Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu macen dare, kude ku cigaba da biyoni acikin wannan lbr na namijin dare*


*_masu min fatan alheri da addu'a ina godiya sosai Allah ya bar zumunci, ga wanda keda tambaya ko wani sharhi zai iya tintiɓata a Whatsapp number na kamar haka. 09137879957_*
*Whatsapp only*





*More comment*
*More typing*
*Pls share*








~MRS KHAMIS CE🥰💃~
[5/28, 12:58 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*18 & 19*




__________Yau da gobe kullum kwanaki ƙara tsayi suke, yayin da Ma'u tayi matuƙar sabo da Haidar, dan yanzu ako wani lokaci takan iya ganin shi ta kowanne yanayi..
Tun tana ganin wasu abubuwan ban barakwai, har yanzu tazo tayi wani mugun sabo da hakan, ga soyayyar da yake nuna mata mai tsayawa arai..
★★★
Wasu hamshaƙan motoci ne suka faka a ƙofar gidan su Ma'u, wani dattijo ne mai cike da kamala ya fito daga ɗaya daga cikin motocin, wanda kallo ɗaya zaka mai ka gane hutu dajin daɗi su zauna a jikin sa, ɓangare gidan kawu salisu yayi fuskarsa ɗauke da fara'a.....

Shi kuwa kawu Salisu da yake tsugunne a ƙofar gida yana al'wala, mamakine ɗauke a fuskar sa ganin mutum ya nufoshi da murmushi, ƙura masa ido yayi dan bai gano ko waye ba. Saida ya ƙara matsowa kaɗan sannan kawu Salisu ya zabura da sauri yace "Ibrahim! Ashe rai kan ga rai..?"
Wanda aka kira da Ibrahim ɗin kuwa murmushi yayi yace
" wllhi kuwa ashe rai zai ga rai." Shiga dashi cikin gida kawu Salisu yayi fuskarsa da murnar da takasa ɓoyuwa..
Bayan ya gabatar mai da abinci da ruwan sha, babu ƙyama ko nuna isa Alhaji Ibrahim ya zauna yana cin abincin, bayan ya gama ne sai kuma suka ɓarke da hirar yaushe gamo, wani abun ayi ƙwala wani abun kuma a saki dariya, dan sun kai tsawon shekara sama da talatin basu haɗu ba, anan ne kawu Salisu yake ba Alhaji Ibrahim labarin rasuwar yayansa Bashir wato mahaifin su Ma'u, nan ya jajan tame haɗe dayi mai addu'ar Allah ya jiƙansa...
Cigaba suka yi da hirar su, inda suka kwashe tsawon awanni uku suna zantawa, tashi Alhaji Ibrahim yayi yace "To ni yanzu tafiya zanyi fatan dai zamu cigaba da zumuncin mu, ta yadda ko bayan ran mu iyalain mu zasu cigaba dayi..
Fitowa suka daga cikin gidan a tare, yayin da Alhaji Ibrahim yayi wa kawu Salisu sha tara ta arziƙi, har yazo zai shiga Mota sannan ya jiyo yace "amma ina ne gidan marigayi ina son na gaishe da iyalinsa..” kawu Salisu yace ga gidan nan ai a ƙofar gidan ma kuka ajje mota,." Alhaji Ibrahim yace "to masha Allah ai sai ka yi musu magana koh, sai in shiga mu gaisa." Kawu Salisu yace "ah bissimillah ka shigo ai ba wata matsala." Sallama sukayi cikin gidan, Ma'u dake zaune tsakar gida tana dakan barkono ita ta amsa musu sallamar, ganin kawu Salisu da wani Alhaji yasa ta shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarma, shimfiɗa musu tayi haɗe da tsugunnawa tana gaishe su, amsawa Alhaji Ibrahim yayi yana ƙare mata kallo, komawa Ma'u tayi ta cigaba da dakan barkonon ta, kawu Salisu ne yace "ke Ma'u ina adda Hajaran take?." Inna da ta fito daga cikin bayi hannunta ɗauke da buta tace "gani nan ina zuwa, ɗaki ta shiga ta ɗauko mayafin ta rufe jikin ta tayi dashi, zuwa tayi ta zauna dab da su gaisawa sukayi inna tana wa Alhaji Ibrahim kallon rashin sani, kawu Salisu kuwa ganin inna bata gane Ibrahim ba, yasa yayi saurin cewa inna "adda Hajara!, Amsawa inna tayi tace "na'am." Kawu Salisu cigaba yayi da cewa "ina wani abokina wanda a lokacin kina amarya, muke zuwa in kinyi abinci mucinye miki.."
Shiru inna tayi tana tunanin abun dan anyi wajen shekara arba'in, can inna sai tace "kodai Ibrahim ne." Kawu Salisu yace "eh shine." Fuskar inna da mamaki tace "Allah mai iko! Ibrahim ashe dama kana nan.?" Yace "wllhi kuwa adda yau gani kin ganni." Na suka ɓarke da wata hirar, har saida suka gaji dan kansu sannan Alhaji Ibrahim yayi musu sallama, tare da musu alƙawarin insha Allah zai kawo matarsa da ƴaƴan sa su gansu.
Itama inna sha tara ta arziƙi yayi mata kamar yadda yayiwa kawu Salisu, bayan kawu Salisu ya raka shi bakin mota ne sai Alhaji Ibrahim ya lalle shi yace "amma wannan yarinyar budurwa! Ƴar waye.? Kawu Salisu yace "ai ƴar wajen yayana ce itama, itace ƴar adda Hajara ta uku."
"Ayya fatan dai ba'a mata miji ba."?
Kawu Salisu yace "eh to gsky bata da wani tsayayyen saurayi, dan duk anyi wa ƙannan ta aure, ita ce kawai Allah bai kawo mijin auren ba..."
Alhaji Ibrahim yace "to shikenan nidai na yaba da hankalin ta, insha Allah zanyiwa *suraj* magana akan yazo ya ganta, idan ya mata, shima ta masa kaga sai su daidaita kansu... "
Sallama sukayi da kawu Salisu sannan escort ɗinsa suka ja motar.....

★★★
*WANENE ALHAJI IBRAHIM*


______Alhaji Ibrahim wani shahararren ɗan kasuwa ne, kuma shahararren ɗan siyasa, dan yanzu haka shike kan kujerar sanata cikin Katsina ta tsakiya.
Alhaji Ibrahim aboki ne ga kawu Salisu tun suna yara tare suka taso, abotar su ta koma ƴan uwan taka, dan a ta dalilin abotarsu ne har suka haɗa iyayen su suke zumunci..
Alhaji Ibrahim yana da shekara ashirin da biyar iyayensa suka tashi daga cikin batsari suka koma cikin garin Katsina, kasancewar mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne, amma duk da haka yana ziyartar abokinsa kawu Salisu..
A lokacin ne iyayen Alhaji Ibrahim suka mai aure, harkokin gida da na neman kuɗi suka sa ya rage zuwa batsari...
Allah cikin ikon sa ya ɗakaka kasuwanci Alhaji Ibrahim har yazama daga wannan kasar zuwa wannan ƙasar, Alhaji Ibrahim yaran sa uku duka maza babban ɗansa shine suraj sai mai bi masa mubarak sai ƙaramin su Salisu....
WANNAN KENAN


Shi kuwa kawu Salisu da yaga Alhaji Ibrahim ya tafi, da sauri yazo yana sanar da inna abinda Ibrahim ɗin ya faɗa, inna tana nuna tsatsar farin cikinta tace "Allah ya tabbatar da hakan, dako nayi farin ciki dan Ibrahim abin a haɗa zuri'a da shi ne, ya cika mutumin kirki.."
Kawu Salisu yace "wllhi kuwa! Ni kaina nayi mamakin yadda bai mantani ba."
Inna tace "ai kuwa ya kyauta sosai wllhi, Allah dai ya tabbatar mana da alkairi."
Kawu Salisu yace "ameen! " Yana shirin barin gurin...
Ma'u kuwa dake gefe tana zumɓura baki, ji tayi har ta tsani suraj ɗin da ko sanin shi bata yi ba, tashi tayi ta shige ɗaki tana jin haushin su inna dake neman kai da ita, sai kace an gaji da ita.......✍️





*YAU INSHA ALLAH ZAN CIKA ALƘAWARIN DA NA DAUKA AKAN YIN BAYANI NAMIJIN DARE✍️

*ALAMOMIN NAMIJIN DARE.*

_Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar sune:-_

*_Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita acikin barci,yawancin mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayi,amma sai su dauka halin mafarkine kawai,to a gaskiya ba haka lamarin yake ba._*

*_Yadda lamarin yake shine:-_*
_Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin zaka sameta tana fama da wadannan matsalolin zatace maka tana fama dasu._

*Gasu kamar hak:-*

*_[1]Bacin rai ba tare da anyi mata komaiba,haka kawai taji tanajin haushin kowa har ma mijinta,ko kuma taji kamar mijin nata ya saketa,ita ta gaji da auren,wanda da zaka tambayeta laifin mijin nata bazata iya fadin komaiba akai,kai wata rana ma taji ta tsani y'ay'an data haifa._*

_[2]Yawan ciwon kai daga lokacin zuwa lokaci kuma baya jin magani ko kadan._

_[3]Tsananin ciwon kirji da ciwon baya mai tsanani._

_4]Tsananin ciwon mara lokacin jinin al,ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace,kuma tasan wannan ruwan ba al,adarta bane,_

*kuma ya kasu kamar haka:-*

*[a] mai yauki*

*[b] marar yauki*

*[c] ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi*

*[d] ko fesowar kuraje masu zafi.*

*[5] Idan mijinta yana sauwa da ita sai take jin zafi,ko kuma yana saduwa da ita batajin zafi,amma bata samun biyan bukata.*

*[6]Kusan sallar magriba sai ta fara jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawa firgita,ko kasala da bacin rai.*

*[7]Idan ta dauki al-qur'ani zata karanta,saita rinkajin kasala, da hamma mai sanya hawaye, kuma tanajin barci sosai,amma da zarar ta ajiye Al-qur,anin sai taji ta wartsake kamar ba itace takejin bacci dazu.*

*[8]Kuma idan ta kwanta zatayi barci sai ta kasa yin baccin tayi ta juyi akan katifa,idan mijinta yazo kusa da ita sai take jin firgici da tsoro.*

*[9]Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga zubewa ko ya canja ya zama jawur,lebenta kuma ya rinka bushewa ko yayi jawur.*

*[10]Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani,amma ba amosani bane.*

*[11]Yawan kaikayin kunne dana hanci kamar mura zata kamata,amma kuma ba mura bace,ko yawan kumburin ciki.*

*[12]Yawan zubar da jini wanda ba jinin hailaba,ko hailarta ta dinga yi mata wasa.*

_Sannan kuma harma wacce bata da aure budurwa ko bazawara zata iya tsintar kanta acikin wannan matsalar,amma ita ban-bancinta da mai aure._

*shine kamar haka:-*

*_[1]Ita marar aure zata kasance duk lokacin da wani yazo wajenta da maganar aure kamar za,ayi sai abin ya lalace daga bangarenta ko bangaren wanda zai aureta._*

*_[2]Zata dinga munanan mafarkai tare da ganin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita acikin bacci da fuskar wanda ta sani ko da fuskar yar,uwarta mace._*

*_[3]Sannan zata rinka samun cututtuka masu wuyar waraka,kai harma da yawan zubar da jini ko jin ciwo,ko jinin yake zuba amma ba lokacin hailarta ba,ko ta rinka jin kasala ayayin da take karatun al-qur'ani tana fara karatun sai hamma ,kasala su baibayeta,ko kuma idan ana sallama da ita,sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsorata._*

*_[4]Kuma zata yawaita samun sabani da kiyayya tsakaninta da iyayenta ko 'yan uwanta ko jama'a ko kuma ta zama mai rashin kunya da rashin magana da iyaye da sauran dangi. Allah ya kara tsaremu daga sharrinsu tare da yi mana katangar karfe dasu, amin._*



*IN ALLAH YA YARDA NEXT PAGE ZANYI BAYANI AKAN YADDA ZA'A MAGANCE WANNAN MATSALA TA NAMIJIN DARE*





*More comment*
*More typing*
*Pls share*




~MRS KHAMIS CE 🥰💃~
[5/30, 10:32 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*page 20 & 21*



_________Cikin ƴan kwanakin nan Ma'u kullum cikin ɓacin rai take, kuma ba komai bane musabbabin haka sai su inna da basu da wata magana sai ta zuwan Suraj, Ma'u a koda yaushe cikin zullumi take, ba maganar da take ɗaga mata hankali sai irin taji an ambaci za'a mata aure..
Shiru shiru Alhaji Ibrahim bai kira kawu Salisu ba akan maganar ɗansa da kuma Ma'u ba, tun yana jira har yabar abun a ƙila ko ɗan nasa ya samu mata shiyasa bai kira sa ba, ko kuma yana jin kunyarsa ne..
Ana haka aka ɗau tsawon watanni, hakan yasa kawu Salisu ya dage da yiwa Ma'u addu'ar, Allah ya kawo mata miji nagari itama ko ta huta...
Kasancewar lokacin siyasa ne, duk wani mutum da yake harkar siyasa, to idan lokacin yayi sun fi neman mutane, haka ta kasance ayau , kawu Salisu ne tsaye da chairman ɗin L.G wato Alh Tanko suna tattaunawa, inda kawu Salisu yake ce mai "wato na fahimci cewa ku ƴan siyasa ɗin nan, ba kwa neman mutane sai siyasa ta matso, sai ku fara jan mutane a jikin ku dan wai a zaɓe ku, to ba campaign ɗin da zan ma."
Dariya Alh Tanko yayi yace "haba aboki na! Wllhi da alkairi nazo, dama zuwa nayi na cema ka taramin mata wanda mazajen su suka rasu, kuma suke da marayu, akwai wani tallafi da za mu basu suja jari.."
Murmushi kawu Salisu yayi sannan yace "ban tarawa! Ni kaina yaushe rabon da ka neme ni, ina ga tun kan ka hau kan kujerar chairman, sai yau kuma da buƙatar ku ta ƴan siyasa ta taso..."
Cigaba sukayi da tattaunawa, Ma'u da ta dawo daga aiken da inna tayi mata, ganin kawu Salisu tsaye da baƙonsa hakan yasa ta tsugunna ta gaishe su, shi kuwa Alh Tanko kallo ya bita dashi, saida ta shige cikin gidan sannan ya dawo da kallon sa zuwa ga kawu Salisu yace "wannan kyakkyawar yarinyar fa daga ina.?" Kawu Salisu yace "ƴata ce." Sosa ƙyeya Alh Tanko yayi sannan yace "ko za'a bani auren ta!, idan ba'a mata miji ba.?"
Shiru kawu Salisu yayi yana ɗan wani nazari yace "nace ma fa ƴata ce ko!."
"Eh ai naji ! Sanin haka yasa na nemi auren ta, kuma nasan kasan waye ni, idan ina da wani mugun halin kasani, idan bani dashi kasani, saide ban sani ba ko baza ka bani ba, idan kuma an mata miji sai ka faɗa min in haƙura.."
Kawu Salisu yace "a'a gsky ba'a mata miji ba, zaka iya zuwa idan ta amince da kai to na baka ita.." murmushi Alh Tanko yayi yace "to Masha allah!
Allah ya tabbatar mana da alkairi.."
"Ameen!." kawu Salisu yace suna yin sallama, bayan Alh Tanko ya tafi sai kawu Salisu ya shiga gidan yana labartawa inna abinda ya faru tsakanin sa da Alh Tanko, cikin murna inna tace "ai kawai kace yazo ya ganta gobe ma inda hali.."

_________________________________________
TO FAH READE'S IDAN BAKU MANTA BA FARKON LBRN KENAN INDA ALH TANKO YAZO GURI MA'U YANZU ZAMU DAWO KAN LBRN NE...✍️

____________________________________

Kwance take kan katifa tayi rufda ciki, sai raira kukanta take gwanin ban tausayi, ita ba komai bane yafi ƙara karyar mata da zuciya ba illah cewa da inna take Alh Tanko taimakon ta yake so yayi, kuma a rasa wanda zai taimake ta sai wannan tsohon banza, ita wllhi ta tsane shi da wani fuskarsa sai kace biri...
Ganin kukan bazai mata ba hakan yasa, ta tashi taje tayi al'wala, sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar ne sai ta miƙe da niyar yin nafila Sannan tayi addu'a akan Allah ya kawo mata sauƙin cikin lamarin ta, amma sai ta kasa yi, cire hijabin nata wurgi tayi dashi a ranta tana jin baƙin cikin hakan..
Komawa tayi kan katifar ta kwanta, ba tare da tayi addu'a ba bacci yayi awon gaba da ita...
Cikin baccinta take mafarkin Haidar ya kunna wata ga garumar wata wuta, ɗaukar wutar yayi da hannunsa ya jefata a cikin wani gida, lokaci ɗaya gidan ya kama da wuta, jiyo da kallonsa Haidar yayi zuwa ga ma'u yace "duk wanda yayi gingin neman auren ki, kaɗan daga cikin irin hukuncin da zan mai, har sai na tabbatar da baya numfashi a doron duniya........✍️





*AFUWAN KUMIN HAƘURI WLLHI BANDA CIKAKKEN LOKACIN YIN DOGON TYPING AMMA INSHA ALLAH NA SAMU LOKACI ANJIMA ZAKU IYA JINA*🥰



_SANNAN WANDA BASU FARA KARANTA LBRN NAN DAGA FARKO BA , ZASU IYA NEMA DAGA FARKO SU KARANTA SAI SUNFI GANE KAN LBRN_👌




*MORE COMMENTS*
*MORE TYPING*
*PLS SHARE*







~MRS KHAMIS CE~🥰💃


[6/3, 12:23 PM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata ko wani ba idan yayi kaman ce ceniya da rayuwar ka/ki afuwan akasi aka samu💁‍♀️```



```bissimillahir rahamanur rahim```



*_dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah ( s w a ) aminci da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu {s.a.w}_*



______________________________________



SADAUKARWA!!

ZUWA GA DUK MASOYA NA🥰💃




*bissimillahir rahmanir rahim*


____________________________________________________________




*22 & 23*



____________a firgice Ma'u ta tashi daga baccin, nishi take kamar wacce tayi gudun tsawon kilo mita dubu, dafe ƙirjinta tayi tana maida numfashi, a ranta tana ayyana miye fassarar wannan mafarkin da tayi yanzu...

Jin kiraye-kirayen sallar asuba da tayi ne, yasa bata koma baccin ba, zama tayi tana ta tinane-tinane, inna ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, haske Ma'u tayi da (tochlight) fitila ɗin dake hannun ta, ganin ta zaune sai abun ya bata mamaki..

,,, Inna tace "lafiyar ki kuwa Ma'u! Na ganki zaune a wannan lokacin.?"
Numfasawa Ma'u tayi sannan a hankali tace bakomai innan mu kawai dai naji kiran sallah ne, shine na tashi.."
Inna tace "ohhh! Nasha ba lafiya ba, yanzu sài ki tashi kiyi sallah.." inna ta faɗi haka tana barin ɗakin....
Ma'u kuwa tashi tayi tsaye a sanyaye, kamar wacce ƙwai ya fashe wa a ciki, da ƙyar ta idar sallar nan sakamakon wani azababben ciwon kai da ya saukan mata, bayan ta samu ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita...


★★★
Da safe kuwa misalin ƙarfe 7:30 daidai, kawu salisu ya shigo gidan a firgice, inna dake zaune tana haɗa musu abin kari tace "lfy Salisu naga ka shigo ba ko sallama."

"Hmmm! Kede bari adda Hajara, yanzu Alh Tanko yamin waya yake cemin jiya gidan sa gobara akayi, suna cikin bacci wuta ta kama, Allah yasa sun tsira da ransu, amma yace bai fitar da komai ba."
Kawu Salisu ya ƙare maganar yana cigaba da cewa

"Kuma Ni babban abinda yaban mamaki da tu'ajjabi shine, da yake cemin wai ya fasa auren Ma'u, in mun sami wani mu ba shi, amma shi wai ya fasa.."
Dare ƙirji inna tayi tace "ohh ni Hajara! yanzu shi Alh Tanko dan ƙaddara ta same shi sai yace ya fasa, Allah ka dubemu ka fitowa da Ma'u mijin aure.."
Inna ta faɗa tana ɗaga hannun ta sama....
Ma'u kuwa Allah sarki tana can tana baccinta, bata san abinda ke faruwa ba, sai bayan da ta tashi take jin labarin fasa aurenta da Alh Tanko, da kuma gobarar da yayi, bata san meyasa ba, haka kurum ta tsinci kanta da ji daɗin hakan a zuciyar ta....

Shi kuwa Alh Tanko abinda ya faru dashi shine......
Da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare, kwance yake shi kaɗai a kan gado dama tun da ya zowa da matansa batun auren sa da Ma'u, yaga kowacce cikinsu ta fara kawo masa da maganar rainin wayo, sai ya bi duk ya watsar dasu gefe, saide idan su suka neme shi, juyi yake shi kaɗai a ɗaki jin zafin da ake sai yà tashi dà ñiyar yín wanka bathroom kawai ya shige, koda ya fito kai tsaye kan bed ya nufa dan ya kwanta, jin yayi karo da wani abu yasa da sauri ya ɗago kansa..

Abin mamaki Haidar yagani xaune akan gadonsa, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya, cike da dauriya Alh Tanko yace

"me ya kawoka gidana a halin yanzu! Sannan ma ta ina ka shigo?, Bayan na rufe ƙofar, kodai can dama da kai na rufe...?”
Haidar fuskarsa babu alamun rahama yace

"kaga nayi ma kama da wanda in zai shigo wuri sai yabi ta ƙofa, ta kowani yanayi nakan iya riskar mutum a duk inda yake.."
Alh Tanko yace
"to mai kake nufi da haka, ko kana nufin kai al'jani ne..?"
Tashi Haidar yayi cikin isah da ƙasaita, yayi taku biyu zuwa uku, yace

"naji daɗi da ka fuskanci hakan, ashe dama kai ba daƙiƙi bane, to ma'u ita ɗin mata tace, kuma bazan taɓa barin wani ya aureta ina kallo ba, saboda haka kaje ka janye aurenta da ka nema, inba haka ba zan salwartar da rayuwar ka.."
Alh Tanko kuwa kawai binsa da ido yake Sa'annan kuma ya bushe da dariya yace "oh ni ɗan babana! yau wai ni akewa barazana, dan zan auri ƴar baiwar Allah ma'u, to bari kaji in gaya maka wani abu, na daɗai da sanin irin ku a gari, sai kunga yarinyar kirki kyakkyawa kuma mai nasibin samun manyan mutane, sai ta samu mijin aure saiku bi duk hanyar da kuka ga dama, kuyiwa wanda yazo neman aurenta barazana dan ya fasa ko, to kasani ni ba irin barazanar da zakamin wacce zata yi tasiri a gareni ba, kuma banga wanda ya isa ya hanani auren ma'u ba, ba aljani ba ko sarkin aljanu ne kai sai na auri ma'u kayi duk abinda zakayi.."
Haidar da ya matuƙar fusata ya jiyo ga Alh tanko ,wata kalar girgiza yayi wacce lokaci ɗaya, halittun sa suka sauya izuwa abin tsoro, yace

"dama nazo maka da aminci ne, a tinani na zaka amsawa buƙata ta, amma tunda kace haka bari kaga ƙarfin ikon aljani.."
Alh Tanko da ya raɓe jikin bango, ko cikakken motsi ya kasayi, shidai kawai bin Haidar yake da kallo, yana so ya buɗi baki dan yayi magana, amma ya kasa cewa uffan..
Yana ji yana gani Haidar yasawa gidan sa wuta, sannan ne ya samu kƙarfin tashi ya fita da gudu dàn tàimaka ma iyalen sa,
da ƙyar suka samu suka fita daga gidan basu cire komai ba..

Da asuba kuwa Haidar ya sake dawowa wajen alh Tanko yace "kaga bala'i na farko kenan, sauran kuma duk baza suma dad'i ba, amma wata alfarma da zan iya ma shine, idan ka janye daga aurenta, kaga wannan gidan naka da ya ƙone zan mallaka maka wani wanda ya fishi sannan na dawo maka da linkin abinda ka rasa.."
Shidai alh Tanko shiru kawai yayi, zuciyarsa cike da tausayin ma'u da iyayen ta, haka ya kira su yace ya fasa auren ta.
aransa yana mata fatan alheri da kuma fatan Allah ya rabata daga tugun wannan azzalumin shaiɗanin aljanin, da yake iƙirarin cewa shi musulmi ne......








*KWANA BIYU KUNJI NI DAN ALLAH KUMIN AFUWA, NI KAINA BANSO HAKA TA FARU BA SAIDE KOMAI SAI ALLAH YAYI, AMMA INA TARE DAKU MASOYA BOOK ƊIN NAN*








*MORE COMMENTS*
*MORE TYPING*
*PLS KU RIƘA MIN SHARE DAN ALLAH*







~MRS KHAMIS CE~😍💃
[6/5, 10:24 AM] Matar Khamis,: 👄👄👄👄


*NAMIJIN DARE*
_aljanin soyayya_✍️



```story and writing```



*by*
*_ummy mrs khamis_*
09137879957


________________________________________________________________________________


*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚

_(Domin Marubuta Mata)_

✨(W.W.A)✨


https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*short story*



*TSOKACI* :
```Wannan lbri ne ƙirƙirare ban yishi dan wata

Please Login or Register in order to submit comment