Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

goyi bayansa akan auren jinsin bil'adama, shima a zuciyarsa basan hakan yake ba, dan aikata hakan ya saɓawa al'adarsu ta al'janu, musamman da suka kasance musulmai...




*To fa reader's ya zata kasance, tsakanin Ma'u da Haidar🤔*


*Shin ya Haidar zaiyi mu'amala ta aure da Ma'u🤔*


*kuma anya zai barta tayi aure da bil'adama irinta🤔*


*duka ku biyoni cikin wannan labarin domin warware rikicin dake ci*




*more comments*
*more typing*



*pls share*




~MRS KHAMIS CE🥰💃~
[5/20, 3:37 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________



*page 10 & 11*



__________Ransa fes yake gudanar da al'amuransa, musamman yanzu da yake jin ya samu nasarar mallakar Ma'u, yanzu duk wani shirinsa shine da yake so ya cimma, shine yaga ya hana ko wani ɗa namiji gaɓar inda Ma'u take..
Haidar bai bar Ma'u haka ba, sai da ya tabbatar da Yasa mata tsoron maza a zuciyar ta, dan duk wata sabga da ake mu duk akwai maza a cikinta, to baza kaganta a gurin ba..
Rayuwa tana ta tafiya Ma'u kullum manema aurenta suna ta zuwa, saide in wani yazo sau ɗaya ba llale ya ƙara zuwa ba, ana cikin haka akayi auren ƙannan ta biyu mata, wanda suke bi mata, kasancewar a dangin su suna auren wuri, dan duk inda yarinya ta kai shekaru sha tara to ta isah aure, saide kawai in bata samu mijin da zai aure tan bane...
A yanzu Ma'u tana da shekaru ashirin da uku, kyawun ta da dirinta sun ƙara fitowa, ba shakka yanzu Ma'u take cikakkiyar budurwa, dan ba wani ɗa namiji da zai kalli Ma'u yace bata burge shi ba, dan Allah ya mata kyawu da suffar da ko wani namiji yake da burin yaga ya mallake ta..
Saide kashh! muguntar Haidar tasa ya sanya wa Ma'u kwarjinin da ba ko wani namiji ne yake iya tunkarar Ma'u, yace yana sonta ba, sai wanda ya isah yake jin shi wani ne, a fagen mulki ko kuma a kasuwanci, hakan yasa ƙananun samarin dake da burin zuwa gurin ta, su sha jinin jikin su, suma wanda suke zuwa sai Ma'u tace bata son su, ko kuma de akasin haka, wani lokacin har sai maganar aure ta shiga, cikin ikon Allah saide a rasa ya akayi auren ya warware, Ma'u ita da iyayen ta basu san meye matsalar ba kawai suna ɗauka, lokacin auren ne baiyi ba....



★★★
Tafiya take kamar tana tausayin ƙasa, sai ka rantse daga gidan wani sarautar ta fito, lalle ba shakka Ma'u akwai iya tafiyar ƙasaita, kanta sunkuye yake tana tafiyar ta cikin natsuwa da kamala..
Bata ankara ba taji tayi karo da mutum, ɗagowa tayi da sauri dan ta bashi haƙuri, amma mai maganar da take niyar mai ce, ta maƙe mata a maƙogwaro, sakamakon ganin kyawun mutumin, da kwarjinin da ya cika mata ido, in-ina ta fara wajen yi masa magana, amma ta kasa furta komai, shi kuwa mutumin duƙawa yayi ya ɗauko mata jakarta da ta yadda, saboda yadda zuciyarta ta tsorata da ganin mutumin, miƙa mata jakar yake yana Binta da wani sihirtaccen kallo..
Gaba ki ɗaya Ma'u ta shiga wani yanayi, mayataccen kallon da yake binta dashi, yasa taji tsikar jikinta tana tashi, hakan yasa ta juya baya da sauri, da niyar barin gurin, dan ita har ga Allah zuciyarta bata kwanta mata, da ganin bawan Allah nan da tayi ba....
Bata ƙara firgita da lamarin mutumin ba, sai da taji ya damƙi hannunta, bin hannun nasa tayi da kallo, har izuwa fuskarsa, hannun nata yake murzawa, yayin da idanunsa suka kasance a kumshe, hakan yaba Ma'u damar ƙare masa kallo, ranta take yaba irin kyawun da yake dashi, dan tana jin bata taɓa ganin wani mutum da yake da kyau irin nasa ba, sai da ta kalle shi up and down, sannan tace a ranta, "Wannan kyawu naka ai yafi kama da na al'janu." Buɗe idanun sa yayi da sauri akan fuskanta,
Kamar yasan mai take cewa a zuciyar ta.
Ita kuwa Ma'u da ya riƙe mata hannu na ɗan wani lokaci, hakan yasa taji natsuwa yazo mata, kallon shi tayi cike da tsiwa tace, "malam sakan min hannu, ka waniriƙen, sai kace ka Sanni."
ta ƙare maganar tana hararsa , shi kuwa murmushi kawai yake, sannan ya sakan mata hannun yace "muje na rakaki inda zaki ɗin"
Ƙasa mai musu tayi, hakan yasa tayi gaba, shi kuma yana Binta a baya, saidai tazo inda zata, sannan ta tsaya tace mai "dama nan zanzo."
" Ok" kawai yace mata yana shirin juyawa, tana so ta tambaye shi sunan shi amma ta kasa, sakamakon ko shi shima bai tambaye ta sunan ta ba.
Ji tayi yace "shine ko ki tambayi sunana" tsorata tayi dan har ga Allah gani take kamar yasan mai take cewa a zuciyar ta..
Tana cikin wannan tunanin taji yace mata "suna na *Haidar* fatan zan iya dawowa na kaiki gida....✍️







*WLLHI IN BA'A MIN COMMENT LITTAFIN NAN YA KUSA DAWOWA NA KUƊI, ,😳*






*More comment*

*More typing kullum😄*

*Pls share*




~MRS KHAMIS CE~🥰💃
[5/23, 8:09 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*Page 12 & 13*



__________"Eh." kawai tace tana shirin shiga cikin gida, ji tayi yace
" *Asma'ul husnah* Haƙiƙa ina sonki," da sauri ta juyo baya fuskarta shanye da mamaki, ita ba wai cewa da yayi yana sonta ne ba, ya bata mamaki illah da taji ya faɗi, full name ɗin ta..
Saida ta ƙura masa ido na ɗan wani lokaci, sannan tace "amma a ina kasan suna na! Na ga tunda muka taho baka tambayi sunana ba, Gashi kuma naji ka faɗi cikakken sunan."
Wani gajeren murmushi yayi, yace "baiwa ta kenan, duk lokacin da na haɗu da mutum, to kai tsaye zan iya ambaton sunan shi."
"Uhmm sai kace wani al'jani, baka san mutum ba, amma har zaka iya sanin sunan shi.". Ma'u ta faɗa cikin sigar tsokana...

Wani dogon numfashi yaja tukunan yace "oh kina ganin al'jani ne kaɗe yake da wannan baiwar.?"
"Eh mana" Ma'u tace ataƙaice,
"Ok ko Nima al'janin ne ban sani ba."
"Ah ah rabani, ni WLLHI ba haka nake nufi ba, kaga tafiya ta, Allah da aka fara maganar aljanu, har naji tsikar jikina na tashi..".
Ma'u ta faɗa haɗe da shigewa cikin gidan...

***


Da yamma kuwa Haidar kamar yadda ya ce, sai Gashi yazo, sa yaro yayi yakira masa Ma'u, koda Ma'u ta fito ganin shi ya matuƙar bata mamaki sosai, dan batayi tsammanin dawowarsa ba, tayi tunanin wasa kawai yake mata....
Da murmushi a fuskarsa ya tare ta, yace "muje to Madam."
"Uhmm! Madam kuma." Ta faɗa tana ware idanun ta, Hakan da tayi sai ta ƙara birgesa, dan shi komai yaga tayi burgeshi take...
Kusa da wata hamshaƙiyar baƙar mota, ya tsaya, saida ya mata key, sannan yace da Ma'u "bissimillah! gimbiyata"
Koda Ma'u ta shiga cikin motar yanayin sanyi AC da kuma ƙamshin dake Cikin motar, sai ya saukar mata da wani yanayi, lumshe idonta kawai tayi tana shaƙar ƙamshin dake gurin, jin shiru bai tada motar ba yasa ta buɗe idonta, kamasa da tayi yana kallon ta yasa tace "lfy kuwa." Girgiza mata kai kawai yayi alamun lfy klau, sai da yaja ajiyar zuciya tukunan yace "kinsan wani abu?."
"Ah ah". kawai tace ɗorawa yayi da cewa "kin kwa san Yadda kike da kyau, dan ina ganin ko a al'janu babu mai irin kyanki."
Dariya Ma'u ta saki sosai sannan tace "tofah kaide kam akwai ka da abun dariya wllhi."
Ta faɗa tana ƙara sautin dariyar, tada motar yayi sannan yace
"Ko! Ai haka nake so naga kina cikin nishaɗi, shiyasa nake saki safiyar." Tunda suka tafi kuwa Ma'u shiru tayi, aranta tana mamakin yadda aka yi ta sake dashi, kamar wani ta sanshi.
Bai gama bata mamaki ba Saida taga yayi paking ɗin motarsa a ƙofar gidan su, cike da al'ajabi Ma'u tace "wai shin dama ka San gidan mu ne?." Yace
"Eh mana! ".
Ma'u tace "shiyasa naji ka ambaci suna na ɗazu." Saida yayi murmushi sannan yace "ai na sanki tun kina ƴar ƙaramar ki. " Kallon ban yarda ba Ma'u kawai tayi mai, Sannan tace mai bari ta shige gida, sallama suka yi ta shige gida shi kuma yayi tafiyar sa...
Koda Ma'u ta shiga cikin gida, ba abinda take tinani illah mutumin da suka haɗu dashi, komai nasa gwanin birgewa, Gashi da abin al'ajabi ga salo, a taƙaice dai Ma'u ta rufta soyayyar wanda bata san ko shi waye ba...

Shi kuwa Haidar murucin kan dutse ne, bai fito ba Saida ya shirya, cikin ƙanƙanin lokaci yasa Ma'u ta kamu da soyayyar sa mai tsanani, ta yadda duk ranar da baizo ya ganta ta ganshi ba to sai tayi rashin lafiya...
Kamar yau kwanan sa uku bata ganshi ba duk ta wani firgice, tun inna na kulata har ta ƙyaleta gaba ɗaya.
Washe gari kuwa Ma'u tana zaune, tana tsefe kanta wani yaro ya shigo, yace ana sallama da ita, da sauri tasa hijab ɗin ta, dan tasan babu wani saurayin da yake zuwa gurin ta, inba Haidar ba.
Tana fita shi ɗin kuwa ta gani, murmushi kwance a fuskar sa, dan shi murmushi kamar yazama ɗabi'ar sa, dan ko da yaushe cikin fara'a yake.
Ƙara sawa tayi cikin motar fuskanta fal murna yau taga masoyinta, bayan sun gaisane take mai ƙorafin lfy taga ya daina zuwa, "Wallahi lafiya klau nurul aini," ajiyar zuciya Ma'u ta yi harda dafe saitin zuciyar, sannan tace "har hankali na ya kwanta, wllhi dana ga baka zoba, ji nake kamar zan mutu dan Allah karka rabu dani, wllhi ina sonka sosai idan ka rabu sani mutuwa zanyi.."
Ma'u ta ƙare wannan maganar har cikin ranta, kamo hannunta Haidar yayi sannan yace "a halitta ta, a ɗabi'a ta, da kuma soyayya ta agreki, baza su taɓa canjawa, na soki tunda daɗewa, kuma babu abinda zai sa na rabu da ke, ina sonki kamar bugun numfashi na, a kanki zan iya aikata komai saboda irin ƙaunar da nake miki, kuma keɗin mallakina ce, babu wanda ya isa ya mallake ki face ni, na miki alƙawarin daga yau bazan ƙara yin wata tafiya ba, da zata nisan tani daga gare ki ba, zan kasance tare dake a koda yaushe, kuma a duk inda kike.....✍️


_A GSKY INA JIN DADIN YADDA KUKE NUNAWA LBRN NAN SOYAYYA, SHIYASA NAKE YIN KU OVER ALLAH YA BARMU TARE_ *LOVE YOU ALL*🥰😘






*More comment*
*More typing*
*Pls share*








~MRS KHAMIS CE~🥰💃


👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*14 & 15*



___________Haka ya cigaba da gaya mata kalamai masu daɗi da kuma ratsa zuciyar mai sauraro, duka a cikin kalaman sa babu wanda suka yi kama da yaudara, ko wacce kalma tana fitowa ne daga zuciyar sa..
Ita kuwa Ma'u ta yarda Haidar masoyinta ne na gaskiya, kuma bata da tamkar shi, shiyasa take masifar sonshi.
Abinda Ma'u bata sani ba, a gidan su babu wanda yasan da batun Haidar, asali ma ita kaɗe ke ganin sa, domin duk soyayyar da yake nuna mata yana amfani da tunanin tane..
Yadda yake yi kuwa shine idan yaso ya ganta, zai yi amfani da ƙarfin su irin na al'janu, ya juyar mata da hankalin ta ta yadda komai zata gani kamar komai normal ne....
A zahirin gaskiya kuwa ko innah idan tazo gurin Ma'u, saide ta tarar tana bacci abin ta, domin Haidar yana da wayo sosai, bai bar wata kafa da za'a gane cewa Ma'u al'jani ya aure ta...
Zaune suke a tsakar gida misalin wajen bayan isha'i, hira suke jefi-jefi kuma suna shan iska da ke kaɗawa a gurin, kasancewar ana zafi sosai a garin sosai..
Ma'u dake kwance gefe kan shimfiɗar ta, Wayar dake hannun ta ne tayi ƙara, kai duban ta tayi ga inna sai taga ta fara gyangyaɗi kaɗan kaɗan, tashi tayi da sauri haɗe da naɗe shimfiɗar ta ta shige ɗaki..
Faɗawa tayi kan katifar haɗe da ɗaga kiran, cikin zazzaƙar Muryar sa yace "Amincin Allah da yardar sa su tabbata a gare ki ya hasken idaniyata."
" Uhmm tare da kai kaima". Ma'u ta faɗa cike da shauƙi, yace "Ameen! Masoyiyata, kinsan wani abu.?" Ma'u tace "ah ah" yace "nayi kewarki wllhi."
Murmushi Ma'u tayi mai sauti, sannan tace "nima haka nayi kewar ka sosai." Haka sukayi ta musayar kalamai a tsakanin su har saida Ma'u, ta fara yin shiru alamun bacci take ji, sannan ya rabu da ita, sukayi sallama...

★★★

Zaune take kan ƙayataccen gadon ta na alfarma, wanda babu wacce ta isa ta haushi sai wadda take matsayin ta na amarya, shigowa yayi bakinsa ɗauke da sallama, murmushin dake kan fuskarsa ne ya kasa ɓoyuwa, takowa yayi izuwa gare ta cike da ƙasaita, yayin da annurin fuskarsa yake ƙaruwa...
Lulluɓin dake kanta ya yaye a hankali, cikin zumuɗi yake ƙare mata kallo, inda zuciyar sa ke daɗa ta'azzara da begen wannan kyakkyawar halittar dake gaban sa..
Ya tsunsa guda biyu yasa ya ɗago da fuskanta, kyakkyawar fuskanta yake ƙarewa kallo, ji yake kamar ya haɗiyeta dan tsananin son da yake mata, hannunta ya kamo cikin nasa murzawa yake a hankali, cikin kasalaliyar Muryar sa yace "masoyiyata! Gaki a matsayin matata kuma mallakina, wata kulawa zaki bani?, fatan dai baza amin rowa ba." Ya faɗi haka yana ɗaga mata gida, ita kuwa yanayi yadda yayi maganar sai ya bata kunya hakan yasa tasa hannunta ta rufe fuskarta, cikin tsantsar so da begen ta ya matsa kusa da ita, hannun da ta rufe fuskarta dashi ya cire, haɗe fuskarta da tashi yayi, ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, yayin da yake goga hancinsa akan nata, muryar sa can ciki yace "Nidai gsky bansan wannan kunyar a rage ta, dan ita ke cuta ta pls a rageta," ya ƙare maganar yana shinshinarta..
Ita kuwa da duk tabi ta firgice da irin salon da yake mata, dama shi ya daɗi akan network...
Sosai yake sarrafa ta iya son ransa tun ya nabinta a hankali har ya fara da sauri sauri, baibar taba har saida ya cimma burin sa, bayan komai ya lafa ne sai ya rungume ta a jikin sa cikin kunnen ta yake raɗa mata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya..
Ma'u dake kwance take wannan mafarkin, yanayin ya mata daɗi sosai, hakan yasa tayi wata doguwar miƙa, pillon dake kusa da ita ta rungume tsam, kamar ta samu Haidar ɗin ne, wanda a zahirin gsky shi ɗin ne kuwa, Haidar kuwa da yaji ta rungume shi, wani ƙayataccen murmushi ya saki, yana jin bazai taɓa iya rabuwa da ita ba, musamman yanzu da ya sadu da ita, sai yake jin koda mutanen duniya zasu taru dan su raba shi da ita, to bazai rabu da ita ba.
Tashi yayi zaune haɗe da tallabe fuskarsa kallon kyakkyawar suffarta yake, ciki da bai yana yiwa kansa fatan kasancewa da ita na har abada.........✍️





*_Tofah Reade's Nima fa na fara tsorata da lamarin Haidar fa😳_*






*More comment*
*More typing*
*Pls share*








~MRS KHAMIS CE🥰💃~


[5/26, 3:11 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*16 & 17*




________washe gari da safe Ma'u da ta tashi Jikin ta duk ba daɗi, asalima ji take kamar bata da lfy, tun asuba da ta fito tayi salla bata ƙara fitowa ba, kwance take a ɗaki amma zuciyar ta maƙale take da tunanin Haidar, tuno mafarkin da tayi jiya ne hakan yasa ta cusa kanta tsakanin filallika, wani kalar yanayi take ji a tattare da ita, hakanan taji son Haidar ya ƙara lunkuwa a zuciyar ta..
Wayar ta dake ƙasan fillonta ta janyo, dubawa tayi taga ko Haidar ya kirata, ganin bai kirata ba hakan yasa ta danna mai kira, amma sai kiran yaƙi tafiya, ajje wayar tayi a gefe tana ɗan sakin ƙaramin tsoki.....
Bata daɗe da ajiyewa ba, wayar tayi ƙara jiki na tsuma ta ɗauko wayar ganin Haidar yasa da hanzari ta ɗaga kiran...
Cikin kukan shagwaɓa tace
"Uhmm! Uhmm,. tun ɗazu nake so naji muryarka, amma kiran yaƙi tafiya saura kiris na fara kuka."
Haidar cikin ruɗewa yace "yi haƙuri masoyiyata, wllhi inda nake ne ba network shiyasa, amma ai ina zaune naji zuciya ta ta gayamin kina kewa ta, shiyasa ban yi ƙasa a gwuiwa ba na kira ki,
yanzu faɗa min me kike so?, ba tare da ɓata lokaci ba yanzu na miki."
Cikin ƙasa da murya tace "kai nake so." Yace "to ai kin daɗe da samuna Nurul aini, ko kina so ki ganni ne."?
"Eh mana."
"To yanzu zaki ganni ko minti ɗaya ba za'a ƙara ba".
Cikin kiɗima Ma'u tace "taya kenan."
"Hmm kede rufe idonki zaki gani."
Rufe idon Ma'u tayi, cikin ƴan sakanni taji kamar an ɗauke ta kan iska ana tafiya da ita, bayan ƴan wasu sakannin taji komai ya lafa, Muryar Haidar ta tsinkaya yana cewa
"to buɗe idonki," a hankali take buɗe idon har ta kammala buɗewa, tsintar kanta tayi a kwance kan wani makeken gado na alfarma, yayin da Haidar yake gefen ta yana aika mata da wani irin saƙonnin kallo iri iri, zuciyar ta na lugude ta tashi zaune cikin tsoro da firgicin me ya kawo ta nan, juyowa tayi da niyar ta tambaye shi ya akayi hakan...
Shi kuwa Haidar ganin ta tsorata da yanayin, sai ya janyo ta izuwa jikinsa rugumeta yayi tsam, kamar za'a ƙwace masa ita, ita kuwa Ma'u kicikicin ƙwatar kanta take dan har yanzu tana cikin ruɗu...
Ganin ta kasa bashi haɗin kai, hakan yasa yace "kalleni." Kallon sa take irin kallon ƙurulla ɗin nan, yayin da Haidar yake kallon ta wani nau'in abubuwa suna fitowa daga cikin idanunsa suna shiga nata, lokaci ɗaya Ma'u jikinta yayi sanyi jinta ta riƙa yi kamar ba ita ba, wani bacci ne mai nauyi yayi awon gaba da ita, shi kuwa Haidar ganin Ma'u tayi bacci, sai ya saki wani shu'umin murmushi, haɗe da gyara mata kwanciya a jikinsa..

Bai barta haka ba har saida yabiya buƙatarsa, ita kuwa Ma'u bata san abinda ke wakana ba tana can duniyar baccin ta, mafarki ta kumayi irin na jiya wai gashi Haidar yayi amfani da ita....

★★★

Da misalin ƙarfe sha biyu inna ce zaune a tsakar gida tana tsintar shinkafa, sai faman sababi take tana cewa "haba dan Allah mutum shi sai yayi ta bacci ko gajiya ba yayi, duk baccin da kika yi da dare bai isheki ba, har sai kinyi na safe, na safe ma ba ayi kaɗan a tashi ba a'a har sai anyi na wuccin misali, gashi yanzu rana tayi..."
Ganin hakan bai mata ba yasa ta tashi, ta shiga ɗakin da Ma'u take kwance, kiran sunan ta inna take amma shiru Ma'u bata tashi ba, kamar wata matatta..
A fusace inna ta ɗaka mata duka, da hanzari Ma'u ta tashi tana cewa "haba innarmu!, Kede kam baki so kiga mutum yana hutawa, yanzu fa na ɗan kwanta."
Inna kuwa dake faman aika mata da harara tace "au yanzu ma kika kwanta ko, to ai sai ki koma ki cigaba da yin baccin, tunda kin zama malalaciya, wllhi duk namijin da ya aure ki idan baya da kuɗi ko wllhi ƙazama zaki koma.." inna ta faɗa tana shirin barin ɗakin, tashi Ma'u tayi da sauri dafo inna tayi ta baya tace "ai wllhi innarmu in na auri mai kuɗi ke kanki saide a miki komai, kawai aikin ki kwanciya ki huta, sai cin abinci sai sallah."
Daƙuwa inna tayi mata tace "gidan ku an gaya miki kowa malalacine kamar ki.". Dariyar shaƙiyanci Ma'u tayi tace ai wllhi innarmu har tsintar shinkafa sai kin daina yi, saidai kina zaune inji ya tsince miki shinkafar ki."
Cikin dariya inna tace ƙarfi da yaji kin mai dani kakar ki ko,? To nidai fatana Allah ya kawo wannan lokacin, bani da wani buri da ya wuce inga aurenki husnah, Allah ya fito miki da miji nagari da gaggawa..."
Inna ta ƙare maganar cikin marereta, Ma'u kuwa bata ce komai ba tayi tsakar gida, ruwa ta ɗiba a botiki zata yi wanka, koda ta cire pant ɗin ta ganin ya ɓaci sosai hakan yasa ta ɗaura niyar wankan janaba, a zuciyar ta tana mamakin yadda akayi dan jiya da dare ma da tayi mafarkin Haidar yayi sex da ita, da asuba saida tayi wanka, yanzu ma wannan dan baccin da tayi, Saida tayi mafarkin yayi sex da ita, a ranta tana so ta tuna wani abu saide ta kasa tunawa, kawai abu ɗaya take tunawa, shine! Daɗin da Haidar yake jiyar da ita da kuma soyayyar da yake nuna mata, murmushi tayi saboda amsar da zuciyar ta, ta bata idan kana son abu komai ma yakan iya faruwa.........✍️








*Mutane da dama suna tambaya ta meye namijin dare, wasu sun sani wasu basu sani ba, To amma insha Allah next page zanyi magana akan shi namijin dare, da kuma alamomin sa, bawai iya mace ke da namijin dare ba, harma maza akwai

Please Login or Register in order to submit comment