Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman Auren Hooriyah ko zaka yi hankali"

"Baki kalli abinda ake haska wa bane a TV?"

"Ni kasan ba kallon nan nake so ba da ita da babu duk ɗaya a gurina, me yake faru wa a garin kuma?"

"Ba abinda ake a gari, Yaya kuma bai sanar dake komai ba"

"Ni mun kwana biyu bamu yi waya dashi ba ko gidan banje ba, Meya faru a gidan"

"Yanzu aka daura wa Hooriyah Aure da Ɗan Sarkin Abuja shi kaɗai ake haska wa a TV wllh"

"Wace Hooriyah'n, Hooriyah tamu dai"

"Umma wadda kika sani mana, ta gidan yaya"

"Ban gane Aure ba Sulaiman Aure wanda na sani?"

"Shi Umma"

"Kace ɗan gidan wa"

"Ɗan Sarki"

"Dan Sarki kuma? A ina ta samo shi? Kai kuma da zaka aure ta fa?"

"A Abuja da suka tafi mana. Wallahi Umma bari in nuna Miki a facebook na gani yanzu naki yarda ina shiga gidan Abdul naga ana haskawa ko zama banyi ba na taho sanar dake"

"Kan Uba Ni yaya zaici amana yayi mata Aure bai sanar dani ba, sai faɗi tashi nake yi dan ka Aure ta, ita kuma matar nan algunguma aiko ita ma sai nata Auren ya mutu" ta faɗa tana miƙe wa

"Wace Mata Umma?"

"Ba ruwan ka" tace tana shiga ɗaki mayafi ta ɗauko tana ce masa

"Ka jira Ni yanzu zanje in dawo"

"Ina zaki kuma" ya tambaye ta

"Auren wata zanje kashe wa" ta faɗa tana fice wa da sauri



Gidan Noor ta nufa dama ta sa an nemo mata shi saboda irin wannan rana a buɗe ta tarar da gidan tana zaune a palour kamar kullum da tagumi ba sallama ba komai kawai ta banka kai tana cewa

"Ashe kin san Hooriyah wani zata Aura shiyasa kika shirya wannan manakisar?"

"Kamar ya kenan? Ce miki aka yi ina da Haɗi ne da ita" ta ce tana watsa mata wani kallo

"Ban sani ba, kamar yadda Sulaiman ya rasa Hooriyah kema sai na kashe miki naki auren"

"Ai aure na mutu ka raba takalmin kaza, ke a wa da zaki raba wannan auren" ta faɗa tana jin kanta On top Nan suka cigaba da musuyar yawu tare da tonawa kansu asiri kowa tana sai ta ɗau mataki.



Turo Kofar Palour akayi a firgice Noor ta kalli kofar bata yi tsammanin kowa zaizo gidan a wannan lokacin ba shigowar Zaaheed ne ya sata shiga tashin hankali addu'a ta fara a ranta Allah yasa baiji abinda suke tattaunawa ba ƙara so wa kusa da su yayi sannan yace
"Kin kyauta Noor kije gida na sake ki, ke kuma kije ke da Allah shi zai mata sakayya akan sharrin da kika yi mata"

Ko a jikin Aunty Safiyya dan haka take so, Noor ce ta ɗora hannu aka tana cewa "wallahi Yaya ba abinda kake tunani bane ka tsaya nayi maka bayani"
Ko Ni takan ta baiyi ba ya shige ɗakin sa juyo wa tayi gurin Aunty Safiyya
"Allah ya isa na muguwa kin kashe min Aure"

Dariya ta saki "ai dama nayi alƙawari indai Sulaiman bai auri Hooriyah ba kema sai na raba ki da Auren ki, anyi biyu babu kenan dan bazan dau asara ni kaɗai ba"

Taho wa tayi kanta gadan-gadan da sauri taja baya
"Allah ya kiyaye da ina yarinya ma banyi wannan rayuwar ba balle yanzu da girma na, aje aji da idda da gabzar gidan Baba" ta faɗa tana hararar ta tare da fice wa ranta fesss ko banza itama ta rasa mijin sun zama ɗaya da Sulaiman bata zame ko ina ba sai gidan su Hooriyah.

Lokacin data isa gidan babu kowa shiru gidan a palour kawai ta zauna tana jiran mutanen gidan su fito bata wani jima ba sai ga Aunty ta fito daga ɗakin ta zama tayi tana Facing ɗin ta fuskar ta fess bata nuna komai ba

"Safiyya yau kece a gidan namu da rana tsaka"

"Nice kamawa tayi zuwan, da fatan wanda nazo gurin sa Yana nan"

"Yaje ɗaurin Aure bai dawo ba"

"To bari in jira ya dawo" ta faɗa tana hararar Aunty. Ita ma tashi tayi ta bata guri dan tun lokacin da suka samu labarin ita ta raba auren Hooriyah take jin ba daɗi a lokacin taso Daddy ya barta taje mata da ƴan sanda an kama ta amma yaƙi, bata da lokacin raba hali yanzu ga ƴan ɗaurin Aure da zasu dawo kar a shigo da ɓaki taji kunya dan Safiyya ko a jikin ta indai abin kunya ne.



Har bayan Uku tana zaune jiran shigowar Daddy amma babu shi babu alamar sa ga matan gidan yau iskanci suke ji ko ruwa ba'a kawo mata ba tashi tayi ta ƙara duba ƙofa a karo na barkatai ko zasu shigo sai ga ƙarar Horn ɗin su wata bahaguwar ajiyar zuciya ta sauke fita tayi ta tsaya a ƙofar palour yadda yana shigowa zaici karo da ita suyi Maganar da zasu yi ta wuce suna parking ya hango ta bai kawo komai a ransa ba ya fito ya ƙara so kusa da ita

"Yaya sannu da dawowa tun ɗazu nake jiran dawowar ka" ta faɗa tana tsugunawa ƙasa
"Ina wuni, fatan mun same ku lafiya"
Shi abin ma dariya yaso bashi Safiyya da ko abu tazo nema bata tsuguna wa ta gaishe sa amma yau har da tsuguna wa

"Tashi mu shiga daga ciki Koh" ya faɗa yana wucewa

Dariya Khaleel dake kallon su ya kwashe da ita Abduljawwad ne ya juyo yana cewa "lafiya" "yaya wani abin dariya na gani, Aunty Safiyya ce da durkusawa yau dan zata gaida Daddy"
"Ina ruwan ka, in ta hango ka fa ga jama'a tazo tayi ta rashin mutunci, ka wuce muje" ya faɗa yana nuna masa hanya. Sim-sim ya shige girgiza kai kawai yayi shima ya bishi.



A cikin palour kuwa Aunty Safiyya ce zaune a ƙasa Daddy yayi yayi da ita yau ta hau kujera amma taƙi tace gaba yake da ita yana sama tana sama ai ba zai yiwuwa ba dole ta bashi girman shi {😂😝}

"Yanzu yaya sai ka Aura wa Hooriyah wani bare bayan kasan Sulaiman yana sonta" ta faɗa tana share kwalla

Kallon ta ya sake yi shi ya rasa abinda zai faɗa ma tun da ya shigo take share masa hawaye can sai yace "Ke yanzu Safiyya baki ji kunyar zuwa gida na ba, har da wani zancen Sulaiman kike?"

"Yaya dan zanzo gidan ka sai inji kunya sai kace wadda tayi wani abu" cewar Aunty Safiyya

"Bari kiji yau duk abinda kika yi wa Hooriyah an sanar min na sharrin da kika yi mata, na ɗauka ko wani kika ji ya fadi haka zaki yi masa faɗa Hooriyah ƴar kice amma baki ɗauke ta a matsayin dana ɗau Sulaiman ba. Ki tashi ki bar kin gida bana son na ƙara ganin ki balle ƴaƴan ki a cikin gidan nan"

A firgice ta kalle shi dan bata yi tsammanin abinda tayi zai dawo kunnen sa ba "wallahi Yaya ba haka bane Sulaiman na matuƙar son Hooriyah, sharrin Shaidan ne kayi haƙuri nayi nadama"

"Haƙuri! Safiyya hakuri kike so nayi to bazan haƙura ba ki bar min gida yanzu" ya fada yana fita daga Palour.

Ji take kamar ta kurma ihu ko zata ji sassauci a zuciyar ta bata yi tsammanin zai samu Labarin ita ta rusa auren ba gashi yanzu ta Auri wanda basu taɓa harsashe ba ina zata saka kanta ita Safiyya dama shine yake taimaka mata yanzu yace babu shi babu ita Sulaiman ba wani abin arziki yake yi mata ba shima wani lokacin ita ke taimaka masa. Da kyar ta tashi ta nufi gidan ta dan ji take kamar zazzaɓi ya kama ta.

*Dama Hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi dai-dai da kai. yanzu wa gari ya waya?*



💫💦🖤


ABUJA


Sajeedah ce ta turo ƙofar ɗakin a kwance ta tarar da ita tashi tayi ta zauna ganin Sajeedah ce ta shigo da sauri ta ƙara so kusa da ita rungume ta yi bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana jin tausayin ta sosai. Ɗago ta tayi daga jikin ta ganin fuskar ta da hawaye yasa ta ce mata " me ya faru Aunty?, Ko wani ne ya mutu?"

"Kukan daɗi nake Hooriyah, Yau dai Allah yayi Hooriyah Aunty ta zama Amarya" ta faɗa tana share hawayan

"Amarya kuma, like how?"

"Yes kamar yadda kika ji"

"Ban gane ba Aunty"

"Zaki gane ne soon, ki shirya zamu bi Flight ɗin 6 zuwa Kano, gobe zamu dawo" ta fadi tana tashi tazo buɗe Ƙofa ta ƙara ce mata

"Kano kuma? Kuma gobe mu dawo"

"Kin fiya tambaya fa, ki bari in munje zaki ji komai ai"



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/31, 10:01 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡




Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I




بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟕&𝟓𝟖


Second to the last Page



————————————————————————————————————————



A bangaren Kareema kuwa ƴaƴan ta ta zaunar su bata shawara yadda kowa zai yarda da ita a gidan a daina zargin ta Shawara ta gari suka bata ta fara zama da kowa lafiya a gidan ba tashin hankali.



🤍💥🖤


Suna sauka daga Airport direct gidan Daddy suka yi gidan cike yake da ƴan uwan ta da matan yayyanta da ƙannen ta gaisawa suka yi ta shige ciki ba wanda yayi mata Allah ya sanya alkhairi dan duk sun san bata sani salla tayi ta kwanta ba jima wa sai ga Khaleesat ta kira ta sun daɗe suna waya sannan ta katse cigaba da kwanciyar ta tayi dan babu abinda zata yi.


Gurin goma sai ga Aunty ta shigo sai a lokacin suka gaisa dan da suka zo bata nan ita da Mami suna part ɗin Daddy. Ce mata tayi tazo inji Daddy sai da taji wani iri dan indai ba magana nace mai muhimmanci Daddy baya yin ta da daddare sai da safe tashi tayi suka tafi.

A palour ta tarar da duka Yayyan ta da Mami suna gurin Daddy gaishesu su tayi bada ɓata lokaci ba Daddy ya fara magana da cewa
"A'isha"

"Na'am Daddy" Tunda taji ya kira sunan ta ta faɗa kanta a ƙasa

"Menene matsayi na a gunki" ya faɗa

Maganar taji ta wani iri amma ta daure ta amsa da "Daddy Kaine Mahaifina"

"A'isha na zaɓa miki kuma kika karɓe shi Allah bai yi za'a yi auren ba yanzu ma mun ƙara zaɓa miki wani har mun Aurar da ke yau"
Wani dumm taji kanta yayi "Aure Daddy yace sun min fa" Waye Mijin? Sulaiman mana zuciyar ta ta bata "kai ina Daddy ba zai taɓa aura min Sulaiman ba" ta bawa kanta amsa ji tayi Daddy ya cigaba da cewa

"A'isha kibi mijin ki sau da ƙafa, kinga duk ƴan uwan ki kowa yana zaune lafiya a gidan sa kece babba acikin su amma sai yanzu Allah yayi naki auren kar inji kar in gani A'isha"
Nan su Mami da Aunty ma suka yi mata nasiha Yayyan ta ma haka. Ta yiwa Daddy alkawarin zama da duk wanda suka zaɓa mata a matsayin miji.


Washegari
Ba wani taro suka yi ba ƴanuwa da abokan arziki ne kawai suka zo sukuku ta yini tana ɗaki sai da rana ne ta fito da aka kira ta da yamma aka shirya amarya da duk wanda yake son zuwa ta sha kukan rabuwa da su.

Tsaya wa faɗa muku tsarin gidan ma ɓata lokaci ne kyawun sa da tsaruwar sa ɗakin ta aka kaita dan Ammi tace a barta gobe sa so gaishe ta yanzu ta huta. A nan gidan Amarya suka kwana washegari zasu yi bikin su a nan da safe suka shirya ta suka kai ta gurin mai martaba sannan aka wuce da ita gurin Ammi suna tare da Mommy da wasu daga cikin matan gidan sun karɓe su an musu tarba ta mutunci sun dau Amanar ta da alkawarin kula da ita. Da rana yini suka yi da daddare aka yi dinner dole anan dangin amarya suka ƙara kwana ba dan sun so ba washegari da safe suka wuce, ita kadai suka bari har lokacin bata san waye mijin ba.



💃💥🥰


Bai shigo gidan ba sai ranar da daddare tunda aka ɗaura auren ya bar gidan ko dinner da suka yi bai je ba iya mata kawai suka yi kayan su.

Yana shigowa direct part ɗin Ammi yayi ba abokin daya rako shi bashi da abokan ma balle su rako shi bata palour sai hadimar ta kawai ya tarar shiga yayi nasiha tayi masa sosai tare da addu'a har kwalla sai da yayi duk da ba barin gidan zai yi ba part ɗin sa yana gidan sai da ta kore shi sannan ya tafi.


Zaune ya tarar da su a ɗaki ita da su Husna ne Sannu da zuwa suka yi masa sai Zainab ta cewa
"Yauwa Yaya dama kai muke jira mu tafi, sai da safe"
Raka su yayi yana kulle kofar ya dawo tana nan zaune alwala ya sata tayi salla raka'a biyu suka gabatar,addu'a mai tsaho suka yi ta neman alkhairi da samun zaman lafiya da haduwar kai a tsakaninsu sannan ya waiwayo ya kama kanta ya karanto addu'ar da annabin rahama ya koyar da mu
'' *Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa a uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi*'',da salatin annabi ya rufe musu suka shafe tare.


Noor


Bata nufi ko ina ba sai gidan su Zaaheed kuka ta sawa Mommy wai ya sake ta bata san laifin da tayi masa ba. Mommy waya ta ɗauka ta kira shi yana zuwa ya sanar mata da abinda yaji suna tattaunawa da Aunty Safiyya Salati Mommy ta saki tana cewa

"Yanzu dama Noor ke kika kitsa abin nan duk irin ƙaunar da nake Miki amma kika yi haka"

"Mommy wllh Sharrin Shaidan ne baza sake ba ki bashi hakuri ya maida Ni dan Allah"

"Kinci gidan ku Noor ai ko Zaaheed bai sake ki ba ni nace ya sake ki, baki kyauta ba Noor kika sa na daga hankali na har sai da aka fasa Auren"

Nan tayi ta mata faɗa da taga kamar ba ɗauka take ba tace ta shirya ta koma gidan su. Sati ɗaya da haka Mommy ta samu Abiee da maganar a nemo wa Zaaheed Auren Hooriyah ta yarda yanzu ya aure ta, ta gane ba laifin ta bane nan yake sanar da ita bakin alkalami ya bushe yau satin ta ɗaya da aure.


Sai da Zaaheed yayi gurin shekara yana jinyar rashin Hooriyah da kyar ya samu wata Rukayya ya aura ita ma student ɗin sa ce tare suka yi Graduating da Hooriyah ta daɗe tana sonsa amma yaƙi amince wa duk da bata kai Hooriyah ba amma ya haƙura haka ya Aure ta tana da ladabi da biyayya yarinyar bata da rashin ji.


Noor kuwa tunda Mommy'n ta taji abinda tayi ta ɗauke mata wuta babu ruwan ta da ita ga gida ɗaya suke kwana su tashi amma bata shiga harkar ta ko ta gaishe ta bata amsawa gurin wata biyu suna haka da Abban su yaga ba zasu shirya ba ya Aura mata ɗan Abokin sa Junaid. Junaid dan shaye-shaye ne na gaske dan har Cocaine yana sha idan ya bugu ya kamata ya zane dama shi ba sonta yake ba dan kawai kar ya musa wa mahaifin sane ya sa ya aure ta ta sha wahala a gidan sa Daga baya Auren ya mutu tayi nadamar abinda tayi ga Zaaheed ya mata nisa ko gidan su taje Mummy da kyar take kula ta.


🤍💥🖤



Five Months later

Zaman su suke lafiya ita da mijin ta ba wanda yake jin kansu ko saɓani suka samu anjima zasu sulhunta kansu ba tare da wani yaji ba Sajeedah tana leƙo mata lokaci lokaci sau ɗaya taje gidan Yaya. Bata taɓa zuwa Kano ba kullum tana masa naci amma sai yace ba yanzu ba sai wani lokacin haka ta haƙura sai dai suyi waya.


Kareema kuwa Tunda aka kawo Hooriyah ta zama ta gurin ta, Tsakani da Allah take sonta jinta take kamar su Husna so take duk laifin da tayi wa Ammi ya goge saboda kyautatawar da take wa Hooriyah dan tana sonta Addu'ar ta ta karɓu dan Ammi ta yafe mata tuntuni yanzu zamansu suke lafiya ba wani kishi sai dai dan kaɗan da ba za'a rasa ba. Ko abu Hooriyah take so kai tsaye take tambayar ta dan tana jin nauyin Ammi ba komai take tambayar ta ba kowa a gidan yana son Hooriyah bata da matsala da kowa..................✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡




Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟗&𝟔𝟎
________________________________________________________________________________________


Anisah


Tunda ta rasa ƙafa take halin wuya watan Amaryar sa shida da Aure mahaifin sa yayi accident ya rasu ya shiga tashin hankali sosai bayan anyi rabon gado ƴan fashi suka shigo duka suka yi musu suka tafi da kuɗi da Amaryar sa. Ya rasa idanun sa gaba ɗaya biyun. Sai daga baya suka gane ita ce ta turo su da kyar aka kamo su aka kulle. Ga Mommy su ba iya kula da shi take ba tsufa ya kamata dole dai sai Anisah ce take kula da shi kullum sai yayi kukan kuntata mata da yayi bayan yayi aure ga neman Hooriyah da yake ruwa a jallo ya bata haƙuri ko zai samu sauƙin Ƙaddarar da take ta afka masa.



Aunty Safiyya


Ta shiga rayuwa mai wahala da kunci Sulaiman ɗin da take yi wa fafutukar neman Aure ya guje ta tunda bata da abinda zata bashi yanzu da kyar aka shawo kan Yaya ya yafe mata kowa yaje gurin sa sai yace babu shi babu Safiyya in suka dage sai ya sanar musu da abinda tayi duk ƴan uwa duk wanda yaji abinda tayi sai yace ba ruwan sa sai da ta Ringa haɗawa da ƴan unguwa wajen zuwa neman yafiya Sannan ya haƙura.



✨💕✨💕✨



Two Years Later




Abubuwa da yawa sun faru ciki harda zaman Arshad Sarki, Mai martaba ne yayi murabus tsufa ya kama sa ya kamata ya huta duk da baya so haka suka tilasta masa ya karɓa. Allah ya albarkace su da ƴan biyu masu kama dasu lokacin watan sa biyu da zama Sarki, ɗaya kamar Hooriyah sak komai nata ta ɗauko ɗayar kuwa kamar ta ɗaya da Arshad mai kama da Hooriyah aka saka wa Abeedah ita kuma mai kama da Arshad suka sa mata A'isha yana so tayi halin Hooriyah, Abeedah suna kiran ta da Minha ita kuma A'isha suna ce mata Mirha yanzuwatan su Uku a duniya.



Sun taɓa haɗuwa da Zaaheed a Abuja yaje wani meeting ita kuma sun fita Arshad lokacin bai zama Sarki ba anan yake sanar da ita sun rabu da Noor da abinda ya faru da shi ta tausaya musu matuƙa har ya haɗa ta da matar sa suka gaisa ta gane ta sarai lokacin da yace yana sonta har zuwa ja mata kunne tayi akan ta fita a harkar Zaaheed ashe itace matar sa a yanzu taji kunya lokacin da ta tina abinda tayi tace mata ba komai ya wuce ai.



💦✨💦✨💦✨



A shirye take cikin atamfa riga normal doguwar riga, tayi lite make up feshe jikinta da turaruka masu dadi tayi, ta daura dankwalinta bayan ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici, haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar, ba qarya ta mata kyau matuqa, motsi ta jiyo a palour tasan shine ya dawo, cigaba da tsaya wa tayi gaban madubin ba tare da ta zauna ba, turo ƙofar aka yi harshen nata ya tabbata Shine ya dawo tsayawa yayi yana kallon ta dan tayi masa kyau sosai ƙaraso wa Yayi ta rungumeta ta baya
"Kinyi kyau sosai" ya rada mata a kunne

Murmushi ta saki "Barka da dawowa, ka dawo lafiya My" ta faɗa muryar ta ƙasa-ƙasa

"Zanyi missing ɗin ki in kika tafi, anya ba zaki fasa tafiyar nan ba"

"Haba sai kace wadda ba zata dawo ba, Just ten days fa zan yi in dawo" ta faɗa a shagwaɓe

"Yayi nisa Habibty, ko One week kika yi ya isa"

"Sau ɗaya fa naje Kano tunda nazo Abuja, Mi Amor ka taimaka Please" ta faɗa tana juyo wa tare da kama kunnen ta, shiru yayi mata an ta cigaba da cewa

"Allah zan faɗa wa Ammi da Mommy ince ka hana tafiyar" ta faɗa tana diddire ƙafa

Zaro ido yayi yana cewa"Ammi fa a'a sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo mun daku lafiya"

"Ameen ya Allah, muje kayi wanka" ta faɗa tana wuce wa Toilet. Binta yayi a baya...



Washegari Jirgin Asuba tabi suka nufi Kano ita kaɗai sai Mirha da Minha sai hadimai guda Uku ta tafi. A gidan ta dake Aminu Dabo Road ta sauka gida ne mai kyau da ya tsaru in ka shiga ciki sai ka zata ba'a Nigeria kake ba.

Ko su Mami bata sanar musu da zuwan ta ba bayan La'asar ta shirya ta nufi gida sunyi murna sosai dan rabon su da ita anfi shekara sai gurin Sha ɗaya ta tafi. Da safe gidan Khaleesat taje ta ƙara haihuwa tana son ganin Baby kafin ta koma goma ma a can tayi mata anan ne Khaleesat take ƙara bata labarin halin da Anisah take ciki.

"Wllh Hooriyah Rayuwar Anisah Abun tausayi yanzu bata da kowa, danaje na ganta sai da nayi mata kuka tana halin rayuwa" cewar Khaleesat

Nisawa tayi sannan tace"Allah sarki Anisah, yaushe ya kamata muje gurin ta kafin in koma"

"Duk lokacin da kika shirya amma ki fara sanar wa mijin ki sannan mu tafi"

"Bani da matsala da shi Khaleesat ko da yamma in kin shirya ma je"

"Allah ya kaimu bari in sanar da Abban Fadil kar ya dawo bama nan" ta faɗa tana ɗauko wayar ta kiran sa tayi ta sanar masa. Hira suka cigaba da yi anan ne ma take sanar da ita bikin Zee ƙawar su daya rage saura kwana Ashirin tayi mata murna sosai.


Ko da suka je gidan Anisah sai da tayi musu kuka ganin halin da suke ciki duk kyan nan na Zaid yanzu babu ya zama wani iri Maman sa sai kuka take duk da bata taɓa ganin Hooriyah ba sai yau tana jin labarin ta a gurin su da halin da suka saka ta. Bata taɓa tsammanin haka zai faru da Anisah ba da tini itace a wannan Rayuwar. ta yafe wa kowa a cikin su duk laifin da suka yi mata Allah ya yafe musu baƙi ɗaya. Da zata tafi tayi musu kyauta sosai da alkawarin zata ringa turo wa ana kula da su koda bata zo ba.


Tako ina rayuwa tayi mata dai-dai. A kullum gode wa Allah take daya bata miji kamar Arshad samun irin sa a wannan zamanin sai an tona gani take tafi kowa Sa'ar Miji a duniya. Ko yaushe yana jin matsalar ta baya son kukan ta ko gani yayi bata da lafiya shima zaka same sa sukuku kamar shine mara lafiyar. Taje duk gidan ƴanuwan ta har gidan Aunty Safiyya sai da Daddy ya tilasta mata zuwa. Kwanan ta goma cif ta koma Abuja dan tayi missing ɗin mijin ta.


Tammat Bi Hamdulillah🥰🔥


Godiya Ga Allah SWT daya bani Ikon Kammala wannan Littafin.


Ya Allah ka tsare mu da cin amanar wanda suka aminta damu Allah ka haɗa mu da Abokai na gari👏


Saƙon godiya zuwa ga Hooriyah fans, Fateyzahraah Fans group & WhatsApp Channel Allah ya bar Kauna Allah ya haɗa mu a Aljanna Firdaus💋 Nagode da Kauna da Kulawa.


Nainarh Kd, Nanameera, Aunty Amal, Ummeta Sannun ku da ƙoƙari😍



Saƙon Jinjina ga
Ammi Hisham
Aunty Amal
Aunty 40
Issy's Cuisine
Ummi's Makeover
Zarah
Chouchou
Babyn Daddy
Fauziyya Hashim
Lubabatu Muhammad
~Shukura
Her Xcellency
Dama waɗanda ban lissafo ba Sannun ku da ƙoƙarin Comments da Like Nagode ƙwarai.


Ku kasance sani bayan Sallah da sabon Littafi na mai suna *Sune Silar Ƙaddara* Paid Book ne.💕 Nice dai takun nan Fatima Intisar Abdulhadi ◎Fateyzahraah◎
Thank You So Much💋



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯




Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da

Please Login or Register in order to submit comment