Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Koda kadan ya ga cewa ya samu nasarar tarwatsa jirgin ruwan sai kawai ya yunƙura izuwa kan su yana wani irin kuka mai ban tsoro.
Koda ganin hakan sai kowa ya zare makamin shi ya afka mashi. aka ruguntsume da azababban yaƙi.
Sai yazamana cewa a duk sa'adda suka sari jikin kadan sai su ji tamkar dutse suka sara ko gezau bai yi ba.
Shi kuwa ya wanzu yana kai masu hari da jela da haƙora gami da faratanshi, kuma duk inda ya kai FARMAKI sai ya salwantar da ran ɗaya daga hadimai.
Shi kansa boka kaddad da aljani Ramsisul-Ayyam wankin hula yana neman kai su dare.
Wani abu da ya basu mamaki shine gimbiya Aslaima na tsaye a gefe guda amma kadan ya kasa afka mata. Abin da ba su sani ba shine a halin yanzu gimbiya ta musulunta domin kadan ba zai iya cutar da ita ba.
Shi kuwa jarumi Muhassin yana tsaye a gefe guda baya kai hari sai idan kadan ya kawo masa MAMAYAR BAZATO.
Kaico! Haƙiƙa tashin hankali ba a sa maka rana, iya tsawon wanzuwar wannan teku halittun dake ciki basu taɓa ganin tashin hankali tamkar na yau ba, saboda yadda tekun ke yin famjam-famjam sai ka rantse cewa YAKIN DUNIYA ne ya taso.
Kafin shudewar daƙiƙa ɗari kadan ya hallaka gaba ɗaya hadimai da dakarun rakiya kuma ya yunƙura izuwa kan su boka kaddad a dai-dai lokacin da ya zamana cewa basu iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu.
Koda Muhassin ya hango abin da ke shirin faruwa sai kawai ya ƙwala kabbara da ƙarfi sai ga shi ya taso izuwa saman tekun ya ruga izuwa kan kadan yana takawa da ƙafafuwan shi tamkar yana tafiya a turba, sannan ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya dira a gadon bayan kadan ya shiga zabga mashi sara da takobin shi.
Haƙiƙa! JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji dukiya da mulki basu bayar da ita sai dai tsananin rabo.
Nan fa boka kaddad, Ramsisul-Ayyam suka cika da matuƙar mamaki domin ko da a tarihi basu taɓa ganin jarumi mai sadaukantakar Muhassin ba.
Ana cikin wannan fafata wa ne kadan ya mako Muhassin da jelar shi ya faɗo ƙasa saboda da ƙarfin makewar sai ya yi nutso izuwa ƙasan tekun ya ɓace ɓat!.
Kawai sai kadan ya yunƙura kan gimbiya Aslaima ya wangame bakinshi domin ya laƙume ta ya yi loma ɗaya da ita.






BABI NA SHA UKU

Kwatsam! Bazato babu tsammani sai a kaga jarumi Muhassin ya yi fitar burgu daga ƙarƙashin tekun Baharul-imfal tamkar an janyo shi da ƙugiya yana mai ƙwala kabbara ya sauka akan ƙoƙon kan kadan ya zabga mashi naushi a haƙoranshi. Saboda ƙarfin naushin take haƙora uku suka yi fitar burgu daga cikin bakin jini ya yi tsartuwa.
Ya yin da kadan ya ga haƙoranshi sun zube ƙasa sai ya fusata ainun ya kaiwa jarumi Muhassin wawan hari da nufin ya taune shi a baki, amma sai Muhassin ya wurƙila ya zame wa harin.
Kawai sai kadan ya takarƙare ya kurma wawan ihu ya afkawa Muhassin a lokacin da ya suɓuto ƙasa daga kan shi, bisa mamaki sai su gimbiya suka ga Muhassin yana tsaye bisa diga-diganshi tamkar yana tsaye bisa tsanɗauri ba saman ruwa ba.
Nan take suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, Muhassin ya wanzu yana yakin cikin JURIYA DA BAJINTA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan baƙin artabu, nan fa ya zamana cewa tekun ta hautsine tamkar annobar GOBARA DAGA KOGI ce ta bayyana ga halittun tekun, ana cikin wannan fafatawa ne Muhassin ya shiga taimakon Ubangiji yana yiwa annabin shi salati, kawai sai ya sanya hannayenshi biyu ya shiga ɓara bakin kadan da dukkan ƙarfin shi yana kammala hakan ya yi jira da gawar shi gefe.
Wohoho! Haƙiƙa JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji, komai hassadar mutum idan ya ga wannan BAJINTA da Muhassin ya yi dole ne ya jinjina mishi ya tabbatar da cewa ya cika GWARZON MAYAKI kuma MAGOGIN KARFE.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Aljani Ramsisul-Ayyam da boka kaddad kai kenan domin koda a tarihi basu taɓa jin gwarzo mai SADAUKANTAKA tamakar Muhassin ba.
"Haƙiƙa kowa ne Ubangijin Muhassin ya cancanta a bauta mashi domin ya zartar da abin saboda kaddad ya gaza a matsayin shi ya mashahurin boka";
Ramsisul-Ayyam ya yi wannan furuci a ranshi batare da bayyana wani ya ji ba.
Gimbiya Aslaima kuwa nan take ta ji ƙarfin imani da ubangijin halitta ya cika zuciyarta,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga boka kaddad ya ɓace ɓat an neme shi sama ko ƙasa an rasa.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba Muhassin, Ramsisul-Ayyam da Aslaima mamaki kenan. Daga can sai aka gan shi ya bayyana a saman tekun yana tsaye sanye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro a hannunshi na hagu yana riƙe da wani dogon mashi mai baki biyu, fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, aka fara kallon-kallo tsakanin shi da Muhassin, daga can sai taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga can ya haɗe rai cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "ya kai Muhassin ka yi sani cewa haƙiƙa ka tafka babban kuskure da ka shiga soyayya da wacce zata zamo mata a gare ni bayan na mallaki rigar tsafi, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan aike da ruhinka izuwa barzahu, sannan na farke cikin wannan kada na ciro ALLON TSAFI wanda da shine zan samu nasarar shiga kogon dutse na ɗauko hular LAUHUL-SIHIR, domin cika muradina na mulkar duniya baki ɗaya. Ina mai rantsuwa da boka kuddamul-Barzahu mai mallaki hular LAUHUL-SIHIR sai naga bayan ka.
Kafin kaddad ya gama rufe bakinshi Muhassin ya tari numfashin shi yana kai daka mashi tsawa ya ce "ƙaryar ka ta sha ƙarya ya kai la'anannen Allah ka yi sani cewa ba za ka taɓa cimma mugun nufin ka domin har kullum KARYA DA GASKIYA ba su taɓa kasancewa a haɗe ba sai gaskiya ta ji RINJAYE kuma abin da baka sani ba shine tuni gimbiya Aslaima ta yi imani da Allah yar uwata musulma a halin yanzu, kuma tun farkon wannan tafiya idanuwanta suka warke daga shirin da ka yi mata domin cimma buƙatar ka. Ka sani cewa da yardar Allah ba zaka ci amanar mahaifinta ba, domin masu iya magana na cewa RAMIN KARYA kurarre ne".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai kaddad ya takarƙare ya kurma wawan ihun baƙin ciki ya ɗaga mashin shi izuwa sama ta ruga izuwa kan Muhassin. Koda ganin hakan sai Muhassin ya zare takobin shi ya ruga gare shi domin tarar juna yana kabbara.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro. Jaruman biyu suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai SADAUKAN DAUKAR FANSA da suka saba GWAGWARMAYA a SANSANIN AZABA.
Idan juriya da naci a yaƙi suka haɗu waje guda dole ne tsagwaron KARFIN DAMTSE su yi aiki, kuma idan gwani da gwani suka haɗu a yaƙi dole artabu ya zamto abun tsoro da tashin hankali.
Wohoho! Nan fa Taurarin biyu suka wanzu suna bawa hammta iska, duk sa'adda makamai suka haɗu da juna sai kaga tartsin wuta ya tashi gami da wata farar walƙiya.
Sai da sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan fafatawa babu nasara ga kowanne ɓangare.
Sa'adda boka kaddad ya ga cewa ya gaza nasara akan Muhassin sai ya shiga aiki da shiri, inda ya dinga tura mashi musibu idan ya tura masa wuta da zarar ta doshi inda Muhassin yake sai kaga ta zamto hayaƙi. Idan ya tura kibbbau, da sun isa gare shi sai su ɗige a ƙasa su zama ruwa.
Koda kaddad ya fahimci cewa wankin hula kai shi dare sai kawai ya rikiɗa izuwa mutum huɗu, masu matuƙar kama da shi tamkar an tsara kara, komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya tantance boka kaddad na gaskiya ba.
A lokaci guda mutanen huɗu suka yiwa Muhassin rubdugu domin yi mashi farat ɗaya, suka shiga kai mashi sara ta sama da ƙasa. Amma saboda juriya da ƙarfin addu'a sai Muhassin ya zamto tamkar shaiɗani a tsakanin su yana kare hare-haren su kai kace wata na'ura ce ke sarrafa shi.
Duk wannan artabu da ake yi gimbiya Aslaima da Ramsisul-Ayyam suna kallo cike da matuƙar mamaki.
Abu biyu ya bawa Ramsisul-Ayyam mamaki na farko shine yadda aka yi mutanen huɗu suka kasa hallaka Muhassin, na biyu kuwa shine yadda Muhassin ke iya tsallake hare-haren.
Ita kuwa Aslaima tana mamaki ne bisa ganin yadda Ubangijin talikai ke zartar da ikon shi a wannan fafatawa.
Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe nan take mutanen huɗu suka fara samun yiwa Muhassin rauni da masun dake hannayensu, har ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani, ana cikin wannan hali ne suka sanya tsinin masun suka soka mashi a gadon bayan shi, nan take Muhassin ya ƙwala kabbara saboda raɗaɗi da zurfin da ya ji ya sulale ƙasa magashiyan.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai mutanen huɗu suka cure waje guda suka rikiɗa izuwa wata ƙatuwar mucijiya mai ɗauke da kawuna guda arba'in da ɗaya, kowanne kai ya kai girman na raƙumi.
Komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da halittar dole ne ya ɗimauce.
Kawai sai mucijiyar ta sanya jelarta ta kanannaɗe Muhassin kuma ta buɗe dukkan bakunanta guda arba'in da ɗaya tana zurfar da dafi domin ta kaftawa jarumi Muhassin sara a sassan jikinshi, duk inda dafin na ya zuba a akan ruwa sai wuta ta kama.




BABI NA SHA HUƊU


Lokacin da yaro usaiba mai hatimin takobi ya kunna kai izuwa cikin daji babu fargaba a tattare da shi hannunshi riƙe da sanda domin ya farautowa su shalmirat abin da za su yi kalaci. Sai ya wanzu yana ratsa hamada, duwatsu gami da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu,ba tare da ya ji koda kukan tsuntsu ba ko kuma ya ga wani abu mai cutarwa ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai gami da dugunzuma hankalin shi.
Yana cikin wannan hali ne ya hango wani kyakkyawar barewa ta kafa kai a bakin wata ƙorama tana shan ruwan cikinta.
Cikin matuƙar farin ciki maral musaltuwa ya durfafi inda take yana sanɗa domin ya cimma ta, tamkar barewar ta ji motsin shi kawai sai ta ranta a na kare ya ruga izuwa cikin daji. Cikin zafin nama Usaiba ya rufa mata baya suka kasa tsere.
Tsawon daƙiƙa ɗari suna wasa diga-digansu ba tare da ɗayansu ya cimma abokin faɗan shi ba.
Lokacin da ya zamana cewa tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma ba, kwatsam! Bazato babu tsammani sai Usaiba ya ga wannan barewa ya rikiɗa izuwa surar wata mummunan tsohuwar aljana.
Saboda matuƙar firgici bai san sa'adda ya faɗi ƙasa ba jikinshi yana tsuma da kyar ma, koda ya yunƙura domin ya miƙe tsaye sai ya ji ya kasa koda motsa gaɓarshi.
Koda aljanar ta ga halin da Usaiba yake ciki sai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, sannan ta buɗe baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haushin kare ta ce "haƙiƙa yau ni ce na fi kowa sa'a da nasara a duniya domin gashi na tsinci dami a kala, wannan shine masu iya magana ke cewa rabon kwaɗo baya hawa sama, kuma idan rabo ya ranste to ko kana barci sai arzikin ka ya same ka. A yau ne zan yanka yaro Usaiba na shanye jininshi, domin na cimma burina na zamtowa GAWURTACCIYA uwar hatsabiban duniya";
Koda mummunan aljanar ta zo nan azancen ta sai ta busawa Usaiba wani farin hayaƙi daga bakinta ya shaƙa take ya faɗi ƙasa yana sharar barci.
Cikin matuƙar farin ciki ta sanya hannayenta biyu ta ɗauki Usaiba ta yunƙura izuwa sararin samaniya tana mai bushewa da dariyar mugunta, ta ɓace ɓat a cikin gajimare tamkar bata taɓa wanzu wa ba.




Lokacin da ma'aji Kulairu, sarkin yaƙi Lauzar, waziri Yazid da sarkin fada suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, duka jagororin suna yaƙinne cikin JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan fafatawa babu sassauci kuma babu alamun nasara ga kowanne ɓangare. Al'amarin da ya matuƙar karya zukatan dakarun musulunci kenan suka fara tunanin cewa da yiwuwar babu nasara a wannan karon ma, abin da ba su sani ba shine kamar yadda suke neman taimakon Ubangijin musulunci suma su waziri suke yi.
Tur! Da aikin fasiƙai maƙiya Allah, ga shi dai su waziri sun kasance maƙiya Allah da Manzonshi, amma suna roƙon shi ya ba su nasara akan ingantattun bayinshi.
Ana cikin wannan hali ne su waziri suka samu rauni da addu'a, al'amarin da ya bawa tawagar musulunci nasara kenan suka fara samun RINJAYE akan arna, kafin a ɗauki wani lokaci su waziri Yazid sun galabaita ainun har suna suɓutowa daga kan dawakansu.
Kwatsam! Sai aka hango wani kyakkyawan aljani yana saukowa daga sararin samaniya ɗauke da wani kyakkyawan dattijo ma'abocin kwarjini da haiba sanye da fararen tufafi tun daga sama har ƙasa yana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi da jikin aka rubuta kalmar shahada.a dai-dai lokacinne ma'aji Kulairu ya take wuyan waziri Yazid yana shirin soka mashi takobi a maƙogaronshi. Cikin kuzari aljanin ya shimfiɗe fuka-fukanshi a turba.
Lokacin da jama'ar dake filin yaƙin suka yi arba da dattijon sai suka cika da matuƙar mamaki ba wani ba ne dattijon ba face sarki Nu'umanu.
Wannan shi ne abin da ya faru da dakarun birnin Zainul-Ansar da su waziri Yazid.


Darul-Ashmar


Sadauki Ukaiza shugaban dakarun da suka fita farautar yaro Usaiba mai hatimin takobi yana zaune a cikin 'yan uwanshi fursunonin kurku. Sai wani kyakkyawan saurayi mai matuƙar kwarjini da haiba ya duba shi ya yi gyaran murya ya ce "ya kai Ukaiza an ya kuwa ba za su amfani da tafiyar sarki Lamsarul-Azlam yaƙi domin nemar wa kanmu 'yanci ba daga KANGIN BAUTA, kuma mu yi mashi JUYIN SARAUTA
Tun da kai jarumi kuma kwararre da ya san dukkan wani sako da lungu na wannan birni da kuma sanin tuggun yaƙi, kuma a jiya lokacin da muke gudanar da aiyukanmu na gifta ta wajen masu gadi na ji wani na cewa sarki Lamsarul-Azlam ya buƙaci a sake tura nashi ƙarin dakarun yaƙi, kaga kenan babu tabbacin ga lokacin da zai dawo tun da bai yi nasara ba. Kuma zamu dami damar yin GABA DA GABA da duk wata barazana, domin matuƙar yawan fursunonin dake kurkukun nan ya isa ya sanya mu cimma nasara, domin masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI, kuma tabbas hannu da yawa maganin ƙazamar miya ne";
Koda jin wannan batu daga bakin bawa Amral sai gaba ɗaya fursunonin dake wajen suka zurfafa izuwa kogin tunani domin samun mafita.
Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali sai daga bisani wani daga cikin su ya yi gyaran murya ya ce "gaskiya ni shawara ta ina ganin mu tsaya a batun samun 'yancinmu mu ajiye batun JUYIN SARAUTA domin sanin kanku ne cewa karo da sarki Lamsarul-Azlam tamkar tunkarar ANNOBA DARI ne".
Da jin wannan batu sai sadauki Ukaiza ya yi caraf! Ya tari numfashin shi ya ce "ba za mu taɓa janye juyin mulki ba domin koda ba mu yunƙurin hakan ba. Ƙarshe dai mutuwa ce makomar mu. Shin yanzu ina amfanin baɗi babu rai, ka sani cewa har abada matsoraci ba ya zama gwani.
Koda jin wannan batu daga bakin Ukaiza sai kowa ya yi na'am da batun.
Ukaiza ya ci gaba da cewa "muhimman abubuwan da zamu yi sune. Samun haɗin kan dukkan fursunonin dake cikin kurkukun nan cikin sirri ba tare wani bare ya sani ba.
Na biyu kuwa muna buƙatar haƙa rami da ya kai tsawon kamu ɗari, sannan mu cika shi da itace, za mu yi wannan aiki ne a tsakiyar dare lokacin da dakarun ke sharar barci.
A cikin daren zamu tattare a waje guda tun daga mata yara da tsofaffi nesa kaɗan da inda ramin yaje. Wasu a cikin mu sai su kaure da faɗa da hayaniya ta yadda dakaru su zasu kawo ɗauki, wajen kawo agajin za su afka cikin wannan rami, sai mu jefa wuta izuwa cikin rami dakarun su ƙone ƙurmus ba tare da an zubar da jinin kowa ba. Hatta sauran dakarun da za su farmake mu za mu jefa su cikin ramin.
Hikimar yin hakan shine babu wasu dakaru da za su kawo ɗauki domin sai an samu ƙarar takubba za a yi zaton akwai abun ya faru.
Lokacin da alfijir zai keto za mu tunkari masarauta zamu yi amfani da dawakai da makaman yaƙin dakarun kurkuku ne.
Amma ya zama wajibi mu sanya yara da mata a tsakiya a lokacin da muke tunkarar abokan gaba.
Ya ku yana 'yan uwana fursunoni kuyi sani cewa matsawar ba ku sauka daga kan wannan tsari da na kawo ba haƙiƙa babu abin da zai tsare mu daga kawo KARSHEN ZALUNCI a wannan masarauta da nahiyar mu baki ɗaya;
Sa'adda Sadauki Ukaiza yazo nan a jawabin shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, cikin hanzari kowa ya watse domin yaɗa shirin bazato ga sauran fursunoni.




Al'amarin shugaban 'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-amir da yan majalisar shi, sa'adda suka luluƙa cikin gajimare suna tsala gudu akan wannan mikiya, bayan sun kammala fafata artabu da su jaruma Rusayyat.
Tafiyar rabin sa'a kacal suka yi suka iso gida. Lokacin da suka sauka sai Fitinatul-amir ya huce kai tsaye izuwa fadarshi. Har A wannan lokacin fadar cike take maƙil da jama'a, bayan ya haye bisa karagar mulki sai ya yi umarni ga MAGAYAKI ya tara dukkan dakarun yaƙi.
A wannan lokaci duk wanda ya ɗaga idanunshi ya kalli Fitinatul-amir sai kaga ya sunkuyar da kanshi bisa ganin yadda yake tsananin fushi.
Al'amarin Hairat 'yar uwar yaro Usaiba mai hatimin takobi kuwa, tun sa'adda Fitinatul-amir ya fita farautar yaro Usaiba da uwar gidansu Rusayyat. Sai ta kasance a hannun waɗansu kuyangi na musamman ba su bari ta fita koda waje. Duk da cewar Hairat ba ta san abin da ya wakana da yayanta da ummunsu ba amma ta ji hankalinta a tashe yake.


***
Kamar yadda sadauki Ukaiza ya tsara haka al'amarin yakasance a cikin kurkukun, bayan an sanar da dukkan bayi abubuwan da aka tsara, wato an kammala ginin wannan ƙaton rami mai ɗauej itace, a daren kwana na biyu sai dukkan jama'a maza da mata suka taru a waje guda, kawai sai samari majiya ƙarfi suka kaure da artabu tsakanin su ta hanyar kaiwa juna naushi da bugu nan take waje ya kaure da ifice-ifice.
Koda jin hakan sai dakarun su ka ɗimauce suka, domin a tunanin su FARMAKIN BAZATO aka kawo masu.
Kash! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, da yake a wannan lokaci gaba ɗaya fitilun kurkukun a kashe suke sai dakarun suka dinga afkawa izuwa cikin wannan rami suna masu tsandara ihu, kuma wani abin mamaki da al'ajabi shine da zarar sauran dakarun sun daina jiyo motsin 'yan uwansu sai su kunno kai wajen, lokacin da su Ukaiza suka tabbatar cewa dukkan dakarun sun afka izuwa cikin ramin sai nan take zaratan samarin suka kunna fitilun ice gami da jefa izuwa cikin wannan rami, nan take wuta ta kama jikkunan dakarun suna ihu da kururuwar neman taimako wasu lokutan sai dai ka ji randan cikin su tana bindiga suna fashewa.
Koda kammala samun wannan nasara sai aka shiga aikin mayar da ƙasar da aka tono cikin matuƙar farin ciki suna masu kiɗe-kiɗe da raye-raye.
Daga nan sai aka shiga fir-fito da fursunonin dake kunne a ɗakunan duhu, aka ɗebi makaman yaƙi aka buɗe ƙofar kurkukun aka kunna kai izuwa gari kamar yadda aka tsara.
Tun kafin a iso izuwa fada aka fara gwabza artabu da dakaru, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje ya cika dodon kunne, jama'a suka kaure da guje-guje gami da ifice-ifice.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya zamana cewa an murƙushe dakarun ta hanyar saukar masu da azabar KAIFIN TAKOBI.
Sa'adda al'ummar birnin suka hango cewa fursunoni ke yin YAƘIN YANCIN BAYI sai suka dinga ɗebo makaman su suna yin shirin yaƙi suna shiga cikin ayarin, domin suma sun gaji da zama a KANGIN BAUTA na sarki Lamsarul-Azlam, wasu kuma farin ciki ne ya cika zukatansu bisa saduwa da masoya da 'yan uwansu da suka shafe tsawon shekaru a kurkuku suna cikin azabar sarki Lamsarul-Azlam.
Kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin birnin ya cika da mayaƙa babu masaka tsinke,
Nan fa birnin ya ƙara yamutsewa da azababban yaƙi mai matuƙar muni da daban tsoro, a wasu lokutan sai kaga badakare ya cika wandonshi da iska, amma sai kaga jama'a sun yi tara-tara sun rafke shi ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Nan fa JINI DA KASA suka cakuɗu waje guda, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda kofatun dawakai ke kartar ƙasa suna turmutsutsu.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tsoro ne da tashin hankali ga dukkan wata halitta a doran ƙasa, domin wata musiba bata kai yaƙi ba, shi ne ke haifar da rasa rayuka, dukiya, mutunci da daraja kuma mayar da yara marayu mata ta zamo bazawara, yaƙi maishar da 'yan maza mataye kuma ya haddasa yunwa, fari da cutuka.
Wannan shi ne abin da ya wakana a ƙasar Darul-Ashmar a lokacin da fursunonin kurkuku suka yi yunƙurin JUYIN MULKI a lokacin da sarki da sarki Lamsarul-Azlam ya kai FARMAKI birnin Madinatul-Afnan.


Sa'adda boka kaddad ya rikiɗa izuwa mucijiya mai kawuna arba'in ya kanannaɗe jarumi Muhassin domin ta kafta mashi sara da kawunan arba'in, a bisa saman tekun Baharul-saljir.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai gimbiya Aslaima ta dako wawan tsalle tamkar an harbo ta daga cikin baka ta sauka akan mucijiyar ta ƙwala kabbara da ƙarfi gami da dunƙule hannayenta biyu ta gabzawa wuyan mucijiyar ɗaya wawan naushi ji kake ruƙus! Ƙas kan ya kare. Kafin cikar daƙiƙa ashirin Aslaima ta ƙarya kawuna ashirin na mucijiyar.
Wohoho haƙiƙa JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji, babu abin da zai burge mutum face idan ya ga yadda Aslaima ke ƙarya wuyan mucijiyar tamkar tana ƙarya siraran busassun ƙirare. Wani abun al'ajabi ma shine yadda Aslaima ke iya zillewa hare-haren mucijiyar.
Sa'adda mucijiyar ta ji TSANANI DA UKUBA sun tsananta gare ta sai ta saki jarumi Muhassin ya faɗo ƙasa ba tare da ya nutse cikin tekun ba yana mai fitar da numfashi sama-sama,
Duk wannnan abu da yake wakana aljani Ramsisul-Ayyam yana tsaye a gefe inda gawar wannan kada yake yana kallo sai ya cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin bajintar da Aslaima ke yi ya ce a cikin ran shi "haƙiƙa Ubangijin jarumi Muhassin buwayi ne gagara misali domin ga shi ya bawa Aslaima JARUMTAKA wacce ba ta daɗe da yin imani da shi ba, amma ya aka yi gimbiya ta kasance jaruma bayan cewa a wannan tafiya koda sauro bata iya kashe wa, amma tana iya yiwu wa saboda makauniya ce ya sanya bajintar ta bata bayyana ba. Amsar tambayoyin da Ramsisul-Ayyam ya kasa bawa kansa kenan kawai ya yi shiru yana mai zuba idanu.
Koda gimbiya ta samu nasara sare kawunan mucijiyar baki ɗaya sai ta sake dako wawan tsalle cikin gwaninta tana mai taka tekun da ƙafafuwanta tamkar tana tsaye a turba.
Take mucijiyar ta rikiɗa izuwa boka kaddad an yi mashi yankan rago jininshi

Please Login or Register in order to submit comment