Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, zan dai bincika,nan take ta ɗauki waya ta kira maigidan.

"Assalamu alaikum,darling kana ina ne?" Ta tambaye shi.

Cikin murna ya ce, "muna asibiti da A'isha,na manta ban sanar da ku ba, A'isha tana nan asibiti."

"Me ya same ta?"

"Ciki ne." Ya bata amsa a taƙaice.

Ya kira layin Jummai lokacin tana lissafa kuɗin da zata kai ma wasu malamai guda biyu, ɗayan yana mata aiki kan Hadiza, ɗaya kuma kan A'isha. Ta ɗaga wayar cikin raha ta ce, "Maigidana na kaina." Ya ce, "Jummai yau dai Allah ya amshi addu'armu." Ta ce, "Ta me fa?" Ya ce,"A'isha tana da ciki." Da sauri ta miƙe tsaye, "Ci me?" Ya ce,"Ciki." Ta yi ƙoƙari ta saisaita numfashinta,"kai Allah mun gode maka,kuna asibitin ne? Ya ce eh,ta ce gani nan zuwa,ya ce dama na sani Jummai za ki yi murna,ta ce ai faɗa ma ɓata baki. Ya kashe wayar.

Jikinta har rawa yake wajen neman number Hajiya Karima,daƙyer ta samu taga number saboda fita hayyacinta da ta yi,tana ɗauka ta fashe mata da kuka "Na shiga uku!, Shikenan tawa ta same ni,ni nasan tawa ta ƙare."

Hajiya Kari ta ce,"Sakinki aka yi? Ta ce,wane saki ba gara a sake ni ɗin ba da wannan takaici! A'isha fa ke da ciki." "Ciki?" Inji Kari, Hajiya Jummai ta ce "Ciki kuwa," Hajiya Kari ta ce, to share hawayenki,ba sai mun barshi ba, sannan zai zo duniya,tankaɗar da ɗan iska zamu yi ya bi sokawe kawai,ai haka zai zauna yanda baki haihu ba babu shegiyar da zata haifa. Ki shirya zama guri ɗaya a tsautsayine. Hajiya Jummai ta ce, to sai na ganki Aminiya ta, mai maganin kuka na."

Suna gama wayar,ta zabga tagumi a yanzun babu abinda ya fi dacewa face ta bar batun fitarsu, ta koma kan batun cikin nan. Don haka ta soma tattara kuɗin guri ɗaya,tana yi tana magana ita kaɗai cewa take yo in ma ta fitar da ita alhali ga ciki ai nayi ta banza, tunda ɗan shi da ita zai zo duniya. Kaji masu ja da ikon Allah.

A'isha sai da tayi baccin wajen awa biyu sannan ta farka,Uncle dake zaune kujerar gefen gadon ya yi tagumi yana kallon ta,jin hannunta a riƙe ne yasa ta buɗe ido ta kalli ko ina, sannan ta kai dubanta ga Uncle ɗinta wanda ya ke kallonta cike da murmushi, ta ce har yanzun muna asibitin? Ya ce,eh muna asibiti, ta ce Uncle baka je Ofis ba? Ya ce, Ofis sai da lafiya ai Beby. Ta kalli ƙarin ruwan suna min ƙarin ruwa ne? Ya ce eh,ta ce gashi ina son inyi sallah. Ya ce za kiyi Beby,bari ki ɗan ƙara jin ƙarfi. Ta ce to. Ya ƙara matsowa kusa da ita,"kin san ciwon da ke damunki? Ta ce, a'a ya saka hannunshi cikin tafin hannunta ya ce "Beby ashe ɗana ne nake ta neman inda zan saka na sha wuya, Allah ya dube ni da rahamarshi ya sa ni na ɗauko ki tun daga makaranta na saka cikin mahaifarki. Beby don murna yau ji nake tamkar yau aka haife ni, nima zan zama uba,kina ɗauke da cikina ƙwana goma sha baƙwai." Ta juyar da fuskarta gefe don kunya.

Ya miƙe tsaye "Beby kina jin kunya ne? Yana magana yana ƙoƙarin leƙa fuskarta. Tasa hannu ta rufe fuskar, ya ce a'a Beby kada ki cuci ɗanmu,kada ki mishi yanda Hajiyarmu ta yi mini har yau na kasa yarda cewa tana sona kin ji? Ta ɗaga kai alamar eh, amma kanta na ta can gefen, ya ce to gaya min ki yi murna? Ta kuma ɗaga kai,kina son Bebyn? Ta kuma ɗaga kanta, ya ce na gode. Bari na ce ma Likita kin farka,bai ce dasu Nafisa ta farka ba,ya nufi gurin Likitan tare suka shigo da Likitan ya duba ta tare da tambayar inda ke yi mata ciwo,ta ce babu, sai dai jikinta Duk a gajiye,sannan bakinta babu daɗi, kuma tana jin yinwa sai dai ta san in ta ci zata yi amai ne.

Likitan ya ce, yanzun dai faɗa mana me ki ke marmari? Ta yi shiru tana tunani,can ta ce tuwo da miyar kuɓewa,tuwon garin masara. Uncle ya ce,to bari na sanar da Nafisa ta je tayo miki yanzun kin ji? Ta ɗaga kai. Likitan ya ce ya kamata dai ta sha ko ruwan tea ne haka saboda cikinta ya warware.

A'isha ta girgiza kai, tare da cewa,ba zan sha ba,in na sha tea bakina tsami yake yi, Likitan ya ce za ki jira har a kawo tuwon? Ta ce eh, Uncle suka fito da Likita. Lokacin ne ya ce musu ta farka suka shigo.

Nafisa tana cewa,"Maman biyu, Maman biyu" A'isha ta rufe fuska, Uncle ya shiga ya dubi Nafisa "Sister ki je ki yo mata tuwon garin masara da miyar kuɓewa,ya dubi Beby ɗin ya ce, wace irin kuɓewa? Ta ce ɗanye. Nafisa ta suri jakarta,ta ce bari naje na cika aikin Bebynmu. Ta fita tana cewa, sai na bi ta gidan Hajiyarmu na amshi garin,don ba ni dashi a gidana.

***. **** ****

Hajiya Jummai suka yi sallama ita da Hajiya Kari,ɗakin cike da dangin maigidan nata aka amsa musu. Ta shigo tana cewa, sannunku, sannunku fa. Ina A'ishan? Suka ce ga ta nan a ƙwance. Hajiya Kari ta ce sannu kin ji, Allah ya inganta miki. Hajiya Jummai ta ɗora hannunta a goshin A'isha tana cewa Allah mun gode maka, ashe mu ma zamu ga ɗanmu? A'isha ko jin hannun ta yi tamkar an ɗora mata dutse, ita tun fil'azal in dai Hajiya Jumman nan ta zo inda take gabanta sai ya yi ta faɗuwa,don haka yanzun ma addu'a take yi cikin ranta.

Hajiya Jummai kuwa saboda tsabar makirci sai ta kama kuka tana faɗin, ni ƴa su wannan yarinya kin share mana hawaye, shekaru sha baƙwai! Babu ɗa cikin gidanmu." Anty Sadiya ta ce, Jummai ki daina kuka, insha Allah sai kun samu dozin.

A ran Jummai ta ce,tir da maganarki tsinanniya amma a fili sai ta ce,amin Sadiya. Karima ta ce,ƙya koka Aminiya,kukan farin ciki ne" Fatima ta ce, "Nafisa ta daɗe ko in kira ta ne?" Anty Sadiya ta ce,ai Bros ya bita. Rufe bakinta ke da wuya sai gashi da sauri yana ɗauke da cooler, Nafisa tana biye dashi, itama ɗauke da ƙwando da su plate, Jabiru ya shigo ɗauke da ƙwalayan ruwan (EVER) da kalolin juice,ya ajiye ya koma ya shigo da manyan ledoji cike da tarkace

Hajiya Jummai dai suna gefe suna kallon ikon Allah,suna taɓa baki tare da girgiza kai ƙunci cikin zuciya kuwa ba a magana, shi ko maigidan sam bai ma kula da su ba.

Ya ja kujera ya zauna gaban gadon, ya ciro waya ya kira Likitan yana shaida mishi sun kawo mata abincin, Likitan ya ce, gashi nan zuwa. Ya shigo Nurse's ke biye da shi ɗauke da ƙwanonin silver, Likitan ya dube ta da murmushi ya ce, sannu Madam. A'isha dai hannunta na kare a fuskarta,ya ce da Nurse's ɗin bata ta wanke bakinta,ta shi ko? Ta yunƙura kafin ta ankara tuni Uncle ɗin ta ya ɗagata zaune yasa filo ya jingina ta, kunya duk ta rufe ta. Ya amshi ƙwanan daga hannun Nurse ɗin ya ce Nafisa bani ruwa ɗaya a can cikin ƙwalin,ta miƙo mishi ya ajiye ƙwanon kan cinyarta ya buɗe ruwan,ta ce kawo zan iya da kaina. Likitan ya cire mata ruwan da ake ƙara mata. Ta kuskure bakinta, Nafisa ta miƙo mata tuwon nama ya yi wa tuwon zube, Uncle ya amsa ya ajiye mata a cinyarta,ta taɓa baki ta ce,a cire naman,ya ce to Nafisa cire mata naman. Aka cire ta kuma cewa a rage tuwon. Ya ce,ki ci iya cinki, in kuma ba zaki iya ba, bari na baki ko? Ta ce, a'a zan iya sai dariya su Nafisa suke mata.

Ta soma ɗan ci loma ta uku ta ajiye ta ce ta ƙoshi,ya ce, haba Beby ɗan ƙara mana,ta ci kaɗan nan fa zuciyarta ta soma tashi. Da sauri ta miƙa mishi ƙwanan kafin ta ce wani abu tuni ta soma sheƙo amai. Kai kawai ya riƙe yana kallonta,kowa sai sannu ya ke mata,su Hajiya Jummai dai ana ta kallon ikon Allah,da ƙyar aman ya tsaya.

Nurse suka shiga gyara wurin. Ya ba Nafisa makullin ɗakin A'isha ya ce, "Ki ɗauki mata kaya ta cire wannan Uniform ɗin ta amsa ta fita.

Bayan an gama gyara komai, dole sai dai ruwan aka maida mata,jim kaɗan bacci ya ɗauke ta don ya yi mata allurar bacci, cikin ruwan.

Koda aka kira sallar magriba, Uncle ya ce to duk su koma gidajensu. Nafisa ta ce wa zai zauna da ita? Ya ce, shi ne suka sa dariya, tare da cewa, "haba dai" ya ce Allah kuwa. Nafisa ta yi wa mijinta waya ya ce gashi nan ma cikin asibitin. Shigowarshi Katsina kenan daga Kaduna,ko gida bai je ba.

Bayan sun gaisa ya taya abokinshi murnar samun ƙaruwa. Nafisa ta nemi iznin zama da A'isha, jin cewa Alhaji Saddiƙ ne zai zauna, Alhaji Bello ya ce, ya yarda Nafisa ta zauna tunda su Fatima duk suna da yara.

Hajiya Karima ta kira Jummai gefe ta ce,sakarya ki zauna da ita mana in yaso na amso magani sai mu kaɗar da shegen cikin tun daga nan. Hajiya Jummai ta ce,jinina zai iya hawa ba zan baki a ɓoye ba, matsawar zan cigaba da kallon yarinyar da kuma rawar jikin da Alhaji ke yi kanta,wai baki ga dauriyata ba ne wannan zuwan da nayi ma? Ni dai gobe mu shirya mu bazama."

Ƙarfe taƙwas daidai su Hadiza da Hajiya Lanti suka shigo,su da shirinsu ma suka shigo. Hadiza tana ɗauke da kula anyo farfesun kayan ciki wanda ya ji haɗin magungunan salwantar da ciki. Cikin raha Hadiza ta shigo, ina A'ishan ƴar'uwa rabin jiki, lokacin ta farka tana ƙwance.

Nafisa kuma tana sallar Isha'i, shima Uncle yana masallaci. Hajiya Lanti ta ce sannu ƴar nan,kin ji Allah ya raba ki lafiya. Mun yi murna mun yi farin ciki." Nafisa ta idar suka gaisa ta ce, Nafisa ke ce gurinta? Nafisa ta ce,eh, Hajiya Lanti cikin makirci ta ce,haba dai ga ƴar'uwarta ba sai ta zauna ba? Kema sai ki koma gidanki,ki ji da kanki" Hadiza ta ce,ai kam ki tafi kawai". Nafisa ta ce, a'a ai babu komai maigidana ne ya ce in zauna. Hajiya Lanti ta ce, to shikenan.

Hadiza ta buɗe kular hannunta, ta ce ga farfesu na ɗan yo miki ko za kiji daɗin bakin ki." Ƙamshin shi ya doki hancinta, ta ce to na gode." Nafisa ta taso tana cewa,anya za ta ci? Komai ta ci fa sai amai. Hajiya Lanti ta ce "Wayyo, amma kuma kin san ciki sai ki ga in ta ci wani abin ya zauna,in tana so a barta ta ɗan taɓa" Nafisa ta ce to." Ta kalli A'isha za ki ci ne? Ta ce eh, Hajiya Lanti da Hadiza suka kalli juna, suka yi murmushi. Nafisa ta lura da hakan da suka yi don ta gani,don haka sai ta tsargu da wannan girkin,don haka sai ta ce to bari Uncle ɗin yazo ya kira Likitan don ya ce duk abinda ta ce zata ci sai yazo tukunna.



#######
[12/16, 08:36] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 14*



Hajiya Lanti ta ce,ke rabu da su, waɗannan likitocin masu tsirfar tsiya,ba ni plate nan ki gani in bata. Nafisa ta ce,ki dai yi haƙuri mu bi dokarsu kada ta ci ta kuma yin aman su ce sun faɗa mun ƙi ji. Hadiza ta ce, haka ne kuma a bari ɗin. Tana magana tana taɓa Hajiyar alamun ta bari.

Uncle ɗin ne ya yi sallama ya shigo da sauri Hajiya Lanti ta ja baya tana faɗin sannu da shigowa Alhaji, ya amsa da cewa yauwa sannu da zuwa. Suka gaisa har tana durƙusawa. Ta ce,ya ya me jiki? To Allah ya inganta mana yasa a sauka lafiya, ya ce Amin nagode. Hadiza ma cike da fara'a ta gaishe shi, tare da yi mishi murna. Ta ƙara da cewa, insha Allahu ƴan biyu zata haifa,sai a bata ɗaya. Ya ce, Allah ya bi bakinki Hadiza. Hajiya Lanti tana dariya tana cewa,kai waɗannan yara.

Ita dai A'isha tana ƙwance tana jin su. Ya matso kusa da gadon ya duƙa ya ce "Sannu Beby" a hankali ta ce,zan ci naman da su Hadiza suka kawo,da hanzari ya ce Nafisa zuba mata,me su Hadiza suka zo dashi? Wai zata ci. Nafisa ta ce, sai in Likitan ya zo,ɗazun ya ce kada ta kuma cin wani abu sai in yazo. Hajiya Lanti ta ce,ni dai na ce da kun bata,ba lallai ne tayi aman ba. Nafisa ta ce bari dai in kira Likitan.

Uncle ɗin ya tashi, bari in kirashi ta ce zauna kawai Bros,bari na kirashi,ta fita. Ko da ta samu Likitan cikin Office ɗin shi, suka gaisa ta ce mishi,ta zo ne don Allah ya yi ma yayansu magana ba kowa ba ne zai kawo abinci ta ringa ci, saboda yanda ya daɗe babu haihuwa, wasu za su yi baƙin ciki,da samun cikin musamman kishiyoyinta,don haka ya zo yanzun ma an kawo wani nama wai zata ci, kuma ita bata yarda da naman ba,don haka tana son ya hana ta ci. Da hanzari Likitan ya miƙe tare da cewa, Madam nima nayi wannan tunanin,ba zan so wata matsala ta faru ba,na gode da wannan taimakon da ki kai min."

Likitan ya shigo suka gaisa da Uncle ɗin,ta hanyar riƙe hannu. Ya ce,ka ce inzo? Uncle ya ce eh, wani nama ne aka kawo shine take son ci. Likitan ya ce, "Yallaɓai ba zata ci komai ba yanzun ba sai zuwa da safe, saboda wannan ruwan da muke ƙara mata yana tare da abinci,ba ma buƙatar ta ci komai yanzui."

Fuskar su Hajiya Lanti Nafisa ta kalla, sai ko taga sun kalli juna da ɓacin rai. Likitan ya fita tare da cewa,in ka fito ina Ofis,ya ce to Doctor nagode."

Hajiya Lanti ta ce, to ni zan tafi ke zaki jira mijinki ne? Ta ce , to. Tana dubanshi ya ce to jira sai muje ɗin. Hajiya Lanti ta ce to bani cooler in tafi da ita mu ma ci can ko? Hadiza ta ce to ko Nafisa tana so? Nafisa ta ce a'a nagode." Ta ɗauki kular,wai bari ta rakata ta hau mota. Nafisa ta ce , to.

Suna fita shima ya nufi gurin Likita, Nafisa ta koma kusa da A'isha ta ce,ke wace irin wawiya ce zaki ce za ki ci? So kike ɗan cikin muna murna kisa ayi watsi dashi? Baki san su Lanti ba ko? Kar su kuma kawo wani abu ki ce za kici kin ji ko? Ta ce,to. Shima Uncle ɗin naki yasan komai don dai su maza ba su cika ɗaukan irin waɗannan abubuwan da mahimmanci ba ne, likita ya ce baya son kowa ya kawo abu ace ki ci, ya yi taka tsantsan, duk abinda tace tana so ta ci to ya kasance shi ne zai sa waɗanda zuciyarshi ta yarda da su su dafa mata. Uncle ya ce shikenan. Likitan ya ce ko gidan mahaifiyarka kawai ya fi dacewa a dinga kawo mata duk me zata ci,ya ce ƙwarai kuwa na gode insha Allah zan kiyaye.

Hadiza kuwa suna tattaunawa da mahaifiyarta kan cewa, duk wannan Nafisar ce ta ɓata musu shiri, Hajiya Lanti ta ce,ni ba wannan ne matsalata ba, damuwa ta kuɗin da na kashe gurin amso wannan maganin. Kai ina ma wannan cikin jikinki yake,kinga tun cikin asibitin nan sai mun ƙwashi kuɗi. Hadiza ta ce,ke dai bari, Hajiya yanzun ya ya zamu yi da wannan abin? Lanti ta ce wa? Ai tunda ranta na so sai ta ci shi, gobe zan ɗinɗima tunda yau ne aka ce kada ta ci saboda ana mata ƙarin ruwa, gobe da sassafe in zaki taho ki biyo ki amsa. Ki zo mata dashi,sai ki ce wani ne ki kayi. Ta ce, to shi yasa ai na ce su bari na tafi da shi tunda ba zasu ci, tunda ba nice nazo dashi ba,na su zaton ke ce ki ka dafa. Haka ne inji Hadiza, zan biyo, suka yi sallama,ta dawo Hajiya Lanti kuma ta hau mota.


**** *****. ****

Goma dai-dai Uncle ya kula Nafisa tana hamma, A'isha tuni ta yi bacci,don haka ya miƙe ya je bakin A'isha ya tsugunna ya sumbaci kumatunta, sannan ya zo gurin Nafisa ya ce "Sister tashi ki je ki ƙwanta kema sai da safe." Hadiza ma tayi musu sai da safe, sannan suka fita.

A cikin mota take ce mishi "Darling amma ran A'isha ya biya da naman nan ko in yo mata wani gobe tunda tana so? Gashi ance mace mai ciki in ta buƙaci abu a bata in dai da shi kada ta haifi ɗanta da tabo." Ya yi ɗan murmushi, "inji hadisin hausawa ko?" Hadiza ta ce, "Allah gaske ne." Ya ce,to ki kawo mata, amma fa ba lallai ba ne ta ci tunda Likitan bai ce da safe zata ci wani abu,kai ko dai ki barshi kawai ma." Hadiza ta ce, a'a zan mata ko bata ci ba na san mutanan gurin za su ci, ya ce shikenan.

Ranar ƙwana Uncle ya yi yana sallah, ya kasa bacci. Washegari tunda Asubahi ya kira Abbanta. Bayan sun gaisa, Abba ya tambaya ko lafiya? Uncle ya ce, A'isha ce bata jin daɗi ba, tana asibiti. Abba ya ce, "assha gado aka bata kenan?" Uncle ya ce wallahi, amma da sauƙi ba sai kun zo ba. Sannan ka taya ni addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Abba ya ce,ashe? Lallai nayi murna Friend, Allah ya bamu masu albarka. Uncle ya ce Amin. Daga nan ya nufi asibitin don yaga yanda suka ƙwana. Zaune ya same ta tana sallah, gaskiya yaji daɗi sosai,ya zauna har ta idar ta juyo ta dube shi, ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby ya ya jiki? Ta sunkuyar da kai ta ce,da sauƙi. Ya ce ina Nafisa? Ta ce ta shiga wanka. Ya ce,to daƙyau,kema kin yi ne? Ta ce eh, nayi shi ne na ji ɗan ƙarfi. Ya ce su Abba suna gaishe ki,ta ce gaya musu ka yi bani da lafiya? Ya ce eh mana, har ma nace musu kina da ciki." Ta saka kanta a gwiwarta tare da faɗin haba dai don Allah. Ya ce to mene ne? Ta ce,ni ina jin kunya yanzun su Hajiyarmu sun ji? Ya yi murmushi.

"Sun ji mana,tun lokacin da Likitan ya sanar damu."

Ta ce, "Shi kenan ba zan kuma zuwa gidan ba" ya ce "Don me?" Ta dube shi, yanzun kowa ya san abinda na yi na samu cikin kuma? Ya yi dariya, sannan ya ce, a'a ba wanda zai sani,ke da ki ke makaranta, wasu za su ce a ruwa ki ka sha." Ta ɗan yi murmushi don ganin ya maida ita doluwa,ta ce "Ai na san ba'a sha a ruwa." Yasa dariya.

Nafisa ta shigo tana cewa "Bros ka zo kenan?" Ya ce, "wallahi ya ya kuka kwana?" Ina ta tunanin dare? Nafisa ta ce bacci sosai mu ka yi kaga gashi har ta yi wanka,ta yi sallah. Ya ce aiko naga da sauƙi yanzun me zaku ci inje gidan Hajiyarmu in sa ayo muku? Nafisa ta ce,Mama two me zamu ci? Ta ɓata rai Anty Nafisa bana so, Uncle ka ce ta bari fa, cikin murmushi ya ce , Sister bama so gaskiya, ya dubi A'isha ƙyale ta Beby gaya min me zaki ci? Ta ce,da zan samu waina ko irin ɗan waken nan? Ya ce zaki samu ya miƙe, har ya fita. Ya dawo zaki ci farfesun irin na jiyan a zo miki da shi? Ta ce a'a, ya ce shi kenan.

Hadiza ta zo lokacin suna karyawa. Hadiza ta aje mata kular a gaba gashi kin ji ƴar'uwa na yi miki wani ne. A'isha ta ce na gode, yanzun kam na ƙoshi amma anjima zan ci. Ta miƙa ma Nafisa ta ce Anty Nafisa gashi ki sa can gefe kada ku ci min fa. Nafisa ta ce, to A'isha Hadiza kam daɗi ne ya rufe ta.

Hajiya Jummai kam an bazama nema,an nemo kuma an samo,ana kan aiwatar wa. Satin A'isha ɗaya a asibiti, ta samu sauƙin aman. Sai dai kasala tare da tsirfa iri-iri har yau abinci in ba daga gidan Hajiyarmu ba ne bata ci. Hajiyarmu kuwa ko yaushe mai aikin ta tana kicin tana dafa duk abinda A'isha ta buƙata, sannan addu'o'i ko yaushe tana nan tana tofa mata su cikin ruwa tana sha. In za'a kawo abinci sai an kawo, shi kam Uncle shi ne mai jinya, duk wadda yake ɗakinta zai je ya bata haƙƙinta in ya kintsa jikinshi zai dawo gurin A'isha.

Ya lura da ita, musamman saboda dare Hajiya Jummai ce ta so ta nuna rashin amincewarta ya ce haba Jummai,in kin lura A'isha tana buƙatar kula,ba fa wai ta samu sauƙi ba ne, dole sai da mai kula in kuma da wanda ya dace ya kula da ita,to ni ne. Ta dai ƙyale shi ne kawai.

Kullum sai Ummanta da Abbanta sun kira ta sun tambayi jikin umma ta kan bata shawarwari masu kyau game da rainon ciki. A daddafe cikin ya yi wata biyu, suka yi waya da Samira inda Samira take cewa wannan satin ne za'a koma makaranta, ta ce, ina sane ni da nasha ciwo kamar ba zan tashi ba tun daga wannan dai ciwon? Samira ta ce ayya amma me yasa ba a samun wayarki? Ta ce,ke dai bari,ni da tunanina manta da batun wata waya, sai dai mun haɗu a makaranta. Samira ta ce to shikenan, Allah ya sawwaƙe, A'isha ta ce Amin.

Koda Uncle ya dawo ta ce mishi an koma makaranta, sai ya ce mata wace makaranta? Beby gaskiya ba zaki koma makaranta da ciki ba." Ta dube shi cikin rashin walwala ta ce, Uncle kana nufin ba zan zana (S.S.C.E) ba? Ya ce haba Beby,ke sai ma ance miki,kina ganin yanzun ban bari ki yi nisa da ni? Ta ce, gaskiya ba zan so haka ba, wata uku fa kawai ya rage min in gama duka,don Allah Uncle ka daina wannan maganar." Ya ɗaure fuska wata shekarar kin zana, ganin yanda ya ɗaure fuska, abin da bai taɓa mata ba,sai ta yi shiru ta kifa kanta kan filo, shi kuma ya fita abinshi. Kuka ta ringa yi wiwi,na ta ganin Uncle bai mata adalci ba, ita a nata son ran ta koma makaranta tunda ba wanda ya san tana da ciki, har ta gama.

Da daddare ko da ya shigo ta bashi ruwa, sai dai ba ta cikin walwala,ya amsa yana sha yana kallon fuskarta, wadda ta kumbura ta yi dam. Ya aje kofin da sauri,me ya samu fuskarki Beby? Ta sunkuyar da kai babu komai, ya ce ban yarda ba kin yi kuka ko? Ta ɗago ta ce mishi, a'a sai hawayen da take maƙalewa suka zubo ya kama hannunta suka zauna, yanzu saboda na ce ba ki komawa makaranta ba shi ne ki ke kuka? Beby na fiki son karatun ki domin alƙawari na ɗauka cewa zan tsaya har sai kin ji da kanki cewa kin gaji da karatu, amma yanzu koda ba ciki duka-duka yaushe aka sallamo ki daga asibiti? Ba ki gama murmurewa ba" Ta ce, Uncle ko a makaranta fa zan kula da kaina." Ya yi shiru yana kallonta,sam baya so ko kaɗan ya ga yarinyar cikin damuwa, ya ce to daina kuka za ki koma, amma sai kin ƙara murmurewa, sannan in naga kina cin abinci. Ta ce, to Uncle zan dinga ci. Nan fa A'isha ta dinga ƙarfafa jikinta don kawai ta samu ta koma makaranta, sai dai duk da haka cikin nata mai saka laulayi ne da tsirfar zan ci kaza ba zan ci kaza ba,ga saurin fishi. Wata rana tunda safe ta ce da Uncle idan zai dawo ya zo mata da agwaluma, ya ce ni kam ina zan ga wata agwaluma? Ba na zaton cewa duk Katsina za'a samu agwaluma, amma zan sa a duba. Yinin ranar neman agwaluma gurin mutum huɗu ya baza,neman agwaluma. Ita kuma tana ta yi mishi waya a ƙarshe washegari a Kano aka siyo cikin baƙar leda ya tashi Jabiru ya dawo gida lokacin ƙarfe uku na rana ya

Please Login or Register in order to submit comment