Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fitinatul-Amir, shin yana samun nasarar hallaka yaro Usaiba mai hatimin takobi?


Sarkin Musulunci Nu'umanu na kuɓuta daga sharrin wazirinshi ?


Shin aljani Husubul-luzwar yana samun nasarar sato sarki Rayyan daga sansanin musulmai ?


Ina makomar sadauki ukaiza da koma Izuwa birnin Darul-Ashmar domin ceto rayuwar iyalanshi a hannun sarki Lamsarul-Azlam ?




BABI NA TAKWAS






Lokacin da dakarun sarki Madsur suka ɗauke shi daga filin yaƙi cikin mawuyacin hali da ke tsakanin RAYUWA DA MUTUWA , suka ruga da shi izuwa sansani suka shiga da shi Izuwa tanti suka shimfiɗar da shi a bisa wani ƙayataccen gado, cikin hanzari likitoci suka duƙufa akan shi suna shuga bas shi taimakon gaggawa, ta hanyar ɗinke raunikan dake jikinshi suka sanya magani.
Gama aiwatar da hakan ke da wuya nantake ya samu ƙwarin jikinshi ya tashi zaune, a wannan lokaci ne waɗansu tsala-tsalan'yan matan kuyangi sun shigo ɗauke da abin kalaci a bisa ƙayatattun farantai da nau'ikan abubuwan shaye-shaye nau'i daban-dabam suka ajiye abisa wani dogon teburi dake tsakiyar tantin.
Take likitocin suka da kuyangin suka juya suka fice daga turakar, koda sarki Madsur ya ɗauko wani kofin zinare mai ɗauke da abin sha, koda ya kai bakinshi domin ya kwankwaɗi abin da ke ciki, nan take ya ga hoton fuskarshi a jiki an sanya mata audugar tsaida jini, kawai dai ya yi jifa da kofin yana mai kurma wawan ihu.


***
A can sansan su sadauki Huzlaif kuwa tun da aka shiga da shi Izuwa tantinshi likitoci suka taru a kanshi ba su ɗauki wani lokaci mai tsawo suka samu kan shi ba, har ya miƙe tsaye yana takawa da ƙafafuwanshi, yana cikin wannan hali ne wani saurayi ma'abocin kyawun ya bayyana a gare shi, sanye yake cikin baƙaƙen sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayanshi yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi.
Saurayin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, Huzlaif ya dube shi cikin nutsuwa ya ce "ya kai Himar ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka ba sai domin na ji a jikina cewa a kowa ne lokaci sarki Madsur zai iya turo mana dakarun HARIN BAZATO, saboda haka bai kamata mu shantake ba, kasancewar masu iya magana na cewa komai mammakon ka wani a hanya ya kwana, hakan ba zai sanya mu gaza yin namu tanadin ba, yanzu abin da nake buƙata a gare ka shine ka tashi dakarun leƙen asiri izuwa sansanin abokan gaba, sannan ka umarci dakarun mu cewa su kaso uku, kaso na farko su yi barci yanzu, sauran su yi gadin, idan sun farka da sulusainin dare sai kaso na biyu su yi ko yi da su haka ma na uku, ta a yadda dai gajiyar dake tare da su ba za ta sanya kashe gari su gaza a filin MUBARAZA ba";
Koda jin wannan umarni sai barde Himar ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice daga tantin.
Wannan shi ne abin da ya faru da rundunar Shugaban'yan fashin duniya da ta sarki Madsur.


***
A can birnin Zainul-Ansar kuwa sai da aka shafe tsawon kwanaki uku ana cikin alhinin abin da ya faru na asarar rayukan 'yan uwa musulmi a masallaci lokacin da ake gudanar da sallar asuba. A iya tsawon kafuwar birnin al'umma ba su taɓa tsintar kan su a cikin wannan yanayi ba. Kuma a iya tsawon kwanaki uku rashin lafiyar sarki Nu'umanu ta yi tsamari, domin ba ya iya komai sai dai a kwantar a tayar, binciken likitocin ya tabbatar da cewa takobin da aka yi masa rauni gabar da take ɗauke da ita ba ta yi tasiri a cikin jininshi.
A ranar kwana na ukun ne bayan sallar azahar ma'aji Kulairu ya kira taron gaggawa na 'yan majalisa a wani ɗakin sirri.
Lokacin da ya ga cewa kowa ya hallara a ɗakin taron kuma ya yi shiru sai ya katse shirun da ta wanzu ta hanyar yin gyaran murya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata ga Annabin rahama ( S'A'W) da iyalanshi masu tsarki gami da sahabbanshi masu haske.
Baya wani dogon jawabi zan yi ba kowannen ku dai masani game da abin da ya tara mu anan, sai dai zan yi mabuɗin zance, da farko dai abin baƙin ciki ace ana zaton wuta a maƙera sai a same ta a masaka, waziri Yazid da yake jagora na biyu a wannan ƙasa da sarkin yaƙi Lauzar sune suka haɗa kai da sarki Rakibu domin rushe addinin Musulunci da birninmu baki ɗaya, haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce makashin ka yana tare da kai".
Kuma saboda da illar munufiki Ubangiji ya sanya azabar da za 'a manufukai ta zarta ta kafurai, domin suna cutar da musulunci fiye da kafurai, yanzu mene ne shawararku game da hakan?;
Sa'adda Kulairu ya zo dai-dai nan azancen shi sai ɗakin taron ya sake yin shiru a karo na biyu, sai daga bisani wani dattijo ma'abocin kwarjini da cikar kamala ya yi gyaran murya ya ce "ya ku 'yan uwana 'yan majalisa ku yi sani cewa abin da ya wakana ya tabbatar mana cewa kakarmu ta yanke saƙa, dalilin da sanya na faɗi hakan kuwa shine da can baya mu gano abinda ya haddasa mana matsalolin ba, amma cikin taimakon Ubangiji yanzu mun gano bakin zaren, yanzu za mu shirye rundunar MAYAƘA domin mayar da martani, sannan wane irin hukunci za mu yanke wa sarki Rakibu tun da ya saɓa yarjejeniyar zaman lafiya da muka ƙulla tsakanin mu".
Lokacin da hakimin unguwar Ɗaibat Sha'aban ibn Kumais yazo dai-dai nan a jawabin shi sai ya sarkin fada wani kyakkyawan matashi ya yi gyaran murya ya ce "Allah ya taimaki Sha'aban kamar yadda addininmu ya tsara shine duk lokacin da kafurin amana ya saɓa yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninku, to za ku yaƙe shi domin kare rayuka, addini da dukiyoyinku, saboda haka a shawara ta a daren yau mu shirya dakarun yaƙi, kashe gari tunda duku-dukun safiya mu farmaki sarki Rakibu da su waziri";
Sa'adda sarkin fada yazo nan azancen shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa samun mafita, daga wannan kowa ya kama gabanshi ɗakin taron ya zamto wayam.
A can ƙasar sarki Rakibu tun sa'adda suka yi rashin nasara akan sarki Nu'umanu da al'ummarshi sai suka kasance cikin matuƙar baƙin ciki a kowace rana sai sun karanta wasu daga cikin surorin Alkur'ani mai girma domin samun nasara a akan sarki Nu'umanu.
Tir! Da aikin fasiƙi ga shi sun saɓawa Ubangiji amma suna suna neman taimakon shi akan ba su RINJAYE akan bayinshi mumunai.
Kuma ya zamana cewa a kowa ce rana ana ƙara bawa dakaru horon Yaƙi domin tunkarar birnin Zainul-Ansar.


***
Wohoho! Lokacin aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro. Fitinatul-Amir da jaruma Shalmirat suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare.
A ɓangaren su Usaiba kuwa sun wanzu suna kaiwa 'yan majalisar naushi da bugu hannu da ƙafa tamkar waɗansu ifritai, shi kan shi Usaiba ya yi matuƙar mamakin yadda aka yi ya iya kare hare-haren MAZAJEN tare da mayar da martani, bayan cewa shi koda wuƙar yankan lemo bai iya riƙewa ba.
Lokacin da Jaruman suka shafe tsawon rabin sa'a suna wannan ɗauki-ba-daɗi, sai suka tashi hankalin duk wata halitta dake dajin bishiyun suka dinga karairaye wa suna faɗuwa ƙasa, tsuntsaye kuwa suna canza sheƙarsu domin TSIRA DA RAYUKA, inda ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda tsirarun jaruman suka tashi hankalin dajin sai ya rantse rundunar ifritai ne ke bawa hammata iska.
Ana cikin wannan fafatawa ne Fitinatul-Amir da jaruma Shalmirat suka kai wa juna wawan sara a kafaɗa, cikin zafin nama suka zillewa saran, sannan Fitinatul-Amir ya kaiwa Shalmirat wani domin ya datse mata wuya. Cikin baƙin zafin nama ta sanya takobi ta kare amma saboda ƙarfin saran ya yi tsanani sai da Shalmirat ta durƙushe ƙasa, kafin ta yi wani yunƙuri Fitinatul-Amir ya sanya ƙotar takobinshi ya maka mata a goshinta da dukkan ƙarfin shi.
Saboda ƙarfin dukan sai da Shalmirat ta yi katantanwa sau biyu a ƙasa, sannan ta faɗi tim! Tana mai tsandara ihu lokacin da jini ke zuba daga gashinta.






BABI NA TARA


Cikin matuƙar farin ciki Fitinatul-Amir ya durfafi inda Shalmirat take kwance hannunshi riƙe da takobi tsirara da nufin datse mata wuya, ya yin da ya rage saura kamar taku ɗaya tsakanin su sai kawai ya ga Shalmirat ta miƙe tsaye zumbur ta shammace shi ta gabza mashi wawan naushi a fuska sai ga jini na zuba a hancinshi, cikin zafin nama ta ragi wani yanki a tufafinta ta ɗaure goshinta ta tsayar da jinin dake zuba.
Koda Fitinatul-Amir ya ga jini na zuba a hancinshi sai ya jifa da takobinshi kuma ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, kawai sai ya afkawa Shalmirat da dukkan ƙarfin shi yana kai mata naushi da bugu hannu da ƙafa, ita kuwa ta wanzu tana zillewa hare-haren cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA.
A ɓangaren yaro Usaiba, Rusayyat da 'yan majalisa kuwa, dukkanin su sun wanzu suna kaiwa juna hare-hare cikin zafin nama gami da MUGUN TANADI! Inda yan majalisar ke kai masu hari da makamansu su kuwa da ƘARFIN DAMTSE. Ana cikin wannan BAƘIN ARTABU ne wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko a cikin 'yan majalisar ya kaiwa Usaiba wani bahagon sara da gatarinshi a kafaɗa da nufin tsarga shi gida biyu, cikin zafin nama baban al'ajabi ya kaucewa harin tare da ka tsalle sama ya kai mashi wawan naushi a fuska, saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da kan bafaden ya gwaru da wata ƙatuwar bishiya ya tsage jini ya yi feshi, kuma ya sulale ƙasa rikica! matacce ko shurawa bai yi ba.
Sa'adda sauran 'yan majalisar suka yi arba da gawar ɗan uwansu sai mamaki da al'ajabi suka turnuƙe zukatansu, shin ta ya aka yi yaro Usaiba ya samu salon yaƙin da ya kashe bafade Nafiyaz.
Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, abin da ya fusata su shine ta ya za a ce yaro ƙarami ya zame masu tamkar ANNOBA ƊARI sun rasa yadda za su yi da shi, a matsayin su na GWARAZAN JIYA da suka saba yin KARON MAZA a FILIN ARTABU, wannan shi masu iya magana ke cewa ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu.
Lokacin da suka zo dai-dai nan a tunanin su sai sake ZAGE DAMTSE wajen kai wa su Rusayyat miyagun hare-hare fiye da ɗazu.
Abinda ba su sani ba shine babu wani makami da zai yi tasiri akan Usaiba face takobin SAIFUL-ZAYYAD dake zanen hatimin ta yake a gadon bayanshi. Ita kuwa jaruma Rusayyat abinda ya sanya makaman basu tasiri akan ta shine saboda sinadarin tsafin dake tare da su ya fito ne daga tushe ɗaya wato daga Fitinatul-Amir.
Kafin cikar sa'a ɗaya yaro Usaiba ya samu nasarar hallaka mutum uku daga cikin 'yan majalisar ta hanyar karya masu wuya, nan fa 'yan majalisar suka fara amfani da ƙarfin sihirin tsafin su wajen cutar da shi amma ba ta sauya zani ba jiya i yau.
A ɓangaren Fitinatul-Amir da Shalmirat kuwa labari ya sha bamban, domin masu iya magana na cewa idan rawa ta canza dole ne rawa ta canza, domin a halin yanzu Fitinatul-Amir yana yaƙar Shalmirat da tsagwaron ƘARFIN DAMTSE.
Domin kuwa a halin yanzu duk sa'adda ya gabza Shalmirat naushi a jikinta sai jini ya taru wajen ya yi tsami, a wasu lokutan idan da ƙafa ya dake ta sai kaga ta yi sama tamkar an janye ta da ƙugiya sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAR ASALI sai ta miƙe tsaye cike da jarumataka, ta ci-gaba da kai hare-haren. Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi, kafin shuɗewar rabin sa'a Fitinatul-Amir ya haɗa wa Shalmirat jini da majina fuskantarta tayi luhu-luhu.
Inda ba don Shalmirat na da juriya da nacin tsiya ba da tuni Fitinatul-Amir ya yi mat mata farat ɗaya. Ana cikin wannan hali ne Fitinatul-Amir ya gabzawa Shalmirat naushi a maƙogaro ta faɗi ƙasa wanwar, kawai sai ya tsugunna a gaban ta ya taffo wuyanta yana mai yi mata murmushin mugunta, sannan ya ɗora hannunshi a kan goshinta da nufin ya murɗe mata wuya.


***
Lokacin da aljani Husubul-luzwar ya ɓace ɓat! Daga tantin sarki Lamsarul-Azlam, bai bayyana ako ina ba sai a sansanin musulunci, nan take ya tarad da dakaru na ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro, kuma ko ina a haskake yake da fitilun ice ta yadda koda allura ce ta faɗi ƙasa da zarar muutuiya duba zai ganta. Nan fa Husubul-luzwar ya baza idanu yana nazarin wajen. Nan take ya fahimci cewa babu wata hanya da mutum zai ƙetare face an gan shi, domin haka sai kawai karanto waɗansu ɗalasimai tsafi, nan take surar shi ta canza Izuwa dakarun wajen shanye cikin sulken mai hatimin musulunci.
Koda kammala hakan sai ya durfafi sansanin batare da wata shakka ba, duk inda ya kutsa sai kaga dakarun na risina mashi, al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan, abin da bai sani ba shine sulken yaƙin da ke sanye a jikinshi iri ɗaya ne sak da na sarkin yaƙi, sai dai abin da ya bawa dakarun mamaki shine lokacin da sarkin yaƙi zai fita daga sansanin ya fita bisa ingarman doki fari, amma yanzu ya dawo a ƙafa, amma bisa ganin cewa shi shugaba ne mai cikekken iko babu wanda ya ce uffan.
Haka dai ya cigaba da ratsa saƙo da lungu na sansanin, yana cikin tafiyar ne ya hango tantin sarki Rayyan kuma ya zamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma ba ga waɗansu zaratan dakaru ne tsaye a ƙofar tantin ɗauke da miyagun makamai, nan take ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi, har ya yanke shawarar ya ɓace, amma sai wata zuciyar ta ce da shi ai matsoraci ba ya zama gwani, domin haka kawai ka kusance su.
Koda gama yanke shawarar hakan sai ya cigaba da tafiya har ya iso bakin tantin, dakarun dake gadi suka risina a gare shi sannan suka buɗe mashi ƙofa ya kunna kai Izuwa ciki, inda ace dakarun dake gadin za su shiga zuciyar Husubul-luzwar suga yadda take bugawa da sauri saboda matuƙar tsoro sai su yi tsammanin zuciyarshi zata buga.
Lokacin da ya shiga sai ya tarad da sarki Rayyan kwance bisa gado yana sharar barci a gefe guda kuwa an ajiye wani kofin a zurfa mai ɗauke da ruwan magani, hakan kenan ya tabbatar da cewa sarki ya sha magani ne domin huce gajiyar dake tare da shi, koda gama tunanin hakan sai ya matsa daf da gadon da yake kwance ya buɗe bakinshi take wani baƙin hayaƙi ya fita daga ciki ya durfafi fuskar sarki Rayyan.


ZAINUL-ANSAR


Sarki Nu'umanu na kwance bisa kan gadonshi cikin mawuyacin hali, uwar gidanshi Lawisat na zaune a gefen shi na dama tana yi mashi fifita hawaye na zuba daga idanuwanta, suna cikin wannan hali ne sai aka yi sallama a ƙofar shigowa, saboda haka sai Lawisat ta sassauta kukan ta kuma ta yi gyaran murya tana mai nuna bayar da umurnin shigowa.
Jim kaɗan sai ga ma'aji Kulairu ya shigo turakar shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, ya yin da yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku uku ba sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, kana ya sunkuiyar da kanshi ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa sannan ya buɗe baki ya ya gyaran murya ya ce " ya shugabana Ubangiji ya baka lafiya kuwa ya tashi kafaɗunka don haske zatinshi. Bayan haka kuma ya shugabana binciken da muka yi ya tabbatar mana da cewa waziri Yazid da sarkin yaƙi ne suka ci amanar ka ta hanyar haɗa kai da sarki Rakibu, kuma a daren yau ne za mu afka masu domin RAMUWAR GAYYA.
Koda jin wannan batu daga bakin Kulairu sai sarki Nu'umanu ya buɗi baki da ƙyar! Muryar shi na sarƙewa ya ce "ya kai Kulairu ka yi sani cewa a daren jiya na yi istihara game da batun FARMAKIN BAZATO da ake kawo mana da kuma batun jinyar rashin lafiya ta, kuma na samu nutsuwa a raina, hakan ya tabbatar min da cewa nasara za ta zo gare mu asirin makiyan mu zai tonu kuma zan samu lafiya da yardar Allah.
Sai dai nayi matuƙar mamakin yadda aka yi waziri Yazid ya ci amanata, ya Kulairu ka yi sani cewa na fi kowa sanin wane ne Yazid kuma tun muna yarinta muke tare babu abinda ke raba mu da shi face kwanciyar barci.
Haƙiƙa Manzon tsira ya yi gaskiya da ya ce " ka so masoyinka sannu-sannu wata rana zai iya zama maƙiyinka. Haka ma ka ƙi maƙiyinka sannu-sannu wata rana zai iya zama masoyinka";
kuma ina ƙarfafa gwiwa ina fatan za ku yi nasara alfarmar Annabi SAW TAFARKIN TSIRA zai tabbata za'a rabe tsakanin ƘARYA DA GASKIYA";
Lokacin da sarki Nu'umanu ya zo nan a jawabin shi sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanshi, koda ganin hakan sai Lawisat ta sake fashewa da kuka.
Al'amarin da ya karya zuciyar Kulairu kenan ya kamu da matuƙar tausayin su, bai san sa'add ƙwalla ta cika cika mashi idanu ba, kawai sai ya miƙe tsaye tsam! ya juya ya fice daga turakar ya kama dokinshi ya haye ya sakar mashi linzami yana fitowa ƙofar gidan sarauta ya iske dakarun musulunci sun yi sahu-sahu waɗansu na zaune a bisa dawakai, wasu a raƙuma wasu a ƙafa.
Domin haka sai kawai ya shige gaba dakaru suka mufa mashi baya, tun kafin su iso tuni waɗansu ZARATAN DAKARU sun wangame ƙofar birnin suna zuwa suka kunna kai izuwa cikin daji aka shiga tafiya cikin sauri domin isa ƙasar sarki Rakibu.






BABI NA GOMA



Sa'adda aka ci gaba da fafata ƁAKIN ARTABU tsakanin su boka kaddad da Waɗannan samudawan dabaru sai aka shafe tsawon rabin sa'a ana GUMURZU babu sassauci, lokacin da sa'a ɗaya ta cika sai ya zamana cewa su boka kaddad ba su iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu, saboda samudawan sun fara galabaitar da su.
Ana cikin wannan fafatawa ne jarumi Muhassin ya hango waɗansu dakarun sun samu nasarar kai aljani Ramsisul-Ayyam ƙas suna shirin afkawa su gimbiya Aslaima. Koda ganin hakan sai ya ƙwalla kabbara da ƙarfi, yana mai neman taimakon Ubangijin Musulunci, ya daka tsalle sama sai ga shi yana shawagi a saman su ya shiga amfani da takobinshi yana sare kawunansu cikin wani irin zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, domin a cikin daƙiƙa hamsin yana hallaka dakarun fiye da goma, yazamana duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga dakarun na zube wa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda.
Sa'adda samudawan suka ga irin muguwar ɓarnar da Muhassin ke yi masu sai suka fusata ainun suka ƙyale kowa suka taru akan shi, kai kashe dandazon kudaje ne suka yanyame ƙwallon mangwaro. Nan fa waje ya kaure da ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihun MAZAJE, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya bishiyu suna rangaji rassansu na karairaye suna zubewa ƙasa.
Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, sa'adda boka kaddad, gimbiya Aslaima da sauran dakarun rakiya suka ga yadda jarumi Muhassin ke ragargazar dakarun tamkar yana sassabe a gonar auduga, sai suka cika da matuƙar mamaki suna cewa a cikin ransu, anya kuwa jarumi Muhassin bil'adama ne, domin ko a tarihi ba su taɓa jin jarumi mai jarumta irin ta shi ba.
Ita kuwa gimbiya Aslaima duk da kasancewar ba ta iya ganin kowa da idanuwanta sai jarumi Muhassin, ya yin da ta ga irin bajintar da yake yi sai ta ji ta ƙaruwa da matuƙar ƙaunar shi a zuciyarta.
Haƙiƙa jarumi Muhassin ya cika GWARZON DUNIYA kafin cikar sa'a ɗaya ya samu nasarar hallaka baki ɗaya dakarun babu ɗayan su da ya rage a raye, duk inda mutum ya kalla babu abinda zai gani face gawarwakin dakarun kwance fulu-fulu cikin jini.
Koda samun wannan nasara sai MUHASSIN ya yi godiya ga Allah maɗaukakin sarki bisa ga wannan nasara da ya samu. Kawai sai ya durfafi wata ƙorama yana isa ya ɗebi ruwanta ya ɗauraye jini da jikin tufafinshi da takobinshi, kuma ya ɗaura alwala sannan ya fuskanci alƙibila ya shiga gabatar da sallah.
Duk wannan abu da yake gudanar wa kowa ya kallo, ya yin da suka ga yadda ibadar MUHASSIN na cike da tsafta da nutsuwa, nan take suka ji kwaɗayin addinin shi ya kama su, suna masu rayawa a zukatansu cewa anya kuwa addinin Muhassin ba shine addinin gaskiya ba? Domin ga shi mun kasa hallaka dakarun duk da ƙarfin sihirin boka kaddad, shi kuwa ya yi hakan.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, har Muhassin ya kammala ibadar shi, cikin hanzari boka kaddad ya bayar da umurnin ya sanya wa waɗanda suka samu rauni magani waɗanda suka rasa rayukansu aka binne gawarwakin su.
Kasancewar a wannan lokaci duhun magariba ya kunno kai sai aka yada zango nesa kaɗan da inda aka fafata artabu, domin a kwana anan zuwa safiya a cigaba da tafiya.
Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan anyi kalaci kowa ya kimtsa cikinshi, sai boka kaddad ya ɗauko madubin tsafin shi ya shiga gudanar da bincike, daga bisani ya ɗago da kanshi ya dubi kowa dake wajen cikin kakkausar murya ya ce " "ya ku abokan tafiya ku yi sani cewa bisa binciken da na gudanar ya tabbatar min cewa tazarar dake tsakanin mu da tekun Baharul-imfal domin ɗauko ALLON TSAFI dake ajiye a cikin masifaffen kada. Ku yi sani cewa musibar da zamu tarar acan ta shafe wacce mu ƙetare a baya, domin hakan sai kowannen mu yakasance cikin shiri, da wannan nake yi mana fatan samun nasara.
Koda jin wannan bayani daga bakin boka kaddad sai kowa ya sha jinin jikinshi kuma cikinshi ya ɗuru ruwa, aka kunna kai cikin dajin kowa na taka wa da ƙafafuwanshi, tafiyar daƙiƙa hamsin kacal! Aka yi aka iso iyakar dajin kuma aka hango gaɓar tekun Baharul-imfal, domin haka sai boka kaddad ya sake gudanar da bincike a cikin madubin tsafin shi a karo na biyu, bayan ya kammala sai ya juya ya fuskanci jama'a ya ce "ya abokan tafiya ku yi sani cewa bisa binciken da na yi ya bayyana mini cewa ba zamu iya ƙetare takun da ƙarfin sihirin tsafi ba, akwai buƙatar mu koma da baya domin mu sassaƙa kwale-kwale ( jirgin ruwa ) da zamu yi amfani da shi domin saura wa zuwa tekun";
Koda jin wannan batu daga bakin boka kaddad sai jarumi Muhassin ya yi caraf! Ya tari numfashin shi yana mai ce "ina so a bani damar sassaƙa kwale-kwalen cikin sa'a ɗaya kacal kawai".
Koda jin wannan batu daga bakin MUHASSIN sai boka kaddad da waɗansu daga cikin dakarun rakiya suka tuntsire da dariya, bakomai ne ya sanya su dariyar ba sai na isa ganin cewa ya faɗi abin da hankali ba zai ɗauka ba, domin ta ya ya mutum zai iya sassaƙa kwale-kwale a cikin sa'a ɗaya kacal!
Boka kaddad ya dube shi fuskarshi a murtuke ya ce "to shike nan muna jiran ka mu ga ikon

Please Login or Register in order to submit comment