Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

الله الرحمن الرحيم





𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️











𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟗&𝟐𝟎







𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯





✫✫✫✫





An sallame su daga asibiti bayan Magariba lokacin da suka dawo ragowar mutane kaɗan ne duk an watse sai Yan gidan su da basu tafi ba kowa sai sannu yake mata.Zama tazo yi Aunty ce ta riƙe hannun ta"Tashi mu shiga ciki ki huta" tashi tayi ba dan taso ba suka shiga cikin ɗakin wayar ta ta janyo zata kunna Aunty tayi saurin karɓe wa "Me zaki yi da ita"

"Kunna wa zanyi mana"

"Kwanta ki huta sai gobe zaki kunna"

"Aunty bazan da ɗe ba zan kashe Anisah kaɗai zan kira please"

"Har kina da lokacin kiran wata Anisah kenan yarinyar da taci amanar ki" "Ai kinji kashe ɗin doctor yace karki zauna da damuwa shine zaki kira ta, ta ƙarasa kashe ki, kwanta maza" kwanciyar tayi gyara mata bargo tayi ta kashe wutar ɗakin ta fice. Fitar ta baifi da minti biyar ba ta tashi zaunawa tayi ita fa har yanzu bata Yarda zasu iya cin amanar ta ba mutan en data fifita akan kowa tana ƙaunar su tsakani da Allah amma sunci amanar ta "Ya Allah dama mafarki nake, bazan iya jurewa ba, Ya Allah kasa min dangana" haka tayi ta maganganu ita kaɗai.



₍ᐢ⑅•ᴗ•⑅ᐢ₎♡



𝗚𝘂𝗿𝗶𝗻 Ɗ𝗮𝘂𝗿𝗶𝗻 𝗔𝘂𝗿𝗲🤸



Bayan An daura Aure Mutane sai zuwa suke gurin Ango yin Allah ya sanya alkhairi, Yawancin mutane basu gane an Chanja sunan Amarya ba Abokansa ne na kusa suka gane Auwal ne ya janyo shi gafe "How Comes, Naji an canja sunan Amarya" "Zan maka bayani daga baya" kawai yace ya tafi. Sallamar mutane suka ƙara sa yi sannan ya suka tafi gidan su Amarya...



𝐆𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐬𝐮 𝐀𝐦𝐚𝐫𝐲𝐚...



Amarya ta sha kwalliyar ta tayi kyau kamar ba gobe suna zaune a ɗaki tare da ƴan uwanta sai bata gayyaci ƙawaye ba kwata kwata. Yan uwansu sai san Barka ake mata ta Aure Mai kuɗi ba'a daɗe da ɗaura Aure ba ango yazo aka sha hotuna suka tafi. Basu jima da tafiya ba sai ga su Rukayya sun zo su biyar shigowa suka yi ba sallama ba komai sai cewa Zainab tayi "Ina Amaryar take" wata tsohuwa ce tana daga zaune tace "Ke ko ƴar nan lafiya kike mata wannan kiran" "Baba ba gurin ki muka zo ba gurin Maciya Amana muka zo" inji Khaleesat. Kallo kansu duk ya dawo.

Tana daga ɗaki ta jiyo su gaban ta ne ya yanke ya faɗi "Innalillahi wainnaillaihir rajiun, na shiga Uku Ni Anisah, na janyo wa kaina matsala" tashi tayi ta fito gurin su "Ya na ganku a haka ku shigo ciki mana" Wani kallon banza Rukayya ta watsa mata "Ba zama ya kawo mu ba, ke in banda abinki ai kin san munfi ƙarfin zama anan Koh" "Ke dan Allah baki ji kunyar abinda kika yi ba, ki rasa wa zaki ci Amana sai Hooriyah yarinyar data taimaka Miki, kin san dukkanin mu munfi ƙarfin kula ki amma saboda da ita muka kula ki ta fifita ki akan kowa da komai amma kika Aure mata wanda zata Aura" "Ki rubuta ki ajiye sai Allah ya saka mata ko badaɗe ko ba jima, sai anjima" suka juya zasu tafi tsohuwar ɗazu ce ta ƙara magana "Yaran nan bamu gane inda Maganar taku ta dosa ba, ku dawo kuyi mana bayani" "Tsohuwa ki kama kanki, wadda muka bawa sako ka gane inda muka dosa, ita da Uwarta zasu iya yi muku bayani dalla dalla" Zainab ce mai wannan jawabin suka yi fice War su. Baki ta kama sai ta kalli Anisah "Ai sai ki yi mana bayani kamar yadda suka ce Koh" juyawa tayi ba tare da tace komai ba ta shige ɗaki. "Ke ai Sai kiyi mana bayani Koh" ta faɗa tana kallon Umma "Iya ƙyale su ina ganin bata suka yi, Anisah da bata da Ƙawa ko ɗaya, Sharri ne kawai dan anga tayi Aure kinsan halin mutane"

"To Allah ya sawwaka". Nan aka fara tsegumi ƴan unguwa wanda suka san su Zainab suna ta magana Amma Umma tayi biris tace basu san su ba dan Haka a boye ake maganar.

Bayan magariba aka kai Amarya ɗakin ta gida ne na Alfarma aka kaita nan fa zance ya ƙara tashi da gaske Auren cin amana tayi tunda aka ga gida wasu sai cewa suke basu taɓa ganin ta tana zance ba Amma gashi Auri Mai kuɗi. Nan aka dawo ana ta zancen ta.



✦✦✦



Bayan Kwana Uku

Kwance take akan cinyar Mami kalba take mata a hankali kuma tana mata nasiha Aunty ce ta shigo "Har kin dawo, ashe ba daɗe wa zaki yi ba" "Ina zan dade na bar ƴar lele ba lafiya" dariya suka yi gaba ɗaya "Aunty ai Naji sauki, Ya hanya" "Ai haka ake so, Hanya Alhamdulillah, Fasa kwana nayi nace gwanda in dawo kawai" "To Masha Allah, ai na zata sai gobe" "A'a Wallahi" "Naji daɗi da kika rungumi ƙaddara gashi har kin ware" "Aunty ai hakan yafi min, Abinda kafi so sai kaga ba alkhairi ne a Rayuwar ka ba" "gaskiya Hakane, To Allah ya baki wanda ya fishi" "Ameen ya Allah"tashi tayi tace bari ta shiga ciki ta huta.



Tunda aka fasa Auren Mama take sintiri Sulaiman yazo su sasanta tunda ta rasa wanda zai Aure ta duk ta zama wata iri duk sanda Mama zata zo sai ta taho da mutane wai a ganta ta rasa wanda zai Aure ta kuma taki yarda da ɗan uwanta wannan abinda da take mata ne yasa ta yanke shawarar komawa gidan Yaya Abduljawwad da zama ba tare da ƴan uwan su sun sani ba. Tayi shawara da su Aunty kuma sun amince da Yamma zata tafi.





( ̄▽ ̄)~*



Zaune suke a Palour ita da Auwal tunda abin nan ya faru kullum jikin jajjanta wa suke yanzu ma maganar suke Khaleesat ce tace

"Wallahi Abban fadil kunyar Hooriyah nake ji ina zan iya zuwa gidan su" "Da wane ido zan kalle ta Ni nayi ta convincing ta kula Zaid da kyar ta amince amma ya watsa mana kasa a ido"

"Duk kunyar ta da zaki ji ai baki kaini ba, kawai ki kirata muji tana ina mu bata hakuri, Ni fa duk laifin na nake gani da banzo da Zaid gurin Biki ba ai ba zasu haɗu ba har haka ta faru"

"Bari in gwada in ji ko zata ɗaga dan bana tunanin zata ƙara kula Ni" wayar ta ta ɗauko ta kira anci Sa'a tana kusa da wayar ɗagawa tayi wata nauyayyar ajiyar zuciya Khaleesat ta sauke "Ummu Fadil ya da haka, baki da lafiya" shine abinda ta faɗa "Ai dole in Sauke ajiyar zuciya Hooriyah na zata bazaki ɗauki waya ta ba" "Me kika yi min haka da zafi" "in munzo kyaji, yaushe zamu same ki a gida"

"Yaushe kika fara tambayar appointment in Zaki zo gurina"

"Sorry, mu bar zancen wasa yaushe kike gida"

"Kizo ko anjima ne, amma karki kai yamma zan fita"

"Ga amsa ta nan ta fito zaki fita, sai munzo" ta kashe wayar.

"Ga ba shi ba da kika kira ta, tashi ki shirya mu tafi" tohm tace ta shiga ciki.

Bayan Azahar suka zo sun samu tana nan bayan sun gaisa suka yi ta bata hakuri akan abinda ya faru tace ba komai basu suka janyo ba nan take sanar da Khaleesat yau zata koma gidan yaya Abduljawwad da zama......✍️





Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



Follow My Pages



Arewa Books: fatimaintisar1


Wattpad: fatimaintisar1




#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯





Please Share & Comments 🙏





𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽



𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



тԋє ɯɾιтєɾ σϝ


*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم





𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟏&𝟐𝟐





𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝚐𝚘𝚍𝚒𝚢𝚊✯




𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝐝𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐇𝐨𝐨𝐫𝐢𝐲𝐚𝐡 𝐅𝐚𝐧𝐬 ❣ 𝐊𝐮𝐲𝐢 𝐲𝐚𝐫𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐤𝐞 𝐬𝐨 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐢. 𝐌𝐮𝐜𝐡 𝐊𝐚𝐮𝐧𝐚❤❤❤





✫✫✫







Bayan magariba ta shirya tsaf shi kaɗai take jira yazo su tafi tun yamma tace zata tafi yace ta jira shi shiyasa duk a ƙage take su tafi sallama akayi da sauri ta amsa "Kai Hooriyah, duk azarbaɓin tafiyar ne" inji Aunty dariya Khalil ne ya sheke da dariya "Allah Sis kin cika zumuɗi, sai kace wadda baki taɓa zuwa ba"



"Ba zaka gane bane, amma na gaji da zama anan" "Gwara in tafi kafin gobe tayi taxo ta saka Ni a gaba, Aunty ko ƙara kiran sa sanyi"



"Tunda yace ki jira shi ai zai zo Koh"



"Wa ake jira ne" cewar Yaya Abduljawwad "Har Naji daɗi" sallama yayi ya shigo "Wai wa ake jira"



"Ga ta nan kai take jira tun ɗazu" inji Mami, Khalil ne yace "Yaya Kasan tun ɗazu ta gama haɗa kaya kamar ta tashi sama take ji ta tafi" ya saka dariya. Gaisawa suka yi da su Mami sai ya shige part ɗin Daddy sai gurin tara ya fito lokacin har ta kwanta a Palourn Khalil ne ya tashe ta "Ashe har kin yi bacci"

"Tunda kaƙi fitowa shiyasa na kwanta, dan kaga ina son zuwa sai wulakantani kake"

"Ni na isa in wulakanta ki, ta shi mu tafi" tashi tayi tana yiwa su Mami sallama suka fice Khalil ne ya ɗauko mata akwatin ta har baƙin mota ya rako su yana ta tsokanar ta wai ta guje su

"Allah Khalil ka raina Ni da yawa"

"Ni na isa in raina Yaya ta, yaushe zaki dawo"

"Tun ban tafi ba har ka fara tambaya, sai nan da wasu watanni"

"Kin san zanyi missing ɗin ki da yawa"

"Da yake gida ɗaya muke Koh, yaya muje Ni ya ishe Ni da surutu, Kanin Good Night ka gaida Adeel da Mama sa"

"Zasu ji, har kin gaji da Ni, ku gaishe da mutan gidan"

"Tohm" tace, rufe musu kofar yayi yana cewa "Yaya sai da safe" "Allah ya tashe mu Lafiya" yace yana kunna motar suka tafi...



Baifi minti talatin ne ya kaisu gidan suna shiga gaisawa kawai suka yi tana ta yi mata tsiya ta saka ta girki kuma bata zo da wuri ba. Kare kanta tayi tayi da taga abin nata bana ƙare bane sai tayi shigewar ta Ɗaki ta kyale ta. Dan in ta zauna sai su kwana tana mita.

Duk cikin matan yayanta sunfi shaƙuwa da ita Sajidah tana da hakuri bata da hayaniya shiyasa tasu yazo ɗaya.







Bayan Sati Biyu





Lafiya ƙalau suke zaune bata da wata matsala yanzu shirye-shirye koma wa makaranta take yi.

Tun Asuba da ta tashi bata koma Bacci ba break fast ta haɗa musu duk da akwai masu yi amma tace ita zata yi bayan ta gama ta shiga ɗaki wanka tayi Shirya wa tayi Sea green Abaya ta saka da mayafi Golden tayi kyau sosai. Fito wa palour tayi nan taga duk sun fito suna zaune a dinning ita kaɗai suke jira

"Wow, Masha Allah irin wannan kyau haka, wannan ai sai ki rikita maza, Tabarakkalah"

"Anty Sajeedah Kenan ina abin yake, Good Morning" Kujera taja ta zauna Yaya ta kalla

"Yaya Good Morning"

"Morning"

Su Fudail ne Suka gaishe ta Amsawa tayi tana karɓar Batool a hannun Sajeedah karya wa suka fara. Da Sauri-Sauri tayi ta gama ta mike "na tafi, sai na dawo"

"Allah ya kiyaye hanya, Ki duba kan TV stand ki ɗau key"

"Ok Thank you" "Sai kin dawo" Tohm tace tana fice wa.





𝐁𝐔𝐊 𝐔𝐧𝐢𝐯𝐞𝐫𝐬𝐢𝐭𝐲 𝐊𝐚𝐧𝐨.





Shigowar ta makarantar kenan Parking tayi ta fito Kicibis suka yi "Sorry Sir" "Barka"

"Ahhh Bakomai, Barka kadai" "Ashe haka abu ya faru Allah ya baki wanda ya fishi" Ameen tace tayi saurin Wuce wa. Binta yayi da kallo.

Tafe take tana tunanin Ashe kowa ya san abinda ya faru amma da tasan haka ne da bata dawo makarantar ba kowa kallon wata iri yake mata kenan.





❥❥❥





Knocking ƙofar akayi Kallon kofar yayi "Come in" ya maida kansa kan abinda yake yi. Wanda yake ƙwanƙwasa kofar ne ya shigo neman guri yayi ya zauna "Zaaheed kai dai ba zaka Chanja hali ba Koh"

"Me kuma nayi ne" ya faɗa ya ɗagowa

"Ya wuce, kasan menene"

"Ya za'a yi na sani, Ni da ba sanin gaibu nake ba"

"Matsala ta da kai kenan, Da gaske ne fa zancen da muka ji"

"Wanne daga ciki?"

"Na Ba'a yi Auren A'ishah Harith ba, yau ma har mun gaisa da ita"

"Dan kun gaisa da ita Shine yake nufin bata da Aure"

"A'a baka gama jin zancen ba, ai har jaje nayi mata dan na tabbatar" dafe kai yayi

"Wallahi Naseer ka shiga uku, gulma kamar mace"

"Ai dama kace haka, Ni da nake so kaima kayi Auren nan" "Dan Allah wannan lokacin Karka ƙi faɗa mata kana son ta karta suɓuce"

"Da ai kai kasa nace ina son nata Koh"

"A'a Ni dai shawara ce na baka, karka yi sake sai anjima"

Tinani ya shiga yi akan maganar tasa dan gaskiya tunda ya fara ganin ta yaji yana son ta bai taɓa kamu wa da ƙaunar wata ba sai ita, Dole ya nemi mafita kafin wannan damar ta ƙara kufce masa...





****



Zaune suke a cafeteria hira suke tabawa Khaleesat ce tayi tsaki Zee ce tace Lafiya "Waccan Banzar na gani wallahi"

"Kace kema kinyi mugun gani" inji zee

"Wai wace ne haka" cewar Hooriyah

"Wace wadda ta wuce Anisah mana" Ruky ta faɗa. Zaram ta miƙe "Ina zaki kuma" ba tare da tace komai ba ta fice. "Abinda na guda kenan shi yasa ban faɗa ba wallahi" "Bari inje inga ina tayi" Cewar Khaleesat, Karɓar Fadil tayi ta bita.



Can ta hango ta zaune a cikin Mota Karasa wa tayi ta buɗe shiga tayi sannan tace "Meyasa kika taho, ai bai ka mata ki taho ba"

"Me zanyi in ban tashi ba nayi Wa kaina Alkawarin babu Ni babu ita, ko inuwa ɗaya bana son mu zauna"

"Abin ba daɗi amma da baki nuna kin ganta ba"

"Ai bata isa zuwa inda nake ba"

"Allah ya Kyauta" "Ameen". Hira ta ringa janta da shi har ta saki jiki Bayan wasu mintina suka fito suna da wata lecture.....







✰✰✰





𝐸𝑚𝑖𝑟'𝑠 𝑃𝑎𝑙𝑎𝑐𝑒 𝑨𝒃𝒖𝒋𝒂.





Motoci ne suke shigo wa cikin masarautar a tsare suke tafiya basu tsaya ko ina ba sai baƙin fada nan suka yi parking Buɗe kofar Motar ba faɗe yazo yayi "Allah ya ja zamanin yarima Barka da dawowa yarima" shine abinda fadawan suke ta faɗa Kusan minti ɗaya sannan Aka zuro ƙafa sai da ta ɗau wasu seconds sannan aka sako ɗayar kafar fito wa yayi gaba ɗaya Tunda ga Kallon Kafar sa Kaɗai Kasan Mamamlakin ta ya haɗu dogone ba shi da ƙiba sosai Kyakkyawa ne abin farko in ka gansa zaka yi tunanin Balarabe ne ya haɗu, ɗaga musu hannu kawai yayi ba tare da yace komai ba Cikin fadar suka shiga cikin takun izza...





**** **** ****



Zaune take akan kilishi ta kishingiɗe a cikin ɗaki ita kadai Kofar aka ƙwanƙwasa izinin shigowa ta bayar buɗe wa akayi aka shigo Amintacciyar Hadima ta ce zube wa tayi a ƙasa "Ranki ya daɗe Barka da Rana"

"Barka kadai" tace cike da izza

"Me yake faruwa a cikin gidan"

"Ranki ya daɗe ʏᴀʀɪᴍᴀ mai jiran gado ne ya dawo, daga gani kuma ya samu lafiya"

A zabure ta mike "Mai kike nufi da ya dawo, Jiya ma sai da muka yi magana da mai Martaba amma bai Sanar mun da dawowar sa ba".............✍️




𝐄𝐧𝐝 𝐎𝐟 𝐁𝐨𝐨𝐤 σɳҽ



Alhamdulillah Anan na kawo ƙarshen Book One sai mun haɗu a Book Two zan tafi hutu sai bayan sallah Idan Allah SWT ya Kaimu bayan Sallah Zamu cigaba.

Tafiyar mai nisa ce..



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



Follow My Pages


Arewa Books: fatimaintisar1



Wattpad: fatimaintisar1



#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯







Please Share & Comments 🙏





𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w




𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Ina yiwa ƴan uwa musulmai Barka da sallah da Fatan munyi Sallah Lafiya Allah ya karɓi ibadun mu yasa muna cikin ƴantattun bayi Ameen




بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟐&𝟐𝟑


————————————————————————————————————————


*Gidan Amarya*


Soyayyar su suke zuba wa basu da damuwar komai tun tana jin ɗari-ɗari har ta saki jiki da shi zaman su suke lafiya ƙalau.

Buɗe motar tayi ta fito cikin gidan ta shiga tass yake ba abinda yake tashi sai kamshi ba kowa a cikin palour sama ta haura. Zaune yake a palour aiki yake yi a system, a hankali ta fara tafiya har ta isa inda yake baiji shigowar ta ba. Rufe masa ido tayi,dafe idon yayi "Be cika min ido mana aiki nake fa"
Dariya ta ƙyalƙyale da ita
"Ya akayi ka gane Ni ce"
"Ai nasan babu mai wannan aikin sai ke"
Dariyar ta cigaba da yi tana dawowa kusa da shi zama tayi a jikin sa
"Kin tsorata Ni da yawa Habibty"
"Sorry Noory, Har ka dawo"
"Eh, Babie ya makarantar"
"Alhamdulillah duk ba daɗi ina ta kewar ka"
"Ba gashi kin dawo ba, fatan babu abinda ya faru"
"A'a babu komai, Kasan yau na haɗu dasu Hooriyah"
"Amma dai baki kula su ba Koh, dan nasan suna ta jin haushin mu"
"Ban kula su ba, in na kula su ai sai suyi min duka ko zasu hu ce Haushin"
"Innnnnnaaaaaa dako munyi Shari'a dasu kawai su dakar min mata, Ni fa ko sunan su bana son kina ambata haushi nake ji"
"An dai na daga yau ranka ya daɗe" anan ta cigaba da zama tana kallon sa yana aiki kiran sallah ne ya tashe su ɗaki suka yi yayi alwala ya fice ita Kuma ta shiga wanka tana fito wa tayi sallah ta tashi zata fice Wayar tace tayi ƙara dawowa tayi ta ɗauka ganin Ummanta ce take kira
"Umma na ina wuni"
"Fatan kuna zauna lafiya ba wata matsala"
"Babu Matsalar komai wallahi, lafiya ƙalau muke zaune"
"Masha Allah haka nake son jin, dan Allah ki bishi sau da ƙafa kar a samu matsala"
"Babu abinda zai faru Umma, yana sona fa"
"Allah yasa dai" "Ameen" nan suka cigaba da hirar su cikin nishaɗi da walwala.


*To dama ina za'a samu saɓa ni tunda yanzu kuka yi auren, har yanzu amarya ce fa😌*


★★★


Bata dawo gida ba sai Kusan Magariba Sajeedah ce kaɗai a palourn duk yaran basa nan neman guri tayi ta zauna tana yi mata ya gida ta amsa da lafiya lau
"My Only Anty Ina su Fudail"
"Yau kuma shakiyanci kike ji kenan sun fita da Abban su"
"Ba shakiyanci bane ba, kin san babu ya ke Babu ke ba kishiya, Shine basu jirani ba"
"Ai ko shi in ya faɗan haka nasan zolaya ce, Kun fi kusa da shi ai"
"Shikenan sa wasa, kin san in na faɗi Abu kamar shi ya faɗa Koh"
Nan take bata labarin abinda su Khaleesat suka yi ranar biki da suka je gidan su Anisah
"Kai amma basu kyauta min ba da sun sanar da Ni zasu ai sai nayi abinda yafi nasu" galala tayi tana kallon ta
"Ke dana kawo wa ƙara in sunzo kiyi musu faɗa"
"Wane irin faɗa za'a yi musu, ai kamata yayi da suka je sunci ubanta, ko ta gane Shayi ba Ruwa bane"
"Chabbbbb Ni dai banji daɗi ba wallahi, in tani ne ma da basu je ba"
"Ni Ko sun min dai-dai, da sun sanar dani dana raka su, dan Duka zamuyi mata wallahi"
"Abin naki babba ne gwanda da baki sani ba"Bari in tafi ɗaki.
Tashi tayi ta shige ɗaki bata fito ba sai da taji hayaniyar yaran sun dawo. Fito wa tayi ta ringa yi masa mita bai jira ta dawo sun tafi tare ba. Hakuri ya bata yana ce mata baisan zata ba da ya jira ta amma ta bari next time sai suje da kyar ta yarda. Zaman cin abincin suka yi bayan sun gama gurin yaran ta koma tana ta yi musu wasa sai gurin shabiyu ta fito shima dan Sajeedah ta saka yaran suyi bacci ta koma ɗakin ta sallah daren ta tayi tun lokacin sai ta dau Kur'ani ta fara tilawa bata kwanta ba sai gurin uku.


♥♥♥


Zaune suke a cikin fada tsitt ba ka jin komai sai ƙarar AC hayaniya ce ta fara tashi daga waje wani bafade ne ya fita dan dubawa bai jima ba sai gashi ya dawo "Allah ya taimake ka Yarima ne dawo" yayi mamakin jin Yarima ne ya dawo Jiya ma fa sunyi waya amma bai sanar da shi ba, ɗazu ma yayi waya da likitan sa shi ma bai faɗa masa ya taho ba *"Me kake jira da ba zaka shigo da shi ba" da sauri ya miƙe zai fita sai gashi ya shigo fadawa suna ta masa kirari

Gurin Sarki yazo ya gaishe shi tare da mutanen Fada bai daɗe ba ya tashi yayi musu sallama yana ficewa daga fadar.


⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟


"Tabbas Ranki ya daɗe ya dawo chan na hange shi ya shiga Fada"

"Bai mutu ba kenan" Shiru ɗakin yayi na yan Mintina Wata Harara ta wurga wa Hadimar da sauri ta mike jikin ta na ɓari "A huta Lafiya" tace ta fice da Sauri tsaki taja tashi tayi ta fara zaga ɗakin magana ta fara

"Yanzu yaron nan bai mutu ba kenan, yana raye, kuma ya dawo Fada"

"Dole ya koma inda ya fito tunda bai mutu ba"......✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1



Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️


𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟒&𝟐𝟓



————————————————————————————————————————


Part ɗin sa ya nufa ya tarar da komai tass kamar yana nan Toilet ya shiga yayi wanka fito wa yayi ya shirya bai zauna ba hanyar fita yayi Fadawa ne guda Uku A gurin saurin taho wa gurin sa suka yi ɗaya daga cikin sune yace

"Ranka ya daɗe fita zaka yi"
Eh kawai yace musu ƙara magana ya cigaba da tafiya biyo da suka yi a baya

"bani makullin ba tare da kowa zan fita ba" yace musu. Kallon juna suka yi

"Ranka ya daɗe Mai martaba yace kar a bar ka kai kaɗai ka fita"

wuce wa yayi zuwa gurin motar kawai yayi cikin izzah ba tare da ya ƙara ce musu komai ba.


✿✿✿✿ ✿✿✿✿ ✿✿✿✿


Kano Nigeria.

Buɗe gate mai gadi yayi parking yayi Fitowa yayi daga motar da sauri ta ƙara so kusa da shi Kyakkyawa ce sosai Doguwa ce amma ba sosai ba dan ba za'a kira ta gajeriya ba, Magana ta fara yi masa "Tun ɗazu nazo ina jiran ka" Kallon banza ya watsa mata sannan yace
"Mai zan Miki da kike jirana? Na faɗa miki Bana son irin haka Koh, Kizo kiyi ta jirana sai kace wadda take bina bashi"

"Kawai zuwa nayi mu gaisa, in ganka ko naji daɗi a raina" cewar ta. Shiru yayi mata cigaba da yi masa magana tayi

"Har yanzu baka gama yarda da irin son dana ke maka ba Yah Zaaheed, naga kamar kana tantama akan haka"

"Noor In kin gama surutun kya iya tafiya gidan ku, na gaji da jin maganganun nan naki" wucewar sa yayi, riƙe baki tayi tace
"Au haka kace, Chabbbbb ai ko baka isa ba, dole kaji abinda zan faɗa" fuuuu ta wuce ta bi shi.

A palour ta tarar da shi tare da wata babbar Mace suna Magana Juyowa tayi ta kalle ta sai tace
"Noor dama ba tafiya kika yi ba"

Noor ce ta bata amsa da "Eh Mommy dama shi nake jira ya dawo"

"Ai gashi nan ya dawo, sai Kizo"cewar matar da aka kira Mommy

Ɗagowa yayi ya ɓalla mata Harara ba tare da Mommy ta lura ba da Sauri ta ɗauke kanta daga kallon shi

"Ai Mommy Tafiya gida ma zanyi kawai"

"Saboda me zaki tafi Bayan gashi ya zo"

"Baƙuwa nayi yanzu tayi min waya"

"Ahhh ya kamata ki ganta gaskiya"
Tace tana tashi
"Kya gaida Hajiya in kinje gida"

"Zata ji Insha Allah, Mommy kya yi wa su Kausar Sallama bazan koma Gurin su ba"

Tohm tace ta haye sama

Kallon ta maida kansa ko zai kalle ta amma taga ba ta ita yake ba tashi tayi jiki ba ƙwari zata fice yace

"Idan kika sake zuwa nema na gidan nan sai ranki ya ɓaci, wai Ni sa'an ki ne"

Ba tare da tace masa komai ba tayi ficewar ta.



╰╮o( ̄皿 ̄///)

Please Login or Register in order to submit comment