Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kudin yayi can qasan aljihunsa..
Dama kullum daga anyi magriba nake dawowa nayi sallh isha anan.
Zaune nake quryar daki akan abun sallh. nagama sallhn ne nazauna ina adu'a,,, dayake yau akwae nefa guri dukya dau haske.
Ganin mutun kawae nayi tsakar dakin kaman wanda aka jefo........
1/25/24, 10:57 - Seerat. 🥰😇: SANADIN AUREN WURi.

Story & writing

By

YASEERA NASEER.

Free book

Pg23.

A raxane nakai dubana gunsa dukda indq sabo nasaba d halinnasa.

,Ko uffan baicemun b nikuma bancemai b ganin ko gaisuwa bayaso shiyasa naja bakina na tsuke,.

Gefen gado yaje yazauna trd ajiye bokitinda yashigo d shi ,, bokitin naketa kallo trd san sanin meye a ciki ,saidae ba halin naymar tambayar,,.

Tsit dakin yayi nadan lkc ,, inasan namar tambayar batun xuwana gida saedae km tsoronsa yahanani,

Saina Budi baki da niyar magana km SAINAGA nagaza,.sai musumusu nake da baki.

Dan dagoda idona nayi dannaga yanayi nda fuskarsa take,saidae muna hada Ido yagame gavas da yamma kudu d arewa, yagame girar sama data qasa, kaman wanda baitaba ganin abun farinciki b a rayuwansa,,.

Yanda naga yasha mur dinne ya matuqar tsoratani wanda Saida naji kaman xuciya ta xata tsage.,

Nan take jikina yahauyin rawa kaman wanda aka fitar DAGA fridge.da sauri namiqe inasakin marayan kuka,,trd komawa falo.

Ss gumburajo yakejin haushinta ,, musamman baqin kukannan na muna furci.tom kodae tasan da batun kudinnan ne ??,,

Harna kai falon natsinki muryarsa a tsawace yana fadin kee zo nan,'

Nan take naji WANI irin tsoronda nakejin yaqaru kaman naruga a guje saedae b Halin yin hakan .,,
A matuqar tsorace nadinga bin hango ina rakubewa jikina sai kyarma yake,,inata kuka qasaqasa harna qarasa dakin.

Haushine yaqara kamashi ganin yanda takeyi din.

Tasowa yayi yayo inda take tsayedin,,a hasale yakama gashin kanta wanda yakenan da dan banxan yawa dkm tsawo,,sulbinda gashin yakeda ne yasa saiya kama ya subuce mar.

Ke da baqar burar uba wa kikewa kukan iskanci??cikeda qara kidimewa fitsarinda banama jinsa naji yafara biyar qafafuna zuwa qasa,.

Ganin fitsarinda takeni yaqara tunxurasa ,yaqara Jan gashin d qarfin tsiya har wuyanta nayin baya.


Wllh saikin gayamun ubanme kikewa kukA,baqar muna fuka, shegiyar yarinya mai xubin aljanu,.

Ss jikinta ke kyarma hawaye kuwa kaman badaga idone suke fitaba, tanasan tayi magana saidae sam muryarta taqi fita tsananin axaban xafin kama mata gashi d yayi ,km ga wuyanta yayi baya kaman xai karye,.

Qafafunta ne suka gaxa daukanta wanda tsananin axaban da take ji yasata sulalewa xuwa qasa.

Qasan yabita trd cewa baraki gayamun b,eye lallai yauko saina ci qaniyarki,wllh,,.

Cikeda radadin abun ga idanuwana sunfito quruquru kaman xasu fado ,,,

Nashiga magana a rarrabewa ,, Dama dama dama inasan nasanarma inasan naje naga Amanane,,

WANI mugun kallo yamata kafun yace wacece aaamanki,,cikeda sheshsheqar kuka tace mamana.

Sakinta yayi kafun yaqara game fuska yace .,,"ci Kika rasa ko Sha Kika rasa.,

Sam banma fahimce nufinsa b Amma tsaban tsoracewa ne yasa nashiga gyadamar kai ,,"

To baki rasa ko1 b ,Amma kike maganar xuwa gida,ke a dole ga mai aure burni,mtsssss shegiyar yarinya Auran jaraba,,wllh nikam an laqamun wahala,

Ni banma taba ganin muna furci irinnaki b,salan kije kisamu shairinda Kika laqamun koh,,.

Amma ai wannan yama xama cutarwa kaman Kinga mugun abu,haka kawae kitasani a gaba kinamun kuka,a dole ke naji tausayin ki,.

Tom wllh duk abunda kike nina fiki xama tsohon shege,

Maxa tashi kibarmun guri nakumajin bakinki kina damuna d kukA ko km kisake cewa xakije gida kiga abunda xanyi miki.

Saina cire miki haqoran gaba,,baqar muna fuka yar qarama dake sai iya kissa,.

Bacemun da gani,,

jikina na rawa namiqe nakwasa d gudu har Saida qafata tadaki bakin qofar dakin,

Daidai babban yatsar qafatane yadaki ginan,,aiko jinayi kaman raina xai fita ,,.

A matuqar axabe nafadi qasan falon Ina kama qafar trd ratsa WANI irin uban kukanda yafito daga rayuwata,,.

Bude baki nayi iya inda yankan bakin YAKE trd sa tafukan hannayenna ina dade bakin gudun kada qarar kukan yafito waje,.

Murqususun wahala nake inajin kaman raina xaifita.

Inacikin yanayin axabar ne naji yana fadin da qaniyanci wa Kika ajiye xai goge fitsarinda kikama mutane.

Da sauri namiqe,, trd xuwa dakin inajan qafa,

nakam rufe bakina Amma sam nagaxa nahanama hawaye xubowa daga idona.,

Qyalle na dauko nashiga goge gurin jikina sai kyarma yake.,

Harna tashi xanfice,'yace tom wanda yasamu qafata fa,'ko nine xan goge??

da sauri naje nashiga goge mar qafar dukda banga INDA fitsarin yataba b,,.

Cikeda rashin sa'a hannu na yakai gurin uban fasonda ke qafarshi,,aiko kaman rexa sai radadi naji a dan qaramin yatsana,.

Da sauri nakai dubana gurin qafafunsa, 'tsorone yakamani ganin fasonda ban taba ganin mai irinsa b, dama bantaba ganin qafafunsa b da sauri namiqe trd komawa falo,.
Mtssss wllh duk ranarda Kika kuma mun fitsari a daki sainasa kin lashe sa,,.tunda abun iskanci ne.

Kwanciya nayi akan dogowan kujera,,'hawayene suka shiga wanke mun fuska
,
'ga radadinda farcen qafata kemun ga km tunanin abunda gumburajon yamun.,

Yanda naga safe haka naga dare,Sbd daga nadan runtsa ynx yatsar nan na suka ,,ba shiri xanmiqe xaune nakama qafar,,har aka Kira assalatu a kunnena,,

Km sai lkcnne bcc yakwasheni,,kamar daga sama naji WANI uban duka a tsakiyar bayana,,wanda saura kadan nayi hauka sbd naxaci tabaryace ko guduma aka danqaramun.

Tsaye namiqe daniyar guduwa saidae 'jinaye ansa qafa antakemun daidae farcenda kemun balain ciwo gashi dukya kunbura.

Aiko cikeda ficewar hankali nabuga razanannen ihu nda Saida yajanye qafar TASA daga takanda yamun.,,,

Fadi nayi ina kama farcen trd bude baki kaman bakin xai bare ,saidae tsananin axaba yahana qarar kukan fitowa.,,'

Mulmulawa nayi nakuma na mulmula ,narasa duniya nike ko akasin hakan.

,cikeda tashin hnkl ,,kafun naiya furta ( innalillahi wa'inna ilaihi raji'un).

Wayyo Aaamana wayyo mama jaana ,, mutuwa zanyi,dan allh kuxo KU taimakeni,,'

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,.


Dan girman allh Kayi hqr, wllh baxan kuma tambayar ka zuwa gida b.

Tadan bashi tausayi Amma saidae bayasan yanuna,Sbd sam bayasan ta rainasa sbd ya lura so take ta tonamar asiri.

Sbd idan taje gida aidole AYI maganar kudinda aka bashi yabata,.

Qara tamqe fuska yayi ,kafun yace,,da kaxakaxa uba ,,wa Kika ajiye a gidannan daxai dinga diban ruwa.

inace ,

,a qauye da rijiya ma AKE amfani,''tom barae nan dayake famfo ne dasu,,Amma tsaban iskanci d lalaci,,so kike sai anje andibo miki,,gashi yanxu natashi ko ruwan tsalki babu a gidan.'

Girgiza kai nahauyi trd uban hawaye .

Shuri yayi da tukunyar lakarda ke gurin,,,Saida tafashe.

Hakanne yasani miqewa b shiri,trd fadin dan Allh Kayi hqr xanje nadibo idan safiya tawaye.

Kaxan ubannan tom yanxu da wasu xanyi arwalar ,,wllh maxa wuce kije kidubomun,,..

A matuqar tsorace namiqe jikina sai rawa YAKE,,qafana kuwa sai dingishi nake,,.

Madafi nabude trd dauko babban roba,

,dukda nasan bana imata Amma saidae itace a kusa km ina tsoro n natsaya neman wata yaqara takamun farce.

Da tsoro nafito garka kasancewar da asubace,,km kowa bangani b, hakanne yaqara rudar dani nakife a qasa inata faman kukA,,

Kafun namiqe nakama hanya cikeda tausayin rayuwata,..

Gashi km bantaba fitowa garka b,barae nasan INDA famfon YAKE,,tsayawa nayi cikeda rashin sanin abunyi.

Ga sanyin hunturu nda ake dana asuba sun hade guri1,,sunbada WANI irin sanyi mai keta fata daqashi yakai har bargo,,..

Sai rawan dari nk har haqoran a na hadewa SUNA bada qara.

Harna fito bakin titi bansan INDA famfon YAKE b,,km ga duhu,, hakanne yaqara tsoratani,,

Jikina yaqara daukar makyarkyata kaman ,,sauran gabobin jikina xai rabuda jikinnawa.,,,

Shuru nake inata zaran Ido,,kaman xasu fito ga dan uban haushinda sukayi ,,harda WANI tsaki2 nakeji acikinsu,.

Duk abunda naiya na adu'a Saida najanyo,.

Tsaye nk ina neman mafita daga maji roqon bayinsa.

Kaman daga sama naji qarar ruwa ta gefena koda najuya sainaga wanine ya bude famfo yana arwala.

Saida naga yagama kafun naja qafana xuwa gurin,,"'

Ina zuwa sainayi tsaye sbd bansan yanda AKE bude famfon b,,,na dade ina kallansa kafin cikin rawar hannu ,,nakai hannu nawa saman WANI abu dana gani saman fanfon na matsa,,.

Saidae ruwan Basu xoba,, hakanne yasa,,naqara kai hannun trd juya abun kadan 'nan naga ruwa sun xubo.
Diban rabin robar nayi Sbd koma wanda xai azani babu,.

Murdawa nakumayi naga famfon yadauke.

Daqyar na ciccibe roban zuwa kaina ,,,.

Saurinda nake ne yasa duk ruwan xubomun ajiki,,.

Aiko sanyi kaman qanqara AKE liqamun.

Ina kaiwa yahau fadan na dade ,.

Km yasani komawa naqaro,,,

Nice bansamu sukuni b,,,sai bayan fitarsa sallhn asuba din.

Daki nashige na gurji kukana Saida nafarajin xaxxabi,,,tukun namiqe nafada bayi nayi wanka trd dauro arwala.

Ina sallh ina kukan harna gama nahau adu'a inata fadawa allh ,,inakanyin kukan.

Yaukam komai bantsaya nayiba,,nawuce qofar inna,

Koda nafada na sameta tana hasa wutanda zata aza Mana dumame.

A matuqar tsorace takalleni ganin dukyanda na birkice duk jikina yayi jaaa km idanuwa a kumbure.

Daga sallama naxube kusada qafafunta trd sakin marayan kuka.....
1/25/24, 10:57 - Seerat. 🥰😇: SANADIN AUREN WURl.




Story & writing
By
YASEERA NASEER🥳.





Pg24.


*******†****************************************************.


Kallo1 zakama inna zaka fahimce tsananin tashin hnkl fal fuskarta,.

MAGANA tafara yiwa jidon ,tana tambayar ta,meke faruwa?
Ganin taqi Bata amsa sai kuka takene yasa innar janyo jidon a jikinta,,saidae me zata gani,.

Idanunta Basu sauka ko'ina b,sai ga babban farcen qafarta,wanda yayi suntum dashi,dayake qafar farace,kana iya ganin yanda jini ya kwanta a gurin,harma kalan yakoma pink,.

Innalillahi,jido yaushe dan kakkare yaka maki harya kai haka bansaniba,,inace duk kwanakinnan nikam Banga koda alamarsa bace a qafarki,.

Ganin sai kukan take yasa inna fadin"jido kiyi shiru ki nutsu kimun bayani ,kingafa hankln yay matuqar tashi.

Dasashiyar muryarta tabudu,tafara bama inna LABARIN dukyanda sukayi itada gumburajo.

Imanine yama Innar yawa harma takasa furta komae,,Saida ta tsinki muryar jidon na fadin dan allh inna kibarni nadawo qofarnan taki d xama,wllh wataran yacema harda haqoran gaba saiya cire mun.


Sai a lkcn inna tasamu sararin ,furta Cire miki haqora pa??"gyada kai tayi ,, aa lallai yau naqara tabbata gumburajo nan bayada isasshen kai"ai wannan yazama cutarwa dkm rashin imani,,
amma insha'allh xansamae naymar nasiha,,ai muzgunawar yayi yawa.

Shine WANI lkcn zakaga iyaye sunajin tsoron aurarda yaransu WANI gari,sunfisan su xauna gari1 ,koba komae Saji duriyarsu dkm halinda suke ciki a gidajen auransu.

Saidae nikam abunma yabani mamaki ,,sbd tun zowanki gidannan bantabajin kince ga WANI dan'uwa nki yaxo b,,.

Km ba waya b komae,,Anya kuwa jido hannun iyayenki kike??

Zafafan hawaye ne suka qara zubowa daga idanun jidon wanda harma sungaji d kukan ,,hawayenne dai sukaqi sutsaya,,"

Lumshe idanun tayi a hnkl kafun tafara bawa inna lbrnta ,,wanda tasani a lkcnd tafara wayau har kawo sanda akai mata auran,,harta Fara ta gama innar kallon ta take bako kyafta ido,,,



Mlm gumburajo🥳.

Tasowansa daga makaranta kenan,kaman kullum yauma bawasu kayan arziqine a jikinsa b,,yayi huri harya yagaji,,.

Tafiyan ce dae taqasa yakeyi,,,harya kawo anguwar tasu ,,sabon gurin xamansa YAKE dosa,,tagurin INDA abokinsa Ilya YAKE kasa rakensa,yabi yawuce btrd yamar magana b,wanda kuwa tun bayan maganarda sukayi da ilyan, gumburajo yakama yariqesa da'ita,ko magana yadaina yimasa.

Harda gurin xama ma yacanja,,ynx can gaba da INDA Ilya YAKE kasa raken ,gurin wasu gayu na anguwar ,chan gumburajo yake xama.

Harzai wuce ilyan ,, ilya ,,yace sannu abokina andawo lfy??"cigaba yayi d tafiyan sa kaman bazai tankasa b,,kafun yace lfy,km cikiciki,,.

Ss Ilya yaso gumburajo yatsaya suyi magana ta fahimtar juna,,sbd sam bayasan xamansa da sababbin abokanda yayi,wato su inusa,, Sbd kaf anguwar bawanda baisan halinsu b,,

Suduka samarine,Amma tsoffin samari,wanda rashin abunyi ya hana musu aure,cikinsu kuwa bawanda baije gaba da secondry b,,aikinne dae Basu samu b,km gashi gayunsu yahana musu su nemi koda qwadago ne suyi.


Kullum tun fitowar rana har faduwarta SUNA zaune INDA suke xaman,,idan inwar safe tawuce,,su kakkabe sukoma ta rana,hakadae harsae dare sannan suwatse.

Su5 ne suke xaman ,,,inusa,habu,bilya,ilyasu,bala,.

Mayaudaran mutane ne naqin qari,madar gatane naqwarae,sukanyi amfanida ilminda sukeda su cuci dukwanda yaxo hannunsu, qare d qarau harda filaye sukewa takardar bugi su sayar,,sai mutum yafara Gina masu abu sunzo sugani,sai ayta darga,shiyasa a anguwar baruwan kowa dasu,Sbd mutane qalilanne Basu yaidara b,,Kota fanni n kudi kodae WANI abun.


Dukda yasan gumburajo bashida kudinda xasu yaudaresa Amma yana tsoron kada su jefasa baqar hanya. hardae yanda yasan halin sa da dan uban san banxa.

Shine yaso gumburajo n ya sauraresa amma yaqi, hasalima saiyau ya amsa gaisuwar da yakemar kullum yagansa,sbd shikam sam baya iya gaba, kullum sukayi fada da abokinnasa hukuma,shine ke Fara yimar magana.

Tun daga nesa suka tsinkesa tafe, hakanne yasa suka Fara sakarmar fara'arda su kadae sukasan manu farta,.

habu ne,yadanyi magana qasa2,inusa gafa mutuminnamu nan sarkin san banxa.

Gumburajo na qarasowa kuwa yashiga Basu hannu ana gaisawa,,kafun bilya yace"sannu mlm gumburajo y makarantar ?y qoqari?y dawainiya d yara?"'kai sai gdy bilya,ana fama.

Habune yakarbe maganar trd cewa,,ai mlm gumburajo kana qoqari,,sbd ynx babu malamai irinku,wanda sukasan aikinda sukeyi.
Nan suduka suka rufa SUNA qara xuga gumburajo,,akancewa tunda sunji ance hausa YAKE koyarwa ,km kaf fadin garin birnin Kebbi,b wanda yakaisa sanin aiki,INDAE GAMEDA koyarwane.

Suma zasuxo yadinga koya musu.

Sbd sunsan turanci Amma basusan hausa dakyau b,,,.suka qara dacewa Amma b takura mlm gumburajo,alfarma ce muke nema,.kaga mu bamuda girman kae,,Sbd INDA ace mune muka dade dakai kaman yanda kukA dade kaida Ilya,aida yanxu mun roqeka ,ka koya Mana karatun hausa.amma dayake Ilya kidahumi ne, yafisan yazauna da jahilcinsa,bai iya komai b,inbanda kasa rake.

Ss hancin gumburajo yaqara girma tsaban xugashinda sukayi,,yaji Dadi ss,Sbd kamar yanda sukemar kullum ,koyau sisinsa batayi ciwon kai ba,hatta d ruwan pure water,sune ke sayamar,barai shi abunci,harna dare , kullum saisun sayamar dafuwar qato,wato indomie dafaffa tagurin masu shayi,yauma harda qwai,a cewarsu,shi malamin mutum karramasa akeyi.

Gumburajo kam ss yau yakejin kansa wanine,,tunda harda manya YAKE koyarwa,,.

Yana gamacin abuncin yamusu SALLAMA trd godiya,,nan suka qara nuna mar ai hakan b,komai bane,tunda ai muma WANI abu mukeso dg gareka,,cikeda rashin fahimta gumburajo yace aff ita koyarwa ,shine WANI abun,,allh dae yakaimu gobe ,saimu Fara.

Ss jikin inna yamutu sbd itakam Bata tabajin tarihi irinna mlm hakkiwala b,.ss ta jinjina abun,tawani bangaren km tausayin jido,hardae da taji wai ba'a yaji a gidansa,duk halinda ' ya zata tsince kanta a gidan muji saidae ta daure tayita xama.
To ya kenan ga wannan mujin na jido tunma ba'a je ko'ina b,yafara d wannan to inaga anje gaba,Anya ko wannan zaman zai daure,,?? Haka suka wuni jugum jigum,,ita jido tanaji d ciwan yatsa,,ita km inna sai tunane2 take,,.

Hakadae suka wuni bamai cikakkiyar walwala,,har bayan isha.

Yaukam inna ce kadae tayi aikin abunci,,
Tana gamawa
taaxama jido ruwan dumi tayi wanka,,

Taxubo musu abuncin sukaci tare,,bayan sungama ne ,,ta kasa kunne danjin motsin dawowansa.

Shuru2,,saichan taji qarar bude shashin,,,.

Tashi tayi tadauke mayafinta,,taje tasameshi yana qoqarin shiga daga ciki,,,.

Sallama tayi trd fadin sannu d qoqari fa,,.
Juyowa yayi trd fadin yuw.

""Nace dama inasan magana dakae INDA Hali??"inajinki yace,,wanda tanan xaka fahimce rashin tarbiyarsa a fili.

aa ba'a nan b,a chan qofata,jidonma tanacan.
WANI kallo yashiga yimata,mai cikeda ma'a nonin rainin wayau,,kafun yace ,,muje.

Itace gaba yana biyanta har suka isa qofar,,.
Falonta tamar iso ,, yashiga,,
Jidonda yagani zaune ce,,yaqurawa ido,,yana mata kallan tuhuma,,

Gurin xama inna ta nunamae trd fadin bismillah,,

Zaman yayi trd fadin gani,,gyara Zama inna tayi kafin tafara da cewa
"Tom madallah gumburajo,,dama inasan ne ,,nama wata yar nasiha GAMEDA xaman takewar aure.

Mlm gumburajo shi aure d kake gani abune wanda allh ya halattashi tsakanin halittu2 na biladama,,km ya wakilta namuji a matsayin babba.

Saidae matsayinda yabasa na kasancewa babba ,bayana nufin namujin yadinga take haqqin mace bane,km b yananufin namuji n yadinga muxgunawa mace bane,km b Yana nufin namujin yadinga yin abunda yakeso bane.

Saidae yana nufin namujin yaxamo jagora km mai kare mutuncin macen,km mai kula d haqqoqinta wanda suka rataya akansa ,daga anshafa fatiha,,yana nufin nuna soyayya d tausayi agurin mace,,yana nufin taimakawa mata,akan kowane lamari da zata tsince kanta,,bi maana ,,

Kayi koyi d fiyayyen halitta manxon tsira,,wanda ingantaccen tarihinsa ne,,yakan taya matansa aikin gida km ya kasance yana ,, kiyaye haqqoqinsu,,

Yana xama yayi labari dasu km btrd tsangwama ko tauye haqqi b.


Daga ganin yanda gumburajo ke kada kafa zaka fahimce cewa ,b INDA tunatarwarr tayi tasiri a gareshi,,.

Juyawa yayi ya kalli jidon wacce tun shigowarsu kanta YAKE a qasa km batace uffan b,.

Kee nine nake muzguna miki??,,ko nine nake tauye miki haqqi??
Ss jikin jidon yadau rawa dukda tasan inna bazata bari yayi mata WANI abu a gabanta b,,Amma yanda YAKE maganar kadae Saida taji antar cikinta ta takada.

Ganin yanda gumburajo yadauke abunne,yasa inna saurin karbe maganar

,trd fadin A'a ko1 ni b abunda jido tagaya mun,,saidae kasan koba komai ,,

Dukwata mai irin shekaruna ,,bama jidon kadai b,harda kai na aifi sa'anka,,
Tom dan haka danna zauna daku namaku nasiha GAMEDA zamantakewar aure ai baxaixamo laifi b,
Kawaidae inasan ne kuduka kudaukeni a matsayin babba wacca tafiku shekaru km tafiku sanin al'amura GAMEDA zaman aure,,wacca insha'allh zanso kudaukeni matsayin uwa,,wacca zata dinga kula d ,abubuwan KU ,,na daidae dkm kuskure,,

Saina dinga muku nasihohi,,dukda nasan insha'allh kaima kanada naka sanin GAMEDA du wa'yannan abubuwa dana lissafo.


Hakanne kam,,yafada batareda ya amunce da abunda innar tafada b,,.
Kafun yamiqe yace Saida safe.

Itakam inna Ido kawae tabisa dashi ,,dantaga tsagwaran rashin mutunci,a tattare da yaran.

Numfasawa tayi kafun takai dubanta ga jido,,wacca keta faman sharar qwalla,,.
Tashi tayi trd komawa INDA jidon take,,tafara dacewa,,jido kiyi hqr jarabawa kowa da irintasa,,km insha'allh,,nikam xanxame miki uwa'uba,,ke xanxamemiki dangi,,

Xan cigaba da taimakonki harsae ranarda mai rabawa ta raba,,.

Kiyi hqr kitashi kikoma dakinki,,kar kuma abun yazama WANI saban laifi.

Miqewa tayi trd lumshe idanun ta ,,wanda xafafan hawaye suka sauko kan kuncinta,,.

Innace ta rakata har bakin qofar,,kafun tajuyo takoma qofarta cikeda tausayin,yanda jidon tasamu kanta a cikin matsalarda qananun shekarunta bazasu iya daukaba,,.

Irin hakanne idan yaro baisamu makwabi b,,saiya fada baqar hanya.

Tsayi tayi bakin qofar Tanata son hana hawayenda ke ambaliya a idanunta fitowa,,.

Saidae sam takasa,,hardae idan ta tuna wanda xataje ta tarar a qofar,,

Lumshe idanun ta tayi kafun tafara karanto adu'a tana saka qafarta a falon......




Seerat...........🖊️
1/25/24, 10:57 - Seerat. 🥰😇: SANADIN AUREn WURI.




Pg 25.



Da sanda nashiga falon batareda koyin dogon numfashi b,.
Ganin baya falonne yasa nasaki dogon ajiyar xuciya,.
Dogon kujera nahaye trd yin adu'a nayi kwanciya ta,Saidai inata fargabar yanda yadauke abunda inna ta Fadi masa,kada yaxo yamun duka.

Tun ina fargabar har bcc ya kwasheni,.

Shikam gumburajo tunda yafada dakin yayi kwanciya rsa,km yamaji motsin shigowarta,saidae shi b abunda ya damesa GAMEDA nasiharda innar tamasa,.
Shikam tunanin YAKE abunda yakamata yayi da kudinnan,sbd b qaramin buri ya axa musu b,
Yayi niyan raba kudin2 yabama jidon Ravi,,saidae dukya kalleta saiya ji haushi,.

A ransa kuwa yana ganin malm yaci amanarsa daya auramar rabun mace,Sbd shikam a gurinsa jido Ravi ce,tunda komae babu ajikinta,shi yanxu m,yarage tarewa daita, sbd bayasan raini,

km abun haushin kullum sai yaga yawuce wurin Amma koda xai dawo saiya km neman hanya,abu kaman Gam,.

Da tunane2 har shima bccn ya daukesa.

Kwanci tashi b wuya a gurin allh,.yau yakama sati2 kenan da jimuwanda jido tayi,.
Km Alhmdllh qafar ya warke,.

Kamar kullum yauma tana qofar inna kwance take a a qarqashin inuwar iccen diriminda ke qofar,dukda kasancewar lkcn hunturu ne,Amma yau ana xafi kasancewar rana ta bude ss.

Kwance take visa tabarma da filonda tayi matashin kai dashi,,,yar ves ce ajikinta,dkm dankwalin inna data daura, wanda baikai qasa duka b kasancewar tanada alamar tsawo ,.

Dukda bawasu kayane a jikinta b,Amma tayi MATUQAR kyau, musamman yanda take kwancen a rigingine,,"wanda hakanne yafitoda tsantsar kyau na cikinta har xuwa qugunta,,dayake ves ce ,,hakan ya bayyana jigidarda kenan fam mararta,,.


gurin cikinta kuwa,, kaman abunda aka saka xare aka tsuke,,inda kunkurunta ya taso gwanin burgewa,,.

Taqara fari tayi wanin irin kyau na burgewa,.
Ayanda take lamo din,xaka zaci bcc take ,,saidae idanta viyu, tunane2 ne kawae takeyi.

Inna ce tafito daga daki sanyeda hijab,cikin shirin fita,,.
Gurin jido tanufa trd cewa "jido wai bana hanaki tunane2 nan b,,.

Banaso ina ganinki shuru haka,Zama tayi trd kallon jidon ,kafun tace,,

dukda NASAN dole kidinga tunanin "gida"Amma namiki alqawarin insha'allh,idan allh yakaimu akai hutu xanje xuru km ,idan xandawo xansaka a ajiyeni ta DALIJAM din,.

dukda bansan gidanku b,Amma saiki gayamun sunanda xanfada ,,akaini gidan,saina karbo koda number mamanki ne,naxo daita Kinga ko gaisawa kuka dingayi kya rage wannan damuwar.

Yunquro wa tayi taxauna tana kallan innar,, murmushi fal fuskarta ,,kafun ta rungume ina,tana fadin ,,ngd ss inna allh saka miki da alkhair,,Amma Aaamana batada waya,,Kinga sai ki karbo number mlm ,babana.

Tafada tana kallan innar,, murmushi inna tayi kafun tace tom b matsala,, insha'allh haka xaa yi,,.

Kinga yanxu xanje kasuwa,na Mana cefane,idanna dawo,sai ayi kitson kannan naki, tunda hunturu ne dole ko anayi yana walwale kansa ne,yafi abarshi b kitso.

Dariya jidon tayi kafun tace,inna wllh kannan nawa haka YAKE Kinga ko lkcnd xaayi aurennan dayake ansan yanda gashina YAKE,ba wanda yabi takan amun kitso,

Saida mm jaana ,tace ai baxai yuwuba,takoma har ruga, taxoda wata maiyin kitso,a cewarta matar ta qware ss,komin santsin gashin mutum a rugarsu intayi mar kitso yana dadewa,,.
Inna ingaya miki haka tawuni a kaina,tanamun kitson, Amma wllh koda na kwanta' bcc safiya tawaye,,duk Ravi ya warware,.

Koda aka kawoni garinnan bako gutun kitso akaina.

Cikeda so da QAUNA irinna uwa da 'ya inna ke kallan yanda jido ke Bata lvr,,.
Murmushi tayi kafun tace ,to nimadae koda kullum xai warware ,saina km yimiki sabo,,.

Dariya jidon tayi ,,trd cewa inna xaki gajifa,,Hala kin iya kitso?? Eh tace trd miqewa tana fadin jido ,barni natafi danna samu nadawo d wuri,,,""
Tom inna Amma saina rakaki kinhau adaidaita""dariya inna tayi kafun tace tom muje,,.

Mayafina nadauko muka fice,,tafe muke muna fira har muka kawo bakin titi.

Dayake rana tayi tsaka,ba mutane a wajen,,km ko abun hawan ma bb,,.

Munjima a tsaye ba kowa sai qana nan yara masu wasa, kafun chan,,wata murya ta ratsa kunnuwanmu,,

Ana fadin ase tanka,"ase tanka,.

Dasaurina na juyo jin muryar ,,tukur na gidanmu,,shine babba a gidanmu dan henno ne,,.Amma sam ba ruwansa shikam,bai dauko halinta b,.

Koda na juya kuwa shidinne,,
Yanata fama da buhun tanka akansa,dukyayi xufa,,.

Sam bai lura dani b,,.
Da gudu naruga trd dalewa a bayansa,cikeda tsoracewa ya yada buhun tanka nda ke kansa,,kafun yasa hannu ya fincikoni.

Bude Ido yayi cikeda mamaki,,nikam sai qyalqyala dariya nake kafunna ce, lahh yaya tukur ashe harnan kake xuwa.

Sauke ni yayi a qasa kafun yacee lahh jido anguwar nan kike aure,,
Cikeda WANI irin farin cikinda sam nakasa misaltawa nace""eh kagama ga gidan can.

Juyowa nayi fara'a fal fuskata harma da raina,ina kallan inna wacca ta kafeni da idonta wanda ke taf da alamar tambaya.

Dariya nakumayi wanda yau jinake kamar anban aljanna,"nace inna kinga ya tukur,,dan gidanmu ne ,,babanmu1 dashi,,.
Ashe yasan garinnan,,Kinga harda yawoma

Please Login or Register in order to submit comment