Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita sai dai hakan in ya tuna ya ya zata ɗauke shi,don tana girmama shi.

Sannan ya kan yi tunanin in har ya kai ga saduwa da ita to zata iya mutuwa. Na shi zaton rashin saduwar da bai da ita ba ne yasa har yanzu bata mutu ba. Yana ta tunani bai ma san ta gama komai ta zo ta zauna kusa da shi ba, tana ta kallonshi zuciyarta tana son gano me yake tunani, fuskarshi take kallo yana da ƙyau Uncle,ta raya ma ranta, gashi mai tsafta da son ƙamshi. Uncle ɗan gayu ne tsawonshi yana burgeta,ringing ɗin wayar shi ce ta dawo da shi daga tunaninshi da yake yi, itama haka. Firgigit suka dubi jt, cikin cinya A'isha ta saka kanta duk kunya ta rufe ta, Uncle ya kamata tana kallonshi.

Washegari Jummai ta zo tana son yiwa A'isha kashedin gulmar da ta soma kawowa gurin maigidan, sai kuma ta same shi a ɗakin,don haka sai ta juya zancan da cewa,dama nazo ne in baki haƙuri,kan abinda su Suwaiba suka yi miki, insha Allahu ba zasu ƙara ba. A'isha ta ce, "Ya wuce ma." Alhaji Saddiƙ ya ce, "Haba Jummai,ki daina damun kanki,ai ni ma dai nayi musu barazana ne, amma ba wai zan kore sun ba ne. Cikin sanyin jiki ta ce na gode, ta fita. Tana fita ta banko ma ɗakin harara, sannan ta ce da sannu zaku ga aya in dai nice Jummai.

Ranar juma'a, A'isha suka nufi jihar Jigawa cikin motar Uncle (Annaconder) Jabir direban shi na Ofis shi ne yake jan su.

Yafi son tuƙin Jabir don ya san titi, suna zaune a bayan motar, harkokin shi kurum yake yi a cikin laptop tare da abokan kasuwancinsa, A'isha kam tagumi ta zabga, murna ce fal ranta Allah yasa Uncle ɗinta ya baro ta can har hutunta ya ƙare. Kai yau zata ga su Ummanta,can ta soma hamma, kafin sukai Kano tuni bacci ya yi awon gaba da ita, Uncle ya kalle ta,ta jingina kanta da gilashin mota,ya yi ɗan murmushi, sannan ya ajiye laptop ɗin shi gefe sannan ya kamata ya ƙwanto ta a jikinshi,yana ƙoƙarin gyarata ai tuni ta gyara kanta. Juyo da fuskarta tayi saitin mararshi ƙirjinta yana ƙwance saman cinyoyin shi har ma yana jin tudun ɗan ƙirgan danginta akan cinyarsa hannunta ɗaya yana kan kujera ɗayan ko yana ɗayar cinyar ta shi, sannan ta ɗan takure kamar tana jin sanyi. Nan take ya ɗauko babbar rigar shi ya rufa mata, sannan ya ce, "Jabir rage ƙarfin (A.C) ɗin nan. Jabir ya ce,to ranka ya daɗe, haka suka yi ta ƙwararar hanya har suka isa Kano, Uncle yana son fita ya ƙara masu Friend tsaraba Amma baya son ya tashi, Beby don haka sai ya ce Jabir su bi ta cikin gari kai tsaye ya wuce jifatu suna isa ya ɗibo kuɗi ba tare da ya ƙirga ba,ya ba Jabir ya ce ya shiga cikin jifatu ya lissafa mishi abubuwan da yake so.

Bayan ya dawo da kaya niƙ-niƙi, yaran shagon da wasu suka loda a bayan motar, sannan Jabir ya shiga. Ya juyo ya miƙa ma Uncle sauran kuɗin tare da cewa, gashi maigida, kuɗin sun rage. Kasa a aljihunka Jabir muje Allah dai ya sauke mu lafiya. Jabir ya ce Amin,. Sannan ya ce "Na gode maigida, Allah ya ƙara buɗi." Ya ce "Amin" suna tafiya ta sake yin juyi ta gyara ƙwanciyarta, sai dai numfashinta da ke sauka ka saitin cibiyarshi,yana sa shi jin wani yanayi, ya jingina kanshi da kujera ta baya, ya lumshe idanunshi, kasa daurewa ya yi,ya lalibo tafin hannunta ya saƙala cikin nashi. A hankali yake murzawa,nan ta yi miƙa tare da juyawa rigingine. Sai taji duk ta takura, don haka ta buɗe idanunta a hankali gami da lalubawa ta ji ko kan gado take. Sai taji ta damƙo cinya,da sauri ta tashi zaune ta kalli jikinta,tana rufe ne da rigar Uncle,nan take ta tuna cewa a cikin mota suke. Shi ko ya ce, sleeping Beby kin tashi? Kunya ce ta rufe ta, har ma ta kasa kallonshi, ta kifa kanta a cinyarta, ya ce, "Beby kenan, gaskiya kin shari bacci,ko dai jiya saboda murnar zuwa gida ba ki runtse ba ne?" A zuciyarta,ta ce "kamar Uncle ya sani, amma kunya ta hana ta ɗagowa a haka suka ci gaba da tafiya hannunta cikin nashi in ta ɗan ɗago da kai sai dai ta kalli yanda suke wuce ƙauyuka da dajika, da ya ɗan murza yatsun sai ta kuma sunkuyar da kai cikin cinyarta tana son yanda yake mata da yatsun in yana yi ta kan ji wani irin abu shi yasa ko ya riƙe hannunta bata ƙwacewa.

Jummai ko ba ƙaramin murna ta yi ba da wannan tafiyar tasu. A cewarta, Allah ne ya dube ta da idanun rahama ya sa su wannan tafiya, domin koda yaushe cikin lissafin ya ya zasu tafi Nijar ɗin suke tunda ƙwana za su yi ƙila ma ba ɗaya ba, kuma ta san Uncle ba zai taɓa barinta ta ƙwana bikin ƙawa ba,balle ta mishi ƙaryar cewa ƙawarta ce zata aurar da ƴa, dangin su ɗaya balle ta ce bikin danginta zataje,ya kuma san dangin ubanta duk ƴan Katsina ne, cikin wannan halin ne ya ce mata zai yi tafiya zai kai A'isha gida.

Don murna har da turamen zannuwa ta ba A'ishan,wai gashi ta kaima mahaifiyarta,da zasu tafi kuwa rakiya har mota. Dama sun gama shirya ta su tafiyar ita da Aminiyarta,don haka suna tafiya itama ta suri jakarta ta kira direban su ta ce ya kai ta gidan Aminiya wato Hajiya Kari, daga can suma suka nufi Nijar.

A'isha da gudu ta shiga cikin gida, tana kiran Ummata! Ummata! Tsalle ta yi tare da ɗane Ummar tata wadda ke ta kujuba-kujubar haɗa musu abin sauka, kafin su iso. Gefanta Hauwa ƴar maƙotansu da ke taimakon ta da aiki ce, Umma ta ce "yau ku ji mu da ɗiya, A'isha an girma ba'a san an girma ba?" Cikin murya shagwaɓa ta ce, "Kai Umma wanne girma nayi? Umma ta tsaya tana kallon ƴar Tata, duk da bata ƙara girma ba ta ɗan ciko,idanu sannan fatar ta ta murje gwanin sha'awa, sannan ta ƙara haske. Ta ce, "To ina ki ka bar maigidan naki?" Ta ce Uncle yana waje Abba fa? Umma ta ce "tunda ya fita sallah bai shigo ba,muje ki amshi makullin sashen baƙi ki je ki buɗe mishi kafin Abban naki ya zo," ta ce to,da gudu ta sheƙo tazo tana buɗe ƙofa, shi kam Uncle kallonta ma yake yi yana dariya......



#######
[12/9, 21:27] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 3*


Bai taɓa ganin tana murna irin haka ba,ta buɗe sannan ta iso gurinshi "zo ka shiga Uncle" ta shiga ya bi ta, ta ce "Uncle bari na kawo abinci." Ya ce "Haba Beby daga zuwa? Bari dai mu sauke nauyin dake kanmu,watan mu yi sallah. Ya zauna tare da ɗaukan waya bari na ce Jabir ya shigo shima tunda da toilet nan sai mu yi sallah ta ce, to ya ce yau kam Beby sai murna ko? Anga Umma, ta fita tana dariya.

Bayan su Abbanta sun dawo nan ya shiga gurin amininshi sirikin shi kuma maigidan shi ta fannin aiki,nan suka shiga hirar yaushe gamo A'isha ce ta kawo musu abinci ita kuma ta koma gida yau kam murna ba sauƙi gata cikin family ɗin ta tana cin abinci ƙwano ɗaya da Ummanta, gefanta ga su Jafar da Munnir ƙannanta, dole ne ta yi murna domin ba ta yi zaton zata sake zuwa wannan gidan ba,ga zatonta ta yi banƙwana da gidan har abada. Yini sukayi zaune da Ummanta duk inda Umma ta yi A'isha tana biye da ita, tana ba su labarin makarantar su,ƙawayanta su Samira da kuma tsaruwar makarantar,wata dirama kuma sai da dare,ta haye gadon Ummanta ta ƙwanta, Umma ta dube ta, tashi mana A'isha ki je gurin mijinki,ta tashi zaune in je in masa me? Umma ta ce kin ji shirme bangane ki je ki masa ba,ta koma ta ƙwanta nafa riga ya na kai musu abinci, Umma ta ce to ba za kiyi mishi sai da safe ba? Ta ƙara jan rufa tare da cewa zai kira waya.

Shi ko suna can suna shan hirarsu da Abba, goma dai-dai sun gama kallon labaran ƙasa. Abba ya miƙe tare da bashi hannu gami da cewa friend mu ƙwana lafiya,bari na turo maka A'ishan, wani iri Uncle ya ji, ya ce a'a friend ka barta ta kwana gurin Ummanta, Abba dai bai ce ƙala ba, ya wuce yana shiga ɗakin Umman ya same ta ƙwance, Umma kuma tana ƙoƙarin shiga wanka, ya ce Ummansu ya ya zaki riƙe ƙawallin ta ki ki hana ta zuwa gurin mijinta?" Ta ce,ka ganta nan ba yanda ban yi ba,ta tafi ta ƙi wai zasu yi waya, gashi nan har ta yi bacci, ya ce A'isha! A'isha ta ce,Umm, cikin yanayi na bacci ya ce ke tashi maza mijinki yana kira,ta zuro ƙafafunta ƙasa sannan ta ce wash Allah na, duk gajiyar hanya ta isheni,ta fita ta nufi ɗakin baƙi,shi Jabiru yana can gurin Yaya Abdulrahman, ta ƙwan-ƙwasa ƙofa tuni shi Uncle lokacin ma ya kulle ƙofa yana saka kayan bacci duk jin shi yake a takure shi yasa ya so ya sauka a Hotel amma Abba ya ƙi shi nauyinsu yake ji ya zo ya buɗe ƙofar ya ce a'a Beby ba kiyi bacci ba? Cikin yanayin shagwaɓa ta ce, "To ba kaine kasa Abba ya tasoni ba,?" Ya ce muje in rakaki ki koma, har bakin ƙofar ya rakata. Koda ace yana ƙwana da ita to ai ya haƙura a gidan su komai fitinar shi ya shafi kumatunta sai da safe Bebyna,ta ce to mu ƙwana lafiya.

Ɗakin Ummanta ta shige ta haye gado sai da Umma ta fito bayi ta ganta ƙwance ta ce, a'a dawowa kika kuma yi? A'isha ta ce don Allah Umma ki bar ni Allah kuwa shine ya ce ba kirana yake yi ba,in zo in ƙwanta, Umma ta ce to ai shi kenan.


Su Hajiya Jummai,ƴan Nijar tunda take bata taɓa shan wahala irin ta yau ba. Musamman da yake motar haya suka bi, amma ita wannan baya gabanta,tata damuwar bata wuce su isa yau lardi ba, inda zasu samu bokan da aka yo musu ƙwatance,tata damuwar kenan. Sai guraran goma saura suka shiga ƙauyan. Yanda aka ƙwatanta musu haka suka bi. Sun iso gidan bokan wanda yake gida ne na kara,an sauke su da hura. Bokan Bororo ne, irin masu kitson nan haka ma matarshi sam baya jin Hausa don haka dole su ƙwana a nan kamar yanda ya ƙwatanta musu,in gari ya waye za'a samu wanda zai musu tafin ta,sai dai daga Jumman har Karimar sun ƙwana ne cikin ƙyan-ƙyamin gidan da komai ma,don ma sun riƙe ruwa, can hantsi ya ɗaga me yin tafinta,ya zo nan suka sanar da shi buƙatar su, Jummai ta ce tazo ne saboda tana son a kashe kishiyarta, sannan ta ringa juya mijinta yanda taga dama, sannan tana son in da hali ta haihu, bayan mai tafinta ya sanar da shi komai sai ya tambayi sunan kishiyar da mijin,nan ta sanar da shi, bayan ya zuba tsafin ya kuma zubawa, ya ce kafin wannan ta kashe wasu rayukan ko? Mai tafinta ya tambaye ta, bata ji shakka ba,ta ce ƙwarai,ya girgiza kai sannan ya ce, to aikinta yana da matuƙar wahala,don ita wannan ta sha banban da sauran tana da kariya sosai, sannan yaga wasu abubuwa da take yawan kira tana samun tsaro daga abin bautarta. Sannan koda yarinyar zata mutu to fa ba ƙwana kusa ba,don tana da tsawon rai. Koda aka mata bayanin ta hau zufa ta ce ka gaya masa in ma batun kuɗi ne kada ya damu,in har za'a kashe min ita ko nawa ne zan bada, kace da shi tun daga Katsina fa muke don munji labarin aikinshi yana ci tamkar yankan wuƙa. Kada ya nuna kasawar shi mana, inji Karima. Jin haka sai ya ce shikenan. Nan ya shiga haɗa musu kalolin nashi surkullen, sai da suka sake ƙwana sannan suka kamo hanya.

Shiko Uncle duk jin shi ya yi takure, shi yasa gari yana wayewa ya ce to fa shi zai yi haramar komawa,in an yi kwanaki zai dawo kafin hutunsu ya ƙare, da ƙyar Abba ya yarda, don cewa ya yi su juya tare ai an gaisa, lokacin da ta je ɗakin don suyi sallama,tuni ya gama shiri,yana shafa turare.

Cike da murna ta shiga tana cewa, Uncle wai zaka tafi? Ya ce "Eh, Beby shi ne ki ke murna? Don zan tafi ko?" Ta ɗan canza fuska zuwa yanayi na tausayi, ta ce "Ayya, Uncle ba wai don zaka tafi ba ne,naga ba mu yi zaka barni ba ne" Ya ce "Naga ya dace ki ɗan yi ƙwana biyu ne,zan yi kewarki da zoɓonki da ruwan da ki ke bani kullum." Ta yi ƴar dariya, "Nima ai zan damu da rashin ganinka." Cikin mamaki ya ce, "Don Allah da gaske ne za ki damu da rashin ganina?" Ta rufe fuska, ya kama hannunta yana murzawa, zan rinƙa kiranki ko yaushe kin ji? Ta ce to Uncle,yasa hannu cikin aljihu ya ciro kuɗi dami ya miƙa mata gashi saboda kashewa. Ta zaro idanu,haba Uncle, sun yi yawa gaskiya ba zan amsa ba,ya ce riƙe in zaki dawo sai ki sayi me kika ce sunan? Corry ɗin nan? Ta ce Amrif an fi samun shi a Kano ne, ya ce to in zamu koma in nazo sai mu tsaya mu siya. Ta ce, "To." Ya ce,in kin dawo ke ce zaki cigaba da min girki, kafin hutunku ya ƙare,ki fa koyo wasu ina son irin su ɗanwake,waina,burabisko,dambu kin dai ga ne,abincinmu na gargajiya ko? Ta ce "Eh,ai dama fa duk fa na iya su, yasa tafukan hannunshi ya riƙe kumatunta,ki kula da kanki,kin ji Bebyna? Ta ce, to sai naji wayar ko? Ya ce, to Bebyna ya shiga ya yi sallama da Umma tana ta godiya, Abba da A'isha zuwa su Abdulrahman da su Jafar sun yi mishi rakiya har mota. Jabir ya ja mota suka yi gaba,ga mamakin A'isha sai ta ji wani irin kewar Uncle cikin zuciyarta, ta ce Allah ya sauke mata da Uncle ɗinta lafiya. Lokacin da Alhaji Saddiƙ ya iso gida yamma ta yi kis,don ma basu tsattsaya a hanya ba, rashin samun Jummai a gidan ya yi mugun ɓata mishi rai,shi dai wannan ɗabi'a me yaƙi da addini,da matan zamanin suka ɗauka tana ɓata mishi rai, ace mace ba zata nemi iznin miji ba,in zata fita saboda rashin sanin hukuncin musulunci,ko a waya ba zata kira ta nemi izini ba,ya samu su Suwaiba sun cika gidan da kiɗa tare da ƙawayansu,sun sha wanduna suna ta rawa ga ƙwalaban totolyn emzolyn nan zube a ƙasa, ranshi ya ƙara ɓaci ya shiga ya tarwatsa su tare da yi musu tatas. Ya ce, ina Jumman da ta ɗaure muku gindi? Cikin maye Sofy ta ce,ta yi tafiya tun jiya, al'ajabi ya cika shi,ya nufi ɗakinshi ranshi yana matuƙar zafi. Ya zauna bakin gado ya soma kiran layin ta, ga mamakin shi tama ƙi tafiya,a ƙarshe ma sai aka ce a kashe layin yake.

Wasa-wasa har wayewar garin ba ta babu labarin ta, kazalika ci gaba da neman layinta ko zai samu,shiru kai daga baya sai ya soma tunanin ko dai ta ɗan fita unguwa ne, ta samu matsala ko mota ta kaɗe ta haka? Yin wannan tunanin ya saka shi kiran danginsu, har da nata wato makusantanta,yana sanar dasu rashin ganinta tun jiya. Ya san ba nisa tayi ba,don ba ta fita da mota ba, kuma bata saba tafiyar ƙwana ba ma in dai ba ƙasar ta bari ba, komai dangatakar ku da ita ba zata taɓa zuwa ta ƙwana don zumunci ba,nata ganin ƙasƙanci ne ta ƙwana gidan da suka fi su kuɗi, amma gata can ai ta ƙwana a bukka,nan fa hankula suka tashi.aka shiga neman asibitoci,ranar basu iso ba sai daf da magriba,kai tsaye gida kowacce ta nufa, lokacin da ta iso gidan yana cike da dangi shi kuma yana daga harabar gidan in da wani ɗan sandan ciki yake neman ƙarin bayani daga bakinshi.

Sai kurum gata ta shigo, ganin maigidan yasa ta ji faɗuwar gaba,don sam ba tayi zaton zai riga ta dawowa ba, amma da yake tana zaton yau ya dawo,tun da haka suka yi dashi, sai ta isa gurinshi tana cewa "Sannu da zuwa Alhaji, har ka iso? Na ɗan fita ne" bai iya ce mata komai ba, sai dai ya dubi wannan (C.I.D) ɗin ya ce shi kenan ma gata nan ta dawo.

Suka yi sallama ya tafi, shi ko ƙin shiga ma gidan ya yi,yana tsaye cike da mamakin baƙin halayen da Jummai ta zo mishi da su yanzun yi,abin har ya kai ta da yin ƙwanaki. To ina taje? Ya na nan har aka kira sallah, ya shige masallaci, ita ko tana shiga cikin gidan ta same shi cike da dangi ana ta jaje. Turus ta ja ta tsaya, tana son sanin wanene ya mutu? Shin ko dai A'isha ce har ta mutu kafin ma ta dawo? Ta yi amfani da maganin? Kai in ko haka ne lallai zata sake komawa ta mishi sabon biya,don ya cancanta,haba shiyasa taga Alhaji a waje babu fara'a,ya ma kasa amsa ta,ta dubi jama'a sannan ta ce, "Haɗarin mota ne?" Nan kuma sai taji sun ɗauki salati, suna tambayarta a ina abin ya faru? Sai kuma ta yi sororo tare da cewa,wai dama me ya tara su haka? Nan suka shaida mata labarin ɓatanta,nan fa ta hau masifar cewa inji uban wa? Ita da taje biki? Shi ne za'a ce wani ta ɓata? Wata Yarsu ta ce, to mu dai maigidan ki ne ya yi waya tun jiya kuma sai nemanki ake yi cigiya gidajen radiyo da na talabijin. Ta ja tsaki, "To ni biki naje, shima bayanan ne kuma na kira shi a waya ban samu ba." Nan dai kowa ya tashi yana Allah to ya kiyaye gaba, gaskiya ta ji haushi don duk tasa ma ranta cewa A'isha ce ta mutu.

Sai bayan da kowa ya tafi sannan ta kira su Suwaiba,tana tambayarsu yaushe ne Alhaji ya dawo? Suka shaida mata tun jiya, kuma ya tambaye su sun ce ta yi tafiya. Cikin ɗar-ɗar ta zauna,shi kam bai ma shigo gidan ba da ya yi isha'i gidansu Hajiyarmu ya nufa, don ya sanar da su dawowar Jumman,nan har yake yiwa Hajiyarmu complain ɗin halayen da Jummai ta shigo da su, ya ce ada bai san ta da duk waɗannan halayen ba, sai yanzun.

Hajiyarmu kuwa haƙuri ta bashi tare da cewa, zatayi mata magana. Sai sha ɗaya saura sannan ya nufo gida,tana ta gadin zuwan shi,don haka tana kallon shigowarshi, sanda ta shiga ɗakinshi yana watsa ruwa,ta zauna. Yana fitowa da ya ganta fuska ya ɗaure tamkar bai taɓa dariya ba,ta rasa ta ina zata soma mishi magana,can dai ta daure ta ce, "Alhaji ka min haƙuri,na san ban ƙyauta ba, amma wallahi na kira wayarka taƙi shiga,dama wata ƙawata ce dake Kaduna ta ke aurar da ƴarta," ya ce "to yanzun sai ki koma Kadunan," ta zaro idanu, Haba don Allah,ka yi haƙuri Alhaji, nayi laifi, ya eh da haka ni ne dama sarkin haƙuri shiyasa sai ki min abu ki ce inyi haƙuri to na gaji ba zan ɗauki yawon gantali ba, don haka sai ki koma".

Tayi saurin zubewa gwiwa biyu a ƙasa,don Allah ka rufa min asiri, insha Allahu ba zan ƙara ba,don Allah.

Ya ce ,don Allah ni tashi ki bar min ɗaki,shashasha wadda ba ta san darajar kanta ba,bare na aurenta,ke kenan yi nan yi nan,gara ma kin canza hali,don wallahi ba zan ɗauki wannan rainin wayon ba. Ta fita dai tana mai jin zafin abinda ya yi mata, amma cikin ranta tana cewa,ƙwanan nan zaka zama zauna nan in Allah ya yarda,duk wannan cin mutuncin da ya yi mata sai ta rama.

Shi ko ƙwanciyarshi ya yi tare da yi mata addu'ar Allah ya shirye ta, ita ko A'isha tana can gurin Ummanta, suna shan hira, tana ba Umma labarin yanda Uncle ya ke kashe mata kuɗi,ko da Ummanta ta ce, to suna zaman lafiya da abokiyar zaman tata? Cewa ta yi suna yi har ma take bata labarin zannuwan da ta ba da a kai mata, Umman ta fahimci ƴarta bata zuwa gurin mijinta a cikin hirar tasu, inda take cewa, ita sau ɗaya ta taɓa zuwa ɗakin Uncle ya ce ta gyara mishi shimfiɗa, sai kuma taga shimfiɗar a gyare.

Umma ta ce,ai yanzun ke don rashin hankali ba zaki shiga ɗakin mijinki ba duk ranar girkin ki ki gyara safe da yamma?" A'isha ta yi shiru, Umma sai faɗa take mata, ta ce "Lallai yarinya in ko haka za kiyi,za kuwa ki zama koma baya gurin mijinki,ai wannan gyaran ɗakin shi ne zai sa yaji dake fiye da yanda ki ke labari yanzun, duk irin biyayyar da zaki mishi na banza ne in har ba zaki gyara mishi shimfiɗa ba."



######
[12/10, 19:21] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 4*



Aisha ta ce , to Umma shi ne fa ya ce wai ba zan iya ba,wai sai nan gaba. Shiru Umma ta yi don ta san A'isha yarinya ce, amma har da ma shirmenta,in ban da haka yara ma ƙanana waɗanda ba su kai ta ba sun san aure bare kuma ita? Sam ta kula A'ishar ma bata gane me take nufi da gyaran shimfiɗa ba.

Aisha ta ce, to in na koma ai zan ringa yin gyaran.

Kafin ranar dawowarta, Umma ta zaunar da ita ta koya mata shan kayan marmari masu saka ni'ima a jikin mace,duk da yanda Umma ta nuna mata cewa su kankana,shan rake,aya,ayi kununta da dabino shan romon kaza da sauransu,suna saka mace tayi ni'ima. A'isha ba ta gane wacce irin ni'ima Umma ke nufi ba,ga nata zaton jikinta zai yi fresh ko ƙiba zatayi ko ko fari, Umma take nufin zata ƙara? Oho. Ita dai tana can ta soma amfani da su, sai wasu tsumi da dai sauran abubuwan sha na mata, waɗanda basu da illa.

Itama nata gefen Hajiya Jummai ta gama aiwatar da komai nata,wato guzurin Nijar, don haka jiran sakamako kawai take yi.

Ana saura sati ɗaya hutun A'isha ya ƙare, Uncle ya yi mata waya cewa yana nan bisa hanya,don haka ta soma shiri da ya zo zasu juya. Tamkar kada ta tafi ta ji, sai dai wata damuwa tun jiya ta soma jin wata faɗuwar gaba har ta sanar da Umma. Umma ta ce, tayi ta addu'a itama zata taya ta.

Sun tsaya a Kano sun yi siyayya, Uncle dai sai tuni yake mata da Amrif Cory, dariya ta ringa mishi, shi kam ya ce na yaba da ƙamshinsa gami da ɗanɗanonsa, duk tsarabar da A'isha ta zo da ita gurin Jummai ta kai ta ce gashi nan ta raba ta ba kowa.

Hajiya Jummai ta ce, a'a bani da wanda zan ba tsaraba,ki dai aikawa da su Hajiyarmu,ni kuma bari in ɗan samu riɗin.

A'isha ta ce, to da kanta ta ce don Allah Uncle ya kaita ta ba su Hajiyarmu tsarabar su. Sun yi godiya mai tarin yawa, a nanne ma take jin zancan auren Nafisa, lokacin da Uncle suke magana da Hajiyarmu, ashe wani abokin Uncle zata aura, mai suna Alhaji Bello,yana da mata ɗaya da ƴaƴa uku,fatan A'isha Allah yasa lokacin bikin suna hutu, har ma tayi wa Uncle ƙorafin hakan, Uncle ya ce kada ta damu,in tana da rabon za'ayi tana nan to za'ayi cikin hutun. Lahadi tana zagayo wa Uncle ya haɗa komai na makarantar A'isha ya maida ita. Sun maida hankali kan karatunsu yanda ya kamata.

Jummai kuwa, kullum cikin zuba idanu take yi taga ta ina aikinta zai fara? Amma shiru. Nan fa hankalinta ya sake tashi, ta shiga surutu ita wane laifi ta yi? Duk abinda ta yi ba ya ci,da yake an ce duk abinda ka ke yi shi kake zaton kowa yana yi,don haka sai ta bar abin kan cewa suna tufka mata asirine, shi yasa. Yin wannan hasashen yasa ta garzaya gidan Aminiyarta don neman wata mafitar.

Aisha ta zamar mata annoba, bala'i. Aminiyarta ta ce,sake neman wani gurin

Please Login or Register in order to submit comment