Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ƙutsa ta gefen hajarul Aswad.
Wani irin matsa taji taro jama'a sunyi mata har numfashinta na kwabcewa Amman hakan bai hanata kutsawa ba, zuwa yanzu ji take kamar sawunta baya taka ƙasa, tana makalene a tsakanin kafaɗun manyan matan Chaina mutane masu kama da aljanu dan ƙarfi.

Wani nannauyan ajiyan zuciya mai tafe da raunataccen kuka ta saki lokacin da taji ta jikin ka'aba.
Fuskar ta ta manna da jikin Ka'aba murya na rawa ta fara jero tarin addu'o'inta da buƙatunta cikin raunatacciyar Muryar da tasa makusantatan juyowa suna kallonta.
Wanda gefen damanta Ummeyn Tajj ne, gefen hagunta kuma Addawa ne sai Tajj ɗin dake tsakanin kafaɗarta data kakar tashi domin itace ta kutsa ta shiga tsakanin nasu, jin yadda ta kutsone yasa ya ɗan janye jikinshi duk da bai ga waye bane.
Jin sautin kukanta da muryarta ne yasa ya juyo ya kalleta cike da mamaki.

Ita kuwa Aysha cikin raunatacciyar murya da sassayan kuka take addu'o'in da yaruka uku Larabci, Hausa, fillancin. Kusan duk take haɗesu waje ɗaya.
”Yah Allah ka sauƙaƙamin ƙaddarata, ka juya min ita izuwa kekkyawa mai daɗi, Alhamdulillah Allah na gode maka ka bani rai da lfy, da damar zuwa wannan tsarkakekken wuri, Yah Allah kaine kace mu roƙeka.
Ya Allah ka tabbatar min da alkhairi tsakanina da wannan bawa naka Barrister Kamal, idan har aurena dashi alkhairi ne ya Allah ka tabbatar mana dashi, ka tausashi zuciyar matarsa, ka bamu zaman lfya, ka hanani samun damar cutar da ita, itama ka hanata samun damar cutar dani.
Yah Allah idan har ba alkhairi tsakanina da Barrister Allah ka sauya mana da abinda yafi alkhairi a garemu. Ka fito min da mijin aurena na alkhairi ka bayyana minshi akan alkhairi kasa mana dangana tsakanin zuƙatanmu ya Allah in dai Barrister ba alkhairi bane a gareni, ka alaƙanta wanda yake alkhairi a gareni ka kuma nuna min ranar aurena.
Ka kuma sa mana haƙuri nida Barrister.
Ya Allah kayi min kekkyawar rayuwa ka bani kekkyawar ƙarshe ka shafe zunubaina.
Ka haskaka duhun zunubaina da hasken gafararka. Yah Allah ka raya min yarana kayi musu al'barka, ka shirya minsu bisa tafarkin gsky.
Yah Allah ka bawa Mahaifiyata lfya mai ɗorewa.”
Sai kuma ta kakare saboda kukan da ya taso mata daga can ƙasan zuciyarta, wanda yake son fizge numfashinta ta, da kyar ta iya jawo numfashi kana taci gaba, da jero bukatar ta, na nan gidan duniya da ƙiyama.

Yayin da Ummey da Addawa da Yah Abana, duk suka zame daga wurin dan bawa wasu damar samun kusantar ka'aba, ita kuwa Aysha ji take yi tamkar wahayin buƙatunta akeyi mata Shiyasa suka ƙi ƙarewa.

Tajj kuwa, tsintar kansa yayi, da shiga lamurran addu'o'inta, more especially yadda take yawan, mai-maita Allah ya bawa mahaifiyarta Dadey ta lfya ya yaye mata cutan dake damun, kawai ji yayi yana mai kwaranyowa Dadeey addu'o'in samun, lfya tare da ambaton babban sunanta Fatima kamar yadda yaji Aysha nayi.
Sai kuma ya ɗaura da tayata, Addu'ar shirya ga ƴaƴanta, da take kira.
Mahmood, Minat, da Khalid.
Ya tsinci zuciyarsa da tayata, Addu'ar.
Kana ya ɗaura dayi mata addu'ar da ta buwayi kunuwansa da ita.
Samun miji na gari, da fatan in dai tsakaninta da Barrister ba alkhairi to Allah ya sauya mata.
A ƙarshe suka shagala da neman rabauta na duniya da ƙiyama, da neman tsari da azabar ƙabari, da wutar jahannama, suka cike gurbin du'anin da neman jannatul Firdausi.
Yayin da gaba ɗaya kwayar idanunsa ke kan ƴan yatsunta da Maryam ta watsa mata mashahurin lallen amarci.

Cikin sanyin jiki, ta fara kiciniyar juyowa.
Ido cikin ido sukayi dashi,
lumshe idanunta tayi, sai ga hawaye shar sun kwaranyo.
Kai ya jujjuya mata alamun tayi shiru, sai kuma ya zaro tattausa hankicib dinsa mai ni'imtaccen ƙanshin ya miƙa mata, tare da juyawa yayi mata alamar su fito.
Ba musu ta amsa, tare da sharce hawayenta da kuka yasa idanun suka ɗan kumbura.
Da hanzarin ta fara bin bayansa, duk inda ya cire ƙafarsa nan take dire tata ƙafar, domin ya zame mata Garkuwa daga cunkoson mutane ba dan shiba tana da yaƙinin wannan gabza-gabzan Matan sun turmusheta.
Tafiya mai yawa sukayi, har suka fito can wajen harabar masallacin.

Shi bai tsayaba ita bata daina binshi ba.

Wani shago dake farkon titin da suka miƙa ɗin ya shiga,
ita kuwa a bakin wurin ta tsaya, jim kaɗan da shigansa ya fito, da wata ƴar leda a hannunsa.
Hannunshi yasa ya zaro, wasu tattausan safan hannun masu masifar kyau da taushi ya miƙa mata.
Cikin ɗan tsura mata ido tare da tausasawa yace.
“Kisa wannan, in kinyi lalle ki dai yawo haka ba safan hannun, domin junnu suna saurin shigarku ta wannan sigar, musamman ma irinki, da kike da ƙalwaya.
Kuma ko a sheriya ma bai halatta ki bayyana adonki ga ko wanne Tom and Jerry ɗin ba.”
Ya ƙarashe mgna da danne wani abun dake taso masa a ƙahon zuciyarsa.
Amsa tayi ta sanya, kana ta amshi ledan.

Daga nan suka fara tattaki, suka nufi masauƙinsu domin tsakaninsu ba nisa.
Nashi ne a forko, so a bakin ya tsaya tare da kallonta cikin fuskar aminci yace.
“Fatan Allah ya maidaku lfya, Allah yasa munyi Hajji Mabrooq.
Idan kin koma ki gaida min Dadeey da jiki, Allah ya bata lfya mai ɗaurewa, yasa wannan ciwo nata zakkan jikine.
Allah yasa kuyi farar jinya ki gaida min su Mahmood kuma kiceea Abba ina gaidashi”.
Ya ilahi bazata iya hana hawayenta zuba ba, domin a duniya maiyiwa Mahaifiyarta da yaranta da Abbanta Addu'a ya gama mata komai.
Kawai sai ji tayi hawaye na kwaranyo mata, kana tana amsawa da.
“Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati ngd matuƙa da addu'o'inka garesu, ka gaida Ummeey da Yah Abana, kace inayi musu fatan alkhairi Allah yasa ka kasance musu al'wadussaliha”.

Cikin kauda kai yace.
“Amin ya rabbi”. Daga nan ya wuce ciki.

Ita kuwa Aysha ji tayi kamar an dasata a wurin, sai kuma ta juya da sauri jin Maryam na kiranta, nan suka shiga ciki.

Alhamdulillah misalin ƙarfe.
Shida kamar yadda suka zo, haka suka taso.

Zuwa yanzu gaba ɗaya Mahajjata duk sun koma ƙasashensu, sai waɗanda jinya ta riƙesu, da kuma ire-iren shugabannin mahajjatan da dole, in akwai ɗan yankin su da ba lfya suke tsayuwa a kula da komai nashi.
Mahajjatan Adamawa duk sun dawo cike da farin ciki da jin daɗin irin karamcin, Amirul Hajj ɗinsu yayi musu.
Gashi duk kayan mutane ya dawo kan lokaci.

Bayan wata ɗaya da, dawowarsu.
Garkuwa ce zaune a Parlour'n Dadeey yayin da Aysha ke miƙa mata cup ɗin data zuba mata, Juice mai sanyi.
Amsa tayi tare da ɗan kurɓa kana ta ajiye, tare da yiwa Dadeey sannu da jiki.
Cikin yanayin alamun sauƙin jikin tace.
“Yau dai ga Garkuwa a Parlour'na, tunda kuka dawo kullum sai Aysha ta bani labarinki”.
Murmushin Garkuwa tayi cike da girmamawa tace.
“Ayyah Dadeey ai kullum ina son zuwa Allah bai nufaba sai yau.”
Murmushin Aysha tayi tare da cewa.
“Maryam jiya uwar haka muna tare ai, Yah Abubakar ne ma ya maidata”.
Gyara zaman Garkuwa tayi tare da cewa.
“Ayyah Maryam nima last two weeks taje min, ita ce ma ke cemin Barrister baya ƙasa ko?”.
Kai Aysha ta jinjina tare da kallon Dadeey dake cewa.
“Uhmmmm Allah dai ya kyauta, Garkuwa lamarin Aysha akwai buƙatar addu'a kigafa irin hidimar da Barrister yayi mata, da yadda yake sonta, Amman batun aurensu ya shiririce.
Ko an mishi mgna sai yace.
Su bari sai gaba akwai abinda yake damunshi.
Ya fito ya faɗi damuwar kuma yaƙi, abinda da kuna dawowa da kwana biyu nefa za'ayi bikin”.
Cike da jimami Garkuwa tace.
“Bakomai Dadeey in sha Allah, wata rana zai wuce kamar ba'ayi ba Dadeey ke dai muyi ta matta addu'a _INDA RAI to da RABO_”.
Cikin danne ƙunan dake zuciyar Aysha tace.
“Kayya Aunty Garkuwa ni na fara karaya da lamarina fa, hakafa duk wanda yake sona sai mgna tayi zurfi tayi nisa na gama duk shirin biki, sai abu yazo ya watse, kuma ka rasa dalili,
Hakafa mukayi da Mukhtar Garkuwa naso Mukhtar har raina, Babanshi yayan Sarkin Gombe ne, lokaci ɗaya abun ya lalace, Garkuwa haukane kawai banyiba lokacin da mgnata da Mukhtar ta watse nayi kuka har na rasa hawaye, Abin takaici kuma haka ma ya faru da Yah Muhammad wani dan Kaduna, abin har ya zame min jiki yanzu kuma ga wasu ma neman sun tasoni gaba basu saniba Ni tsoro suke bani”.
Abba dake shigowa ne dan duba jikin Dadeey yayi ɗan gyaran murya tare da cewa.
“Ba komai Aysha in sha Allah komai zai zo da sauƙi, addu'armu gareki ba zata faɗi ƙasa banza”.
Da sauri Garkuwa ta ɗan zame ƙasa tare da gaida shi,
Cike da kulawa ya amsa kana ya tambayi Dadeey ya jiki, kana ya juya ya fita.

Yana fita sukaci gaba da hirar, tsoron Aysha a haka har mgnar tazo kan abinda tayi a jirgi.
Nan sukayi ta hirar Garkuwa na bawa Dadeey labarin yadda tayi, da yadda Taj ya taimaka daga nan sukayi ta hirarsa.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Shifa da gaske gani yake aljanu gareni”.
Cikin dariya Garkuwa tace.
“Yoh ai koni lokacin kallon mai aljanu nayi miki.”
Tana gyara zamanta tace.
“Ai baki sani ba, rana ita yau iwar haka, kawai sai naga, kira naso in gane number Amman sai na sha'afa.
Ina ɗagawa naji shine!”.
Da sauri Garkuwa tace.
“Ke haba dai dan Allah”.

Tana gyara wuyan rigarta tace.
“Wallahi kuwa, wai ya kirani yaji ya jikin Dadeey har na bata waya suka gaisa dashi, harda Abba ma, sun gaisa”.
Da sauri tace.
“A'a Aysha ko dai? Ko dai?”.
Da sauri cike da gsky da gsky da ya ƙini Aysha tace.
“Yah salam ba wannan mgnar wlh, kin dai san ni nafi son babban mutum”.
Kai Garkuwa ta jinjina domin tasan yes Aysha tafi son babban mutum irin mai mata da yara haka dai.
Ganin la'asar tayi ne yasa suka miƙe sukayi sallan la'asar.

Bayan sun isar ne, Garkuwa ta gyara zamanta tare da cewa Aysha.
Yayan ta Usman nefa ya aikota cewa yana sonta.
So sanin su waye su yasa tace, Allah ya tabbatar musu da alkhairi duk da Usman saurayine Amman tasan ya girmeta nesa ba kusa ba, duk da dai tasan bata da ra'ayin auren saurayi Amman ta nemi zaɓin Allah, daga ranar Usman ya shiga cikin jerin masoyanta.


Yau watansu biyu cib da dawowa, konce take a ɗakinta, tunda tayi sallan azahar bacci yayi gaba da ita cikin, baccin ta fara jiyo ringing ɗin wayarta, a hankali ta ɗan motsa tare da buɗe idanunta ta kalli Fuskar wayar, number Ethiopia ce kana ga sunan Tajj yana yawo a sama ne yasa ta ɗauka tare da karawa a kunne.
A hankali ta kuma lunshe idanunta saboda jin sassayan sautin muryarsa daya ratsa kunnuwanta, cikin yanayin bacci tace.
“Assalamu alaikum Tajjj”.
Sai kuma tayi kasake jin yana cewa.
“Wa'alaikissala Afwan Ishmah bacci kikeyi ko na tadaki?”.
Kai ta ɗan jujjuya tare da cewa.
“Gwarama daka tada ni, ai lokacin salla ya ƙarato”.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da cewa.
“Toh yanzu dai ya jikin Dadeey”.
Murya a narke tace.
“Alhamdulillah jiki da sauki kwanan kuma ya sake tashi”.

“Allah ya ƙara mata lfy, ya Abba dasu Khalid suna lfya ko?”.
Cikin jin daɗin kulawarsa ga iyayenta da yaranta tace.
“Lfy Lau Alhamdulillah, Yah Ummey da Yah Abana”.
Cikin sanyi yace.
“Suna lfya. ki bawa Dadeey waya mu gaisa”.

Toh tace tare da kaiwa Dadeey wayar suka gaisa, kana tace.
“Ba kaƙi ka haɗani da Ummeey ba, sai Addawa sarkin rigima”.
A hankali yace.
“Kiyi sallan zan kiraki”.
Toh kawai tace kana ta katse kiran.

Bayan ta idar da salla kuwa ya kirata sukayi ta, hira wanda mafi akasarin akan abinda tai a cikin jirgine.
Ya ƙara da cewa.
“Yau ne na samo wata passinger daga Jordan zuwa Palastine itama tai tayin yadda kikayi, sai ta tuna min da ke, tunda na fara aikin ku biyu ne, naga kunyi haka”.
Cikin murmushin mai haɗe da kunya tace.
“Wai kai baka mantuwa ne”.
Kai ya ɗan rausayar tare da cewa.
“A dai naki kam bazan manceba”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kwanan ma da Garkuwa tazo muna hirar mukayi ta dariya”.
Cikin kulawa yace.
“Me tazo yi?”.
Kamar a fizge taji mgna ta fito bakinta.
“Wai tazo ta gaya min wai yayanta Usman na sona, yana nan da fuskarsa kamar mace ba saje”.
Sai kuma tayi saurin rufe bakinta.
Shi kuwa Tajj a hankali ya ɗaura hannunsa bisa tattausar fuskarsa, da mafi akasarin ranaku sai ya yaɗe sashensa da gemun.
Cikin nazari yace.
“Toh ina Barrister abin ya watse ne?”.
A hankali tace.
“Eh”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, fahimtar kamar ya fama mata mikin rantane ya sashi cewa.
“Toh ke me ruwanki da rashin sajen na miji ai ba saje zaki auraba ko?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ai fuskar namiji in ba saje da gemu, bata da banbanci da fuskar mace, ni bana son namiji ba saje”.
Kai ya jinjina, tare da cewa.
“Ok yanzu dai bawa Dadeey waya inyi mata sallama”.
Miƙewa tayi ta shiga Parlour'n Dadeey bisa sallaya ta sameta a zaune, miƙa mata wayar tayi tare da cewa.
“Tajj ne wai zai miki sallama”.
Amsa tayi, ita kuma Aysha sai ta zauna a gefe
Dadeey kuwa gyara riƙon wayar tayi jin, Tajj na cewa.
“Dadeey ya jikin da sauƙi sosai ko”.
Yayi mgnar cikin gyara fillancinsa na Ethiopia yadda zata gane sosai.
“Eh Alhamdulillah Tajuddeen jiki da sauƙi sosai ma”.
Cikin jin daɗi yace.
“Masha Allah haka nake son ji, Allah ya ƙara lfy Dadeey sai kina ɗan motsa jikin”.
Kai ta gyaɗa kana yana mai ci gaba da bata shawarwari irin nasu na Doctors.
Daga bisani sukayi sallama.


A hankali rayuwa taci gaba da juyawa, yanayi na sauyawa.
Kwanaki na tafiya makkoni na shudewa watanni na mirginawa izuwa shekaru.

Bayan tsawon shekaru huɗu kenan.
Abubuwa da dama sun faru cikin shekarun nan.
More especially tsakanin Aysha da Tajj, wanda suka gina wata tsabtacecciyar amintakar, dake bisa wani ɓigiggiren, da su kansu basu san na menene ba, sun zama aminai na musamman wanda duk motsin ɗaya, ɗaya na sani.
Sunyi wata iriyar shaƙuwa mai haɗe zuƙata tasa su bawa juna dukkan yarda, Tajj bai taɓa wani abokiba a duniya sama, da marigayi pilot Irfan Imran wanda aka kashe a faɗar tsakanin Palastine da Isra'ila.
Dashi da iyayensa baki daya sai ƙanwarsa Laylah yar shekaru sha biyu, wacce Taj ya ɗaukota riƙonta ya dawo gareshi a Ethiopia a gaban Ummeeyshi. A rayuwar Taj ba abinda Aysha bata saniba, haka shima, hatta denginta ba wanda bai sanshi ba, zuwa yanzu Abba da Dadeey kam jinsa suke tamkar ɗansu, duk da bai taɓa zuwa sun ganshi ido da idoba.

Aysha kuwa Jarrabawar Aure har gobe, tafiyar bata sauya zaniba.

Shaƙuwarta da Garkuwa kuwa abin ya wuce ƙawance ya zama ƴan uwantaka babu abinda ke ɗan sata faranci gami da ɗebe mata kewa kamar karanta littattafan Garkuwa domin a littafinta take samun Darussan rayuwa Ilmantar, Faɗa karawa,kana da Nishaɗantarwa idan tana karanta littafin ji take tamkar azahiri abubuwan ke faruwa...

Maryam ƙanwar Barrister kuwa, Yah Abubakar ɗinta ya aureta har su haihu, Barrister da kanshi zumunci sukeyi sosai dan yana yawan zuwa duba jikin Dadeey da yake ɗan yawan matsa mata ga kuma ƙarin zumuncin da ƴar uwarsa na gidan.

Hakama Mukhtar sosai suke zumunci haka Yah Usman auren ne dai Allah bai sauƙar da shiba.

Shaƙuwarsu da Taj ya wuce dukkan zaton ma zato da nazarin mai nazari, domin halattacciyar shaƙuwace wacce babu saɓon Allah ko kuma gurɓacewa wanda mafi yawan Samari,Ƴan mata da kuma Zaurawa keyi Abota ce da aka gina ta saboda Allah mai cike da sanya zukata nutsuwa.

Zuwa yanzu kuwa, karatuttukan Taj da muryarsa sun zaga duniyar social media, Musamman,Tik-tok,Instergram, Facebook, WhatsApp da sauran Man hajojin sada zumunta domin salon Muryasa tana da maganaɗisu na musamman ga zukatan musulmai koda kuwa baka san mai ake faɗa ba Muryarsa nada wani irin ƙwarjini mai tafiya da hankalin mutum da samar da cikakkiyar nitsuwa da cika zuciya da shauƙin ƙaunar jin karatun ƙur'ani.


Yau ta kasance ranar jumma'a ce.
Ƙarfe ɗaya dai-dai jirginsu ya sauƙa a Addis Ababa bole intranational Airport.
Jim kaɗan da sauƙarsu, bayan an gama gwada dukkan lafiyarsa.
Da sassarfa ya fito ya shiga motar da tuni aka tanadar masa da driver'nsa da tafiya gida.
Yana shiga motar yacewa driver.
“Dan Allah kayi gudu na gasken-gaske domin so nake, in samu jami'in sallan jumma'a a matsalacin. Grand Anwar Mosque nadan Ya Abana na jin daɗi in jashi jam'i”.
Ya ƙare maganar yana kallon Driver da sam baya sauri yadda yakeso, kuna shi sauri yake domin so yake ya samu ya kasance a sahun forko bayan Yah Abana domin shine yake limancin masallacin.
Wayarshi ya zaro tare da kiran Aysha tana ringing kuma bata ɗagaba.

Tsaki mai sauti yaja, domin badon sanin cewa, dokar sune pilot bazasu jan motaba, saboda zasuyi gudu na fitan hankali kasan cewar sun saba da gudun jirgi, badan haka ba da tuni ya amshi tuƙin nan.
Damin cike yake da begen ganin shi cikin ahlinsa, dan yanzu a ƙalla wata uku kenan bai zo Ethiopia ba, kuma duk saboda Meymey ce.

Sake kiran Aysha yayi a karo na uku, numfashi mai sanyi ya fesar jin ta ɗaga.
Cikin aminci yarda shaƙuwa mai zurfi yace.
“Ina kika shiga inata kiranki bakya ɗagawa??”.

“Ina shafawa Dadeey maganine”.
Tayi mgnar tana nazartar muryarsa sai kuma tace.
“Kamar kana hanya ko?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Eh shine na kiraki ai muyi tafiyar tare, yanzu na sauƙa cikin Ethiopia”.

Tana gyara kwanciyarta tace.
“To muje in rakaka”.
Hannunsa yasa yana shafa tattausan sajensa mai masifar sulɓi da sheƙi, kana yace.
“So nake in samu jami'in sallan bayan Yah Abana, kuma sam driver nan baya sauri, ji nake zanfa karɓi tuƙin”.
Da sauri ta ɗan ware manya idanunta alamar tsoro sai kuma ta langwaɓar da kai cikin sanyi tace.
“Please kada ka amshi tuƙin nan, bana so”.
Cikin zu bawa tarin motocin da ya hango a gabansu bila adadin idanu yace.
“Toh yadda kika ce za'ayi”.

Ya ƙare maganar yana leƙa gefe da gefen hanyar ya gane, sun iso Ousman Ibn Affan Tero Masjid ne, kuma shima masallacin jumma'a ne, duk da ya hana subi kan manyan titunan ne saboda sanin, zasu samu an rurrufe hanyoyin yasa yacewa driver subi tsakiyar anguwannin, cab yama mance da wannan masallacin.
Bisa dukkan alamu kuma ana gab da tada iƙamane, gashi hanyar an rufesu tako ina.
“Yah Salam”. Shine abinda yace a dai-dai lokacin da yaga ta bayan nasuma motoci sunfi takwas.
Cikin sanyi yace.
“Dole inyi salla anan fa Ishmah”.
Cikin son amintar mishi da hakan a zuciyarsa tace.
“Eh ba matsala ai Tajj kayi a wurin, ana idarwa sai ka tafi, ka samu ayi liyafar family na yau da kai, tunda kana garin”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Toh in kashe ko in bari, zakiji sautin sallanmu”.
Cikin yanayin shaƙuwa tace.
“Bari inji karatun limamin ko zai samu rabin maki naka”.
Murmushi yayi sai kuma ya ɗan jin-jina kai kana yace.
“To an gama”. Sai kuma ya kalli Dottijon driver nashi tare da juya harshe zuwa Ethiopia's language *Amharic* yace.
“Abu Hashim mu tsaya muyi salla a nan, kana da al'wala ko?”.
Cikin alamun tarin mutunta juna Abu Hashim ɗin yace.
“Na'am”.
Daga nan suka fara kutsawa cikin masallacin.
Kasancewar babban masallacine kuma a ɗan luƙu yake a tsakiyar anguwannin Shiyasa baya irin cika da batsewar nan.

Cikin hikima suka samu suka shiga a har ciki, cikinma sahun farko saboda shiɗin ya kasance mutum sanne a duniya ma baki ɗaya bare kuma ƙasarsa ta haihuwa, duk wanda aka cewa Sheykh Afif Muhammad Taj dole zai sanshi, domin Ethiopia baki ɗaya tana alfaharin kasancewarsa ɗan ƙasar tasu.
Ahankali ya zuro ƙafarsa daga cikin mota wanda ke sanye cikin wani sau ciki baƙi mai masifar kyau da sheƙi yayin da jikinsa ke sanya cikin wani yadi mai sulɓi da taushi Army Color daya haska fatarsa yayin daya ɗaura Farin Suit asama Kansa na sanye da hula yayin da kwantaccen sajensa ya sake ƙawata kyawun fuskarsa cikin sassarfa ya ƙarasa shiga harabar masallacin.
Suna isa ana data iƙama.

Bayan an idar da salla an sallame, kowa yayi addu'o'insa da tasbihansa.
Shima haka Taj, a hankali ya zaro wayarshi tare da karawa a kunne murya a sanyaye yace.
“Kinji mun idarko yanzu zamu fita”.
Murmushi mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
“Naji karatun limamin Amman bai kai naka daɗiba fa.”
Yunƙura yayi da niyar tashi sai kuma yaji ana sanarwar akwai ɗaurin auren da za'ayi yanzu ana roƙon mutanen su ɗan dakata.

A hankali ya koma ya zauna bayan Abu Hashim.

Kana yaci gaba da mgn da Aysha.

Da sauri ya ɗago kanshi ya kalli mutumin dake sanarwar cewa.
“Dangin angofa sun fasa auren bisa wani dalili mai girma da kuma tuburewar ango na cewa ya fasa aure.
Innalillahi wa innalillahi rajiun.
Shine abinda wani kamilin dottijon mai cikar kamala ya fara nanata wa, yayin da lokaci ɗaya jikinsa ya ɗauki kerma tuni idanunsa suyi jazir.

Da sauri ya kuma kalli tawagar dangin angon da suka ɗauki, kayan ɗaurin aurensu irin Goro, Dabino, cingam, da dai sauransu, sun juya sun fara fita.
Da sauri ya kuma maida ganinsa kan dottijon nan da yaga ya fara rarrafawa, ya isa gaba Abu Hashim, wanda dai-dai wurin dangin Angon suke, cikin wata iriyar matsoracciyar murya mai nuna dottijon bashi da ƙoshin lfyma, ga kuma gigita, hawaye na kwaranya a idanunsa ya riƙo sawu, ɗaya daga cikin dangin angon murya na rawa cike da raunin neman alfarma yace.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun, dan Allah da son Manzon mu Muhammad (S.A.W) ku rufa min asiri. Ayi auren nan wlh bani da wani buri da fargaba da ya wuce in aurar Adaya kafin barina duniya.
Nayi muku magiya da girman Allah, ku bari ayi auren nan”.
Sai kuma ya fashe da zazzafan kuka.

Wanda har Aysha najin duk abinda ke faruwa, cikin sanyi tace.
“Allah tsarki, meyasa zasu fasa, dan Allah Taj ka tayashi basu haƙuri ayi auren nan”.
Ta ƙare maganar da iya gskyarta da kuma sanin irin ciwon da mahaifin yarinyar da ita kanta yarinyar zataji, saboda ita tasan zafin dake cikin fasa aure, in ba mai ƙarfin zuciyaba, sai ta buga ya mutu.

Shar-shar taji hawaye na kwaranyo mata, lokacin da taji sautin muryar dottijon nan ya saki raunatacce kuka yana cewa.
“Ma'aruf ka gani ko, yan zuma a karo na uku kenan ɗaurin auren Adaya na watsewa. Ma'aruf zuciyata zata buga saboda matsalar Adaya,
Zatayi ajalina, Ma'aruf ka bisu ka roƙesu da girman zatin Allah su cika min burina kafin wa'adina ya cika, nasan idan na mutu nabar Adaya batayi aureba, ruhina bazai samu salamaba”.
Ya ƙare maganar da kife kanshi a jikin filar masallacin ya saki maraitaccen kuka, wanda aka kira da Ma'aruf ɗinma kuka yaleyi.

Tajj kuwa lip inshi na kasa ya jiza da ƙarfi, sai yake misalta da ace Yah Abananshi ne ke kuka hakan ya zaiji a cikin ransa,
Yasan ji zaiyi kamar zai suma, ya kuma tabbatar sai yayi duk yadda zai yi ya tsaida mishi hawayen nan.

Sai kuma ya maida hankalishi kan Ishmah dake mgna cikin tausayawa.
“Dan Allah Taj ka taimakawa tsohon nan, Please ka tsayar mai da zuban hawayensa”.
Cikin sanyi murya yace.
“Please Ishmah kada kiyi kuka, kin san cewa kukanki na ƙona min zuciya ko, gaya min wanne irin taimako zan mishi”.
Da sauri tace.
“Ka tayashi basu haƙuri ayi auren!”.
Cikin jin kukanta na hautsuna mishi lissafi yace.
“Ai har sun riga da sun tafi”.
Da sauri ya zazzaro idanunsa jin abinda tace, murya a kaɗe yace.
“eyeh hello mai kikace”.
Cikin rauni da kuma iya gskyarta kana da shesh-sheƙan kuka mai cike da rauni tace.
“Tajj ka aureta!!!”.
Da ƙarfi ya koma ya jingina da jikin gini, sai kuma ya kalli Dottijon nan da yake kuka harda majina yana bin.
mutane yana kama hannunsu yana cewa.
“Dan Allah ka auri ƴata Adaya na baka ita.”
Mafi akasari sai su kauda kai.
A haka har ya iso gaba Taj.
Riƙe hannayensa yayi duka biyu, murya na rawa yace.
“Dan Allah dan soyayyarka da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, dan tsarkin Alkur'ani da yake kanka a haddace, da kimar iyayenka Afif ka auri ƴata Adaya na baka ita duniya da ƙiyima ka aureta ka amintar da ita domin irin kane mijin daya dace da ita.”
Jin kalamansa ne yasa jikinsa wani irin saƙewa yayi luƙus sai kawai ya zauna dirshan.
Kana a sashin Ishmah kuwa cikin taya dottijon nan magiya tace.
“Taj! Taj!! Taj!!!”. Sai a kira na ukun ne ya iya furta.
“Uhmmmmm”.
Cikin tausasa lafazi murya na rawa tace.
“Dan Allah dan Annabi da darajar Yah Abana da kuma ƙaunarka da Ummey da Amincinmu, da gskyar abotarmu, da mutuntakarmu, ka aureta ka tsaida hawayen dottijon nan”.
Ya ilahi ya mujibat da'awati, yah hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, innalillahi wa innalillahi rajiun”. Sune iya ababen da yake iya furtawa a bakinsa sai kuma yayi saurin cewa.
“Shiru Ishmah na amince zanyi wannan taimakon saboda Allah da Manzonsa da ke”.
Yayi mgnar da Yaren Hausa da zama shi da itane yasa ya fara iyawa kaɗan kaɗan.
Kana yayi Hausanne saboda yasan da wuya a samu wanda zai gane a cikin mutanen wurin, Amman in fillancin Ethiopia yayi wasu zasu iya ganewa.

Sai kuma ya saki wani irin sassayan numfashi tare da kallon kamilin dottijon nan mai cike da kima kamala da rauni da yake ta zubda hawayen da magiya.
“Ka taimakeni ka auri Adaya Afif kayi min wannan

Please Login or Register in order to submit comment