Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini
ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda
nagama zan fita aka ce min kunja mota kun
tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake
waya dashi wani ne sunansa barr muazzam ,
bansan kai kira ba da na bashi hakuri na
katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi
hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar
da yakeyi yace waye barr muazzam? Na
fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki,
kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba?
A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa
ya kamata sannan tambayar ta daga mata
hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki
my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da
ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode
ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka
tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim
kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a
bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min
laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka
baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani.
Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah
Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a
lokacin da na shiga ukuba, sai muke
gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr
janan bai same ni ba, shine yake shaida
min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya
tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace
kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin
rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta
shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr
shuraim yace tabbas ta dade ana shariar
nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki
nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai
Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi
aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban
taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura.
Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki
bani labari mai dadi mana wanda zai sani
inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun
bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji
anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha
farida tayi dariya tace zanso nima ka
kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na
biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare
ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin
jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da
alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi,
yau farida ta zama ta shuraim, shima ya
zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace
bani labarin me ya faru? Haka dai suka
cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da
kauna har tsawon awa guda. Abida na
kwance ta kafawa farida ido sai murmushi
takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta
mike tayi rawa don babu hali ne. Tana
adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi
auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI
AISHA FARIDA!!!
BABI NA GOMA SHA TARA! Abu kamar
wasa karamar magana ta zama babba.
Auren farida da shuraim sai kankama yake
sake yi. 'Yan lungu yanzu sun gasgata, don
da jita jita akeyi ko kuma ana ganin abin ba
mai yiuwawa bane, wahalar da kanta kawai
zatayi, yaudararta zaiyi ya tafi don ba ajinta
bane. Sai gashi idan da a sati sau daya ake
ganinsa , yanzu a sati a kalla yazo sau biyar.
Ba sai an fada ba, rayuwa da tukunyar su
aisha farida ta canja gaba daya, sun fara
bankwana da talauci, dr shuraim ya tsaya
musu. Tun ba a yi auren ba ma har ta
kidime ta canza salo da yanayi, kai kace ba
wannan faridar bace ta da. A yanzu farida
ta zama gangariyar 'yar gayu. Komai nata
mai tsada ne (high class) , kama daga
suturunta, takalmanta, da jakunkuna,
mayukan shafawarta da kayan kwalliyarta.
Sai ta canja tafiya, ta canja magana ta kuma
canja tsarin rayuwarta. Bata wulakanta 'yan
lungu amma bata cika shiga cikinsu a yita
wasannin banza ba da surutai barkatai.
Zama da dr shuraim ta koya nutsuwa ga jan
aji , magana ma sai an daidaita baki. Haka
ba a cika dogayen jimla da hausa ba sai an
tottoshe da turanci. 'Yan lungu sunyi
gulmar, sunyi zumden, sunyi yaficen, abin
ya wuce tunaninsu. Sai cigaba suke gani
kala kala musamman da suka ga ta fara aiki
ya daukar mata mai adaidaita sahu ya kaita
ya dawo da ita.
DUK KYAN TAKALMI 3* 10
Abida na tsakar gida tana kallon bakinsu
bata ce musu komai ba suka gaji, har takai
ta kawo ma sun zo sun same ta don suji
wani labari game da wannan aure na farida,
sai ta nuna musu ba lallai sai dr shuraim ba,
duk wanda yafi alkhairi a farida shi zata
aura. Basu ankara ba sai suka ji tashinsu,
sai ana gobe zasu koma sabon gidansu suka
fada musu. Mamaki ya rufe jama'a, 'yan
rakiya mata lodi lodi suka bisu don su
ganewa idanuwansu. Gida mai kyan gaske
babu abinda ba'a zuba ba, tun daga gadaje
a dakuna uku da kujeru a falo duk shuraim
ya siya, gida gini bulo da bulo sama da kasa
duk tiles. Rayuwa sabuwa ta tabbata a
gidan hussaini, farida bata rasa kudi. Dr
shuraim yana bata, ta dauki albashinta
kuma. Babur ta fara siyawa yayanta, kuma
ta canja wa 'ya'yanta makaranta ta kudi
anan court rd, mai adaidaita ya kaisu ya
dauko su. Sun koma sabon gida ba dadewa
aka saka ranar kawo kayan sa rana da na
lefe gaba daya. Kudin mota baiyiwa su
aisha farida wuya ba, suka turawa
magabatansu a shagamu, mata bakwai
maza uku suka shigo mata suka zo kano
don karbar kaya. Abida bata mance da
kawayenta na tsohon gidansu ba, fiye da
bus uku suka ciko suka zo don su ganewa
idanuwansu. Tunda kan 'yan uwan shuraim
kallo ya fara kafin a bude kayan lefe. Masha
Allah! Tabarakallah! Kaya sun yi kyau.
Akwatuna shida da kit biyu. Da saitin
sarkokin gwal da awarwaraye hudu manya.
Wata uku kacal aka saka ranar bikin, kowa
yana sam barka tsakanin dangin amarya da
dangin ango, har aka watse.
An sha dauki ba dadi a bangaren dr
shuraim kan maganar aurensa, 'yan uwansa
mata da yawa basu son auren, kasancewar
sun iske dangin amarya basu da hali. Cece
kuce kala kala sukayi tayi amma shuraim bai
damu ba , tunda mahaifansa sun yadda,
sunyi masa fatan alkhairi , don haka suje
suce duk abin da zasu ce. Da farko dai
mahaifiyarsa taki yadda, amma da yake
tana jin maganar mijinta, kuma kaifi daya
ne, duk abin da ya fada ya zauna a gidansa
dole a bi. Amma a sanda guguwar rigimar
ta buso daga bangaren matar shuraim wato
faiza sai ta kore ta danginsa saboda tafi
karfi. A sanda shuraim ya shaida mata a
waya cewar zai kara aure aure cikin
lallabawa da tattausan kalamai, sai ta hasala
tayi ta zage zage har da koke koke wai bata
yadda ba. Ya shaida mata aikin gama ya
gama, saura wata uku, kuma ba zai fasa ba.
Haka aka tashi dai baram baram a wayar,
shi ba dadi, ita ma ba dadi. Bayan sati guda
da wayarsu sai gata a Nigeria ita da
mahaifiyarta. Ba sulhu ne ya kawo su ba,
rigima ce tsantsarta. Mahaifiyarta tace sai
dai ya saki 'yarta , dama can ita ba son
auren take yi ba. Tunda yace zaman nigeria
zaiyi tasan zai cuce su. Ta gangaro kan
mahaifansa tace dama sun tsani 'yarta faiza,
sune suke hadasu fada. Da kyar rigiman
nan ta lafa, su dai mahaifan shuraim ba su
rama ba, amma 'ya'yansu sun rama musu,
akayi ta cece kuce. Shuraim ne yayi ta bada
hakuri har aka samu hayaniyar ta sauka,
zuciyar kowa ta dan lafa aka zauna taro a
babban falon mahaifinsa aka fara bayanai
da yadda za'a gano bakin zaren. Kiri kiri
matar shuraim ta fada wa mahaifiyarta tana
son mijinta, ba zata iya rabuwa dashi ba.
Mahaifin shuraim yace to ki kwaso kayanki
kizo ki zauna da mijinki da 'yarku a
gabanku. Karatun fa? Inji mahaifiyarta ta
fada a fusace tana harararta. Tace saura
'yan watanni na gama, zanje na gama na
dawo na zauna. Ta sha adduoin albarka a
wajen mahaifin shuraim da shuraim din
kansa, gami da danginsa. Yayin da ta
sacewa mahaifiyarta gwiwa don ba haka
taso ba. Ta fusata tace to ko sau daya kada
kizo kice an miki wulakanci, kije can ki
karata.
A daddafe ta bari sukayi kwana uku sannan
suka koma london. Kafin su tafi kullum kuka
faiza take yi wa shuraim tana cewa baya
sonta yanzu tunda zai auri wata. Ya iya
dadadan kalamai masu kwantar da hankali,
gami da bayanai masu ma'ana ya hada da
yi mata alkawari zaiyi musu adalci a
tsakanin su. Sai taji sanyi a ranta, ta kuma
yadda da duk abinda yake fada mata.
Rabuwar lafiya yayi da matarsa, uwar ce dai
ko sallamarsa bata amsa ba a airport.
Hankalinsa ya kwanta a wannan bangaren
kuma bashi da sauran rigima. Duk dauki ba
dadin da suka yi aisha farida bata sani ba,
bai bari ta sani ba. A bangaren ta matsala
kadan ta samu daga musbahu, a inda ya
tayar da hankalinsa, ba ci ba sha da yaji
abar kaunarsa zatayi aure ta barshi. Ya hada
kayansa zai bar garin, zai shiga yawon
duniya a rasa shi har abada. Tunda ya rasa
farida, to shima mahaifiyarsa da matarsa sai
sun rasa shi. Hankalin 'yan gidansu da
mahaifiyar sa ya tashi, mahaifiyarsa da
kanta tayiwa aisha farida waya ta shaida
mata halin da musbahu yake ciki kuma suka
roke ta tazo ta bashi baki ko zaiji. Sai kawai
ta fashe da kuka ta kashe wayar. Abida tazo
ta iske ta tana kuka ta tambaye ta suka
zauna suka yi shawara. Ta bata shawara ko
bata je wajensa ba, ta saka kati a waya ta
kira ta bashi hakuri akan yayi tawakkali , ya
daure ya karbi kaddararsa , zai yiwu shi ba
alkhairi bane a gareta, itama haka. Ya zauna
kada yace zai gudu, baisan inda zai fada ba.
Kuma Allah Zai barshi da gudun tunda bai
yadda da hukuncin da Ya yanke masa ba.
Haka aisha farida tayi, sai bayan kwana biyu
ta kira shi a nutse tayi masa nasihu masu
ratsa zuciya. Har sai da yaji ba zai tafi ba,
ya fasa. Yana kuka, tana kuka, tanayi masa
fatan alkhairi da godiya. Shima irin
wadannan adduoin ya dinga zuraro mata
har ta kashe wayar.
Banbancin bikinta da na barr muazzam sati
uku ne, don haka sanda taje dinner party'n
bikinsu a tahir guest palace da daddare ta
tafi musu da katin bikinta ita ma. Barr
muazzam yayi farin ciki da ganin farida da
shuraim a wajen bikinsu. Da farko ma bai
ganeta ba, saboda kyan da tayi ta goge, ta
waye ta tsatso da wani kyau na daban. Duk
da dandazon taron nan kowa yana kokarin
ya gaisa da ango da amarya, sai da
muazzam ya taso ya tare su ya kamo
hannun amaryarsa ya gabatar mata da aisha
farida da ya dade yana bata labarinta.
Daman ta san shuraim har ta gayyece shi
bikinta, shuraim ma ya gabatar mata da
farida a matsayin amaryarsa. Daga karshe
muazzam ya kaisu wajen barr nuruddin suka
gaisa, suka zauna a kurkusa. Tabbas daga
gani babu tambaya, nuruddin yayi mamaki
da ganin farida, shi bai taba tunaninta ba
tun wacccan ranar, sai ya dinga tuno
wulakancin da yayi mata a baya, yana jin
nauyinta. Ya sake yin mamaki da yaga
matarsa ma ta santa, sun kebe sai hira suke
yi kuskus suna ta tuntsira dariya kamar sun
saba. Ya kalli shuraim ya sake kallonsa, ya
tabbatar ya hadu, Allah Ya tsara halittarsa a
nan ko ba'a fada masa ba yasan akwai kudi
da ilimi, kuma ita zai aura. Ya tara
tambayoyo jifgi guda a zuciyarsa yana so ya
samu muazzam ya jero masa su akan
farida. Baraka ta dubi aisha farida tayi
murmushi tace ina ta jin labarin aisha farida
kullum, sai yau Allah Ya nuna min ke. Babu
abinda zance miki ni da muazzam a duniya
sai dai godiya, kin ceci rayuka. Ni da na zata
ma soyayya kukeyi da barr muazzam, sai
daga baya na gane jininku ne ya hadu, ya
bani labarin ki da likita, kuma naji dadin
ganinku a tare. In Sha Allah kuma zanzo
bikinku duk da watan haihuwana ne
wannan. Farida tayi dariya tace nafi kowa
farin ciki da dukkanin mu Allah Ya amsa
adduar mu , Ya bamu wadanda muke so.
Ina nafisar ta sa take? Yaya suke a yanzu?
Baraka tayi dariya tace ai ko zancenta ba
yayi, ko kiransa tayi sai ya katse. Baya son
abinda zai bata min rai, yanzu duk abinda
nake so shi yake min.
DUK KYAN TAKALMI 3* 11
Tunda bikin farida da shuraim ya rage saura
sati guda basu zauna ba, daga ango da
amarya har danginsu. Sai shirye shirye
akeyi kala kala. Bayan yinin biki da
kowanne bangarorin biyu zasuyi, akwai
shagulgula har guda biyu da dangin ango da
amarya zasu hadu a waje daya ayi. Daya da
yamma za'ayi a tahir guest palace sai
dinner a Chinese dragon da daddare za'ayi,
kowanne kuwa sai da aka fitar da anko.
Kayan fitar bikin ango da amarya daban aka
dinka musu yadda zasuyi shigar kala iri daya
tsadaddun gaske. Asabar ce yau misalin
karfe biyar na yamma n shuraim ya sauke
aisha farida a kofar gidan kawarta khadija
sani dake sokoto td don ta mika mata katin
gayyatar bikinta ta fito su tafi. Saboda
akwai wurare da yawa da zata kai kafin
magriba ya mayar da ita gida,saboda dokar
da yaya hussaini ya saka mata cewar duk
inda taje ta dawo gida kafin magriba ko da
kuwa tana tare da shuraim ne tunda ba a
daura aure ba. 'Ya'yan abida dukka hudun
ne 'yan rakiya suna zazzaune a bayan mota
sunyi dai dai da kayan ciye ciye da shuraim
ya dau nauyin tulo musu. Suci biskit su kora
da alewa, sai su dora da ice cream da
shawarma. Ehm! Dadi kan dadi wai kunama
ta harbi gyambo, abinda basu taba ci ba a
yau gashi sun samu. Kada ki shiga ki zauna
kiyi ta labari fa a ciki. Shuraim ya fada a
lokacin da ya kashe mota dai dai wani bakin
gate. Ta dube shi tayi murmushi ta gyara
farin gilashin fuskarta tace bazan zauna ba
yayana, yaya za'ayi in iya zama inyi hira
alhali nasan kana jirana? Ina mika mata zan
fito. Ta juya ta dubi yara tace ku zauna
yanzu zan fito ba sai kun bini ciki ba.
Ta bude mota ta fito, takawa take a nutse
kafarta sanye da wani cogen takalmi mai
tsinin gaske, launin baki da bakar jakarsa.
Sai ya kara mata tsawo. Doguwar rigar
jikinta (gown) da aka dinka mata a jikin
super holland purple da baki ta sake fitowa
da kyauwn dinkin. Dr shuraim ya bita da
kallo saboda kyauwnta da yake gani, ji yake
tamkar zai hadiyeta don kauna. Tana shiga
gidan khadija ta iske ta a falo ita kadai tana
kallon MBC action, bayan ta amsa
sallamarta ta nuna mata kujera ta zauna,
sannan ta sake kallonta sosai, sai a lokacin
ta gane aisha umar ce. Khadija ta zabura ta
mike tsaye, ta jawo dogon salati ta dire, ta
rike haba tare da dafe kirji. Tace aisha
umar dama kece na kasa gane ki? Ikon
Allah kece kika zama haka? Daman maryam
ahmad tace idan na ganki yanzu ba zan
gane ki ba. Saboda kin sauya gaba daya kin
zama 'yar gayu. Dariya kawai farida ke
kyakyatawa, khadija ta matso kusa da ita ta
zauna ta shafa jikinta, ta sake nanikarta don
ta tantance kamshin turaren da take ji a
jikinta , tabbas designer ne. Kudinsa ba zai
gaza dubu ashirin ba. Ta janye dankwalinta
don taga gashinta. Sai taga waccan
cunkusheshen gashin na farida mai tauri da
ba a shamfo sai kitson zane kullum yanzu
ya sha mai (relaxer) yayi yalo yalo kamar na
larabawa, baki sidik da shi, ya warware ya
mike daman can mai yawan gashi ce da
tsawo, don haka ya wuce kafadarta. Babu
abinda khadija ke kira sai ikon Allah! Aisha
umar yaushe kika zama haka? Aisha farida
tayi sauri ta gyara daurin dankwalinta ta
mike tsaye tana dariya tace Khadija bana
son wulkanci, wane irin tonon silili kike yi
min haka? Ke dai wani labarin zamuyi shi
idan muka hadu, yanzu sauri nakeyi na bar
shi a kofar gida. Katin bikina na kawo miki,
rana ita yau yini da party. Ta zaro wasu
hadaddun katina guda biyu ta mika mata
daga cikin hadaddiyar jakar dake rataye a
kafadarta. Ta juya da sauri ta fara tafiya.
Khadija sani ta watsar da katunan akan
kujera ta biyo bayanta da sauri. Tace ke
aisha umar ko ruwa ba zaki tsaya ki sha ba?
Dan mai adaidaita sahu ba sai ki sallame shi
ba sai in mayar dake anjima da daddare
ba? Ko angon ne ya fara hana ki kaiwa dare
a waje? Lallai kina ji da wannan angon naki,
ance mai kudi ne shi ya tsaya miki, ance
yana sonki tamkar ransa. Auwal dan ajinmu
yace min a likita zaki aura , rannan na hadu
dashi auwal din a ministry of health yace
min tare kuke aiki. Wai meye gaskiyar
maganar? Aisha farida dai har yanzu dariya
take yi, tace khadija don Allah ki ajiye
tambayoyin nan naki sai mun nutsu zan
amsa miki su. Daidai lokacin khadija ta tura
kofar gate din suna kokarin fitowa, ta daga
kai ta dubi dankareriyar motar da aka kawo
aisha farida a ciki, sai tayi ajiyar zuciya kafin
tayi magana. Sai ta daga kai ta hango
santalelen saurayin da yake tsaye a jikin
motar. Ya kalle ta, ta kalle shi, ta daka
tsalle ta koma cikin gida da gudu, ta labe a
jikin gate din tana salati. Aisha farida ta
firgita itama tabi bayanta da sauri ta rike ta
tana tambayarta lafiya? Khadija ta rike kirji
tace aisha umar kamar dr shuraim nake
gani a kofar gidana? Lafiya ya biyoni? Ba dai
asirin da nayi masa bane yanzu ya fara
cinsa ya biyo ni har gidan mijina? Yaya zanyi
yau?
Aisha farida tayi dariya tace ta yaya dr
shuraim zai san gidanki har ya biyo ki? Wa
ya fada miki asiri yana ci? Tabbas sihiri
gaskiya ne amma bai cika kama wanda yayi
imani da Allah ba. Dr shuraim ni ya kawo,
don ni yazo gidannnan, shine angona.
Khadija ta bude ido da baki gaba daya tana
duban aisha farida, mamaki marar
misaltuwa zaka gani a idanuwanta. Tace
aisha umar yanzu dr shuraim zaki aura
shine baki fadawa kowa ba? Ashe daman
kema kina sonsa a lokacin da muke sonsa
kika boyewa kowa? Ta ya kika same shi? Ke
kuwa wane irin asiri kikayi masa haka?
Aisha farida ta girgiza kai tace babu asiri
acikin lamurana, sai dai addua. Addua na
rike, ita ta kaini ga matsayin da ban taba
zato ba. Khadija nayi alkwawri idan na
samu nutsuwa zan fada miki dalla dalla
yadda muka hadu da dr shuraim har ya
zama mallakina. Sai anjima, sai kinzo bikina,
adireshin wuraren duk suna jikin katin.
Aisha farida ta juya ta tafi, yayin da ta bar
khadija a sankare a tsaye, baki a bude don
gigicewa da mamaki. Daga gidan khadija,
gidan maryam ahmad suka wuce dake
unguwar sallari. Irin wannnan mamaki da
figici da ya samu khadija sani shi ya fadawa
maryam ahmad. A lokacin da ta fito har
mota don su gaisa da angon kawarta, ta
iske dr shuraim ne. Sai da aisha farida ta
tare ta don ta kusa faduwa don tsorata. Ta
shiga yiwa farida rada tana cewa ke dr
shuraim ne wannan ko kaninsa? Aisha umar
ina kika same shi har zakuyi aure? Labarin
yana da tsawo! Amsar da ta bata kenan ta
shige mota suka ja suka tafi ta bar maryam
a sankare a kofar gida.
Aisha farida ta sake kyalkyalewa da dariya
tace tunda kace Allah ai ka gama daure min
jijiyoyin jikina. A lokacin tabbas nima
mutum ce kamar kowa, kuma mace yadda
suke mata. Naji abinda suka ji a raina,
amma sai na fisu hakuri da tawakkali. Na
sama raina har abada ba zan same ka ba
gara ma kada in jefa kaina cikin wahala.
Don haka ban cusa kaina ba, ina gefe ina
addua, Allah masanin komai, sai Ya bani kai
a lokacin da ban taba zata ba. Dr shuraim
yayi murmushi ya lumshe ido yace na
fahimce ki, kuma na gamsu da bayananki.
Amma maiyasa kika tsorata baki zo kin
gwada sa'arki ba? Kika sani ko kici nasara ki
same ni? Ta girgiza kai tace karfina ko
wayona da kwarkwasata ba zasu amfana
min komai ba. Saboda naga 'yan mata da
suka fini komai basu same ka ba. Yayi
dariya yace kin taba sanin kina da kyau
kuwa? Kyawun da tunda nake ban taba
ganin wacce ta yi min kyau kamar ke ba.
Tun ranar da na fara ganinki a duniya na
tabbatar kina da kyau , da zan iya samunki
da naji dadi. Sai aisha farida ta dafe haba ta
bude baki tayi ajiyar zuciya ta langwabar da
kai gefe. Tace shikenan my dear tunda har
abin ya zama ba'a. Dr shuraim ya juyo a
hankali ya dubi kwayar idon abin kaunarsa
yace na taba yi miki karya ne? Toh ki yadda
da magana ta, kina da kyaun da ba a ko ina
ake samunsa ba, babu kantin da za'a iya
samunsa a saya.
DUK KYAN TAKALMI 3* 12
Yace,na taba miki karya? toh ki yarda da
maganata,kina da kyan da ba a koina ake
samunsa ba,babu kantin da za a iya samun
irinsa a saya saboda dalilaina masu zuwa.na
daya kina da kyakkyawar fata irin ta 'yan
kasar itiofiya,mai hasken duhu(chocolate
color).na biyu,kina da gashi mai kyau,irin
na asalin Africa mai gazar-gazar da baki,irin
wannan gashin shine a girarki da fatan
idonki.na uku,kina da kyawun kwayar ido
dara dara,farare sol!idan kina kallon mutum
sai yaji wani yarr a jikinsa saboda kina da
idanuwan nan da ake kira sexy eyes.na
hudu,hancinki bashi da tsayi sosai,haka
bashi da fadi ya dace da fuskarki.na
biyar,bakinki dan karami,kina da hakora
farare sol,ga 'yar siririyar wushirya a
tsakiya.ga ki da fara'a idan kika yi dariya sai
gefen kuncinki su loba dukka biyun,na
shida,Allah yayi miki wata irin murya mai
dadin gaske,wacce ko yar uwarki mace taji
muryarki sai ta waiwayo balle da na
miji.dadadan lafuzzanki su suke karawa
muryarki dadi.na bakwai,Allah ya miki kirar
jiki mai kyau,a dire kike,baki da kiba,ba ki
da rama.sannan bakiyi gajarta ba,ba kiyi
tsawo zalolo ba.amma duk wannan bai jaa
hankali na na fara sonki ba,sai da na gama
karantar halayenki na tabbatar kina da
hankali,kirki,t awakkali,sannan kina da aji.
Abubuwa biyu ne suke tafiya da tunanina a
wajen mace,shine,idan mace tana da aji da
kuma kamun kai wacce ba yar iska ba.kin yi
sa'a kina da duk wadannan.aisha farida tayi
hamdala a zuciyarta,tayi murmushi a
sarari,ta dube shi tayi fari da ido.ta ce,nayi
sa'a da nayi dace na sameka.Dr shuraim
hakika kana da kyau babu inda Allah ya
rage ka tun daga halittarka,ilimi da
dukiya.duk wadannan basu dameni ba,sai
na dinga lura da halayyarka.na shiga halin
damuwa alokacin da ka gwada ni cewar
zaka tafi da ni gidanka ko ba kayi bayani ba
na fahimci abun da kake nufi,sai na kudiri
niyyar rabuwa da kai har abada,kyawunka,
dukiyar baza su taba burgeni ba,tunda kake
sabawa Allah.sai daga baya na tabbatar ba
haka kake ba,kai mutum ne mai tsoron
Allah da tausayi shine na saki jikina na
tabbatar nayi dace da miji nagari.su dukka
sukayi dariya a lokaci guda.
Dr shuraim yace kin cika mai hankali mai
zurfin yunani,kuma ba zakiyi da na sani ba
tunda kika farga kika san kyau da kudi ba
komai bane in dai mutum bashi da hali na
gari.matsalar da ke damun yanmatan
zamanin nan ke nan,shi yasa ake samun
matsala a zaman aure,sakin aure ya yawaita
a kasar hausa.hirar so da kauna da fahimtar
juna suka yi tayi,har suka isa kofar
gidansu.yayin da yaran suke baya suna ta
hidima da kayan dadi,sai ci suke tayi,ya ki
ya kare saboda ledoji da yawa ya ciko
musu.aisha farida tayi godiya suka fito daga
motar suka shiga gida,dr shuraim yana daga
muau hannu,su ma suna daga masa har ya
tafi.su dukka suka ji kamar kada su rabu da
juna,sai kuma gobe idan Allah yaa kaimu zai
dawo don yanzu ba ya fashin zuwa wajen
farida.ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA!!!
BABI NA ASHIRIN BIKI!BUDIRI! BIREDEDE!
Rana bata karya sai da uwar diya taji
kunya.tun ranar laraba aka fara gudanar da
shagalin bikin farida da angonta dr
shuraim.akayi kamu laraba,alhamis akayi
kunshi,jumaa akayi sisters eve da
yamma.ranar asabar aka daura aure da
misalain karfe goma sha daya na safe abisa
sadaki mafi kankanta don neman albarkar
aure,kuima a ranar akayi yinin biki.dangin
farida sunzo da yawa maza da mata daga
shagamu,tun sanda biki ya rage sati guda
suka fara zuwa don su taya ta murnar biki.a
ranar asabar da daddare akayi hadadden
party a hotel din tahir guest palace,wanda
mutane da dama suka halacci wajen.
Manyan likitoci abokan ango da kawayen
amarya,da yanuwaansu da abokan arziki
kowa yazo.makada kala kala sunzo kamar
mai dawayya,dan asharalle,yaron saadu
bori,fati niger,rabi mustapha,kowannensu
an bashi fili ya cashe.wannan yayi sai ya
matsa ya baiwa wani fili.babu abun da ake
kira sai likita shuraim angon sista
farida.barista muazzam da amaryarsa
janan,barista nuradin da uwargidansa
baraka su ma sun hallara.yan unguwansu ta
da duk sun zo babu wanda yasan adadin
wadanda suka zo,saboda yawansu.taro yayi
taro har amarya da ango basu iya gane
wadanda suka zo da wadanda basu zo
ba.kallo daya zaka yi wa ango da amarya ka
tabbatar suna tsananin murna.idan ka kalle
su zaka san maauratan nan suna tsananin
son junansu.sun ba wa kowa shaawa sosai
saboda sunyi kyau matuka,shigarsu ta
burge kowa,kowacce rana akwai kalar
kayan da zasu saka kala daya.
Kawayen amarya su ma sunyi nasu
ankon,dangin ango da irin nasu ankon
daban.'yan shagamu ma da irin nasu ankon
daban.masu daukar hotuna da bidiyo suna
ta aikin dauka,sai yau mutane da yawa suka
gasgata shuraim yayi saar mace mai
kyau,don kyawunta ya fito kamar ba ita
ba.ana daf da za a tashi sai ga uwar gidan
shuraim faiza ta shigo fili,ta yi wa kowa ba
zata ita da kawayenta guda biyu hafsat da
halima su ma mazauna london ne,tare suka
zo daga can.don da shuraim yayi yayi tazo
bikin tace baza ta zo ba,toh ashe ta taho
bai sani ba.ta danne kishinta tayi ta musu
kari da daloli sai a lokacin aisha farida ta
fara ganinta,ita ma haka,don ko a hoto ma
bai taba nunawa ko wacce ba.kyawunta bai
tsorata aisha farida ba ko kadan,don bata
fita kyau ba.fari kawai zata nuna
mata,tsayinsu daya,har farida ta fita tsawo
da yawan gashi.faiza ce ma ta tsorata da
ganina aisha farida saboda tayi mata ba
zata,ba ta zaci ta hadu haka ba,don 'yan
gulma sun tsegunta mata yar talakawa
ce,baka mummuna,ashe abun ba haka yake
ba.
Faiza ta kudiri aniyar zama na kishi,ba
kishin dokedoke da zage zage ba sai dai
zata nuna mata ruwa ba saan kwando
bane.wayewa da gogewa a cikin wayayyun
duniya tabbas abun da ta sani farida bata
sani ba,kuma ba zata taba sani ba.zata san
tayi garajen aure mata mili,don mai karbar
shuraim ahannunta sai yayi shirin yaki sosai
DUK KYAN TAKALMI 3* 13
Sai dr shuraim yaji dadi da ganin faiza ta
saki ranta,suka gaisa da farida sosai,har da
baby yarsa mai kama da uban kamar an
tsaga kara.babu wacce ta fi jin mamaki da
ganin aisha farida ita ce amarya sai
kanwarsa da suka hadu da ita a asibiti.suna
ganin juna suka shaida kansu,suka gaisa
cike da farin ciki.
Washegari ranar lahadi da

Please Login or Register in order to submit comment