Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaida kowa dake parlon sannan Nana ma ta gaidasu,su Aliyu ne da Hameed sai Abbas suka shigo suka zauna suma kamar yanda yayi haka suma suka gaida mutanen parlon sannan sukai shiru ,Daddy ne yafara magana da cewa"Aliyu jiya kun ban wata takarda me d'auke da result din scanning din Nana amma banga ne Abun da takardar ta kunsan ba shi ne nakeso kamana bayani kowa ya ji ,Ajiyar zuciya Aliyu yasauke sannan ya ce"eh daddy dama scanning d'in da akawa Nana ne shi ne muka kawo muku Ku gani " kallonshi daddy yayi sannan ya ce"eh to me scanning d'in yace" murmushi Aliyu yayi ya ce"ca akai wai tanada ciki "ita wad'in ?daddy ya katseshi ita Nanan Aliyu ya fad'a kallonshi daddy yayi ya ce " ok kana nufin wannan yarinyar ce takeda ciki?wannan yarinyar ce zata haihu?ya fad'a yana nuna Nana ,kallonsa Hameed yayi ya ce"daddy akwai matsala ne? ko bazata iya bane?naga..wata tsawa da daddy yadaka masa yasa shi yin shiru cikeda masifa daddy ke cewa "Wallahi k'aryane wannan y'ar k'aramar yarinyar ta haihu saboda rashin imani ko saboda bakusan ciwonta ba,to wallahi tun huri gwara kusan Abun yi dan narantse bazata haihu yanzu" A firgice Abdussamad ya d'ago idanunshi yana kallon daddy cikeda karfin hali ya ce"

Story and written by
Nanameera

Meera Love's yhu[12/26/2023, 10:19] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

Naanah


PAGE 0️⃣8️⃣

__________✍️Tsabar shock kasa magana yayi sai kallon daddy yake kamar yanda suma suke kallonsa,Abba ne ya ce"A'a kar ayi haka idan hakanne mafi alkhairi allah ya raba lafiya " a fusace daddy ya ce "Wallahi bazai yihuba kamarya allah ya raba allah? Ai ya raba ma saboda babu yanda za'ai wannan yarinyar ta haihu idan ka matsu kasami yara to ka k'ara aure babu Wanda zai hanaka" Aliyu ne ya ce da mamaki"wai daddy da gaske kake? Nanan ce bazata haihu ba tab!" Cikin jin haushi Abbas ya ce"nima abunda nagani kenan tunda har ta ke da cikin kenan zata iya haifeshi" Uncle Jabeer ne Wanda tun d'azu baice komai ba ya ce"Abbas rashin kunya zakuyi wa mutanen?wato kun girma ko?to wallahi ranku duk zai b'aci,kai Abdussamad d'agowa yayi ya kalleshi ya ce"na'am "kaji abinda akace? Ya ce " naji" to yanzu yayi dare amma idan Allah ya kaimu gobe sai aje asibitin Gidan nan acire cikin"A fusace shima ya d'ago ya ce"what? Uncle cire ciki akanme?meyasa?tab uncle zan iya d'aukar kowane Abu amma banda wannan wallahi, bazan tab'a yarda azubar da cikin jikin Nana ba saboda Nana wahala tace ni nasha wahala akanta bawani ba "yana gaba fadin haka yayi waje rai amatuk'ar b'ace binshi da kallo su Hameed sukai kana suma suka fita..



Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidanshi yana zuwa ya samu Nana zaune tana game a laptop dinshi,tana ganin shi ta tafi da gudu ta rungumeshi ta ce" oyoyo daddyna welcome back " d'aga ta sama yayi ya ce"thank you cweetie ya gidan?" Turo baki tayi ta ce"babu dad'i bakanan kuma har kuka nai " murmushi yayi ya sauketa ya ce"allah sarki Nanan daddynta allah ya barmu tare " murmushi tayi ta ce"ameen daddy amma daddyna me akaima naga ranka ab'ace? Kallonta yayi ya ce"me kikaga?" Kama hannunshi tayi ta ce"kawai tun d'azu naji kamar anb'ata maka rai,amma ka rabu dasu babu abunda zai sameka ga Nana kaji daddyna d'an albarka na " murmushi yayi ya ce"insha allah Nana"murmushi itama tayi sannan ta ce"yawwa daddy muje kayi wanka kadafa mana indomie da kwai tun d'azu nake sha'awarta,kallonta yayi ya ce"yau kuma indomie kikeso Nana?"d'aga mishi kai tayi alamar eh,OK ya amsa sannan ya ce"muje to yafad'a yana rik'e hannunta..



Wajen k'arfe biyu da rabi ne kwata-kwata yakasa barci har yanzu babu abunda yake ji akunnenshi sai kalaman daddy na "sai anzubar da cikin Nana" yarasa wani ma'auni zai saka maganar kenan nufi suke bayanzu zaici moriyar rik'on Nana na tsawan shekaru goma sha shida ba?idan Nana batai masa amfani yanzu ba to sai yaushe? Ganin bashi da amsa yasa shi tashi yayi alola kamar yanda yasaba duk dare yahau sallolinshi har asuba....


Gama shirya warta kenan tasha wani bakin less mai adon fari tayi kyau sosai,sallama akayi ta amsa sannan hajiya Fadeela tashigo kallonta tayi ta jikin mudubi ta ce"good morning mommy "murmushi hajiya tayi ta ce" morning daughter sai ina? Fari Hafsa tayi sannan ta ce"Wallahi zan d'an fita ne kafin anjima saboda inason had'uwa da Abdussamad yau"kallonta mommy tayi ta ce "to kiyi sauri kafin daddynku ya tashi" ok Hafsa ta ce"sannan ta d'auko hand bag da car keys tayi waje ....

Misalin k'arfe uku na rana ne,Zaune suke su kusan goma suna tattauna maganar jiyan sapwan ne ya ce"haba wannan ma ai rainin hankali ne wato duk walahar dayasha akanta ya tashi abanza kenan? Nufi suke sai sanda suka yarda sannan zai bukaci matarsa ?to wallahi bazai yiwuba ai duk ku kuka jawo da Baku wani fad'a musu ba,idan yaso inta haihu saisu kashe abunda ta haifa," murmushi Abdussamad yayi ya ce"easy Mr man ai duk ba Abun tashin hankali bane nagadai yarinyar nan a hannuna take kuma idan yau nacewa Nana kar tasake kulasu nasan wallahi har abada to basai sun ganta ba?" Hameed ne ya ce "ni Wallahi ji nayi kamar na mak'ure daddy ajikin bango saboda yadda yaban haushi,kasa barci nayi jiya ina tunanin mafita" dariya Aliyu yayi ya ce"yanzu dai kubari su dawo muji yanda za'ai ...

Fitorwasu kenan daga masallacin gida ita kuma motarta nashigo wa parking tayi ta inda zasu wuce sannan tafito dai-dai lokacin sukuma suka k'araso kallonsu tayi da murmushi afuskarta ta ce"a'a sannunku daman ana ganinku?dariya Named yayi ya ce"Hajiya Hafsa kin b'uya to ya farin?ya Spain d'in kuma?"murmushi tayi ta ce"wallahi alhamdulilah Mr President yaushe ak'asar?sai asannan ya kalleta ya ce"ai na kwana biyu dazuwa to ya karatun?dariya tayi ta ce"alhamdulilah muna nan munata fama abunka da yara " kallon agogon hannunshi yayi ya ce"to allah ya taimaka broth nizan huce nabar Nana na barci Hafsa sai anjima ko?"murmushi takaici tayi ta ce"allah sarki ina kuwa Nana?nasan yanzu ta girma"murmushi yayi ya ce"tananan kalau "to agaisheta tafada sannan ta ce" nima bari nashiga ciki sai nazo ganin babyn tamu"murmushi yayi ya ce"to allah ya kawoki sai anjima ya fad'a yanayin gaba "sallama suma sukai kowa yayi nashi gidan sai asannan tace " Karka damu zakazo hannu ne dole saina mallakeka "sannan tayi kwafa tayi gaba..

Dukkan y'an familyn sun hallara sakamakon meeting da akace za ayi,shigowa sukai sannan ya gaida kowa na parlon itama Nana dake gefansa ta gaishesu,daddy ne yabud'e taro da addu'a sannan ya ce" abunda yasa natara wannan meeting bakomai bani ila iyaka kowa na family d'in nan yaji abunda ake ciki ,kamar yanda wasu suka gani munyi jiya wasu kuma labari yaje musu ,to yau nakeso komai ya k'are ,Abdussamad yakira sunanshi tare suka d'ago kai da Nana ya ce" na'am daddy "kallonshi daddy yayi sannan ya ce " ba shawara muke nemaba ,umarni ne mun rigada munyi shawara saboda haka yau basai gobe ba za'a zubar da cikin jikin yarinyar nan "kallonshi yake har yagama sannan ya ce" wallahi daddy zan iya bada rayuwata akan azubar da cikin jikin Nana kuma indai ina Raye wallahi bazai tab'a yiwuhu ba yana gama fad'in haka Yakama hannun Nana yayi waje abinshi, Mamace ke kiran Abdussamad!! Abdussamad!! Amma inaa ko juyowa baiyi ba yayi gaba abinshi


Story and written by
Nanameera


Meera Love's yhu
[12/26/2023, 10:19] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

🌹Naanah🌹

PAGE 0️⃣9️⃣

______________✍️Abba ne ya ce"Allah ya kyauta " Aliyu kam mik'ewa yayi ya ce "saida safe" kallonshi Mama tayi ta ce"Aliyu idan ka fita ka kirawon Abdussamad, kace masa yazo yanzu ina jiransa kar kuma nak'ara magana " tom Aliyu ya ce sannan yayi waje,bayan fitarshi Daddy ya mik'e sannan ya ce"dani Abdussamad yake magana wallahi saina koya masa hankali "Uncle Jabeer ne ya ce" Yanzu dai abar maganar sai gobe sai asan abinyi" daga haka kowa yatashi yay gaba.....


Yana isa gida ya tadda Nana tana game kamar yanda tasaba,shiga yayi yana ganin zata taso yayi saurin shigewa daki ya rufe kofar ,kallo ta bishi dashi sannan taje wajen kofar ta tsaya tana knocking tana ce wa"Daddy!! Daddyna!! Kabud'e kaji Daddyna d'an albarka na,yana jinta amma bashi confidence din bud'e mata dan yasan data ganshi zata gane abunda yake b'oyewa,haka taita y'an koke-kokenta har tayi bacci agurin,sai wajen k'arfe goma sannan yafito ya d'auketa yaje ya kwantar da ita sannan yayi mata addu'a ya kwanta......


Wajejan k'arfe uku ya farka yafara sallolinshi kamar yanda yasaba saboda yama rasa ya zaiyi da wannan al-amarin daya tunkaro shi wannan, haka yayta addu'a har aka kira sallar asuba sannan yatashi yatafi massallaci dan gabatar da sallah....


Misalin k'arfe Tara na safe ne suna zaune suna breakfast ,kallonta yake tanata jagwalgala abincin murmushi yayi sannan ya ce"Nana k'oshi kikai ne? "Kallonshi tayi ta ce" A'a Daddy ban k'oshiba kawai abincin ne ba dad'i tafad'a tana kwabe fuska ,murmushi yayi ya ce"ok to yanzu ya za'ai?" Turo baki tayi ta ce"kawai Daddy kabada asiyan fresh milk da cake sai naci" murmushi yayi ya ce"fresh milk ai akwai and cake,bai k'arasa fad'aba Hafsa tayi sallama tashigo, kallonta yayi ya ce"Hafsa ya gida"murmushi tayi ta ce"ina kwana yaya" lafiya lau ya amsa, Nana ta kalla ta ce "Nana zo mana masha Allah kin girma" da sauri Nana ta tashi ta koma wajen Daddynta ta ce"Daddyna bana sonta!!bana sonta!!mu tafi kaji tafada tana Jijjiga shi"murmushi Hafsa tayi ta ce"yaya me take cewa? Murder yayi ya ce"kawai rigima take, fashewa Nana tayi da kuka harda birgima,tsawa ya daka mata sannan ya ce"tashi anan gurin ko ranki ya b'aci" dagudu ta tashi tashiga daki tana kuka,kallonshi Hafsa tayi ta ce"ayyah yaya ai dabaka koretaba yarinya ce"tashi yayi ya ce"rabu da ita Hafsa bansan rigima " tashi itama tayi ta ce"to ni zan tafi daman shigowa nayi mu gaisa " murmushinsa yayi mai kyau sannan ya ce"Allah sarki nima kuwa zani gurin Mama tana kirana bari mu fita tare,ok ta amsa sannan sukayi waje.....


Sallama yayi yashiga parlon baiyi zaton zaiga mutane dayawa haka ba ,zama yayi ya gaishesu, Mama ce ta ce"Abdussamad sai yanzu ko kai baka gudun Abun magana ko?" Sauke idonsa k'asa yayi ya ce"ayi hakuri Mama ban k'arawa" Allah ya kyauta Mama tace sannan ta ce"Abdussamad bansan jayayya kabi abinda aka fad'a maka yanzu za'a je azubar da abinda ke cikin yarinyar nan,idan kanada rabo Allah ya baka a taskar sa kayi hakuri" shuru yayi ya kasa ce wa komai banda kallon Mama dayake ,Ma'a ce tazo ta dafashi ta ce"kayi hakuri kaji son Allah yasa hakanne mafi alkhairi " kamar yanda yayi wa Mama shuru itama haka yayi mata ,uncle Jabeer ne ya ce "ina yarinyar take lokaci na hucewa?" Batare da ya kalli kowaba yatashi yayi waje not too long yadawo da Nana rik'e a hannunshi ya mik'awa Mama ita ,tashi sukai suka nufi asibitin gidan inda manyan likitoci ke jiransu dan yin aikin, suna shiga aka miko mishi file dinta Wanda zaisa hannu,karb'a yayi yasa hannun sannan ya d'auko wata y'ar takarda a hannunshi yayi rubutu kamar haka"Ni Abdussamad MUHD SHUWA IDAN HAR AKA ZUBAR DA CIKIN JIKIN NANA To NIKUMA NA SAKETA SAKI UKU" sannan yamik'awa Daddy yayi gaba abinshi ,warware takarda Daddy yayi ya karanta sannan ya mik'awa uncle Jabeer ya karanta shima Kallon- kallo aka shiga yi sannan Abba ya ce "wai meya faru?" Daddy ne ya mika mishi takarda ya karanta sannan ya ce"subhanallah me Abdussamad yayi haka?",dai-dai lokacin Nana ta k"araso ta ce"Abba Daddyna zani"kallonta Abba yake cikeda tausayawa kafin ya ce"to za'a kirashi jeki ki kwanta" to ta amsa sannan takoma dakin da dake....


Jiniyar motar y'an sanda ce taketa aiki acikin gidan kai daga jin jiniyar kasan wani babba be a hukumar y'an sandan ,murmushi Aliyu yayi ya ce"Alhamdulilah ga kawu nan ya dawo"a firgice suka juyo suna kallonshi.

Story and written by
Nanameera


Meera Love's yhu[12/26/2023, 10:19] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

Nanah

PAGE 1️⃣0️⃣

_____________✍️kallonsu yake har ya k'araso,yana zuwa suka durk'usa har k'asa suka gaishesa, amsawa yayi da fara'a sannan yace "kutashi ya yaran? Mik'ewa sukai sannan Daddy ya ce" lafiya lau yaya sannu dazuwa" yawwa ya ce sannan yayi gaba yana cewa"nagaji bari nahuta sai mu gaisa sosai "yana fad'in hakan yayi part d'inshi, yana shiga Daddy ya kallesu ya ce" toh yanzu Mene abinyi aje ayi aikin ko ajira sai yaya yayi magana? " murmushi Abba yayi ya ce"Eh!hakan ma yafi yanzu bari naje gurinta saboda tafara rigimar kiran Daddynta "OK uncle Jabeer ya ce sannan sukai sallama kowa ya tafi.

Suna tafiya Aliyu ya ce" Alhamdulilah yanzu ai magana ta k'are saboda nasan kawu bazai tab'a yarda azubar da cikin ba" ajiyar zuciya Aliyu ya sauke sannan ya ce "Allah ne yake sonmu da rahama dama ita yarinyar saboda bazata iya hakura dashiba " Hameed ne ya ce"guys ni zan tafi saboda na cewa Ayrah bazan dad'eba,murmushi Aliyu yayi ya ce"wato kai na fuskanci Ayrah ta gama dakai ko? harararshi yayi ya ce"to ba dole ba kullum cikin farantamin take,kaga kuwa dole na sota" murmushi yayi ya ce"OK lemme find my way nima Jalhan na can najira na ,daga haka suka rabu

Wanene kawu ?
Shid'in k'anine ga Alhaji Muhd shuwa kuma shine yake binsa,Ana amatuk'ar girmamashi a family d'in, saboda ya kasance kamar uba a gurinsu ,ya kasance shugaban y'an sandan k'asar nan,wannan kenan.


Misalin k'arfe sha d'aya na dare Nana tafito parlon gidan nasu tana waige-waige kamar me neman wani Abu, Amma ce tafito dan d'aukar Abu idanta ya sauka akan Nana wacce tayi shuru kamar me tunani,k'arasawa tayi kusada ita ta dafa kafad'ar ta ta ce"daughter me yafaru bakiyi bacci ba a wannan Daren? Kwabe fuska tayi ta ce"Amma Nana nason taga Daddynta, ta fad'a cikin sigar tausayi " jawota jiki Amma tayi ta ce"sorry daughter kibari idan Allah ya kaimu gobe sai kije wajen Daddyn naki kinji" shuru Nana tayi ta ce"kinyi alk'awari gobe zaki kaini? D'aga mata kai Amma tayi alamar Eh ,murmushi Nana tayi ta ce"OK nagode amma idan gobe baki kaini ba to zanyi kuka sosai " shafa kanta Amma tayi ta ce "OK naji tashi kije ki kwanta,d'aga mata kai tayi sannan ta tashi tashiga d'akinta ta kwanta..

Next day

Tashi sukai Nana batajin dad'i ,Abba ne yagama shiryawa zai fita Amma tashigo d'akin,zama tayi gefen gado ta ce" yallab'ai Nana fa ba lafiya tunda ta tashi tak'i cin komai, shine nace bari nafad'a maka ko za'a kaita asibiti" tashi Abba yayi ya ce"subhanallahi let me check her yana fad'in hakan yayi waje,tashi Amma tayi tabi bayanshi..

Yana shiga d'akin ya tadda ita ta rufa da blanket yaye blanket d'in ,afirgice ya d'ago ya ganin yanda take jijjiga dasauri ya d'auketa yayi waje da ita.

Sosai akasha wahala kafin asamu kanta Doctor ne yakira Abba office d'in shi uncle Jabeer ya bishi ,Bayan sun zauna likitan ya cire glasses d'inshi sannan ya ce "Alhaji yarinyar nan nafama da ciwon zuciya Wanda kuma na tab'a fadawa sir Abdussamad haka sannan kuma na d'orata akan magani,numfashi ya sauke sannan ya cigaba da cewa" yanzu abinda ya sameta shine ciwon nata ya tashi kuma suna d'aya kawai take kira shine "Daddyna" munyi iya bakin k'ok'arin mu amma abin yaci tura,dole saidai idan shi Abdussamad d'in da take kira yazo shine kawai za'a samu mafita " jinjina kai Abba yayi sannan ya ce "OK bari akirashi " daga haka suka fito dan kiran Abdussamad d'in.


A hanya suka had'u da Aliyu ya sunkuya ya gaidasu sannan ya ce

"Abba daman kawu ne ke kira yana parlon shi" OK sukace sannan uncle Jabeer ya ce "Aliyu je ka kira Abdussamad kace masa yazo yanzu" murmushi Aliyu ya ce "ai uncle dude bai kwana a gidan nanba tun jiya yasa aka kawo masa jet ya koma America" afirgice Abba ya kalleshi ya ce "what? Subhanallahi meyasa son zaiyi haka ?" Kallonsu Aliyu ya ce"to Abba tunda ya gama amfani ai gwara yayi tafiyarsa daga nan ya samu shima yayi aure " shuru sukai sannan uncle J ya ce"Allah ya kyauta " sannan sukai gaba dan tafiya kiran babban yayan nasu..

Zaune yake a katafaren parlon nashi yayinda sukama y'an Gidan suke zaune k'asa Mama ce kawai sai Ma'a akan kujera Wanda kuma su kad'aine mata agurin, kusan five minutes yayi shuru kallon fuskarshi sukai nan suka hango tsananin b'acin ransa ,d'aya Bayan d'aya yake kallon kowa sannan ya ce"sadeeq!! Daddy da yaji an fad'i sunan shi ya kalleshi cikin girmamawa ya ce"na'am yaya" cikin b'acin rai kawu ya fara magana ya ce
"Yanzu Mene amfanin abinda kukayi? me yaran nan yayi muku? Ni a tunanina godemasa ya kamata kuyi sannan ku tayashi murna ,har tsawan yaushe zai d'auka yana kulawa da rayuwarta? ku tunafa sanda aka aura masa ita yaci ace sannan yanada shirin aure ,sa'aninsa duk sunyi aure wasu ma sunada ya' kamar yarinyar da yake riko,amma Abdussamad baiyi jayayyaba ,bai nuna baya soba,haka ya karb'eta hannu bibbiyu kuma yayi ta Kula da ita har kawo yanzu, yayi mata abinda ko iyayenta idan kacire haihuwa basu yimataba amma duk da haka kukeso sai kun rabashi da ita .wallahi kun bani mamaki kuma kunbani kunya ace dai kune zakuyi masa haka,duk hak'uri irin nasa dakuma biyyayarsa saida kuka k'ureshi har takai takawo ya ce idan aka zubar da cikin ya saketa ,kuma duk da haka kuke k'ok'arin zubar da cikin, shashashu kawai,ya k'are maganar cikin Jin haushi.
Shuru sukai dukkaninsu suna sauraransa ,cikin sanyin murya Daddy ya ce" ayi hak'uri insha Allah haka bazai sake faruwa ba" dauke kai yayi ya ce"Allah ya sa,yanzu ina Abdussamad d'in? Aliyu ne ya ce"ai kawu tun jiya da daddare.yabar k'asar, kuma nakirashi wayarsa baya shiga" murmushi Kawu yayi ya ce "Allah sarki mutumina bari ni na kirashi nasan zai d'auka.
Wayarsa ya d'auko dan kiransa Jalhan tashigo da gudu ta ce" Daddy!! Abba!! Doctor ya ce Nana " bata k'arasa maganar ba sukai waje da gudu dan ganin me yasami Nanan


Story and written by
Nanameera


Meera Love's yhu
[12/26/2023, 10:19] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

Naanah

PAGE 1️⃣1️⃣

_____________✍️Suna isa suka tararda Nana kan gadon marasa lafiya tana Jan numfashi yana guduwa,lokaci d'aya kuma ta hau aman jini irin guda-gudan nan,da sauri likitoci sukai kanta ..

Wajen 30minutes kafin asamo kanta, Doctor na fitowa ya tadda su Abba a kofar dakin ,murmushi yayi sannan ya ce

"Alhaji ka kwantar da hankalinka Insha Allah zata samu sauki "

Shuru Abba yayi sannan ya ce

" yanzu Doctor Mene abinyi? "

Kallonsu likitan yayi sannan ya ce" yanzu dai idan har anaso asamu ta samu sauk'i to dole Abdussamad yazo saboda shi kad'aine zata yarda dashi "

Shuru Abba yayi kana ya ce

"To amma yanzu matsalar itace Add baya k'asar nan kuma wayoyinsa duk akashe"
Jinjina kai Doctor yayi ya ce" to kuwa akwai matsala, saboda dole ne Abdussamad yadawo, har yanzu sunanshi kawai take fad'a " cikin damuwa Abba ya ce"bakomai za'a San yanda za'ayi ,daga haka yayi waje..


Tsaye suke sunyi curko-curko akalla ankira number shi yayi sau ashirin amma duka abanza kwata-kwata ma bata shiga,ganin basuda mafita yasa Kawu cewa

"Zaki kashirya kaje America ko a jet ne ka kirawan Abdussamad kuma kace masa yazo yanzu nasan halin taurin kanshi"

Cikin girmamawa Aliyu ya ce
"Insha Allah Kawu zan tafi " daga haka yayi yayinda shi kuma kawu ya ce" bari naje na duba Nana " sannan sukai waje...


Tana kwance tarufe ido saidai ba barci takeba sukai sallama suka shiga ,tanajin maganar mutane ta k'ara rufe idanta kamar me bacci, Kawu daya Kula da ita yakarasa kusada ita ya ce


"Nanah ya jikin naki?"

Jin muryarshi ya data tabud'e idonta ta kamo hannunsa ta ce" Kawuna inaso naga Daddy please " ta fad'a tana zubar da hawaye

Zama yayi kusada ita ya ce

"Karki damu Nana nasa akirawo miki Daddynki kinji"

D'aga mishi kai tayi sannan ya ce

"Yawwa y'ar albarka azuba miki indomie ko?"

Girgiza kai tayi ta ce" nidai A'a bana ci"

Babu yanda yayi da ita haka ya barta har akai kiran sallah suka fita dan yin sallar akabar Jalhan a gurinta ...


America

Wajen k'arfe biyar na yamma ya isa, zaune ya taddashi yana cin abinci,sallama yayi ya amsa sannan ya zauna kusadashi,shuru yayi baiyi magana kana ganinshi kasan akwai damuwa atare dashi, murmushi Aliyu yayi ya ce

"Dude ba magana ne?koda yake nasan bazaka kula niba amma albishirinka?"

Kallonsa Abdussamad yayi sannan ya d'auke kai ya ce"sannu da zuwa ya gida?da mutanen Gidan?"

Sanin halinshi yasa Aliyu share maganar yace

"Niba wannan ba Kawu ne ya ce" nazo na kiraka ,ya ce bayasan ya k'ara magana kazo"

Murmushi yayi ya ce "Da gaske ? To kaje kace bazan zoba"
Yana gama fad'in hakan yayi gaba abinsa

Bai kai gashiga d'aki ba Aliyu ya ce

"Idan bazaka zo kiran kawu ba wannan matsalar ka ce kai dashi amma kasani Nana tana kwance a asibiti ciwon zuciyarta ya tashi"

Cak ya tsaya sannan ya juyo,Aliyu ya tako gabansa ya dafashi sannan ya ce"


Story and written by
Nanameera


Meera Love's yhu[12/26/2023, 10:19] Nanameera: *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

Naanah

Mallakar Amina I Ibrahim
(Nanameera)


PAGE 1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣


____________✍🏻Ganin yanda ta had'e rai yasa yayi dariya sannan ya ce

"Babyn Daddy lafiya?" Ya fad'a ya Jan gashin kanta.

Turo baki gaba tayi sannan ta ce

"Daddy bakai bane kake Kula su Daddy da Abba kumani bana kulasu "

Murmushi yayi ya ce

"Toh! Me sukai miki?"

Kwabe fuska tayi ta ce

"Saboda sunyi maka fad'a rannan kuma ni ban mantaba "


Jingina yayi da fuskar gadon sannan ya ce

"Toh bakyaso ayi min fad'a?"

Komawa tayi kan cinyarshi tana Jan gemunshi ta ce


"Eh mana ya za'ay adinga maka fad'a Bayan bakayi lefiba shiyasa bana sonsu kwata-kwata"

Rufe mata baki yayi ya ce

"Kul! Kar insake ji ,su Abbane bakiso?to idan bakya sonsu nima bakya sona"

Fashewa tayi da kuka ta ce

"Daddy kayi hak'uri bazan sake ba "

Ganin yanda take kukan yasa yayi dariya sannan ya ce

"ok na hakura amma karki sake"

D'aga mishi kai tayi alamar Eh. Murmushi yayi ya ce
"Good girl "

Kwantawa tayi akan kirjimshi suna tab'a hira har bacci yayi gaba da ita.


Tashinta kenan daga bacci ta duba agogon wayarta taga har kusan k'arfe sha biyu na safe,da sauri tashiga bandaki dam yin wanka da alola .Hafsa kenan Babu ruwanta da sallah sai sanda tatashi.

Hajiya Fadeela ce zaune kan kujera tana Danna waya cikeda isa ,Hafsa ta k'araso ta rungemeta sannan ta zauna gefanta ta ce

"Good morning mommy"

Shafa kanta mommy tayi ta ce

"Morning dear how was your night?"

Langwabar da kai tayi ta ce

"Fine mommy, thank you"

Murmushi hajiya tayi ta ce

"Bari akawo miki breakfast"

Thank you mommy Hafsa ta ce sannan ta hau Danna wayarta hankali kwance.

Gama cin abincin ta kenan ta Mike dan tafiya mommy ta kalleta ta ce

"Yanzu sai ina?"

Murmushi Hafsa tayi ta ce
"Wallahi mommy zani Gidan Ikram ne sai kuma na biya gurin Abdussamad"
Shuru mommy tayi ta ce
"Hafsa kina ganin zaki iya kuwa?yaran nanfa baya sonki kwata-kwata"

Murmushi tayi ta ce "
Mommy kenan wallahi ko baya sona sai ya aureni"
Tashi mommy tayi ta ce

"Toh Allah ya kyauta, nizan shiga daki na kwanta"


Ok tace sannan tayi waje.


Zaune take akan cinyarshi tana ta surutu wani ya tanka mata wani kuma yayi shuru, Doctor ne ya shigo da gudu takoma Bayan shi ta ce

"Daddyna banason allura please kace mishi kar yayimin kaji Daddy"

Murmushi Aslam yayi ya ce
"Nanah rigima! Ce miki nayi allura zan miki? Ni zuwa nayi na sallame

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment