode.!

Morning Update🕊️
"Aaliyah Su duka suka Haɗa baki Wurin Kirar Sunan Aaliyah ,wanda tayi zumbur tana Wurwurga Idanun ta cike da Tsoron Abun da zai kai ya kawo . Shiru Abba yayi ,yayin da Inna Turai ta fashe da Kuka mai tsuma zuciya tare da Jin matsanancin nadama . Abba ne yayi magana cikin Sanyin murya da Son Ganin ya Ƙwantar mawa Aaliyah da Hankali yace" Aaliyah mai yasa Zaki zauna A soron gida , baki shiga Daga ciki ba ? . Malam nine na sa Aaliyah yin hakan , tsoron shigowa take ji a tunanin ta har a yanzu nice Turai da ta sani... Aaliyah nayi nadama ,ki yafe mun kan Abun da nayi miki ,nasan na Wahalar dake na kuma azabtar dake a rayuwa , Amma a sanadin ki yau gashi Mahaifin ki ya samu lafiya , Sanadin ki muke cikin Wannan Rufin Asirin , Aaliyah taho na nuna miki Wani Abu .! Inna Turai tayi maganan tana kai hannun ta tare da kamo na Aaliyah wacce ta tsaya ta saki baki ta kalli Abba ta kalli Inna Turai . Cikin gidan suka shiga inda Hasken Fitilar Nepa ya haska Tsakar gidan. Wata matashiyar mata ta gani wanda a shekaru zata kai 35 zuwa sama ,sai kai kawo take tsakanin kitchen Da Ɗakin Aaliyah kamin ta bar Gidan . Larai Ga Aaliyah na Ta Dawo.! Inna Turai tayi maganan cike da jin dadi fuskar ta dauke da matsanancin Farin ciki na ganin Aaliyah . Allah Sarki Aaliyah kene da Saukar yamma ? To shiga Ɗaki yanzu za'a Sauke Abincin dare a kawo miki naki . A'a A dai sa mata Ruwa ta fara watsawa Tukun na . Cewan inna Turai tana maganan tare da Kallon Aaliyah ,Wanda ita sam ta rasa Gane inda Maganganun nasu duka ya dosa . Murmushi Larai tayi kamin tace To bari na Haɗa A electric stove Sai na Ɗaura mata a Ga Nepa a sun kawo yan Albarka . Ta ƙare maganan tana nufar madafin tsakar gidan . Inna Turai ne ta riƙo Aaliyah da ta tafi duniyar Tunanin Wacece Kuma Larai , me take yi a cikin gidan su?.


Ɗakin Inna Turai Suka nufa Har da Abba , Wanda yau yafi masa ko wacce Rana jin Dadi a rayuwar sa ,tabbas Aydaaan ya cika ɗan halal babu Abin da zamuce dashi sai dai Allah ya saka masa da Alheri . Abun da Abba ke faɗi kenan tamkar mai sambatu . Juyowa Aaliyah tayi cike da Mamaki kamin tace " Abba wai kaine ka samu lafiya ? Allah Alhmdlh ." Ta furta kalmar tana rintse ido sai Hawaye ,dama ita kuka bai mata Wuyan zuwa . Abba A ina kasan Aydaaan?. Kamin Abba ya mata magana ne Inna Turai ta amshe ta da cewa " Aydaaan ya gama mana komai Aaliyah , Aaliyah har abada ki kasance yar Halal wurin biyayya ga Aydaaan , baki da Abun da zaki saka mishi dashi ,don ya gama miki Komai a rayuwa . Shine yazo ya kwantar ma Mahaifin ki da Hankali a rana Daya ya sanar mana cewa " Kina Gidan su aikatau ,kuma bayan nan shi ya dauki duk Wani nauyin aikin Mahaifin ki , a kayi masa komai ya samu lafiya . Ina kuma zaune ya kawo Larai mai tayani aikin gida ,nasan baki san ta ba . Aaliyah don Allah ko bayan ba Ran mu kar ki mawa Aydaan Butulci domin baki da masoyin da Akaf rayuwa yake son ki ,da Son ganin farin cikin da ya Wuce Aydaan . Saboda ya taimaka kwarai akan Mahaifin ki damu duka .

Shiru Aaliyah tayi tana tunanin furucin ta akan Aydaaan , ( Nace ina Son ka ne? ,Ni bana Son ka ,don Allah ka yafe mun kan Abun da nayi maka ,sai na tafi). Rintse ido Aaliyah tayi tana jin Zafin maganan da tayi masa , wani irin kuka ta saki mai ban tausayi tare da jin tausayin Aydaaan ɗin ya kamata , a zuciyar ta ne ta fara cewa" Yana nan yana kula da iyaye na ,amma Ni a daidai lokacin da nake neman faraga na wani Abu duka don naga karshen nasa Rayuwa , Kaico Na Ni Aaliyah." Kuka take yi Sosai tare da zama tana aje koman ta . Rungume ta Inna Turai tayi itama tana share ƙwallahn dake zubo mata . Aaliyah kiyi hamdala ki gode mawa Allah , da Allah ya baki masoyi kaman Aydaaan , Ina kuma neman Afuwan ki akan Abubuwan da nayi miki a rayuwa . Inna Inna..."

Aaliyah ta kira Sunan Inna Turai har sau biyu kamin ta girgiza Kai tana cewa " Inna Ina Son ku duka , dai dai da rana Daya Ban taɓa riƙe ki a zuciya ta ba , na Dauke ki tamkar Ummana , Inma kin mun Wani Abu na yafe miki Inna , nima ki yafe mun Don Allah . Jan Ajiyar zuciya Inna Turai tayi tana furta Aaliyah baki taba mun komai ba na ɓacin rai , Aaliyah na gode na gode kwarai .


Alhmdlh Allah kenan , Ko mai yayi zafi dama maganin shi Allah ,yau gashi Allah yakara hada mun kan gida na , Addu'ar da na dade ina yi ,yau gashi Allah ya amsa . Abba yayi maganan tare da daga Hannun sa sama yana mai godiya ga Allah . Murmushi duka suka yi ,kamin Aaliyah tace " Inna To ita Larai a ina take? Kuma me take yi ,yanzu tun da na dawo ita sai ya koma gidan su.


Murmushi Inna Turai tayi tare da cewa " Ai Aydaaan ke biyan ta kudin aikin ta , sannan har abincin da muke ci ,Kinga Dakin can na ki na da ,ciki yake da kayan abinci duka shine ya zuba . Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un , Inna Aydaaan ɗin? To Wa ya sashi? Inna don Allah Ace masa yazo y kwashe kayan sa ,saboda Bama bukata Ni zan cigaba da kokari a cikin gidan mahaifina ,bana bukatar Taimakon sa . Tsayawa Duka suka yi suna kallon ta na mmkin wannan magana na ta. Inna ne zata yi magana sai Abba ya daga mata hannu Alamun ta dakata . Okay Aaliyah yanzu ki huta zuwa Safe Zamiyi magana. To Abba ". Tayi maganan tana kallon Abba da ya mike yana cewa " Turai ina Son magana dake . Miƙewa Inna Turai tayi tana cewa " Tom malam .


Bin bayan Abba tayi tana cewa " Aaliyah ina zuwa. Bayan fitan su ne Aaliyah ta tsaya shiru tana Tunanin me Aydaaan ke nufi Da ita da Rayuwar ta? Yace baya Son ta ,amma me yasa yake mata hidima? Sannan yace Yana da Wanda yake So Jidderh , to me yasa yake son kuntata ma Rayuwar ta? Haushi ne ya kama Aaliyah a hankali ta furta , Wallh ba zan yarda ba , haƙar ka bazata cimma Ruwa ba ,kaje ka Auri Wanda kake so , Tuno da maganan sa yasa shi cewa " Oh Yanzu na tuna ,yana son Aure na ne ,don ya cutar dani akan Abun da nayi yunƙurin yi masa. To ba zan yarda ba , ba kuna zan Aure sa ba . Ta ƙare maganan tana cuno bakin ta gaba cike da Tsiwa da yarinta .

***

Bayan ya gana Training kaman yanda ya saba duk safiya , Kai tsaye Bedroom Ɗin sa ya nufa Don ya sha Cofee kaman yanda Aaliyah ta saba tanadar masa ,dama duk Wani mai aiki na cikin Wannan gidan. Idan ya sha Cofee ya watsa Ruwa kamin daga Bisani ya shirya sai ya wuce Asibitin sa. Nufar Can sofa yayi yana goge zufan Jikin sa da Towel ,ganin Wurin Empty yasa Aydaaan yin shiru cike da mamaki , ina Aaliyah ? Me yasa bata zo Wurin sa ba jiya da Dare ?. Sauke Ajiyar zuciya yayi tare da girgiza kan sa ko tunanin me yayi Allah masani ,sai kuma ya juya yana nufar Toilet. Da kan sa yayi komai ,aka sin da baya Da komai Aaliyah ke yi masa. Mintuna sha biyar ya fito ɗaure da Towel a kugun sa ,don bai tsaya saka rigar Wanka ba . Komai sauri² yayi shi kamin daga Bisani ya kammala cikin shigar Suit din sa baƙaƙe yana nufar Part ɗin Ammie" .


Saukowa Ammiee take daga Up stairs hannun ta na dafe da Ƙarfen Stairs Ɗin . Sanye take cikin Lace dark blue Wanda yayi matuƙar mata ƙyau , Abun ka ga Cikakkiyar Hausa Fulani. Wuyan ta kuwa da hannun ta Babu Hasken abun da kake Gani sai Na Gold . Saukowa take a hankali cikin Salɓi na Fulani tare da ƙariko tsakiyar ƙayataccen Falon ta . Aydaaan.!

Ta kira Sunan shi cikin mamakin ganin sa da wannan lokacin , don tasan ko breakfast baiyi ba . Ammiee Ina Aaliyah take? Ta dawo nan ne da aiki? . Aaliyah Kuma? Ammiee tayi maganan tana masa kallon Rashin fahimta . Humm sauke Numfashi yayi tare da saka Hannun sa yana sosa Sumar kansa kamin yace " Sorry Ammiee ,An tashi lafiya.? Murmushi Ammiee tayi tana masa kur da ido ,tana fahimtar Abubuwa da yawa game dashi akan Aaliyahn . Aydaaan Aaliyah fa ka tambaye Ni? Kaman ta na baka ita amana ce ,ko bayan Raina ? . Wani irin bugawa Ƙirjin sa Yayi ,yana Ɗago da Lulun idanun sa yana Sauke su a na Ammiee da itama shi take kallo . Ammiee wai Aaliyah bata anan tare dake?. Ya kuma tambayar Ammiee cikin Wani irin yanayi , Where is she Go? Ina ta tafi ne?. wani irin kallo Ammie ta yi masa kamin tace " Ban gane ba , ina Aaliyah take ? Ai na barku tare jiya? Me kayi mata?. Nothing Ammiee , ban mata komai ba . But I'm coming now. Yayi maganan tare da juyawa cikin Sauri yana ficewa daga Falon Ammiee tare da.........!



*Mamanteddy🧸*
*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*

Night update🥱

Nufar Farfajiyar Gidan kan sa tsaye , Don mun kuwa tabbas yasan Tun da Yau Aaliyah bata taho Part Ɗin sa ba to Bata yi kwanan gidan Moddibo's Family ba . Shi mutum ne marar Son damu da damuwa ,Wannan yasa Aydaaan Ɗaukar Moton sa yana dakatar da Drivern sa ,don a yanzu zaifi samun sukunin Ganin shi da kan sa yayi driving har ya isa Garin Yobe . To mu sai dai muce Allah ya kaisa Lafiya ".
**
Tun Safe Aaliyah ta fara Aikin ta ,tana kimtsa gidan tare da Ayyukan cikin gidan , Komai ganin sa take tamkar Sabon Rayuwa , musamman Yanda Inna Turai duk tayi nadama ,sai nan nan da ita take yi . Bayan sun kammala Karin kumallo , Nan Aaliyah ta Dauki Jug Ɗin Kunun gyaɗan da suka sha da sauran plastic Cups tana Ficewa zuwa Wajen Tsakar gidan dasu don ta Ɗauraye . Inna Turai ne ta fito tana kallon Aaliyah tare da cewa " Aaliyah wai bakya gajiya da Aiki ? Da kin huta tun sassafe kika fara Aikin har yanzu kusan ƙarfe Goma baki huta ba . Ɗago da Narkakkun idanun ta tayi ,wanda a kullum suke tamkar Ruwa ya kwanta a cikin su ... Murmushi tayi tana kallon Inna Turai kamin tace " a'a Ina , wannan ai ba wani Aiki bane ba. A'a Aaliyah da dai kin huta , don Allah idan kin gama Wannan aikin kibar Larai ta cigaba haka nan . To Inna Aaliyah tayi maganan kamin cikin Sauri don sai a yanzu ta ankare da babu Su Hajara a cikin gidan wato ƴaƴan Inna Turai da ta kawo su na gidan tsohon mijin ta ...Inna Wai Ni kuwa nace " Ina Su Hajara ne? Tun juya Bamu hadu ba ."

Dakatawa Inna Turai tayi daga Tafiyar da take yi ,kamin ta juyo tana kallon Aaliyah , Allah sarki Aaliyah kenan , Fara mai farar Aniya ,ina jin Dadin kasancewar ya ta a yanzu . Murmushi Aaliyah tayi tana cigaba da Ɗauraye Jug ɗin kamin tace " Inna Suna ina ?. Nisawa Inna Turai tayi tare da cewa " Sun koma gidan uban su , Ai a ganina ɗa zaifi Samun Tarbiyya a tsakanin mahaifin sa , Wannan yasani mai da su gidan mahaifin su ,saboda ina so naga Sun zama mai tarbiyya hankali kamar ke Aaliyah ". Tsayawa Aaliyah tayi tana kallon Inna Turai don sam hakan bai mata dadi ba . A'a haba Inna,don Allah su dawo ,wallahi Gidan naji babu daɗi yau dana ga ban gansu ba .


A'a Aaliyah ki kwantar da Hankalin ki , Su Hajara zasu zo su ganki ,amma fa ba zasu zauna ba , saboda kinji dalili na dana Faɗa miki a baya ,kiyi Hakuri kinji ?. Gyaɗa Kai Aaliyah tayi a sanyaya tare da cewa " To Inna Ki aika su zo yanzu . Murmushi Inna Turai tayi har tana Ɗan Darawa kamin tace " To Aaliyah Babu damuwa , Saura ma kwana nawa ne ki tafi Ɗakin mijin ki ai dole suzo kuga Juna . Inna Turai ta ƙare maganan tana nufar Ɗakin Dabbobin ta ,inda take kiwon Tumakai . Da ido Aaliyah ta bita kan ta na kullewa ,don ta kasa fahimtar inda Zancen Inna Turai ya dosa .

Bayan ta kammala Wanke wanken nata ne ta juya tare da Ɗaukar tsintsiya tana Fara Share Dattin Tsakar Gidan . Larai ne ta fito daga Ɗakin Aaliyah inda tayi mata Magaji da shi , tana Ɗaga Hannayen ta Sama tare da furta kalmar La'ilah ha'illallah kamin ta waiga tana hamma na tashin mutum daga Barci . Aaliyah Aiki kike yi haka? . Eh Inna Larai An tashi lafiya? . Murmushi Larai tayi tana washe baki tare da cewa " Lafiya kau Ɗiyar Albarka . Kin ma gama komai na Gidan ?. Eh Inna Larai , Kunun ki da komai na karin ki yana Ɗakin Inna na aje can , saboda kar na tashe ki yasa na kai miki can . Allahu Akbar , Aaliyah Aaliyah....Larai ta ambaci Sunan Aaliyah tana jin dadin Abubuwan da tayi , Gaskiya mijin ki ya dace . Humm To Barka da Fitowa Larai , yau Kinga an kammala Aiki shi yasa kike ta wannan zuban naki . Su kaji Muryar Inna Turai daga Bayan su . Dariya Larai tayi tana cewa " ai Gaskiya na ji dadi ,yanzu nayi na rana da dare ,da kuma Sauran Aikace aikace Gidan . mashaallhu haka ake So . Assalamu alaikum ". Suka ji bakuwar Muryar sa ,cikin dakiyar murya wanda daga ji kasan Arrogant ne , yayi Sallamar . Cikin Sauri duka suka juyo yayin da Inna Turai ke amsa masa Sallamar cike da Faɗaɗa Fara'ar ta . Larai kuwa Ƙasa tayi tana zubewa tare da gaishe da Aydaaan , wanda idanun sa ke cikin ɓakin Space . Ɗagowa Aaliyah tayi cike da mamakin ganin sa a wannan lokacin , hannun ta na rike da tsintsiyar yayin da zuciyar ta ke har ba mata da ƙarfi .


You?. Tayi maganan a sarari wanda a tunanin ta a zuciyar ta tayi shi . Yeah nine My wife Kinyi mamakin ganina ne? I just surprise you ... Tun da haka ake tafiya , Inna yana da kyau mata ta tafi unguwa ba tare da ta sanar mawa mijin ta ba?. Sakin baki Aaliyah tayi tana mamakin wannan salon shaharan nasa . Abun da ya kara bata mamaki bai wuce yanda Inna Turai tayi dariya ba tana cewa " Aydaaan shigo ciki ,yau bakin Safe muka yi ne?.


Tsayawa Aaliyah tayi tana kallon sa har ya shige Dakin Inna Turai , kansa tsaye ,alamun ya saba shigowa gidan ba bakon sa bane ba . shiru Aaliyah tayi tana kasa motsa ko dan yatsar ta ,kamin taji Muryar Larai tana cewa " Aaliyah muje ki gaida Sir Aydaaan . Wani iri kallo ta yi ma Larai ,hankalin Aaliyah duka ya gama tashi . Aje tsintsiyar tayi tare da shigewa Ɗakin ta ,inda Larai ta fito. Cike da Rashin fahimtar wani Abu Larai ta nufi Dakin Inna Turai don ta gaisar Da Yallaɓai Aydaan Moddibo .

Kusan mintuna Goma ya ɗauka suna dan taba fira da Inna Turai , Don shine me zancen yanda kasan bashine wannan miskilin mutumin ba ,kayi masa magana sai yafi minti biyar sannan ya baka amsa idan yaga dama kuma yaso ,idan bai so ba haka zai bar ka a

Please Login or Register in order to submit comment