Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai haƙura ya sake ta, Ma'u kuwa kuka kawai take tana so ta ƙwace daga riƙon da Haidar ya mata amma yaƙi sakinta.....

Ibn muzzafar kuwa dake zaune yana kallon yadda Haidar yake ja inja da bil'adama, sai abin ya matuƙar bashi mamaki, lalle Haidar ya daɗe da makancewa a soyayyar bil'adama, wata tsawa ya sake daka mai a karo na biyu, da sauri Haidar ya sha jinin jikin sa amma bai saki hannun Ma'u ba, cike da isa ibn muzzafar yace
"Haidar!!!! Ina mai umartarka da ka sakin mata hannun ta..."
Sakin hannun Ma'u haidar yayi yana aikawa da Suraj wani irin mugun kallo, mayar masa da martani Suraj yayi a ransa yana ayyana
"ai ba tsoron ka nake ji ba.."

*Kai Suraj kodan kaga da ibn muzzafar ne a kusa🤔dan shi kanshi haidar ba kanwar lasa bane😹*



Gyaran murya ibn muzzafar yayi Yana kallon haidar daga bisani kuma yace
"Nasan izuwa yanzu ka fahimci cewa, nasan komai kuma nazo ne dan na kawo ƙarshe al'amarin..
Haidar yaushe ka zama mai zalunci.? Yaushe ka zama mai tauye haƙƙin rai.? Shin ko ka manta cewa hakan da ka aikata ya saɓawa al'adar mu da addinin mu, kuma sai ka fuskanci hukunci na dai dai da abinda ka aikata, saboda haka ina mai umartarka a karo na biyu, da ka rabu da wannan bil'adamar tayi rayuwar ta cikin salama, kazo cikin jinsin ka nama alƙawarin duk wacce kace kana so, ko ƴar waye acikin duniyar aljanu zan nema maka auren ta..."
Durƙusawa haidar yayi cike da rauni yace
"Allah ya gafarceka! Na yarda da duk hukuncin da zaka min, amma dan Allah kar kace sai na rabu da ita, wallahi ina sonta fiye da rayuwa ta, bazan taɓa barinta ba koda da daƙiƙa ɗaya ne..."

Ibn muzzafar yace
"Ba wai na tambaye ka abinda ke cikin zuciyar ka bane, umarni ne na baka ba shawara ba, ina so ka furta da bakin ka cewa ka rabu da ita.."

Cikin dagiya da taurin kai Haidar yace
"Allah ya gafarceka! Ban fara sonta ba dan in rabu da ita, na fara son tane dan in dauwama da sonta na har abada...."

Fusata ibn muzzafar yayi da yadda Haidar ya ke mai jayayya, cikin tsawa yace

"A karo na ƙarshe haidar Ina umartarka da ka rabu da ita..."

Miƙewa tsaye Haidar yayi ido cikin ido yake kallon ibn muzzafar yace
"Gaskiya bazan rabu da ita ba, kawai ka cire kanka a wannan al'amarin, dan zan iya fito na fito da koma waye, kuma zan iya faɗa da koma waye a kanta..."
Nuna Suraj yayi da ɗan yatsarsa yace

"Kayi gaggawar sakin hannun matata, idan ba haka ba zan illataka anan gurin.."

Ibn muzzafar ne ya nuna haidar da wata sanda dake hannun sa, take anas sarƙa ta bayyana jikin Haidar duk ta ɗaɗɗaure shi, fisge fisge Haidar ya fara nasan ya ga ya fidda sarƙar daga jikin sa, amma ya kasa, ɗagowa yayi yana kallon ibn muzzafar kallo irin na tuhuma, takowa ibn muzzafar yayi har ya ƙara so kusa da Haidar, sannan yace
"Ina ga kamanta cewa duk wani hatsabibanci da shu'umanci da kake taƙama da shi, a gurina ka ɗauki darrusa..
Saboda da haka dole ka rabu da ita ko ka ƙi ko ka so.."

"Ya Shaikh!! Karka aikata haka, ina sonta itama tana sona, kar ka shiga tsakanin masoya biyu.."

Shanye da mamaki ibn muzzafar ya kalli Ma'u yace
"Yarinya wai haka ne..?"
Girgiza kai Ma'u tayi alamar a'a, ibn muzzafar yace
"magana zakiyi yarinya.."
A hankali Ma'u tace
"A'a ni ba muyi haka da shi ba...."
Ibn muzzafar yace
"To kaji dai.."
Cike da rauni Haidar yake kallon Ma'u yana girgiza kanshi yace
"Haba Nurul aini! Karki aikata haka, zaki yi babban kuskure...."
Cikin kuka Ma'u take girgiza wa Haidar kai tace
"Kayi haƙuri Haidar! Hakan da nayi shine dai dai, ka barni haka dan Allah inyi rayuwata kamar yadda kowa yake yi.."

Ƙiyasta yatsu ibn muzzafar yayi, take anas waɗannan samudawan aljanu suka matso suna jiran umarni, kallon Haidar yayi sannan yace
"Har yanzu kana nan akan bakan ka? Ko kuwa ka yanke shawarar rabuwa da ita.."

Cikin kafiya Haidar yace "ina nan kan bakana.."

"Anya kuwa kasan wani kalar hukunci zan yi maka...?"

Cikin rashin tsoro Haidar yace
"nasani kuma na Amince.."
Kallon waɗannan samudawan aljanu ibn muzzafar yayi sannan yace
"Ku kai Haidar cikin kogon dutse mai feshin wuta, a tsare shi a ciki na tsawon wata huɗu baci ba sha, kuma muduk bai furta zai rabu da wannan bil'adamar ba, har wata huɗun nan ya cika to za'a sashi acikin ruwan narkakkiyar dalma, har tsawon shekaru biyu..."

Haidar kuwa ko ajikin sa, asali ma sai murmushi yayi mai ciwo yana bin Ma'u da kallo, ta sowa Ma'u tayi da gudu tana dafa ƙafar Haidar cikin roƙonsa tace
"Dan Allah haidar ka amince, banso a ta dalilina ka shiga cikin wata wahala.."

Murmushi ya ƙara saki mai ciwo yace
"A kanki zan iya jure ko wacce azaba da wahala, kuma duk mun daren daɗewa sai na dawo gare ki..."

Yana gama faɗa ya ɓacewa ganinta tare da samudawan aljanun nan................✍️


















*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*









~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/27, 5:06 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


__________________________________________________





*57 & 58*






________________Durƙushewa Ma'u tayi a ƙasa tana sakin wani kuka mai sautin gaske, Ba haka taso ba, taso ace Haidar ya amince da umarnin da aka bashi, saidai shi ɗin rayuwar sa ba kamar ta kowa take ba, ko a cikin jinsin al'janu haidar daban yake, duk da cewa ya zalunce ta amma har yanzu akwai ɓarɓashin sonshi a zuciyarta, baza taso ace a ta dalilinta wani abu mummuna ya same shi ba......
Tana cikin wannan yanayin taji andafata ta baya, ɗagowa tayi a hankali yayin da idanun ta ke zubar ruwa, Suraj ta gani durƙushe a kusa da ita yana girgiza mata kansa, share hawayen ta tayi tana sakin ajiyar zuciya.....
Ibn muzzafar kuwa da ya ƙurawa Ma'u ido yana nazartar ta, gyaran murya yayi sannan ya kalli Ma'u yana cewa
"Yarinya kije kuyi auren ku cikin kwanciyar hankali, insha Allahu ina mai tabbatar muku Haidar bazan taɓa sakin shi ba, har sai ya janye a ƙudirinsa, saboda haka keda iyayenki ku kwantar da hankalin ku, daga yanzu baku da wata matsala, *NI NABARKU LAFIYA* "
Ya faɗa yana ɓacewa ganin su.....
Cikin farin ciki da tsananin murna malam muddasir yace, "kunga ikon Allah koh! Cikin ƙanƙanin lokaci gashi komai zai zama tarihi.."
Kawu Salisu da Daddy suma cikin murna Da farin ciki, suke godewa Allah abisa kawo musu ƙarshen Wannan al'amari da yayi, can kuma sai kawu Salisu yace "to amma wani hanzari ba gudu ba, shine batun cikin da ma'u take da shi na wannan *AL'JANIN SOYAYYAR*..."
Murmushi malam muddasir yayi sannan yace
"Ai cikin al'jani ne! Kaga Bana mutum Ba, saboda haka wannan ba wata matsala bace, da zarar anyi mata aure mijinta ya yi mu'amalar Aure da ita, to insha Allahu cikin nan zai zama tarihi..."
Nan suka cigaba da tattaunawa akan Maganar, daga ƙarshe Malam muddasir ya basu wasu magunguna da za'a bawa, Ma'u ta riƙa sha......
Shi kuwa Suraj yana ganin an kammala komai, ya janye Ma'u suka yi waje cikin mota.....
Sosai yake nazarin ta ganin kamar tana cikin damuwa, yasa ya riƙo hannuwanta yana cewa
"Husnah meye yake faruwa ne naga kamar kina cikin damuwa.."
Ɗago da kanta Ma'u tayi idonta cike da hawaye, girgiza kai kawai tayi alamun babu komai...

"Ah ah! Sai kin faɗa min, gashi nan yanayin ki kaɗai! ya isa yasa a gane cewa kina cikin damuwa...."

Hawayen da take ƙoƙarin maida wane suka zubo, hannu tasa ta share sannan tace
"Wallahi yaya Suraj! sai nake ganin kamar hukuncin da aka yiwa Haidar yayi tsauri.."
Sakin baki Suraj yayi yana kallon ta cike da mamaki, rasa abin faɗa yayi! Can kuma sai yace

"Yanzu ke kina ganin hukuncin da aka yi mai yayi Tsauri, karfa ki manta Haidar shi ya kashe miki yusif ɗinki, kuma ma ko ba haka ba ai shi Haidar al'jani ne, duk wata azaba da za'a yi mai to mai sauƙi ce a gurinsu su al'janu, ba kamar mu bil'adama ba..."
Ajiyar zuciya Ma'u tayi tana cewa "haka ne kuma."
Suna cikin hakan ne su Daddy suka fito tare da malam muddasir, sosai Daddy yayi wa malam muddasir alheri mai yawan gaske, a cewar sa ai duk a ta dalilin sa ne komai yazo ƙarshe...
Sallama suka yiwa juna cike da mutuntawa, kai tsaye cikin garin Katsina suka nufa, kasancewar inna da take kwance a asibitin cikin garin....
Murna gurin inna kuwa! faɗa ma ɓata baki ne, yaji daɗin labarin da su kawu Salisu suka zo mata da shi, aikuwa ba shiri inna ta miƙe, Dama ciwon nata na ɓatan Ma'u ne, yanzu kuwa tunda taga Ma'u cikin kwanciyar hankali ta samu lafiya....
Bayan likita ya bata sallama suka ɗunguma sai gidan Daddy, anan suka yi kwana biyu, tukunan aka sa ranar bikin Ma'u da Suraj Sati biyu, momy kuwa tuburewa tayi sai an bar mata Ma'u, ba haka inna taso ba, taso ace ta tafi da ma'u kodan ta gyara ƴarta tsab, haka su inna suka wuce batsari Suka bar Ma'u a wajen momy........
Zaman Ma'u a gidan yasa wata shaƙuwa da soyayya a tsakanin su ita da Suraj, sosai suke nunawa junan su kulawa da tsantsar soyayya, batun Haidar kuwa ya zama tarihi a zuciyar Ma'u, musamman yanzu da ta samu Suraj, kasancewar shima baƙaramin ɗan soyayya bane.....
Mai gyaran jiki ta musamman momy tasa aka kawo mata tun daga nijar, sosai Ma'u take shan gyara ciki da waje, sam ba kama hannun yaro, abinka ga farar fata tuni gyara ya ɗau jiki, sai ta zama kamar wata sarauniya......

★★★
Ma'u ce zaune a falo baƙi tare da Suraj, suna hirar su ta masoya gwanin birgewa, tsura mata ido Suraj yayi ko ƙiftawa baya yi, haɗa ido sukayi da ma'u, sai ta Sunkuyar da kanta cike da jin kunya, ita wallahi in yana mata irin wannan kallon, sai ta ganshi kamar wani mayen dake shirin cinye ta, ɗagowa tayi tana mai hararar wasa sannan tace
"Wannan kallon fa.."
Murmushi ya sakan mata cike da shauƙin ƙaunar ta yace
"Kawai naga ƙin ƙara kyau ne, kin kalli kanki kuwa a madubi (mirror), wallahi ki zama wata tauraruwa acikin taurari, faɗa min meye sirrin....?"
Ya ƙare maganar yana matso da kansa, shiru Ma'u tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta, cigaba Suraj yayi da cewa
"Kodai duk a cikin gyaran jikin ne...."
Gira kawai Ma'u ta ɗaga mai alamar eh,
"Gaskiya ne! Amma momy tamin ƙoƙari Allah ya biyata, nasan duk dan farin ciki na ake wannan gyaran, Nima zansa akawo min mai gyaran jiki na musamman na maza, yazo ya gyara ni tunda ba wanda ya kula dani....."
Maganar sa ta ƙarshe ta matukar ba Ma'u dariya, hakan yasa ta dara abinta.
Shagala Suraj yayi da kallon ta, ganin yadda take dariya cikin natsuwa, sai hakan ya matuƙar birge shi, gimtse dariyar Ma'u tayi tana cewa
"Gaskiya yaya Suraj kana da abin dariya, a ina ka taɓa jin ana yiwa namiji gyaran jiki..?"
Murmushi Suraj ya saki mai tsada sannan yace
"To za'a fara a kaina! amma kin san wani abu.?"
Ma'u tace "a'a sai ka faɗa.."

"To nidai gaskiya bansan yaya Suraj ɗin nan ya kamata a canza min suna, idan ba haka ba zanyi hukunci.."
Da sauri Ma'u ta kama kunnen ta tana cewa
"Afuwan ya *ZAUJIY*."
murmushi Suraj yaƙara saki sannan yace "maimaita naji.."
A hankali Ma'u ta ƙara cewa
"Afuwan ya*zaujiy*."

"Wow!! Gaskiya sunan yamin daɗi ya *ƙalbiy*
Haka sukayi ta hirar su gwanin sha'awa, kamar bazasu rabu ba............










*AFUWAN KUN JINI SHIRU KWANA BIYU KO, WLLHI HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON BANI DA LAFIYA AMMA YANZU DA SAUƘI, KUMA NA GODE MUKU SOSAI DA IRIN ADDU'O'INKU A GARENI, DA MASU KIRA NA DA MASU TURO MIN DA SAKO DUKA INA GODIYA.*
*ALLAH UBANGIJI YABA MARARSA LAFIYA NA GIDA DA NA ASIBITI LAFIYA DA ABINDA LAFIYAR ZATA AMFANA DASHI...*










*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*
*Kar fa amanta da share dan Allah a riƙa yimin share zuwa wasu group din*



















~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~


[7/1, 8:33 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________







*59 &. 60*






____________Shirye-shiryen biki na ta kankama, inda ayau ta kama ranar kamu, yayin da ake komai cikin wadata, babban hall suka kama wanda za'a gabatar da kamun amarya.......
Ma'u amarya tayi matuƙar kyau wanda bazai misaltuba, sanye take cikin wani ash colour ɗin materials da yake da ɗan ratsin baƙi-baƙi, Yayin da aka ɗaura mata baƙin gwaggwaro, sai abin yafawa ma shima baƙi, kasancewar ta fara tas, sai kayan suka matuƙar amsar yanayin jikinta...
Ta ɓangaren ango ma, shima ya haɗu matuƙar haɗuwa saide muce masha Allah, a haka aka gudanar da kamun nan cikin kwanciyar hankali da birgewa, har aka tashi kowa ya koma gida....
Washe gari kuwa akayi walima kasancewar Ma'u tace ita ba sai anyi wata bidi'a ba a bikin ta kawai ayi walima ma ta wadatar, Suraj kuwa yaji daɗin hakan da Ma'u tace, kasancewar sa shima baya da wannan ra'ayin, ranar Lahadi kuwa dubbanni mutane suka sheda auren SURAJ IBRAHIM SENATOR DA ASMA'U BASHIR BATSARI, akan sadaki dubu ɗari biyu, Alhamdulillah biki yayi biki, saide muce Allah ya bada zaman lafiya.....

Farin cikin da inna take ciki kuwa, faɗa ma ɓata baki ne, dan wuni tayi tana sallar godiya ga Allah, da ya nuna mata wannan rana mai albarka, duk wani masoyin Ma'u ya taya ta farin ciki da wannan ranar, ita kanta Ma'u da aka ce mata an ɗaura auren, ɗaki ta shige ta kulle kanta tana kukan murna, a fili take furta "ashe haka ake ji idan aka ɗaurawa mutum aure?, da raban nima ashe zanyi aure.."
Ta ƙare maganar tana ƙara sakin kuka, ganin hakan bazai fishshe taba, yasa ta tashi ta shiga bathroom, al'wala ta ɗoro ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu, ta daɗe a zaune tana addu'o'i na neman tsari da kuma sharrin shaiɗan, sannan ta ƙare addu'ar da yi musu fatan zaman lafiya na har abada, ita da Suraj ɗin ta......
Bayan ta idar ne taji wayarta tana ringing, da sauri ta ɗaya kiran ganin momy ce, murya a dashe tayi sallama sakamakon kukan da tasha, cike da kulawa momy tace

"Asma'u ina kika shige ne! Ina ta faman neman ki..?"

"Ina cikin ɗaki.."

"Ok! Ina zuwa jira ni anan.."
Ba'a ɗau lokaci ba Momy ta turo ƙofar ɗakin, hannunta riƙe da kofi, zaunawa tayi tana dafa kafaɗar Ma'u cikin kulawa tace
"lafiya naga kamar kinyi kuka."
A hankali Ma'u tace

"Ah ah ba kuka nayi ba! Kawai kaina ne yake min ciwo.."

"Ayyah! Allah ya sawaƙe, karɓi wannan ki shanye, kafin na kawo Miki maganin ciwon kan.."
Momy ta faɗa tana miƙa mata ruwan markaɗeɗɗan zogale da madara, karba Ma'u tayi tana sha haɗe da ya mutsa fuskarta, fita Momy tayi daga ɗakin tana cewa
"ki kwanta ki ɗan huta ko! Nasan hayaniyar biki ce ta gajiyar dake.."

Bayan kwana biyu da gama sha'anin biki, Daddy yasa akai Ma'u batsari wajen su inna, kasancewar nan da sati ɗaya zasu wuce America, tunda a can Suraj yake da zama, shiyasa aka bari in sunje can sa tare...
Ɓangaren Suraj kuwa ba haka ba yaso, ya so ace an bashi matar sa ya nuna mata kulawa, in yaso kafin su tafi ya kaita batsarin tayi bankwana da ƴan uwanta, amma ba yadda ya iya dole ya bi Abinda Daddy yace....

Inna kuwa ba ƙaramin daɗi taji ba, hakan yasa Ma'u tana zuwa ta shirye gyare-gyaren su na gargajiya dan yiwa Ma'u, badan ta raina ƙoƙarin momy ba, kawai tana son ƙanƙarowa ƴarta daraja da martaba a gidan mijine..
Cikin sati ɗayan nan kuwa inna ba ƙaramin dagewa tayi ba, wajen gyaran Ma'u dan hatta ruwan wanka na musamman inna take dafawa Ma'u da lallen hausa..
Ranar da ma'u zata wuce kuwa, kuzo kuga kukan rabuwa da inna da ƙyar aka ƙanƙareta daga jikin inna, ƴan uwa da abokan arziƙi kowa yana kukan rabuwa da ma'u, haka aka wuce da ita sai gidan Daddy......
Bayan magribah kuwa! Dukkanin su suna zaune a falo, Daddy da kawu Salisu sai momy da goggo (matar kawu Salisu) sai Suraj da Ma'u dake durƙushe a ƙasa, bayan kawu Salisu ya buɗe gurin da addu'a, sannan ya ɗora da yi musu nasiha mai ratsa jiki, sosai dukkanin su jikinsu yayi sanyi, bayan ya ƙare ne Daddy ya ɗora da cewa
"To Suraj gadai Asma'u nan! Mun baka ita amana, idan ka tafi da ita to kasani cewa, bata da kowa sai kai, kaine komain ta, dan Allah ina roƙonka da ka zama mijin marainiya a gare ta, kaji tausayin ta in tana cikin damuwa, kazama kaine gatan ta a ko wani yanayi..."

"Insha Allahu Daddy! Bazan baka kunya ba.."
Suraj ya faɗa cike da ladabi.
Daddy yace "ƙarfe nawa jirgin naku zai tashi.."
"Na ƙarfe 8.00 pm ne." Suraj ya faɗa yana duba agogon hannunsa..
Daddy yace "ai lokacin ma ya kusa, bari mu tashi mu shirya koh.."
Nan suka ɗunguma gaba ki ɗaya suka wuce airport, Ma'u kuwa hannun ta na cikin na momy, har Saida aka zo shiga cikin jirgin, sannan momy ta kamo hannu Suraj ta haɗa da na ma'u tana cewa "to son ga ma'u Nan na baka ita, kar inji kar ingani, ina so ta kasance cikin farin ciki a koda yaushe.."
Rungume Ma'u tayi tana ce mata "Asma'u kema ki kasance mai ambaton Allah a ko wani hali, kar ki bar karatun Alqur'ani da nafilfili, sannan kiyi wa mijinki ladabi da biyaya, duk abinda yake so kiyi masa bakin gwargwado, inde bai wuce ƙa'idar addinin Musulunci ba, kuje Allah yayi muku albarka, insha Allahu zamu ziyarce ku nan da wata uku, har da innarki zamu taho ki daina kuka kinji.."
Kama hannun ta Suraj yayi suka fara hawa matattakalar jirgin, kasancewar an bada sanarwar shiga cikin jirgin, su Daddy basu tafi ba har Saida jirgin su Suraj ya ɗaga...
Suraj kuwa ganin irin Yadda Ma'u take zaune a cikin jirgin, duk tabi tayi tsuru tsuru alamun rashin sabo, rungumota Suraj yayi jikinsa, yana ɗan shafa bayan ta alamun rarrashi, numfashi take saukewa haɗe da nan nauyar ajiyar zuciya, bata daɗe ba bacci yayi awon gaba da ita.........











_ANA TA SHAGALIN BIKI KO INA HAIDAR 🤔_









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*












~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[7/2, 7:11 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


___________________________________________________




*THE END*

💃💃💃💃💃💃





________Misalin ƙarfe sha biyu na rana jirgin su, ya sauka a ƙasar America, mayan motoci na alfarma suka zo tarfansu dan ɗaukar Suraj, yadda turawan suke bawa Suraj girma, hakan kaɗai ya isa a gane cewa ba ƙaramin mahimmanci yake dashi ba a gurin su, saukowa yake daga matattakalar jirgin, hannun sa riƙe da na Ma'u, ita kuwa Ma'u ganin yadda turawan suka tsura musu ido, suna kallon su, duk sai tabi ta tsargu, dan saura kiris tayi tuntuɓe ta faɗi, rungumeta Suraj yayi a jikin sa, a haka suka ƙara so jikin motar da zasu shiga, buɗe mata motar yayi da kansa ta shiga, sannan shima ya shiga cikin motar, ita kuwa Ma'u sunkuyar da kanta tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta, a hankali Suraj yace
"Madam!! What happened..?"
Yayi maganar cikin raɗa, rufe fuskarta Ma'u tayi da tafukan hannayen ta, sannan tace
"Ba komai fa.."
Murmushi yayi mai ƙayatarwa, haɗe da matso da fuskarsa zuwa gare ta, cikin wani salo yake goga karan hancinsa akan nata, murya a sanyaye Suraj yace
"Wannan kunyar taki! Ita kaɗai ce zata hanani rawar gaban hantsi, pls dan Allah a rage ta.."

Ma'u kuwa da take jin kamar ƙasa ta tsage, kodan ta shige ta ɓoye wa rashin kunyar Suraj, tun jiya ta lura da take-taken sa a cikin jirgi, sai wani abu yake gwanin ban kunya🙈, gashi a fuska kamar bazai aikata ba, ƙwace fuskarta Ma'u tayi tana mai da numfashi, ganin yana ƙoƙarin kissen ɗinta, hararar wasa ta mai tana nuna mai direba da yake tuƙinsa kamar ma baisan da zaman su ba, noƙe kafaɗa Suraj yayi alamun naƙi wayon, kallon ta yake kamar wani tsohon maye, ita kanta Ma'u idan taga Suraj yana mata irin wannan kallon, gabanta har faɗuwa yake, amma inda take jin daɗin abun ya iya takunsa sosai, a haka har direba ya ƙaraso gidan suraj wanda zan iya wa lakabi da aljannar duniya, haƙiƙa gidan ya haɗu iya haɗawa, saide muce Masha Allah...

Fitowa Suraj yayi haɗe da zagayawa ya buɗewa Ma'u ƙofa, tana fitowa ya cicciɓeta yayi sama da ita yana cewa
"Amarya tazo gidanta.."
Be direta ba a ko ina sai da yazo bakin ƙofa ya ajje ta, yana cewa
"To bissimillah!! Ki shiga gidan ki da ƙafarki ta dama, sannan kiyi addu'a da bakinki mai albarka.."
Shiga Ma'u tayi da ƙafar daman tana karanta wannan addu'ar a zuciyar ta...👇
رب انزلن منزلً مبارك وانت خيرٌ
منزلي. sau bakwai 7
Bin bayan ta suraj yayi hade da kamo hannun ta, wani bedroom ya shiga da ita, da dukan alamun dai nasa ne, zaunar da ita yayi a kan gadon sannan ya kalleta cike da kulawa yace
"Me kika fi buƙata a halin yanzu! Wanka ko abinci, ko hutawa."

"Uhmm! Gaskiya nafi bukatar wanka da hutawa.."

"Ok! Yayi kyau.."
Ya faɗa yana tashi, rage kayan jikinsa ya fara yi, iya boxe kawai ya bari sannan ya kamo hannun ma'u yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta, noƙewa ma'u tayi alamar bata so, ƙyele ta suraj yayi ta cire da kanta sannan ya janyo ta yana cewa "taho to muje muyi wankan ko.."
Cikin shagwaɓa ma'u tace "ah ah kaje kayi! In ka fito sai na shiga nayi nima.."
Kallon ta yayi da kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, a sanyaye ya shige cikin bathroom ɗin, ganin kamar baiji

Please Login or Register in order to submit comment