Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITER'S FORUM

*SAFIYYA GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY.


SHAFI NA ƊAYA. 1


Tun daga nesa gabanta yake faduwa lokacin data doso hall din tana neman wurin da zata ajiye motar ta, ganin babu kowa a gaban hall din kamar yadda suka saba tsayawa kafin lecturer din ya iso su jira shi, wannan ya tabbatar mata da bazai barta ta shiga ba, hankalinta duk a tashe ta gyara mayafinta bayan ta tsaida motar ta dauki littafinta da karamar Jakarta sai wayarta a ta fito tareda danna lock din motar ta nufi hall din.

Ita kadai ce a wurin ko ina shuru sai muryarsa dake tashi daga cikin hall din da alama dictation yake musu gefen kofar ta samu wuri ta labe tana tunanin shiga dan bata sani ba ko zai barta ta shiga bata taba ganin ya kori kowa ba amma tana matukar tsoronsa, wayarta ta danna tareda kiran kawarta Nana Sule bata dauka ba ta sake lekawa sai suka hada ido dashi tayi saurin ja baya tana dafe kirjinta.

Duk abinnan datake idonsa yanakanta, yana lura da duk wani motsinta, yarasa dalilin dayasa ba dama ta ganshi gaba ɗaya saita firgice masa.
Lokacin daya shigo ajin saida duk ya karewa matan ajin kallo bai ganta ba ya fara tunanin yau bazata zo ba kenan dan bata saba yin latti ba sannan koda yaushe zai ganta a sit ɗin gaɓa sam bata wasa da karatun ta,tunda yaji tsayuwar mota hankalin sa ya lula cen har hakn ya kusa dasa tasirin abinda yake kallo daga ɗaliban dake sauraronsa, wayancewa ya yi ta hanyar ƙara haɗe ransa tare ɗauke dauke idonsa daga kofar dan ya san indai ya maida hankali bazata shigo ba sai dai ya lura da hakan da yayi ma bai sa ta cire tsoron ta shiga ba sai faman lekensa take yi,hakan kuwa ba ƙaramin tasiri yake a kansa ba dan gaba ɗaya ya kasa mayarda hankali akan abinda yake koyarwa,daga nesa da yake ya daga muryarsa tareda cewa "Aisha Nabila is either you come in or disappear from there you are distracting my class(Aisha Nabila kodai ki shigo kokuma ki ɓace daga nan saboda kina ɗaukar hankalin class ɗina)" zaro ido tayi tareda sake lekawa suka hada ido ya dauke nasa tareda ce wa cikin ɗaga murya "get lost if you are not ready(Ki ɓace mun dagani idan har baki shirya ba)" da sauri ta shigo tana jin yadda ido ke matukar yawo akanta tana tafiya kafafuwanta na hardewa, yabita da kallo tareda yin shuru yana mamakin yadda jikinta ke rawa haka, Jakarta da wayarta dake hannunta suka zube a kasa sakamakon tuntuben da tayi yaja dogon tsaki tareda maida hankalin sa ga littafin dake gaban sa.

Saurin kallonsa tayi daga saman stage dinda yake taga ba ita yake kallo ba ta tarkata Jakarta tareda samun kujera daga gaba ta zauna.

Bayan ya gama lectures dinsa ya tarkata yanashi ya fita yana fita ta sauke ajiyar zuciya tareda juyawa bayanta ta kalli Nana sule tana cewa "Banza bazaki kirani ba kinga ya shigo" Nana data taso tazo kusa da ita tana cewa "nima fa yau ina shigowa yana shigowa shiyasa ban kira ba kinsan yadda yake hade rai bazaka ga fuskar yin dogon motsi bama" tsaki tayi ta ce "bar banza gashi ba abinda ya iya se note ni banma san ya akayi yakai matsayin Dr ba" Dariya Nana tayi tana cewa to nidai tashi mu tafi bacci nakeji wallahi" mikewa tai tana cewa "muje amma sena siya abu a refreshment centre din can dan tsabar sauri ba abinda naci yau" fitowa sukayi suna tafe suna surutu irin na kawaye tareda gaisawa da sauran yan ajinsu suka nufi shagon meat pie ta siya guda bakwai tareda sprite babbar roba tayi sanyi sai tsiyayar ruwan raba take, suna tafiya Nana Sule ta ce "ke wai har yanzu baki rage ci ba" ta buntsire bakintana cewa "ai wannan dan tabawa ne zanyi ina gaya miki ga dumamen tuwo can na baro ayimin ina komawa zan bashi mamak..." wani irin dauke numfashi tayi sakamakon karon da suka ci da Dr zaki, shikanshi ta bashi tsoro ganin yadda tayi amma sai ya raba gefensu ya wuce batare daya nuna yama kula da hakan ba, muryarta tana rawa ta furta, "Am so sorry sir" ko waigowa baiyi ba bare ta saka ran zai kula ta. Nana Sule ta dungure mata kai tana cewa "ke dan ubanki ajalinki kika gani"? Bata ce komai ba ta sake rike ledar dake hannunta tayi gaba da sauri tana tuno yadda suka hada ido tana cewa zata bawa tuwo mamaki, sai da ta zauna a mota ta dauki meat pie guda daya ta Gutsira tareda lumshe ido tana cewa "akwai abinda yafi abinci dadi a duniya"? Nana ta harareta ta ce "Akwai wallahi" ta girgiza kai tanancewa "karya kikeyi babu shi, duk me zakimin duniya ki burgeni befi kiyimin abinci kala-kala ba masu dadi" Nana tace akwai shi fa sai dai dan baki sanshi ba ne amma ki bari idan lokaci yayi zan fada miki akwai abinda yafi abinci dadi, ko hadi babu yarinya" shuru tayi mata lokacin da take reverse saida ta hau babban titi ta ce "ina so insamu waje daya mai inuwa inringa ajiye motar nan kinji yadda ta dau zafi" Wayar Nana Sule tayi ringing ta bude Jakarta tareda daukowa murmushi tayi tace "kiyimin shuru na gasken ya kira" dariya tayi kawai, baka ce ba sosai ba amma dai baka ce siririya gaba daya batada jiki irin wanda kallo daya zakaga mace cikakkiya mai daukar hankali sai dai tanada kyau da gashi sannan kuma tana da tsayi daidai misali wannan dalilin ya saka batada kayan da suka wuce doguwar riga, sam bata shaawar dinka riga da skirt duka kayanta doguwar riga ce.

Dr zaki Rike da robar ruwan faro ya fito daga shagon yayi saurin dauke idonsa daga kallonta, baisan wane department take ba amma kullum sai ya ganta a lokuta mabambanta, shigarta tana kona masa rai saboda irin tsarin halittar ta ta kasance mai daukar hankali gata fara tas mai kyau kamar balarabiya, wannan karon riga da skirt ne ajikinta na atamfa sun kamata ta sosai sai wani munafikin mayafi sannan ta bude rabin gashinta duk a waje tana tafiya da earphone a kunnenta, samun kansa yayi da juyawa yabi ta parking space a tsakiyar motoci ya haura sama ta baya ya shiga office dinsa dayayi matukar tsaruwa, zama yayi kan doguwar kujera ya janyo table dinda ke gabansa tareda dora ledar takeaway dinda ya aika aka kawo masa ya bude tareda karewa abincin ciki kallo yayi murmushi mai ciwo saboda Sam baya kaunar abincin siyarwa, gashi shi mutum ne mai son yaci abincin daya yarda dashi amma ya kasa samun wannan damar saboda wani dalili.




Baki ne shima saidai ba sosai ba lip dinshi na kasa pink na sama brown yanada manyan ido da madaidaicin hanci dogo ne sedai yanada jiki baya tara sugar kai amma yana tara saje da gemu wayanda yake kashe lokaci wajen gyaransu suna kuma kawata faffadar fuskarshi da kara masa kwarjini, ya kasance mutum mai son manyan kaya irin na aladarshi ta hausa.

Yana kokarin kai spoon bakinshi aka kwankwasa kofar ajiye spoon din yayi ya kurawa kofar ido....

Fiyyah.


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM

*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA BIYU




Mikewa yayi tsaye tare da gyara rigar shi sannan ya nufi kofar ya bude, daga kasa ya dauki kallonta har sama ya sake dawowa da idonsa kasa yai mata irin kallon nan na rainin wayo fuskarsa babu alamar fara'a ya hade girar sama data kasa muryarsa a hankali amma acikin tsawa ya ce "menene"?.

Tunda ya bude kofar taga irin kallon da yake mata tasha jinin jikinta tareda diriricewa bayan ya tambayeta ta soma kame-kame tana cewa "oppis din malam Umar nake nema lakcara ne" kallon kofarsa yayi ya kalleta amma sai yaga taci gaba da tsayiwa shikuma sunan dake jikin kofar yake nuna mata amma bata fahimta ya dan ja baya ya ce "wane department" tana sosa wuya ta ce "political adminisitirashon" ya yamutsa tareda cewa "ke get out" ya rufe kofar shi tareda komawa ya zauna yana cewa "wasu ma samun admission dinsu a jami'a kawai sa'a ce ayita yayibo mana jidali" zama yayi tareda daukar abincin ya soma ci bayan yayi bisimillah.

Nana sule ta fara saukewa gida sannan ita ta wuce, tana shiga gidan ta hadu da babban yayansu mayafinta ta gyara tareda gaida shi tana washe masa hakora yana amsawa ya karbi ledar da take mika masa meatpie ne aciki ya dauki guda daya yana cewa "Acici mala'ikun tauna, har yanzu dai sai abinda yayi gaba ko" tayi murmushi tana cewa "yaya nafa rage tunda kace kar inrasa miji" dariya yayi yana mika mata kudin daya ciro daga aljihun sa ya ce "to Nabila ai ko yanzu gashi kinki ki kawo mana mijin" ta langabar dakai gefe tana cewa "Nagode babban yaya Allah ya kara budi na alkhairi mijina yana nan zuwa insha Allahu" ya juya yana cewa "to muna zuba ido" ya fita daga gidan ita kuma ta karasa ciki Mama ta samu da kaninta a zaune wanda shine Auta sunansa Haliru suna kiranshi da Baffa saboda sunan yayan mama ne ta zauna gefensa tana shafa kansa tareda cewa "Kunnaizy ya akayi ne" mama takai mata duka tana cewa "tashi daga kusa dashi daga zuwa zaki sashi a gaba kina gani kuma beda lafiya" turo baki tayi tana cewa "kato dashi kin wani sashi a gaba" wayarta tayi kara tanajin mama tana cewa "kece dai katuwa shekarunki yaci ace kina dakin miji amma kinki fito da mijin" hankalinta yana kan wayar dake ringing Nana sule ce ta daga tana cewa "daga ajiye ki gida kuma sai kira" Nana tayi tsaki tana cewa "kije dai ki duba result dinki na pol 2204 ya fito" ta dafe kirjinta tana tuno test dinda sukayi ma 15 taci saurin kashe wayar tayi tana kokarin shiga account dinta amma sai taga ba a saka mata result din ba, da farko tayi zaton karya Nana Sule take mata saida ta shiga group din makarantar taga ana ta complain akan irin grade dinda ya bayar wasu suce E wasu D wasu ma F duk sai ta rasa nutsuwarta, washe gari sunada lecture 10am:12pm sai ta shiga da nufin idan sun fito lecture zata je ta samu lecturer din ta masa complain, sha daya da minti arbain suka fito dan haka sai ta nufi office dinshi bayan sunyi sallama da Nana Sule ita ko mijinta jiranta ma yayi zasu je kebbi zai kaita sai Sunday zata dawo.

Ta dade bakin kofar kafin tayi jahadi ta kwankwasa kofar ta dan saurara tajiyo shi yana cewa "yes, come in" a hankali ta tura kofar tareda sallama shiga tayi ta maida kofar ta rufe sannan ta gaida shi ya amsa ya kura mata ido tareda dage mata Girarshi "sir I haven't seen my result" ya janyo wata takarda ya ce "which level"? A sanyaye ta ce "200 level" ya girgiza kai ya sake tambayarta "from which department"? Ajiyar zuciya ta sauke ta bashi amsa "Sociology" ya yamutsa fuska "ya sunanki" ta ce "Aisha Nabila Abdullahi" yayi shuru yana dube-dube can ya dago ya kalleta tareda cewa "D kika samu amma bakya karatu ko"? tayi shuru tana kallon kasa ya sake cewa "baki karatu a course mai 3 unit kin kwaso D xaki lalata GP dinki, next time ki gyara, kije wajen Exam officer na department ki rubuta application ki bashi" ta dan durkusa tareda yi masa godiya sannan ta wuce yabi ta da kallo shi dai tana burge shi mantawa yayi gaba daya da grade A zai bata.

Direct can ta wuce wajen Exam officer din kwankwasa kofar tayi yana ciki sai yayi gyaran murya, bude kofar tayi ta shiga sai ta sameshi akan sallaya yana addu'a tsayawa tayi daga gefe har ya kammala ya juyo yana kallonta gaidashi tayi ya amsa kafin ya koma kan kujera yana tambayar ta abinda ya kawo ta, ta fada masa "kiyi logging into your account now and see the course code you registered is pol 2204 or 204, amma pls do that outside" kamar ta harare shi dan ya bata haushi sai ta fita ta duba ta dawo ta fada masa yace taje ta rubuta application ta kaiwa exam officer na department dinsu, nan ma godiya tayi ta fito da sauri ta koma ta bude mota ta dauki shawarma data siya jiya da dare tasa a fridge ta dauko ta cinye daya sannan ta rubuta application din sannan ta nufi office din gabanta yana faduwa.

Ta dan jima a gaban office din tana tunanin ya zata kwankwasa kofar, sai da tayi jahadi sannan ta daga hannu zata kwankwasa aka bude kofar..... 


*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 

*SAFIYYAH GALADANCHI*

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA UKU




ja da baya tayi tana kallon kasa shiko ya fito da niyyar shiga office din head of department "Nana Aisha lafiya"? Ya tambayeta, dan dagowa tayi ta kalleshi shi tare da cewa "gyara za'a yimin na wani course code danayi mistake" karasa fitowa yayi daga office din sannan ya ce "kije ki rubuta Application ki kawo cewa you registered the old course code kina so a canza miki zuwa new course code" sai ta mika masa paper tana cewa "gashi nayi" ya kalli paper din tareda juyawa jikin kofar yasa key ya rufe office dinshi ya ce "wait, I'll be back in few minutes" binsa tayi da kallo dan tafiya yake lokacin da yake yi mata maganar, zuwa tayi ta jingina bayanta da bango, mutane kalilan ke dan wucewa tana binsu da kallo wasu su gaisa wasu kuma bata ma taba ganinsu ba sai ranar sai lecturers dake kaiwa da kawowa wayanda keda office a wajen, har wani lecturer daya Santa class dinshi ya tambayeta ko ta kwankwasa kofar yana ciki ta ce "na ganshi cewa yayi injira shi zai dawo" ya gyada kanshi yana bude office dinshi ya shige.
Tsayuwar ta soma gundurarta dan takai minti arba'in tana jiranshi kafin daga baya ta kama hanya ta wuce ranta a bace sai jera masa zagi take a zuciyarta, har ta tada mota zata wuce wata zuciyar ta hane ta tafa san halin lecturers kar ta dawo ya wulakanta ta, ruwa ta siya kawai ta sha sannan ta ja yan kafafuwanta ta koma, kwankwasa kofar tayi taji ko ya dawo sai taji bai amsa ba tsaki tayi ta rankwashi kofar sannan ta dora hannunta kan handle din zata juya kawai sai jintayi kofar ta bude sun tafi tare saboda nauyinta data sakewa kofar, shiko yana tsaye rike da waya ya dago yana tunanin wanda ya daki kofarsa haka sai gata kamar an jehota tana shirin faduwa, a tsorace ta dago tana kallonshi, shima ita yake kallo yana kokarin danne dariyar da ke son zubar masa da aji, samun kansa yayi da juyawa ya nufi kujerar teburinsa ya zauna yana murmushi, ganin kamar zata kalleshi ya saka shi hade rai tareda yi mata magana a tsawace ya ce "ke come in mana" ta shigo tareda tsayawa gefe ya sake cewa "Nan" sai duk ta daburce seda takai kusa dashi ta tsaya, da hannu ya nunata yace "dan matsa baya" ta matsa jikinta sai rawa yake a boye, wallahi tsoron idonsa take, admission number dinta ya karba sannan ya karbi paper data rubuta application yayi stamping ya ajiye gefe sannan ya kalleta bayan mintuna biyar, "Nana Aisha Nabila go an check you portal" dan rusunawa tayi tareda yi masa godiya sanann ta fita, yabi bayanta da kallo yana mamakin wannan sirantaka haka gata ita kullum cikin dogayen riguna, yana son ganin yadda kasan nan nata yake.
Bayan ta koma gida ta samu iyayenta zaune da yayarsu mace da alama magana mai muhimmanci sukeyi, ta gaida su tareda zama Baba ya ce "Nabila ya karatu"? Tana murmushi ta ce "Alhmdllh Abba, yanzu ma na dawo ne wani gyara ne dakyar na samu aka yimin" yayi murmushi yana cewa "to Allah yasa aci amfanin karatun, ya maganar miji kuma munjiki shuru" ta sosa kai tana murmushi tare da fadin "Baba ai kasan da Mubarak ko"? Ya girgiza kai tareda cewa "Kayya Nabila! akan ki kawai na soma yin wannan uzurin saboda kece karama, amma Nabila kinsan Mubarak bada gaske yake yi ba, wanda kawai zai je Uganda yin masters ya turo iyayensa asan da zamansa yaki wai sai ya dawo, idan da wani kike kiyi nazari ko kuma nayi yadda naga dama dake daga yau dai na rufe babin Mubarak" shuru tayi kamar bazata ce komai ba sai kuma ta ce "Baba kayi hakuri" gyada kai kawai yayi sannan ya kalli Mama ya ce "shekarar ta nawa yanzu"? Mama ta kalleta tareda cewa "wata mai fita jibi zata cika ashirin da hudu dan ga Baffa nan shekara shidda ta bashi yanzu ya shiga sha takwas" Jakarta ta dauka jiki sanyaye ta shiga dakinta, zama tayi kan gado tana ta nazari, to ita yanzu inba Mubarak din bama ko saurayi batada wallahi data gabatar dashi ko Baba zai daina takura mata haka.
A haka dai ta samu semester tayi nisa sosai har an fara test yau ne kuma zasuyi wata test ta Dr A.S. Zaki gashi ta tashi da zazzabi yau hakanan ta lallaba ta zo saboda haka ma bata dau mota ba ta hau napep sannan ta shiga bus, tunda ta shiga a kwance take rike da paper da biro Nana sule na can daga gefe tana kallonta dan tayita kiranta a waya bata daukaba yanzu kuma taga ta shigo bata nemeta ba sai taji haushin hakan dan haka ta kudurta a ranta daga ta gama bazata nemeta na itama gida zata wuce dama mijinta na jiranta ya wuce da ita gida.
Nabila kuwa akwancen da take nazarin rashin ganin Nana sule takeyi dan so take su sauketa gida tunda bata zo da mota ba.
Daddaya ya waresu kafin ya bayarda question, yana lura da yadda take ta bin kujera tana kwanciya har aka kusa minti talatin sannan yazo kanta ya tsaya yana kallonta, rubutu takeyi a hankali amma sai yaga kamar jikinta yana rawa, yadan bubbuga teburinda kanta yake kai ta dan dago katan ta kalleshi sai kuma tayi sauri ta tashi zaune tana goge idonta, "Bakida lafiya ne"? Ta gyada masa kai alamar Eh, paper ta ya karba ya duba dayake question biyu ne ba masu wahala ba yaga dai tayi daya na biyun kuma ko rabi batayi ba, ya durkusa gefenta tare da cewa "Zaki iya ko zaki wuce gida" a hankali ta ce "zan iya" ya mika mata paper din ya ce "to kiyi sauri se ki wuce" sannan yayi gaba, tunda ya barta ta sake kwantawa sai da ya sake dawowa yaja takardar ya ce "kiwuce kawai" a hankali ta tashi tsaye taga an ragu sosai ta soma tafiya dakyar takai wajen kujera ta zauna tana jiran tava napep ta wurga ta shiga ya sauketa bus stop, har yayi gaba daya zo wucewa ya ganta ta rufe idonta kawai ya juya inda take ajiye motar ta yaga bata nan sai ya wuce kawai office dinsa ya shiga ya ajiye test dinsu da sauran tarkacen dake hannunsa, hakanan yaji bazai iya barinta taje gida ba ita kadai, sauri yayi ya dawo ya sameta a inda ya barta, parking space yaje ya dauko motarshi yazo kusa da ita ya tsaya "Nabila" ya kira sunanta, ta amsa tana dago kanta fuskarta duk hawaye "Tashi in kaiki gida" bata yi musu ba ta mike dakyar tana Jan kafa ta nufi motar, shi kuma ya daure fuska ganin yadda aka bisu da kallo yasan student da shegen tsegumi, ya riga ta isa ya bude mata kofar ta shiga tareda dora kanta bayan kujerar ta jingina, shiga yayi shima ya tada motar tareda hawa titi yana tafiya a hankali.
Saida suka fita Gari sannan ya kalleta ya ce "ina ne unguwarku"? Ta fada masa tareda dan yi masa kwatance da irin muryar da take nuna duk abinda yake damunta yana matukar takura mata, tausayinta yaji sai ya tsaya wani bakery ya siya mata meatpie guda uku da yoghurt roba daya sannan ya nufi kwatancen da tayi masa suna shiga kwanar tace "ga gida nan" wuri ya samu ya ajiye motar ya fito da ledar hannunsa yana mika mata aka bude gate din gidan wata mota ta fito zubawa motar ido sukayi ita ta danji tsoron karbar abinda yake bata sanann kuma ga mahaifinta ya gansu....



*Dr A.S. Zaki*

EXQUISITE WRITERS FORUM 
SAFIYYAH GALADANCHI

_sadaukarwa ga yayata Billy galadanchi_

SHORT STORY 

SHAFI NA HUDU




Ganin dattijo da kamar da yake yi da Nana Aisha yasaka Dr fahimtar mahaifinta ne, Baba kuwa ganinsu a tare ya saka shi tsayawa, yana zuwa ya mikawa baba hannu sukayi musabaha tareda durkusawa ya gaidashi Baba ya fadada murmushinsa tareda amsawa ya kura masa ido yana neman karin bayani, Dr ya dan durkusar dakai sannan ya ce "Dama daga makaranta take batada lafiya shiyasa na dawo da ita gida" Baba ya gyada kai tareda cewa "Eh tabbas batada lafiya da zazzabi ta kwana ma, amma bansanka ba" baba ya fada yana sake duban Dr, shikuma dan kasa dakai ya sake yi ya ce "Eh baba, sunana Abubakar, idan babu damuwa Baba anjima idan ka dawo sai in shigo muyi magana" Baba yaji dadi sosai har ya sake mika masa hannu yana cewa "karfe hudu ina gida insha Allahu" Dr A.S yayi masa godiya tareda kama hanya ya shiga motar shi, nan

Please Login or Register in order to submit comment