Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yanzun Beby ta fito mu wuce gida. Bayan sun fito, Nafisa ta ce to telan fa bai san measurement ɗin ki ba, A'isha ta ce,zan aika da kayana sai ya yi min girman su, masu ƙyau inji Uncle. Nafisa ta ce kada kaji komai Bros, bayan sun shiga mota ta miƙo ma A'isha tsarabar da ta bata, tare da ki fa yi amfani da shi yanda na miki bayani, A'isha ta ce to na gode,sai mun yi waya.

Bayan Jabir ya ɗauki hanya ne sannan Uncle ke cewa, tsarabar me ki ka samo Beby? Ya kai hannu gurin ledar, kawo in gani. Ta yi saurin ɓoye ledar ba fa wani abu ba ne,ya yi ɗan murmushi tare da cewa, "Mata ba ku rabuwa da tarkace."

Tun fitar su A'isha, Suwaiba da safiya suka shiga gurin Jummai,suna bata labarin abinda A'isha da maigidan sukayi har ma da ƙarin gishiri,wai ya rataya jakarta. Jummai ta ce jaka fa ku ka ce? Suka ce jaka mana, kuma ta ratayawa ko kunya da girmanshi da komai,tsaki ta ja ni ku daina gaya min tunda ku baku da fus cikin gidan,ba ƙwa taimakaman da komai. Safiya ta ce in mun yunƙura zamu daki banza sai ki ce a'a," ta ce Allah wadaran halinku tunda ba ku da wata dabara sai ta duka,ku fitar min daga ɗaki, ance muku yanzu ana ya yin duka ne? Sai dai na ƙarƙashin ƙasa. Suwaiba ta ce to ba sai ki nuna mana yanda zamuyi ba? Ta ce,ai yanzun duk zamanku tare da ni ba ku ɗauki wani darasi ba? Allah wadaran zamanku tare dani, ta miƙe ta nufi toilet tana masifa,shegu kun iya yawon bin ƙana nan yara suna rarake ku, amma baku iya sanin yanda za ku zauna da mutane ba, yanda za ku ƙuntata ma yarinya, ya gagare ku.

Ranar dai haka ta yini cikin ƙuncin zuciya, gefen Hadiza yau kam a cike da A'isha ta yini ga takaicin jiya,nata ganin ya danne mata haƙƙinta, sannan yau ba girkin A'isha ba, amma ya fita da ita don itama tana kallonsu ta window ɗinta, nata ganin ya fi son Aisha. Ƙaramar yarinya tana juya shi son ranta,don haka koda lokacin ƙwanciya ya yi,ya yi sallama da sauran matan nashi ya shige ɗakinshi ba tare da ya shiga gurin Hadiza ba,don ta san ita ce dashi,ƙin zuwa ta yi, dole tana fushi, shima bai neme ta ba, kuma ko washegari bai leƙa inda take ba,hakan ya ƙona zuciyarta.

Ranar Alhamis suka sauka Jigawa,niƙi-niƙi da tsaraba,ga kuma gudunmawa. Aisha ta tattala dubu biyar ɗinta zata bada, sai kuma ta ji Umma da Abba suna mata godiya,wai Uncle ɗin ta ya bada dubu hamsin, talatin nata, ishirin na shi. Tun ranar A'isha suka wuce Gumel, ita da Umma,su Abba sai gobe in sun zo ɗaurin aure. Inna Rabi ta ji daɗi sosai da wannan gudunmawa,nan A'isha ta zama tauraruwa gidan bikin kowa sai birge shi ta ke yi.

Washegari ana gama ɗaurin aure Uncle ya yi mata waya cewa ta leƙo suyi sallama shi zai wuce, lokacin suna cikin gidan maƙota, tare da su Naja da ƙawayanta. Nan ta fito ta same shi cikin mota,ta shiga ta zauna ya rufe. Sannan ya ce Beby ƙwana nawa za kiyi? Ta ce, duk sanda ka ce Uncle zan shirya in jira ka. Ya ce, to zamu yi waya? Ta ɗaga kai alamar eh,ya sa tafukan hannunshi biyu ya ɗago fuskarta. Kallo ɗaya ta mishi ta lumshe idanunta,tana jin nauyinshi. Cak numfashinta ya tsaya lokacin da taji saukar leɓunanshi kan nata leɓunan ƙamshin turaranshi ne ya doki hancinta.

A hankali ta buɗe idanunta,na shi idanun a lumshe ƙyakƙawar fuskarshi irin ta fulanin Katsina KT cike da annuri. Ba zato shima ya buɗe nashi idanun zata rufe nata, da idanu ya yi mata alamar kada ta rufe. Suka zuba ma juna ido, Kasa jurewa ya yi ya jawo ta zuwa jikinshi, sannan ta yi ajiyar zuciya tare da runtse idanunta sakamakon jinta cikin wani yanayi, muryarshi a sarƙe ya ce Beby yaushe zan zo in tafi da ke zanyi kewarki da yawa. Ta ja numfashi muryarta ƙasa-ƙasa ta ce,nace duk randa ka zo. Ya ɗagota tare da cewa shi kenan sai nazo kanta yana ƙasa don kunya ta ce, to . Ya ɗauki kuɗi daga gaban motar ya ce gashi,ta dube shi ka fa bani kuɗi jiya, ya ce ki ƙara Bebyna, sai mun yi waya? Ta ce,eh ya kuma kama tafin hannunta ya sumbaci tsakiya,tsigar jikinta ta yi yar,ta kalleshi, sannan ta fita daga motar. Ta koma ciki bayan ta ɗaga mishi hannu alamun bye-bye.

Kano ya ƙwana,sannan washegari ya nufo K.T lokacin da ya shigo gidan tsit, wannan lamarin yana taɓa zuciyarshi, kullum ya shigo gida tamkar ya shigo maƙabarta. Ya buɗe ɗakinshi ya shige kan kujera ya zube, sannan ya jingina da bayan kujerar,kai wannan abu yana damun ƙwanyar shi, duk gidan abokanshi in sun shiga,ya kan ji hayaniya sa'an nan ƴaƴan su kan shigo suna oyoyo, saɓanin gidanshi kullum shiru mata biyu a ciki amma ko T.V da wuya, ya shigo ya taras an kunna kowace tana ɗaki tana ƙwance, ya ja tsaki shi yasa in A'isha tana makaranta ko son tuno gida ba ya yi,ita kaɗai ce wadda in ya kalleta ya ke jin annuri.

Ta tare shi da ruwa mai sanyi ko zoɓon nan nata mai daɗi, ya kai hannu kan leɓunanshi yana son tuno yanda ya ji lokacin da leɓunanshi suka mannu da nata,ya sauke ajiyar zuciya, sannan yasa hannu cikin aljihu ya ciro wayarshi. Layin A'isha ya nemo lokacin tana shafa mai,ta fito wanka, tana cikin ɗakin inna Rabi, cikin uwar ɗakanta, da sauri ta ɗaga wayar.

Ta ce, "Assalamu alaikum! Uncle ina ta neman layinka network ya ƙi shiga, ya yi ɗan murmushi gani na sauka gida yanzun nan, ta ce ina ka ƙwana? Ya ce Kano mana,ta ce ka sauka lafiya?" Lafiya lau Bebyna,ki kula min da kanki. Tayi murmushi,nima haka. Ya ce ke ma me?" Ta ce, yanda ka ce,ya yi ƴar dariya, zanyi yanda ki ka ce,kafin ki dawo ki cigaba da kula dani...


#######
[12/14, 07:15] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 10*


Ta ce na manta kana da wasu masu kula da kai ɗin har su biyu, ya ce "ai Beby yanda kowa ke kula dani daban, sannan in muna tare da ke ki ringa ji a zuciyarki ba kowa cikin duniyar nan daga ni sai ke,kin ji ko?" Ta ce to Uncle, ya ce yauwa Bebyna, bari na watsa ruwa, ta ce to. Suka yi sallama.

Ya yi shiru, ya kula A'isha tana matuƙar son shi, kunya ce kurum ke ɗawainiya da ita, shi yasa shima yake jin nauyin yi mata wasu abubuwan, amma yanzu ya san ya ɗauko gangarar cimma burinshi.

Bayan ya yi wanka ya fito zuwa (Dinning table) bayan ya yi wa Uche waya kan cewa ya kawo mishi abinci, ya dubi Uche ba kowa a gidan ne? Uche ya ce Madam ta fita, amma bai ga fitar amarya ba. Zuciyarshi ta tafi ga tunanin yaushe rabon da ya samu kulawa daga Jummai? Ba zai iya tunawa ba, domin tun lokacin da ya zo mata da labarin auranshi da A'isha, ta canza har yau bai gane kanta ba. A fili ya ce, "Allah ka shirya wannan baiwa taka." Yana rufe baki tana shigowa,ta nufo shi "ka dawo ne? Wallahi nima na je gida ne na duba Innarmu." Idanu kurum ya zuba mata.

Ta ja kujera ta zauna,ba ka yarda ba ko? Ta soma magana cikin karya murya, irin ta wanda ke cikin damuwa ɗinnan, ta ce ni yanzun ai ko zan haɗiyi Alƙur'ani ka daina yarda da magana ta, duk abinda na faɗa ƙarya ka ke ɗauka, tun da ka samu yara masu jini a jika, ni ko na tsufa."

Ya ajiye cokalin hannunshi.

"Jummai don Allah ki zauna ki yi tunani, irin yanda ki ke tafiyar da gidan nan matsayinki na uwargida ya dace? Ni kaina yanda ki kayi watsi da duk lamurana,ki ka kama ƙawayan bariki masu kai mutum ga halaka,yawo tamkar an yi miki ƙauri da kan kare. Da na miki magana sai ki kawo duk maganar da ta zo bakinki ki caɓa min." Ya nuna tebur ɗin gabanshi "Look at, yanzu tafiya fa na dawo ku biyu cikin gida amma sai kuku shi ne mai kawo min abinda zan ci, shima ɗin sai da na roƙa. A ce kamar ni bani da wata ƙima cikin gidana?"

Ta ce, "To kai ne ai duk ka canza min, yanzu A'isha ce a gabanka." Ya ce,"Ita ce take ganin girmana, amma fa duk wanda na kawo na ajiye ai so ne ya kawo haka ba wai ƙi ba. Ni dukkanku ina sonku,ki kula da wani abu A'isha, yarinya ce kuma ba mazauniya ba ce,ku ko kullum muna tare da ku, amma duk da haka sai ƙorafinku ya tsaya a kanta? Kun yi mata adalci kenan? Shiru Jummai ta yi, amma a zuciyarta faɗi take yi, adalcin banza,za ku gane kuskuranku. A fili kuwa sai ta ce, to shikenan, kayi haƙuri yanzu me kake so inyi? Cike da jin daɗi ya ce, ina so ne ki canza ki koma Jumman da na sani da, kici gaba da kula da ni tare da yin riƙo da muƙaminki na uwargida sarautar mata, kada ki yarda ki yi watsi da shi, wata ta samu. A'isha ki ɗauke ta ƙanwa, bata da raini zata girmamaki, ta kuma sunkuyar da kai tare da cewa , insha Allahu zan yi yadda ka ce." Ya ce, "To na gode, sai batun yarannan su Suwaiba ya kamata su fito da miji ko ya ya ki ka gani?".

Ta ce, "Haka ne,nima fama nake da su,samarin na su duk ƴan yara babu mai shirin yin aure yanzu,ka yi musu magana da kanka,ni sun riga sun gama raina ni." Ya ce, "Shikenan, zan gan su." Sai suka ci gaba da hira tana gaya mishi cewa kayan shafanta gami da turarukanta sun ƙare, ya ce, to za ya bata ta saya. Da yake ranar ita ce dashi,ta kula da shi yanda ranshi ya gamsu cewa ta gane kurenta, ta yarda da dabarar da zasu sake tunda magani ya ƙi sai a koma kissa, don haka ko gurin ƙwanciya ta yi mishi ba zata, sannan ta sake ba shi haƙuri.

Hadiza tana ƙwance suna waya da Hajiya Lanti mahaifiyarta, tana kuka tana sanar da ita cewa, Saddiƙ ya mata wulaƙanci saboda wannan A'ishar,tun suna can ƙasar da suka tafi ya dawo don kawai ya ɗauko ta daga makaranta, sannan tunda ta dawo sai abinda ta ce.

Haka ya ɗauki ƙwanana ya kai mata, na yi magana ya fi ni fushi, yanzun da haka zancen da nake miki yau ƙwananshi biyu,ya ɗauke ta sun tafi ko'ina ni,ni ban sani ba. Sai yanzun na ganshi suna zaune da waccan tsohuwar Hajiya Jumman,ko tun yaushe ya dawo be neme ni ba? Oho."

Hajiya Lanti ta ce,da Allah ni rufe min bakinki, kin bani kunya, kishiya ki ke wa kuka, sai ka ce ba nonona ki ka sha ba? To bari ki ji in zaki dage ki dage, kuɗi za ki ƙwaƙwalo in bazama kin tsaya yin zuciya,an ce miki fada ko kishi ne silar kawo ki gidan nan? In baki sani ba, bari ki sani, na shiga na fita na kutso ki Wannan gidanne don kawai ki wawuro min dukiyarshi,ke dai dage ki samu ciki kada ki tsaya kishin banza." Hadiza ta ce, "Hajiya ni dai na fi son ki samo min taimakon da hankalinshi zai dawo kaina." Ta ce, kuɗi za ki kawo Hadiza." Ta ce, "zan kawo." Hajiya Lanti ta ce,a to, Hadiza ta ce to dama gobe ni ce da girki,in sauke kenan in daina fushin?.

Lanti ta ja dogon tsaki, "in ba iskanci ba dama ina ke ina fushi? Sauke ki kuma bashi haƙuri yaƙi ɗan zanba ne Hadiza,kin ji ko?" Ta ce, "To Hajiya sai kin zo."

*** **** **** ***

Satin A'isha biyu, Uncle ɗin ta ya yi mata waya cewa, gashi nan zuwa. Ta ce Uncle sauran fa sati ɗaya mu koma makaranta,ka bari mana sai ana sauran ƙwana uku". Ya ce, "Lallai ma Beby,waton ba kiyi missing ɗina ba ko?" Ta ce, "Nayi mana Uncle." Ya ce, "To gaya min da me ki ke tunani?" Ta ce,Da abubuwa da yawa nake tuno ka, ya ce gaya min ɗaya.

Ta yi shiru, ya ce ina jin ki mana." Ta ce, "Ka bari dai ai zan gaya maka in na dawo." Ya ce, "ke ɗin? Kin kasa gaya min yanzun a waya sai a gabana ne za ki iya? To ni bari na faɗa miki ɗaya,kina ji na? Ta ce, Eh." Ya ce, da lallausar fatarki, da kuma zazzaƙan leɓanci..." Da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska sai ka ce a gabanta yake. Shi ko dariya yake mata, ta kunna wayar ta tura mishi saƙon cewa "Uncle kai fa babba ne,ba ka jin kunya?" Ya duba saƙon, sai ya tura mata cewa,a cikin soyayyar ma'aurata Beby ba jin kunya wani abu ma sai in kin dawo." A ranshi ya raya cewa, bari na kashe maganar, sai ya rubuta cewa Beby shin za ki iya gaya min ya ya kike ji a duk lokacin da jikina ya haɗu da naki? Ya tura mata,aiko ya kashe magana don tana karantawa ta kashe wayar gaba ɗaya. Ta ƙwanta tana tunanin shi, Uncle tamkar zuga shi ake yi.

Umma da Abba sun yiwa A'isha nasiha a lokacin tahowarsu, Umma ta ce,"Ni dai A'isha ina ƙara yi miki nuni ne da haƙuri, musamman kasancewar ku,ku uku gidan mijinku. Ki kama kanki da bakinki, kada ki yarda ki haɗa kai da wata don kawai ki musguna ma wata,gara ace ke ake cuta ba ke kike Cutar ba. Sannan ki riƙe mijinki."

Abba ya ɗora da cewa,"ki zamo mai yi masa biyayya ki zamar masa wadda zata kai shi gidan Aljanna,ba wuta ba."

A'isha a cikin aurenki ki sa ma ranki cewa, bautar Ubangiji ki ke yi, kada ki kalli ƙyale-ƙyalen duniya da abinda ke cikin ta. Ta ce,"To Abba insha Allahu zan yi yanda ku ka ce."

Jabiru Sarkin tuƙi ya ɗauki hanya da su,yayin da suke zaune a baya suna ƴar hira. Lokacin da suka iso gida ta yi mamakin ganin Hadiza ta zo mata sannu da zuwa, cikin dakewa ta amsa,yau kam Hajiya Jummai tana gida. A'isha taje ta gaisheta, itama cikin sakin fuska ta amsa. A ran A'isha ta ce, ina ma ace har zuciyarsu, saboda gajiya A'isha ko tashi daga kan sallaya bata yi ba, bacci ya yi awon gaba da ita. A haka Uncle ɗinta ya same ta,bai tashe ta ba cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan gado.

Hijabin kurum ya zare mata daga ita sai ɗaurin ƙirji, da alama ma wanka ta yi kafin sallar,zama ya yi ya zuba ma fuskarta idanu, komai na yarinyar yana son shi.

A hankali ya runƙufo ya sumbaci leɓunanta, sannan ya miƙe don yin shafa'i da wuturi, sannan ya zauna gaban laptop kafin lokacin da zaya ƙwanta. Ya so ƙwarai ya sami hutu da ƴar Bebynshi, amma ta gaji sai dai ya mannata a jikinshi suka ci gaba da bacci.

Washegari girkin Hadiza, da rana A'isha ta yi zoɓo don ya yi waya za ya aiko a ɗauka, Hadiza tana zaune a babban falo taga Uche ya zo ya amshi ƙwando kamar ta yi magana ta dai share.

Da yamma da ya dawo bayan ya shiga gurin Jummai, ya fito ya shiga gurin Beby, duk da cewa duk inda ya shiga lokacin shigowa gida ko lokacin fita ba ya zama, amma ya kan ɗan yi jum gurin A'isha saboda yana shan ruwa ko zoɓo.

Bayan ya fito ne ya nufi ɗakinshi kamar yadda ya saba, sai mai girki ta bi shi. Wani sabon salo wai sai Hadiza ta shigo wai ta zo (danning) inji darling don su ci abinci, kamar kar taje amma jin cewa Uncle ke kira sai ta fito. Ba shi a gurin sai Hadizan kaɗai, sai ga Hajiya Jummai,jim kaɗan shima ya fito. Ya kallesu, kowacce fuska a ɗaure in ban da A'isha wadda hankalinta ke kan T.V Hadiza ta ce, tana son ya haɗa su su dinga cin abinci tare, sai shima ya ga da hakan zata yiwu,da zai so. Don haɗin kansu yake nema ba rabuwar kansu ba. Ya yi musu sallama su suka amsa. A'isha ta ƙara da cewa sannu da fitowa." Ya ce,"yauwa Beby." Ya dubi Hadiza "Na ji daɗin wannan zaman, Allah yasa ya ɗore" duk suka ce, "Amin." Nan Hadiza aka buɗe abinci, maigidan aka soma zuba mawa, sannan ta tura ma saura plate kowa a gabanta,wai ta zuba abinda ta ke so.

A'isha ba gwanar cin abinci ba ce,don haka kawai sai ta ɗan zuba romon farfesun kazar dake gurin tasa cokali tana sha. Ya dubi plate ɗin beby wannan ne abincin? Gira ta ɗaga tare da yin murmushi, Hadiza ta ce, shi yasa baki yin ƙiba ko? Kullum kamar a hure ki ki faɗi, tana magana tana dariya, A'isha ta fahimci magana ta gaya mata da wasa,don haka ba tare da ta dube ta ba tace, "ai ƙiba ciwo ne,ke baki sani ba ne." Hajiya Jummai dai tana ji ba ta ce ƙala ba, kuma abincin da tasa sai juya cokalin take yi tana mamakin,yau ita ce zaune da kishiyoyi biyu? Abin tamkar cikin mafarki.

Shi ko sam bai ma fahimci suna jefa ma juna magana ba ne, musamman da yaga Hadiza tana fara'a ta yi maganar. Sannan A'isha bata nuna wani fushi ba. Hadiza ta ji haushin kalmar A'isha, amma bata da ta cewa, A'isha ba ta jima ba ta miƙe, Uncle ya ce, har kin ƙoshi? Ta ce, na ƙoshi Uncle." Ta dube su sai da safenku, dukkansu sun amsa ne a maƙoshi,ko mene ne yasa dukkansu suke jin zafin ta? Ta tafi ya bita da kallo, komai na Beby yana birge shi, musamman tafiyarta cikin natsuwa, tamkar mai tausayin ƙasa, wani sa'in shi kanshi sai ya dinga ganin tamkar yanga take yi. Hadiza ce ta buga cokali akan plate ya yi ƙara, sannan ya dawo daga tunanin da ya tafi, cikin ɓacin rai ta ce "ko yaushe in A'isha na guri kowa banza ne?" Ya ce "haka ki ke gani?" Ta ce, "Eh mana." Ya ce, shikenan. Ranta ya sake ɓaci, ta ce "sai ka ce wata ƴar gwal?" Bai kula ta ba, shima ya miƙe ya nufi ɗakinshi suma suka watse kowace zuciya na raɗaɗi. Washegari ma A'isha ta wuce makaranta, ta bar su suka ci gaba da neme-nemensu.

Wannan karon A'isha sun buɗe wuta,don daga wannan hutun sai na fita.

Hadiza dai kowane wata ana jiran a ji ciki shiga, amma shiru. Zaman su da Hajiya Jummai zama ne na ba ruwan wani da wani, sai dai ana gumawa juna ta ƙarƙashin ƙasa. Cikin haka wata ranar Lahadi maigidan nasu ya tashi da matsuwa ta buƙata, Jummai ke dashi to amma jiyan tana fashin sallah,yau kam Hadiza ce a daddafe ya kai magriba, inda so samu ne ma tunda rana ya biya buƙatarshi, ana idar da sallah ya shiga gida,kai tsaye ɗakinshi ya shiga,ya ɗauki waya ya kira layin Hadiza,sai da ta ɓata lokaci sannan ta shigo.

Ya nufe ya dafa ta, sannan ya cire ɗanƙwalin da ke kanta na shaddar da ke jikinta, doguwar riga. Abubuwan da ya soma yi mata su ne suka fahimtar da ita abinda ya ke so. Nan take mulkinta ya tashi ta ƙwace daga rungumar da ya yi mata.

"Ba ka sanin darajata sai in kana buƙata,to gaskiya nima yanzu lokacina ne, kuma ba zan yi abinda ka ke so yanzun ba." Idanunshi da suka yi jajir, ya dube ta, "Don Allah Hadiza ki bani haƙƙina, wallahi na matsu da yawa,ki min taimako.


#####
[12/14, 18:12] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 11*



Ta sake taɓa baki dama ina da rana?" Ya ce, kada fa ki manta,duk matar da ta gujewa kiran mijinta, tana ƙwana ne cikin tsinuwar Allah da Mala'iku." Ta juya mishi ƙeya kai ka san wannan Ni ban san shi ba, ya ce in ma kuɗi ki ke so zan baki Hadiza, ya zo ya rungume ta ta baya. Ya dace a ce ina da mace fiye da ɗaya, amma ina cikin wannan bala'in?" Ta fisge mai Beby yau ina Bebyn taka? Ya ce, duk ba wannan ba ne,don Allah fa na ce. Ta ce, wallahi ni fa ba yanzun ba,yau ma ƙwata-ƙwata bana jin yi, amma tunda ka matsu goman dare ka zo sai mu yi ciniki a ɗakina kuma nima ni ke so yanda ka kewa Bebyn taka ita ƴar gwal bata bin miji sai dai ya bi ta. Ta dube shi, goma na dare ina jiranka sai ka zo da kuɗi." Ta fice abinta, ya bita da kallo yana haɗiye miyau,jin shi yake tamkar ya kama ta da ƙarfin tsiya.

Kan gadonshi ya zube rigingine mararshi har ta soma ciwo. Ya miƙe tsaye ina zan kai wannan matsalar tawa? Gaskiya kafin goma na dare zan sha wahala. Ya raya a zuciyarshi,ya kalli agogo baƙwai ma yanzu ta yi, ya janyo wayarshi.

Jabir ya kira bayan ya ɗaga ya ce,kana ina ne Jabiru? Ya amsa da cewa, ina nan gidanmu maigida,ya ce na san zan takura maka, amma in zai yiwu ina son ganinka yanzun. Ya ce,ba komai maigida gani nan zuwa. Kamar minti goma ya kira shi gani na iso maigida. Ya ce, yauwa Jabiru ina fitowa. Turare kurum ya ƙara fesawa, sai kuɗi da ya ɗauka ya saka su cikin aljihunan nashi guda biyu,ya ɗibi wayoyinshi ya fita.

Tuni Jabir ya fito da mota, suka fita titi ya ɗan juyo ina zamu ne maigida? Ya ce,mu je makarantar su Beby. Da sauri ya ce "lafiya dai ko?" Ya ce,a lafiya lau." Ya ciro waya ya soma neman shugaban makarantar, bayan sun gaisa ya ce zan zo in tafi da yarinyar nan ne zuwa da safe. Mahaifiyarta ce ta zo yau kuma sammako zasuyi, Allah yasa ba matsala? Shugaban makaranta ya ce, da matsala, sai dai tunda kai ne zan iya yi maka alfarma, amma fa da safe a tabbatar da cewa ta dawo da wuri, saboda ta samu shiga aji. Alhaji Saddiƙ ya ce, don wannan duk ba damuwa insha Allah zata dawo da wuri, ya ce to bari in yi waya cikin makarantar.

Lokacin da suka shigo cikin makarantar, A'isha suna dawowa daga (Dinning) suna tafe suna yi wa juna ba'a irin ta ƙawaye. Samira tana ƙwaiƙwayon tafiyar A'isha.

A'isha ta yi murmushi ko da haka ni ke tafiya da sai na fi awa ban kai ko nan da masallaci ba." Amina ta ce,ba haka take yi ba,kunga yanda take yi nan. Sallamar da aka yi musu ne ta dakatar da su, mai sallamar ta ce cikinku wacece A'isha Mustapha? A'isha ta dube ta, gani nan, ta ƙara da cewa lafiya? Lafiya lau,kina da visitor. Ta dafa ƙirji,ni kuwa? Ta ce ba ke ce A'isha Mustapha ba?" Amina ta ce ki je ki gani mana. Cikin fargaba ta ce,na bani ni A'isha,wa zai zo gurina da daren nan? Samira ta ce, Uncle ɗin fa? Cikin damuwa A'isha ta ce, Uncle ya zo jiya fa. Suka ce muje mu raka ki, kasancewar kowane gurin gal yake da haske,tamkar rana. Tun kafin su ƙarasa ta ce Uncle ne don ta hango motar sannan ga Jabiru a tsaye, ta ce ina zaton ba lafiya ba,ban ga Uncle ɗin ba Samira,Suka ce to bari mu koma sai kin dawo ma ji ko mene ne. Ta ce to.

Tana isa gurin cikin firgici ta ce,"Jabiru lafiya, ina Uncle ɗina?" Ga zatonta wani abu ne ya sami Uncle ɗin. Jabir ya nuna mata mota, ya ce yana ciki, shiga." Ta kai hannu zata buɗe bayan motar,sai taga an buɗe mata, daga ciki ta a shiga da sauri lokacin ne kuma wutar motar ta haska, ta kalleshi "Uncle lafiya?" Ya jawo hannunta lafiya Beby, amma ba lau ba. Ta zaro idanu me ya faru? Abbana ne ko ummat? Ya ce, a'a ni ne. Ta soma leƙa ƙafafuwanshi me ya faru da kai? Ganin yanda ta ruɗe kuma jawota jikinshi taimako nazo nema gurinki, domin yanzun duk duniya kece kurum ki ka rage min da zaki iya yi min wannan taimakon, ta ce mene ne shi? Ya

Please Login or Register in order to submit comment