Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addabarta a rayuwa,
idan ta tuno rashin lafiyar abida sai taji
jikinta yayi sanyi lakwas. Koda yaushe sai ta
saka lambar dr shuraim a gaba tayi ta kallo,
sai taji kamar ta kira shi ko ta tura masa
sako, sai kuma ta fasa. Amma ranar juma'a
ta tura masa sakon adduoin juma'a amma
bai bata amsa ba. Ta fara shiga damuwa,
amma sai tayi masa uzuri , watakila bai cika
karanta sakonni ba kasancewar aiki yayi
masa yawa. Ranar litinin da misalin karfe
goma da rabi na safe aisha farida na
kwance akan tabarmarta tayi shiru tana
tunani, rashin lafiyra abida tana damunta
matuka, musamman yanzu da tayi waya
shagamu tayi tayi su ba wa abida waya suyi
magana, aka ce bacci take yi. Sai take ganin
kamar jikin ne yayi tsanani suke boye mata.
Tana so ta tashi ta dora abincin rana, domin
yara sun kusa dawowa daga makaranta,
amma ta kasa tashi saboda damuwar da
tayi mata yawa a zuciya. Wayarta tayi ruru
tayi sauri ta dauka ta duba, sunan yaya
hussaini ta gani, sai tayi matukar mmaamki
da ganin kiransa, don bai dade da fita aiki
ba ya bata kudin cefane. To me yasa ya
kira? Ko mantuwa yayi ne a gidan? Take
tambayar kanta da kanta. Tayi sauri ta
dannan gami dayi masa sallama cike da
tsananin fargaba, tayi shiru tana sauraron
abin da zai fada mata. Yayi gyaran murya
yace yaya kuke? Gidan duk lafiya? Yara basu
dawo daga makaranta ba ko? Sai tace eh
basu dawo ba. Ina gida kowa lafiya kalau.
Yace to madallah, daman na kira ne naji
halin da kuke ciki. Kada ki damu, ki cigaba
da hakuri, kici gaba da kula da yara. Muyi
wa abida addua, naga kin damu duk kin
rame, kina yawan koke koke. Nima na
damu har bana iya aiki yadda ya kamata,
har 'yan ofis dinmu sun gane ina cikin
damuwa. Yanzu na yanke shawara a raina
idan yara suka yi hutu sai nima na dauki
hutu mu tattara mu kaura shagamu. Idan
hutuna ya kare sai na dawo, idan kuma na
samu aikin yi a shagamu ko wata sana'a sai
muyi zamanmu ba sai mun dawo kano ba.
Rashin abida a kano ya zama tamkar tuwo
gaya babu miya. Ni, ke da yara duk bamu
jin dadin rayuwarmu. Ko abinci kika dafa
babu wanda yake iya ci yadda kika kawo
min haka kike zuwa ki dauke, haka na lura
yara ma ba sa iya ci, kema haka. Tulin
abinci ake juyewa almajirai kullum. Aisha
farida ta rushe da kuka, yayin da shima
kukan ya turnuke shi, sai yayi sauri ya katse
waya. Ta kifa kai akan filo tayi ta rusa kuka
tamkar idonta zai fashe. Tana ta addua
Allah Ya yayewa abida wannan ciwon.
Wayarta ce ta sake yin kara. Nan da nan ta
katse kukan ta dauka ta duba sunan barr
muazzam ne. Ta goge hawaye da sauri ta
tashi zaune, sannan ta matsa waya da yin
sallama. Barr muazzam yayi murmushi yace
kanwata kwana biyu, kina nan kuwa? Tayi
murmushi tace ina nan yayana, na sha
kiranka baka amsawa, ko aiki ne yayi maka
yawa? Yace kwarai kuwa, satittikan nan uku
duk bana zama, daga bakwai na safe zuwa
na dare. Alhmdlh abin da ake nema ya
samu. Daman case din dr janan ne an tafka
sharia na shawo kanta, ta bude baki tayi
bayani, ta tonawa su izzuddin asiri, ta kuma
fadi inda za a iya samunsa shi da abokansa.
Aka yiwa 'yan sandan can garin waya don su
kamo shi. Sun kawo mana shi kano, har ya
bayyana a kotu, kuma ya amsa laifinsa.
Yanzu haka kotu ta wanke janan, an
tabbatar ba ta da laifi, an sake ta tana
gidansu shi kuma yana daure. Farin ciki ya
lullube aisha farida, tayi dariya tace
alhmdlh, Allah Mai iko, amma yaya
muazzam na taya ka murna, Allah ya kiyaye
gaba. Yanzu a wanne hali kuke ciki kai da
ita? Yayi murmushi ya lumshe ido yace
komai ya daidaita amma dai ba dukka ba,
kinsan komai sai a hankali. Kanwata na riki
abubuwan nan guda uku, nayi addua, nayi
hakuri matukar hakuri kuma naci riba. Naja
mata aji, na nuna mata yanzu babu zancen
soyayya a tsakanin mu, ina da wacce zan
aura. Na nuna mata bani da wata alaka da
ita face ta aiki. Ta bani hadin kai kawai in
gudanar da aikina yadda ya kamata. Data
tabbatar da haka, sai ta saduda ta ajiye
wannan zaren da take ja na aji ta bude baki
ta amsa duk abubuwan da na tambaye ta,
sannan ta gudanar da duk abin da na
umurce ta tayi a kotu.
Na lura ashe daman tana sona, boyewa
kawai takeyi, ko kuma nace yanzu ta fara
sona da taga halaka. Ni daman bani da
matsala da iyayenta, tun da can suna sona
balle da suka ga irin taimakon da nayi
musu. Ji suke tamkar su dauko ta su kawo
min ita gidana. Ba soyayyar iyayenta nake
nema ba, ina so janan ta soni da kanta ba
sai wani ya tilasta mata ba, ko don wani
dalili ba. Ta soni don Allah, muyi zaman so
da yadda a tsakanin mu, ko babu ran
mahaifanta. Aisha farida tace gaskiya ne
wannan. Allah Ubangiji Ya tabbatar da
alkhairi. Yace amin malamata, menene
mataki na hudu da zan taka, kin san fa duk
abin da kika ce dashi nake amfani, don kin
fini wayo ke kuma anti abida ta fiki wayo.
Ku dora min karatun. Aisha farida ta
kyalkyale da dariya, tace uhmm yayana
kenan, har ka bani dariya wallahi. To mataki
na hudu da abida ta fada min shine tunda
yanzu ta san da kai, ta kuma san abinda ake
ciki, sai ka zama mai yawan kyautata mata,
da haka zata so ka fiye da kowa. Barr
muazzam yayi murmushi yace idan haka ne
to ai na riga na haye mataki na hudu don ni
mai yawan kyautata mata ne, har ita da
kanta ta rubuto min sakon godiya a waya,
ta yaba da hakan. Dazun nan ta rubuto min
wannan sakon. Mene mataki na biyar
kuma, ko baka taka shi ba? Aisha farida
tace eh to inaga nima a mataki na hudun
nake amma abida ta fada min mataki na
biyar din tace ka nuna kama sonta tamkar
kafi kowa sonta a duniya. Kamar kulawa da
duk halin da take ciki, da kuma tattalinta,
tamkar kwai, ka nuna ko kuda ba kaso ya
taba ta. Idan ka yi mata haka ita ma zata so
ka, zatayi kokarin ta mallake ka a
rayuwarta, kaga sai ka aure ta.
Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace kice
min gangaro na kusa samun janan kenan?
Zanje na dorawa baraka wannan karatun.
Aisha farida tace af! Na manta ban
tambaye ka baraka ba, ina take? Wanne hali
take ciki? Yayi dariya yace mutuminki
nurudden dai ya saduda daya ga ta share
shi, sai yake shishige mata, ita kuma tana
watsar dashi. Yanzu haka ya fara neman
shawarata wai yana ga zai rabu da nafisa.
Yace min baraka tace ta amince ta auro
nafisa ya hada su, su biyu. Ita kuma nafisa
tace sai ya saki baraka kafin ta aure shi.
Shine yake cemin da ya saki baraka gara ya
fasa auren, domin baraka ce mace ta gari
da take yi masa biyayya. Aisha farida tace
yawwa ka cewa baraka ta taka mataki na
hudu shine taci gaba da kyautata masa fiye
da na da. Sannan mataki na biyar ta nuna
masa tsantsar soyayya kamar tafi kowa
sonsa a duniya fiye da yadda nafisa ke
sonsa. Brr muazzam yace lallai ke malama
ce, ke kuma yaya naki gogan, me kuke ciki?
Tayi murmushi ta lumshe ido tace alhmdl.
Dr shuraim yasan dani yanzu, ya san
sunana, har ya damu da halin da nake ciki.
Ta kai ta kawo dr shuraim ya nemo lambar
wayata ya kira ni a waya ya gaishe ni ya
tambayi jikin antina abida. Ina ga yanzu zan
taka mataki na hudu, zan cigaba da
kyautata masa sosai har sai ya kaunace ni
yaji sona tamkar ransa zai fita, sai ya saki
jiki dani, don bana tantama ya fara sona.
Sai in taka mataki na biyar shine ina nuna
masa tsantsar kauna nima. Barr muazzam
yace amma abu yayi kyau, Allah ya tabbatar
da alkhairi, Ya zaba mana abin da yafi
alkhairi a rayuwarmu. Har yanzu jikin anti
abidar ne bataji sauki ba? Aisha farida ta
marairaice tace ba za'a ce babu sauki ba,
amma har yanzu ana nan ana fama. Babbar
matsalar ma da 'yan uwanta suka zo suka
dauke ta shine dr shuraim din yake fada
min kada su jifga mata sassake sassake ya
jawo mata ciown koda, domin ciwon yana
da alaka da ciwon koda. Barr ya girgiza kay
tace subhanallah! Allah Ya kiyaye, Allah Ya
bata lafiya. Kiyi kokari ki kira su a waya ki
fada musu abinda likita ya fada, kada su
bata sassake. Yanzu zan turo miki katin
waya don kiyi magana dasu yadda ya
kamata. Aisha faida ta matse hawaye tace
nagode da wannan hidima da kake yi min
ko wani dan uwan nawa na jini ba yayi min
abin da kake yi min.....sai ta rushe da
kuka. Ya girgiza kai yace dadina dake saurin
kuka kamar wata tsohuwa. Ki daina kuka
kinji ko? Duk abin da ya samu bawa
Ubangiji Yana sane, kuma Zai yaye masa.
Sai kinga sakona sai anjima. Aisha farida
tace sai anjima, Allah Ya saka da alkhairi.
Ya kashe waya ba dadewa taji kara a
wayarta, da alama sako ne ya shigo. Tayi
sauri ta duba sai taga brr ne ya turo mata
da kati. Data loda sai taga na 1500 ne. Ta
kira shi har ta katse bai dauka ba, sai ya
kirata daga baya. Tace dama godiya zanyi
maka, naga kati na gode. Yace ba damuwa
ba sai kin yi min godiya ba, don nabaki
wannan dan kati. Ya kashe wayar ta koma
ta kwanta ta dubo lambar dr shuraim tayi ta
kallo tana shawara a ranta ta kira shi ko
kada ta kira shi? Sai ta yanke shwarar ta
kyale don ta lura baya son damu, idan ya
kira da kansa zaifi kamar yadda rannan yaga
dama ya kira da kansa. Sai ta jiye wayar a
gefe zuwa jimawa sai ta sake jawo wayar ta
fara rubuta masa sakon gaisuwa da fatan
alkhairi. Har zata tura sai ta fasa ta goge da
ta tuna ta tura masa na juma'a bai bata
amsa ba, kuma bai kira ba. Ta duba agogo
karfe goma sha daya da rabi 'yan
makaranta karfe goma sha biyu zasu fara
dawowa daga makaranta, gashi bata dora
abinci ba, don haka sai ta mike tsaye zata
je ta dora abincin sai taji wayarta ta dauki
ruri. Ta dawo ta zauna da sauri ta jawo
wayar ta duba, sunan dr lukman ne ya
bayyana, sai farin ciki ya rufe ta, tayi
murmushi tayi sauri ta danna, cike da fara'a
tayi masa sallama gamu da cewa yayana ina
ka shige ne kwana biyu naji ka shiru? Yayi
dariya yace kaji marar kunya. Ni zan neme
ki ko ke zaki kira ki gaishe ni ki samu lada?
Ko baki kirani ba naga flashing ko pls call
me ai zan kira ki. Amma baki neme ni ba.
Ko da yake jan aji ne irin na 'yan mata ko?
Yanzu muke maganarki da abokina dr
shuraim. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe
ido ta tambaya cike da zumudi, me yace?
Dr lukman yace yanzun nan ya fice da yaga
zan kiraki. Daman nace sai na fada miki ko
baya so. Wai ya akayi kike burge abokina
ne, ni tunda nake dashi a asibitin nan
shekara da shekaru ban taba ganin macen
da ya taba maganarta ba balle ya yabe ta,
sai ke? Yace kina burge shi saboda kina da
hankali. Ga ki da kunya, kara, kawaici, ga
hakuri da shiga ta mutunci, uwa uba kin da
aji ba ki cika shishigi da rawar kai irin na
'yan matan yanzu ba. Sannan haka kawai
yake tausayinki musamman da ake ce ke
marainiya ce. Sannan yace kina da matukar
kirki da yaji ashe kace kike daho mana
dambu da danwake. Kinsan da hannunsa ya
dauki lambarki a wayata, yace zai kiraki ya ji
jikin yayarki. Aisha farida tayi ajiyar zuciya
tayi dariya. Tace Allah sarki, haka Allah Ya
ke shirya al'amuran Sa duk yadda yake so.
Dr lukman yace munafukai ne ke dashi,
kunsan abin da yake tsakaninku. Ai idan
tayi tsami zamuji. Shima sai kwana kwana
yake yi min, idan na tambaye shi. Amma
gaskiya na sha mamaki da naga yana yawan
USA Novels BOOK
DUK KYAN TAKALMI 2* 13
Damuwa dake, don ni nasan shi nasan
ra'yainsa, nga yadda yake kushe mata. Ban
taba jin ya yabi wata budurwa a duniya ba
ma balle a cikin asibitin nan, shine na kiraki
naji meye sirrrin? Aisha farida ta kyalkyale
da dariya tace ba wani sirrri wallahi, Allah
ne Ya hada jininmu, nima yana burge ni
sosai. Dr lukman ya gyada kai yace gaskiya
kanwata idan har wannan abu zai tabbata
tsakaninki da shuraim zanfi kowa taya ki
murna, don kinyi dace da mutum na gari,
mai tsananin kirki da tausayi, mai kulawa.
Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido tace
Allah yayana haka ne? Yace inayi miki fatan
alkhairi, sannan ina taya yayarki da addua ta
samin sauki. Zanje wajen marasa lafiya, sun
taru suna jirana. Ya katse hiran. Aisha
farida ta sulale ta kwanta, tayi shiru tana
sake maimaita kalaman dr lukmann,
mamaki ya rufe ta, tamkar a mafarki ba a
ido biyu abubuwan suke faruwa ba. Anya
kuwa itace, ko dai mafarki ne? Take
tambayar kanta da kanta. Ta sake
gasgatawa babu abin da yafi addua da
hakuri a duniya. Ta dinga yi wa Allah godiya
da Ya nuna mata wannan rana. T dinga
kwararo addua tana rokon Allah ya karawa
dr shuraim sonta, kuma Ya sa ya aure ta. Ta
tuno abida taji daman abida tana nan taji
irin wannan dadadan labari. Sai tayi wa
abida addua Allah Ya bata lafiya. Tana
zaune ta kasa tashi ta dora abinci bata
ankara ba, sai taji muryar 'yan makarnata
sun fara dawowa. Ta ji wani kara
kwarakwacam anyi wurgi da jaka da robar
abinci a bakin kofar dakinta, ta san gajiya ce
da yunwa take addabarsu. Tayi wuf! Ta fito.
Ta shiga llallabasu tana yi musu dubaru
tana koda musu dadin garin kwaki da mai
da yaji, ta aika su suka siyo ta kwada musu
suka ci suna murna. Tace musu haka 'yan
makarantar kwana suke yi, gara ku fara
koyon ci kafin ku tafi sakandire ta kwana.
AISHA SHURAIM HIMMA BA TA GA
RAGO!!!
BABI NA GOMA SHA BIYU Fiye da sati biyu
dr shuraim bai kira aisha farida ba, itama
bata kira shi ba. Don haka sai ta fara shiga
kokonto anya kuwa dr shuraim yana sonta?
Da yana sonta ai ba zai share ta haka ba,
wata kila tausayinta kawai yake yi ba
soyayya ba. Jikinta yayi sanyi, ta fara shiga
damuwa, bata da walwala abubuwa suka
taru suka yi mata yawa. Kowa ya kalle ta sai
ya tambaye ta me yasa ta rame. Taci gaba
da daurewa tana ta addua tana neman agaji
daga Ubangiki Mai kowa, Mai komai. Son dr
shuraim ya zame mata tamkar ruwan
shanta, ya zame mata abincin cinta, kuma
mayafin lullubarta. Duk da daurewa da tayi,
sai da ta kai ta kasa cigaba da daurewa
saboda ji take tamkar zuciyarta zata yi
bindiga ta fashe don kunci. Tsananin son dr
shuraim da kuma rashin abida abokiyar
shawararta, itace mai bata shawara da
kwantar mata da hankali. Tasan da tana
nan da tuni ta fada mata abin da ya kamata
tayi nan gaba. Ranar talata bayan yaya
hussaini ya fita aiki, yara sun tafi
makaranta, sai ita kadai a gida. A kwance
take a daki ba tare da tana jin dadin
kwanciyar ba. Ta yanke shawarar tunda ga
dan kudi a hannunta bari ta harhada tayi
musu danwake, ta kai musu asibiti ko Allah
Zai sa ta dace ya ganta ya tuno da ita don
tana tunanin ya manta da ita ne. Tayi
zumbur ta miike ta shiga shirye shiryen yin
dan wake. Kafin karfe goma na safe ta
gama tsab, ta zubawa yara na su a flask. Ta
shiga tayi wanka ta fito ta dauki fiye da
mintina talatin tana kwalliya.
Wata sabuwar atamfarta ta saka diamond
mai kore da ja, aka dinka mata riga da skirt
matsattsu, ta sami bakin gyale da bakin
takalmi ta saka. Sai dai kash! Ta juya ta
sake juyawa ta dubi jikinta sosai, sai taji ba
zata iya fita a haka ba. Ta san shi kansa dr
shuraim din ma ba burge shi zatayi ba. Don
haka ta ajiye gyalenta ta dauko bakin
hijabinta sabo dal ta siya kwanan nan naira
dubu daya irin wanda ake siyarwa a dinke
mai hannaye kamar riga. Ya shiga da
takalminta mai dan tsini. Ta kullo kofar
dakunan bayan ta debowa yara kayan
makarantar islamita da flaski din abincinsu
ta mika dakin uwani taroke ta arziki idan
yaran sun dawo ta basu abincin su ci su
sauya kaya idan lokacin islamiya yayi su tafi.
Tace itama ba dadewa zatayi ba, zata kai
wa marar lafiya abinci a sibiti. Uwani ta
amsa mata cike da fara'a gami da alkwarin
zata aiwatar da abin da ta umurce ta, ta
hada ta yiwa marar lafiyar adduar samun
sauki. Aisha ta dauki kwandon da ta saka
flask din abinci da plates da cokula, bayan
yaji dakakke a 'yar roba, da 'yar robar
mangyada. Tana tafe cikin nutsuwa har ta
fito daga lokonsu ta sami adaidaita sahu
nan da nan ta haye. Ita kanta tasan tayi
kyau, ko ba a fada mata. Jama' da dama
sun dasa don samari suna ta binta sun kai
su uku sunayi mata magana. Suna sonta
bata kula su ba. Kuyi hakuri an riga an bada
ni. Amsar da take ba su kenan.
Tana isa cikin asibitin malam ta doshi
ofishin dr lukman, sai taji kirjin ta ya fara
dukan uku uku, don fargabar abinda zata
tarar daga dr shuraim. Tana hawa kan
barandar ofishin sai ta hango dr shuraim da
wasu dattijai maza su uku sun tunkaro ta,
ma'an suna fitowa ita kuma tana shiga. Sai
taji wani mummunan faduwar gaba. Ya
tsura mata ido sosai yana kallonta, har sai
ta taji kunya ta sunkuyar da idanuwanta
kasa. Suka wuce ita ma ta wuce, ta juyo a
hankali zata dube shi, shima ya juyo sai
gaba dayansu suka gaggauta juyawa da
sauri. Ta shiga fargaba saboda ta dimauce,
bata gaishe shi ba, kuma ya kamata ta
gaishe shi din. Don haka ne ma yake ta
kallonta har da waiwaye. Abin da zuciyarta
ke zayyano mata kenan. Jikinta a sanyaye
ta shiga ofishin dr lukman, taci sa'a yana
nan shi da abokinsa dr mohd. Bayan ta
gaishe su, sai ta ajiye kwandon abinci a
gaban dr lukman. Tace ga danwake nayi
muku. Yayi farin ciki, yayi godiya sosai. Dr
mohd ta dubi dr lukman yace lukman zaka
bani 'yar kanwar nan taka kuwa? Ina sonta
tun ranar da na fara ganinta. Kirjin aisha
farida ne ya burededen dukan uku uku har
ta fara dana sanin zuwanta nan a yau. Ana
wata sai ga wata, yanzu idan dr shuraim
yaji ko da wasa dr mohd ya furta yana
sonta, ai bar masa zaiyi ba zai kara nuna
alamar so ba. Ta tsunduma cikin wannan
dogon tunani, sai da dr lukman ya ambaci
sunanta ta dawo da hankalinta gare su.
Yace kanwata kinji wai in bashi ke? Tayi
murmushin karfin hali tayi shiru. Dr mohd
yaci gaba da kallonta, kallo mai cike da so
da kauna. Ta sunkuyar da kanta kasa, tana
mai tsananin jin kunya hade da bacin rai. Dr
lukman yayi dariya ya daki kafadarsa yace
kai da kake min tsiya wai ba kanwata bace,
bamuyi kama ba, sai inga wanda zai baka
'yar. Dr mohd yayi dariya yace yi hakuri
don Allah, yaya na daina. Yana rufe bakinsa
sai dr shuraim ya shigo. Nan da na hankalin
aisha farida ya sake tashi. Ta fara addua
kada Allah Ya sa acigaba da zancen soyayyar
nan. Tayi sauri ta sulalo daga kan kujera ta
gaishe shi. Ya amsa cike da far'a, sannan
yaci gaba da kallonta. Can yace lukman
dama kanwarka ce na hadu da ita a baranda
nake mata kallon sani, amma ban gane ta
ba. Naga ta sauya. Aisha farida ta dube shi
a kunyace ta sunkuyar da kai. Dr lukman
yace me ka ga tayi? Ta sake yin kyau ko? Ai
an gama makaranta ana hutawa a gida. Dr
mohd yace kai fa lukman yaya ne ka bari in
fadi da bakina mana, sai kace tayi kyau, kai
yayan kwabo ne ko? Su biyu suka tuntsire
da dariya yayin da dr shuraim ya tsaya cak!
Ya dubi dr mohd ya juya ya dubi dr lukman
ya juyo ya dubi aisha farida nan da nan taji
zuciyarta na dukan uku uku. Daga dukkan
alamu dr lukman ma baiji dadi da dr mohd
ya fadi haka a gaban dr shuraim ba, domin
yana kyautata zaton dr shuraim yana son
aisha farida, furatwa ne kawai baiyi ba.
Dr shuraim ya gaggauta daukar ajiyarsa a
loka ya fice da sauri. Aisha farida ta kame a
zaune, yayin da numfashinta yake kokarin
daukewa gaba daya, babu wanda yake
magana a tsakanin su biyun, dr mohd ne
kadai yake surutunsa. Haushi da tsanarsa
suka bayyana a fuskar aisha farida. Ta
dauke shi a matsayin tamkar mutumin da
ya dauko wuka mai kaifi ya dubi cikinta ya
burma mata, ma'ana ya kashe ta. Domin ya
rugurguza mata walwalar rayuwarta duniya
da lahira. Dr mohd yayi ajiyar zuciya, ya
dubi aisha farida yace bani lambar wayarki
aisha umar. Ta dago da sauri ta dube shi,
duba na takaici ba tare da ta iya furta
kalma gida daya ba. Dr lukman yayi sauri
yace ita zaka tambaya ko ni yayanta zaka
tambaya na ba izini ka karba? Ita ma na
umurce ta ta baka? Tayi murmushin karfin
hali ta mike tsaye a sanyaye ta yi musu
sallama zata tafi. Dr mohd ya nemi ta kara
zama suyi hira, tace gidan babu kowa sai ita
kadai, don haka take so ta koma da wuri.
Dr lukman ya ciro naira dubu daya ya mika
mata, yace tayi kudin mota. Tace ya bari ba
zata karba ba, tana kudin motarta. Dr
mohd ya zabura yace ka bari kawai zan
bata ko kuma ma marasa lafiyan da suke
jirana suyi hakuri sai na kai matata gida
sannan zandawo. Dr lukman yace wannan
kyautata ce ta daban a matsayin na
yayanta, kai da ita kuma daban. Kuma
wallahi sai kin karba kinji ma na rantse.
Aisha farida ta saka hannu biyu ta karba
gami da yin godiya, cikin sassanyiyar
murya. Dr mohd yace Allah sarki, kaji
yarinya mai ladabi, gaskiya nifa da gaske
nake. Lukman zanje in kai ta gida in dawo
muyi maganar gaskiya ba wasa nake ba.
Tayi wuf! Ta fice da sauri don bata so ya
biyo ta, shima ya fita da sauri ya biyo
bayanta ta, ya umurce ta ta jira shi su tafi
tare. Wani babban tashin hankalin kuma sai
ya tura kofar ofishin dr shuraim ya leka sai
ga dr shuraim a zaune a kan kujerarsa yana
danna laptop. Ya dagi da kyawawan
idanuwansa ya dubi dr moh sannan ya sake
daga ido ya hango aisha farida a gefensa.
Sai ya sunkuyar da kai, yaci gaba da danne
dannensa. Amma daga kallon fuskarsa
kasan zuciyarsa a bace take. Dr mohd yace
abokina zo muyi rakiya, wancan dan iskan
lukman yaki yace shi a dole babban yaya
ne. Ya girgiza kai yace nima yaya ne, ba
zanje ba. Kaje sai ka dawo. Aisha farida tayi
wuf! Ta bar wajen, tafiya take ba tare da
tasan inda take jefa kafarta ba. Kawai wani
lungu ta samu ta dinga kutswa cikin asibitin
maimakon ta nufi bakin gate sai tayi ciki.
Kafin dr mohd ya waiwayo sai yaga wayam!
Bata nan. Ya fito da sauri ya dudduba
hanyar gate ba ta nan. Ya duba kudu da
arewa, babu ita babu dalilinta. Sai ya cika
da mamaki, ya shiga kokonto da wasi wasi
don haka ya koma ciki da sauri don ya
shaidawa yaya lukman. Dr lukman yayi
dariya yace kunyarka takeji, kuma tana da
tarbiya bata so a ganta da namiji , ni nasan
halin kanwata. Dr mohd ya takura sai an
kitay a waya yaji inda take. Aisha farida ta
isa ofishin matron maryam ta iske bata nan,
sai sababbin dalibai da aka turo daga
makarantarsu. Yawancinsu ma duk sun
santa. Bayan sun gaisa ta tambaye su
matron sai suka ce ta fita. Aisha ta jawo
kujera ta zauna tana huci, nan da na suka
hau tambayarta bata da lafiya ne? Tace
gajiya ce kawai, tana so ta huta sannan ta
tafi. Bata rufe bakinta ba sai wayarta ta dau
kara. Ta bude 'yar karamar jakar da ta saka
kudin motarta da wayar ta zaro wayar,
sunan dr lukman ne ya bayyana. Sai taki
amsawa har ta katse. Tana katsewa ya sake
kira, don haka ta tabbatar kiran yana da
amfani, sai ta amsa. Tambayar da ya fara
mata itace kina ina? Tayi inda inda sannan
tace ina cikin adaidaita sahu hanyar
komawa gida. Yace toh shikenan. Allah Ya
kaiki gida lafiya. Ya kashe wayar tana jiyo
muryar dr mohd amma bata gane abin da
yake cewa ba. Anan zan dakata mu hadu a
DUK KYAN TAKALMI 3 kuji yadda zata
kasance. Daga 'yar uwarku JUT.
See Translation
January 10, 2015 at 7:26pm ยท Public
35
DUK KYAN TAKALMI 3* 1
Tayi ajiyar zuciya mai karfi.sannan ta
kwantar da kanta akan teburin da yake
gabanta don ta rasa abun da yake yimata
dadi innalillahi wa inna ilahi raji`un,ta ke ta
ambato,sai da ta dauki tsawon mintina 20
bata iya dago waba,ta mike tsaye da kyar
yayin da idanuwanta suka yi ja,alhalin kuma
ita ba kuka takeyi ba daliban dai har yanxu
tambayarta sukeyi,anya kuwa lafia? tace
lafia kalau kawai dai gajiya ce. Tayi musu
sallama tabar musu sako su gaishe da
metron maryam sannan ta tafi,ta cikin
lunguna ta kurkurda ta fito gate,tana fitowa
taci sa`a ta sami A dai- daita sahu babu
kowa a ciki,don haka tayi wuf ta shigo
batare da ta fada masa inda zai kai ta ba
balle suyi cinikin kudin da zai karba,tana
shiga ta zauna tana daga kanta, sukayi ido
hudu da dr shuraim cikin tsaleliyar motarsa
discussion continues,shi ma kallonta yake yi
alokacin da yake kokarin tsallakawa titi,ta
sunkuyar da kanta da sauri,yayin da
shikuma ya tsaya cak yana kallonta,daga
dukkan alamu yana mamaki da ya ganta
yanxu,mai adaidaita sahu yaja ya tafi yayin
da aisha farida ta rike kai,saboda nauyin da
taji kan yanayi mata sai da mai adaidaita
sahu yayi da gaske sannan ta bashi amsa, ta
fada masa inda zai kaita tana shiga gida
sallan azahar kawai tayi ta shiga lungun ta
kwanta ba tare da ta san a duniyar da take
ba,taji dadi da ganin yara a zaune a dakin
uwani,sunci abinci suna hutawa,don haka
tace suyi zamansu a nan zatayi aiki idan
lokacin makarantar islamiyya yayi su
tafi,saboda kawai bata son damu da
magana cikin wanan hali da ta riski kanta
Allah sarki soyayya ruwan zuma tayini tana
duban numbr dr shuraim,sai taga kamar shi
take gani,koda yaushe kunnenta da
idanuwanta ta suna yi mata

Please Login or Register in order to submit comment