Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ubangijin na ka da kake taƙama da shi";
Koda jin hakan sai MUHASSIN ya yi murmushi mai taushi Kawai sai ya juya ya kunna kai izuwa cikin daji yana mai takawa da ƙafafuwanshi, kaddad da tawagar rakiya suka samu waje suna zauna suna masu bin shi da kallo.
Jim kaɗan bayan shuɗewar daƙiƙa talatin sai ga Muhassin ya dawo ɗauke wata bishiya a kafaɗarshi ya sare rassa da jijiyoyinta. Ya zo a jiye a gaban su boka kaddad, nan fa suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi bisa wannan jarumtaka da jarumi Muhassin ya yi.
Batare da wani ɓata lokaci ba Muhassin ya shiga aikin sassaƙa kwale-kwalen ta hanyar amfani da wani gatari da ya kasance na waɗannan ayarin muridan.
Haƙiƙa Ubangiji ba ya kunyata bawanshi a duk lokacin da miƙa dukkan lamuranshi a gare shi kuma ya yarda cewa shine zai yi mishi komai. Domin kuwa cikin sa'a ɗaya kacal kamar yadda ya yi alkawarin.
Nan fa kowa ya cika da matuƙar mamaki bisa wannan bajinta ta Muhassin suka fara ji aran su cewa anya kuwa Ubangijin shi shine na gaskiya ba. Shi kuwa boka kaddad sai ya cika da matuƙar takaici da baƙin ciki domin kuwa ya kunyata a gaban jama'arshi, amma wani tunani da ya faɗo mishi a ranshi shine "ai bai kamata ace ka damu ba koda ace a kowacce daƙiƙa daƙiƙa soyayyar MUHASSIN za ta ƙaru a zuciyar Aslaima, domin kuwa burin ka ya kusa cika na mallakar RIGAR TSAFI wacce da ita ne za ka mulki duniya baki ɗaya a lokacin da zaka auri gimbiya Aslaima.
Lokacin da yazo nan a tunanin shi sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Ba tare da wani jinkiri ba jarumi Muhassin ya sanya jirgin ruwan a gaɓar tekun kowa ya shiga ciki ya zauna, sannan ya umarci waɗansu dakaru suka tuƙa kwale-kwalen aka fara tafiya a saman tekun cikin hanzari.
Ana fara wannan tafiya ne sai kawai gimbiya Aslaima ta taso daga wajen zamanta ta nufi inda Muhassin yake ta na isa ta zauna a daf da shi, fuskarta cike da annuri cikin kallo mai cike da tsantsar so da ƙauna ta ce da Muhassin cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa "ya kai GWARZON ƘARNI kuma JARUMI MAI BAN AL'AJABI ka yi sani cewa a halin yanzu zan bayyana maka sirrin da ya daɗe a cikin raina, haƙiƙa na kamu da matuƙar ƙaunar ka, kuma ina kwaɗayin na shiga addininka, shin ya Ubangijinka yake? Kuma shin zaka iya bayyana min wane sirri ne ke cikin zuciyar boka kaddad a wannan tafiya?;
Koda jin wannan tambaya sai Muhassin ya yi murmushi mai taushi har haƙoranshi suka bayyana masu haske ya buɗi baki ya yi gyaran murya ya ce "ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa Ubangijina shine mahaliccin komai da kowa duniya da abin da ke cikinta, bai haifa ba ba'a haife shi ba. Komai na cikin tasarrufin shi, babu wani abu daya gaba ce shi.
Game da batun boka kaddad kuwa Ubangiji ya bayyana min a mafarki abinda ya baro da ku daga gida domin ɗauko ALLON TSAFI, haƙiƙa dukkan abin da kaddad ya faɗawa mahaifinki ƙarya yake yi, burin shi shine ya mallaki RIGAR TSAFI, domin ya mulki duniya kuma ya aure ki a matsayin abokiyar rayuwarshi.
Ya ma'abociyar kyawu kiyi sani cewa bakomai ne yasanya idanuwanki ke iya gani ba, sai domin shirin da boka kaddad ya yi miki baya tasiri akanmu ma'abota addinin Musulunci. Inda ace za ki bayar da gaskiya da ubangijin musulunci da nan take idanuwanki za su warke sihirin ya karye;
Koda jin wannan batu sai gimbiya Aslaima ta cika da matuƙar farin ciki ta ta ce "yanzu a shirye nake na shiga addininka, kuma zan sanya mahaifina da jama'ata su ƙarba amma bisa sharaɗi guda ɗaya cewa za ka karɓi soyayya ta.
Koda jin wannan sharaɗi sai Muhassin ya yi murmushi ya ce "ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa ba'a karɓar addinina domin wata manufa ko sharaɗi, domin duk lokacin da wannan sharaɗi ko manufa aka rasa ɗaya daga ciki, mutum zai bar addinin. Kawai dai ki yi imani da Allah maɗaukakin sarki domin ya cancanta a bauta nishin.
Ya yin da ta ji wannan batu daga bakin Muhassin sai kunya ta kama ta ta sunkuiyar da kanta ƙas! Ta ce "yanzu sai ka shigar da ni addinin na ka";
Cikin matukar farin ciki Muhassin ya karanta kalmar shahada Aslaima ta maimata. Faruwar hakan keda wuya sai Aslaima ta ji tamkar an zare mata tsakuwa a cikin idanuwanta, nan ta ga dukkan abubuwan dake wajen tamkar cutar makanta bata taɓa samun ta ba.
Nan take ta ji ta ƙara imani da ubangijin musulunci.
Muhassin ya ci gaba da cewa "ya abar ƙaunata ina so ki ɓoye wannan sirri a tsakanin mu kar wani ya san cewa idanuwanki sun warke, har zuwa lokacin da zamu isa inda ALLON TSAFI yake, domin hakan zai tabbatar mana mu ga ƙarshen mayaudari kuma maci amana";
Koda jin wannan batu sai gimbiya Aslaima ta ce "ya abin alfahari na za ka same ni mai kiyaye wannan sirri ba zan bari wani ya ji ba.
Ya yin da Aslaima ta zo nan azancen ta sai su duka biyun suka bushe da dariyar farin ciki. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan kuma ya ɗaure mishi kai, shin ko mene ne dalilin wannan dariya ta su.
Ana cikin wannan tafiya ne aka iso wani waje mai ɗauke da matuƙar sanyi, nan fa kowa ya kama rawar ɗari, amma banda jarumi Muhassin da gimbiya, al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa kowa kai kenan.
Kawai sai gimbiya Aslaima ta ta shi daga wajen Muhassin ta durfafi kuyanginta, koda ganin hakan sai shugaban kuyangin ta tare ta ta riƙe hannunta ta yi mata jagora izuwa wajen su suka zauna a tare.
Lokacin da daƙiƙa hamsin ta sake shuɗewa a cikin wannan hali, kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta yi fitar burgu daga ƙarƙashin tekun, kafin wani daga cikin su ya yi wani yunƙuri halittar ta daki jirgin ruwan ta jelar ya dare gida biyu, kowa ya afka Izuwa cikin tekun, wasu daga cikin dakarun rakiya da kuyangin suna masu tsandara ihu.






BABI NA SHA DAYA



Sa'adda barde Himar ya fice daga cikin tantin sadaukai Huzlaif sai
ya durfafi bangaren yamma a sansanin da dakaru suka fi yawa, kafin ya isa sai ya kwalla wa wani badakare kira ya bayyana gare shi ya zube kasa ya kwashi gaisuwa.
Himar ya dube shi ya ce "ya kai Wahshun ka yi sani cewa ba komai ba ne ya sanya na kirawo ka nan ba sai domin ina so ka yi 'badda kama ka tafi izuwa sansanin abokan gaba ka gano mana shirin su, zaka iya daukar mutum uku da za su taimaka maka, abin da zan sanar da kai na karshe shine ka tabbatar da cewa wani ban gan ku ba;
Gama fadin hakan keda wuya sai barde Himar ya huce gaba domin aiwatar da abin da aka yi mishi, kao tsaye ya je ya debi dakaru suka kunna izuwa cikin daji, ya yin da yazamana tazarar dake tsakanin su da sansanin bata huce taku ashirin ba sai suka kwanta da rub daga ciki suna jan ciki suna tafiya a cikin ciyayi, suka durfafi sansanin. Komai kallon kurillar mutum ba zai iya gane akwai bil'adama ba, saboda yadda suka saje da ciyayin. A wannan lokacin su Wahshun suna iya hangen hasken fitilun dake sansanin.
Abu na farko da suka fara gani shine dakaru suna haka rami tare da binne miyagun tarkuna, Sannan kuma na sanya tarkunan a saman bishiyu. In ba wanda ya ga lokacin da ake aiwatar da hakan ba, ba zai taba zaton cewa akwai abu mai cutarwa ba.
Wannan shi ne abin da ya wakana a sansanin sadauki Huzlaif bayan tsagaita artabu da sarki Madsur.


Lokacin da aljani Husubul-luzwar ya daga takobinshi domin ya yanka makogaron sarki Rayyan a cikin tantinshi dake sansanin musulmai. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya ji an soka mishi takobi a gadon bayanshi ta billo ta kirjinshi.
Nan take ya fadi kasa matacce ko shurawa bai yi ba, wuta ta kama gangar jikinshi ta kone kurmus. A dai-dai wannan lokaci sarki Rayyan ya farka daga barci, aikuwa sai ya yi arba da gimbiya Nuwairat a tsaye daf da shi hannunta rike da takobi tsirara. Daga bisani ya mayar da duban shi izuwa ga inda gawar aljani Husubul-luzwar take dake dauke da siffa irin ta dakarun musulunci.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan ya dubi gimbiya Nuwairat kenan da nufin ya ce wani abu.
Amma sai gimbiya ta tari numfashin shi ta yi gyaran murya cikin ladabi ta ce "ya abbana ka yi sani cewa wannan badakare ka gani ba wani ba ne face aljani Husubul-luzwar, ina kwance akan gadona sai aka nuna min a mafarki cewa sarki Lamsarul-Azlam ya turo wata musiba a gare mu. Bisa wannan dalili ne ya sanya na iso nan domin na bincika abin da yake faruwa;
Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai sarki Rayyan ya dube ta ya ce "hakika laifina ne da ban yi addu'a a Lokacin da zan kwanta ba, kuma suma dakarun tsaro haka, saboda haka ayi sanarwa cewa dukkan jama'a su dage da addu'a domin samun nasara akan abokan gaba";
Koda jin wannan umarni sai gimbiya Nuwairat ta risina ga mahaifinta, sannan ta juya ta fice da sauri.
Wannan shi ne abin da ya faru a sansanin musulmai a lokacin da sarki Lamsarul-Azlam ya tura hadimin aljaninshi domin a sato mishi sarki Rayyan.


A can sansanin kafurai kuwa. Lokacin da sarki Lamsarul-Azlam ya tura aljani Husubul-luzwar sai ya shafe tsawon sa'a daya yana jiran dawowar shi amma shiru babu labari.
Koda ganin hakan sai ya dauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya shiga gudanar da bincike. Nan take ya ga dukkan abin da ya wakana tsakanin gimbiya Nuwairat da Husubul-luzwar, nan take ya cika da matuƙar bakin ciki ya ji tamkar ya kurma ihu saboda takaici.


Sa'adda yaro usaiba ya hango sadauki Fitinatul-Amir yana shirin karya wuyan jaruma Shalmirat, sai kawai ya dako tsalle daga tsakiyar 'yan majalisa tamkar an harbo shi daga cikin baka, yana saman ya saita dai-dai keyar Fitinatul-Amir ya gabza mishi naushi da hannayenshi biyu da dukkan karfin shi.
Saboda karfin naushin sai Fitinatul-Amir ya kurma wawan ihu ya saki wuyan Shalmirat ya yi a dungure sau uku kanshi ya garu da wani dutse.
Kafin ya yi yunkurin mike wa tsaye yaro usaiba ya daka tsalle ya dira a gadon bayanshi ya shiga kirba mishi naushi da dukkan karfin shi duk da kasancewar Fitinatul-Amir GWARZON JARUMI mai tarwatsa ZARATAN MAYAKA a filin fama amma sai ya ji ya kasa mikewa, sai daga bisani ya yi ta maza ya yunkura ya mike tsaye yana mai wurgar da usaiba.
Lokacin da jaruma Shalmirat dake kwance magashiyan ta hango abin da ke wakana sai kawai ta nuna yaro usaiba, da Rusayyat da hannunta na hagu take wata irin kakkarfar iska ta cimimiye su ta ruga da su izuwa cikin daji,
Cikin matukar takaici Fitinatul-Amir ya bude bakinshi ya kwarara wawan ihun baƙin ciki.






BABI NA SHA BIYU


A can cikin daji kuwa lokacin da uwar gidan sadauki fitinatul-Amir da yaro mai hatimin takobi suka ga irin mawuyacin halin da jaruma Shalmirat take ciki, sai hankulan su suka dugunzuma ainun, domin idan ba a bata taimakon gaggawa ba zata iya rasa rayuwarta. Cikin hanzari Rusayyat ta Shiga bata taimako ta hanyar tsayar da jinin dake zuba a jikinta, sannan ta tsinko waɗansu ganyayyakin bishiya ta ɗauraye su ta mitsittsika su a cikin ruwa ta ɗiga mata ruwan a bakinta ta shanye.
Jim kaɗan da aiwatar da hakan sai Shalmirat ta fara buɗe idanuwanta, kuma ta miƙe zaune, koda ganin hakan sai su Rusayyat suka cika da matuƙar farin ciki.
Yaro Usaiba ya dubi Rusayyat ya ce "ya ummina ina neman izini zan shiga izuwa cikin daji domin na farauto mana abin kalaci";
Koda jin hakan sai Rusayyat ta ce "ya hasken zuciyata akwai babbar damuwa shiga wannan daji domin dole ne a samu abubuwa masu cutarwa, domin ina so kayi sani cewa duk da YAƘIN DUNIYA take ciki a yanzu saboda kai ne, saboda haka ka jira Shalmirat ta wartsake sosai sai naje nayi farautar da kaina"
Har Usaiba ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu, amma sai jaruma Shalmirat dake kwance ta bushe da 'yar ƙaramar dariya sannan ta buɗi baki cikin ƙarfin hali ta ce "ya 'yar uwata haƙiƙa Usaiba ya fi ki gaskiya domin duk inda zai shiga yana cikin kulawa ta, ke dai kawai kiyi maishi fatan alheri".
Koda jin wannan batu daga bakin Shalmirat sai Rusayyat ta yiwa Usaiba inkiya da idanu dake nuna bashi umarni. Kawai sai ya ɗauki wata 'yar ƙaramar sanda ya juya ya kunna kai izuwa cikin daji yana takawa sannu a hankali babu tsoro ko fargaba a tare da shi.


A can inda su sadauki Fitinatul-Amir ke zaune kuwa sai da Fitinatul-Amir ya shafe tsawon daƙiƙa arba'in yana wannan kururuwar takaici, daga bisani ne ya turɓune fuska sannan ya umarci sauran 'yan majalisar da su haƙa ƙabari su binne 'yan uwansu da suka rasa rayukansu, shi kuma sai ya shiga sanyawa kanshi magani a raunukan dake jikinshi, bayan an kammala ne sun samu nutsuwa sannan ya yi gyaran murya ya dube su cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya amintattun 'yan majalisata ku yi sani cewa abin da ya faru tsakanina da uwar gidana abin takaici ne da baƙin ciki, sanin kanku ne cewa a duniya bani da wani maƙiyi da ya huce yaro Usaiba, shin yanzu mene ne mafita game da wannan al'amari;
Koda jin wannan batu daga bakin Fitinatul-Amir sai dukkan 'yan majalisar suka sunkuiyar da kawunansu ƙasa suna masu zurfafa izuwa cikin kogin tunani na tsawon daƙiƙa ashirin sai daga bisani ne wani daga cikin su ya yi gyaran murya cikin ladabi ya ce "ya shugabana a bisa nazari da nayi na fahimci cewa rashin tanadi ne ya muka kasa yin RINJAYE akan su yaro Usaiba, a bisa shawarata mu koma izuwa gida domin mu sake MUGUN TANADI, kasan masu iya magana sun ce SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI";
Koda jin wannan bayani daga bakin ɗan majalisar sai sauran suka cika da matuƙar farin ciki tare da nuna goyon bayan su fa shawarar.
Nan take Fitinatul-Amir ya sake kiran wannan mikiya suka hau bisa gadon bayanta suka zauna, kawai sai ta buɗe fuka-fukanta ta yunƙura ta tashi izuwa sararin samaniya ta fara tsala a azababban gudu, jim kaɗan! Ta ɓace ɓat! A cikin gajimare.
Wannan shi ne abin da ya faru da sadauki Fitinatul-Amir, jaruma Shalmirat da yaro Usaiba mai hatimin takobin Saiful-Zayyad.




Lokaci da rundunar birnin Zainul-Ansar ƙarƙashin jagorancin ma'aji Kulairu ibnu Safwan, suka wanzu suna falfala azababban gudu, sai aka shafe tsawon sa'a ɗaya da rabi a cikin wannan hali, ana ratsa dazuka duwatsu da ƙoramu, ba tare da an haɗu da wani abu mai cutarwa ba.
Lokacin da ya zamana an shafe zango uku a dai-dai wannan lokaci ne aka fara hango manyan katangun birnin Baitul-Auman daga can nesa kaɗan, nan take aka yiwa dawakai ƙaimi, lokacin da ya zamana saura taku ashirin sai aka aka ga ƙofar birnin ta buɗe sai ga dakaru shirye cikin gagarumar shigar yaƙi suna ta tuttuɗowa tamkar dandazon kiyasai, sai da daƙiƙa arba'in ta shuɗe sannan aka mayar da ƙofar birnin aka rufe rufe!.
Koda ganin hakan sai DAKARUN MUSULUNCI suka ja dawakansu suka tsaya cak! Aka shiga yin kallon-kallo tsakanin su, daga bisani sai jagororin kowanne ɓangare suka sakarwa dawakansu linzami suka durfafi juna, ya yin da yazamana cewa tazarar taku biyar ce ta rage tsakani, kowannen su ya ja ya tsaya, aka yi kallon kallo na waɗansu daƙiƙu daga bisani sai ma'aji Kulairu ya dubi waziri Yazid, sarkin yaƙi Lauzar da sarki Rakibu cikin matuƙar fushi yana mai daka masu tsawo ya ce "kaicon ku yaku maciya amanar musulunci da addinin Ubangiji. Haƙiƙa shaiɗan ya yi tasiri wajen siye zukatanku wajen ƙawata maku kwadayin duniya, kin siyar da addinin ku akan abin duniya da zai zamto mai ƙarewa.
Ina mai kira a gare ku da kuyi nadamar abin da kuka aikata ku tuba izuwa ga Ubangiji kafin ajali ya riske ku.
Koda jin wannan batu daga bakin Kulairu sai sarkin yaƙi Lauzar, waziri Yazid da sarki Rakibu suka bushe da dariyar mutunta tamkar ba za su daina ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar fusata Kulairu kenan ya ce a cikin ranshi haƙiƙa wanda ya yi nisa baya jin kira.
A lokaci guda waziri ya turɓune fuska tamkar an aiko mishi da WASIƘAR AJALI ya dubi kulairu a wuhakance ya ce "ya kai Kulairu kayi sani cewa ban fito wannan yaƙi ba domin kayi min nasiha ba, shin ka manta ne cewa na hadda ce Ƙur'ani mai girma tare da manyan litattafan addinin musulunci, har ta kai cewa a kaf nahiyar nan babu malami mai amsa fatawa tamk ta.
Kaga kenan babu wani abu da zaka faɗa min game da addinin musulunci, abin da nake so na ji daga gare ka shin kun zo ne domin ku yi MUBAYA'A a gare mu, domin na tabbata cewa gubar da hadimina ya sanyawa sarki Nu'umanu ba zai tashi daga jinya ba domin ajalinshi ya gabato.
Da jin wannan batu sai kulairu ya tari numfashin shi ya ce "tir! Da kai ya kai la'anannen Allah ka yi sani cewa Allah ya tsare ni da nayi mubaya'a ga maci amana kuma mayaudari kamar ka, da yardar Ubangiji da alfarmar annabin shi mai tsarki sai mun yi nasara a wannan yaƙi kuma mai martaba sarki zai samu zai samu lafiya, sai ka shirya ga maza nan bisa kan ka".
Gama faɗin hakan sai sarkin fada ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi ya zaburi dokinshi da nufin ya farma waziri, amma sai kulairu ya dakatar da shi yana mai cewa shi ne ya kamata ya tare shi, yana faɗin hakan ya zare takobi ya yi ɗauki kan shi, shi kuma sarkin fada sai ya tari sarkin yaƙi, magatarda ya tari sarki Rakibu.
Su Kulairu suna ƙwala kabbara da ƙarfi, bisa mamaki sai suka ji su waziri suna kabbarar, kaico! Tir da aikin fasiƙai.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro gami da tashin hankali.
Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar KARFIN DAMTSE JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA.
Ƙarar karafniyar makaman yaƙi ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, tamkar DARE UKU ake yi, dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayan su, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sararin samaniya.
Haƙiƙa yaƙi abin tsoro kuma tashin hankali wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi.
Cikin ƙanƙanin lokaci dakarun kowanne ɓangare suka zamto tamkar GOBARA DAGA KOGI suna ƙuntatawa juna daga nau'ikan ANNOBA DARI.




Kashe gari tunda duku-dukun safiya dakarun musulunci da na kafurai suka yi sahu-sahu a lokacin da hantsi ya ɗaga. kallo ɗaya mutum zai yiwa ɓangarorin biyu ya fahimci cewa kowanne ya fito ne da shirin ko a mutu ko ayi rai.
Sarki Rayyan, gimbiya Nuwairat da sarkin yaki sune akan gaba a TAWAGAR MUSULUNCI sanye cikin shigar fararen sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama, hatta dawakansu fararen ne sol! Sarki Rayyan ya ɗaura farin rawani mai ratsin kore.
A can ayarin kafurai kuwa Sarki Lamsarul-Azlam sarkin yaƙinshi tare da waziri ne akan gaba sanye cikin baƙaƙen sulken yaƙi da dawakai.
A zahiri idan mutum ya ƙare wa rundunonin biyu kallo zai fahimci cewa dakarun kafurai sun ninka musulunci yawa sau goma, ana cikin wannan hali ne kwatsam! Nazari babu tsammani sai dakarun musulunci suka ji ana yi masu ruwan kibbbau ta kowacce kusurwa gabas, yamma, kudu da arewa cikin hanzari aka sanya garkuwoyi, amma duk da haka sai dakaru da dama suka yi shahada saboda matuƙar yawan kibbbau ɗin.
A lokaci guda tamkar ɗaukewar ruwan sama aka daina harbo su.
Har wasu daga cikin dakarun sun yunƙura da nufin su afkawa kafirai sai gimbiya Nuwairat ta yi masu nuni da su ja da baya kamar taku goma.
Da ganin hakan sai kafirai suka suka ruga izuwa kan musulmai suna ihu da kururuwa mai firgitarwa domin suna ganin cewa Musulmi sun ji tsoro ne.
Kaico! Abin da arna ba su sani ba shine abin da masu iya magana ne ke shirin faruwa na cewa. Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne salon faɗa ne. Kuma haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu.
Lokacin da ya rage saura taku goma tsakani sai dakarun kafurai suka dinga faɗa wa a cikin miyagun tarkuna suna sheƙawa barzahu. Kafin su farga fiye da mutum dubu goma sun zube ƙasa matattu. Koda musulumi suka ga yadda maƙiya Allah ke wulaƙanta sai suka cika da matuƙar farin ciki
Su dai waɗannan tarkuna an binne su ne tun a daren jiya.
Lokacin da sarki Lamsarul-Azlam ya ga yadda jama'arshi suke hallaka sai ya cika da matuƙar takaici da baƙin ciki, kawai sai ya dako wawan tsalle sama daga kan dokin yana mai zare zabgegiyar takobi a gadon bayanshi tamkar yana ɗauke da fuka-fukai ya dinga shawagi a sama yana sare kawunan dakarun musulunci.
Tamkar haɗin baki a lokaci guda tawagar kowanne ɓangare suka yi ɗauki izuwa kan juna, musulmi na kabbara kafirai na ihu da kururuwar banza. Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni da tashin hankali.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin sarki Rayyan ma'abocin addinin Musulunci da sarki Lamsarul-Azlam.




A can birnin Zainul-Ansar kuwa bayan ficewar dakarun musulunci izuwa filin artabu sai baƙi ɗaya mutanen birnin maza da mata yara da manya suka ajiye aiyukansu suka duƙufa addu'a masu karatun Alkur'ani nayi masu salati ga fiyayyen halitta (S'A'W) nayi. Ƙananan yara kuwa suna istigfari domin riƙon Allah akan ya bawa tawagar musulunci nasara a wannan yaƙi ya kuma tashi kafaɗun sarki Nu'umanu.

Wannan shi ne abin da ya wakana a cikin birnin Zainul-Ansar.




Sa'adda da wannan shirgegiyar halitta ta taso daga ƙarƙashin tekun Baharul-imfal ta daki kwale-kwalen su boka kaddad ya dare gida biyu suka tsunduma izuwa cikin tekun, sai kowannen su ya shiga yin iyo yana tasowa sama domin ya ga halittar da ta kawo masu farmaki.
Koda aka yi arba da halittar sai kowa ya cika da matuƙar mamaki da firgici, ba wani ba ne halittar ba face wani narkeken namijin kada, kadan yakasance ƙato mai tsawon tsiya gami da kwarjini muni da ban tsoro, yana da zabga-zabgan jela guda biyu, yana da waɗansu wargatsattsun haƙora masu fasali da KAIFI DA TSINI, idanunshi jajaye ne tamkar garwashin wuta, gadon bayan kadan ya kasance mai gurji-gurji tamkar duwatsu aka jera mashi, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa abu ne mai matuƙar wahala a samu KAIFIN TAKOBI ya yi tasiri akan shi.


Please Login or Register in order to submit comment