Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu yi da zai yiwu ni dai da mun dangana da Indiya, can ne ƙarshen tsafi ba ki gani ko cikin fina-finansu? Jummai ta ce,don Allah kuma gaske ne yana yi?" Karima ta ce ,"Zauna nan,ai in zaki miƙe,miƙe sahibata wani aikin sai Indiya,ko Chaina, kafin ma mu dawo tun muna can za'a ɗauki ran banza mu huta."

Jummai ta ce,ba zuwan ba,ba kuma kuɗin nake ji ba,don sai na iya sa duk wani abu nawa a kasuwa in amshi kuɗin,matsalata mutumin gidana, kin san cewa har zuwa yau ba mu koma normal da shi ba? Tun zuwanmu Nijar ɗin nan har yau,na kasa gane kanshi. Sai ya yi ta dakemin yana shan ƙamshi.

Karima ta ce, "ke Aminiyata nemi kuɗi in ma bai barki ba ni sai in je miki. Menene amfanin Amintakar? In ana zuwa lantsandan gaban lahira inji ƴan magana to zani,in samo miki mafita game da kishiya. Ai ki daina damuwa,mu za'a gaya wa Boka? Jummai ta yi ajiyar zuciya, daɗi ya rufe ta,a duniya bata da tamkar Karima, ta ce, "Aminiyata Allah ya ja mana ƙwana,ni na san bani da masoyiyar da ta kai ki duk duniya."
Ji toshewar basira.

In sun samu hutu.
A'isha duk ranar girkinta,ta kan shiga ɗakin Uncle ɗin ta gyara mishi gado har ma da sauran gurare, sannan ta saka mishi turaren wuta mai ƙamshi, amma bata kwana tunaninta ma bai kawo mata ta ƙwana ɗin ba, har ƙwanakinta na hutu suka cika ya yi mata komai ta koma.

A'isha ta maida hankali kan karatunta, bata wasa sai dai zama da su Samira ya yi matuƙar wayar mata da kai. Su kan zauna suyi hirar samarinsu kamar yanda ƴan mata kan yi. Amina kam kullum bakinta yana ba su labarin Kabir,Samira ma bata da zance sai na Adam.

Kowacce in tana labarta yanda take ji game da abin ƙaunar nata, A'isha kam baki take saki ta yi ta kallonsu. Samira ta ce, A'isha wai ke kullum tamkar ba ki waye ba, haka ki ke jin kike wai baki da saurayi ne? A'isha ta girgiza kai tare da cewa,ni bani da wani saurayi.

Amina ta ce,ni wallahi ban da ina da Adam ɗina ko da sai na ce don Allah ki haɗa ni da Uncle ɗinki mana? Samira ta ce,ai gayen ya yi ne, A'isha ta yi ɗan murmushi, sannan ta ce,shi Uncle ba fa yaro bane. Samira ta ce ji wannan ai ba yarinta ake kallo ba a maza,ƙwalitis ake dubawa, shi Uncle ɗin ki yana da duk ƙwalitis ɗin da ake so ga namiji."

Aisha ta ce,ni ban san wani ƙwalitis ba fa da kuke magana" Dariya suka shiga yi mata, A'isha ta ce,kun ji lokacin sallah ya kusa, ya kamata mu soma shirin shiga Masallaci."

Duk lokacin da suke ire-iren wannan hirar, A'isha kan tambayi kanta, menene wannan ɗin da su Samira suka damu kan su dashi? Ita dai ta san burgewa kamar Uncle in ya yi ƙwalliya,yana matuƙar birgeta, bayan wannan ba ta san komai ba.

Ƙwanci tashi su A'isha an shiga (SS3) duk da batayi wata ƙiba ba, amma ta ƙara tsawo.

Ƙirjinta kuma ya bunƙasa har yana ɗan rinjayarta, shi ne ma sanadin yin ɗan rusunawarta wanda wasu ƴan makarantar nasu suka fassara shi da yanga, zuwa yanzun ta san mene ne aure,me ake yi in anyi shi? Sai dai ita mai tsananin tsoro ce.

Shi kuwa Uncle har yanzun ba ya tunanin taɓa ta, domin yanzun ya gama yarda cewa ƙwanciyar da yake yi ne da ƴaƴan jama'a suke mutuwa, duk da yana tsakanin buƙatar hakan, saboda yanzun Hajiya Jummai,damuwarta ma tai yawa,don ta ce an sa mata hannu na asirin da tayi bayi ci,tana nan dai tana fafutukar haɗa kuɗin zuwa Indiya ko Chaina.

Aisha wadda yanzun shekarun ta sha baƙwai kenan ta samu shekara biyu gidan Uncle ɗinta.

Ganin haka ya sanya jama'a suke ta kai-kawo kan cewa Alhaji Saddiƙ dai yanzun mata sun daina mutuwa a gidanshi, sai dai haihuwa shiru,don haka mutanen da a baya suke zaginshi sai kuma suka shiga kawo mishi tallar ƴaƴansu.

Nuna musu yake yi ba shi da ra'ayin sake aure,don haka su yi haƙuri.

Yau bayan tashinsa daga Office,gidan Hajiyarmu ya nufa, ya samu Alhaji Sunusi wan mahaifinshi,amma ƴaƴa maza suke. Alhajinmu yana jin maganar Alhaji Sanusi sosai, domin yanzu ku san shi kaɗai ne ya rage mishi a maza, cikin dangi. Alhaji Saddiƙ ya zauna suka gaisa,ya juya ya gaida Hajiyarmu, Alhaji Sunusi ya ce wannan zuwan naka ne fa Abubakar, Uncle ya dube shi tare da gyara zama sannan ya ce, to ina jin ka Baba. Alhaji Sunusi ya yi gyaran murya sannan ya ce, maganar Hadiza ce ta kawo ni, Uncle ya dube shi wace Hadiza fa? Alhaji Sunusi ya ce,ai ba ka ma san ta ba? To Hadiza ta gidana, tun lokutan baya na sani kaima ka sani tsayawa ta yi tsayin daka kan cewa kai take so, amma a lokacin kowa yaƙi saboda kai ba a son ra'ayinka ba,to sakamakon haka har izuwa yanzun taƙi kowa ta ce ita dai sai kai, gashi an tashi bikin ƙannanta su Hussaina shi ne muka yanke shawarar aura maka ita kawai.

Uncle ya dubi gefen da Hajiyarmu take zaune,tana ta nazarin littafin ƙawa'idi, ya sani tana jin su sai dai ba zata taɓa magana ba. Sannan duk ƙwaƙwarka ba zaka iya gane me ke fuskarta ba, ma'ana zancan ya yi mata daɗi ko ko akasin hakan, sannan ya dawo da dubansa ga Alhaji Sunusi wanda ya san yanzun nan zasu hau sama su faɗo in dai ya bashi amsar da ke bakinsa, ya ce Alhaji ai ko lokutan baya na san anƙi in auri Hadiza ne saboda matsalar da ke tare dani, ta mutuwar matana, yanzun kuma an yarda ne saboda an ga nayi aure matar bata mutu ba,don haka ni dai a bawa Hadiza haƙuri, ta nemi mijinta kawai."

Alhaji Sunusi ya ce, inji wa ya ce maka don wannan matsalar ne? Mu dai burinmu mu ga ƴaƴanka."

Alhaji Saddiƙ ya ce, "Gaskiya ba ni da ra'ayin mace fiye da biyu, kuyi haƙuri."

Ran Alhaji Sunusi ya soma ɓaci, don haka cikin fusata ya ce, "Abubakar ba wai na zo neman izininka ba ne, umarni na zo baka domin ko mahaifinka ne na bashi umarni baya tsallakewa,in ma mahaifiyarka ce zata zuga ka to ku sani daga kai har ita aure babu fashi."

Uncle ya ce, "Allah ya huci zuciyarka,ba ruwan Hajiyarmu cikin wannan zancan, Hajiya da ke jin su ta rufe littafin hannunta, sannan ta dubi wan mijin nata ta ce, Yaya Allah yasa alkhairi, kuma yasa muna da rai za'ayi." Jin haka yasa gaban Alhaji Saddiƙ ya faɗi, ya sani zancan ya tabbata tunda Hajiyarmu ta amince, Alhaji Sunusi ya miƙe yana cewa, "Duk yanda muka yi zaku ji gurin Alhajin gidan nan." Ya tafi.

Shiru Alhaji Saddiƙ ya yi,yana kallon ƙasa,shi da yake tunanin lokaci ya kusa da zai daidaita tsakanin shi da A'isha,don yin zaman aure cikakke, sannan sai kuma a kawo mishi batun wani auran? Shi fa ya sani ya so ya auri Hadiza a lokacin yana cikin tsananin son haihuwa, amma yanzun sam babu Hadiza a ranshi, duk da ko can da ɗin ma ba itace ta ƙi shi ba, dangin mahaifinshi ne suka ƙi, musamman Hajiya Lanti da Alhaji Sunusi mahaifanta yanzun kuwa ya sani ganin daɗewar A'isha a gidanshi ne yasa su amincewa.

Hajiyarmu ta katse shi da cewa,ka ci gaba da addu'a,zamu taya ka. Ka zama mai biyayya sannan ka shiga shirin bikin,to kurum ita ce kalmar da ta fito bakinshi, ya miƙe tare da cewa,ni zan ƙarasa gida. Duk ƴan ƙwanakin yana cikin damuwa.

A'isha tana school, Hajiya Jummai kuwa damuwarta ta sha ƙarfin tashi,don haka ita bata ma kula da me yake ciki ba, ganin haka yasa yau ya shiga har cikin ɗakinta tana ta waya ne da Hajiya Kari,kan cinikin wani gidan ta wanda shi ne kurum ya rage mata. Saboda tsabar ba ta cikin natsuwa sam bata ma san ya shigo ba, sai da suka gama sannan ta gan shi ta ɗan razana don ta san yaji me suke zantawa.

Ya zauna kusa da ita, ya maida hankalinshi kanta cikin sanyin murya, ya ce "Jummai wai menene matsalarki? Me ke damun ƙwaƙwalwarki? Ta dube shi da idanunta da suka yi jajir duk kwanakin nan haka yake ganinsu, ta ce ba komai me ka gani? Ya ce,haba Jummai, duk wanda ke gidan nan ya san kina cikin matsala, ta ce ni dai bana cikin wata matsala, ya ce to shikenan, yanzun menene dalilin ki na saida gida? Ta ce, matsala gare ni, kuma na san in na ce ka bani ba bani zakayi ba,don haka gara na saida ƙadarata, ya ce wacce irin matsala ce? Ta yi shiru tana son ta tuno me zata ce?.

Ya sake tambayarta, ta ce,zan je ne in dama dai wani likita zan gani a Indiya, saboda matsalar haihuwata,don naga wata mai irin matsalata kuma ta haihu,na gane in na ce zan tambaye ka ba yarda zaka yi ba cewa zaka yi ina ne ba mu je ba ance ba zan haihu ba."

Ya dube ta cike da zargi, sannan ya ce, "Ki bari zan shirya muje tare." Ta ɗan zaro idanu,ni dai ka bar shi kawai inje ni kaɗai, tunda kaga kai baka da wata matsala." Ya miƙe yana cewa, "Jummai waɗannan sabbin halayen da ki ka ɗauka sam ba zan ɗauke su ba, tunda ki ka bar gidan nan har ƙwana biyu ba ki gidan danginki ba ki gidan nawa, zuciyata ta soma zargin kin canza layi.....


#####
[12/11, 17:18] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 5*



Sakamakon yawo da kawayan banza,to ba za kije ba,kuma kada inji kin saida wannan gidan,ta ce ai ba gidanka ba ne,ya ce to shikenan. Amma ki sani halayanki sun gundure ni,baki zaman gida ke ba ma'aikaciyar gwamnati ba,kullum sai shegen yawo,ni kaina yaushe rabon da ki shigo dakina? Koda kin zo baki iya tsinana min komai,sai dai ki min jungum kina tunani,don haka ni ba karfe ba ne ina da bukatar kulawa. Aisha tana makaranta,ke kuma baki da lokacina."

Ta dube shi a hasale,to ka dauki mataki mana." Ya fita yana fadin "shikenan."

Gidan su Hadiza ya nufa yau,saboda yana son bin umarni,sannan Hajiya Jummai ta bashi haushi. Daga waje ya tsaya ya aika kiranta. Hajiya Lanti ta ce,maza a bude mishi kofar falo ya shiga. Hadiza kuwa murna tamkar me,don tana bala'in son shi,ba wata hira sukayi ba. Bayan gaisuwa ya ce,mata shi fa yazo ba ta hakuri ne,da zata daure ta nemi miji. Nan ta soma kuka tare da rokonshi,ya ce mata shi kenan sai dai fa ta san yana da mata har biyu,kuma suna zaman lafiya don haka kada ta yi kokarin rusa mishi tsarin gida. Ta ce,in Allah ya so ba wannan. Nan dai suka yi sallama ya tafi.

Tun daga ranar bai sake zuwa ba,sai dai ya kan kira ta a waya. Kafin wani lokaci labari ya watsu cikin dangi,Nafisa da bata so ba,don gaskiya tana ganin za'a kwari Aisha ne,tunda duk cikinsu ita ce karamar yarinya,haka ma su Aunty Fatima suke cewa.

Shi ko da ya tuno cewa bai sanar da iyalanshi ba,duk sai ya damu,musamman Hajiya Jummai,yanda ta daga hankalinta lokacin auren shi da Aisha,amma don Aisha yasan ba zata damu ba,tunda ita yarinya ce sannan ba ya tunanin ta ma san mene ne ma auren,don haka bai damu ba. Sai dai yana tunanin ya ya zai tunkari iyayanta da batun auren shi? Ko me Friend zai kawo a ranshi in ya ji batun auran? Kullum ya kan yiwa kanshi wannan tambayar.

Hajiya Kari ce ta jiyo zancan auran a gari,jin wannan labarin daga gidan mitin din su na gungun mata aiko gidanta ba taje ba,gurin Hajiya Jummai ta nufo,ta same ta zaune tana aikin gyaran kumbunanta. Hajiya Kari ta ce,ke Aminiya,dama wata ta taso shine baki sanar da ni ba?" Hajiya Jummai ta ce "Um zo zauna dama ina nemanki." Kari ta ce, kice muna kukan targade sai kuma ga karaya ta samu? Hajiya jummai ba tare da damuwa ba a zatonta fa zancan hana zuwa Indiya ne sai ta ce ai kan batun nike neman ki wai ni zan yi mishi dabara,sai kuma na rufta.Ya hana tafiya yanzun ya ya ki ke ganin zamu yi? Hajiya Kari ta ce,ke da Allah can,ba wannan zancan nake miki ba, ina miki zancan auren shi, ashe aure zai ƙara? Hajiya Jummai ta yi mutuwar tsohuwa a zaune, kusan minti biyar Hajiya Kari ta girgiza ta sannan ta ce, "Aminiyata me ki ke tunani ne haka?" Hajiya Jummai ta ma rasa ta cewa, zufa ce kurum take keto mata, duk kuwa da (AC) da ke ɗakin.

Can ta ce, "ko dai ba kiji dai-dai ba Karima?" Hajiya Kari ta ce, "Ki dai bincika." Ta suri jakarta tare da cewa, sai naji wayarki,don jin gaskiyar lamarin." Ta fita ta bar Aminiyarta cikin hawan jini.

Inda Hajiya Karima ta bar Hajiya Jummai,tana nan a gurin, har ƙarfe tara na dare. Ta rasa wane irin tunani ma zata yi? Wayarta ce ta shiga ruri, ashe maigidan ne cikin ƙarfin hali ta miƙe. Ta same shi da laptop yana harkokinshi,ta shigo ta zauna, jikinta ba laka, ya dube ta.

"Jummai ba ki jin daɗi ne?"

Ta ce, "shi ne dalilin kirana don ka san ko ina jin daɗi ko bana ji?"

Ya ce, "A'a." Ta ce "To yi maganar ka." Ya ce, "To dama kan batun aure ne da aka bani, cikin cijewa ya yi maganar, ya ci gaba su Baba Alhaji Sunusi ne suka ba ni mata," zaraf ta miƙe kana nufin Hadiza? Ya ce, ita, tayi wani guntun murmushi, sannan ta ce, "Allah ya bada Sa'a." Ta fita ya bita da kallo ya san gatse ta yi da ta ce Allah ya bada Sa'a.

Ya lumshe idanu, ya gama da nan sauran A'isha, duk da ba ya jin ta yasan ita ba zata ce komai ba.

Ranar ko runtsawa Hajiya Jummai bata yi ba,ta ma rasa me zata yi taji sanyi? Ta san Hajiya Lanti kamar yunwar cikinta, duk cikin dangin maigidan nata ɓarayin mahaifinshi ba mafaɗaciya irinta. In ma asirin ne take taƙama dashi ta san zasu goga,don haka dolenta ta nutsu kada ta yi saurin nuna za ta ɗauki wani mataki kan Hadiza,ta sani su Hajiya Lanti lashe money ce,ta jima tana son ƴarta Hadiza ta auri Alhaji Saddiƙ,don dukiyarshi. Wannan lokacin bata damu da cewa ƴar ta mutu ko tayi rai ba,in har za su samu kuɗi Hajiya Lanti gogaggiya ce ta samu duniya, ita ce mace mai faɗa a ji cikin matan Alhaji Sunusi,ku san ita ce ke juya gidan son ranta. Ta taɓa jin labarin ta gurin Boka na kan dutse. Lokacin da taje da buƙatar mallakar mijinta a hannu,Boka na kan dutse ya shaida mata cewa,wata Hajiya Lanti ita ce mace mai tsananin Sa'a, wadda ta samu mallaka ta ƙarshe a gurin Aljanunmu.

Tun daga kanta har zuwa yau ba mu kuma ba da irin wannan mallakar ba, bata samu matsala a gurin gano kowace ce Hajiya Lantin ba, sai dai ta gano dangin mijinta ce, don haka ta haƙura da ta so su haɗa ƙawance da ita, da irin waɗannan tunane-tunanen ne gari ya waye mata.

Ita ko A'isha ba ta san me ake ciki ba, suna ta fama da jarabawar da ke fuskanto su lokacin bikin Uncle baifi sati biyu ba, da yake Uncle bai ɗauki bikin da wani muhimmanci ba, ya yi zuwa gurin A'isha ya kai nawa, amma bai ce mata komai ba game da bikin nashi,hasalima shi mantawa yake yi da batun wani auran shi. Bai ma san dalili ba,in dai yana tare da A'isha ya kan manta da duk wasu lamura na shi, ballantana ma yanzun da ta mallaki abin kallo.

Yana son ganinta cikin kayan makaranta,ko na zaman cikin makaranta , har dai ace bata saka hijabi ba,ƙirjinta yana mishi ƙyawun kallo. Sirantakarta ce kurum yake ganin matsala sai dai yana son yanda take da tsawo,dan tsayinta na sa shi jin alfaharin kasancewar ta matarshi,yana son taɓa jikinta sai dai yanda take ba shi girma na saka shi yaji nauyinta.

Wani daɗi yake ji duk lokacin da ya riki tafin hannunta, ta tsaya mishi cikin zuciya kuma bai rufe mata ba,yana yawan shaida mata yanda yake jinta cikin zuciyarshi, wanda ita kuma haka yana saka ta jin daɗi har ma tayi kewarshi,in ya yi kwanaki bai zo ba.

Yau saura sati ɗaya bikin shi,ya yi dai ta maza ya kira Abbanta a waya ya shaida mishi cewa an bashi mata,wan mahaifinshi ya cigaba da cewa Friend wallahi ba da son raina zan yi auren nan ba, zan yi ne kawai don bani da yanda zan yi, maganar ta biyo ta gurin Hajiyarmu da Alhajinmu ne. Abba ya ce, "Haba Friend,ai ko kai ne ka gani ka ce kana so koyi kayi da sunna, ina fata dai A'isha bata ɗaga hankalinta ba? Don ka san mata ba su da hankali, yanzun sai taga cewa ita ba'a yi mata daidai ba, bayan Allah ne da kanshi ya umurce mu, Uncle ya ce, "Ai ita wannan baiwar Allah ce, wallahi friend tunda yarinyar nan ta zo gidana ko sau ɗaya ban taɓa ganin fushinta ba, kullum cikin fara'a take. Abba ya ce, Alhamdulillah, sai in mun zo insha Allah zan zo ɗaurin aure."

Uncle ya ce "To shi kenan, sai ka zo kenan."

Washegari Sunday (lahadi), Uncle gurin Beby ya nufa, suna zaune suna fuskantar juna, ta rasa dalili in tana kusa da Uncle sai ta samu kanta cikin wani yanayi da ba zata iya cewa wane iri ba ne.

Ya dube ta da murmushi, Beby kullum ƙara ƙyau da girma ki ke yi,ta ce ko dai tsawo? Ya ce,kinsan cewa tsawonki yana ɗaya daga cikin abinda yasa nake sonki? Ta rufe fuska da dogayen tafukan hannunta, sannan ta ce, wai da gaske kana sona? Ya ce, sosai ma, kada ki ga yanda na ƙosa kuyi hutu wannan karon domin na san yanzun kinsan abinda ake yi a samu ciki ko? Cikin cinya ta saka kanta, sannan ta ce ni ban sani ba fa,ya ce to ai koya miki zan yi,kina so? Ta girgiza kai alamun a'a,ya ce amma da ai kin ce in nuna miki kenan kin bincika kamar yanda na ce,kafin ta yi magana wayarshi ta soma ruri,yana cirowa yaga Hadiza ce, bayan sun gaisa take cewa wai ƙawayanta zasu zo amsar kuɗi gurinshi zasu zo ko gurin abokanshi? Ya ce, mata ba ko ɗaya,su gaya mata ko nawa ne sai tayo mishi waya zaya aiko a kawo mata, ta ce shi kenan. Ya dubi A'isha wadda zuciyarta ke son sanin wacece Hadiza? Ya ce Beby dama na zo ne da magana sai kuma na manta kin san cewa in ina kusa da ke ina manta komai da komai ne? Ta yi ƴar dariya tare da cewa, wace magana ce? Ya ce, "Beby mata aka bani." Ta kafa mishi idanu,ko ƙiftawa sannan ta ce,ban gane ba? Sai kuma ya samu kanshi da ɗari-ɗarin gaya mata, sai dai dole ne ma ya daure ya sanar da ita saboda ance magana zarar bunu, kuma ya riga ya furta. Ya ce, "kin san Baba Alhaji Sunusi?" Ta girgiza kai ni ban san shi ba,ya ce kin san Hadiza? Haushi ya ma hanata magana, kallonshi kawai takeyi,ya ce ita ce aka bani ƴar wan Babanmu ce,yau saura ƙwana shida bikin."

Idanu A'isha ta zaro, saura ƙwana shidda? Ta taɓe baki, sannan ta miƙe tsaye tare da cewa, "Allah ya ba da zaman lafiya." Ta nufi cikin makaranta,sam bai za ci haka daga gareta ba, ita ko ko gani batayi, ta isa ɗakinsu kan gado ta ƙwanta, ga mamakin ta sai kurum ta ji hawaye suna ƙwaranya a kan kumatunta.

Wato ita Uncle zaya yi wa haka? Wai an bashi mata kenan, ita ba son ta yake ba,dama bai wani damu da ita ba,shi kenan yanzun zaya daina gaya mata kalamai masu daɗi, haba ita ta sani in ba baya son ta ba ai bazai kasa kula ta ba,bai taɓa neman ta ba haba ya ci ace tun tuni ma ta gano wannan matsalar, amma ba komai yaje ya yi ta yin auran, Umma ta ce,in bana gyara mishi shimfiɗa sai ya ƙara aure, duk hutu sai ta gyara mishi ɗaki amma hakan bai sa ya sota ba. Tana cikin wannan halin su Samira suka shigo, cikin sauri suka isa gurinta, nan suka shiga tambayarta abinda ya same ta. Sun ruɗe ƙwarai,domin ba su taɓa ganin A'isha musty cikin wannan halin ba.

Samira ta ce,"A'isha Musty me ya same ki ne? Don Allah tashi ki ji mu." Jin lallashin da suke mata ya saka ta kukan sosai,ba ta iya cewa komai ba,sai da tayi ma isarta sannan ta share hawayenta. Samira ta ce,me ya same ki? Wane ne ya ɓata miki rai? Ta ce, Uncle ɗina ne. Amina ta ce,me ya yi miki suka haɗa baki gurin cewa, Uncle ɗin ki dake matuƙar ji da ke? Ta ce,wai fa aure zai yi, dariya ta kama su,don zai yi aure ke ba abin murnarki ba ne? Ta yi shiru ita ta manta ma da ba su san cewa Uncle mijinta ne ba,don haka sai ta ce ai ba zaku gane ba ne, duk yanda muke da Uncle wai ace sai yau zai gayan bikinshi saura ƙwana shida bayan duk sati sai ya zo,ni kun ji damuwata." Suka ce ki mishi uzuri,ki ka sani ko abin ne yazo mishi ba cikin shiri ba?" Ta ce,Umh, daga nan ba ta sake cewa ƙala ba, domin ta gane ba zasu fahimce ta ba.

Tun daga ranar ba ta da sukuni, duk bayan awa ɗaya sai ta lissafa sauran ƙwanakin da suka rage na bikin Uncle ɗin nata,su ko su Samira mita suke mata kan cewa ta yi wa Uncle ɗinta afuwa, tare da ba shi uzuri. Ita ko Amina cewa take ina ma ba lokacin makaranta ba ne,su zo mata biki har ma su ga Antin tata,wato amaryar Uncle ɗin nata,a cewarsu ta yi dacen miji. A'isha kan ja tsaki tare da cewa, "Allah ya sutura,ta zama Antynta,su kuma suce dole ne tunda tana auren Uncle ɗinta. Aisha kan yi tsaki ta yi shiru kurum.

Shima Uncle na shi gefen yana cikin damuwa, wato damuwar Beby ita ce ta ɗaga hankalinshi. In ya tuna yanda ta wuce yana kiranta Beby-beby tamkar ba ta ji shi ba haka ta yi. Dama Beby tana fushi? Itama kishi kenan gare ta? To me yasa ba ta kishi da Jummai sam? Koda yaushe tunanin A'isha ke ranshi, tamkar ya ce ya fasa auran yake ji. Cikin haka aka shiga bikin.

Abba ya shigo Katsina,ana gobe ɗaurin aure ka ji daren da ya hana mutum huɗu bacci, A'isha ƙwana tayi sallah tare da addu'o'i, tafi maida hankali ne ga roƙon Allah ya rage mata kishi cikin zuciyarta. Jummai kuwa ƙwana ta yi neman mafita inda ta farka da mummunan ciwon kai...



########
[12/11, 21:33] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 6*


Hadiza kuwa ta ƙwana da farin cikin samun mijin nunawa Sa'a ga kuɗi ga ƙwarjini,shi kuwa Uncle tunanin Beby ne ya hanashi bacci,ya ƙosa gari ya waye sati ya je school ɗin shi da Abbanta.

Aisha ta farka damuwar da ɗan sauki,ta yi tunanin gara ta rungumi ƙaddara tunda auren babu fashi,sai dai matsalarta ɗaya,dama Uncle ba ya son ta? Ta kan ba kanta amsa da cewa eh,tunda gashi ya yi wata a madadinta. Tana son samun natsuwa badan komai ba sai don jarabawar da ke tunkaro su,nan da satin da zasu shiga,ta sani ƙarƙari nan da sati uku za su yi hutu maimakon Uncle ya bari sai sunyi hutun ya yi auran. Sai kuma tayi tsaki ta ce, ita dai tana son cire batun auren nan na Uncle daga zuciyarta.

An ɗaura auran Uncle da Hadiza da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na ranar asabar, bayan an tashi daga sallah,ko jiran walimar abokan da nashi suka shirya bai yi ba,yaja Abba da cewa su zo suje gurin Beby a makaranta, Abba ya ce a'a ka barta kawai,ni yanzun zan ɗauki hanyar garinmu."

Uncle ya ce "friend dole muje ka ganta,zata ji daɗi saboda wancan hutun nan kaita gida ba." Abba ya ce,shi kenan muje.

Suna kan hanya, Nafisa ta kira shi tana cewa, "Brother,tun jiya na ke son ganinka,ya ce gamu nan zamu je

Please Login or Register in order to submit comment