Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 ♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔


ᗩՏᕼᗩᑎTY LOVE.


# WORK OF FICTION.
# ADVENTURE.
# DESTINY.
# ROMANCE.
# HEARTBREAK.
# HOT LOVE.
# MYSTREY.
# Royalty.



⚠︎: 𝑊𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑖𝑟𝑘𝑖𝑟𝑎𝑟𝑟𝑒𝑛 𝑙𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖 𝑛𝑒. 𝐵𝑎𝑛𝑦𝑖 𝑠ℎ𝑖 𝑑𝑎𝑛 𝑐𝑖𝑛 𝑧𝑎𝑟𝑎𝑓𝑖𝑛 𝑤𝑎𝑛𝑖 𝑘𝑜 𝑤𝑎𝑡𝑎 𝑏𝑎. 𝐷𝑢𝑘 𝑤𝑎𝑛𝑑𝑎 𝑦𝑎𝑔𝑎 𝑦𝑎 𝑔𝑖 𝑑𝑎𝑖-𝑑𝑎𝑖 𝑑𝑎 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎𝑟 𝑠𝑎 𝑎𝑟𝑎𝑠ℎ𝑖 𝑛𝑒.


________________❦︎_________________

𝐴𝑙ℎ𝑎𝑚𝑑𝑢𝑙𝑙𝑖𝑙𝑎ℎ ,𝑑𝑢𝑘𝑘𝑎𝑛 𝑦𝑎𝑏𝑜 𝑑𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑖𝑦𝑎 𝑠𝑢𝑛 𝑡𝑎𝑏𝑏𝑎 𝑔𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑘'𝑎𝑟𝑎𝑤𝑎 𝑚𝑎𝑛𝑧𝑜𝑛 𝑚𝑢 𝐴𝑛𝑛𝑎𝑏𝑖 Muhammad (𝑆.𝑊.𝐴)𝑑𝑎𝑗𝑎𝑟𝑎. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘'𝑎𝑟𝑏𝑖 𝑖𝑏𝑎𝑑𝑢𝑛 𝑚𝑢,𝑦𝑎𝑠𝑎 𝑚𝑢𝑛𝑎 𝑑𝑎𝑔𝑎 𝑐𝑖𝑘𝑖𝑛 𝑏𝑎𝑦𝑖𝑛 𝑠𝑎 𝑑𝑎 𝑠𝑢𝑘𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢 𝑟𝑎𝑏𝑜 𝑚𝑎𝑖 𝑔𝑖𝑟𝑚𝑎 𝑐𝑖𝑘𝑖𝑛 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑤𝑎𝑡𝑎 𝑚𝑎𝑖 𝐴𝑙𝑏𝑎𝑟𝑘𝑎. 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑚𝑎𝑖𝑚𝑎𝑖𝑡𝑎 𝑚𝑎𝑛𝑎.


❤︎ EID MUBARAK ❤︎







☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
1/5.




YEMEEN. NIGER


2005.



Bansan taya zan iya kwatanta muku yanayin rayuwar mu ba a wannan lokacin. Muna rayuwa ne can wani yanki dake cikin YEMEN Niger. Buzaye ne mu rayuwa muna yinta cikin kwanciyar hankali da Annushuwa. K'aramin kauye ne inda muke amma Allah ya hore mana jindaɗin rayuwa. Nasan zaku ce me ku ke dashi?. Yaruwa muna yinta cikin y'anci da kaunar junan mu. Kunsan mu buzaye yanda muke rayuwa. Bani da wasu shekaru a wannan lokacin dan shekarata 7. Zan sheda irin matsanancin kauna da iyayena da kuma mutanen kauyen mu kewa juna. D'an kowa na kowane. Muna da matsanancin had'in kai. Wannan kad'ai ya isa mu samu kwanciyar hankali. Duk inda aka ga wani abu dazai kawo mana cikas cikin kauye za'a had'u a tattauna dan samun masalah. Daga ni sai iyayena da nake matuƙar kauna. A duniya bani da wasu masoya daya wuce su. Na taso cikin gata, kauna da soyayya. Bamu da wani ilimi mai zurfi saboda yanayin rayuwar mu. Amma akwai tarbiya. Sannan duk alhamulis da juma'a har zuwa ranan lahadi mahaifina yana tara yara nan k'ofar gidanmu bakin bishiyar Mangoro da tun tasowa ta na tarar da ita. Zai ta bamu tatsuniyoyi da kuma labarai masu Jan hankali musamman na yankin kudu. Abbu na yana yawan cewa shi ba haifeffen d'an Yemen bane. Hasali ma shi dan gudun hijirane shida Innati sun baro k'asar su ta haihuwa ne saboda irin mulki na zalunci . Bansan kuma me yasa ba sam basa son fad'an wace k'asa ce asalin k'asarmu. Duk sanda na kawo zanchen sai su kauce baza su bani amsa ba. Innati tana yawan cewa

"Nadeeyah akwai wata k'asa da zakiyi alfahari da ita banda wannan da ki ka buɗe ido ki ka ganki a ciki?, wancan k'asar ba k'asa bace da za'ayi alfahari ko kwantace da ita , k'asar ki ita ce nan YEMEEN kar ki manta wannan"

Idan Abbu yana bamu labarin irin zaluncin da ake k'asar saboda mulki ba k'aramin tsoro abun yake bamu ba. A koda yaushe yana samana tsoron Allah da kuma gudun cin zarafin wani ko na misk'ala zarratan . Yakan ce duk abunda wani zaiyi muku dan zalinci ku barshi da Allah zai isar muku a duk inda kuke. Addu'a wadda aka zalunta karbabbiyace domin Allah baya yafe hakk'in wani kan wani sai in shi mutum yace ya yafe masa.



✿︎✿︎✿︎✿︎


Mummunan kaddarar da ban taɓa tunanin zata same ni cikin kuruciya ta ba ita ce ta same mu a daren yau. Hayaniya da kuma ihuce-ihuce mutanen rugar mu ta farkar dani daga barcin da nake mai nauyi jikin Innati. Cikin barci na farka ina kallon Abbu dake tsaye bak'in k'ofar d'akin mu yana k'ok'arin rufeta cikin firgici. Tunda na taso ba'a tab'a rufe k'ofar ba sai yau. Sai dai a saki asabari da zai rufe ko ina. Tunda na taso wannan al'ada ce da mutanen kauyen mu ke yi saboda halin rayuwa. Bamu da asibiti ko masallaci, ko makaranta. Dalilin da yasa bama rufe k'ofa dan wani zai iya neman taimako cikin gaggawa. Da y'ar muryar ta ta wanda ya tashi daga barci nake kallon Abbu dake tsaye jikin k'ofa cikin matsanancin tashin hankalin da ban taɓa ganin sa a ciki ba. Kallon Innati nayi data k'ara rungume ni tsam cikin k'irjin ta itama dai tashin hankalin ne kwance kan fuskarta kaman na Abbu.

"Abbu, Innati ihun mene haka naji mutane suna yi?"

Da sauri ya k'araso inda muke ya durkusa. Hannu ya tura cikin rawanin sa ya fito da wata sarka kaman ta zinare. D'aura min ita ya yi yana kallon Innati da naga hawaye masu zafi sun biyu kuncin ta. K'asan rigata ya tura sarkar sai kuma ya kunce gashin kaina da Innati ta nade min shi tsakiyar kaina kaman gammo. Shekara 5 nake amma za kayi mamakin yawan gashi na da kuma tsayin sa gashi baki sid'ik. Har wajen gwiwar kafata yake zuwa. Shi yasa duk bayan wata Innati ke rage min tsayin sa. Da ita da Abbu na rasa wana biyo gurin gashi. Danma Abbu bai cika buɗe fuska ba kullum nad'e yake da rawani ya rufe fuskarsa sai idonsa kawai ka ke gani. Idan kaga ya kwance rawanin to cikin d'aki yake daga shi sai ni da Innati idan kuwa ya kwance har kitso nake masa naita ja masa kai dan gashin sa har gadon baya yake kwanciya. To itama Innati haka. Abun tambayar shi ne meke faruwa ne? Wannan sarkar fa?. Goshi na ya sumbata idan sa tab cike da hawaye yace

"Nadeeyah duk wani bayani da zanyi miki yanzu baza ki fuskanta ba saboda k'arancin shekarunki, amma ina so ki riƙe wannan sarkar da kyau, duk runtsi karki yarda wannan sarkar. Babu wani lokaci da zan iya yi miki bayani da zaki fuskanta, amma kar ki manta a koda yaushe muna tare dake"

Shar naga hawaye sun biyu kuncinsa. Galala na tsaya ina kallon sa .sheshshek'ar kukan Innati ya d'auke min hankali na juya ina kallonta. Cikin rashin wayo da yarinta na rungume Innati na riƙo hannun Abbu shima na jawosa na rungume su kan kirjina. Hannun Innati ,Abbu ya kama yana mata murmushi. Ihuce-ihuce da guje-guje da nake ji na mutanen karkarar mu ya yi yawa ga sawon kaman dokuna . A hanzarce Abbu ya miƙe ya kama hannun Innati da nawa k'ofar da yake b'ulla tacan bayan Sahara ya buɗe. K'ofar kaman boyyayyir hanya ce da Abbu ke yawan bi idan yana san kad'ai cewa cikin sirri. Binsu kawai nake har yanzu na kasa fuskantar komai. Babu zato muka ji wata murya mai kaushi da cikin tsantsan larabci da ban iya shi sosai ba lokacin sai kuma k'arar dokuna a bayan mu.

Wani irin fisgata Abbu ya yi ya sab'a kan kafad'a ya riƙe hannun Innati muka hau gudu bana wasa ba.

Gudu muke mutanen suna biye damu har sun kusa kamomu. saboda nike fuskarta su ya bani damar ganin mutanen dake binmu kan dokuna sanye da kaya bak'ake sun rufe fuska da bakin abu. Kayan dake jikinsu kaman irin kayan nan na yaki irin wanda Abbu ke bamu labari. (Armour ). Wasu riƙe da takobi wasu kuma riƙe da mashi. Cikin wanda ke riƙe da mashin naga wani ya saita Abbu kafin nayi wani yunƙuri ya saki mashin ya tawo da mugun gudu .

Wani irin slow naga abun ya tawo na saki gigitacciyar k'ara ina kiran Abbu. Amma sai dai me Innati naga kawai ta fisge daga hannu Abbu ta tare mashin daya nufushi a guje ya huda saitin k'irji ta ya wuce. A take ta zube a k'asa tana tarin jini. Matsanancin kuka na fashe dashi ina kallon Innati dake kallon na ina sab'e kan k'afad'ar Abbu da murmushi kan leben ta dake motsi kaman mai magana.

Ganin da nayi Abbu kaman bazai tsaya ba sai sharara gudu yake ga Innati can kwance a k'asa cikin jini. Na fara buge -buge zan kwace ina kiran Innati cikin matsanancin kuka. Wani mashin suka k'ara harbowa Abbu ya yi maza ya kauce cikin zafin nama ya shige cikin ciyayi muka samu damar b'ace musu. Saida muka yi y'ar tafiya mai nisa mun shiga cikin dajin sosai babu alamun ana binmu sannan Abbu ya tsaya gindin wata katuwar bishiya.

Sauke ni ya yi yana haki ya jingina jikin bishiyar. Duk da cewar dare ne amma hasken farin wata ya haske sararin samaniya kana ganin komai tar. Sannan ina da wata baiwa koman duhun dare da nisan abu tar nake ganin sa kaman rana. Dalilin da yasa na iya hango mutanen da suka shigo cikin jejin da k'afafuwansu babu dokunan. Rigar Abbu na kama ina nuna masa da hannu. A firgice naga yana kallon inda na nuna masa d'an waige-waige ya yi ya jani da sauri ya tura tsakanin wasu ciyayi. Rawanin dake kansa ya cire ya nade fuskata dashi sai ido na kawai.

Ido na zuba masa ina kallon fuskar sa dake d'igar da hawaye da sai alokacin ma na lura dasu. Wani kuka ne ya k'ara zuwarmun mai k'arfi dan nasan kukan me Abbu yake. Sunan Innati na fara kira ina kuka sosai shima Abbu duk yanda yake daurewa kar ya yi kuka mai sauti kasa jurewa ya yi ya fashe da kuka mai k'arfi jikinsa na girgiza.

Durkusawa ya yi gabana yana sharemin hawaye murya a raunane yace

"Nadeeyah zanje na d'auko Innati kinji ko?, idan na tafi ki irga d'aya zuwa uku sai kibi nan "

Doguwar hanya ya nunamin mai tsayi daga can nesa kanajin k'arar teku.

"Kibi nan har sai kin bulle bakin gaba ki samu guri ki buya har sai na dawo da Innati kinji ko. Ki buya kar ki fito ko kinji motsi sai in na kira sunanki wanda ni kaɗai da Innatin ki muke kiran ki dashi. Gayamin sunan"

Murya na rawa nace "SULTANAAH" Murmushi Abbu ya yi ya kama fuskta yana kallona hawaye kwance kan kuncinsa

" kar ki manta har sai kinji wannan sunan zaki fito kinji SULTANAAH "

Shar hawaye suka k'ara wanke min fuska. Me yasa nake ji kaman sallama ce Abbu shima yakemin?. Goshina dake nade ya sumbata ya miƙe tsaye .

"Ina sanki SULTANAAH, INNATIN ki na sanki. A shirye muke mu bada rayuwar mu dan ceton ki. Muna tare dake a koda yaushe "

Saki na ya yi da sauri kafin nayi wani yunƙuri ya kwasa da gudu ya koma hanyar da muka biyo. Gursheken kuka nake ina k'ok'arin danne bakina. Saboda baiwar da nake da ita na samu ganin Abbu har ya b'ace daga ido na kafin ya fice daga dajin ya juyo yana kallon duhun sa bak'insa na motsi na karanta kalman da yake cewa.

"MY SULTANAAH"

Murmushi ya yi mai had'e da kuka ya juya da sauri ya fice ba tare da yaci karo da mutanen dake nemanmu ba. Kuka nake sosai na kasa motsawa daga inda nake har suka k'araso inda nake b'oye. Ido na runtse ina jin motsin su daf da inda nake .

Wai su waye wad'annan mutanen mai suke so?, mai muka yi musu da suka tarwatsa mana duk wani farin cikinmu cikin d'an k'ank'anin lokaci? . Ina jinsu suka gama zagaye- zagayen suka dumfaro inda nake boye bayan ciyayi. Numfashi na d'auke na k'ara damke ido na tsaya kam rungume da k'irjina dake bugawa. Muryar su naji a kaina da sauri na buɗe ido na na zaro su waje ina shirin kwasa da gudu.

Abun mamaki gasu dai a gaban nawa amma babu wani alamu da yake nuni da sun ganni. Ga d'aya kusa dani kaman zai tab'a ni. Baya naja da sauri ina kallon su dafe da kirji. Babu alun ya ganni ya juya da sauran mutanen sa suka koma inda suka fito. Me hakan ke nufi? Gani gasu amma basu ganni ba?.

Iska naji ta d'an kad'a mai sanyi har saida na k'ank'ame jiki. Wooshh naji iskar tabi bayan kunne na sai kuma naji kaman magana.

"SULTANAAH nan"

A firgice na juya bayana dan ganin wanda ya yi maganan. Wayan babu kowa. Matsanancin tsoro ya k'ara kamani. Iskar ta k'ara kad'awa wajen saitin kunnena na dama ta wuce Wosshh na k'ara jin wata maganan kaman daga cikin Iskar ma take fita.

"Nan SULTANAAH "

A guje na kwasa hanyar da Abbu ya nunamin yace nabi tun d'azu na kasa bi. Gudu nake ina kiran Abbu da Innati ban tsaya ba sai da na fara hango hasken ruwa da farin wata ya haske na k'ara kaimi dan sai nake ji kaman sawun mutum ne bayana idan na juya kuma bana ganin kowa.
Sai dana kai bakin tekun na samu guri na zauna ina maida numfashi. Waige-waige nake ta inda zan hango mab'oya amma babu sai cikin ciyayin dana fito. Sawun k'afafuwa da naji na mutane na yowa inda nake na miƙe a sukkuwanne da y'an kafuwana ina neman hanyar tsira sai gasu sun bullo. Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi ina kallon wasu daga cikin mutanen kauyen mu da yara dana shedasu a take. A guje na nufe su ina kira hakan yasa suka juyo kaina. Ido waje FAHIMA ta nufoni tana kira kaman yanda nake kiranta. Rungume juna kuma yi duk da k'arancin shekarun mu nida ita sai kayi mamaki irin matsanancin k'awance da muke.

Cikin kuka tace " sun kashe Mama da Baffa, sun kashe kowa. Su waye wad'annan mutanen?, me suke su a tare damu?"

Kuka muke sosai abun tausayi sauran yaran suka matso muka rungume juna. Mun jima a haka na d'ago don na k'irga mu nawane. Mu biyar ne yaran sai manya mace da namiji mutum biyu dana gane su. Babu zato mukaji k'arar dawakai. Gaba d'ayan mu yaran muka rude muka fashe da kuka a hanzarce Ma'auratan suka kamamu muka hau gudu bana wasa ba. Saidai duk wannan gudun da muke a banza dan saida wad'annan mutanen suka tadda mu. Zagaye mu suka yi da dawakai. Julde da matarsa Azima suka kamamu suka rungume dan bamu kariya. Hannun FAHIMA na riƙe muka cigaba da zubda hawaye don mun tabbatar muma mutuwar mu tazo kaman sauran mutanen mu. INNATI da ABBU na. Ko yana raye ko shina sun kasheshi?

Gaba d'ayansu suka sakko daga kan dokin suka kewaye mu. Magana suka fara tsakanin su cikin yaran da bama fuskanta sosai.(LARABCI)

Wanda nake tunanin shine ogan nasu ya matso sosai gabanmu yana kallon fuskarmu d'aya bayan daya. K'ara k'ank'ame juna mukayi hawaye na cigaba da ambaliya kan fuskarmu. Yana zuwa kaina naga ya zubamin idon duk na rude Azeema ta k'ara b'oyeni cikin k'irjin ta. Wajen sakan biyu yana kallona duk da fuskata a rufe take sai idona kawai da ake gani.sai kuma ya juya wajen y'an uwansa suka fara magana cikin harshen su.

"Ya zamuyi da wad'annan yaran ne?, banga alamun akwai yarinyar da aka ce mu kashe ba. Ina tunanin ya b'oye ta cikin dajin nan. "

Na kusa dashi ya yi saurin cewa " To su wad'annan d'in fa mu barsu kenan? Gwanda suma a kashe su kawai kaman sauran. Dama ai cewa aka yi kar mubar kowa da rai, babba ko yaro. Kaga muna da kaso mai tsoka musamman idan muka bada shedar nasarar kashe yarinyar da masu bata kariyar"

Jim ya yi yana juya maganan shi cikin ransa kafin yaja dogon numfashi ya fesar.

" yara ne wannan. Enough with the killings. Abunda za'ayi mu sasu jirgi sun zama bayi. Wannan ce shekarar da masarautar Egypt ke daukan bayi dan haka sai mu basu su a matsayin gudunmawa. Kasan irin tsanani na wannan masarauta idan aka shiga ba'a fita sai dai a fito da gawar ka. Hakan shi ne mafita kawai sai su k'are rayuwar su a can matsayin bayi"

Kai suka jinjina gaba d'aya amincewa da maganan sa. Juyowa suka yi kanmu muka k'ara had'a ido dashi sai kawai naji saukar duka tsakiyar kaina a take na zube k'asa kafin na rufe ido naga FAHIMA da sauran yaran uku ,Azima da julde suma sun zube k'asa a sume sakamakon dukan da suka yiwa kowa a kai. Idona na gab da rufewa naji an kira sunana cikin kunne kaman rad'a "SULTANAAH" bayan mutumin naso naga wasu irin kwayar ido masu hasken gaske ga alamun gashi mai tsawo baki sid'ik na kad'awa kaman iska. Runtse ido nayi na k'ara buɗewa don sai nake tunanin ko dukan da sukayi min ne yasa na fara ganin ba dai-dai ba. Har ila lokacin wannan kwayar idon dake lekowa ta bayan mutumin tana nan d'auke da gashin ido mai tsayin gaske. Sai kawai naga kaman mutanen sun zube k'asa suna kururuwa daga nan ban k'ara sanin komai ba ido na ya rufe ruff.























♔︎ ♔︎
𝕊𝕌𝕃𝕋𝔸ℕ𝔸𝔸ℍ
𝒕𝒉𝒆 𝒖𝒏𝒌𝒏𝒐𝒘𝒏 𝒑𝒓𝒊𝒏𝒄𝒆𝒔𝒔




ASHANTY LOVE.






☆𝐈'𝐌 𝐀 𝐒𝐓☆𝐑☆



Chapter
5/10.



❤︎ EID MUBARAK ❤︎




18YRS LATER.
EGYPT.





Bazan iya ce muku ga yanda aka yi muka tsinci kanmu cikin wannan k'asa ba k'ark'ashin wannan masarauta ta zalunci. Mun farka ne kawai mun ganmu anan kewaye da masu tsaro(Gaurds). Tunda muka shigo wannan masarauta aka rabamu kowa da b'angaren daya ke aiki. Tun ranan kuma ban k'ara saka Julde da Azima a ido na ba da sauran yaran da muke tare. Uwar d'akina da nake gurin ta Mama Maria ita ke cemin suna can wani b'angare cikin masarautar saboda girman ta da kuma rashin y'anci da bayi basu dashi basu isa su fita ba sai in aiken su aka yi. Yau tsawon shekara goma sha takwas ban taɓa fita daga masarautar nan ba bare nasan ya rayuwar waje take. Muna can b'angaren bayi dake k'arkashin k'asa. Bamu rasa ciba bare sutura don nikam Allah yaso ni da arziƙi uwar d'akina wato Mama MARIA ita keda ragamar girkin Sarki da sarauniya da y'ay'an su. Ita ke musu wanki da sauran wasu abubuwa daya dangance su.

Babban abun mamakin shine tun ranan da muka tsinci kanmu cikin wannan k'asar na daina wannan ganin da nake cikin duhu. Har zuwa yau kuma na kasa tantance abunda na gani ranan bakin teku kafin na suma. Shin idon da na gani da kuma sillin gashin da naga yana kad'awa cikin iska gaskiya ne ko kuma imagination d'ina ne?. To amma kiran da naji ana munfa da sunan da babu wanda ya san shi sai iyayena fa?. Allah ne kad'ai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment