Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daɗin haka ba yasa ta bishi cikin bathroom ɗin tana sanɗa kamar ɓarauniya.....
Saida suka gabatar da sallolin su tukunnan suka kwanta, basu tashi ba sai wajen gab da magribah, a gurguje suka yi wanka suka shirya, wata baturiya ce ta shigo dan yiwa ma'u make up, kasancewar abokanansa na nan sun haɗa musu wani shagali, sosai ma'u tayi kyau cikin farar doguwar riga ta amaren turawa, itama sai ta fito sak a baturiyar ta, haka ma ɓangaren suraj shima sak ya fito a matsayin Bature ango, shagalin su suka sha cikin kwanciyar hankali da birgewa, ba'a tashi ba har sai waje sha ɗaya na dare, sannan amarya da ango suka sami nutsuwa, wanka ma'u tayi haɗe da ɗoro al'wala dan yin sallar isha'i, shima suraj wankan yayi haɗe da ɗoro al'walar, bayan sun idar da sallar ne, suraj yayi wa ma'u umarnin da ta tashi suyi sallar nafila, bayan sun idar ne, ya gabatar da addu'ar samun zaman lafiya da zuri'a ɗayibba.
Daga ƙarshe ya dafa kan ma'u haɗe da karanto addu'ar da annabin mu ya koyar da duk wani sabon ango....
Fita suraj yayi daga ɗakin, jim kadan kuma ya shigo hannun sa riƙe da ƙaramin filet, ajjewa yayi sannan ya buɗe ƙaramin frij ɗin dake ɗakin, yoghrt da lemun sha,ya ɗauka haɗe da kofina, fidding ɗin ma'u yake cike da soyayya, har saida ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta haka, tashi ma'u tayi taje tayi brush, sannan tazo ta hau kan bed ta kudundune..
Suraj kuwa bai tashi ba har saida ya cika cikin sa nak, sannan yaje yayi brush, bayan ya fito bai hau gadon ba saida ya feshe jikin sa da turaruka masu kamshi, sannan ya hau kan bed ɗin, rungumota yayi jikin sa, setin kunnen ta ya mata magana cikin raɗa, yace

"Zo muyi wasan amarya da ango.."

*NI KUWA GANIN YA FARA TAKURA MATA YASA NA HITA WAJE IN JIRASU ACAN*👩🏻‍🦯👩🏻‍🦯


Suraj bai bar ma'u ba, sai wajen ƙarfe huɗu na asuba, wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, shi kuwa suraj rungume ta yayi tsam kamar za'a ƙwace masa ita, wani tsarkakaken sonta da ƙaunarta yake ji suna ratsa duk wasu gaɓoɓin jikin sa, ada ji yake yana sonta da tausayinta, amma a yanzu jinsa yake ita ce mahaɗin rayuwar sa, idan babu ita bazai taɓa iya gudanar da rayuwar sa ba....
Yana cikin wannan tunanin shima wani daddaɗan bacci yayi awon gaba da shi..
Misalin ƙarfe bakwai na safe suraj ya buɗe idonsa, ganin yadda lokaci ya ƙare yasa ya tashi da hanzari ya shige bathroom, wanka yayi haɗe da ɗoro al'wala, sallar asuba yayi sannan ya dawo kan bed ɗin, shafa fuskar ma'u yake a hankali yana cewa
*"MY LIFE*."
Buɗe idonta tayi a hankali, suna haɗa ido da suraj taja bargo da sauri tana rufe fuskanta, murmushi suraj yayi yana cewa "ai aikin gama ya riga da ya gama yarinya.."
Ya faɗa yana sunkutar ta, haɗa ruwan ɗumi yayi ya sata aciki, wankan tsarki ya sata tayi sannan ta ɗora alwala suka fito daga cikin bathroom ɗin....
Ma'u tana idar da salla tazo gaban suraj ta tsuguna, tace
"Mijina ka tashi lafiya..?"
Cike da jin daɗi suraj yace
"Lafiya kalau matata! Fatan kema haka..?"
Gyaɗa kai Ma'u tayi cike da jin kunya..
Janyo ta suraj yayi jikin sa yana shinshinar kamshin jikinta, cikin wata kalar murya yace
"Husnah ina so ki faɗa min! Duk duniyar nan me kike so Inyi miki, wallahi koda zan ƙarar da duk wani abu da na mallaka ne, ni kuma sai na miki shi.."
Murmushi ma'u tayi tana kallon sa, cike da tsantsan so tace
"Kai nake buƙata! Ina so inyi rayuwata tare da kai har mutuwa ta.."

"Kin same ni kuwa! Soyayyar ki da ita aka halicce ni, babu abinda zaisa inji na gajiya da zama dake bare har na rabu dake.."
Rungume juna suka yi cike da tsantsan soyayya, kowa yana faɗawa ɗan uwansa yadda yake sonsa...

Wajen aikin su suraj kuwa hutun sati biyu suka ƙara mai, sannan ya koma bakin aikinsa, sosai shaƙuwa da soyayya ta ƙara ninkuwa a tsakanin su, tsantsan kulawa suke nuna wa juna, kowa bai son ɓacin ran ɗan uwansa, soyayyar su suke sha mai cike da tsabta...
Bayan wata huɗu su daddy suka zo har da inna da auta zahrah, harma da kawu Salisu, murna gurin ma'u kuwa ba'a cewa komai, satin su ɗaya suraj ya biya musu umarah, suka wuce Saudi Arabia, suje su sauke farali..
Ita kuwa ma'u da take laulayi yanzu, yace idan ta haihu saje aikin hajji, ana cewa ko harshe da haƙori ana samun saɓani, to su wannan ma'auratan ba haka ba yake a gurin su, dan zallar soyayyar su suke sha mai tsabta.....
★★★
Haidar kuwa tunda ibn muzaffar yasa aka tafi dashi, ake gana mai azaba, amma bakinsa sunan ma'u kawai yake kira, ganin haka da ibn muzaffar yayi yasa aka linka azabtarwar da ake mai, amma duk a banza dan kullum cikin begen masoyiyar sa ma'u yake, babu wanda yake tausaya mai sai Iliyas, ba irin roƙon da Iliyas bai mai ba, akan ya furta ya rabu da ma'u, amma fa fur yaƙi amincewa, duk wata wahala da ake bashi shi ake bawa, amma Iliyas shike jin raɗaɗin azabar, dan Iliyas aboki na gari ne...
Tsawon shekara ɗaya ana abi ɗaya, amma kamar ana ƙarara Haidar son ma'u a zuciyarsa...

Iliyas ne durƙushe a gaban ibn muzaffar, cike da ladabi yace
"Ya Shaikh! Alfarma nazo nema, Allah yasa hakan ba zaisa inyi kuskure ba.."

"Ina jinka mana Iliyas! Faɗi abinda kake son fada muku in zai yiwu.."

"Allah ya huci zuciyar ka! Allah ya gafarceka, dama Alfarma nake nemawa Haidar, akan a rangwanta mai, a duba lamarin sa, yana cikin tsananin ciwon so, a halin da yake ciki a yanzu, ina ga azaba baza ta sauya masa ra'ayi ba, dan kullum burinsa ya fita daga wurin nan ya koma gurin bil'adamar nan, nidai alfarma da nake nema, shin mai zai hana ba za'a haɗa dayi masa wa'azi ba, da ƴan nasihohi, sannan a zaburar da shi dokokin Allah, ina ga kamar hakan zaiyi tasiri.."

Girgiza kai ibn muzaffar yayi, cike da gamsuwa da abinda Iliyas ɗin ya faɗa.

"Gaskiya ne Iliyas! Tabbas da ace azaba zata yi tasiri akan Haidar, da izuwa yanzu ya gundura da azabtarwar da ake mai, Ni kaina ina matuƙar tausaya mai, saboda na san illar soyayya, kuma INSHA ALLAHU zamu gwada yadda kace ɗin.."

Kamar yadda Iliyas ya nemi alfarma, hakan ce ta faru, kuma an dace sosai dan hakan yayi matuƙar tasiri a zuciyar Haidar, sosai jikin sa yayi sanyi, dukan wasu makaman yaƙin sa saida ya zubar da su, amma soyayyar ma'u tana nan a cikin zuciyar sa, kullum ƙara sabunta take.....

★★★

Ma'u ce ta fito daga ɗakin suraj sanye da riga da wando, na mutanen ƙasar fakistan, jidda ce zaune a falo, tana yiwa wata ƙaramar yarinya da bazata wuce shekara ɗaya ba wasa, ƙarasowa tayi wajen su da murmushi tace
"to jidda wasa kike keda ƙanwar taki..?"
Ta faɗa tana karɓar ta.
Rawa ta fara yiwa yarinya haɗe da waƙa,
"Ah ah momyna yunwa take ji.."
Ta faɗa haɗe da fiddo nono tana fidding ɗin yarinya, da take tsantsan kama da ma'u, kamar an tsaga kara..
Bayan ta gama fidding ɗin nata ne, ta miƙe tsaye haɗe da kamo hannun jidda, tana cewa
"ohhyah muje gurin daddy.."

Zaune suraj yake kan dadduma yana rera karatun Alqur'ani mai girma, ganin sun shigo yasa ya rufe Alqur'anin yana murmushi, da gudu jidda ta faɗa jikin sa tana ihun murna, yarinya ma dake hannun sai zillo take alamun tana son zuwa gurin daddynta miƙa masa ita ma'u tayi, sannan ta koma gefen sa haɗe da ɗora kanta jikin kafaɗarsa, marairaice fuskanta ma'u tayi cike da shagwaɓa, cikin kulawa suraj yace
"yadai Madam..?"
Cikin shagwaɓa ma'u tace muje gidan su Momy, daga nan mu wuce shopping.."

Amsawa yayi da "to madam! Yadda kika ce haka za'a yi.."
Cikin murna ma'u ta tashi harda ɗan tsallanta, kamar wata ƙaramar yarinya, kissing ɗin suraj tayi a goshi😘, jidda ita ma cikin shagwaɓa tace momy nima, mucch😘 ma'u tayi mata a goshi, kairat wadda taci sunan inna, itama tsalle ta fara alamun ita ma ayi mata, dukkanin su dariya suka fashe dashi sannan ma'u takai mata mucch 😘 a goshi, fita ma'u tayi daga ɗakin tana cewa "bari naje na shirya...."

A gurguje ta shiga wanka ta fito ɗaure da towel a jikin ta, tsane ruwan dake jikin gashinta take da wani ƙaramin towel ɗin dake hannun ta, kwalliya ta fara tsantsarawa cikin nutsuwa, wajen minti 30 tana zaune gaban mirror sannan ta kammala kwalliyar, miƙewar da zata yi kenan, ta hangi kamar akwai wani a bayan ta, da sauri ma'u ta juya haɗe da zaro idonta, ganin Haidar ne yasa jikinta ya fara karkarwa, batasan lokacin da ta saki towel ɗin dake ɗaure a jikin ta, gaba ki ɗaya a tsorace take da ganin Haidar, takowa yayi cike da ƙasaita yana sakin mata ƙayataccen murmushin sa, ɗaukar towel ɗin da ta yarda a ƙasa yayi, haɗe da kauda kansa gefe yana miƙa mata, karɓa ma'u tayi amma ta kasa ɗorawa, murya cikin sarsarfa Haidar yace "ki ɗaura mana.."
Ɗaurawa ma'u tayi haɗe da tsugunnawa a gaban Haidar ta fara magana cikin kuka..
"Ina zaune da mijina da ƴata da na haifa cikin kwanciyar hankali, dan girman Allah Haidar kayi nesa da rayuwa ta, kabarni in huta haka, idan ban manta ba ka taɓa cewa Zaka iya sadaukar da komai akan soyayyar da kake mini, ina mai roƙon ka da Allah, dan girman soyayyar da kake iƙirarin kana min ka barni, inyi rayuwar aure da mijina, saboda ina sonshi.."
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka..
Ɗagota Haidar yayi haɗe da rungume ta, yana bubbuga bayan cikin lallashi yace
*"ASMA'UL HUSNAH* tabbas nayi alƙawarin sadaukar da komai dan farin ciki, kuma Insha Allahu bazan ƙara cutar da rayuwar ki ba, a tsakanina dake daga yau saide taimako, saboda sonki acikin jinina yake, kuma zan cigaba da sonki har duniya ta naɗe...........

*TAMMAT BIL HAMMDULILLAH*.....



ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN, KURAKUREN DAKE CIKI INA ROƘON ALLAH YA YAFE MIN, ABINDA NA AIKATA NA ƘARUWA ALLAH YASA A AMFANA DA SHI, ALLAH UBANGIJI YA GAFARTA MANA ZUNUBANMU ALLAH YA SAKAWA IYAYEN MU DA ALKAIRI MAFIFICI....





RUBUTU DA LABARI MALLAKIN
*UMMUSSALAMA S YAHYA*
(MATAR KHAMIS)✍️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment