Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(╯-_-)╯╧╧



Noor ce Zaune a gefen gado kuka take ta rusa wa turo ƙofar ɗakin aka yi Babbar Mace ce daga gani Maman tace Kamar su ɗaya Zama tayi kusa da ita

"Yaushe kika dawo Noor?" inji matar da ta shigo

Hawayen Fuskar ta Share sannan tace

"Ban daɗe ba, naga ba kya Palour shiyasa na shigo ɗaki kawai"

"Yauma ya ɓata Miki ran kenan"

Shiru tayi ba tace mata komai ba, cigaba da mata magana tayi

"Na rasa wace irin zuciya gareki Noor?, Yaron nan ya nuna baya sonki ba sai ki ƙyale shi ba amma kin nace sai shi, wai shi kaɗai ne namiji a duniya ne?"

"Mommah kin san duk Duniya ba wanda nake so sai Yah Zaaheed tun ina ƙarama nake son shi, na rasa me nayi masa da baya sona ba"

"Mommah ina da wata makusa ne a jiki na ɗaya tsane Ni"

"Ba ki da shi" juya wa tayi ta Maida Kallon ta gare ta "Noor" "Na'am"

"Da zaki ji Shawara ta da tuni kin ƙyale Zaaheed, duk da ɗan ƴar uwa ta ce. A cikin samarinki da kike kulawa ki bawa wani dama, Zaaheed bashi da niyyar Aure, kuma ko yana da niyyar Aure ba Auren ki zaiyi ba ya riga da ya tsane ki"

"Mommah" ɗaga mata hannu tayi

"Karki ce min komai, ki fara Tunani akan wannan maganar" ta tashi ta fice............✍️



Jiya an samu Typing Errors da yawa mantawa nayi Banyi editing ba sai daga baya na lura. Tun cikin Azumi nayi typing ɗin ne Afuwan😰


Posting zai koma Monday, Wednesday & Friday sai Rana ɗaya a Weekend in na samu dama Insha Allah. Kamar yadda muke yi kafin A fara Azumi.


# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



Follow My Pages



Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟔&𝟐𝟕


————————————————————————————————————————


Tagumi ta zuba ta lula duniyar tunani zunbur ta miƙe gaban dreesing mirror ta tsaya kallon fuskar ta tayi sai kuma ta ja wayar ta Number tayi dailing ta fara Kira ringing biyu aka ɗaga

"Aunty Barka da Rana"

"Barka dai, Kwanwas naji Muryar ki kamar kinyi kuka, ko baki da lafiya ne?" aka faɗa daga cikin Wayar

"A'a Ba komai, Yaya yana gari?"

"Baya nan"

"Ok gani nan zuwa" ta kashe wayar

Jaka ta ɗauko ta ɗauki Key ɗin Mota da wayar ta ta fice, a Palour ta tarar da Aliyu yana zaune magana ta fara yi masa "Yaya in Mammah ta sauko kace mata nake gidan Aunty"

"Meya faru? Na ganki haka"

"Ba komai, na tafi" ta fita da sauri



❦❦❦❦ ❦❦❦❦


"Yah Zaaheed sannu da zuwa" cewar Aliyu ƙanin sa
Yauwa kawai yace masa ya tashi ya haura sama bin sa da kallo yayi kawai. Ɗakin Mommy ya shiga waya take yi Zama yayi yana jiran ta gama wayar. "Ba zaka huta ba ne?, Daga aiki fa ka dawo"
"Mommy please ki daina turon yaran nan a matsayin na Aure su" Yace mata.

Kallon shi tayi da kyau "Saboda ta zo gurin ka shikenan ba zaku gaisa ba"

"Mommy ita Yarinyar nan ba gaisuwa ce take kawo ta ba"

"To mene yake kawo ta? Faɗa min inaji"

Shiru yayi sai kuma yace"Mommy bari in tafi in huta"

"Nemi guri ka zauna" tace masa

Guri ya nema ya zauna. Nisawa tayi sannan tace" Zaaheed na gaji da zaman ka haka ba Aure, kowa yana Aure amma banda kai"

"Mommy Insha Allah nan bada jimawa ba zanyi Nima"

"Ko yaushe haka kake cewa, ko sai bayan rai na zaka yi ne" ta share hawayen da ya zubo mata, da sauri ya sauko kasa ya zauna kusa da ita yana riƙe hannun ta

"Kukan ki Azaba ne a gare Ni, dan Allah ki daina Insha Allah zan yi Aure nan bada jima wa ba. Mommy zan cika Miki burin ki ba zaki mutu ba sai Kinga ƴaƴa na In sha Allah"

"To naji yaushe zaka kawo matar, indai da gaske kana son farin ciki na"

"Nan bada jimawa ba Insha Allah"

"Allah yasa" tace tana shafa Kansa


Waye ZAAHEED ???
Wace NOOR ???


Alhaji Yusuf Shine sunan mahaifinsa matar sa Ɗaya Hajiya Sa'a Ƴaƴa biyu Allah ya basu a duniya duk maza Zaaheed shine babba sai Ƙanin sa Al-Ameen. Hajiya Sa'a tana son Mace amma Allah bai bata ba. ƙwanwar ta ɗaya a duniya Habiba suna son junan su ko yaushe suna tare da juna har Allah yayi wa mahaifansu rasuwa ta dawo gurin ta da zama har tayi Aure. Habiba tana da yara Uku biyu Mata ɗaya Namiji, Amina ce Babba ana ce mata Khairat, sai Aliyu, sai ƴar Auta wadda taci sunan Mommy Sa'adatu ana ce mata Noor. Tunda aka yaye Noor Mommy ta karɓe ta. Noor yarinya ce kyakkyawa bata da hayaniya bata da rawar Kai, sun taso tare da ƴaƴan ta har sai da ta gama secondary school sannan ta koma gidan su a Lokacin Zaaheed yana US karatu.


Zaaheed yayi karatun sa a US tun daga Degree har Doctoring Degree duk a US sai da ya gama sannan ya dawo Nigeria ya tarar ƙannen sa duk sun girma bayan dawowarsa ba daɗe wa Noor ta nuna tana son sa amma yayi biris kamar bai san tana yi ba da farko ta so ƙyale shi amma sai ta kasa. In Mommy'n tayi masa maganar Aure sai ya hau neman hanyar da zai guje wa maganar yanzu yana da shekaru 35 a duniya Lecturer ne a B.U.K. Shine dalilin da yasa Mommy duk ta damu yayi Aure......✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan






Follow My Pages



Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404

WhatsApp only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


https://chat.whatsapp.com/Lg8RQ7S5NfX6fSmnSkRA79


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️





𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟗&𝟑𝟎



————————————————————————————————————————


𝒁𝑨𝑨𝑯𝑬𝑬𝑫

Tunda yaga Mommy'n sa na son tada hankalin ta akan Auren ya yanke shawarar yi wa Abiee'n su waya baya ƙasar yana India ya sanar da shi.


Ringing wayar take yi ba'a ɗaya ba har ta katse bai ƙara bin kiran ba yasan maybe Yana meeting ƙyale shi yayi yasan zai kira sa bayan Hour ɗaya sai gashi ya kira shi Bayan sun gaisa ya fara sanar da shi dalilin kiran
"Abiee dama sanar da kai zan yi na samu Yarinyar da zan Aura"

"To Masha Allah, a ina take" cewar Abiee

"A nan Kano take, ɗaliba tace"

"Alhamdulillah, Ƴar gidan wace?"

"Ƴar Alhaji Harith mai Kanwa"

"Harith mai Kanwa dana sani"

"Dama ka san shi ne Abiee?"

"Na sanshi shekaru da daɗewa, wacce daga cikin su"

"A'isha" yace

"Masha Allah, Zan nemi Contact ɗin sa in sanar da shi kafin na dawo" nan suka cigaba da maganar


Mommy tayi murna da jin zancen saboda zamuɗi bata jira dawowar Abiee ba ta sanar wa ƴan uwa aje a nemo masa Auren kar a samu Matsala wani ya riga su.


Abiee ne tuntube shi sannan ya turo musu number Daddy'n su Hooriyah tunda ya sanar da shi zai turo masa baƙi ya basu dama suzo Ranar Asabar.


Ranar Asabar bayan La'asar suka je bayan ƴan gaishe gaishe suka sanar da shi abinda ya kawo su yaji daɗi sosai dan Yasan Zaaheed tun da daɗewa yaron kirki ne nan ya amince yace a turo shi...



♡♡♡
♡♡♡
✭✭✭
♡♡♡
♡♡♡


A bangaren Hooriyah komai yana tafiya dai-dai yanzu bata da wani damuwa ta fawwalawa Allah komai ta ɗauki ƙaddara sai tayi two weeks bata je gida ba sai dai suyi waya dasu Mami kowa so yake ya faranta mata suna zaune lafiya da Aunty Sajeedah.



Tunda Aunty Sajeedah tace mata Yayan ta na neman ta take jin wani iri sau uku tana attempting tafiya side ɗin sa sai ta kasa ta rasa dalili har aka idar da Sallah bata je ba. Turo kofar ɗakin aka yi "Yanzu dama ba kije kiran da yake Miki ba, kina zaune a inda na barki, maybe ko Sallah ma baki yi ba"

"Har anyi salla?"

"Tun ɗazu gani nayi ba kya Palour kuma shima bai dawo daga Masallaci ba nasan kina ɗaki baki je ba"

"Tsoron Zuwa nake, kawai ji nake gabana na faɗuwa"

"Allah yasa ba Su Mami ne suka ce na koma gida ba, wallahi bana son Komawa"

"Ke da baki je kinji mene ba har kinyi hukunci"

"Amma ke zaki rakani gaskiya, in yace in koma Dan Allah ki sa baki ya barni"

"To naji, tashi kiyi salla"
Jiki ba ƙwari ta tashi ta nufi Toilet Alwala tayo tazo ta tada Sallah bayan ta idar ta kalle ta
"Tashi muje Koh"

"Jeki zanzo daga baya"

Rau tayi da ido sannan tace

"Amma ai ba muyi haka da ke ba My Aunty"

"Haba Hooriyah sai abu kike kamar ƙaramar yarinya ko Fudail ba zai yi haka ba"
Bata rai tayi da kyar ta lallaɓata ta tafi ita kuma tayi gurin yaran ta"


✿✿✿✿ ✿✿✿✿


Zaune ta same shi yana karanta Jarida Sallama tayi ta nemi guri ta zauna a ciki ya answer bai ce mata komai ba. kana ganin ta kasan a tsorace take sai da tayi gurin minti Goma sannan yace

"Sai yanzu kika ga damar zuwa kenan"

"A'a naga an kusa tada sallah ne Shiyasa na zauna sai da nayi Sallah sannan na taho"
Jinjina kai kawai yayi

"Daddy ne yace gobe kije yana son ganin ki"

"Shikenan abinda nake gudu ya tabbata" take faɗa a ranta

"Me kike gudu?" Ya jefo mata tambaya, da sauri ta lalle shi "yaya ba magana nayi ba"

"Magana ce akan Auren ki ba wani abu ba, karki saka wa ranki damuwa, Dan har Iyayen yaron sunzo sun tambaya kuma Daddy ya basu dama"

A firgice ta kalle shi ɗan bata taɓa kawo maganar Aure a ranta ba ta riga data soke shi a rayuwar ta ba zata ƙara kula kowa ba balle har a samu damar yi mata Abinda Zaid da Anisah suka mata magana ta fara yi masa

"Yanzu Yaya har zaku iya ƙara bawa wani dama kuce yazo gurina, kun manta abinda su Zaid suka min dududu wata nawa da har zaku manta"
"Ni a ganina ba zaku ƙara bawa wani dama yazo gurina ba"ta faɗa Muryar ta na rawa........✍️


# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯




Jiya nace zanyi posting amma ban samu dama ba ɗan Yayana ne Allah yayi masa rasuwa Allah ya jikan shi ya gafarta masa tare da Al'ummar Musulmi baki ɗaya👏



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan






Follow My Pages



Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404

WhatsApp only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466




بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️





𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟏&𝟑𝟐


__________________________________________________________________



Tausayin ta ne ya kama sa duk sai yaji babu daɗi da Daddy ya sani sun fara tuntuɓar ta kafin ya amince magana ya fara mata cikin kwantar da murya

"Daddy ne ya yanke shawarar, Kiyi haƙuri ki bi umarnin sa kinji Allah yasa haka yafi alkhairi, Yace gobe in Allah ya kaimu kije" magana zata yi masa yayi saurin ɗaga mata hannu

"Hooriyah ya isa haka tashi kije da safe sai ki shirya in sauke ki kafin in tafi aiki"

Tohmm kawai tace ta tashi ta fice.


Da safe Gurin goma ta gama shirin ta tana zaune jiran sa da ganin ta kasan tana cikin damuwa yana gamawa suka fice Yana sauke ta ko shiga cikin gidan bai yi ba ya tafi sai ya dawo zai shigo.



💫💫💫💫 💫💫💫💫 💫💫💫💫



Cikin Gidan ta shiga ba kowa a Palour da alamun mutanen gidan duk suna ɗaki basu fito ba Motsin da taji a kitchen ne yasa ta nufar gurin Mai Aiki ce kaɗai a ciki tana ta kai kawo

"Baaba Barka da Safiya, Ina su Aunty?" Tace mata

"Kece tafe da safiyar nan, Barka kadai, Mami tana Bangaren Alhaji, Aunty kuma tana Ɗaki bata daɗe da shiga ba" ta bata answer.

"Thom idan sun fito kice musu ina cikin ɗaki" cewar Hooriyah

"Insha Allah zan sanar musu" ta faɗa mata, wucewa ciki tayi. Ɗakinta ta nufa shiga tayi ta nemi guri ta kwanta bata jima ba ta tashi waya ta ɗauko kira ta shiga yi ringing biyu aka ɗaga gaisawa suka yi

"Na zata ba zaki ɗa ga ba ai, ya fadil?"

"Ashe kin san laifin naki, Fadil yana nan qlau" cewar Khaleesat

"Anjima zan shigo"

"Kinzo gida yau kenan, Ashe kina son Goge laifin naki"

"Ban daɗe da zuwa ba, mun kwana biyu bamu gaisa ba, sai na shigo"

"To Allah ya kawo ki lafiya"

"Amin, sai anjima" ta kashe wayar.

Tashi tayi ta fito palour ta samu sun fito suna zaune da alamu ita suke jira itama zama tayi ta fara gaida su

"Ashe Da wuri ya kawo ki" Aunty ta faɗa

"Ehh Da zai fita muka taho tare inya dawo yace zai shigo"

"Ai Yayan ku baya fashin zuwa kullum sai yazo"

"Bari mu baku guri, in kun gama kizo za muyi magana" cewar Aunty

"Insha Allah"


🤙🤙🤙


Zaune take a gaban Daddy magana ya fara mata:

"Da fatan Ya sanar dake abinda yasa na kira ki"

"Eh Daddy"

"Na ba shi dama yazo ku ga juna Lecturer ne a makarantar ku yace anan ma ya ganki, Mahaifinsa Abokin na ne a da"
"Daga yanzu zuwa kowane lokaci zaki iya ganin kiran sa"

"Allah ya bani ikon yi maka biyayya" kawai tace

"Amin, Allah yayi Miki Albarka, Ni zan fita in kin shiga ki sanar da su"

"Ameen Daddy, tohmm sai ka dawo Allah ya tsare Hanya"

Ameen yace



❉❉❉❉ ❉❉❉❉❉ ❉❉❉❉


ABUJA


Zaune suke ita da wata budurwa daga gani kasan ƴar ta ce kamar su ɗaya ranta a ɓace daga ni kasan wata maganar suke yi wadda bata jin daɗin ta

"Ammi na faɗa Miki ba tun yau ba ki ƙyale su kinki, Ni banga amfanin abinda kike yi ba"

"Husna nace ki ƙyale ni dasu, wai kamar ni a ce zai dawo ba'a sanar min ba, sai na Kashe shi kowa ya huta" ta faɗa tana yin kwafa

"Ammi baki haife shi ba, mahaifiyarsa na raye ba mutuwa tayi ba, dan zai dawo dole sai an sanar da ke?. Ki daina irin furucin nan kar wani yaji ya zame mana matsala, Ɗan uwan mune fa, wallahi bana jin dadi in kina faɗin zaki kashe shi"

"Husna Ni kike faɗa wa waɗannan maganganun?, Na kira ki ne dan ki kwantar min da hankali amma kinzo kina faɗa min wasu maganganu marasa daɗin ji"

"Tashi ki fice min daga nan" ta faɗa tana nuna mata Hanyar fita

"Ammi ban fadi wata magana dan na ɓata Miki rai ba, Kiyi haƙuri in na faɗi abinda bai Miki daɗi ba"

"Ba zaki fitan ba kenan?, To Ni bari in bad Miki ɗakin" ta faɗa tana ƙoƙarin mike wa, da sauri ta tashi ta fice mata a ɗakin. Ta rasa me yake damun mahaifiyar nan tata da komai na gidan sai an sanar mata in ba'a faɗa mata ba ta Ringa ƙorafi "ya kamata in fara binciken mene dalili" take faɗa cikin zuciyar ta............✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1



09047574404
WhatsApp Only



Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/9, 4:10 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️





𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟑&𝟑𝟒


_______________________________________________________________________________________



Tana barin gurin Daddy ta nufi ɗakin Aunty suna zaune a Palour'n ta da Mami

"Magana dama zamu yi dake Hooriyah" Mami ta faɗa mata

"Mami inaji"

"Yayan ku ya faɗa Miki Maman ku Safiyya tazo?"

A rikeɗe ta kalle ta gumi na keto mata
"Tazo? Me tazo yi kuma?"

"Tabbas Ta ƙara zuwa, Maganar Auren ki da Sulaiman ce ta kawo ta, tace ba zata taɓa haƙura ba har sai kin Aure shi. In Kuma ba ki Aure shi ba dole kiyi Aure a kankanin lokaci"

"Sulaiman kuma Mami? Ai na zata an gama maganar, Mami ya zata ce haka bafa ita take riƙe Ni ba"

"A gurin kine ta wuce amma ita a gurin ta tana nan, Kuma ta taso da ita" shiru tayi Aunty ce ta cigaba da magana

"Hooriyah wannan yaron da yazo Indai na gari ne ki amince masa kafin ta ƙara dawowa"

"ki bashi dama kinji"Aunty ce tayi Maganar

"In Sha Allah Aunty zan bi duk abinda kuka zaɓa min, Allah ya sa Haka ne yafi Alkhairi"

"Ameen, yanzu ki huta Kafin Yayan ku ya dawo ku tafi" cewar Mami

"Ina so Zanje Gidan Khaleesat bayan La'asar mun daɗe baku haɗu ba"

"Khaleesat yarinyar kirki Last week ma ta shigo ai, Allah ya kaimu" Aunty ta faɗa

"Bama ta faɗan tazo ba, Amin"

"Ai nasan ba lallai ta sanar Miki ba"

Miƙe wa tayi tana cewa"Bari inje in taya Baaba Aiki"

"Ke da zaki huta kyau tafi wani aiki, kije kiyi hutawar ki anjima muyi hirar yaushe gamo" inji Aunty

Dariya ta saka sannan ta ce "Bari dai in taya ta daga baya mayi hirar, nayi missing girkin Baaba" ta faɗa tana ficewa.

Kitchen ta nufa gurin Baaba ta tarar har ta kusa gama Girkin hirar yaushe gamo suka shiga yi tana miko mata abu kawai ta ringa yi in ta buƙata bayan ta gama girkin tayi mata wanke-wanke da kyar ta yarda cewa tayi ta huta ita da ba zuwa take yi gidan ba yau kuma tazo ai sai ta huta ba tayi ta aiki ba. Bayan Sun gama suka sha hirar su da su Mami sai da Uku ta wuce sannan ta shirya ta nufi gidan Khaleesat.


A gidan Khaleesat ma Hirar su suka sha har bayan Isha tana gidan sai da Yaya ya kira sannan ta koma gida Fadil har kuka yayi da zata tafi. Tana shiga gida sallama kawai tayi dasu Mami suka tafi sai faɗa yake tayi dare Bacin yasan ba ita kaɗai zata tafi ba.


✨☆★✨☆★✨☆★✨☆★✨


Bayan Kwana Biyu da zuwan ta gida ya kira ta ya mata bayanin kansa a taƙaice kafin ya zo. Taji ya kwanta mata a rai amma taki amince masa har sai yazo ta Ganshi.


𝗔𝗿𝗼𝘂𝗻𝗱 10:00 𝗣𝗺


Saukowa take daga bene waya take duba wa Palour'n shiru alamun duk yaran sunyi bacci Sajeedah ce kaɗai zaune take kallo zama tayi kusa da ita
"Aunty Sannu da Hutawa"

"Yauwa, Har kin sauko"

"Eh Wlh, Har na kwanta nace bari in zo muyi magana kafin kiyi bacci"

"Maganar me zamuyi"

"Zaaheed da Daddy ya turo shi ne yace zaizo Ni na rasa yadda zanyi"

"Eennyyeeh ashe da gaske yake ya shirya in fara shirin Biki"

"Joke apart Aunty"

"Kawai kice yazo mana, mene a ciki kawai sasantawa za kuyi musha Biki"

"Gani nake kamar shima yaudara ta zaiyi Indai yazo"

"Ai baizo ba Koh Balle ki yanke masa hukunci, ki bari yazo sai mu yanke masa hukunci"

"Zan sanar da shi"

Nan tayi ta bata shawarwari tana ƙara mata wayar mata da kai akan Rayuwa har 12 suna palour sai da Yaya ya sauko sannan kowa ya nufi ɗaki. Ko da ta shiga ɗaki bata kwanta ba salla tayi sannan tayi Addu'a Allah yayi mata zaɓin Alkhairi.



💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦


𝟑𝐫𝐝 𝗔𝘃𝗲𝗻𝘂𝗲 𝗔𝘀𝗼𝗸𝗼𝗿𝗼, 𝗔𝗕𝗨𝗝𝗔.


Zaune suke a palour su biyu Tsit sai ƙarar A.C ne kaɗai ke tashi shi da wani Babban Mutum ne a zaune a ƙalla zai kai Shekaru 65-70 Fari ne qal kamar Balarabe da gani magana suke mai muhimmanci nisawa yayi Sannan ya cigaba da cewa

"ARSHAD ina ganin nan zaka dawo da zama, jikin nan kamar bai gama warke wa ba"

"Papi na warke zan iya zama a can Insha Allah" wanda ya kira da Arshad ne ya bashi answer

"Bana son kana zama kai kaɗai a gidan tunda mahaifiyar ka ba lafiya ne da ita ba, ba lallai ayi maka komai da kake so ba"

"A'a Papi na fison in zauna a can, ina son gano wanda ya saka min guba ne, nasan tunda na tashi yanzu yana son haɗa wani abun kuma"............✍️





# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/14, 10:30 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡


https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz


𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟓&𝟑𝟔


__________________________________________________________________



Ta sanar da shi duk lokacin da ya shirya zai iya zuwa bayan sati ɗaya ya zo. Bayan La'asar ya kira ta gashi ya ƙara so. Sajeedah ce tayi wa maigadi waya ya kaishi guest room mayafi ta saka ta nufi guest room ɗin.
Zaune yake yana Facing ɗin Ƙofa Tayi mamakin ganin sa sosai shanye wa tayi bata nuna ba ko a fuska guri ta nema ta zaune nesa da shi gaisawa suka yi cikin mutuncin nan ya fara magana

"Nasan kinyi mamakin ganina duk da baki faɗa ba"
"Kamar yadda kika sani sunana Zaaheed Lecturer ne a BUK nasan duk kin san wannan" nan yayi tayi mata bayanin sa Ita dai nata ji ne dan har yanzu mamakin sa take daga Ehh sai A'a take bashi answer wani zubin tayi masa shiru, bai jima ba yace mata zai tafi ta raka shi har bakin motar sa sai da ya tafi Sannan ta shige ciki.

💣💥


A palour ta tarar da Sajeedah zaune tana yiwa Fudail aiki zama tayi kusa da ita ta rafka tagumi tun shigowar ta tana lure da ita yanayin ta ya chanja Fudail ta tattara wa Littafin sa tace ya shiga ciki zata zo su ƙara sa aikin

"Meya faru na ganki haka"

"Aunty Lecturer mune fa, gaskiya Ni ba zan iya ba bashi da mutunci ko na kwabo"

"To sai me dan Lecturer kune"

"Wlh Aunty ko Lecture zaiyi ya dinga bata rai ga rashin mutunci Ni gaskiya da kyar in zan iya Auran sa"

"In da ya sake fuska yanzu da yazo zaki kula shi ne cewa zakiyi yafiya kula ƴanmata ya kame kansa ma bai tsira ba"
"Sai Kiyi ta yi ai, karki sake yayanki yaji wannan Maganar balle har ta kai kunnen Daddy dan nasan ranki ne zai ɓaci"

"Yanzu kuma sai inyi shiru a cuceni, ba shi da mutunci ko na sisi Wallahi ban taɓa baki labarin abinda yayi wa Anisah ba, one minutes after ya shiga class ta shigo amma korar ta yayi yana faɗa mata magana"

"Anisah daban ke daban" dafa kafaɗarta tayi sannan ta cigaba da cewa "ki dai bashi dama har yanzu ki na da chance in Kinga halin shi ɗaya ne dana makarantar sai ki sanar da Daddy"

"Ai shikenan, amma"

"Amma me kuma kiyi shiru kawai"
Kwanciya kawai tayi a kujerar ba tare da ta ƙara ce mata komai ba


Befi sau biyu zuwa uku yayi yana zuwa ba aka kawo kuɗi sai dai waya da kullum yake kiranta ba fashi duk da har yanzu cewa take bata sonsa amma tana ganin zata iya Auren sa. An saka Biki six Months ya kama bayan sunyi Graduation da wata biyu za'a yi bikin.


💕 ✿★ ❤️ ✿★💕


Shirye-shiryen exams suke duk sun zama busy itace last exam da zasu yi sun gama makaranta basa son su samu matsala ga bikin Hooriyah da yake ta matsowa saura Three months. Sun yi exams lafiya suka gama lafiya anyi Graduating sai jiran results kuma.



⋇⋆✦⋆⋇ 💫 ⋇⋆✦⋆⋇ 


Please Login or Register in order to submit comment