Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai sauti sannan tace
"Ina amsawa.."

Nan Suraj yaja ta da hirar soyayya, ita dai Ma'u saide kawai ta bishi eh ko ah ah, bai kawo komai ba tunda yasan harda rashin sabo da take da shi akan al'amarin...
Cikin farin ciki da jin daɗi suka gama wayar, dan ita kanta Ma'u baza ta iya cewa bata sonshi ba, haka kuma bazata iya cewa ba ta fara sonshi, ita dai kawai yana burgeta ne ga rayuwar sa yana tafi da ita yadda Yakamata, ko kaɗan baya da girman kai, ko jin shi ɗin wani ne, ita dai rayuwar sa ta mata.....

Tana cikin wannan tunanin ne, taji wayar tayi ƙara alamar shigowar saƙo, tana dubawa taga an rubuta
*"Matata insha Allah!*
*Ina so ki tashi kije kiyi al'wala, kizo kiyi sallah koda raka'a biyu ne, sannan kiyi mana addu'a sosai, INA SONKI..*

Murmushi Ma'u tayi tana maimata saƙon, kallon su inna tayi, nan taga inna har ta fara bacci ita kuma zahrah tana chart da wayar ta, dama yanzu tunda inna ta san lalurar Ma'u, suke kwana tare a ɗaki ɗaya, duk dan ta gujewa mu'amala da Haidar.....

Saukowa daga kan gadon inna Ma'u tayi a hankali, fita tayi tsakar gida dan ta ɗoro al'wala, har ta tsuguna da niyar al'walar sai taji tana jin fitsari, da sauri ta shige toilet ba tare da tayi addu'a ba, tana tsugunnawa taji motsi a bayanta, da sauri ta juya cikin tsoro, ganin wajen tayi wayam alamun ba kowa, da hanzari tayi tsarki tana shirin barin bayin, dan Allah Allah take tabar gurin, gaba ki ɗaya ta tsorata da yanayin, ji tayi anyi sama da ita, kama akan iska haka take jinta, lokaci ɗaya ta fita a hayacinta Bama tasan inda kanta yake ba, Saida ta ɗauki tsawon lokaci, sannan ta dawo hayacinta, samun kanta tayi akan wani ƙayataccen gado yayin da haidar yake zaune a gefe ya juya mata baya, yana kallon tarin hannunsa....

Cikin tsiwa da rashin kunya Ma'u tace

"Meye na kawo ni nan! Ni ka mai dani inda ka ɗauko ni..."
Ganin ya mata shiru kamar ba da shi take magana, hakan sai ya ƙara ƙule Ma'u, cikin fushi Ma'u tasa hannu da niyar fisgoshi, ko gezau bai yiba asali ma yana nan a yadda yake kamar ba wanda ya taɓa shi, sai ita da tazo fisgoshi sai taji kamar ita aka fisgah, ta sowa tayi ta zagayo ta gaban shi, kallon shi take tana jin zuciyar ta kamar zata fashe da tsoron shi, ita wallahi ko can dama da tasan haidar al'jani ne, bata ji tsoron shi ba kamar yadda take ji a halin yanzu, bin hannun nasa tayi da kallo, ganin ya ƙura mai ido ko ƙiftawa ba yayi, yasa ta leƙa kanta abinda ta ganine yasa ta zaro idonta.........✍️













*MORE COMMENT*
*TYPING*
*PLS SHARE*
















~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/18, 9:51 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


__________________________________________________




*45 & 46*







_____________Ba komai ta gani ba illah, Suraj zaune kan dadduma sai ƙur'ani mai girma da ke gaban shi da dukan alamun dai karantawa yake...
Da sauri Ma'u ta buɗi baki da niyar yin magana, amma sai Haidar yasa yatsan sa a leɓenta yace

"Shishhht!! Kar inji bakin ki yanzu, a gaba in dawo ta kanki.."
Allah sarki Ma'u sai ta koma gefe ta zauna, yayin da ta rafka uban tagumi wani tsoron Haidar take ji, yana shiga lugu da saƙo na zuciyar ta, cigaba yayi da kallon Suraj ta tafin hannunsa..

Saida ya ɗauki tsawon lokaci sannan ya ɗago, kallon Ma'u yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yace

"Masoyiyata taho gareni.."
Shiru Ma'u tayi tana binsa kawai da ido a zuciyar ta kuwa, sunan Allah kawai take ambato dan shine kaɗai zai kawo mata ɗauki, game da azzalumi HAIDAR..
Tsinkayar muryar sa tayi yana cewa "baki ta so ba fa.."
A hankali Ma'u ta so har ta ƙara so gaban shi, tsugunnawa tayi a gaban shi cikin kuka Ma'u tace

"Haidar! Dan girman Allah karka cutar da sur...."

"Shishsht! Bana ce Miki ba kar inji bakin ki anan ba, kiyimin shiru.."
Ido kawai ta zura mai tunda ya hanata tayi magana da bakinta...

Janyo ta jikinsa yayi ya rungume ta tsam, kamar za'a ƙwace masa ita sai faman jera ajjiyar zuciya yake kamar wanda yayi tseren gudu, magana ya fara cike da rauni yace

"Wallahi Ma'u! Badan sonki da ƙaunar da nake Miki ba, wallahi banga dalilin da zai hana na miki hukuncin abinda kika min a yau ba, meye shi wannan bil'adama yake da shi wanda ni bani dashi, ki duba fa na fishi kyau nafishi sonki ke na fishi komai, meyasa lokaci ɗaya zaki sauya ra'ayi,? meyasa..?"

Ya ƙare maganar yana ƙura mata ido..
Shiru Ma'u tayi haɗe da sunkuyar da kanta, a zuciyar ta kuwa nemon temakon Allah take ta kowanne yanayi...
Cigaba Haidar yayi da cewa
"Ko kin manta alƙawarin ki a gareni, na zaki kasance tare dani a kodayaushe..?"
Nan ma shiru Ma'u tayi me, sai kuma can ta saki kuka tana cewa
"Ni ka maidani gidan mu bansan ganinka, na daina sonka ɗin, kawai ka maidani inda ka ɗauko ni.."
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka....
Sakinta haidar yayi, yayin da idanunsa suka rine baƙiƙƙirin, dan ɓacin ran da yake ciki, komawa gefe yayi ya zauna yana kallon Ma'u da take kuka, kamar ance mata uwarta ta mutu....
Jin kukan nata yake har cikin ƙoƙon zuciyar sa, saidai bazai iya hanata yiba, saboda ko da wasa baijin zai iya rabuwa da ita ba....

Ta ɗau tsawon lokaci tana kukan har Saida ta gaji dan kanta, sannan ta taso..
zuwa tayi gaban Haidar ta durƙusa, kama ƙafafuwan sa tayi tana cewa
"Ina mai haɗaka da Allah da Annabi Haidar ka fita daga rayuwata ko na samu salamah, kabarni in auri jinsi nah, nayi rayuwa ta kamar yadda kowa yake yi, Haidar pls kaji tausayina....."
Ta faɗa tana haɗa hannayen ta......
Kauda kansa Haidar yayi yace
"Bazan iya ba! Saboda ina sonki, in na rabu dake ni kuma sai inyi yaya da rayuwata..."
"To kabarni in auri jinsi na! Kodan farin cikin iyaye na.."

"Shima bazan iya ba! Saboda ina matuƙar kishin ki, kuma ma naga ai yanzun ma kina da aure, tunda kina dani, ko akwai wani abu da na tauye miki a rayuwar mu ta aure ne..?"

Ihun baƙin ciki Ma'u ta kurma, da kuma na rashin sanin madafa......

★★★
Ɓangaren su inna kuwa da inna ta tashi da asuba, ganin bata ga ma'u ba hakan yasa tayi tunanin ko tana bayi, jiranta tayi akan in ta fito itama sai ta shiga ta kama ruwa, shiru shiru Ma'u bata fito ba, hakan yasa inna fitowa tazo wajen bayin tana kiran Ma'un....
Jin shiru bata amsa ba, yasa inna ta fara sababin ta
"Waike Ma'u uwar mai kike yi a bayin da har baza ki fito ba, na hanaki daɗewa a bayi, amma kinƙi ji ko Allah yasa na shigo na sameki anan ciki wallahi sai ranki ya ɓaci..."
Jin shirun yayi yawa gashi kuma bata jin motsin kowa, sai ta tura ƙofar bata ga komai ba, saima butar da ma'u ta shiga da ita jiya da dare, bata kawo komai ba, tayi abinda zata yi ta fito tayi al'walar ta, ta shige ɗauki abinta....
Saida inna ta idar da sallar tukunan ta tashi, zahrah tana ce mata
"Maza tashi kizo kiyi sallah, daga nan ki tashi Ma'u ina ga ɗakin can ta koma ta kwanta, tashi zahrah tayi ta fita, Saida ta kammala al'walarta, sannan ta tunkaro ɗakin ƙwanƙwasawa tayi tana kiran sunan Ma'u, shiru bata amsa ba, hakan yasa zahrah tura ɗakin, wayam babu Ma'u cikin tashin hankali zahrah ta ƙwalawa inna kira....
Da hanzari inna ta fito tana cewa
"Lafiyar ki kuwa zahrah da sanyin asuban nan, zaki riƙa wa mutane ihu.."

"Wallahi innarmu adda Ma'u bata cikin ɗakin nan.."

"Kamar ya bata ciki! Inba ta ciki ina zata shiga to..?"

Saida suka leƙa ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan, amma basu ga ma'u ba, cikin tashin hankali inna tasa zahrah ta kira kawu Salisu, shima da yazo ya shiga cikin tashin hankali, ace babban mutum a neme shi an rasa to ina Ma'u kuma tayi......
Sosai hankalin su ya tashi, dan sun rasa ta ina ma zasu fara neman ta...

★★★
Suraj kuwa tun da asuba da ya tashi ya kira wayar hannun Ma'u, jin ba'a ɗaga ba yasa yayi tinanin ko bata tashi ba, ko kuma bata kusa da wayar ne....

Duka iyalen gidan Daddy zaune suke suna breakfast, bayan sun kammala ne Daddy ya kira Suraj yana tambayar sa yadda suka yi da ma'un, nan Suraj ya labarta mai komai ciki kuwa harda lalurar da aka ce Ma'u tana da ita, kawai abinda ya ɓoye mai shine bai bashi labarin cewa AL'JANIN Ma'u yana kashe mata samari in sun nace sai sun aureta, kuma ko su su inna ya riƙe su akan subar wannan abun a matsayin sirri, bai so su ƙara gayawa kowa...
Nan Daddy yace

"Gaskiya wannan yarinya tana da babbar lalura, Allah Ubangiji ya zaɓa mana abinda yafi alkairi, amma Salisu bai taɓa gayamin ba wallahi.."

Suraj yace "ai da yake suma kwanan nan suka fahimci tana da NAMIJIN DAREN, amma yanzu sun fara nema mata magani..."

Daddy yace "to Allah ya kawo mafita insha Allahu, anjima zan kira shi salisun mu tattauna akan maganar auren.........✍️








[6/17, 7:27 PM] Matar Khamis,: Haidar Wallahi duk nacinka Sai ka rabu da Ma'u.haka kawai ka hanata Aure,Ina ake aure tsakanin mutum da Aljan indai ba Mugunta ba,to wannan Karon dolenka ka hakura.muna gdy sosai Allah ya Kara basira yasa kifi haka.much love for you Sis.🥰🥰👍


[6/17, 7:29 PM] Matar Khamis,: [6/17, 11:17 AM] Marichou: Kai Masha Allah Allah ya kara basira
Ko meye Ma'u ta gano😳😳😳😳


[6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Nashiga fargabar abinda ma'u tagani


[6/17, 11:41 AM] +234 906 547 6395: Allah y kara basira d alama haidar bacin ransa na rashin nasara ne


[6/17, 11:48 AM] +234 816 328 3548: Masha Allah matar khamis Allah yakara basira dakarfin ido dazakin hanu munagodiya Allah yabarki da khamis har aljanna🤣🤣🤣🤣💃💃💃


[6/17, 12:16 PM] Ummu Khalid: Da alama soyayyar Suraj tayi nasara haidar kowa ya hango faduwa! Hmmm kishi da mutum ya Kare balle halittar da baka gani! Ga Dan Adam da shagala! Kishi tsakanin Suraj da Haidar! Bafa sai na fada muku duk Kan ahli biyu suna farinciki ba 😁domin Suraj mutum nai da matar sa ta mutu Yan gidan su suna ta so suga yayi aurai😄ma u ta Jima Bata shiga daga ciki ba😄 Ga haidar Aljanin soyayya!!! Haidar zaka Bari muji yadda yadda a Yi kayataccen biki 💃💃💃😁 ko aa? Da alama fa Suraj dan soyayya nai😍 shin Mai haidar yake so ya nunawa mau? Mrs khamis muje zuwa Allah ya kara fasaha👍🏾


[6/17, 1:25 PM] Fateemah Adam: Muna gdy Allah yakara basira kifi yadda kike yanzu yabiya maki bukatunki na alkhairi damu baki daya
[6/17, 2:21 PM] +234 916 233 5086: Toh me taga ni ?
Munje zuwa...muna godia Mrs khamis


[6/17, 7:30 PM] Matar
Khamis,: [6/17, 12:03 PM] Ummu Abno: Allah ya qwaci Suraj yau a hnnun haidar ita kanta ma'u tashiga taskun shi Allah y qwacesu 🤲🏻



[6/17, 2:10 PM] Maman Khairat: Allah yakara basira da zakin hannu to ma'u kema Allah ya qwace ki


[6/17, 5:48 PM] +234 806 548 4348: Tab🤔narasa me dance dan tsoro



[6/17, 6:30 PM] +234 913 122 9563: Dakyau soRaj ka iyaya soyayya tunda gashi ma'u tafara manta haidar matar khamis Allah y Kara zakinhannu tareda basira






_comment ɗin ku fa yana ƙara fasamin kai, ku taimake ni kar kan ya dagargaje😹_



_yan facebook groups Ni daku akwai amana cau cau💪💃_




_Ƴan group dina na Whatsapp ina yinku over kunfi kowa búrgeni yacin🥰💃😹_

*ALLAH DAI YA BARMU TARE*







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*









~MATAR KHAMIS CE 🥰💃~
[6/20, 4:18 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________










*47 & 48*






______________Suraj ya kira wayar hannun Ma'u sau ba adadi, amma shiru ba'a ɗaga ba hakan ya matuƙar ɗaga mai hankali, kawai sai ya yanke shawarar kiran kawu Salisu dan yaji ko lafiya, shima Saida ya kira shi sau wajen uku sannan ya ɗaga.....
Bayan sun gaisa ne kawu Salisu yake sanar da shi abinda ke faruwa, cikin kiɗimewa Suraj yace

"Yaushe kuma aka sace tan! Ko jiya da dare fa munyi waya da ita...."

Kawu Salisu yace

"Wallahi kuwa dai!
Saida safe muka nemeta muka rasa, amma muna tunanin ko ƴan kidnaping ne suka ɗauketa ..."
Cikin damuwa Suraj yace
"Tabbas haka zata iya faruwa, kasan yanzu yadda ƙasar tamu take, Allah dai ya kawo mana ɗauki..."

"Ameen ya Allah! Insha Allahu muna nan, muna tayin addu'a da yardar Allah Ma'u zata bayyana.."
Kawu Salisu ya faɗi haka cikin rauni, a sanyaye Suraj ya ajje wayar zuciyar sa cike da damuwa, a iya jiya ne kawai ya keɓe da ma'u, amma ba ƙaramin jinta yake a zuciyarsa ba, ta riga da ta zama shi ya zama ita, sosai ya damu da ita da al'amarin ta, hakanan yaji Allah ya sa mai tausayinta da kuma tsantsar ƙaunar ta acikin zuciyar sa...
Dogon numfashi yaja yana jin ransa yana ƙuna, ayyana abubuwa da yawa yake a ransa, ganin hakan bazai fushshe shi ba, sai ya tashi da sauri jin kiran salhar azzhar, al'wala yayi ya wuce masallaci, bayan idar da sallar kuwa, ya daɗai a zaune yana addu'o'in Allah ya bayyana Ma'u cikin aminci......
Da yamma kuwa da Daddy ya dawo daga office, nan yake wa Suraj faɗa akan meyasa bai biyosa office ba, tunda yanzu kana hutu kan ya koma ai sai ya riƙa zuwa yana taya shi aiki..
Cikin ladabi suraj yace

"wallahi Daddy yau ɗin ne nake jina wani kala, gashi kuma ɗazu kawu Salisu yake sanar dani ƴan kidnaping sun ɗauke Husnah.."

"Subhanallahi!! Kaji baƙaƙen mugayen ko, Allah ya mana katangar ƙarfe dasu, Allah Ubangiji ya mana maganinsu.."

Suraj yace "Ameen ya Allah.."

Kai tsaye Daddy kawu Salisu ya kira bayan sun tattauna akan abun, sai Daddy yace "indai har sun kira to kuyi min magana dan Allah.."
Kawu Salisu yace
"Allah yasa to su kira yau.."
Daddy yace "ameen.."

Ɓangaren inna kuwa ta shiga tashin hankali dan bazai misaltuba, Ko abinci ta kasaci, sallah kaɗai ke tadata, amma ko ƙwaƙwaran magana bata iya yi, sai Allah da take kaiwa kukanta dan shi kaɗai zai kawo mata mafita acikin lamurran ta.....
★★★
Ma'u kuwa tun tana kukan har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita anan inda take a durƙushe, shi kuwa Haidar dake zaune yana kallon ta, ji yake zuciyar sa tana ƙuna sosai, musamman idan ya tina yadda Ma'u take cemai, bata sonshi, wani take so, kuma ya fita daga rayuwar ta, sai yaji kamar ya shaƙe kansa ko ya huta....
Duk wani kalar hukunci da ya shirya yiwa Suraj, sai yaji gabaki ɗaya hukunci ya mai kaɗan, dan duk shine silar sa shi cikin wannan yanayin..
Ɗaukar Ma'u yayi ya kwantar da ita kan bed ɗin, yadda take turo baki alamun shagwaɓa take ji, sai hakan ya matuƙar birge shi, ƙura mata ido yayi yana kallon leɓen nata da suka fi komai jan hankalinsa, yadda ya shagala da shauƙin kallon kyakkyawar surar ta, bai san lokacin da ya fara kissing ɗin bakin ta, shashshafata yake ta ko ina, yayin da yake ƙara dulmiya cikin shauƙin ƙaunar ta da kuma tsantsar sha'awar ta...
Cikin bacci Ma'u take jin wani baƙon yanayi a tattare da ita, ƙara shigewa jikinsa tayi, tana ƙara banƙaro masa ƙirjinta, farkawa tayi da sauri kamar ance ta buɗe idonta, kawai sai taga Haidar a kanta yana ƙoƙarin yin sex da ita, sunan Allah ta fara kira, haɗe da sakin a'uziyyah da ƙarfinta, sannan ta fashe da wani marayan kuka.......
Lallashinta haidar ya fara yana cewa
"Haba Ma'u meye haka ɗin! Yau ni kike neman tsari dani, sai kace kinga shaiɗani..."?
Cikin kuka Ma'u tace
"Wallahi Haidar kai kafi shaiɗanin ma! Inba haka ba mai na maka da ka'adabi rayuwa ta, ka rabu dani mana, ka mai dani gidan mu, kuma kabarni in auri Suraj shi nake so yanzu.."
Haidar da yakai ƙololuwar fusata, yanayin sa da kamanninsa gabaki ɗaya sun sauya, saboda ɓacin ran da yake ciki, tashi yayi yabar mata ɗakin dan muduk ya cigaba da zama kusa da ma'u, to zata cigaba da ce mai Suraj take so, shi kuma bazai iya jurar haka ba, gwara ya fita yabar mata gurin gaba ki ɗaya.....

Ma'u kuwa da taga ya fita, haɗa kanta tayi da gwuiwa ta cigaba da rera kukanta....
Washe gari kuwa da safe, Ma'u koda ta tashi bata ga Haidar ba, gashi tana so tayi al'wala tayi sallar asuba, sai dai bata ga ruwa ba, bare kuma taga bayin da zata shiga.....
A fili ta furta
"Allah yasa ma yanayin salsallar
Ta faɗa tana hararar ɗakin sai kace shine Haidar ɗin,
_niko nace kai Ma'u karki yiwa Haidar ɗin mu sharri, dan kinga yana sonki_ 😏🏃‍♀️
tana cikin wannan tunanin, sai taga kamar an ajje ruwa a kusa da ita, tashi tayi ta dauki ruwan, waige waige ta fara, nan taga wata ƙofa ta buɗe, shiga tayi ba tare da taji tsoro ba, dan yanzu lamarin Haidar ya daina bata tsoro, koda ta idar da sallar kasa yin ko wacce addu'a tayi, kuka ta saki dan shi kaɗai ne take yi a halin yanzu taji ɗan sauƙi, komawa kan bed ɗin tayi tana cigaba da kukan ga wata uwar yunwa da take cinta, tana cikin wannan kukan ne taji an dafa ta da sauri ta juyo, ganin haidar ne yasa ta mai da kanta yadda yake, tana cigaba da abinda take...
Ɗaukar ta cimak haidar yayi ya ɗora ta akan cinyar sa, cikin son rarrarashinta yake mata raɗa a kunne
"Pls kiyi shiru kinji! Kina so na maida ki gida ko.?"
Ɗaga kai Ma'u tayi da sauri alamar tana so..

"Ok!! Indai kina so to ga abinci nan ki cinye duka, sannan na maidaki gidan ku.."
Bata abincin yake a baki, Ma'u badan tana so taci ba take ci, saidan kawai ya maidata gun innarta, bai barta ba Saida yaga zata yi ame sannan ya ƙyale ta, tashi Ma'u tayi tana cewa..
"Tunda na gama ci kazo ka maidani.."
Shiru ya mata haɗe da zuba mata ƙwala ƙwalan idanuwan sa, ƙara maimaita masa abinda tace Ma'u tayi, Saida yaja numfashi sannan yace

"Zan maidaki! Amma sai kin yarda da sharuɗɗa biyu.."

Ma'u tace "ina jin ka faɗe su naji.."

"Sharaɗi na farko shine! Dole zaki daina shan maganin da inna take baki, saboda cikina dake jikin ki kar ya zube, na biyu kuma shine, dole sai kin min alƙawarin zaki rabu da Suraj..."
Jin haka da Ma'u tayi yasa ta Sandare a tsaye, ta rasa ma mai zata ce wa haidar, cikin tashin hankali Ma'u ta furta a fili,

"Ciki.!! Ciki fa kace gareni haidar,? Kuma waima naka..? Na shiga uku ni Ma'u.."
Ta faɗi haka tana ɗora hannunta a kanta🙆‍♀️......................✍️







[6/18, 11:04 AM] Matar Khamis,: Masha Allah Allah ya biya Haidar kano kona mun rai haba irin wannan naci inaga suraj shine maganin ka


[6/18, 11:06 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:17 AM] Haskenah: Ikon Allah waikam haidar meyake nufi ne kam wlh karya yake baison ma' u dayanasonta baxai hanata aureba baxai aureta ba saide yake kulawa da ita koda wasu mugayen mutane xasu cutar da ita shikuma sai ya ankarar da ita Amma kwatakwata. Narasa gane meyake nema awajen ma'u tinda duk abinda yake nema ai yasamu sai yarabu da ita🤨🤨 jinjina gareki uwar gida kuma Amarya agidan Mr khamis fatan alkhairi fatan nasara agareki muna fatan Allah yabaki ikon gama wannan littafin cikin koshin lfy Allah yakara basira Allah yakara nisan kwana Mai albarka👌👌


[6/18, 11:05 AM] Matar Khamis,: Ameen ya Allah
[6/18, 11:06 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:43 AM] +234 813 069 6464: Allah yakara karfin ido


[6/18, 10:54 AM] +234 906 547 6395: Haidar sorrynka fa ma'u ta dena sonka dama zalunci baya dorewa Allah y kara basira mrs khamis suraj Allah y baka nasara wlh ina karantawa kamar kar page din y kare hk nakeji😍✌🏻


[6/18, 11:50 AM] Matar Khamis,: [6/18, 10:54 AM] +234 906 547 6395: Haidar sorrynka fa ma'u ta dena sonka dama zalunci baya dorewa Allah y kara basira mrs khamis suraj Allah y baka nasara wlh ina karantawa kamar kar page din y kare hk nakeji😍✌🏻


[6/18, 11:41 AM] Fateemah Adam: Topah wata sabuwa azzalumi shine kasaceta to Allah yanaganinka munafiki insha Allahu saura kiris muga bayanka domin ruwa batsaran kwando bane matar khamis munayinki over Allah yabarmu tare yahadamu a aljannah yakara soyayyarki azuciyan khamis



[6/18, 11:48 AM] Ummu Khalid: Lallai zalinci haidar yayi yawa😭 To ta Allah ba taka ba!!! Shin Mai haidar ya ke son ai watar wa akan Suraj? Da ya ke wani bibiyar sa ? Allah sarki 😢 innah da " Yan gidan su mau .shin gidan su Suraj zasu bar shi ya auri ma u ko sai an Kai ruwa rana! Matar khamis Allah ya Kara basira👍🏾



[6/18, 11:55 AM] Matar Khamis,: [6/18, 11:39 AM] Ummu Khalid: Shin za a ganai caiwa haidar nai ya sacai ma u kuwa? Lallai so makaho Suraj wato har da boyai Ana kashai Mata samari!!! Shin wani irin mataki haidar ya ke son dauka akan 1 Suraj 2 ma u 3 kawu salisu ( Mai naimo malami da kawowa) Ina labarin aljani Abokin haidar Mai tona Masa asiri! Matar khamis Allah ya Kara wa rayuwa Albarka muje zuwa😄🥰👍🏾


[6/18, 11:41 AM] Matar Khamis,: Ameen ya Allah
[6/18, 11:57 AM] Matar Khamis,: Masha Allah Allah ya biya Haidar kano kona mun rai haba irin wannan naci inaga suraj shine maganin ka


[6/18, 12:44 PM] Matar Khamis,: [6/18, 12:27 PM] Marichou: Haidar ka zama sorry🤪🤪🤪 Ma'u dai ta dena sanka😜
Kuma insha Allah☝️ sai ka rabuda ita, han'a kujimin aljani mai nacin tsiya🤭👉 bari nai shiru kar ya jini🤣🤣
Allah ya kara basira da zakin hannu Aunty


[6/18, 12:36 PM] Sadiya: Sis gaskiya inajin dadin wannan lbr naki sosai kuma ina ilmantuwa Allah ya saka da alkhairi


[6/18, 12:39 PM]
Ummulkairi: Inayimiki matar khamis💯Allah yakara basira
[6/18, 2:48 PM] Matar Khamis,: Tofa jama'a me Wannan mugun yake nufi daya sace ma'u?wato kagane cewa Sooraj yafi karfika shine ka bullo ta wannan haryar,to Aradun Allah Sai karabu da ita.itama yanzu Bata sonka kaje kanemi Aljana 'yaruwarka Dan Rainin hankali kawai.Matar khamis gdy trillion Allah ya biyamiki dukkan bukatunki na Alkhairi,inayinki over Wallahi.

[6/18, 6:28 PM] Matar Khamis,: [6/18, 3:14 PM] +234 706 058 4513: Shi zalinci ai baya dorewa

Matar khamis Allah ubangiji ya kara basira da nisan kwana mai albarka
[6/18, 5:43 PM] Maman Samhat: To masha Allah littafi yana tafiya yadda yakamata Allah ubangiji yataimakeki yakareki
[6/18, 5:45 PM] +234 901

Please Login or Register in order to submit comment