Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matuƙar ƙaunar sa.




Tun safe ake kiran ta daga unguwar su tazo jikin Ummanta yayi tsanani sai kiran sunan ta take yanzu ma zaune take a palour ta buga uban tagumi kira ne ya shigo wayar da Sauri ta daga ganin ƴan unguwar tasu ne bansan abinda ake faɗa mata ba kawai ta zaro ido tana cewa

"Ta mutu fa kika ce, Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, na shiga Uku"...................✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡







https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz





𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽





𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷











тԋє ɯɾιтєɾ σϝ



*ʂιʅαɾ ɯαყα*



𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪



♡ ԋσσɾιყαԋ ♡











بسم الله الرحمن الرحيم









𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️









𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟕&𝟒𝟖





__________________________________________________________________________________





Wayar ce ta faɗi kasa faɗa wa tayi ragab akan kujerar hawaye ne ya fara zubo mata surutai ta fara"Umma ta rasu, Ummana fa itace ta rasu" neman wayar Tata ta fara yi a kasa ta ganta number Zaid tayi dailing yana ɗagawa tace "Allah ya isa mugu ka cuceni ka hanani zuwa Duba Ummata gashi har ta rasu banje ba" wani kukan ne ya ƙara kufce mata ajiye wayar tayi ba tare da ta kashe ba bedroom ɗin ta ta nufa mayafi da key ɗin Mota ta ɗauko rufe gidan tayi ta fice a guje. Hanyar babu kowa dan haka ta samu damar sharara gudu san ranta ƙatuwar trailer ce ta taho itama gudu take sharara wa kanta tayo gadan-gadan kafin ta farga Ta kauce mata har tayi gaba da ita.







✨😍✨







A bangaren Hooriyah kuwa kwanciyar ta tayi a palour Sajeedah ta shiga kitchen cigaba da taya su aiki. Yana shigowa gidan ya san ta sani amma ya basar tashin ta yayi zama tayi tana ƙaƙalo murmushi

"Yau da wuri ka dawo" ƙoƙarin rufe damuwar ta sake yi "Sannu da zuwa Yaya"



"Yauwa, ɗauko mayafinki zamu je gida"



"Yaya gida kuma, ai ba sai mun wahalar da kanmu zuwa gida ba dan ku sanar da Ni na riga da na sani" ta faɗa tana aro jarumta dan kar ya gane tana cikin tashin hankali



"Kin sani fa kike ce" gyaɗa masa kai tayi



"Eh Yaya Aunty ma ta sani, kaga babu maganar muje gida wahalar da kanmu na ɗauki ƙaddara Allah yasa haka ya zame min alkhairi"





Jikin sa ne yayi sanyi jin abinda ya fada tashi yayi ya barta a gurin Kitchen ya nufa inda yaji hayaniyar su aiki ya tarar da su suna tayi Sajeedah yayi wa alamu ko ta sanar da su ta girgiza kai



"An fasa Auren ku daina wahalar da kanku, abinda baku yi ba kawai ku barshi" yace musu kawai



Gurin lokacin ɗaya hankulan su ya dawo kansa "An fasa fa kace?" Suka haɗa baki gurin faɗa...





💥💥💥





Tunda ta samu Labarin farkawar Abeedah hankalin ta yake a tashe waya take ta yi amma anki ɗagawa ta rasa yadda zata yi sai zuwa ake yi mata murna sai yanzu ta samu damar kebe wa amma anki ɗaga kiran.







💦💦💦







Rungume ta shima yayi har gurin minti goma sannan ya cika ta maimarta ba ne yayi gyaran Murya



"Abeedah muna son jin abinda ya faru dake" sarki ya faɗa

"Zan sanar wa Arshad sai ya faɗa muku" ta fadi tana ɗauke kanta. Tunda ta farka haushin shi take ji gani take kamar ya Aure ta bata da mai bata amsa ta sai Arshad shiyasa take so ya basu guri tayi magana da ɗanta



Jinjina kai yayi sai kuma ya kalli waziri yace masa "A sanar da kowa gobe karfe goma suzo fada ina neman su, Allah ya ƙara Afuwa" yana gama faɗa suka fice



Har dare yana tare da ita da hadimai tana son suyi magana amma ta kasa cewa su fita su basu guri sai haƙura tayi. sallah ce kaɗai take fitar da shi gani yake kamar in ya fita kafin ya dawo ta koma yadda take ada.







Washegari





Zaune suke a fada kowa na family ya hallara Abeedah kawai ake jira ta fara magana ƙasa ta ƙara yi da kanta tana share hawayen ta Yana Zaune a kusa da ita ƙara Riƙe hannun ta yayi yana magana "Ammi ki daina kuka, ki sanar mana abinda aka yi miki dan Allah, ance kin sani ya kamata ki sanar mana ko zamu fita daga rudanin nan"

Magana ta fara kamar haka:



ᴡᴀɪᴡᴀʏᴇ





Ranar wata Laraba da safe ina zagaye kamar yadda nake yi kowane lokaci naji Habiba tana waya a bayan garden kasa kunne nayi na saurari maganar da take faɗa



"So nake a kashe miji na, kasan nayi ƙoƙarin zama da shi na tsawon shekarun nan, kuma karka manta a dasawa sarki sona a saka tsanar matar sa da ɗansa a zuciyar sa yadda ina gama takaba zai Aure Ni" dan jimm tayi tana jiran amsar da ake bata sai kuma ta cigaba da cewa



"Ai ita bai damu da itaba kamar Abeedah daga ita har ƴaƴan nata ba wani sonsu yake ba kaga bani da matsala da su, in na shiga zan saka ya sake ta"



Jin abinda take faɗa yayi matuƙar tayar mata da hankali ai bata jira ta gama maganar ba a fusace ta hau cewa



"Yanzu yadda muke da ke Habiba abinda kike min kenan? Duk yadda da amanar da na baki? Habiba bani da kamar ki duk gidan nan amma sakayar da zaki nuna min kenan"



A firgice ta juya ba tare da ta kashe wayar ba dan bata yi tsammanin wani yana jin ta ba



"So kike in cigaba da zama a ƙarƙashin ki ba cigaba kullum sai ci baya, kin san ina son mijin ki amma kika sa aka Aura min Hakimi. Sarki nake so ba Hakimi ba kin sani"



"Dan shi kike so shine zaki yi wannan abin? Ai ko sai kowa yasan abin nan" ta ce tana saurin juya wa da sauri ta shaƙo wuyan ta

"Ba sai kin ƙara magana ba sannan zaki tona min asiri? ɗan naki ma da kike tutiya da shi raba ku zanyi kowa ya huta" ta faɗa ta sakar mata wuya tare da wucewar ta



Ɗaki Nima na koma da zummar idan Arshad ya shigo in sanar masa amma tunda ya shigo nake kokarin yin magana na kasa.



Shine abinda ya faru tun daga nan na daina ji kuna ta zargin Kareema bata da laifi ko kaɗan nasha bibiyar rayuwar ta inga ko tana wani abu mara kyau amma ban taɓa kamata ba kawai faɗa ne da yayi mata yawa.



****



Share hawaye ta tayi bayan ta gama basu labarin kowa jinjina lamarin yake matar da take simi-simi bata da hayaniya ba ruwanta da kowa ko faɗa ba tayi amma itace da wannan aikin. Mijin ta ne ya mike da sauri jikin sa sai tsuma yake yi inda take ya nufa yana ɗauke ta da mari Sannan ya cigaba da cewa "Amma kin cuceni kin ɓata sunan gidan mu, Aure na da ke ya ƙare. Bari Ni in fara Kashe ki kafin ki kashe ni"ya faɗa yana shaƙo wuyan ta...................✍️







# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯







Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan





https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I





Follow My Pages





Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1





Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1





09047574404

WhatsApp Only





Comments & Share Fisabillah🥰👏







𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡







https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz









𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽





𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷











тԋє ɯɾιтєɾ σϝ



*ʂιʅαɾ ɯαყα*



𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪



♡ ԋσσɾιყαԋ ♡











بسم الله الرحمن الرحيم









𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️









𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟗&𝟓𝟎





————————————————————————————————————————









Sarki ne yayi masa magana da kyar ya sake ta sai kakari take duk ta shiɗe ruwa aka bata ta sha tana ta nishi



"Me yasa kika yi wannan laifin" Sarki ya jefo mata Tambayar



"Bayan kasan yadda nake sonka tun kafin kayi Auren fari, nayi ƙoƙarin danne san da nake maka in zauna da wanda ka Aura min amma na kasa ƙawata ta bani shawarar bin malaman za'a samo kanka har ka amince ka Aure Ni wallahi ranar da taji ina waya ranar ne na biyu dana kirashi jin zata tona min asiri yasa nace ya rufe bakin ta amma sai ya kurmantar da ita ya makanta ta na tsoro ta ƙwarai da lamarin tunda na gane ba Aure na zaka yi ba na tuba na ƙyale ta ban ƙara neman wani abu a gurin saba. Dan Allah ku yafe min"



"Wane tuba, kin cuceni ana ta zargi na, kuma ai Nima ke kika zo 𝒕𝒂𝒏𝒂 𝒃𝒊𝒏 𝒎𝒂𝒍𝒂𝒎𝒂𝒊 𝒅𝒂𝒏 𝒕𝒂 𝒓𝒂𝒃𝒂 𝒎𝒖 Ni kuma na tada hankalina na daina kula ta Ashe karya kike" Kareema ta faɗa kamar zata dake ta



"Ni kuma?"



"Eh ke din zan Miki karya ne" Kareema ta ƙara faɗa tana huci



"Dama ance rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tame kaya, Sharrin Shaidan ne yasa na faɗa Miki haka Amma Abeedah mutuniyar kirki ce na sani kawai dan ku rabu ne yasa na faɗa Miki haka" ta faɗa tana rushewa da kuka



"Kuyi hakuri na tuba, Abeedah ki yafe min dan Allah" ta faɗa tana tasowa zuwa gurin Abeedah hannunta tazo kamawa zata riƙe Arshad ya buge shi

"Me kuma zaki yi mata" ya faɗa yana tsareta da ido Kwarjini taga yayi mata ƙasa tayi da kanta

"Haƙuri zan bata kawai"

"Ki bata daga inda kike ko wani abin zaki ƙara yi mata"

"A'a Arshad dan Allah ka bata hakuri wallahi nayi nadama"



Papi ne yayi gyaran Murya (𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒏 𝑨𝒎𝒎𝒊 𝒏𝒆) "duk abinda ya faru ya riga da ya faru Allah yasa bata yi kisan ba, Abeedah ki yafe mata munji Uzurin ta sai ayi mata Alfarma tunda bata kai ga aikata laifin ba, Allah ya yafe mana baki ɗaya"



"Alhaji dole ayi mata hukunci" cewar Hakimi



"Papi nakasar da Ammi da tayi kuma ya tafi a banza?" Cewar Arshad



"Duk wanda aka yi wa laifi kaga an bashi hakuri to an cuce shi ne, ba ga sakayya nan Allah ya mata ai bata Auri Abubakar ɗin da take so ba"



"Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Ammi

Da Amin aka yi ta amsawa



Da kyar aka lallashi Hakimi ya haƙura ba sai anyi hukunci ba amma ya sake ta sai cewa yake sai anyi mata hukunci Ta inda yaji daɗi bashi da zuri'a ko ɗaya da ita. Kamar jira mutane suke su gama zaman zancen ya fara zagaye gidan Mutane sai Allah wadai suke yi mata, wadda ta riƙe ki amana tun shekaru da yawa ita zaki cuta.













🅩🅐🅐🅗🅔🅔🅓









Tunda Mommy'n su ta yanke wannan hukuncin yake jin ba daɗi Baya son Noor ko kaɗan kallon kwanwa yake yi mata Kulle kanshi yayi a ɗaki ya daina cin abinci dan Mommy'n ta gane baya son Noor Amma ta masa banza ta nuna bata san abinda yake ba ganin ba mafita bace yasa shi yanke shawarar tunkarar ta ya sanar mata shi baya sonta taje ta nemi dai-dai da ita. Bayan La'asar ya shirya ya nufi gidan su Noor yana zuwa ko ciki bai shiga ba yasa maigadin su yi masa sallama da ita ciki ya shiga a palour ya tarar da Mummy ita kaɗai gaishe ta yayi sannan yace



"Hajiya ana sallama da Noor a waje"



"Sallama kuma?, Su Waye? Basu san Gobe ne Auren ta ba"



"Ai Angon ne yazo yana waje" ya faɗa yana washe baki sai kace wanda aka bawa Kujerar Hajj😂💔



"Zaaheed ɗin mai yasa bai shigo ba"



"Hajiya cewa yayi sauri yake"



"Je kace masa gata nan zuwa"



"Tohm Hajiya Allah ya ƙara girma" ya faɗa da Sauri yana ficewa

Tashi tayi ta shiga ɗakin Noor tana zaune a kan gado waya take yi ganin Mom ne yasa ta katse kiran kana ganin ta kaga Amarya an fara gyaran jiki ta ƙara yin wani kyau ga kamshi sai tashi yake a jikin ta Mummy ce tace

"Kizo Zaaheed ne yazo yana jiran ki"



"Mummy Zaaheed ɗina, gani nan zuwa" ta faɗa tana tashi Drawer ta buɗe ta ɗauko Hijab sakawa tayi ta fice jikin ta sai rawa yake



𝐾𝑒𝑑𝑎 𝐴𝑛𝑔𝑜 𝑘𝑜 𝑎𝑚𝑖𝑛𝑐𝑒𝑤𝑎 𝑏𝑎𝑖𝑦𝑖 𝑏𝑎 𝑘𝑖𝑘𝑒 𝑔𝑦𝑎𝑟𝑎𝑛 𝑗𝑖𝑘𝑖 𝐻𝑎𝑏𝑎 𝑁𝑜𝑜𝑟 𝑑𝑖𝑛 𝑚𝑢 𝑦𝑎 𝑧𝑎𝑘𝑖 𝑏𝑎𝑑𝑎 𝑚𝑢🤣🤣🤣😂😂



A tsaye ta tarar da shi jikin Motar sa ransa a dagule tafiyarta ta gyara tana takun jan Aji Muryarta ta ƙaryar



"Yayana, Habiebie 🤍 yaushe kazo? Me yasa baka shiga daga ciki ba?"



A fusace ya ɗago yana Nuna ta da yatsa " Ke Noor Ba wannan ne ya kawo Ni ba ki dakata, zuwa nayi na faɗa miki ki sanar musu kar su sake su Ɗaura Auren nan dan sai kinyi dana sani tunda aka raba Ni da Hooriyah babu wata mace da zata same ni yanzu" ya faɗa yana watsa mata wani kallon banza tare da shigewa motar sa yayi tafiyar sa. Sagadee ta bishi da kallo zuciyar ta kamar zata fito Aa koma cikin gidan...









𝑯𝑶𝑶𝑹𝑰𝒀𝑨𝑯











A bangaren Hooriyah kuwa Depression ne mai tsanani ya kamata ba Abinda yake ɗaga mata hankali sai jin wai har ciki ta zubar shiyasa aka fasa Aure na farko ita da ko riƙe hannun namiji bata taɓa yi ba Indai ba Yayyun ta ba duk wanda yayi mata sharrin nan bazata yafe masa ba ya shafa mata tabon da ba zai taɓa goguwa ba. Bata tabbatar da tana son Zaaheed ba sai yanzu bata da aiki kullum tana cikin damuwa magana ma sai Sajeedah ta saka ta a gaba take yi ga kusan kullum sai ya kira ta Shiyasa ta kashe wayar tunda Auren shi saura kwana Uku. Tattarawa tayi take gida tayi musu kwana biyu ko zata samu sauƙin abinda take ji amma sai yafi da ƙaruwa dole ta dawo Gidan Sajeedah.











Anyi wa Abduljawwad Transfer zuwa Abuja a gurin aiki kuma dole a cikin satin zai koma Dan haka suka fara Shirin tafiya Hooriyah kuma ta shirya zata koma gida ganin halin da take ciki yasa yace zai ɗauke ta su tafi can ko zata manta da abinda ya faru bayan wani lokaci ta dawo. Da farko Daddy kin yarda yaso yi Mami da Aunty ne suka yi ta lallaɓa shi da kuma ganin halin da take ciki yasa ya amince suka tafi........................✍️







# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯







Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan





https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I





Follow My Pages





Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1





Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1





09047574404

WhatsApp Only





Comments & Share Fisabillah🥰👏







𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️


♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟏&𝟓𝟐


___________________________________________________________________________


Around 9:00 Pm


Cosgrove Smart Estate, Wuse, Abuja.


Anan aka sauke su gida ne Mai kyau da Bedrooms guda biyar sai palour da kitchen kowanne ɗaki da Toilet ɗin sa suna shiga kowa ɗaki ya nufa wanka da sallah Tayi tana kwanciya ta huta.

Washegari

Gyara gidan suka yi suka chanja abinda ba za'a rasa ba Su biyu suka yini sai gurin La'asar Sannan Yaya da yaran suka dawo bayan La'asar suma shiryawa suka yi zawa shopping da Park zaman gidan ba daɗi duk da a Kano ma ba fita suke ba.


💥💦


Duk da an hana yi mata Hukunci tana cikin wani yanayi Sashe aka ware mata a cikin gidan kowa tsoron zuwa gurin ta yake kar ta cutar da shi tunda wadda ta yarda da ita ma ta cutar da ita. Mutum ɗaya ce ta yarda zata iya zuwa kullum da safe tayi mata aiki ta dawo. Bata da aiki sai kukan nadama wanda ba abinda zai yi mata. Kwana Uku tayi a Sashe da safe wadda ke zuwa yi mata aiki tazo a kwance ta tarar da ita jijjiga tayi amma shiru hakan yasa ta fito da sauri. Da akwai Fadawa guda biyu a ƙofar sashen suna tsare ta. Ganin ta suka yi arikice
"Ta suma, kuzo ku gani ko zaku iya dubata"

"Ki yayyafa mata ruwa mana zata tashi" ɗaya daga cikin su ya faɗa
"Na yayyafa mata" itama ta Bashi amsa

"Sai ki haƙura ai" yace yana ɗauke kansa da cigaba da abinda yake

Wuce su kawai tayi cikin gidan ta nufa
"Ta suma kuzo ku taimake ni"

Yawan ci mutane sun firgita dajin zancen nata dan sun gane wa take nufi, Kowa tsoron shiga sashen yake "Wai ba zaku ƙara so ba ne kuga halin da take ciki?"

Da kyar aka samu mutum biyu suka bita suna zuwa ta raka su har ɗakin datake ɗaya ce ta duba ta salati suka ji ta saka tana cewa
"Kamar fa ta mutu"

"Ta mutu" wacce ke kula da ita ta maimata

"Ban tabbatar ba, Amma bari mu sanar a ciki"
Nan suka fita suka sanar a ciki. Likita ne yazo ya duba ta ya sanar musu ta mutu. Mutuwar ta doki mutane da yawa bayan Azahar aka kaita gidan ta na gaskiya. *Allah yasa mu cika da Imani, Amin*



Jikin Ammi ya ƙara warware wa tana jin sauƙi shirun da take yawan yi ne yake damun sa saka ta yayi dole sai ta shirya sun fita. A sirrance suka fice daga cikin gidan ko Mai martaba basu sanar wa ba hadiman tane kawai suka san sun fita suma sai da aka ja musu kunne kar a san sun fita.



✨💫


Jabi Lake Mall, ABUJA.


Tafe suke da Sajeedah
"Aunty Bari in duba ko akwai wani turare da nake ta nema ban samu ba"

"Ok sai kin dawo" Thom tace mata juyawa tayi tana nufar wurin Turaren. Duba su ta fara can ta gano wanda take nema "Yes shine" ta faɗa tana ɗan yin sauri zuwa gurin karo tayi da wani abu ɗagowa tayi dan ganin menene Mutum ta gani tsaye a gaban ta.


Tafe suke shida Ammi Hira yake ta yi mata kiran sa aka yi a waya ɗaga wa magana yake yana tafiyar ji yayi karo da wani abu a fusace ya ɗago Arba yayi da kyakkyawar Budurwa da sauri tace masa
"I'm sorry, I didn't know that would happened"

"Kamata yayi ki ringa kallon hanya in kina tafiya ba waige-waige ba"

"You should stop answering calls when you're walking sir" itama ta bashi amsa tana wucewar ta

Ammi Bata lura da abinda ya faru ba kawai giftawarta ta gani taɓa shi tayi
"Wace wannan kuma"

"Ammi ban san ta ba, bige Ni tayi"

"Ba abinda ya same ka dai" ta faɗa tana duba hannun sa

Hannun ta ya riƙe yana cewa"Ba komai Ammi"


🌟💕


Tunda suka koma gida yake wa Ammi zancen Yarinyar da suka haɗu dazu ta birge sa a nemo masa ita duk inda take. Hakan yasa Ammi ta sanar wa Sarki aka shiga neman ta da kyar aka samo information akan ta.


𝑍𝐴𝐴𝐻𝐸𝐸𝐷


A bangaren Zaaheed kuwa kamar yadda Mommy'n su ta sanar haka ne ya faru Ranar Juma'a bayan Idar da Sallah aka ɗaura masu Aure da Noor Kowa mamakin Auren yake ba sanarwa

Amarya Noor sai murna take ta mallaki Zaaheed ɗin ta shagalin su suka yi har dare lokacin da aka zo daukar amarya dan kukan da amarya take in za'a Kaita gidan miji Noor ko kwalla bata yi ba.


ABUJA


Zaune yake a gurin aiki kira ya samu daga Office ɗin MD da Sauri ya tafi dan jin menene Mutane biyu ya tarar a Office ɗin MD gaisawa suka yi sannan MD ya fara magana
"Abduljawwad waɗan nan mutanen da kake gani gurin ka suka zo daga Masarauta, suna so ka bi su za kuyi magana"
"Amma sir..."

"Babu komai ka bi su"

"Tohmm" yace masa kawai jikin sa a saɓule zuciyar sa cike da wasi-wasi suka tafi.
Isar su Fada sun nemi sanin wace Hooriyah ya sanar da su komai na rayuwar Hooriyah har fasa Auren ta da aka yi da dalili da kuma sharrin da aka yi mata. Suma suka sanar da su Yarima ne ya ganta kuma yana sonta da aure in sun shirya su ko a cikin satin za'a yi......
.....................✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/27, 2:32 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟑&𝟓𝟒


______________________________________________________________________________________


𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰𝙷


A bangaren Anisah Bata san wanda yake kanta ba an yanke mata ƙafa guda ɗaya kwanan ta Uku sannan ta farfaɗo babu kowa a gurin ta har Lokacin da aka kira mijinta aka sanar da shi cewa yayi Allah ya ƙara mata ita ta fita bai sani ba dangin Mahaifinta da suka zo daga Katsina ne suka zauna da ita komai suke mata tayi nadamar gudar su lokacin da take da dama da badan su ba yanzu babu mai kula da ita ga wadda ta dogara da ita ta rasu watan ta guda a asibitin sannan aka sallame ta.


Lokacin da suka koma gida Zaid baya nan sai wata suka tarar a gidan sai a waje suka jira shi ɗan hana su zamar mata a palour tayi Anisah sai kuka take ita da gidan ta amma wata banza ta hanata shiga sai gurin Magariba sannan ya dawo sun sanar da shi an sallame ta ne ta dawo kuma sunga wata a ciki ya sanar dasu Aure yayi ita sai dai ta koma BQ dan ciki yanzu na amaryar sa ne babu yadda ta iya dan yanzu bata da wani muhimmanci a gurin sa haka ta koma can da zama Wulakancin da yake mata yafi na da ga nasa gana matar sa



✨🦋



ɴᴏᴏʀ


A bangaren Noor kuwa abubuwa rincaɓewa suka yi bata taɓa tunanin haka ba tayi tunanin zata same shi da sauƙi tun daren da aka kawo ta bata Ganshi ba ko inda take bai zo ba kuma Taji shigowar sa washegari kafin ta tashi har ya bar gidan ita kaɗai tayi zaman ta har gurin sati sannan suka haɗu tayi ta yi masa magiya tana bashi haƙuri ya nuna bai San tana yi ba yayi tafiyar sa duk ta rame damuwa tayi mata yawa. Ga Mommy'n ta tun washegarin da aka daura Aure tabar Ƙasar shi kuma tun ranar da aka kawo ta ya turo mata text message duk abinda ta gani ita ta jawo wa kanta tunda baya sonta kar ta sake ta faɗa wa mahaifiyar sa inba haka ba a bakin Auren ta Shiyasa tayi shiru bata faɗa wa kowa ba.


Zaune take ta buga Uban tagumi Khairat ce take ta sallama ƙara so wa ciki tayi taɓa ta tayi tana cewa
"Lafiya na ganki haka sis"

A firgice ta ɗago "Lafiya lau ina su Hidaya" ya bata amsa

"Suna makaranta baki da lafiya ne?"

"Lafiya ta kalau me kika gani" ta faɗa tana yin murmushi

"Ba komai" zama tayi kusa da ita nan ta cika mata gaba da kayan ciye-ciye har Dare tana gidan sai da ta fito zata tafi tace
"Ni tunda nazo ban ga Yaya ba ko baya nan ne"

"Ya fita gurin aiki bai dawo ba" ta faɗa tana sosa ƙeya dan itama yau kwanan ta biyu bata Ganshi ba

"In ya dawo kya ce ina gaishe shi"

"Zai ji Insha Allah ki gaida su Hidaya da yaya"

"Zasu ji, ki koma ciki"

Tohmm tace tana shigewa tare da ɗaga mata hannu har ta fice



💦💥🤍



Sunyi da shi zai sanar da Iyayensu daga nan saji komai Shatara ta arziki suka haɗa masa da farko kin karɓa yayi sai da kyar ya karɓa gida aka maida shi maimakon Office da daddare ya kira Daddy ya sanar da shi ce masa yayi zaiyi tunani ya nema sa daga baya. Har kwana biyu Daddy bai kira ba Gashi shi kuma kullum sai an kira shi daga Fada yanke shawarar kiran shi yayi nan yace zai shigo Abuja gobe sa tattauna bayan yazo suka tattauna da daddare ya koma.

Bayan kwana biyu mutane daga Fada sunzo neman Aure An basu An saka daurin auren sati biyu suka tafi. Khaleesat kawai aka sanar wa sai ƴanuwan ta na cikin gida ko su Aunty Safiyya ba'a sanar wa ba dan kar a sake samun matsala.


Duk wannan abin da ake ba'a sanar mata ba suna tsoron kar tace shima yaudarar ta zai yi shiru suka yi in an ɗaura taji kawai. Sajeedah taso ta sanar mata amma yaja mata kunne dan haka tayi shiru. Ko da taga Daddy yazo bata kawo komai a ranta ba tayi tunanin har ya fara missing ɗin su ne ya biyo su.


Two Weeks Later🔥
Kano💦


Masallacin cike yake da Jama'a mai shela ne yake ta sanar wa "An ɗaura Auren Aminu Abubakar Muhammad da A'ishah Harith Yahya akan Sadaki Naira Dubu ɗari Biyu" kawai yake ta faɗa..................✍️


Wai ina Aunty Safiyya ne da Sulaiman ɗin ta 😜😂 shagali💃



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Yau dai nasan na gama burge readers Hooriyah'n ku ta zama amarya 💃 sai a haɗa min Party🤸


Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I


Follow My Pages


Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1


Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1


09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/29, 10:23 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡




https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷





тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم




𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟓&𝟓𝟔


_______________________________________________________________________________________




ᴀᴜɴᴛʏ sᴀғɪʏʏᴀ


Kwance take a Palour tana bacci Sulaiman ne ya shigo a guje "Umma! Umma!!" Yana kwalla mata kira tashi tayi "Har yanzu Sulaiman ba zaka yi hankali ba ne? Kana gani bacci nake ka tashe ni, Ko Sallama baka yi ba, kai dai ba zaka shiryu ba ina ta maka fafutukar

Please Login or Register in order to submit comment