Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duba cards ɗin ta cigaba

Sallama suka yi suka shigo neman gurin zama suka yi

"Hala dai Mommy bata nan"

"Ba kiga gidan kaca-kaca ba, ai kenan kin san bata nan" "Wai harda Amaryar da saura sati biyu Aure amma bata iya gyara gu ba"

"Sarauniyar tsafta ai sai ki gyara, Ni ba wannan ba cards ne ya kawo shine nake tunanin ko gobe mu fara rabo"

"Zumuɗin me kike saura sati biyu fa, gobe fa muna da lectures sai dai ko jibi"

"Me tayi na zumuɗi, kar mu manta da wani a ce bamu da kirki gwanda kowa yazo,Ai da gobe da jibin duk ɗaya Allah ya Kaimu"

"Ameen dai" Miƙa musu cards ɗin suka yi suka cigaba da dubawa.


Sunyi rabon kati lafiya an gama lafiya har an fara shagalin biki anyi Ladies Night ranar Alhamis juma'a da Rana aka ɗaura Aure da daddare dinner sai Ranar Asabar yini da kai Amarya.




✫✫✫✫



Tafiya ta ke yi tayi kyau cikin less ɗin ta babu kwalliya ko ɗigo a fuskar ta amma tayi kyau sosai buɗe motar ta tayi ta shiga Da sauri Zainab ta riƙe murfin motar "Haba Hooriyah ya zaki tafi ke kaɗai bayan kin san kece best friend ɗin ta ai kamata yayi kina motar amarya"

"Kin san bana son harka irin haka Koh?, Abokan Ango su riƙa yi maka kallon raini"

"Sai aka ce Miki duk irin su ɗaya kowa da halin sa, dan anyi mana a wani gurin ai ba lallai ayi mana a nan ba, Kin san AndulFatah yana da kirki ai sai muyi wa Abokansa shaidar ma ai na gari ne"

"In kina son Abu kin dinga kare shi kenan, in na biku inyi Yaya da mota ta? Wa zai maida Anisah gida? Kin san Mama bata barin ta kaiwa dare"

"Ni zan tuƙa motar in zamu dawo sai ki maida ta gida sai ki wuce" "it's okay" fitowa tayi ta mika mata key ɗin motar "Take care, sai mun haɗu, ki kula da Anisah please"

"ok karki damu" ta wuce "Mtwsssss sai kace wata yarinya kullum a kula da Anisah, kamar wata jaririya" motar ta kulle ta koma ciki gurin su, idan sun gama sai su tafi.


Zaune suke a cikin Mota suna jiran Ango da Abokinsa su tafi "Kinga irin abinda bana so, an zo an shanya mu bacin basu gama shirya wa ba"

"kiyi hakuri ayi masa uziri mana kin san mutane ne suka riƙe shi amma da tini mun tafi"


"Mene amfanin ake biki ba'a ga Amarya ba, ni in ana biki na da wuri zanje kowa ya zo akan idona"

"Ce Miki akayi zasu tafi, Allah dai ya Kaimu lokacin in zaki iya" buɗe motar akayi Ango ne ya shigo da abokin nasa "Me ya farunaga duk kunyi shiru"

"Gata nan faɗa takeyi kun daɗe, harda cewa ranar bikin ta kowa a gaban ta zaizo" dariya suka saka gaba ɗayan su

"Hooriyah ayi mana afuwa mana, Wannan tsohon tuzurin ne ya ɓata mana lokaci, Ya kamata kaima kayi Auren nan fa"


"Kaima yaushe ka fita daga sahun tuzuran, Ni ma dai ina ganin na kusa Auren nan dan na samu matar Aure yau"........✍️



#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Follow My Pages

Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1

Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only



Please Share & Comments 🙏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم



𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️


𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟏&𝟏𝟐



𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯



✫✫✫✫


"Haba, a ina take"

"Gata a kusa dani, amma da alama sai kun taya Ni campaign"

"Ba sai mun taya ka campaign ba ma zaka samu shiga Insha Allah" dariya yayi, Ita da yake yi don ita ko ƙala ba tace Ba balle ta ɗago chatting ɗin ta take yi

"Allah yasa"


Tunda suka je yake liƙe da ita duk inda zata yana bayan ta kamar jela har aka tashi daga bikin. Fito wa suka yi daga ciki Zainab ta kalla "ina key ɗina Kinga anyi Isha'i ya kamata mu koma gida, zan ajiye Anisah a gida"

"Ai tare da ke zamu koma, yadda muka zo tare" wani banzan kallo ta watsa masa ɗauke kanta tayi daga gare shi, Zainab ce tayi magana"gashi za'a mai da ke gidan su Khaleesat ɗin ba sai mu haɗu a can ba sai ku tafi"

"Ai daga nan zamu rabu, na gaji sosai wallahi"

"Mu yanzu yaya zamu yi in kika tafi da motar a me zamu koma"

"Da zamu taho ai baki yi wannan bayanin ba, kuzo sai in rage muku hanya sai mu wuce"

"Ai ko baki isa ba, ki samu za'a kai ki Sannan kice A'a" juya wa tayi gurin su Khaleesat "Khaleesat kizo ku saka baki ta biku mana, ma haɗu acan sai ta karɓi Motar"

"Kin san in ta nace akan abu sai tayi ki bata key ɗin sai mu tafi tare tunda ku biyu ne, Babe ka shiga gaba sai mu zauna da su a baya Koh"

"Ya ma fi ai, dan wannan ƴar darun in ta nace sai tayi Abinda take so" suka saka dariya

"Ungo Key ɗin ki, Gobe ma Rana ce" ta miƙa mata "Yafi dai, Good Night bazan shigo da wuri ba gobe, Anisah muje koh"

"To, Sai da safe" mota suka shiga suka tafi. Maida kallon sa yayi kan Ango

"Wallahi Auwal ka kwafsan ban so haka ba gashi sun tafi ko number ta nan karɓa ba"

"Haka yafi maka, Kabi komai a sannu mana"

"Nabi mu tafi Koh" Mota suka shiga duk suka tafi.


Washegari kamar yadda ta faɗa bata zo da wuri ba sai bayan La'asar tazo bayan sun gaisa waje ta fito ta zauna bata daɗe ba sai ga Anisah tazo a kusa da ita ta zauna "Anzo ɗaukar Amarya fa"

"Sai sun dawo, ba zuwa zan yi ba daga baya naje"

"Haba dai, wai me yasa kike haka ne"

"Minti nawa ne a je an dawo" jayayya suka yi tayi daga ƙarshe dai ta haƙura ta tashi ta bita suka fito compound ɗin gidan Duk masu zuwa gidan Amarya sun fito dan Amarya har ta shiga Mota ma Rukayya ce ta ƙara so gurin su"Khaleesat sai neman ki take yi amma dai zaki je Koh" ɗaga mata kai tayi kawai "Amma dai ba'a motar ki zaki ba dan Allah, muje tare mu dawo tare" kallon ta Kawai tayi ta wuce "Yau ciwon ya tashi Kenan, kin dame ta ne Koh" "Eh, da kin zuwa tayi sai da kyar ta tashi" "Allah ya Kyauta, amma in Hooriyah tayi Miki wani abin kamar ki dake ta, muje Koh" Buɗe mota tayi ta shiga kawai ta rufe suma shiga suka yi Basu dade ba suka tafi sun kai Amarya ba jima wa suka taho bayan Ango yazo.


Har compound ɗin gidan aka dawo da su buɗe kofar yazo yi taji ta a lock kallon sa tayi "Malam buɗe min mana" "Zaid nake, magana zamu yi ba zata wuce ta ten mins ba"

"Nidai Sunana Zaidul Haifaffen Kano Sunan Mahaifina Alhaji Sulaiman Former Senator Muna zaune a Nasarawa GRA Cikin Kano. Abokina ya Bani labarin ki kuma na ƙarbi number ki a Gurin amarya, na ganki kuma ina sonki Kuma Insha Allah Auren ki zan yi ki bani dama, zan kira ki please karki ki ɗagawa" kallon banza ta watsa amsa "Sai ka buɗe min Kofar na fita Koh" "Sorry Queen, sai na kira" ya buɗe mata motar, tsaki taja tayi ficewar ta. "Naga kin daɗe" suka haɗa baki gurin faɗa "ba komai, muje muyi musu sallama mu tafi"ciki suka shiga suka yi musu sallama Mommy sai godiya take musu sunyi wa ƴar ta hallaci sun cika ƙawaye motar ta ta shiga su kuma driver ya ɗauke su suka tafi.

A hanya ne take sanar da Anisah Abinda Ya faru tayi murna sosai kuma ta bata shawarwari. Sai da ta kaita gida sannan ta wuce tana shiga a palour ta zube Aunty ce ta fito daga ɗakin ta kallon ta tayi "yaushe kika shigo" "Yanzun nan Wallahi, Aunty ya gida" "Ai na zata sai anjima zaku dawo, Alhamdulillah" "A'a angama biki zaman me zamuyi, bari in shiga ciki na gaji" "Sai kin fito amma ki huta sai ki fito kinji" "Tohm Aunty" ta tashi ta shige ciki.

Wanka tayi ta saka kaya sallah tayi sannan ta kwanta.......✍️


Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Follow My Pages

Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1

Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only


Please Share & Comments 🙏




𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽



𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


بسم الله الرحمن الرحيم



𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟑&𝟏𝟒



𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯



✫✫✫✫



Tana tashi da safe da kiran sa ta fara cin karo sai ƙorafi yake ta kashe waya jiya Ita dai shiru tayi masa, sunyi waya da amarya sai da sukayi faɗa akan me zata bashi number ta da kyar ta haƙura.



Tun daga lokacin kullum shine cikin kiran ta safe, rana, dare wani lokacin ta ɗaga wani lokacin kuma ta share, shi kuma bai taɓa fushi ba ko ya kira bata ɗaga ba zai ƙara kira ne. Anisah kullum tana mata faɗa ta kula shi amma taki.

Duk lokacin da suka yi waya da Khaleesat tayi ta nacin ta kula shi yana damun su amma sai ta nuna bata san wa take magana akai ba.



ღღღ



Zaune take a palour gaba ɗaya hankalin ta yana kan littafin hannun ta exams take da ita gobe tana duba wa, sallama akayi Amsawa tayi ba tare da ta kalli mai sallamar ba "ka wani maƙale daga waje kamar ba gidan ku ba ka shigo mana, ke kuma Har yanzu dai Kina nan da halin ki Koh? baki chanja ba" ɗagowa tayi sai taga Aunty Safiyya ƙanwar mahaifin su



"Mama Barka da zuwa, Ashe kece na zata su Hauwa ne Wallahi, ku ƙara so ku zauna" ta tashi

"Bari in kawo muku ruwa"

"bashi nazo sha ba, ina su Uwar taki" ɗauke kai tayi daga kallon ta, tana jin Haushin zagin iyayensu da take yi in tazo daure wa tayi tace "Sun fita suna"



"Dama gurin ki nazo ba gurin su ba, sai ki nemi guri ki zauna ai" dawo wa tayi ta zauna inda ta tashi

"Gashi nan yayan ki ne kinsan kuma kin sun rabu da matar sa, gashi nan ku sasanta nan da ƙarshen wata a daura muku Aure tunda kunyi kwantai kinki Auru wa duk ƙannen ki sunyi Aure" a firgice ta kalle ta

"Yaya Salisu zan kai wa Daddy a matsayin mijin Aure? waye bai san halin sa ba"

"Kince Yaya, Ashe kinsan da alaqa a tsakanin ku sannan kina zancen hali, wane Hali zaki yi zance, ke da zai rufa Miki asiri ya aure ki"

"Mama ba Rashin kunya zan Miki ba, Amma gwara na mutu ban yi Aure ba dana Aure dan shaye-shaye mai neman mata ko ke baya girmamawa balle wani" ta ƙarasa faɗa tana zabga masa harara"Mama in Baki da wani abin cewa zan shiga ɗaki inada exam gobe"

"Ai ban san kin zama haka ba Hooriyah ina Miki magana kina min rashin kunya, duk halin Hafsa kin kwashe a cikin ki, bari iyayen naki suzo inji kosu suka ɗaure Miki gindin Rashin kunya" tashi tayi ta wucewar ta ɗaki masifarta ta cigaba da yi

"Auu tafiya ma kike yi ina miki magana kenan" ɗan nata ne yace

"Mama kinga Abinda nake guje miki kenan shi yasa nace kar muzo gashi yarinya ƙarama haihuwar yau tana faɗa Miki magana a banza, ai sai ki tashi mu tafi tunda ta gama faɗa Miki magana"

"Ai na gama yi maka komai Dole kace mu tafi, kai in ba Nan gidan nazo nayi jan ido ba ina kake tunanin za'a baka Aure bayan Wannan baƙin hallin naka da kake da shi, ai sai naci mutuncin iyayen nata sannan zata amince babu inda zani ina nan har sai sun dawo" tashi yayi yana magana

"Ai sai kiyi ta zama, in sun dawo sai mai da ke gida, Ni na tafi" yayi ficewar sa.

Cigaba da zaman jiran su tayi har bayan magariba sannan suka dawo ta kare musu tasss sun sha Masifa har da gori Aunty ta so ramawa amma Mami ta hana ta sai da tayi ta gaji sannan ta tafi.


Around 10:00PM



Zaune suke a palourn Daddy Aunty ta gama sanar masa abinda ya faru wayar sa ya janyo kira yayi "Kizo yanzu ki sameni a Palour na" shine kawai abinda ya faɗa ya kashe wayar, ba jimawa sai gata nan neman guri tayi kusa da kafar Aunty ta zauna "Daddy Barka da dare, ya aiki"

"Alhamdulillah, Kin san abinda kika yi baki kyauta ba Koh, Kanwata ce kinsani"

"Nasani Daddy kayi hakuri ba dason raina haka ya faru ba"

"Allah ya kiyaye gaba, Zan baki nan da ƙarshen satin nan ki fito da miji kafin ta dawo".......✍️



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I




#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Follow My Pages

Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1


Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Please Share & Comments 🙏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡




𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


тԋє ɯɾιтєɾ σϝ



*ʂιʅαɾ ɯαყα*



𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪



♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


بسم الله الرحمن الرحيم



𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟓&𝟏𝟔




𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖋𝖆𝖆



𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯



✫✫✫✫





A razane ta ɗago ta kalle shi "Daddy" ɗaga mata hannu yayi "ya isa haka bana son jin komai, tashi ki tafi" jiki a sanyaye ta tashi ta tafi. Aunty ce ta fara bashi hakuri "Daddy'n su ba haka ya dace kayi ba, a hankali zaka yi mata" "Hakan ne zaifi, in ta dawo kawai an mata miji kar wata Maganar ta tashi duk da ƙanwata ce" "Allah ya Kyauta" "Ameen" Mami ta ce miƙewa tayi "Bari in tafi, Allah ya tashe mu Lafiya" Ameen suka ce ta fice.



Tunda ta koma ɗaki take kuka sai da taci kukanta ta koshi sannan ta tashi Alwala tayi sai tayi sallah a Gurin ta kwanta ba ita ta tashi ba sai asuba.



Da safe sunyi waya da Anisah ta sanar mata abinda ya faru da yamma sai gata ta zo ɗaki suka tafi A nan ta ƙara sanar mata da abinda ya faru "Hooriyah zaki bi shawara ta" "Ai saboda haka na kira ki, wallahi kaina ya kulle na rasa yaya zan yi" "Ki amince da Zaid kawai" Wani Kallo ta watsa mata "Waye Zaid" "Ya kike min wani kallo kamar baki san shi ba, Bari in tafi tunda kin fara halin naki" ta tashi da sauri ta riƙo ta "Yi hakuri zauna muyi maganar" zama tayi "ke kika jiyo, indai shawara kike nema wallahi ki amincewa Zaid Kinga mutumin kirki ne abokin Auwal ne" Riƙe baki tayi "Iyyye ashe har kin san shi haka, har kin san yana da hakuri" "Ni fa bana son irin haka, wallahi zan tafi nazo kuma kina wani zance" tashi tayi ta fice, dage kai tayi "Innalillahi, itama zata gudu bata bani shawarar arziki ba" da sauri ta mike ta bi bayan ta a palour ta same ta suna magana da Aunty "Taso mu koma mu gama maganar please" Aunty ce ta kalle ta Sannan tace "Ayi maganar a gaban mu mana" "A'a Aunty sirri ce" tayi dariya "Anisah Meya haɗa ku" "Ba wani abu bane Aunty, bari inje" "Babu inda zaku, ku zauna, Meya haɗa ku" "Wallahi ba abinda ya faru Aunty bari kiji" nan ta sanar mata da zancen Zaid. Sallati Aunty tayi "Amma ban taɓa tunanin baki da hankali ba Hooriyah sai yau, Muda muke neman mafita amma kin san da yaron nan ai da sai ki faɗa masa" "Aunty Ni bana sonsa" "kin ba shi dama ne da har zaki ce bakya son sa, in dai na isa dake daga yau in ya kira ki dinga ɗagawa ki bashi dama, muga abinda Allah zai yi kafin ta dawo" nan ta ringa yi mata faɗa daga ƙarshe har Mami sai da ta kira ta faɗa mata tace sunfi kusa.



(Nima dai haka na gani kunfi kusa ba ruwan Mami😂)



Tunda ga lokacin ta fara sauraren sa inya kira tana ɗagawa ta saurare sa ya nemi ta bashi da ma yazo ta amince yazo har sun daidai ta.



𝐓𝐰𝐨 𝐌𝐨𝐧𝐭𝐡𝐬 𝐥𝐚𝐭𝐞𝐫



Soyayya suke yi tsaftattciya babu algus a cikin ta yana sonta tana son shi yanzu ita gani take bayan Iyayen ta babu wanda yake da mahimmanci a gurin ta sai shi kusan ko yaushe suna maƙale da juna ta waya indai baizo ba. Maganar ta yi nisa dan har manya sun shiga ana shirin kawo kuɗi.





Gidan shiru kamar ba kowa sallama tayi ta shiga ganin babu kowa a palour yasa ta fita part ɗin Daddy tayi shiga tayi a nan ta tarar da su ba sallama ba komai ta hau cewa "Ashe nan kika taho kika bar gida shiru, sai Anzo anyi sata kiyi ta rantsuwa bake bace, ina ita Aseeyar take"

"A'a Safiyya Ashe kece a tafe shigo ciki mana, Yaya taje dubiya"

"To Naji, sai ki tashi ki bamu guri zanyi magana da ɗan uwana" dafe kai yayi

"Wai Dan Allah Safiyya mai yasa ba zaki san Annabi ya gamu ba?, Meyasa kike musu haka ne? Wai ba gaba suke da ke ba Matana ne fa"

"Yaya babu mai mutunci a cikin su duk sun bata yara da rashin tarbiyya" Aunty ce ta tashi ta fice

"Ai gwara ki fita inyi magana da shi" sai kuma ta rissina.

"Yaya Ina wuni, da fatan na sameku lafiya"

"Ba gashi kin gani ba, Meya kawo ki"

"Yaya maganar Hooriyah da Sulaiman ce ta kawo Ni har yanzu naji shiru baka ce komai ba"

"To me zance Miki, bayan diban Albarkar da kika yi, Kuma maganar Sulaiman karki ƙara yi min ita nan da sati biyu zan karɓi kuɗin Auren Hooriyah, ina fatan shikenan sai ki tafi" ya faɗa a fusace.........✍️







Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I








#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Follow My Pages

Arewa Books: fatimaintisar1

Wattpad: fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only


Please Share & Comments 🙏




𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡




𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم





𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟓&𝟏𝟔



𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖋𝖆𝖆



𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯




✫✫✫✫



"Yaya maimake nufi in bar maka gida, saboda nazo ina son Sulaiman ya auri Hooriyah dan zumunci mu ya ƙaru amma kake korata, ai shikenan" ta tashi hawaye shaɓe shaɓe a fuskar ta, jin bai ƙara cewa komai ba yasa ta fice. Kara dafe kan yayi ya gaji da matsalar ƙannen nan nasa sun girma amma basu san sun girma ba kullum sune da matsala gwara ayi auren yarinyar nan kowa ya huta in sunga ba kowa ai sa haƙura cigaba da saƙawa da warwara yayi tayi.



Bayan sati biyu an kawo kuɗin Auren Hooriyah tare da saka rana nan da ten weeks kowa sai murna yake.



☆(❁‿❁)☆



Kwance take tana hutawa basu daɗe da dawowa daga gidan Khaleesat ba shirin biki suke tayi har sun fitar da Anko kira ne ya shigo dubawa tayi ganin bata san number ba yasa ta ajiye bata ɗauka ba ƙara kira aka yi bata daga ba katse wa yayi aka sake kira nan ma kin ɗagawa tayi maimakon mai kiran ya haƙura sai ya cigaba da kiran. Turo kofa akayi "Wai Anisah ba ƙarar wayar ki nake ji bane"

"Ita ce Umma"

"To ba zaki ɗaga ba ne ko yaya"

"Ban san waye yake kira bane"

"Baki ɗaga ba ina zaki san me kiran"

"In an ƙara na daga Umma" fice wa tayi kamar jira aka ta fita wani kiran ya ƙara shigowa ɗaga wa tayi tare da sallama "Wake magana"

"Ashe duk halin ku ɗaya tsiwa, to ba wani bane Zaid ne"

"Uhmmmmm ya kaje gida, har ka sauke ta kace"

"Eh, dama cewa zanyi in ba damuwa ina so gobe inzo zamu yi magana dake"

"Masha Allah, Ni kuma? Ok mu haɗu a gidan su Hooriyah"

"Eh ko ban kai ba, Ba da ita zanyi magana ba dake zanyi maganar sirri ce" dariya ta saki

"Ni na isa ince baka kai ba, Angon Bestie guda ai ka wuce haka, ok a ina zamu haɗu"

"A'a nasani ko zaki ce hakan sai in faɗa mata, gidan ku zanzo"

"Haɗa mu faɗa zaka yi kenan" "Ok Allah ya kaimu"

"Ameen" "Ai ban isa haɗa hanta da jini faɗa ba" haka sukai ta raha har ya kashe. Bayan ya kashe ne take sanar da Umma tace Allah ya kaimu.



𝑾𝒂𝒔𝒉𝒆𝒈𝒂𝒓𝒊


Bayan La'asar tana zaune sai ga kiran sa ɗagawa tayi "gani a kofar gida" shine abinda yace ya katse kallon Ummanta tayi "Umma bari inje " "Sai kin dawo" ta tashi ta fice.

Tsaye yake a jikin motar sa ya sha gayu gaisawa suka yi sannan yace "Da yake ba daɗewa nazo nayi ba magana zamu yi ta fahimtar juna please"

"Ok inaji, Allah yasa ba wani laifin tayi ba"

"Ba akan ta bane, Anisah" "Tunda na ganki na fara sonki amma nayi nauyin baki ban sanar da ke ba har aka kai kuɗi, Maganar gaskiya bazan iya haƙura da ke ba shiyasa na yanke shawarar sanar da ke, Auren ki nake so nayi da yaudarar ki zanyi ba" A kiɗime ta kalle shi bata san lokacin da ta fara zabga masa harara ba daga masa hannu tayi

"Dakata Malam na gaji dajin shirmen ka, Ban taɓa tunanin baka da hankali ba sai yau, baka san yadda nake da ita bane da zaka zo min da wannan shashancin?" "Ban taɓa tunanin maganar da zaka zo yi ba aiko wani ya faɗa zaka yi haka ƙaryata wa zan yi" "kaga nan" ta nuna masa hanya "ka mike ta straight ka koma inda ka fito" ta juya zata shige "wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, dan Allah ki amince min" "Da dawa kake rayuwar, mtwsssss" ta shige da sauri. Umma ce ta ce "Ya na ganki haka wata iri" "Ba komai" ta shige ɗaki, tashi tayi ta bita "Ke Anisah me yayi miki, ya naga kina kuka"

"Umma Ashe da gaske ne ana yaudara" "Meya faru ne kina sani a duhu Anisah" nan ta faɗa mata duk yadda suka yi da Zaid, Riƙe baki Umma tayi

"Ke da muke neman kiyi Aure yanzu Allah ya kawo miki miji har gida shine kike gudun sa, saboda wata"

"Umma saura wata biyu bikin su fa, Amma saboda cin amana ji abinda yace fa"

"Amma ban taɓa tunanin lusara na haifa ba sai yau" kallon ta tayi "Umma" "Karki ce min komai Anisah, shekarar ku nawa kuna tare bata taɓa tunanin hada ki da wani nata ba tace ya Aure ki, yan'uwanta nawa ne suka yi Aure kuna tare ai da sai tace wani a cikin su ya nemi ki, Allah ne ya kama ta shiyasa na ɗora wa wanda zata Aura sonki" "Umma duk yadda nake da Hooriyah amma da abinda zan saka mata kenan, Ni duk wannan abinda kika lissafo bai dame Ni ba"

"Ni kuma so nake kiyi Aure Anisah kullum girma muke ƙarawa, in na mutu yaya zakiyi, kin san dangin mahaifin ki ba ƙarbar ki zaki yi ba"

"Umma a bar maganar nan, wallahi ko daɗin ji babu"

"Ai ko dole muyi ta, Ai shi yazo bake kika je ba" "Ke dole ma ki Aure shi, zan sanar da dangin mahaifin ki yaje can su tattauna" zaro ido tayi

"Haba Umma Muda zamu rufe maganar nan kar muji kunya Hooriyah ce ba wata ba"

"Uwar ki ce, bari kiji indai Ni na haife ki sai kin Aure shi" ta tashi ta fice. Kuka ta Daɗa fashe wa da shi.



Tun da ga lokacin ta zama wata iri ta kashe wayar ta gaba ɗaya ko fita ta daina Zuwan Hooriyah biyu tace bata da lafiya. Ya dawo kusan sau Uku amma taƙi fita, A karshe gurin Ummanta yazo suka yi magana tace ya kawo Kuɗi indai da gaske yake yayi na'am da maganar ta kuma yace zasu zo a Weekend da zai tafi ya bata kuɗi.



(𝙷𝚊𝚓𝚒𝚢𝚊 𝚄𝚖𝚖𝚊 𝚊𝚗 𝚓𝚒 𝚔𝚞𝚍𝚒🤣😂)



Ta yiwa dangin mahaifin ta waya ta sanar musu Anisah ta samu miji zasu zo neman Aure Ranar Asabar.

An kawo kuɗi An saka rana ɗaya Da Hooriyah za'a daura tun tana tsoro har ta saki jikin ta, komai da ita ake yi na hidimar biki itama daga ɓangaren su Ummanta tana yi mata har aka zo ɗaurin Aure Babu wanda ya sani a sirri suka yi aka gama.......✍️

Bari mu koma labari



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I




#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Follow My Pages

Arewa Books: fatimaintisar1


Wattpad: fatimaintisar1



Please Share & Comments 🙏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



тԋє ɯɾιтєɾ σϝ


*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


بسم

Please Login or Register in order to submit comment