Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwaranya a kan tekun, fuskarshi ta yi baƙi wuluk! Idanuwanshi da harshen sun zazzago, kaico! Tir da mutuwar fasiƙi maƙiyin Allah da Manzonshi, inda ace yana tsaye a wannan waje zai ga yadda boka kaddad ya yi mutuwar wulakanci, dole ne ya ji tsoron Ubangiji ya kama shi, domin babu wani abun halitta da ya gagare shi hukunci.
Cikin matuƙar farin ciki Muhassin ya sakarwa Aslaima wani kyakkyawan murmushi, take ta mayar mashi da martani cikin annuri, sannan ya juya ya dubi Ramsisul-Ayyam ta ce "ya kai wannan aljani shin za ka bayar da gaskiya da ubangijin halitta ko kuwa ka zaɓi ka yi mutuwar hasara tamkar yadda mai gidanka ya yi";
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai Ramsisul-Ayyam ya ce cikin ladabi "ya shugabana ai tuni na imani da ubangijinka tsoron ubangidana ne ya hana ni bayyana wa, yanzu a shirye nake na shiga addinin ka".
Koda jin hakan nan take Muhassin ya karanta KALMAR SHAHADA Ramsisul-Ayyam ya maimaita.
Faruwar hakan ke da wuya nan take duk wani gashi dake jikinshi da ya sanya mashi muni ya ɓace ɓat! Kuma ya ji wani ƙarfi da nutsuwar zuciya ta musamman ta same shi.
Muhassin ya ci-gaba da cewa "ya kai wannan aljani ka yi sani cewa sunan da ake kiran ka da shi baya da wata ma'ana a Musulunci yanzu zan canja maka shi izuwa ABU-AYUB, sannan yanzu sai ka ɗauke mu daga nan izuwa birnin su gimbiya Aslaima";
Abu-Ayub ya risina ya ce "an gama ya shugabana, amma a shawara ta a ciro ALLON TSAFI daga cikin wannan kada domin kar wani ya mallake shi ya cutar al'umma".
Muhassin ya ce "kwarai kuwa haƙiƙa ka kawo shawara mai kyau, nan take ya karanta Ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi ya tofawa kadan, nan take ya kama da wuta ya ƙone ƙurmus!
Kawai sai Abu-Ayub ya shimfiɗe gadon bayanshi jarumi Muhassin da gimbiya Aslaima suka hau bisa kan shi suna yin bisimilla, sannan ya yunƙura yana tashi zuwa sama ya na mai kaɗa fuka-fukanshi ya ɓace ɓat! Cikin gajimare.
Sa'adda aljani Abu-Ayub ya wanzu yana keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya, sai aka tsawon sa'a ɗaya ana tafiya babu sassauci.
Ana cikin wannan hali ne gimbiya Aslaima ta buɗi baki sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya masoyina abin alfaharina ka yi sani cewa a halin yanzu ƙaunar da nake yi maka ba zan iya misalta taba, ina jin zan iya rasa rayuwata idan babu kai, ka zamto tamkar gudan jini dake kewaya wa a zuciyata, soyayyar ka ta zamto tamkar bugun numfashi na, ina godiya ga Ubangiji da ya bani abin ƙauna ma'abocin kwarjini, SADAUKANTAKA da DAUKAKA DA BAIWA".
koda jin waɗannnan daɗaɗan kalamai daga bakin Aslaima sai 'yar ƙaramar dariya ta suɓucewa Muhassin har kunci shi suka loma fararen haƙoranshi suka bayyana cikin tattausar murya ya ce "ya abar bege na a dare da rana ki yi sani cewa ni ina sonki ne tsawan rayuwa, dukkan wani abu da ya shafi rayuwar mu addini ya tsara mana shi, Ubangiji ya umarce mu mu ƙaunaci ababan ƙaunar mu da Allah, domin idan saboda da kyawu, kuɗi ko mulki ne wata rana za su gushe;
Inda ace kin taɓa karanta hikayar littafin JARUMAN DUNIYA za ki ji yadda yarima Muzaifar da ya kamu da soyyyar almajira Sharilat yar tsoho Kuhairu da za ki tabbatar da cewa soyyya ta gaskiya babu ruwan ta da dukiya, mulki ko nasaba";
Da jin wannan batu sai gimbiya Aslaima ta gyaɗa kai cikin annurin fuska ta ce "haƙiƙa wannan bayani ya sanya na ƙara ƙaunar Ubangiji domin bai bar wani abu mai muhimmanci na rayuwar mu ba face ya tsara mana yadda za mu yi, kuma bayan an ɗaura mana aure sai na karanta littafin JARUMAN DUNIYA domin jin irin darussan dake cikin shi.
Koda gimbiya ta zo nan a zancen ta sai su duka biyun suka bushe da dariyar farin.
Daga bisani jarumi Muhassin ya dubi Abu-Ayub ya ce "akwai buƙatar mu yada zango anan domin mu yi sallah mu samu abun kalaci tun da guzurin mu ya ƙare"
Koda jin wannan umarni sai Aljani Abu-Ayub ya risina cikin ladabi ya ce "an gama ya shugabana;
Yana gama faɗin hakan ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a turba.
Inda aka sauka ya kasance daji mai ɗauke da bishiyoyu, duwatsu tsilli-tsilli gami ƙoramu, kuma dajin ya yi tsit tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikin shi.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan. Cikin hanzari Muhassin ya yunƙura ya sakko daga kan aljani Abu-Ayub gimbiya Aslaima tayi koyi da shi, suka durfafi wata ƙorama Abu-Ayub na biye da su, ya yin da suka isa sai suka tsafta ce jinin dake jikin tufafin su suka suka ɗaura alwala, sannan Muhassin ya shige gaba ya tayar da iƙama ya tayar da sallah.
Bayan an kammala ne Muhassin ya yi gyaran murya dubi abokan tafiyar shi ya ce "ya ku abokan tafiyata ina ganin bai kamata mu yada zango anan ba akwai buƙatar mu ƙara yar tafiya kaɗan.
Koda gama faɗin hakan sai Muhassin ya miƙe tsaye ya shige gaba gimbiya Aslaima da aljani Abu-Ayub suka mara mashi baya a ka ci gaba da tafiya.
Ana cikin wannan tafiya ne aka hango wani gida guda jal da aka yi ginin shi da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske a wannan lokaci ƙofar gidan a buɗe take alamun dake nuna akwai halitta a ciki,
Sa'adda aka yi arba da gidan sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, Abu-Ayub ya dubi Muhassin ya yi gyaran murya cikin ladabi ya ce "ya shugabana shin zamu shiga cikin wannan gida ne domin mu ga abin da ke ciki ko kuwa zamu ƙetare?
Koda jin wannan tambaya sai Muhassin ya yi shiru yana mai zurfafa cikin kogin tunani daga basani ya dube shi ya ce "akwai buƙatar mu duba ɗin sai dai ina so kar ku shagala da addu'a domin kariya daga dukkan abin cutarwa;
Da jin wannan batu sai dukkannin su suka gyaɗa kai alamar gamsuwa. sannan aka durfafi gidan aka shiga izuwa cikin shi, sai da aka yi tafiya mai tsawo a cikin zaure sannan aka iso farfajiya, daga ciki gidan ya kasance ƙasaitacce mai matuƙar ƙawatuwa yana ɗauke da ɗakuna biyar.
Nan fa aka dinga shiga ɗakunan amma wayam! Babu komai, lokacin da aka shiga ɗaki na biyar ne aka ga wani abun mamaki.
Bakomai aka gani ba face kayan tsubbe-tsubbe nau'i dabam-daban, babu kyawun gani a tsakiyar ɗakin an ajiye wani dogon teburi na azurfa, bisa kan teburin wani kyakkyawan yaro ne mai kimanin shekaru sha uku an ɗaure hannayen shi da waɗansu irin sarƙoƙin tsafi, hawaye na zuba daga idanuwanshi.
Koda ganin halin da yaron ke ciki sai kowa dake wajen ya kamu da matuƙar tausayin shi, kawai sai Muhassin ya matsa daf da yaron ya karanta Ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi ya tofa a jikin sarƙoƙin take suka narke suka zamo ruwa suka ɗige a ƙasa.
Cikin farin ciki yaron ya yunƙura ya sakko daga kan teburin,
Har Muhassin ya buɗe baki da nufin ya ce wani abu, kawai sai aka ga wani dubu ya mamaye ɗakin ta yadda ko tafin sannu mutum ba zai iya gani ba.
Sannu a hankali duhun ya dinga curewa waje guda ya rikiɗa izuwa wata mummunan tsohuwar aljana,
Tana shirye gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a hannayenta tana ɗauke da zaratan takubba masu KAIFI DA TSINI fuskantarta a murtuke babu annuri tamkar an aiko mata da WASIKAR MUTUWA.
Duk da dakewar zuciyar su jarumi Muhassin sai da suka ji hantar cikinsu ta kaɗa,
Aljanar ta taƙarƙare ta daka masu wata tsawa da ta haddasa raurawar ɗakin, daga bisani ta haɗe ta buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ta ce "ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa haƙiƙa tafka babban kuskure da kuka shiga gona ta, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai fice daga wannan gida a raye ba";
Kafin aljanar ta gama rufe bakinta Muhassin ya yi ƙarfin hali ya tari numfashinta yana mai cewa "ƙaryar ki ta sha ƙarya yake wannan la'ananniya kuma tsohon AZZALUMA ba za ki taɓa samun nasara akan mu ba da yardar Annabi Rahma, zaɓi biyu zan ba ki ki ɗauki ɗaya, ko dai ki miƙa wuya zuwa ga addinin Allah ki daina shirka da tsafi ki dawo bisa TAFARKIN TSIRA, ko kuma ki yi mutuwar wulakanci".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai aljanar ta fusata ainun ta sake daka masu tsawa a karo na biyu ta ce "na rantse da gemun kakana boka Zanzamul-Auƙat sai na yi maku kisa mafi muni ta hanyar gididdiba naman jikkunanku ta yadda koda tsuntsaye ba za su mu na yin kalaci ba, sannan na yanka yaro mai hatimin takobi na shanye jininshi domin cika burina na zamtowa GAWURTACCIYA uwar hatsabiban duniya.
Koda aljanar ta zo nan a zancen ta sai ta taƙarƙare ta kwarara ihu mai firgita DANDAZON MAYAKA a FILIN DAGA ta ɗaga takubbanta ta ruga izuwa kan su Muhassin.
Koda ganin hakan sai Muhassin, Aslaima da Abu-Ayub suka zare makaman su suka ruga izuwa gare ta aka tari juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini, muni da tashin hankali.
Cikin hanzari yaro usaiba ya ruga izuwa can gefe yana kallon fafatawar da ake yi.
Aljanar ta wanzu tana kai masu miyagun hare-hare ta sama da ƙasa, su kuwa suka wanzu suna kare hare-haren tare da mayar da martani cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA da suka saba yin KARON BATTA a BIRNIN SADAUKAI.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA ya fi ƙarfin ƙananan ƙwari, idan gwani da gangaran suka yi KARON BATTA dole yaƙi ya zamo abin sha'awa da tashin hankali.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari da sittin ana wannan ɗauki-ba daɗi babu nasara ga kowa ne tauraro har ya zamana cewa gwanayen sun lalata duk wani abu mai muhimmanci a ɗakin sun fara rushe ginin duk da irin ƙwarin shi.
Ba shiri yaro Usaiba ya ruga ya fice daga ɗakin domin tsira da rayuwar shi, domin dai masu iya magana na cewa 'faɗan da yafi ƙarfin ka sai ka mayar da shi kallon.
Ana cikin wannan hali ne Muhassin ya sanya takobinshi ya kaftawa aljanar sara a kanta take takobin ta fasa hular kanta ta fasa kwanyarta. Kawai sai ta faɗi ƙasa tana mai shure-shuren mutuwa, jim kaɗan sai komai na jikinta ya sandare, ashe shirin tsafin aljanar yana cikin hular kanta.
Koda samun wannan nasara sai aka nufi inda yaro Usaiba yake, jarumi Muhassin ya dube shi ya ce " ya kai wannan kyakkyawan yaro shin mene ne labarin ka kuma mene ne abin da ya haɗa ka da wannan aljana?
Koda jin wannan tambaya sai nan take Usaiba ya kwashe labarin abin da ya wakana tsakanin su da Fitinatul-amir tun daga farko har ƙarshe ya zayyanawa Muhassin.
Koda jin wannan labari sai kowa ya cika mamaki ainun, ba tare da ɓata lokaci ba aka cigaba da tafiya, ana cikin tafiyar ne Usaiba ya dubi Muhassin ya ce "ya kai wannan GWARZON GAWAZA so ɗazu lokacin kana magana da wannan aljana na ji ka ambaci Ubangiji shin wane ne shi";
Koda wannan tambaya sai Muhassin ya yi murmushi a gare shi ya ce "Tabbas Ubangijina shine ya halicci komai da kowa babu wanda ya samar da shi kuma babu abin da ya gagare shi, kuma shine ke taimako na a wannan yaƙi da muka yi.
Usaiba cikin mamaki ya ce "haƙiƙa girma da buwayar Ubangijin ka ya kai, idan har ka taimaka mana ni da ummana muka kawar da Fitinatul-amir za mu bayar da gaskiya da wannan Ubangiji na ka;
Muhassin ya gyaɗa kai ya ce "babu damuwa da yardar Ubangiji".
Daga wannan furuci kowa ya yi shiru aka cigaba da tafiya, tafiyar daƙiƙa arba'in aka yi aka hango su Rusayyat suna tsaye suna kai komo, daga Usaiba ya hango ummar shi sai ya ruga gare ta suka rungume juna cikin farin ciki daga bisani suka janye jiki Usaiba ya buɗi baki da nufin ya sanar da ita labarin abin da wakana tsakanin sa da su Muhassin.
Amma sai Rusayyat ta dakatar da shi ta hanyar duban Muhassin ta ce "ya kai GWARZON MAYAKI ka yi sani cewa mun ga dukkan abin da ya wakana tsakanin ka da ɗana kuma ni da 'yar uwata mun gamsu cewa yadda ubangijin ka ya baka nasarar tseratar da yaro na zai baka nasara wajen kawar da mai gidana Fitinatul-amir, muna masu yi maka alkawarin karɓar addininka bayan mun yi nasara.
Koda jin wannan batu sai Muhassin ya ɗago fa kanshi koda ya haɗa idanu da jaruma Shalmirat take suka ji wani abu ya ɗar su a zukatansu a karo na farko a rayuwar su.
Sannan ya buɗe baki ya yi gyaran murya ya ce "haƙiƙa ina mai tabbatar maku da cewa zamu yi nasara da yardar Ubangijin Musulunci.
Ashe duk wannan abu da ke faruwa gimbiya Aslaima ta lura da irin kallon da jaruman ke biyu ke yiwa Muhassin don haka nan take ta ji kishi ya turnuƙe ta, domin ta lura cewa dukkaninsu suna yi masa kallo ne mai tattare da tsantsar so da ƙauna.
Ana cikin wannan hali ne aka jiyo haniniyar dawakai gami da ƙarar takun sawaye ta cika dajin baki ɗaya, domin haka sai kowa ya zare takobinshi aka ruga izuwa iyakar dajin. Nan take aka ji arba da wata ƙasaitacciyar runduna mai matuƙar kwarjini daban tsoro, babu wani sadauki da zai yi arba da rundar dole ya ɗimauce domin a iya kiranta suna ANNOBA DARI. Kai ko makaman yaƙinsu ma abin tsoro ne.
Ba wani ba ne ke jagorantar tawagar face sadauki Fitinatul-amir, yana shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi ta baƙaƙen sulke, jikin shi cike da guraye da layu na tsafi, tamkar wani tsohon mahaukaci yana zaune akan tsuntsun tsafi a hannunshi yana rike da wani zabgegen gatari da aka yi da zallar ƙarfen jauhari.
Lokacin da yazamana cewa tazarar dake tsakanin su bata huce taku ashirin ba sai kowanne ɓangare suka ja suka tsaya aka yi kallon-kallo na tsawon daƙiƙa talatin,
daga can sai Fitinatul-amir ya dubi uwar gidanshi Rusayyat fuskarshi a murtuke tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta cikin kakkausar murya irin GWARZON SADAUKI ya ce "ya ke uwargidana ki yi sani cewa wannan fito wa da na yi ta musamman kuma ina mai tabbatar miki da cewa ɗayan ku ba zai bar nan a raye ba.
Har Rusayyat ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu sai Muhassin ya tari numfashinta ya dubi Fitinatul-amir ya ce "ya kai Fitinatul-Amir ka yi sani cewa JARMAI SHA YAKI shine ke fitowa filin artabu ya tari maza ba wai ya fito da karnukan farauta ba".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai Fitinatul-amir ya fusata ainun ya dube shi ya ce "ya kai wannan tsagera mai tsaurin idanu ka yi sani cewa yanzu zan gane da kai kuskuren ka domin ya zamo izna ga ƙananan ƙwari irin ka.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Fitinatul-amir ya dako wawan tsalle daga kan abin hawan shi ya falfala da azababban gudu zuwa kan Muhassin yana ihu da kururuwa mai firgitarwa DANDAZON MAYAKA komai tsananin yawan su yana mai ɗaga gatarinshi sama.
Koda ganin hakan sai Muhassin ya yi koyi da shi yana mai ƙwala kabbara,
Lokacin da Taurarin biyu suka haɗu da juna sai aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA da suka saba yin KARON BATTA.
Duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai ka ga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare.
Wohoho! Haƙiƙa a wannan Ubangiji ya nuna ikon shi akan halittarshi, domin duk irin ƙarfi da sihiri na Fitinatul-amir ya tashi a banza domin kuwa Muhassin ya zame mashi ƙadangaren bakin tulu, kuma bisa taimakon Ubangiji ya samu nasara hallaka shi ta hanyar sare mashi wuya da takobi a lokacin da ya rikiɗa izuwa tsuntsun batoyi.
Ya yin da mayaƙan marigayi Fitinatul-Amir suka ga uwan gidansu ya zamo gawa jarumi Muhassin ya yi RINJAYE akan su sai baki ɗayan su suka miƙa wuya, ba tare da wani ɓata lokaci ba ya karanta KALMAR SHAHADA Rusayyat da jama'ar ta suka amsa.
Aljani Abu-Ayub da gimbiya Aslaima suka ɓarke da kabbarar godiya ga Ubangiji,
Ba tare da wani ɓata lokaci ba jarumi Muhassin da gimbiya, yaro Usaiba, Rusayyat da jaruma Shalmirat suka sake hayewa bisa kan Abu-Ayub suka ɗunguma izuwa birnin sadauki Fitinatul-amir.
Ya yin da aka isa sai aka kafa TUTAR MUSULUNCI aka rushe gumaka, aka fito da dukkan fursunonin kurkuku aka 'yan ta su, bisa amincewar sabuwar majalisar sarki sai aka zaɓi yaro Usaiba mai hatimin takobi a matsayin sabon sarki birnin Madinatu-Salam, 'yar uwarshi Hairat a matsayin shugabar sarauniyoyin birnin,
A rana guda aka yi shagalin naɗin tare da ɗaurin auren jarumi Muhassin da 'yan mata uku wato gimbiya Aslaima, jaruma Shalmirat da Rusayyat uwar gidan marigayi Fitinatul-Amir.
Mako ɗaya da hakan sai ango Muhassin ya aike da wasiƙa izuwa ga sarki Hilaifu na cewa 'yarshi gimbiya Aslaima ta karɓi musulunci kuma ta samu lafiya da kuma abin da ya wakana tsakanin su da boka kaddad a wajen ɗauko ALLON TSAFI.
Ya yin da labarin ya riski sarki sai ya yi farin ciki ainun har ya haɗa gagarumar walimar da bai taɓa yin tamkar ta ba, kuka kuma ya amince cewa gimbiya ta zauna a tare da Muhassin duk bayan mako huɗu zai dinga zuwa yana ziyararta.
Lokacin da labarin abin da ya faru na mutuwar Fitinatul-amir ya watsu ga sarakunan nahiyar sai suka dinga yin zuwa suna yin MUBAYA'A ga sarki Usaiba suna karɓar addinin Musulunci, sannan sarki Usaiba ya tashi runduna ta musamman suka tafi izuwa inda su sadauki Huzlaif suke fafata yaƙi da sarki Madsur aka kai masu ɗauki aka murƙushe sarki Madsur da mayaƙan shi.
Wannan rana farin ciki ya mamaye nahiyar baki ɗaya bisa kawo KARSHEN ZALUNCI. Hasken musulunci ya mamaye ko ina.




BABI NA ƘARSHE


A can FILIN FAMA kuwa artabu ya ci-gaba da wakana tsakanin TAWAGAR MUSULUNCI da ta kafirai. Haƙiƙa Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan rana, domin sai da dakarun musulunci suka murƙushe baki ɗaya arna ɗayan su bai tsira da rayuwar shi ba. Sarki Rayyan ya yi wa sarki Lamsarul-Azlam kisan wulakanci ta hanyar sare masa ƙafafu da hannaye, bayan ƙura ta kwanta ne aka ɗunguma izuwa birnin Madintul-afnan farin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
A daren wannan rana sarki ya tashi wata tawaga ta musamman suka tafi izuwa birnin Darul-Ashmar domin a mamaye masarautar tun da sarki Lamsarul-Azlam da mayaƙan shi sun rasa rayukansu.
Lokacin da suka isa sai suka tarad jama'ar kurkuku na yin YAKIN KWATAR 'YANCI ƙarƙashin jagorancin sadauki Ukaiza, nan take suka mara masu baya har aka samu rinjaye, lokacin da labarin abin da wakana ga sarki Lamsarul-Azlam da mayaƙan shi a filin fama sai jama'a suka cika da matuƙar farin ciki da al'ajabi ba tare da wata jayayya ba Ukaiza da jama'a suka karɓi KALMAR SHAHADA, sadauki Ukaiza ya sadu iyalanshi cikin farin ciki bayan an naɗa shi sabon sarkin birnin Darul-Ashmar.
A can birnin Madinatul-afnan kuwa bayan mako uku da yin nasarar yaƙi sai aka shiga shagalin ɗaurim gimbiya Nuwairat tare da sarkin yaƙi Zuhairu kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.


***


Lokacin da aljanin ya sauka a turba sai sarki Nu'umanu ya yunƙura ya sakko ya durfafi inda ma'aji Kulairu yake fuskarshi cike da annuri ya yin da ya isa sai ya dubi waziri Yazid cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya kai abokina haƙiƙa ka ci amanar addinin Allah (SWT) shin yanzu ba ka bayar da gaskiya da shi ba ka yi nadamar abin da ka yi tun da ga shi kansa gaɓar mutuwa";
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Nu'umanu sai waziri ya bushe da dariyar ƙarfin hali ya furzar da GUDAN JINI daga bakinshi muryarshi na sarƙewa ya ce "da na miƙa wuya na gwammace na yi MUTUWAR JARUMTA".
Kafin ya gama rufe bakinshi sarki Nu'umanu ya sanya takobinshi ya sare mashi wuya, kan yi fitar burgu jini ya yi tsartuwa gami da jeshi, gangar jikin ta faɗi ƙasa rikici!
A dai-dai wannan lokaci ne Sarkin fada ya hallaka sarki yaƙi Lauzar ta hanyar burma mashi takobi a ciki. Magatakarda kuwa ya hallaka sarki Rakibu ta hanyar soka nashi tsinin takobi a idanu.
Nan take musulmi suka yi kabbara domin nuna godiya ga Ubangiji.
Tir! Da aikin mushrikai inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da gawarwarkin su waziri ke kwance a ƙasa cikin ƙasƙanci da tozarci dole ya godewa Allah bisa ganin yadda maƙiya Musulunci suka kunya ta.
Babu wata Yarjejeniya sauran dakarun su waziri da suka rage a raye suka karɓi KALMAR SHAHADA a hannun sarki Nu'umanu sannan ya fuskanci dakarun musulunci ya ce "ya ku jama'a ta ku yi sani cewa na samu lafiya ne bisa addu'a dake kuke yi min, saboda haka sai mu sake yiwa Allah guda tare yawaita salati ga fiyayyen halitta S'A'W domin shine tsanin dukkan wata nasara".
Sa'adda da sarki yazo nan a zancen shi sai aka sake ɓarkewa da kabbara,
Sarki ya dubi ma'aji Kulairu ya ce " ya Kulairu daga yau kai ne za ka maye gurbin karagar sarki Rakibu. Sarkin fada zai zamto wazirin ka. Magatakarda kuwa shine zai zamo waziri na";
Ya yin da sarki ya sake zuwa nan a zancen shi sai kowa ya kama dokinshi ya haye.
Ma'aji Kulairu da sarkin fada suka durfafi hanyar da za ta sada su da ƙasar sarki Rakibu dakarun haɗin gwiwa suka mara masu baya.
Sarki Nu'umanu da magatakarda suka jagoranci dakarun musulunci izuwa birnin Zainul-Ansar.
Tun daga bakin ƙofar gari jama'a suka yi cincirindo domin tarar dakarun musulunci cikin farin ciki da annashiwa aka ɗunguma cikin gari.
Bayan mako bakwai sai uwar gidan sarki gimbiya Lawisat ta samu juna biyu farin ciki a wajen al'umma ba a cewa komai.
Daga wannan rana farin ciki ya mamaye nahiyar baki ɗaya saboda tabbatar HASKEN MUSULUNCI.






Ƙarshe


Alhamdulillah
Allahumma Salli ala Sayyadina Muhammad (S'A'W).




Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaki
08137237071


Mu haɗu a sabbin littafai na masu zuwa.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website

Please Login or Register in order to submit comment