Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai yiwu ta iya ganin shi ba.
Ana cikin wannan hali ne ya lura cewa gimbiya na satar kallo shi wanda ke nuna alamun so da ƙauna, nan take ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi a karo na farko ya ji wani abu ya ɗar su a ran shi wata 'ya mace ta ƙayatar da shi.
Muhassin ya buɗi baki cikin murmushi mai taushi har fararen haƙoranshi suka bayyana ya dubi gimbiya ya ce "Ya ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa idan har zan yi maku rakiya a wannan tafiya to akwai bana buƙatar wani lada face sharaɗi guda shine ke da mahaifinki za ku bayar da gaskiya ga Ubangijina, ku daina bautar gumaka da dodanni har abada".
Koda jin wannan batu sai gimbiya ta ja gwauron numfashi ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Na amince da wannan sharaɗi naka, kuma na tabbata cewa Ubangijin da ya baka nasarar tseratar da rayuwata daga sharrin zakanya zai baka nasara a wannan tafiya. Sai dai na manta ban faɗa maka cewa a wannan tafiya muna da shugaba wato boka kaddad, kuma shi ne ya san wajen da zamu samu abin da muka fito nema, saboda dukkan wani umarni muna karɓa ne daga gare shi"
Koda gimbiya ta zo nan a zancen ta sai ta juya ta yi taku ɗaya, take kuyangi suka yi mata jagora domin komawa zuwa sansanin da aka yada zango, take boka kaddad ya rufa masu baya fuskarshi a murtuke har gyatsine take yi, dakaru na biye da shi jarumi Muhassin ne a ƙarshe, 'yar gajeriyar tafiya aka yi aka iso izuwa sansanin kowa ya kunna kai izuwa cikin tantinsa, shi kuwa jarumi Muhassin sai ya koma gefe ya yi alwala ya haye bisa kan wani faffaɗan dutse ya fuskanci alƙibila ya fara sallah.
Wannan shi ne abin da ya wakana da su boka kaddad akan hanyar su ta nemo maganin makantar gimbiya Aslaima, wato tekun Baharul-imfal domin ɗauko ALLON TSAFI a cikin masifaffen kada.


***
Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin rundunar sarki Madsur da ta shugaban 'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir bisa jagorancin sadauki Huzlaif. Sai yaƙin ya zamo abin tsoro kuma tashin hankali domin ɓangarorin biyu sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, haniniyar dawakai haɗe da ihu da kururuwar MAZAJE ta cika dodon kunne, sararin samaniya ta yi duhu tamkar dare biyu ya haɗu waje guda,
Wohoho! Haƙiƙa maza sune maganin maza, idan ka ji an ce ga mugu na ɓarna bai haɗu da mugu ba ne, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha JININ SADAUKAI a artabun GOGA SHA FAMA, inda ace mutum yana wannan waje lokacin da sassan jikkunan bil'adama ke shawagi a sama, JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda, sai ya rantse cewa YAKIN DUNIYA ne ya taso domin hatta dawakan abokan gaba hari suke kaiwa junun su.
A ɓangaren sadauki Huzlaif kuwa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga abokan gaba suna zubewa ƙasa matattu tamkar yana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu. Haƙiƙa Huzlaif ya cika SARKIN SADAUKAI domin da ace mutum zai ga yadda yake yaƙin babu alamun gajiya a tare da shi, sai ya rantse cewa jikinshi na ƙarfe ne ba jini da tsoka ba, a wasu lokutan har da ƙafa make abokan gaba yake yana sanarwa kan shi hanya.
A ɓangaren sarki Madsur kuwa ya zamto tamkar ANNOBA ƊARI tsakanin dakarun Fitinatul-Amir duk inda ya sanya gaba sai ka ga gawarwaki na zubewa ƙasa, a wasu lokutan sai ka ga ya taka kawunan abokan gaba ya sanya KAIFIN TAKOBI yana sare kafaɗunsu suna zubewa ƙasa tamkar ruɓaɓɓiyar kabewa. Kai wasu lokutan ma badakare yake janyo wa daga kan dokin shi ya take mishi wuya ya sheƙa barzahu, ko ya gabza mishi wawan naushi a wuya ya jefar da gawarshi gefe guda.






BABI NA BIYAR






Lokacin da sarki Madsur da sadauki Huzlaif suka ga irin muguwar ɓarnar da suke yiwa junan su, sai zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su ƙone, domin hakan sai kowannen su ya ruga izuwa kan ɗan uwanshi yana mangare dakarun dake gaban shi domin samarwa da kan shi hanya.
Lokacin da suka iso daf da juna sai suka taru juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, suna artabun ne cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare. Sai da GWARAZAN JARUMAN suka shafe tsawon rabin sa'a suna wannan ɗauki ba daɗi har makamansu suka lalace suka yi jifa da su duka cire waɗansu sabbi a jikkunansu, suka sake kacame da sabon artabu da ya fi na ɗazu tare da canza salon faɗan su.
Ana cikin wannan GUMURZU ne kowannen su ya kaiwa abokin gwamin shi hari a fuska, cikin nasara suka yanki juna akan kumatu jini ya yi tsartuwa. Cikin zafin nama suka yagi wani baƙin yanki a tufafinsu suka ɗaure raunin domin tsayar da jini, sannan suka ja da baya kamar taku huɗu suka tsaya cak! Suna cirko-cirko suna haki tamkar waɗansu zakaru.
A lokaci guda tamkar haɗin baki suka sake yin kukan kura suka afkawa juna, kaico! Hakika KARON MAZA abin tsoro da tashin hankali, lokacin da jaruman biyu suka fara wannan sabon artabu a karo na uku sai abin ya yi tsamari yazamana cewa a wannan lokaci sun yiwa junan su miyagun raunuka jini na zuba a jikkunansu, ma'ana an yi KARE JINI BIRI JINI jiri na ɗibar su, ana cikin wannan hali ne suka zube ƙasa magashiyan numfashin su na fita saman-sama.
Lokacin da tawagar rundunonin biyu suka ga halin da jagororin su ke ciki sai aka tsayar da yaƙi suka ruga izuwa gare su, aka ɗauke su kowannen su ya durfafi sansanin sa.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin dakarun sarki Madsur da ta sadauki Huzlaif shugaban tawagar dakarun sarkin 'yan fashin duniya.




Lokacin da ma'aji Kulairu ya durfafi ƙofar fita daga cikin gidan sarauta dakaru na take mashi baya, bayan ya samu nasarar hallaka wannan hadimi mai ɗauke da sura irin ta waziri Yazid, kuma ya yi umarni an shiga da sarki Nu'umanu izuwa turakarshi domin ba shi taimakon gaggawa sakamakon sukar takobin da hadimin ya yi mishi.
Sai suka ci-gaba da ratsa saƙo da lungu na gidan suka hallaka dakarun sumame. Lokacin da suka shiga gari sai ƙarin waɗansu dakarun suka rufa masu baya, suna masu ƙwalla kabbara da ƙarfi suka tari abokan gaba aka ruguntsume da azababban yaƙi.
Sa'adda mata,yara da tsofaffi suka ji gari ya kaure da kabbarar dakarun musulunci sai suka shiga addu'a suna kai kukan su wajen Ubangijin Musulunci akan ya bawa MUJAHIDAI RINJAYE. Al'amarin da ya jefa tsoro a zukatan dakarun sumame kenan.
Duk inda Kulairu ya sanya a gaba sai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar yana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu.
A ɓangaren dabarun sumame kuwa duk inda waziri Yazid da sarki Rakibu suka sanya a gaba sai dai ka ga dakarun musulunci na zube ƙasa, lokacin da waziri Yazid ya fahimci cewa idan aka cigaba da wannan artabu a haka dakarun musulunci za su samu nasarar murƙushe su, sai kawai ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi yana mai nuna sarki Rakibu da sarkin yaƙi Lauzar da yatsanshi na hagu take suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba.
Sa'adda sa'a ɗaya ta shuɗe a dai-dai wannan lokaci ne dakarun musulunci suka samu galaba akan dakarun sumame, nan fa gari ya kaure da koke-koken yara da mata, kaico! Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda yara ke rungume da gawarwakin mahaifansu suna rusa kuka dole ya kamu da matuƙar tausayin su, har ƙwalla ta cika masa idanu, babu abin da zai ɗimauta mutum face irin mugun kisan da aka yiwa jama'a waɗansu an farke cikinsu tumbinsu ya fito waje, wasu an sare kawunan su wasunsu ƙafafu da hannuwa abin babu kyawun gani.


***
Koda ficewar hadimi Masnur daga tantin sai sarki Lamsarul-Azlam ya runtse idanuwanshi ya karanto waɗansu ɗalasimai, yana gama rufe bakinshi sai wani narkeken aljani ya bayyana a gare shi, aljanin yakasance mummuna mai kwarjini da ban tsoro, yana da ƙwala-ƙwalan idanu masu girma tamkar gwanda, hancinshi a takure yake kofofin sirara tamkar ba da su ne yake shaƙar iska ba, bakinshi makeke ne mai kama da bakin rijiya, a tsakiyar kanshi yana da dauƙe da wani ƙaho irin na ɓauna, gwiɓin hammatarshi yana ɗauke da waɗansu fuka-fukai guda huɗu irin na jemage,
Hakika komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da wannan aljani dole ya ɗimauce.
Aljanin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sarki ya dube shi cikin kakkausar murya ya ce "yakai Husubul-luzwar ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa sansanin dakarun musulunci ka ɗauko mini sarki Rayyan a raye cikin ƙoshin lafiya, ka kawo shi izuwa gare ni"
Koda jin wannan batu sai Husubul-luzwar ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "An gama ya shugabana amma kar ka manta cewa akwai wani sirri da sarki Rayyan da jama'ar shi ke amfani da shi wanda matukar ka kusance su sai komai naka ya lalace, sannan kar ka manta cewa wannan shine aiki na ƙarshe da zan yi na samu 'yanci daga ƘANGIN BAUTA a ƙarƙashin ka",
Koda jin wannan batu daga bakin Husubul-luzwar sai sarki Lamsarul-Azlam ya dube shi ya ce "kar ka bawa maza kunya mana kaine fa ANNOBA ƊARI mai saukar da gajimaren musifa, magajin GAWUTACCIYA kake mai shanye JININ SADAUKAI, SARKIN SADAUKAI kake duk wanda ya ja da kai zai faɗa TURBAR AJALI"
Lokacin da sarki ya zo nan a kirarin sai Husubul-luzwar ya kama tsuma yana kyarma, ganin jikinshi ya mimmiƙe ya buɗi ya ce "kwantar da hankalinka ya mai duniya na rantse da gemun kakana boka Luzwar sai na kawo maka sarki Rayyan cikin ƙoshin lafiya".
Yana gama faɗin hakan ya bugi ƙasa da hannunshi ɗaya ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba, kawai sai sarki Lamsarul-Azlam ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya ƙwallawa sarkin yaƙin shi kira bayan ya bayyana gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa sai ya dube shi ya ce "ya dirkar birnin Darul-Ashmar ina so ka tafi izuwa masarauta ka ƙaro mana dakarun yaƙi mafiya ƙwarewa a harbin kibiya ka tabbatar ka sanya a cikin duhuwar bishiyun dajin dake dai-dai wajen da zamu fafatawa a da abokan gaba, za su amfani ne a lokacin da za mu gwabza domin za su yiwa abokan gaba MAMAYAR BAZATO".
Koda jin wannan umarni sai sarkin yaƙi ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice daga cikin tantin ya kama dokinshi ya haye ya sakar mishi linzami ya sukwane shi ya durfafi hanyar fita daga sassanin.
Wannan shi ne abin da ya wakana a sansanin sarki Lamsarul-Azlam.








BABI NA SHIDA


Koda ɓacewar makiyar sai sadauki Fitinatul-Amir ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu wanda ya ɗimauta duk wata halitta dake fadar, jama'a suka shiga guje-guje gami da ifice-ificen tsira da rayuka, domin rabon da Fitinatul-Amir ya yi wannan kururuwa yau tsawon shekaru ashirin tun ranar mutuwar Mahaifiyarshi.
Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa talatin a cikin wannan hali sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya ɗauko madaidaicin madubin tsafi a cikin aljihun rigarshi ya shafe shi da hannunshi na hagu yana mai runtse idanuwanshi gami da karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi sai ga taswirar mikiyar ta bayyana a sararin samaniya ɗauke da Rusayyat, Usaiba mai hatimin takobi tare da Hairat, tana tsala gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya ƙwallawa 'yan majalisar shi kira cikin hanzari suka fito daga maɓuyar su jikkunansu na ƙyarma! Kaifin ɗayan su ya furta wani abu ya nuna su da ɗan yatsanshi na hagu nan take shi da su suka bayyana akan wata jibgegiyar mikiya mai kwarjini daban tsoro, cikin hanzari mikiyar ta tashi zuwa sama ta ratsa rufin fadar ta ɓace ɓat! a sararin samaniya.


***
Al'amarin wannan mikiya kuwa da ta ɗauki Rusayyat uwar shugaban 'yan fashin duniya, yaro Usaiba tare 'yar uwarshi Hairat, sai ta yi wanzu tana ratsa giza-gizai babu sassauci. Duk wannan tafiya da ake yi su Usaiba ba su san halin da ake ciki ba domin suna cikin halin suma su duka ukun.
Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe a wannan lokaci ne ta iso wani ƙasaitaccen daji domin haka sai kawai ta saki fuka-fukanta ta yi ƙasa luhhhh! Ta sauka a turba a daf da wata ƙorama mai ɗauke da ruwa garai-garai, kawai sai ta gicciya gadon bayanta ta sauke su yaro Usaiba, sannan ta kafa bakinta a ƙoromar ta guntsi ruwa ta fesa masu, Rusayyat ce ta fara farfaɗowa ta hanyar buɗe idanuwanta, sannan yaro Usaiba yana mai jan dogon gwauron numfashi, Hairat ce a ƙarshe tana mai motsa ƙafafuwanta, nan take kowannen su ya yunƙura domin ya miƙe zauna amma sai hakan ya gagara bisa dole kowanne ya haƙura zukatansu na bugawa cike da matuƙar tsoro da firgici.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka ji wani abu mai nauyi ya sauka a daf da hanyar shigowa dajin, ba wani ba ne face sadauki Fitinatul-Amir tare da 'yan majalisar shi guda sha biyu zaune a bisa kan wannan mikiya.
Da yake tazarar dake tsakanin su bata huce taku talatin ba dai aka fara kallon-kallo na tsawon daƙiƙa goma, daga can wannan mikiyar da ta ceci rayuwar su Usaiba ta yi girgiza take ta rikiɗa izuwa surar wata kyakkyawar budurwa.
Budurwar takasance mai matsakaici jiki mai launin fata wankan tarwaɗa tana sanye da tufafi na fatun dabbobin daji da suka kama jikinta har surar kyawun ƙirjinta ya bayyana a tsaye suke ƙyam! Basu rankwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi, ƙugunta daga gaba a tsuke yake ta baya kuma ya yi tudu inda za a sanya tuffa zata ita zama daram, dara-daran idanuwanta farare ƙyal da baƙin cikinsu ya kasance siɗik mai kwarji da haiba haɗi da yalwataccen gashin kanta da ya zuba har ƙasan kwankwasonta sune abubuwan da suka sake tona asirin kyawun ta.
Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kamu da matuƙar ƙaunar ta.
A gadon bayanta tana rataye da wani rantsattsen Kwari da baka da kwansonta, a kwiɓin cinyarta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta.
Sa'adda shugaban'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir ya yi arba da kyakkyawar budurwar sai ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi,
Ita kuwa sai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta,
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya daka mata tsawa wacce ta sanya hantar cikin 'yan majalisar shi ta kaɗa saboda firgici, amma bisa mamaki sai ga ko gezau ba ta yi ba, sai da ta yi dariyar ta ishe ta sannan daga bisani ta tsahirta ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai tamkar sarewa cike da taƙama da BAƘAR IZZA ta ce "ya kai Fitinatul-Amir ka yi sani cewa na ɗauki tsawon lokaci ina tsumayen zuwan wannan rana da zan yi GABA DA GABA da kai domin ɗaukar fansa, haƙiƙa na san ba ka san ko ni wece ce ce ba wannan ba abun damuwa ba ne amma na san cewa baka mance wane ne sarki Kushuful-Himras ba, ni 'yarshi ce Shalmirat bintu Kushuful-Himras";
Koda jin wannan batu daga bakin Shalmirat sai idanun Fitinatul-Amir suka zazzaro ya cikin matuƙar firgici ya nuna Shalmirat da ɗan yatsanshi bakinshi na kyarma ya ce "ke 'ya ce ga sarki Kushuful-Himras?






BABI NA BAKWAI




Shalmirat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu sannan daga bisani ta murtuke fuska ta ce "shin kana tunanin cewa ka kashe mahaifina da jama'ar birninmu a banza? Haƙiƙa ka kashe maciji ne baka sare kanshi ba.
Babban kuskuren da ka yi shine bayan ka ƙone dukkan gidaddajinmu ka shafa'a baka rushe wani ɗakin bauta ba, abin da baka sani ba shine lokacin da mahaifina ya fahimci cewa babu wata halitta da zata tsira da rayuwar ta a cikin jama'arshi, sai ya ɗamƙa min dukkan sirrikan tsafin shi ta hanyar busa mini wani koren hayaƙi daga bakinshi, sannan ya sanya ni a ciki ɗakin bautar ya janyo ƙofar ya rufe, sannan ya ruga izuwa filin daga.
Tun daga ranar da na rasa mahaifina na rasa duk wani farin cikin rayuwata, babu abin da idan na tuna yake sanya ni zubar da hawaye face yadda ka yiwa abbana yankan rago ka farke cikinshi ka fito da zuciyarshi ka daddatsa ta da takobi ka cinye ta a haka, hatta lokacin da ku kazo giftawa ta daf da ɗakin bautar ina rusa kuka amma ba ku iya jina ballantana gani na, sakamakon sirrikan tsafin abbana dake bani kariya";
Lokacin da Shalmirat yazo nan a labarin ta sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta.
Shi dai Fitinatul-Amir bakomai ne ya sanya hallaka sarki Kushuful-Himras ba sai domin bisa binciken da ya gudanar a halarar tsafin shi ya gano cewa shine sarkin da anan gaba zai ɗara shi tarin dukiya da ƙarfin sihirin TSAFI. Bisa wannan dalili ya sanya ya aika manzo gare shi domin ya yi MUBAYA'A a gare shi, amma saboda kare martabar al'ummar shi ya sanya ya ƙi bayar da haɗin kai, domin hakan sai Fitinatul-Amir ya jagoranci rundunar MAYAƘA ya afkawa birin su Shalmirat da rana tsaka.
Koda jin wannan batu daga bakin Shalmirat sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan daga bisani ya murtuke fuska ya dubi Shalmirat cikin gadara ya ce "haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tsammanin cewa za ki iya GABA DA GABA da ni shin kin manta ne cewa mahaifinka ma da ya kasance JARUMIN KWARAI na ga bayan shi ballantana ke karan kaɗa miya kuma ƙaramin alhaki, ina mai tabbatar miki da cewa take yanzu ba tare da wani ɓata lokaci na zan aike da ruhinki Izuwa duniyar da ba'a dawo wa, sannan na kashe babban maƙiyi na Usaiba mai hatimin takobi da 'yar uwarshi Hairat";
Kafin Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi Shalmirat ta tari numfashi tana mai daka mishi tsawa, sannan ta zare takobinta take koren haske naban mamaki ya dinga fita daga jikin takobin yana shiga jikin su yaro Usaiba, lokacin da ya kammala shiga nan take wani irin gagarumin ƙarfi ya shige su suka miƙe zumbur tamkar babu rauni a tare da su.
Sannan ta riga Izuwa kan Fitinatul-Amir tana ihu da kururuwa mai firgitarwa, koda ganin hakan sai yaro Usaiba, Hairat da Rusayyat suka rufa mata baya suna masu yin ɗauki kan yan majalissa su sha biyu batare da sun riƙe wani makami ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da wannan mikiya bayan ta ceto rayuwar su Usaiba mai hatimin takobi daga hannun shugaban'yan fashin duniya.
Al'amarin su boka kaddad kuwa tunda duku-dukun safiya bayan anyi kalaci sai aka cigaba da tafiya ba aka kan aljani Ramsisul-Ayyam, ana tafiya cikin hanzari tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya a cikin gajimare. Sai da aka shafe tsawon mako guda ana tafiya, a iya tsawon wannan tafiya babu abinda ke sanya wa ayada zango face idan lokacin ibadar jarumi Muhassin ya yi ko gimbiya na buƙatar bawali, ko kuma za a yi kalaci hatta barci da abisa kan Ramsisul-Ayyam ake yi.
A ranar kwana na takwas ne da la'asar sakaliya Ramsisul-Ayyam ya sauka a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin bishiyu, ƙaramu, duwatsu da sarƙaƙiya, babu wata halitta mai numfashi da zata tsinci kanta a cikin daji face tsoro da firgici sun mamaye ta, babu abin da zai sake ɗimauta mutum face yadda dajin yakasance tsit! Tamkar babu wata halitta mai rai domin koda kukan tsuntsu babu.
Lokacin da aka sauka ne fa kowa ya sha jinin jikinshi kuma ya zare makaminshi domin yin shirin ko ta kwana.
Boka kaddad ya dubi Ramsis ya ce "kai zaka tsaya anan ka kare lafiyar gimbiya da kuyangin dake yi mata hidima;
"An gama ya shugaban";
Ramsis ya faɗa cikin ladabi.
Sannan kaddad ya mayar da duban shi ga jarumi Muhassin fuskarshi a murtuke babu annuri cikin kakkausar murya ya ce "ya kai Muhassin ka yi sani cewa bamu buƙatar taimako daga gare ka a duk wata musiba da zamu shiga sai idan dukkan wata dubara ta gaza, sai ka nemi taimakon na ka Ubangijin da kake iƙirarin cewa shine mahaliccin kowa.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai boka kaddad ya sake zare wani makamin a jikinshi yazamana cewa yana riƙe da guda biyu,
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ganyayyakin tsirrai na motsawa, alamun dake nuna cewa akwai abu mai numfashi da ya yi tajalli a wajen. Al'amarin da ya sanya kowa ya dage kuben takobinshi kenan,
Daga can sai aka ga waɗansu irin gabza-gabzan dakaru suna yin fitar burgu daga cikin duhuwar bishiyu, waɗansu ya sakkowa daga kan rassan bishiyun, su dai dabarun sun kasance masu ƙirar samudawan farko suna da girma tamkar toron giwa, suna sanye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, suna ɗauke da miyagun makamai fiye da nau'i arba'in, fusakunsu baƙaƙe ne wuluk masu muni tamkar basu taɓa dariya ba, adadin su kuwa ba zai ƙidayu ba, idan mutun ya kai duban shi babu abinda zai gani face kawunan su birjik babu masaka tsinke.
Kaico! Haƙiƙa waɗannan dabaru sun cika ANNIBA ƊARI babu wani jarumi da zai yi tozali da su face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Shi kan shi Ramsisul-Ayyam duk da kasancewar shi matashin aljani sai da ya ɗimauce da ganin dakarun, jarumi Muhassin ne kaɗai bai razana ba shi ma addu'o'i ne ke ɗawainiya da shi.
Nan fa aka fara kallon-kallo a tsakanin su na tsawon daƙiƙa hamsin ba tare da wani ya yi yunƙurin farmakar abokin gabar shi ba.
Kawai sai samudawan suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa DANDAZON MAYAƘA suka yi ɗauki kan su boka kaddad suna masu ɗaga makamansu Izuwa sama.
Koda ganin hakan sai jarumi Muhassin ya ƙwalla kabbara ya yi ɗauki kan su, boka kaddad da tawagar dakarun rakiya su kayi koyi da shi suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, shi kuwa Ramsisul-Ayyam sai ya tsaya a kofar tantin gimbiya domin kare lafiyar ta hannunshi riƙe da wata garkuwa ta baƙin ƙarfe gami da wannan zabgegen zatari mai KAIFI DA TSINI.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka yi GWAGWARMAYA a DUNIYAR MAYAƘA, haƙiƙa yaƙi abin tsoro ne kuma tashin hankali, lokacin da TAWAGA BIYU suka yi KARON BATTA sai ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne suna amsa kuwwa Izuwa cikin daji, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, bishiyu suna dinga karairaye wa suna faɗuwa ƙasa, a duk sa'adda ɗaya daga cikin dakarun ya kai wa su boka kaddad hari idan suka kauce duk abin da makamin ya sauka a kan shi sai kaga ya tarwatse ya yi bindiga koda kuwa dutse ne .
Ana fara wannan artabu ne su boka kaddad suka fara gane cewa haƙiƙa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi, domin matuƙar zafin naman dakarun ya ninka na su sau arba'in, kuma suka fahimci cewa idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka dakarun za su iya murƙushe su. Nan fa hankulan su suka DUGUNZUMA ainun.




Wane ne zai samu nasara a wannan yaƙi tsakanin samudawan dabaru da su jarumi Muhassin?




Wane ne zai samu nasara tsakanin Jaruma Shalmirat da shugaban 'yan fashin duniya sadauki

Please Login or Register in order to submit comment