Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turmutsitsi da
wahalar zaman haya na siya mata gida a
shagamu mai kyau na siminti, na bawa
mijinta motar haya bus yana tuki yana
samun na cefane, na biya mata makka taje
ta sauke farari ta dawo na hada mata jari
tana 'yar sana'a a cikin gida tana samun na
batarwa,ita da 'ya'yanta suna saka sutura
masu kyau suna makaranta mai kyau.
Musbahu tsohon saurayina kuma tamkar
dan uwana yanzu shima nayi masa rana don
na bashi dubu saba'in ya kama shago na
siya masa computers 3 da injin photocopy
ya bude business center tasa ta kansa ya
daina aiki a karkashin wasu. sai ga mamarsa
data tsaneni da matarsa an rakosu gidan
nan tana ta kuka tana neman gafara a bisa
tsana da cin mutuncin data yi min a
baya.harda cewa dama ace baya zata dawo
mana data bar Musbahu ya aureni ashe ina
da mutunci haka.tayita kallon gidana tasan
nayi musu zarra,
kyauta ta ban girma nayi musu na suturu da
kudi mai yawada zasu tafi kadan kenan
daga irin rahamomin da Allah yayi min duk
a sanadiyyar shureim bai rageni da komaiba
dan nima ban rageshi da komai ba.khadija
tayi ajiyar zuciya tace"ai ko baki fada ba
Aisha umar kallo 1 za'ayi miki mu2m yasan
kina cikin daula,jikinki ya nuna kuma muma
shaidu ne don babu abinda bakya yi
mana,kici gaba da godewa Allah sai ya kara
miki"Ummi tayi ajiyar zuciya tace"shiyasa
nazo daukar darasi kibani dama indinga
zuwa
kullum har tsawon wata guda inji ina ganin
abubuwan da kikeyi ni ban iya komai ba.AF
tayi dariya tace"zaki iya zuwa kullum amma
banda ranar weeEnd don mijina yana
gida"Ummi tace to, a wata zan zo sau
KWANA ASHIRIN DA HUDU. Saboda naga
alamar har yanzu GANGAR JIKINSA NA
AURA, zuciyarsa na wurin amaryarsa
surayya. gara inkoma kacokan indinga koyi
da abinda YARENA ADDININA, yazo mana
dasu.duk wanda na tara na fada masa
abunda Yasar yakemin sai yace INA RUWAN
WANI, dan abaya anyi min shaidar tsiya
as sanni da bin bokaye. nakan cewa Yasar
KAI KAFI CANCANTA' ka lura da cewar na
canza yanzu bana bin bokaye irinna da bai
cika kallonaba ma balle yasan nayi kwalliya
tsabar yariga dayayi min shaidar kazanta
abaya.sai Ummi ta fashe da kuka.Khadija ta
tabe baki tace wannan shi ake kirada ADON
DAWA'kenan kinyi kwalliya abanza don
baya lura"AF tayi murmushi ta dafa kafadar
Ummin Yasar ta girgizata tace"kwantar da
hankalinki kawata,sannu ahankali zaki gane
kan mijinki.Yasar zai zama takalmin takawa
tana rufe bakinta sai ga Dr.shureim ya
shigo, ya dubesu 1by1 yayi murmushi. yace
Farida, hakika ni takalmin kafarki ne, nayi
miki lamuni ki takani kije duk inda kikeso
dani 'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake
takawa......................**
*************** ***************
*************** *********ALHAMD
LILLAHI karshe
DUK KYAN TAKALMI 4
Aisha farida tayi karfin hali tace ba
damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da
mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni
ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a
son mace marar kamun kai. Barr muazzam
ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane
dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru
ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da
kika zo kika same mu kinyi mana sallama
duk da tun kafin mu amsa har kin zauna.
Daman kamata yayi ki gabatar mana da
kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da
bamu labari shine abinda ya daure mana
kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi
ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin
ko na sanki ne. Aisha bani labarin
takamaiman abinda ke damunki, muma nan
da kika ganmu matsala ce take addabarmu,
ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu
taimaki juna da shawarwari. Barr
nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi
abokinsa yace malam in ka gama kazo ka
same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan
iya zama ina sauraron wannan shirmen
naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji
ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau
hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan
taji matsalar ka me wannan zatayi maka?
Itama bata san yadda zatayi da kanta ba
balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake
ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai
ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya
tafi bai daina fada ba yana tafe yana
magana yana wurwurga hannu har ya fice
daga cikin gate din. Aisha farida da barr
muazzam suka bishi da kallo har sai da suka
daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa
sai hawaye ya fara zubowa daga
idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar
da komai ba komai ba. Kece fa kika gama
bani labarin cewa zaki iya zama da
kowanne irin mutum a duniya. Inji brr
muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge
hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji
haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min
kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club,
karuwa kenan. Shine mutum na farko a
rayuwata daya taba jifata da wadannan
munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai
dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr
muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba
da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin
sauraronki.
Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura
gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da
irinkukannan yaukimani wata takwas
kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa
mamawa kinsani cikintausayin
ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa
tsayarda hawayendake zuba'a idona.
kitaimaka kibani lbrin cigabanki da
daukakardakikasamu kozansamisukuni
yau...wallah nafisa natausayamiki sosai.
BABI NA BIYU Da na karasa makarantar
primary sai yaya hussaini ya kaini wata
makaranta a wajen sabongari na zana
jarabawar common entrance ta shiga
makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai
naci jarabawa aka turani makarantar da na
zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya
karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden
makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya
barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo,
gashi bansan kowa ba a makarantar amma
daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai
na fara jin dadin rayuwar makarantar.
Jama'a na sona saboda yadda nake da
fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don
haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina
da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar
nan da nan malamai ma suka sanni saboda
kwazona da wayo, ga iya magana.
Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji
hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu
sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min
siyayya ba da biyan kudin makaranta ba
kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere
ba kakkautawa abida take haihuwa,
'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza
abubakar da umar, sai ta haifi mace
mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta
goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu,
cefane ya karu, farashin abinci ya karu,
gashi an kara kudin makaranta ya kusa
ninka na da ma. Daman duk sanda zan
koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya
harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar
da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai
ya bani hakuri cewar zai mayar dani
makarantar gwamnati ta ;yan mata dake
shekara. Dole na koma makarantar shekara
naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai
na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa
kokari saboda dana sami horo a FGC a
wajen yaran kabilun da basa jin hausa da
yaran hausawan da suka sami horon turanci
tun daga primary. Ajin kimiya na shiga
(science class) har Allah ya kaini aji shida
aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko
muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu
makarantun ni nake tsayawa
makarantarmu, idan bana nan babau abinda
yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu
tana alfahari dani, kullum tana kwatance
dani saboda kokarina. Da muka gama
makarantar ita da malamai sai da sukayi
takaicin rashina saboda ba'a sami madadina
ba.
Bayan gama makarantata da wata uku
yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani
kudin mota da guzuri na zuwa shagamu,
saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa
da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani.
Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da
tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu
daga cikin yayyena sun murmutu duk banje
ba. Ina samun wasikun kanwata
munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta
sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min,
ta shaida min cewar an cire ta daga
makaranta tana secondary aji 3 anyi mata
aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya
hussaini ya saka a mota zuwa shagamu,
dana isa garin shagamu a tasha na hau
acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba.
Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba
sai daga baya suka gane ni, sunga na girma
nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke
ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani,
cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya
dangi na kusa dana nesa har sai da naji
kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu.
Na ziyarci gidan kanwata dake agege a
lagos anan take aure, rayuwarta abin
tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da
dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar
hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka
daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda
asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta
iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos
yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa.
'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin
halinda na same ta kusan dukka kayana na
sakawa na bata kyauta, sannan na hada
mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda
dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu
na bata dukka kudin mota na komawa ta
kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da
nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da
iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don
munsan zamu dade kafin mu sake haduwa.
Na dawo kano jakata kwalam babu komai
duk na rabar da kyana kuma da masu kyan
na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin,
yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo
na dinga karancin kaya duk sun ragargaje
dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan
kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi
garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban
ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai
dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba.
Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan
abida in saka inje, ina dawowa in cire mata.
Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa
yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki
iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi
mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya
'yan abida suna bugun cikinsu suna
tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar
na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai
da ta wuce kan matan gida ta koma wajen
mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana
hussaini, suka ce masa bai dace in dinga
arar kayan abida ina fita kofar gida ina
tsayawa da samari ba, ina yawo da
kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a
duhune sai a zaci abida ta fara bin maza.
Sukayi ta zuba masa bayanan da dole
hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi
mummunan baci.
Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a
kwance yace min in kira abida itama ta
shigo nan dakin yana da magana da ita.
Mukazo muka durkusa a gabansa muna
karkarwa saboda yadda muka ga ransa a
bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya
umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta
kuskura tayi masa karya akan abinda zai
tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya
yi mana tambayoyin. Muka yi masa
alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti
karya ba. Cike da fargaba mai tsanani
muke sauraron abinda zai fada mana. Ya
cewa abida da gaske ne aisha farida tana
aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai
abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna
ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai
firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da
nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace
eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da
ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta
hada kayanta ta tafi gidansu.
Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe
mata ba laifinta bane nice na tambaye ta.
Nima din ya yafe min na daina daga yau.
Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana
tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni.
Munafukan matan gidan ne suka zo suka
kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci
sai fada yake yana zaginmu wai sai mun
harhada kayanmu mun bar masa gidansa.
Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi
dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun
daga lokacin baya raga mana, komai mukayi
sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe.
Sai na daina fita koina , koda yaushe ina
fama da dinkin yaga da zare da allura.
Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa
abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya
amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta
zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara
yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta
bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje.
Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye
tace ka yafe mana laifukan da muka maka,
munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya
hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu,
rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada
maka bane halin da ake ciki kada ranka ya
baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki.
Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta
kakaf a shagamu saboda tausaya musu da
tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo
bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya
fita wajen kawayenta shine nake bata aron
kayana ta saka tana dawowa take cirewa,
bansan abinda 'yan gulma suka fada maka
ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki
mataki cikin fushi.
Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai
duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min
halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da
wasu suka fada min a waje? Kinsan irin
zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman
saka ido ne, duk shige da ficen mu akan
idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar
ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya
bata naira dubu biyu yace ta bani inje in
sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari
takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu.
Abida mace mai hakuri da tsananin wayo,
ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa,
tabbas macen da bata da hakuri da wayo
ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da
kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai
yaji kunya yazo yana lallaba mu.
DUK KYAN TAKALMI 5
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna
musbahu, lungun mu daya dashi kowa
yasan mu tare, yana sona sosai nima haka
saboda yana kula dani. Tun sanda na gama
sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi
zancen aure sai aka sami matsala daga
gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar
kanwarta take so ayi musu auren gida, shi
kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta
tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe
ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa
gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa
jamila kawata ce ajinmu daya a shekara.
Musbahi ma yaji labarin duka dana sha
saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi
guda daya da atamfa ya hada min da naira
dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada
in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa
ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada
masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi
min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba
da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo
gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da
mu dage da addu'a Allah Ya karkato da
zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi
auren dani.
Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya
fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace
idan ya sami kudi zai saya min form din
jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya
karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu
kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin
mota da kudin sayan handout, gashi dole
sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya
gasgata zancena yaga shima bashi da halin
da zai dauki nauyin duk wadannan sabida
dan abinda yake samu ba mai yawa bane.
Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da
yawa suna samun kudi a business center
yake aiki, suna typing a computer, suyi
kalandu ko meme. Sai yace to zai samo
min management in fara, nan ma nace
bana so nafi son inyi schl of nursing saboda
ba ruwana da neman kayan sakawa, suna
da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara
jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa
akayi masa sallama da yayana hussaini ya
kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min
da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya
amince yayi masa godiya. Musbahu da
yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk
kudaden da ake bukata na shiga
makarantar koyar aikin jinya ta malam
aminu kano dake unguwar court road.
Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne
muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe.
A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa
court rd akan acaba saboda idan nace zan
hau bus zan bata lokacina zanyi in makara.
Kudin acabana kit da kit babu canji wata
rana ko purewater zan sha sai dai
kawayena su saya min. Duk da idan za'a je
sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana
binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni
kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi.
Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata
gajiya da taimakona kuma duk sanda tace
muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na
gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani.
Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro
uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai
ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna
nuna min bakin hali daga baya kuma in
dinga jin kananan maganganu cewar na cika
san banza kullum bana fitar da kudina ina
sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai
dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi
dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo.
Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da
fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf
dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin
guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari
yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata
iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai
dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text
book) babanta yana saya mata duk
tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai
hazakar karatun ba ita ba.
Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah
Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da
wata rana ma ba zanje makaranta ba
saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi
bashi da kudi sai yace in hakura kada inje
makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma
bana so inyi fashi, da kudin kitson nake
harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar
bashi da tsada, kan manya naira talatin ko
arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma
ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina
ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a
ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya
wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan
da harshena a koda yaushe. Babu wanda a
cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu
taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun
fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da
sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu
ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta
su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa
gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a
abkin gate ne mu rabu idan an tashi.
Bana jin dadin rayuwata a wannan
bangaren saboda bani da wata
takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin
matsalolin da suke addabata. Kawata guda
daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata
wato matar yayana abida. Muna zama ni da
ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna
matsalolinmu, koda yaushe ina samun
nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta
bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina
da shawarwari, sai inji sanyi a raina,
tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno
min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da
walwalata, ni burina guda daya ne shine in
gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina,
in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar
ma da tafi damuna shine zaman cakudi a
gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa,
babban burina ba wuce inga mun bar gidan
nan da umguwar mu canja gida ko haya ce
dai mu kama gidan da muke mu kadai.
Dakina daya da yara, ga dakin dan karami
mun cunkushe gashi su dukka yaran abida
fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake
yin wani sallar sannan in shimfida. Har
yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen
shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan
'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a
birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar
banza, ban taba sha'awar makalewa gidan
kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike
talaucina na kama kaina bana sha''awar
kayan wani. Daga makaranta sai gida, a
gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya
abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin
girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan
unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai
ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin
fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe
su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a
iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance
mai butulci ne.
BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da
misalin karfe daya na rana muna cikin a
sibiti, a bangaren marasa lafiya muke
wadanda aka kwantar dasu sakamakon
wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna
biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam
tana nunnana mana yadda ake aiki, domin
neman karin bayani sai tace bari ta hada
mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin
daukan darussa ne sabida naga kujeru ne
zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar
yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim
imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin
tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza
biyu, mace daya da alama sunzo sunyi
masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan
da basu gane ba. Bayanai yake yi musu
cikin harshen turanci kai kace baturen
america ne, kalmomin kimiyyar (botanical
names) da yake ta ambato yana jerowa layi
layi da ka ba tare da yana duba littafi ba,
kai kace shine ya lakaba musu sunan don
ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa,
daddada take sake shiga kunnuwanmu sai
duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli
fuskar mai muryan nan daddada.
Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don
muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna
kokarin fitowa sun gama daukar darasin.
Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai
daddadar muryar nan, keyarsa kawai na
fara hangowa daga nesa sai na tabbatar
bakar fata ne dan uwana saboda ban hango
jan kunne ba da farin gashi irin na turawa
ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na
hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana
sanye da bakaken kaya riga da wando
(suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki,
ya daure wuyansa da jan kyalle wato
necktie. Dana matso ciki sai na fara hango
gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na
fara hangowa mai dauke da launi mai
tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a
duniya wato hasken duhu (chocolate color).
Ko dana sake samun daman na matso kuda
dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato
idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai
naji wata mummunar fadywar gaba ta far
min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke
kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi.
Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin
wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar
ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da
wasu gashin ido da gashin gira masu yawa
da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai
kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da
kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube
mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da
take wajen sai dataji a ranta dama ace
wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa
maza ma sai da suka raya a ransu dama ace
sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana
ke hango gefen fuskarshi ban hango komai
ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi
gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa.
Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura,
bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama.
Yayi kama da irin bakaken turawan nan da
ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama
da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne
suka hadu suka same shi bakar fata da farar
fata.
See Translation

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge

Please Login or Register in order to submit comment