Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi Amour har yanzu anata fama, insha Allahu, Allah ze kawo sauki…” jinjina kai kawai tayi nan da nan yanayinta ya sake sauyawa tace “Wallahi Sadiya tacuceni , ni nasan ita tamaka wannan mugun asirin, duk inda mukaje cewa akeyi itace tayi wannan kullin saboda taga ita bata taba haihuwa ba, seni nahaihu kuma nahaifa d’ana miji, da mata biyu, shine ta kashemin namijin yadda bazaka moruwa, Allah ya isa tsakanina da Hajiya Sadiya, wata shara’ar nida ita se munje lahira…” hajiya fatima ta karashe tana sharar kwallah. Cikin muryar kwantar da hankali JAROOD yace “Ki kwantar da hankalinki Amour, kinga fa ba’atabbatar ita tamin asirinba, ni nadauka jarrabawar ubangiji ne kawai, insha Allah seya yayemin Amour bawanda yasan gaibu se Allah, duk lalube ake Cikin duhu…” humming kawai hajiya fatima tayi tace “kai yarone JAROOD nafika sanin wacece hajiya sadiya ta azabtar dani tin kana ciki ubangijine ya rubuta sena haifeka JAROOD …” JAROOD yace “Haka ne Amour toh Abar masa komi shi yasan yadda zeyi dani…” ya karashe yana kokarin danne damuwarsa saboda yadda yaga mahaifiyarsa nacikin damuwa. “shikenan Allah ya kawo mafita…” hajiya fatima ta fadi, daman ita macece me hakuri da saukin kai. JAROOD ya amsa da Amin. “Wanzan yacemin ansamu wani me maganin kou ?” Hajiya fatima ta jefo masa tambayar. JAROOD ya amsa da “Ehe Amour, amma nagaji da ziryar neman maganinnan…” “Me nema ai baya gajiyawa JAROOD, ka jure insha Allahu wata rana za adace, inata maka adduah bana bacci sbda kai wallahi…yanzu tinda nazo ma tare zamuje gun masu maganin…” Cewar Hajiya fatima. JAROOD yace “Toh shikenan Amour…” sukaci gaba da hira irin ta d’a da uwa çıkın So da kauna.
Anan gidan yayi azahar tare da mahaifiyarsa sukaci abincin rana, se hira sukeyi taso da kauna, sukayi video call shida mahaifinsa ta wayar mahaifiyarsa. Se wuraren 3;pm suka bar gidan shida Malam Abdullahi wanzan , hajiya fatima taso sutafi tare gun maganin amma JAROOD yaki da kyar yasamu ta hakura bata biyosunba sun rabu Akan ze dawo zuwa dare.

“Wai har Ina ne gun me maganin?” JAROOD ya tambaya malam wanzan dake driving tin Dazu sunata tafiya har sunyi tafiyar 1H amma basu isa ba. Malam wanzan yana driving yace “Mun kusa isa, ,,” JAROOD yace “Wani irin gurine wannan amma dagani dajine kou ?” Malam Abdullahi yace “Ehe amma ba daji sosai ba, karka damu ranka ya dade mun kusa isa…” cikin gajiyawa JAROOD yace “Wallahi nagaji da zakan motarnan..gaba daya ma nagaji da yawon neman maganinnan…” ya karashe kmr ze fashe da kuka. “Insha Allahu wata rana se labari, kwanan nan zaka hau Aiki kama hajiya babba ciki ka dawo kama hajiya karama ciki…” Cikin kwarin guiwa malam wanzan ya fadi hakan. JAROOD yayi murmushi kawai. Yace “Allah amince …” “Amin..” Cewar malam wanzan. “Inka samu masallaci mu tsaya muyi sallah…” Cewar JAROOD malam wanzan Yace “Toh ranka ya dade…” tafiyar 2H sukayi suka isa wani masallaci acikin gari, sukayi packing da motar securities dinsa. sukayi sallar la’asar suka idar sukaci gaba da tafiya acikin wani kasurgumin kauye dake Cikin zariya. “Tafiya kamar ta barin kasa..” Cewar JAROOD daya gaji da tafiyar, seya kwantar da kujera ya tasar ya rasa ma yazeyi dukya gaji saboda be saba tafiya me nisa ba a mota sede ajirgi. “Mun kusa insha Allahu…” Cewar malam wanzan. Jarood yaci gaba da mita “Ai da kawai jirgi muka hau dakasan da nisa har haka…” Malam wanzan de yayi shiru se basa hakuri yakeyi danya kula yagajine. Seda suka kara tafiyar 20mnt kana suka isa wani d’an karamin gida Awani daji gabaki daya dajin gidanne kawai gida adajin, gabas da yamma bawani gida se wannan gidan, mutanen dake zaune awajen gidan sunyi layi sunfi mutane dari uku, kama daga kan jinsin maza da mata, amma gaskiya mata sunfi yawa sun baibaye ko ina ga manyan mutane tako Ina, anyi packing motoci sunfi motoci dari biyu ata farfajiyar bukkar gidan. “Wani irin gida ne wannan kamar gidan matsafa? Dan duk mutumin dake shuka alkhairi baze baro çıkın gari ba yadawo daji…” Cewar JAROOD daya fadi mgnr yana kallon gidan yana kallon malam wanzan. Malam wanzan ya bude baki zeyi mgna JAROOD yaga wani mutum ya fito daga gidan hannunsa rike da wani jan kyalle irin na tsafi. Haka kawai JAROOD yaji sam hankalinsa be kwanta ba gaskiya. “Gidan bada maganine ranka ya dade bakaga mutane tankanba…” JAROOD ya girgiza Kai yace “Gaskiya wallahi ban yadda da gidannan ba, nan gidan matsafa ne, dagani ba Aikin ubangiji ake shukawa ba a gidannan…ajuya mota kawai ka mayar dani Gidan Amour maza cikin hanzari kafin gari ya fara duhu kasarnan ba lafiya bace da ita…” malam wanzan ya kalli JAROOD yace “Haba ranka ya dade musha wannan doguwar tafiyar kuma kace mu juya? Dan Allah ka fita muje kashiga kagani bawai gidan tsafi bane gidan maganin gargajiya ne, shiga kawai zamuyi nariga naje jiya nakama mana layi yanzu shiga kawai zamuyi…” “wallahi bazan shiga ba… dan Allah mu juya kawai wallahi nagaji , bazan kara dawowa ba gun wani neman magani daga yau wallahi, nariga na hakura…@ JAROOD ya fadi. Malam wanzan yashiga lallaminsa da lallabasa kan yashiga amma JAROOD yayi fır yaki, wanzan yayi-yayi JAROOD ya tubure. Dole suka juyo da motar suka dawo kaduna ran Wanzan adagule, sam ba haka yasoba, yaso ace su shiga su amshi maganin yanaji ajikinsa za adace. Amma JAROOD yaki, hakan ba karamin batama wanzan rai yayi ba. A anguwar sarki sukayi sallar Magriba, awajen gidan kana suka nufa falon Hajiya Fatima atare shida JAROOD, daman Hajiya fatima tanata kiran malam wanzan saboda tasan inta kira JAROOD bezama lallai yana kusa da wayarsa ba, sbda shi ba ma’abocin waya bane, amma yana kiran mahaifiyarsa sede itadin tafiso takira malam wanzan, tafi sabuwa da hakan. amma JAROOD inyaga kiran mahaifiyarsa yana dauka. “Malam ina
zakaje? JAROOD ya juyo ya kalli malam wanzan ya jefo masa tambayar, ganin yanaya binsa zuwa falon mahaifiyarsa.


This book is 1k 08101626484.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
FIL’AZAL
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
(Romantic and love story)

https://chat.whatsapp.com/CyBhsjJtnx7C5FWgP88xX1

SAADATUBINTUABDULLAHI✍🏽(Writer of Kyautar Allah)

This book is 1k 08101626484.
Free page3
Malam wanzan ya kalli JAROOD yasan dalilin dayasa ya masa wannan tambayar. “Zanje gun uwata ne nima mu gaisa ,ko angaya maka kai kadai keda Giwar ne…” cewar malam wanzan. JAROOD yayi murmushi yace “Ku tsaya a gaisuwar, wlhi karka sake ka gayama Amour naki shiga gun me maganin…” “toh..” kawai malam wanzan yace da JAROOD, amma badan ya dauka ba. Suka isa falon da sallahma Hajiya fatima na kasa tana zaune da charbi a hannunta sanye da maroon hijjabi har kasa, dagani yanzu ta idar da sallah tana lazimi. wani sabon kamshi ke tashi a Falon da Sassanyar sanyin AC. Tin shigowarsu ta washe baki hadi da Amsa sallamar tasu tace tana kallon JAROOD. “Sannu Vie moi…” “Yawaah Amour…” JAROOD ya fadi yana karasowa gareta ya tsugunna ya gaidata ta amsa kana ta dawo da dubanta ga malam Abdullahi wanzan wanda shima ya zube se kwararo mata gaisuwa yakeyi. Ta amsa fuska sake tace “Ga kauna, ga kaunah…” JAROOD yayi murmushi shima malam wanzan din murmushi yayi, sun fahimci me take nufi, daman hakan takece Musu inta gansu tare. “Zauna mana malam wanzan kabani bayanin yaya ake cikin Yanzu kuka dawo daga gun maganin? Ina fatan de a dace?” Hajiya fatima ta fadi mgnr tana kallon malam Abdullahi dake tsugunne tinda ya gaisheta be zaunaba. Zaunawa yayi Akan lallausar carpet din dake falon yana facing hajiya Fatima ya kalli JAROOD yaga shima shi yake kallo ya wani hade rai. Amour ta kalli Wanzan ta kalli JAROOD ta kula da irin kallon da yake ma wanzan. “Inajinka bani bayani nana, kasan wannan Karan bazanbar kasar nan ba insha Allahu se naga ya Ake ciki?” Hajiya fatima ta kara fadin hakan tana tsare malam wanzan da idanuwa. Yayi shiru ya kasa magana saboda ya rasa meze ce. “Ya kayi shiru kuma inata magana ko kana tunanin wani abunne??” Hajiya fatima ta kara jefo wa Malam wanzan tambayar ganin yayi shiru tanata mgna shiru. Malam wanzan ya dauke idanuwansa Akan JAROOD ya dake ya fara magana cikin girmamawa kansa kasa yace “Ranki ya dade Allah ya kara Miki lafiya, wallahi munje gun maganin amma JAROOD yaki shiga, kuma munasa ran maganinsa zeyi aiki amma nayi-nayi JAROOD yaki shiga wai gun tsafine, wallahi ranki ya dade seda na tabbatar da inganci gurin me maganin sannan na kaisa…” nan da nan hajiya Fatima ta hade rai jin bayanin malam wanzan, ta kalli JAROOD Wanda ya hade rai sam beso wanzan ya fadama Amour abinda ya faru ba. “Kai haka akayi?” Hajiya fatima ta taare JAROOD da ido hadi da jefo masa tambayar ranta a matukar baci. Kallonta yayi yaga bacin ran dake kan fuskarta yayi hanzarin sauke idanuwansa , yayi kasa da kansa. “Kiyi hakuri dan Allah Amour…” JAROOD ya fadi cikin kankan da murya. “Hakurin me? Meyasa zakayi haka ? Waishin ko zugaka akeyine? Yaya kakeso amaka ne wai? Atunaninka Wanzan ze kaika inda za a cuceka ne? Dashi me cutarwa ne, da tini mu iyayenka baka taso ka ganmuba! Wani irin rashin tunani ne wannan ka farayi JAROOD? wannan ai rashin mutimcine ana fafutukar lafiyarka kanawa mutane wulakanci da rashin mutumcin, wannan Ai tsantsar wulakancine,,” hajiya fatima taketa fadin hakan cikin fada. JAROOD ya jima bega fushi da fadanta ba se yau, tadinga masa fada ta inda take shiga bata nan take fita ba. Shi kansa malam wanzan yayi nadamar gayamatan da yayi ganin yadda taketa fada, tamaki bari JAROOD din ya bude baki ya mata bayani, se fada take masa, shi kanshi malam wanzan be taba ganin fushinta irin na yau ba. “Dan Allah ranki ya dade Kiyi hakuri wlhi bansha zakiyi masa fada haka ba, nasha natsiha zaki masa Dan Allah ki masa natsiha kawai ranki ya dade, yafimu damuwa da abinda ke damunsa, abunne da gajiyawa ranki ya dade…” malam wanzan ya fadi cikin kidimewa bakaramin kidimasa fadan da takeyi yayi ba, sam ma besha haka take ba se yau. Nan da nan JAROOD ya shiga hayyacinsa ganin yadda taketa fada, se yanzu yake nadamar rashin shigarsa gun me maganin, danma Allah yasa wanzan ya d’an mata magana dan yaga ta d’an sassauta fad’anta. “Kiyi hakuri Amour dan Allah, zamu koma gobe insha Allahu, Dan Allah baba malam ka bata hakuri Gobe da sassafe zamu koma insha Allahu…” Cewar JAROOD daya fadi cikin kwantar mata da hankali. Se yanzu Hajiya fatima tadanji sanyi aranta jin yace ze koma gobe. Ta kalleshi tace “Kamin Alqawari zaka koma goben?” JAROOD yayi hanzarin cewa “zan koma wallahi insha Allahu Amour, bansan abinda ze bata ranki wlhi…” d’an sakin ranta tayi tace “Yawwa ko kaifa Allah yamaka Albarka JAROOD wlhi ina tsananin san inga ka warke, shine burina na duniyarnan dani da Sarki, Allah ya nunamin randa zanga ka warke, wlhi duk Akan lafiyarka naketa wannan fadan, gobe in Allah yakaimu dani za Aje insha Allahu…” malam wanzan yajin dadin mgnrta t karshe yace “Yawwah Ranki yadade kwara aje dake din..” JAROOD ya kallesa ya masa wani kallo, malam wanzan yaki yadda ya kallesa. “Wai sekace dole zuwa gun maganin…” JAROOD ya fadi aransa cikin gajiyawa, tinda ya taso yake zuwa gun neman magani ina zakaje neman magani daga ina kake neman magani, yana çıkın jarrabawa. Anan gidan sukayi sallar isha’i a masallacin wajen gidan. Ranar a nan sukaci abincin dare, sukasha hira su ukun se sha biyu nadare Sukabar gidan zuwa gidan JAROOD. A hanya JAROOD ya dinga kunkunan meyasa Malam wanzan yagaya ma Amour yaki shiga gun me maganin. Malam wanzan najinsa bebi takansa ba harya gama kunkunan nasa.
Suna dawowa gidan. direct JAROOD ya nufa part dinsa yasan yau ranar girkin Hajiya Zulaikha ne bazuwa zatayi ba. Bedroom dinsa ya nufa wanda yayi kyau ya gaji da kyau. Ya fada bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya shirya cikin lallausar kayan bacci Se sanyin AÇ da AÇ kawai ke Aiki a dakin. Ya fara jero sallolinsa na dare kmr yadda ya saba, ya sallame. Ya zauna yanata lazimi, har zuwa lokacin sallar Asubahi, seda yayi sallar asuba 6:30am ya kwanta bacci haka yakeyi akullum baya bacci se yayi sallar asubah,. Juyi ya dingayi akan makeken dankareren gadonsa na alfarmar komi a bedroom dinsa green ne da milk color. Juyi kawai yakeyi timeis to time yanata tsuki ga bacci cike da idonsa amma ya kasa yinsa sbda tunanin dake cike fal da zuciyarsa, gaba daya tunaninsa ya ta’allaka ne dazuwa gun amsar maganinnan shifa harga Allah besan zuwa amsar maganin wallahi, amma ba yadda ya iya kodan Amour yazaman masa wajibi yaje. Se wuraren 8:30 yasamu bacci ya fara figarsa. Yajawo wayarsa yayi typing message ma Lambar malam wanzan ya tura masa kamar haka. “Se 2:pm inna tashi a bacci zamuje amsar maganin in case in Amour takiraka kace mata se 2:Pm zamuje gun amsar maganin kaddarar.” Ya tura masa malam wanzan naganin karashan abinda yace asakon yayi murmushi kawai. abangaren jarood yana tura masa sakon ya kifa kai nan da nan bacci me nauyi yayi Awan gaba dashi.


*** *** *** *** *** *** *** ***
*SHIN WANENE JAROOD?*
*** *** *** *** *** *** *** ***
Asalin mahaifinsa Sarkin Agadez Abdulmuminu Haifaffen cikin garin Agadez ne, shi kadai iyayensa suka haifa amatsayin namiji, yanada yayyi hudu duk mata ne. Abdulmud’allab da Fa’iza sune iyayensu. mahaifinsa Abdulmud’allab ya gaji sarauta ne agurin mahaifinsa, kasancewarsa shi kadai namiji a yaran babansa. Shima se ubangiji ya bashi namiji d’aya wato Abdulmuminu, bayan rasuwar mahaifinsa Abdulmud’allab da mahaifiyarsa hajiya Faiza mace me kirki duksun rasu. Abdulmuminu ya Auri Hajiya Fatima matarsa ta farko itama cikakkiyar buzuwa ce, kmr yadda yake shima buzu ne, tin tana 10yrs ya aureta har takai 20yrs bata samu haihuwa ba, dan haka ya karo aure saboda haihuwa yake nema ido rufe musammamma ta d’ana miji saboda yanaso yasamu magaji. Ya Auro hajiya Sadiya itama cikakkiyar buzuwa ce, hajiya sadiya tinda tashiga gidan sarki Abdulmuminu taketa neman yadda za ayi tasamu haihuwa kota halin yayane, amma abu yaci tura, ko bari takasa yi itama duk bin bokayenta da malamanta Amma abu ya faskara. Ana çıkın haka ubangiji yabawa Hajiya Fatima Wacce Ake kira da Giwar Sarki ciki, nanfa sarki ya rikice da murna, ya ninka tarairayarsa da kauna Akan hajiya fatima daman yana santa kowa ma yasan yana santa sbda Auren Soyayya sukayi da ita, Hakan ne yasa yake kiranta Da giwar Sarki Abdulmuminu. ita kuma hajiya sadiya ya Aureta ne danta haifa masa yara, sam baya santa zan iya cewa de arashin uwa ne yayi uwar daki. Hajiya sadiya tinda takula hajiya fatima nada ciki tashiga shige ficen yadda za’ayi çıkın ya zube, tayı-tayi abu ya faskara, seda aka haifi cikinnan akayi rashin sa’a agareta aka haifa d’ana miji. Ranar hajiya sadiya batayi bacci ba, tanada Aminiya Hajiya bara’atu ta kirata a rikice tini suka dunguma gurin boka sukace akashe yaron, boka be boye Musu ba yace baze yuba akashe yaron, ya sanar dasu in suka matsa se sun kashe yaron su suna iya mutuwa har lahira. Jin hakan ya matukar firgita Hajiya sadiya ta kalli kawarta tace “Toh meye mafita…” hajiya bara’atu tace ba wata mafita domin ita kanta ya kulle. Hajiya sadiya tayi jim can wata dabara ta fado ranta, ta roki bokan daya kashe masa gabansa na har abadan ta yadda baze moruba har abadan a tunanin hakan zeyi sanadin daze kashe kansa da kansa, sbda namiji ba Bura Ai ba namiji , wato de ze zama Gashi a raye amma matacce ma yafisa daraja. Tini boka ya aiwatar mata da hakan, sannan ta karada asa masa tsanar sarauta da masarauta, tasa a nisanta zuciyarsa ma da kasar Agadez baki daya, acewarta bataso ya girma ya mulqa kasar Agadez tinda ita bata haihu ba kwara kowa ya rasa mulkin ita da hajiya fatima. Batare da Hajiya fatima da sarki sun sani ba akasha suna yaro ya amsa Sunan mahaifin babansa wato kakansa Abdulmud’allib ake masa lakabi da JAROOD, sarki ya dauki san duka duniya ya daurama JAROOD, Hajiya sadiya takasa cire San JAROOD azuciyar sarki, wannan San na Allah ne tayi kadan ta rabasa, haka bokanta yagaya mata.
JAROOD Yanada 5yrs aka haifi Mardiya,. Kasancewarta mace yasa Hajiya sadiya rashin jin damuwa sosai amma fa bakin ciki kmr ya kasheta ganin ita shekaru nata tafiya Amma shiru bata haihu ba bama alamar zata haihu kullum tana ziryar yawon zuwa gun bokaye amma ba riba, kullum se kara dilmiyewa takeyi kudinta nagun bokaye Gashi ba kudine dasu ba se abinda tasamu agun miji, amma taki nutsuwa kai inka ganta bakace matar sarki bace kullum a lalace take sbda tasawa rayuwarta mugun Abu da hassada da bakin ciki, ta rantse tukunyar Hajiya fatima bazata tafasa ba, gashi ta-ta ko zafi takiyi, karfin asirinta ke zaunar da ita agidan Sarki Amma Sam ba kaunarta yake ba, danginsama sam basa santa saboda bakin halinta da rashin haihuwar da batayi ba.
ita kuma hajiya Fatima daman yar Waziri mahaifin Abdulmuminu ce, sam ba ruwanta ga hakuri ga Addini, ko magana ma bata dameta ba, seda Aka Auro Hajiya Sadiya shine tayi baki na dole ganin irin cutarta da Hajiya Sadiyar keyi, tashigo tasameta da mijinta amma kuma ta dage dole seta fitar da ita a dakin mijinta bayan ita tazo tasameta. Hajiya Fatima tazo ta kara haihuwar yarinya mace Sajeeda,. Hajiya sadiya tashiga shige da fice har seda taga ta dakatar da hajiya Fatima daga haihuwa tinda ita bata haihu ba, ahakama bada san ranta aka haifa ukun ba, da ace da yadda zatayi databisu dukta kashe yara ukun. Sarki yakuma san hajiya fatima ita da yaranta saboda yafi samun kwanciyar hankali da hajiya fatima ita hajiya sadiya ko iya tarairayar miji da kulawa batayi ba se hauka dabin bokaye da makirci. Haka JAROOD ya taso kwata-kwata bayasan harkar sarauta, har zuwa balagarsa, ko irin mafarkannan na balaga sam bayayi, bayasan mata kwat-kwata, koya gansu basa burgesa kuma basa bashi sha’awa ko kadan, baruwansa da kowa, inka gansa da wani toh da malam wanzan ne shine ko ina zasuje tare suke zuwa , makaranta ma tare suke zuwa kafin dağa bisani yazo yabar kasar yake Egypt yayi karatunsa Akan Kasuwanci, burinsa kawai kasuwanci bayasan wani harkar sarauta ko mulki-mulkinnan. Seda JAROOD yakai 20yrs mahaifiyarsa ta fahimci a gaskiya beda lafiya saboda sam bata ganin yana Abu yadda maza keyi , Ya taso da kyau sosai da kwarjini ga kwakwalwa mata nasanshi sosai amma seta kula shi sam mata basa gabansa, sema daya zauna taji yanata sukar mata yana zaginsu, afari tasha aljanace ta auresa. Dan haka ta dukufa nemo masa magani. seda yakai 25yrs ne sukaje gun wani me magani shi yake tabbatar musu da gabansa be Aiki acewarsa kuma gaban nasa baze taba Aiki ba har abadan. Ba karamin tashin hankali hajiya fatima da sarki suka shiga ba harshi JAROOD din hankalinsa ya tashi. Hajiya Fatima tadinga kuka tin kafin ace asiri aka masa taji Ajikinta asirin aka masa kuma tasan hajiya sadiya ce ta masa dukda de batasan gaibu ba amma biri yayi kama da mutum. Me martaba ya dinga bata hakuri yace insha Allahu ta kwantar da hankalinta duk inda magani yake seya nemo masa. Aka fitar da JAROOD kasashen waje domin a nemo masa lafiyar gabansa Amma duk inda akaje sede likitoci suce su lafiya lau suka gansa basuga wani ciwo a tattare da gabansa ba. Ko ina akajefa mgnr daya ce agun lokitoci har şarkı ya gaji ya dawo ga magungunan gargajiya sune basu can basu nan, amma har yanzu ba’adace ba, hajiya sadiya kam tana gefe tana dariya zuwa yanzuma wanda yama JAROOD mugun asirin ya rasu tanada tabbacin bawanda ya isa ya karya asirin afadin duniya acewarta. A haka har JAROOD yakai 30yrs har yanzu yana kan karatunsa a egypt ya hadu da Abokai yan Nigeria harma yakan bisu Nigeria ağarın Kano, in anyi Hutu a school dinsu, da haka yasaba da Nigeria yaji Tafi masa dadih Akan Niger, tin me martaba beson zuwansa Nigeria har yazo ya hakura ganin yadda JAROOD din keson nigeria suma suka fara zuwa Nigeria gün iyayen abokanayen nasa sbda JAROOD din zumunci ya kullu atsakani toh acikin abokan nasa Akwai wani Hassan dan kaduna ne, JAROOD yazo yana Binsa kaduna daga kanon gidansu İbrahim, har yazoma yafi sabawa da kadunan, yazamana har gidaje sarki yasaya a kadunan sbda JAROOD suma kuma sukazo suka saba da kadunan, JAROOD ya fara kasuwanci kadan-kadan a kano da kaduna yana duba abinda babu seya Saro Akasar waje, a haka yadinga habbaka yana karatu kuma yana kasuwanci shide ba ruwansa da mace. Zuwa lokacin tini anyima mardiya aure anan cikin agadez din. Hajiya fatima taje nemawa JAROOD magani awani kauye dake Cikin Agadez, anan me maganin yace ai warakar JAROOD na jikin mace, yace amasa aure. Hajiya fatima Nadawo wa tasanar dame martaba, ya gayama Babban amininsa wato wazirinsa sarki beda wani Amini daya wuce Waziri İbrahim,. Tini Waziri İbrahim yace ya bama JAROOD yarsa Zulaikha dukda kuwa yasan da rashin lafiyar gabansa. Şarkı yayi murna sosai, hajiya fatima ma tayi murna sosai Abangaren JAROOD sam beyi murna ba sbda shide yasan beda abinda zeci yarinyar mutane, dan haka besan yazeyi ba, yaso subarsa ya mutu a haka. Mahaifiyar Zulaikha da Zulaikha sunyi murna sosai, mahaifiyar Zulaikha bahaushiya ce Hajiya Safiya cikakkiyar yar nigeria ce haifaffiyar kano. Zulaikha daman tanasan JAROOD amma Sam batasha abinda ake fadi nacewar gabansa be Aiki da gaske bane seda akayi Aure, akasha bikin da ba atabayin irinsa ba Akab garin Agadez din. Amarya ta tare a gidan sarauta Agadez, tanata jira taga miji yazo dakinta amma har Akayi 1week bezoba, Zulaikha atime din kusan 20yrs take daman a hannu, a hannu take takosa taji namiji a gabanta. Seda tayı 2month agidan taji still shiru bata rasa ciba bata rasa shaba, amma sede ango beshigo ba sbda koya shigo besan meze mata ba. Seda tayi 1Month agidan zuwa lokacin JAROOD ya shigo dakinta sun kwana tare ma sun tashi shiru, tafiya tayi tafiya har akayi 3yrs shiru Zulaikha se atime din ta tabbatar da dagaske ne abinda ake fadi, sbda ko hannunta JAROOD be taba rikewa ba, kuma gata cikakkiyar mace ta tara kayan ruwa ajikinta. Akayi 5yrs zuwa lokacin taje ga iyayenta da niyar araba Auren mahaifinta ya mata fada sosai, ya tabbatar mata da duk randa tasake ta rabu da JAROOD toh karta dawo masa gıda kuma ta tabbatar da tsinuwarsa ta tabbata akanta inhar tamatsawa JAROOD yasaketa. Sarki Abdulmuminu beji dadin wannan hukukçun da Waziri ya yanke ba, ya basa hakuri akan kawai araba Auren, Waziri yace ai baze yuba Yarima ba mata ai mutumcinsu ze zube, hakan kuma zesa mutanen Niger su dinga zargin JAROOD wasuma bacewa zasuyi beda lafiyar Gaba ba, sede akwakulo wani sharrin amasa. Dole Zulaikha takoma dakin Aurenta taci gaba da zaman hakuri, bata inda JAROOD be wadata ba kawai matsalarta rashin Bura, ita daze dena mata komi ya bata bura yafi mata komi dadih wallahi ita kadai tasan me takeji, dataji ta koshi se gabanta ya fara Ruwaaaaa, da vibrating. Daman karatun likitanci takeyi taci gaba da karatunta, har JAROOD ya gama nashi karatun ya roki iyayensu Dazu yadda ya koma nigeria domin zuwa lokacin kasuwancinsa yayi kwari sosai a nigeria musamman a arewar nigeria dama kudun baki daya, har gidajen mai garesa sunfi goma a arewa musammanma a kaduna, ga motoci yanadasu Treloli sunfi dari. kuma kawaishi yafijin dadin zama akaduna, yasan Kano sosai , amma gaskiya kaduna tadanfi masa dadin

1 Comments On FIL'AZAL
avatar
nana-4-8

6 months ago

Reply

Mungode Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment