Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyi murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Yanzu ina Abuja gobe Thursday zan koma Yola. In sha Allah ranar Sunday zan iso Ethiopia domin in samu in ɗan huta dan inada tafiya ranar Tuesday, kuma Ummeey malam ƙasar ne suka ɗan riƙeni shiyasa.”
Ya ƙare maganar cikin Yaren Amharic wanda shine asalin Yaren Ummeeyshi, yayi mgnar cikin sanyi tare da juyowa jin sallar Sheykh Isa Ali Pantami.
Da sauri ya sallami Ummynsh tare da katse wayar.
Ruggume juna sukayi shida Sheykh Isa Ali Pantami.
Yayinda PA'nsa keta ɗaukarsu hoto, gami da ɗan video.

Bayan sun gaisa ne suka wuce wurin taronsu da manyan malam Sunnan.
Inda suka bashi kyautar murya kira'a mafi daɗi da soyuwa a shekarar.

Washe gari da safe jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Adamawa Yola

Cikin farin ciki da jin daɗin mutumtaka da kima daya samu daga Manyan Malamai da kuma jama'ar Nigeria.

Yah Abubakar ne ya ɗaukoshi a Airport ɗin.
Awaje suka haɗu da Abba wanda ya fito daga Masallaci bisa alamu yayi walaha ne.
Cikin so da kulawa Abba ya ɗan ruggumeshi tare da cewa.
“Barka da sauƙa lfy”.
Sai kuma ya kalli Adam daya buɗe but ɗin motar ya fito da jakarsa yana ɗan ja.
“Masha Allah isa daga ciki, ka samu ka huta, kasha zirga-zirga a titunan ƙasarmun nan da ba cikekken kyaune da suba bare tsaro”.
Kai ya ɗan jinjina domin Allah ya sani a gajiye yake, ga yunwa dake kwaƙular cikinsa haka Allah yayinsa baya iya cin abincin kirki in ba matsa mishi akayi ba, so yake yayi wanka yaci abinci yayi bacci.

Shi yasa yana shiga BQ ɗin kai tsaye bedroom ya wuce.
Adam kuma jakar tasa ya ajiye mishi kana ya nufi cikin gida.

A kitchen ya samu Ishmah tsaye cikin wani tattausan lace pink and sky blue collar mai ɗan ratsin Royal blue.
Ɗinkin doguwar rigace da Idris ɗinta ya watsa mishi ɗinki na alfarmar, sosai ya zauna a jinkinta ɗas da ita.
Sai wani irin fitinenne ƙamshi take zubawa, ta murza daurin a setta tayi kyau sosai a ciki.

A hankali take motsa gas meat and Emargency Sultan chips da yaji naman kaza ziryan ɗinta ba ƙashi ko kaɗan sai ɗan Vegetables kaɗan.
lashe baki yayi tare da cewa.
“Uncle Taj ya iso fa”.
Da sauri ta juyo dan bata san ya shigo ba.
“Ya Salam to miƙo min Food flack' and mug ɗinnan”.
Ta ƙare maganar tana jawo trayn.
Miƙo mata yayi tare da ɗan jawo plate ya miƙa mata kana yace.
“Toh nima a saka min a nan”.

Tana juye Gas meat ɗin a wani kekkyawan food flack's dan madaidacin tace to.
Sai kuma ta juyo Sultan chips ɗin ma.
Kana duk ta jerasu a kan tray ɗin.
Sai kuma tasa plate, bowl, mug, sai spoon and fork.
Duk ta jerasu kana ta miƙa mishi tray tare da cewa.
“Yauwa gashi ka kai kan Dinnin table na BQ sai ka dawo ka amshi naka.
Sannan ka ɗauko min Laylah a gidansu Minat, tun juya suka tafi basu dawoba gashi ya dawo bata nan”.
To kawai yace kana ya ɗauki trayn ya juya ya fita dan sauri yake ya samu ya dawo yaci wannan haɗin.

Ita kuwa Ishmah da sauri ta buɗe fridge Yoghurt fruits data haɗa mishi ta ɗauka tare da faro water ta sasu a tray tare da glass cup.
Kana ta fito, a Falo ta samu Rahman bisa alamu da Khadijah take waya dan jin tana cewa.
“Tunda kika komafa nake ta cewa ki haɗani da Maamah amman kinƙi, Maamah ɗiyar Khadijah babbar kenan”.
Tana fita ne tace mata.
“Please ki gyara kitchen nan, kuma ki maida tukunyar danderun nan kan gas”.
Tana miƙewa tsaye tace to.

Shi kuwa Taj a hankali yake feshe jikinsa da turare, lokacin da ya gama kimtsa kansa cikin tattausar jallabiyarsa Black collor.
Ɗan gajere tsaki yaja tare da gyara robar boxer ɗin jikinsa.
Allah ya sani shi baya son takura, musamman ma Taj ɗinsa dake fama da tsaurin ido, shiyasa in a gidansa yake baya iya zama da Boxers dan bazai iya takura kansaba Allah bai takurashi ba.

A hankali ya ɗan shafa cikinsa jin yadda ya ɗanyu ƙugin yunwa.
A hankali ya fito Parlour.

Dai-dai lokacin kuma Ishmah ke ajiye trayn hannunta bisa Dinnin table ɗin kana ta kalli Khairat ɗiyar Yah Abubakar wacce saboda Laylah bata nanne yasa ta biya ta ɗaukota suka taho tare.

A tare suka sauƙe numfashi mai nauyi kamar da sauri ya kuma rumtsa idanunsa saboda jin alamun zaiyi loosing confidence ɗinsa aiko tuni ya gaza control ɗin bakinsa kamar a fizge yaji yace.
“I miss you so much Ishmah”.
Wani tattausan murmushi ta sakar mushi tare cewa.
“Miss U to my friend”.
Ɗan kwaɓe fuska yayi tare da shafa kan Khairat kana ya ɗan kalli bayan Ishmah yace.
“Laylah fa?”.
Kujerar dinnin table ɗin ta jawo mishi tare da cewa.
“Bismillah zauna, Laylah tana gidansu Minat yanzu Adam zai ɗaukota”.
Cikin sauƙe numfashi gaji ya zauna tare da juya gajiyayyun idanunsa murya a gajiye yace.
“Im tired my heart”.
Ya ƙarashe mgnar can ƙasan maƙoshinsa saboda shi kansa baisan ta fitoba, hakazalika itama bataji ƙarshenba.
Cikin tausayawa da kulawa tace.
“So sorry sun gajiyar da mijin Meymey ko”.
Ganin kallon da yayi mata ne yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta, kana a hankali ya jawo trayn nan Yoghurt fruit ɗin ta zuba mishi a bowl mai ɗan girma kana tasa mishi table spoon tare da miƙa mishi tana faɗin.
“Gashi fara da wannan kafin in zuba maka abinci, so nake ka shanye kafin in zuba maka”.
Amsa yayi tare da ɗan lumshe idanunsa su huɗune kacal suke mishi haka a duniya.
Ummeeyshi, Yah Abana, Addawa, da kuma ita, sai kuma Aunty Rashidansa.
Ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe lokacin da ya kai Yoghurt fruit ɗin bakinsa ya Salam, garɗin madara Apple Banana da kuma zaƙin inabi ne suka haɗu suka sashi fara sha.

Murmushi tayi tare da kallon Khairat dake cewa.
“Goggo Ishmah bani wayarki”.
Miƙa mata wayar tayi kana ta ɗauki plate gefe kaɗan ta sa mishi farar shinkafa, tare da ɗan ɗaura yankakken lemun tsami daya a kai, sai kuma gefen tasa Sultan chips ɗin ɗaya gefen kuma tasa gas meat ɗin da yake zuba ƙamshin da kan iya tada yunwa.

Cikin kulawa ta ɗan jawo bowl ɗin gabanshi ganin ya shanye saura kaɗan,
Table spoon da fork ta sa mishi a gefe da gefen, kana ta miƙa mishi.
Da sauri ya fidda idanunsa waje alamun yayi yawa.
Ita kuwa kwaɓe fuska tayi cikin yanayin da bata san tana shigaba tace.
“Please ka cinye”.
Ta ƙare maganar tana sa mishi ruwa a glass cup ɗin.
Shi kuwa Taj kanshi ya ɗan longwaɓar yana yi mata wani irin amintaccen kallon dake fita daga wani sirri daga can cikin ƙahon zuciyarsa yana cusa shi cikin tata zuciyar a sirrance.
Ganin ta tura bakine yasa ya fara ci.
Ya salam ya gamsu Ishmah ƙarshece a komai.
Yanayin yadda ta haɗa mishi abincin kawai ya ishe ka sha'awa.
A hankali ya fara ci suna ɗan hira.
“Uhmmm kasan yanzu naga an buɗe TikTok da IG da sunanka sosai, har Channel aka buɗe a You tube da sunanka. Suna ta saka karatuttukanka.”
Murmushin yayi tare da tauna tsokar kazan da yasa a baki yace.
“Da haka suma zasu samu lada”.
Ruwan ta miƙa mishi tare da cewa.
“Harma da kuɗi ai ƴan You tube kam zasu samu”.
Kanshi ya jinjina tare da zuba mata ido jin tace.
“Wannan trolling fa, naga bada shi ka tafi ba”.
Ruwan ya ɗan kurɓa tare da cewa.
“Gomnan Borno ne zulum yayi min irin kyautar da kikayi min, da naje Bauchi kuma Sheykh Tajuh Usman Bauchi shima ya bani tsala-tsalan alƙyabbu guda uku, harda rawaninsa”.
Cikin murmushi tace.
“Basu dai haɗa maka da mata ba kam ko? Dan naga yadda suke ta ribibinka nace wannan dai da alama zasu baka mata biyu ka cika ta huɗunka a Nigeria”.
A hankali ya ture plate ɗin tare da jawo Tissue box.
Ita kuwa plate ɗin ta kalla yaci yafi rabi, tunda yazo ma baici abinci mai yawa kamar hakaba, hakanne yasa ta ɗauki ɗaya plate ɗin ta rufe abincin kana ta tura trayns ɗin gefe.
Shi kuwa Taj ruwa yasha, sassayan gyatsa yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.

Ita kuwa Ishmah a hankali tace.
“Ɓoye min zakayi dan an baka mata a ƙasarm..”
Sai kuma tayi shiru tare da ɗan zuba mishi idanunta saboda ganin yadda ya longwaɓar da kansa kana idanunsa sukayi jazir, lip inshi na ƙasa ya ɗan ciza murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ai dama kafin in samu matar aure a ko ina a faɗin duniya a Nigeria na fara samu, damace da ban samuba, da ƙaddara dake ta ɗawainiya da rayuwata yasa bamu kasance a tare a inuwar aureba”.
Da sauri tace.
“Taj a Nigeria kuma? Wacece ita? Me sunanta? Yaushe kuka haɗu? Meyasa baka gaya min ba?”.
Kafe kwayar idanunsa yayi cikin nata, itanma shi ta tsare da idanunta tana jiran amsarta cikin sanyi ya motsa lips inshi a hankali yace.
“Ita na fara sani kafin ko wacce mace, bayan Mahaifiyata kakata da yayuna mata. Rashin ta ne yasa ƙaddara samun damar juya rayuwata, domin da na aureta bazan taɓa auren wata ɗiya mace ba a duniya, ita kaɗai ta isheni, inada yaƙini zata kula dani kulawar da mata huɗu zasuyi min, shiyasa a kanta na ajiye burina na auren mata huɗu, domin da wannan burin na tashi a rayuwata Inyi mata huɗu kamar Yah Abana, ko wacce ta haifa min yaya 12 ko 6-6 Kinga in na samu ƴaƴan sha bibbiya zan samu yaya 48 in kuma shida shida na samu kinga 24, Inyi musu irin tarbiyyar da Yah Abana yayi mana, domin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam yayi alfahari dasu a ranar goɓe ƙiyama.”
Sai kuma ya fesar da wani irin raunataccen numfashi mai cike da dafin so kana ya juya gajiyayyun idanunsa cikin nata.
Hakan yasata kasa janye idonta cikin nata.
Shi kuwa Taj murya can ƙasan maƙoshinsa yaci gaba da cewa.
“Tun randa na ganta naji na janye wannan burin domin nasan zatayi min duk abinda mata huɗu zasumin, kuma bazan iya yi mata kishiyaba dan inayi mata kishin kaina da kaina, dan nasan in na aureta ta isheni ko yaya 6 ko biyu ta haifa min sun isheni kai ko bata haihuba zan rayu da ita, kin mance ina gaya miki in na auri wacce rai da zuciyata keso bazan mata kishiya ba”.
Ya ƙare maganar da iyakar gsky zuciyarsa, da sauri tace.
“Taj ashe akwai wani abu naka a duniya da kake ɓoye min ban saniba, toma me yasa baka aureta ba Taj?”.
Cikin sanyin halinsa da murya yace.
“Ɓoyeyyiyar ƙaddara, bata buƙatar namiji irina, gashi kuma Kinga yadda ƙaddara ta kawo Meymey cikin rayuwata, ke kuma kika liƙo min Adaya a rayuwata, so yanzu bani ba ƙara aure a duniya, domin zan bar gurbin wacce nakeso, shiyasa bazan taɓa cika mata huɗuba, dole zan bar gurbin da duk randa ta soni so na aure zan aureta”.
Ido kawai ta zura mishi tana mamakin kalamansa.
Sai kuma tayi saurin cewa.
“Yauwa ya batun Adaya ma yaushe zata tare”.
Da sauri yace.
“Kiyiwa Allah ki bar brain ɗina ya huta”.
Ya ƙarashe maganar cike da alamun tarin bacci da gajiya.
Da sauri tace.
“Toh amman wai meyasa baka haɗani da Meymey ba, ko ta'aziya baka bari tayi min ba”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Nace miki bazan taɓa haɗaki da duk wacce akace matata bace”.
Da sauri tace.
“Wai dan Allah saboda menene?”.
Ba tare daya bari ta ƙarasa mgnar ba yace.
“Saboda kada wata rana suce, kin munafurcesu ko kin hancincesu koma suce kinci amanarsu”.
Da sauri itama ta miƙe tsaye.
Sai kuma ta tsaya ganin ya juyo ya zuba mata ido tare da cewa.
“Itama dayar shiyasa ban haɗaku ba”.
Ta buɗi baki zatayi mgna kenan akayi kiran salla.
Haka yasa tayi shiru.

Bayan sun gama bin kiran sallan da yin addu'a ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Da jarida kika karanta dan shi ya dace dake ba aikin likitanci ba. Kin wani tsareni da tambayoyi tuhuma, takaicina ma ba gane komai zakiyi ba, Ni bari inje inyi salla in na dawo kuma zanyi bacci ne”.
Da ido ta rakashi har ya ɓacewa ganinta, daga nan itama ta kama hannun Khairat suka nufi side ɗin Aunty Nana a falonta suka sameta tana salla, itama salla ta niyanta.

Azahar yana dawowa yayi baccinsa, kiran salla la'asar ne ya tada shi.

Suna dawowa su Laylah na shigowa da gudu suka nufi BQ ɗin ganin ya shiga, Mahmoud, Minat, Khalid, da kuma Khairat cikin nitsuwar tarbiyya suka gaidashi daga nan suka fara kallon Tom and Jerry da akeyi.
Shi kuwa Taj System nashi ya ɗauka ya fara duba shirye-shirye tafiyar da zayyi da ƙasashen da zai jajje in ya koma ma sai yayi kusan mako biyu yana zirga-zirga in yayi hutun mako ɗaya kuma zai sake tafiyar da zayyi kwana goma.

Yau asabar, ta kama gobe Sunday ne jirgin Adamawa to Abuja zai tashi da safe, na Nigeria to Ethiopia kuma zai tashi da yamma.

Bayan an idar da sallan la'asar ɗin. tare suka shiga falon Abba cikin sauƙe numfashi Abba ya kallesa kana yace.
“Tajuddeen ɗazu da muke shigowa naji kamar kana cemin yaushe zaka tafi?”.
Cikin girmamawa da mutumtaka ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh Abba in Sha Allahu ina so gobe zan tafi Abuja daga nan zan wuce Ethiopia da yamma”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Abba ya sauke kana cikin fesar da numfashi yace.
“Taju mun gode Ubangiji Allah ya saka da al'khairi”.
Kansa aƙasa ya amsa da.
“Ameen ya Allah Abba”.
Numfashi mai nauyi Abba yaja kana ya fesar tare da cewa.
“Taju akwai wata alfarma da nake nema awajenka”.

Cikin wani irin baƙon yanayin da zuciya ke ɗauka abaxata ya kalli Abba cike da girmamawa yace.
“Abba Kace Umarni zaka bani ba alfarma zaka nema ba. Saboda kafi ƙarfin neman alfarma awajena sai dai ka bani Umarni kamar yanda Yah Abana zai bani Umarni”.
Zama Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin gskyar zuciya da amincin da yakeji akan Taj ɗin yace.
”Um-um Tajuddeen Alfarman dai nake nema”.
Cikin jin nauyi da ganin kimansa ya sake risinar da kansa tare da cewa.
“Abba idan kana faɗin haka kunya nake ji”.
Kai Abba ya girgiza cikin sauke ajiyar zuciya da sanin kiman da muntuncin Taj yace.
“A'a Tajuddeen dole ne ince haka”.
Manyan Idanunsa Masu haske ya lumshe Muryarsa dake cike da nutsuwa ya gyara tare da faɗin.
“Abba wace alfarma ce wannan?”.
Zama Abba ya gyara kana yace.
“Tajudden Nasan al'aƙarka da kai da Mamana alaƙace data kasance mai tsabta cike da tsarkakekke zuƙata, irin hasken nan dake haskaka juna wanda aka gina saboda Allah kasan irin ƙaddarar dake bibbiyar rayuwar Mamana?”.
Cikin wani irin yanayi mai gauraye da zaƙuwar jin ƙarshen mgnar ya jinjina kai. Tare da sunkuyar da kansa ƙasa Muryarsa cike da sanyin da ƙasan sa farin cikine yace.
“Sosai ma Abba na sani”.
Cikin damuwa da rauni Abba yace.
“N.....!



Littafin nan dai na kuɗine ki biya ki karanta cikin aminci 1k ne 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa.



*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/13, 1:34 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 11*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Littafin INDA RAI na kiɗine wannan free pages ne mukeyi kuma suna gab da ƙarewa, 1k ne kacal kuɗin samur karanta littafin ki saya ki karanta cikin aminci. 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc ne jaka ɗaya kenan rak zaku tura Kuɗin karanta littafin +22790899076 ita zakuyiwa magana*

“Nasan cewa tana fuskantar matsala akan Aure, amma itama ya kamata ace ta gyara niyarta, banason in matsa mata saboda banason tayi tunanin na takura mata akan matsalar rashin Aure, bana kuma jin daɗin zamanta haka babu aure abin yana min ciwo yana hanani bacci Tajuddeen, domin mutane laifina suke gani, faɗi ake na barta tana abinda takeso ta hau babbar mota taje aiki tana zirya a gari ba aure”.
Cikin tausaya Taj yace.
“Bakomai Abba in Sha Allahu watarana zai wuce kamar bai faru ba”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Abba ya gyara zamansa tare da cewa.
“Haka nake fata shiyasa nake so ka taimaka min da wani abu saboda naga Mamana tana fahimtar maganar ka tana kuma jin shawararka”.
Ahankali Taj ya sake sunkuyar da kansa ƙasa yana mai sauraron bugun zuciyarsa dake tabbatar da mgnar Abba haka take, yasan Ishmah na bin shawararsa sosai yasan akwai good understanding a tsakaninsu.
Abba kuwa cikin sanyi da yaƙinin Taj zai fahimtar da Ishmah ya cigaba da cewa.
“Kaga ga Mahaifin Yaranta nan yana sonta yana ta ziryan zuwa zai maida ita itace taƙi bada haɗin kai, bamu sani ba wala Allah Rabo ta dashi ne yaketa kauda sauran Mutanen da suke zirya wurinta.
Zuwa yanzu Yayana Muhammad Bello, ya fusata a kaina, baya ƙasar ne shiyasa baku gabana, ya tafi Uhmra dashi da iyalansa, kuma da yake su a Gombe suke da sauran ƙannena zaman aiki ne ya kaisu can duk mafiya akasarin Family na suna Gombe, babban yayan mu ya fusata sosai a kan Aysha yace min kusan dominta ya tafi umra zai roƙi Allah yayi mata zaɓi da mafi alkhairi, ya tabbatar min wlh muddin ya dawo zai ɗaura mata aure da duk wanda yaga dama ko tana so ko bata so.
To dan Allah ka tayani bata baki sannan ka nuna mata amfani da muhimmanci yin auren da kuma muhimmancin komawa kan ƴaƴanta saboda ɗa sai da Uwarsa kuma itama uwa saida ƴaƴanta, ka sanar mata yadda mukayi da ɗan uwana in fa ta sake har ya dawo ya huta gajiya ya taho daga Gombe zuwa nan tofa tayi kuka da kanta a kan duk abinda yayi mata ta sanshi tasan halinshi zai aikata duk abinda yace, gashi suna tare da wasu manemanta a can Gombe”.
Lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tana bugawa yayinda zufa ya shiga tsatstsafo masa duk da sanyin da ake yi ga kuma sanyin AC.
Haka nan yake ji kamar wani abu mai masifar nauyi ne Abba keson ɗaura mishi, ji yake yi kalaman Abba na firgitashi kana suna sauƙa a kan jiki da zuciyarsa tamkar rushi yake watsa mishi, shiru yayi batare da yace komai ba saboda lips inshi sun mishi nauyi...

Abba kuwa ganin yanayinsa ne yasashi sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.
“Tajuddeen Shiyasa nace maka al'farma nake nema saboda na san zakayi tunanin idan kasa baki acikin maganar zata yi fushi da kai ko wani abu amma koda tayi fushi da kai nan gaba zata fahimci gaskiya ka faɗa mata tunda dama ai ita gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata”.
Kai Taj ya jinjina ba tare da ya iya motsa lips inshi ba.
Abba na gyara zama yace.
“Toh ka nuna mata muhimmanci haka idan kuma tace.
Dr Nafi'u zata jira toh ta cigaba da jiranshi amma Dr Nafi'u bazai Aureta ba ka gani tun yaushe ake abu daya sai abu yazo sai yaja kwanaki”.
Runtse Idanu Taj yayi cikin tsananin bugun zuciya daya baibaye shi.
Abba kuwa cigaba da cewa.
“Ko yaushe sai jan kwanaki yake yanzu haka ya dawo yace wai akwai wani course da zai je Indi'a yayi na wata shida sai dai ta jira idan ya dawo daga course ɗin sannan ya ƙara da cewa wai idan ta samu wani tayi Aure ta kawai.
Toh kaga wannan alama ce ta ya janye hannunsa akan neman Aurenta kuma ga Alqasim mahaifin ƴaƴanta yana bibiyarta tayi haƙuri ta koma kan ƴaƴanta ta riƙe ƴaƴanta ta bawa ƴaƴanta tarbiyya da kanta shi yafi mata Al'khairi ”.
Numfashi mai nauyi yaja kana ya ɗago idanunsa tare da cewa.
“Abba nayi al'ƙawari zanyi mata magana kuma in Allah yaso ya yarda zaka ga sauyi”.
Cikin jin daɗi da samun sassauci Abba yace.
“Toh Allah yasa adace”.
Cikin sanyi da rauni ya sake sunkuyar da kansa tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Abba kuwa Idanu ya zuba masa yana mai tuna mafarkin da Dadeey ta faɗa masa tsakanin Taj da Ishmah cikin sauri ya kawar da tunaninsa Aransa yace.
“Ai mafarki ba gaskiya bane”.
Nan dai Yah Muhammad ya shigo sukayi hira dashi.

Bayan an idar da sallar Isha'i Ishmah da Tajuddeen ne aharabar gidan agarden amma ba ainihin cikin garden ɗin ba suna daga farko ƙasan Bishiyoyin ayaba yana zaune tana masa Video fuskarta ɗauke da Murmushi kana tana mai jujjuya fararen idanunta acikin nasa tace.
“Kayi karatu mana kayi karatu”.
Ƙwayar idanunsa ya juya kamar yanda takeyi yace.
“Toh wace surah zan karanta Miki?”.
Tana mai gyara wayar tayi Murmushi tare da cewa.
“Ni kowanne ma ka sani ina so in dai acikin muryar kane tana yimin daɗi”.
Ɗan murmushi yayi tare da faɗin.
“Toh Bismillah”.
Camerar ta saita akansa tana mai cigaba da Murmushi dake bayyanar da fararen haƙoranta.
Shi kuwa Taj anutse yake kallonta tare da motsa lips inshi yace.
“Dawo nan kusa dani”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Laylah Minat dake can gefe tare da cewa.
“Laylah!, Laylah!! Zo ki riƙe wayar”.
Da sauri Laylah tazo ta amshi wayar video ta fara.
Miƙewa yayi tare da ɗan gyara tsayuwarsa, a hankali itama Ishmah ta mike ta matsa kusa dashi kaɗan.
Sai kuma ta kallesa shima kallon ta yayi kana ya ɗage mata girarsa ɗaya tare da faɗin.
“Ya dai?”.
Tana tura baki tace.
“Ashe dai ka fini tsawo?”.
Murmushi yayi wanda ke sake fitar da kyawun fuskarsa yace.
“Ohhh dama ke tunani kike dama tsawon ki ya kai matakin da zaki iya kamani atsawo?”.
Narkar da Idanu tayi kana tayi Murmushi tare da cewa.
“Aini nayi tunanin baka fini tsawo ba”.
Hannunsa ya ɗan ɗaga kana ya ɗaura saman akanta..

Laylah kuwa murmushi take tana cigaba dayi musu Video Minat ma murmushi takeyi.
Shi kuwa Taj kuwa murmushi yayi cike da aji yace.
“Kalli fa zan iya daura plate akanki inci abinci”.
Ware idanunta tayi tare da faɗin.
“Lallai dai kam haka kace amma idan na sa hill ai bazai yi ba”.
Lallausan sajensa dake ƙyalli da sheƙi ya shafa kana yace.
“Um-um ai ko kin sa bazaki gagareni ba dole dai kece a ƙasa na”.
Sai kuma ya gyara tsayuwar sa tare da yin Bismillah Laylah kuwa cikin sauri tayi serving wannan video ta sake farawa daga farko wanda ba ƙaramin kyau sukayi ba.
Ita kuwa Ishmah shiru tayi tare da tsura mishi ido, tana mai sake mishi lallausan murmushi.
Kallonta yayi tare da faɗin.
“Wacce surah kike so in karanta Miki?”.
Sanyayyan numfashi ta fesar kana tace.
“Aini kasan cewa kowacce surah ce ina jin daɗin saurara”.
Murmushi yayi cikin jin daɗin yanda take son muryansa yace.
“Ok bari in karanta Suratul Rahman”.
Cikin jin daɗi tace.
“Masha Allah Ubangiji ya mana Rahma arayuwar duniya da kiyama”.
Ameen ya amsa kana ya fara karanta Suratul Rahman.
_“Alrrahman”_
Ahankali Ishmah ta lumshe Idanunta tana mai motsa laɓɓanta.
Shi kuwa cikin sanyayyan sauti mai sanya nutsuwa azukatan dake saura ya cigaba da cewa.
_“AAallamal Ƙur'an”_
Ahankali ta buɗe idanunta dake lumshe ta zuba masa tana jin wani irin nutsuwa na ratsa ko wani ɓargo da tsokar da jinin dake gudana asassan jikinta.
Kallon gefen Idanu ya mata tare da faɗin.
_“Khalaƙal Insaan”_.
Wannan karon kam kasa jurewa tayi haka nan taji alamar idanunta nason tsatstsafo da ruwan hawaye yayin da wani irin salama da aminci ke baibaye ta...
Haka ya riƙa jero ayoyi dake ratsa zuciya.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Nana ta fito harabar gidan da alamu zasuje unguwa ne dan ga Khalid da Yah Muhammad har zata shiga mota ganinsu yasa tayi Murmushi tare da kallon mijinta da yake gaisawa da Taj ɗin.

cikin girmaman darajarsa da kwarjin hasken Alqur'ani tace.
“Barka da dare Sheykh”.
Cikin sanyinsa cike da kamala ya ɗan risinar da kansa yace.
“Aunty Nana Barka da fitowa”.
Tana murmushi tace.
“Barka dai al Sheiky bari muje Unguwa”.
Yana kallon Ishmah yace.
“Sai kun dawo”.
Kai ta gyaɗa kana ta shiga mota, da sauri Minat ma tabi bayansu .

Ahankali ya maida kallonsa kan Ishmah tare da cewa.
“Gobe in Allah ya kaimu da safe zaki rakani gidan Hajja Umma in gaisheta, da Aunty Hawwa, Aunty Aysha, har ma da gidan Garkuwa inje in gaishe su ko”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh Allah ya kaimu lafiya”.
Ameen ya amsa kana sukaci gaba da hirarsu.

Washe gari da safe tsaye Ishmah take a kitchen ta jingina jikin sink ɗin kitchen numfashi ta fesar tana tunanin mai zata girkawa Taj na breakfast.
Fridge ta buɗe ta ɗebo naman rago zallan tsoka ta wanke kana ta yanka albasa tare da saka maggi, garlic, curry, seasoning, sai ruwa kaɗan gass ta kunna ta daura tana tsaye ya tafaso kwashewa tayi ta zuba man gyaɗa cikin ƙaramin lokaci ya soyu bata

Please Login or Register in order to submit comment