Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bane" shuru yayi ya ce "yau kuma da Daddy kikayi fad'a?" Had'e rai tayi sannan tabashi labari kamar yanda tabawa Mama, Shuru yayi nad'an lokaci sannan ya numfasa yace "shikenan Nana kije zan dauki mataki karki damu" murmushi tayi ta ce "yawwa kawuna nagode sosai Allah yasa kazama president irin daddyna" murmushi yayi ya ce "Ameen daughter tashi kije dan kada azo ana nemanki" tashi tayi ta ce "sai anjima sannan tafita.

Sosai ransa ya b'aci da abinda ta fad'a masa tana fita ya dauki wayarsa yakira Abdussamad yana d'agawa ya ce" Abdussamad duk inda kake kazo ina nemanka"yana gama fad'in hakan ya kashe wayarsa. Sosai yayi mamaki abunda zaisa Kawu yakira irin haka,ajiyar zuciya ya Sauke ya ce "Allah yasa lafiya"...



Duk mazajen gidan suntaru sakamakon kiran da Kawun yayi musu shi kad'ai ake jira, shigowa yayi dauke da sallama abakinsa amsawa sukai sannan ya zauna cikeda mamaki.Numfasawa Kawu yayi sannan ya bud'e taro da addu'a kamar yanda ya saba ,shuru yayi nad'an lokaci sannan ya bayyana musu musabbabin yin taron, kowa cikin mamaki yake shikuwa Abdussamad fuskarsa tayi jajur saboda matukar fushi bai tab'a tunanin Nana zatayi masa haka ba, kiran sunansa da kawu yayi yasa yadawo daga duniyar tunanin daya tafi, kallonsa Kawu yayi sannan ya ce" Abdussamad bashawararka nake nemaba kuma ba yardarka nake nemaba umarnine gobe idan Allah ya kaimu za'a daura auranka da yarinyar nan y'ar gurin sadeeq Hafsa nagama magana tashi katafi" tsabar bakin ciki baisan sanda yafara hawayeba Abbane yazo gabansa ya dafashi ya ce"Abdussamad kayi hak'uri kaji dan Allah kadauki wannan amatsayin kaddararka kaji son" tashi yayi ya goge hawayen fuskarsa bai kalli kowaba yayi waje.





Story and written by
Nanameera




*Meera Love's yhu*[12/26/2023, 10:20] Nanameera: *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Naanah*


PAGE 2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣


__________✍️Yana fita bai huce ko inaba sai gidanshi, koda yashiga bai ganta parlour'n ba hakan yasa yashiga bed room nashi. Zaune yasameta tana kallo a system tad'ago kai takalleshi tace" Daddy sannu dazuwa" ko kallonta bai yiba yajuya ya fita , bedroom d'inshi yashiga yazauna kan bed gabadaya tunaninshi ya kwance ya rasa ta'ina zai fara, yarasa laifinwa yake gani saboda haka yatashi yashiga toilet dan watsa ruwa..


Itakuwa oganniyar ganin yanda ya'ki kulata yasa taji haushi tahau kuka, takusa awa tana kukan ganin har sannnan bai shigoba yasa tayi shuru sai kuma tafito parlon dan ganin yana ina , lek'a ko'ina tadingayi shiga tayi d'akinsa taganshi zaune yana karatun al-qur'ani, zama tayi gefen gado harya idar da karatun sannan takalleshi ta ce" Daddyna shine d'azu kak'i kulani ko?" Shuru yayimata sai kallonta yake ganin ya'ki magana yasa tafashe da kuka harda birgima, wata gigitacciyar tsawa yadaka mata dayasa tamik'e da sauri jikinta narawa. Kallonta yayi ya ce"Nana bakida hankali ko?bakisan menene yake miki ciwoba ko? Kodan saboda narikeki kamar y'ata shiyasa?, bandauka rashin hankalinki yakai hakaba,nasan dole akwai yarinta atare dake amma bandauka zaki iya bud'ar baki kifad'i irin abinda kika fadaba Nana you disappointed me Nana"yakarashe Maganar yana zubda hawaye. Iya rikicewa ta rikice tunda take bata tab'a ganin Daddynta nakukaba sai yau hakanne yasa hankalinta yatashi ,kuka tafara sannan ta ce "Daddyna dan Allah dan Annabi kayi hak'uri bazan sake ba kaji Daddy kadaina kuka dan Allah" tafada tana gogemasa hawayen fuskarsa, kallonta yayi sannan ya jawota jikinshi ya ce "Nana kenake tausayawa ,kezaki shiga matsala, natabbata abinda yake tunkaroki bazaki iyaba Nana never!!" Cikin shashshekar kuka ta ce "Daddyna kayi hak'uri bazan k'araba nayi maka alk'awarin zanjure koma menene amma dan Allah karkayi fushi dani " rungemeta yayi ya ce "bazanyi fushiba Nanah Saidai zanyi addu'ar Allah yasa hakan yazama al-khairi agaremu " shuru tayi tana Sauke ajiyar zuciya duk yanda Abu yakai da damunta indai zataga Daddynta to zata jure kamar yanda shima baya iya fushi da'ita kome zataimai....


Fitowarsu kenan daga masallaci Hameed ya ce "gobe akwai shagali agidannan kallonsa Aliyu yayi ya ce" kajika inawani shagali Bayan baso yakeba ?yaushe rabon dakaga Dude yana kuka tun mutuwar Baba amma yau yazubar da hawaye akan wannan maganar ni yanzuma gurinshi zani naga bai fito sallaba "murmushi Hameed yayi ya ce" nifa wallahi abunnan yayimin dad'i, menene aibun Hafsan ni nafisanta madashi akan Nanan ammashi kwata-kwata baya ganin hakan barinma da akace yarinyar tanada ciki ko maganar Mama bayaji kamar yanda yakejin tata , dariya Aliyu yayi ya ce "OK wato ku kuna bayan Amarya ko?" murmushi Hameed yayi ya ce "wallahi kam 100% ina bayan Amarya yarinya beauty ga mutunci aidole mu sota" gaba Aliyu yayi yana cewa "wallahi kam munanan zaku dawo daga rakiyarta saboda Hafsa ba y'ar mutunci bace halin uwarta tayi " dariya Hameed yayi ya ce "naji aibawai mundena son Nana bane kawai munbata hutune zuwa wasu shekaru ai Nana fine girl ce" dariya Aliyu yayi ya ce "kaji dashi sannan yayi gaba..


Yana shiga gidan kaitsaye bedroom yashiga yasameshi yana operating laptop Nana kuma na barci akan gado. Zama yayi sannan ya ce" Dude naga yau baka fitoba?" Kallonsa yayi ya ce "banajin dad'i shiyasa" murmushi Aliyu yayi ya dafashi ya ce "Dude dan Allah kayi hak'uri karka d'aga wannan maganar kayi hak'uri kayi kuma addua Allah yasa hakan yazama mafi Alkhairi" murmushi yayi ya ce "Dude kenan aiko baka fadaba dole nayi hak'uri saboda Kawu yafi karfin haka agurina amma wallahi badaban kawu baneba narantse babu wanda ya'isa yasani na aure wata Hafsa , Dude bakaina nake ji tausayin Nana nakeji Aliyu, saboda narigada nasan Nana farin sani nasan mezata jure nasan wanda bazata iyaba , kuma tunkan haka Nana batason Hafsa jininsu bai haduba to yanzu tayaya zanfara tunanin aldarci atsakaninsu I can't do it Dude" Numfasawa Aliyu yayi cikeda damuwa ya ce "sorry Dude nasani dawahala amma kayi hak'uri dan Allah itama Nana kabata hak'uri kuma ai kasan Nana batasan kai mijinta bane saboda haka bana tunanin zata bada matsala" murmushi yayi ya ce "amman yanzu dole tasani saboda idan Hafsa tasan batasan matsayintaba to zatayi ta wahalar da'itane kagako dole ne yanzu tasani" shuru Aliyu yayi sai kuma ya ce "ehh,kuma hakane yanada kyau ace tasani d'in , saika fad'a mata kuma ka lallasheta saboda nasan halin Nana da taurin kai" murmushi yayi ya ce "toh! Allah yasa tayarda" Ameen Aliyu ya ce sannan suka cigaba da hira har lokacin sallar magrib yayi zasu fito Nana tatashi saboda haka suka fito tare ta huce gurin Mama.



Tana shiga tasamu suna sallah hakan yasa itama tashiga toilet dan yin alwala tagabatar da sallar.

Bayan sun idarne ta tafi tagaishesu Mama ce kawai ta amsa itakuwa Ma'a rufeta tayi da fad'a tana cewa "amma Nana kinban mamaki bantaba dauka zaki aikata hakaba, ai nayi zaton ko namanki Abdussamad yake gutsura tsawon lokaci bazaki fad'awa kowaba, amma akan yayi abinda yake dolenki arayuwa shine harkika iya zuwa kikai k'ararsa kuma yanzu abun yadawo kanki saboda ke za'ayiwa kishiya bawaniba shashasha kawai " murmushi Mama tayi ta ce "a'a fa yarinyar nan dagaskiyarta shi bashida hankali ai yasan yarinyace k'arama amma ya iya turmusheta to mene laifinta dan takai k'ararsa?" akufule Ma'a tace"wallahi a'a wannan badaidai bane kinsan abinda ta aikata ba dai-dai bane rashin hankaline irin nata yasa ta aikata waima kinsan matsayinsa dakika aikata haka?" girgiza kai Nana tayi ta ce "a'a" kallonta Ma'a tayi ta ce "dole! to bari kiji bakina cemasa Daddynki!! Daddynki ba shid'in mijinki ne, kinsan miji ko?" d'aga mata kai tayi, murmushi Ma'a tayi ta ce "good, to mijinki ne saboda haka mata bata zuwa tafadi sirrin mijinta kome yay mata hak'uri takeyi kinji" fashewa tayi da kuka ta ce "a'a Ma'a ni Daddyna ne wallahi Daddyna ne" jawota Mama tayi ta ce "rabu da'ita daddynkine kinji" d'aga mata kai tayi dai-dai lokacin sukai sallama suka shigo. Dagudu tatafi ta rungumeshi tana kuka , rik'eta yayi suka zauna kan kujera ya ce"kedawa?" K'ara fashewa tayi da kukan batare da tabashi amsaba " tallafo hab'arta yayi ya ce "ya'isa haka daina kukan ki fad'amin kedawa?" cikeda shagwaba take cewa"koba Ma'a bace"murmushi yayi ya ce "ta ce me?" kwabe fuska tayi ta ce "tace min wai kai ba Daddyna bane mijina ne" murmushi yayi harsaida beauty point dinsa suka loma sannan ya ce "to kekinyarda?" girgiza kai tayi ta ce "kai Daddyna ne ko?" d'aga mata kai yayi sannan ya kalli su Mama suka gaisa Aliyu ma ya gaishesu sannan Mama ta ce" Abdussamad " d'ago kansa yayi ya ce "na'am Mama" cikin kwantar da hankali take cewa "kayi hak'uri kadauki hakan amatsayin jarraba kaji , dan Annabi karka tada zancen kokuma kabata ranka gobe kaji" cikeda k'arfin hali ya ce "insha Allah Mama zanyi yarda kikace Allah yasa hakan yazama al-khairi atsakaninmu " murmushi Mama tayi ta ce "yawwa Allah yayi maka Albarka Allah yadawwamar da farinciki acikin rayuwarka" sosai yaji dad'in addu'arta cikin sakin fuska ya ce"Ameen Mama nagode sosai " Aliyu ne ya kalleta ya ce" Mama shikad'ai zaki yiwa addu'ar? " dariya Abdussamad yayi ya ce "toh uban y'an kishi baza ayibad'in" harararshi yayi ya ce "dallah nibadakai nake maganataba da mama nake saboda haka rufemin baki" murmushi Mama tayi ta ce "ya'isa haka kuda bakwayin zaman minti biyar bakuyi fad'a ba dukkanku Allah yayi muku Albarka" Ameen suka amsa sannan suka tasa suka fito...



B'agaren Hafsa kuwa jitake kamar tafi kowace y'a sa'a aduniya tana hira da kawarta mommynta hajiya Fadeela tashigo d'akin ta ce"Hafsa wannan murnar taki tayi yawa kibari ad'aura auren sannan kyayi" had'e rai tayi ta ce "dan Allah mommy kiyi mini fatan Alkhairi kawai " murmushi tayi ta ce "ai dama shinake yimuku daga haka tafita sukuma suka cigaba da hirarsu..
*Next day*



Story and written by
*Nanameera*


Meera Love's yhu
[12/26/2023, 18:38] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8BB

https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️....2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣



__________✍️Kasancewar yau antashi da biki yasa duk mutanen gidan suka tashi tahuri dan yin ayyuka, zaune yake yana kallon Al-Jazeera Nana tashigo parlon tazauna akan cinyarshi tace "Daddy kazo mutafi kaji" kallonta yayi ya ce "ina zamuje Nana?" kwabe fuska tayi ta ce "gidan Mama mana bakaga nayi kwalliyaba kasan yau za'ayi biki inji Ma'a" shuru yayi yana jinjina rashin wayonta kuma yana matukar tausayinta saboda yasan halinta , ganin baice komaiba yasa tadakeshi akirji ta ce"Daddy katashi mana" kallonta yayi ya ce "babu inda zaki Nana banson rigima" fashewa tayi da kuka ta ce "dan Allah Daddy zani " zaiyi magana Aliyu yayi sallama yashigo, zama yayi kan royal cusion d'in parlon yasha shadda gezner fara k'al kamar shine angon ya ce"wai Dude sai yaushe zaka bar wannan zaman kowa sainemanka yake" tsaki yayi ya ce "aita nemana d'in ko akwai Wanda naciwa bashine ban biyaba?" murmushi Aliyu yayi ya ce "Allah yahuci zuciyar ango aikai hukumane saida rarrashi " harararshi yayi ya ce "kasan Allah ranka zai b'aci" dariya yayi ya ce "kaga angon Hafsa" zaiyi magana Nana ta ce "uncle waye angon Hafsan?" dukkaninsu saida suka kalleta dan basuyi zaton tanagane abinda suke fad'aba, kama hannunta yayi ya ce "zo mutafi kirabu dawannan bashida sense" dariya Aliyu yayi ya ce "ok harda mannamin hauka ai shikenan" batareda yabashi amsaba yayi waje abinsa..


Wajen tafiyar three minutes sukazo parking lot d'in gidan inda wasu motoci sukayi parking. Wata kyakyawar matace tafito ak'alla zatakai shekara arba'in tasha lufaya kana ganinta kasan balarabiyace, Rukayya kenan tana rayuwa ak'asar turkey ne itada mijinta wanda shima dan family d'in ne itace babba y'ay'a matan gidan , k'arasowa tayi tana murmushi suka gaisa ta ce" ango ansha kamshi Allah yasa hakane mafi Alkhairi " kallonta yayi kamar zaiyi magana saikuma yayi shuru yayi gaba, murmushi tayi ta ce "Abdussamad kenan sai zafin zuciya" dariya Aliyu yayi ya ce "ai kad'an kika gani yanzu yagama zagina saboda nayi maganar auren " girgiza kai tayi ta ce "Allah ya kyauta " Ameen Aliyu ya ce sannan suka shiga apartment d'in Mama.


Parlon cike yakeda y'ay'an gidan duk anzo sai hira suke suka shigo, gaisawa akayi sannan suka zauna kamar y'an uwansu. Fateema ce ta ce "ikon Allah yanzu Nana harkin girma haka?" murmushi Ma'a tayi ta ce "tagirma ba hankali kumaba" dariya tayi ta ce "haba Ma'a ai dukda haka tagirma kodan rabon dana ganta tun mutuwar Baba" Eh gaskiya kin dad'e Ma'a ta ce sannan takalli Nana ta ce "Nana bakiga aunties dinki ba kizo ki gaishesu " durk'usawa tayi ta ce "ina yini" amsawa sukai sannan takoma tazauna kusada daddynta.


Kusan minti ashirin Kawu yakira su awaya ya ce sufito alokacin Nana tayi bacci ajikinsa , bedroom d'in Mama yakaita ya kwantar sannan sukai waje..


Sosai akacika awajen d'aurin auren , Bayan and'aura ne photographer sukazo akadinga hotuna , Hafsa kuwa da k'awayenta fito sukai akadinga hoton dasu sai wajen k'arfe sha biyu sannan aka watse kowa ya tafi shikuma yatafi companynshi saboda kiransa da'akayi..




Zainab suke adakin Hafsan sunata hira don jitake kamar tafi kowace mace sa'a aduniya , kawarta zeeta ce ta ce "wai yanzu shikenan kinyi aure abinki kin auri Abdussamad abin kamar mafarki" wani killer smile Hafsa tayi ta ce "toh bamafarki bane dagaske ne na aureshi yanzu nazama matarsa wayyo dad'i" dariya zeeta tayi nusy tace"toh yanzu kinyarda zaki zauna da kishiya kenan? kuma kishiyar ma dakika tabbatar dayafi sonta akanki" had'e rai Hafsa tayi ta ce "haka nacemiki? ai yanda kika sanni ada yanzuma haka nake wallahi bazan zauna dakishiya ba amma kuma yanzu bazan nuna ba sai naje gidan cikin salo da dabara wallahi sai tabar gidn bari nahar abada" dariya suka tuntsura suka tafa sannan suka cigaba da hirarsu....



Misalin k'arfe biyar na yamma tatashi tayi sallah sannan tafito parlon, Mama ce sai wasu daga y'ay'an gidan takalli Mama ta ce "Mama ina Daddyna?" kallonta Mama tayi ta ce"yaje unguwa amma yakusa dawowa" shuru tayi tazama abin tausayi gabadaya jikinta yayi sanyi kamar yanda nakowace yake sanyi idan akayimata kishiya , ganin yanda tayine yasa Mama ta ce "nazuba miki abinci?" girgiza kai tayi ta ce "nak'oshi bari naje gurin Amma Nadawo" toh Mama tace sannan tayi waje, tana fita Rukayya ta ce "Allah sarki wallahi har taban tausayi " sa'adatu ce ta ce "nima haka wallahi amma dai bayau zai tafi da'ita bako?" kallonsu Mama tayi ta ce "Allahu ya alamu" ....




Tana shiga taga Amma bata parlon hakan yasa tashiga d'aki nanma taga batanan , kamshin girkin dataji yasa tashiga kitchen tasameta tana aikin abincin dare. Kallonta Amma tayi ganin tarame ta ce"Nana meyasameki? bakida lafiya? " matsowa tayi kusada Amma ta ce "lafiyata klau amma kibani abinci yunwa nakeji" tab'a jikinta tayi taji baxafi sannan ta ce "shikenan jeki parlon kizauna nazubo miki"toh tace sannan tayi waje..



Fitiwarta kenan daga kitchen bayan tagama abinda take tasamu Nana harsannan bataci abincinba , zama tayi kusada ita ta ce" Nana meyasa baki ciba?" kallonta tayi amma bata bata amsaba hakan yasa tajawo plate d'in abincin tad'ebo ta ce "hhh" babu musu tabud'e baki haka tadinga bata har takoshi sannan ta ce "yanzu bagashinan kinciba ,jeki d'aki kiyi brush kizo kiyimin hira" toh ta ce sannan tashiga dakin...




Bayan sun idarda sallar magrib lokacin bai dad'e da dawowaba suna tafiya da Aliyu share ce"wai yanzu Dude yazakayi da Nana saboda tunda kafita take nemanka " ajiyar zuciya yasauke ya ce "wallahi nima bansani ba,amma bari naje naganta tukunna" ahaka suka shiga apartment d'in Mama ....



Tana zaune tana cin abinci suka shiga, kallonta Aliyu yayi ya ce "hajiya Mama irin wannan ci haka" kallonsa tayi ta ce "zakaci ubanka ne wallahi" murmushi Abdussamad yayi ya ce "rabu dashi Mama, ina Nana?" k'arasa cin abincin bakinta tayi tadauki ruwa tasha sannan ta ce"ta gudu gun uwarta tun yamma" OK yace sannan yatashi zai fita ta ce "ina zaka?" zajenta zani ya fad'a kallonsa Mama tayi ta ce "baikamata kajeba karabu da'ita ko zuwa wani satinne saboda idan yanzu kace zaka tafi da'ita kasan za'a samu matsala" badan ransa yasoba ya ce to sannan yadawo yazauna suka cigaba da hira har lokacin sallar isha'i ya suka fita dan yin sallah daga nan kuma suka tafi da harkr gabansu ..



Wajen k'arfe tara aka kawo Hafsa gurin Mama sannan aka huce da'ita gidanta, komai nagidan ansauyashi ansa sabo saboda yayi kyau fiye dana da k'awayenta sai santi suke. Tun suna jiransa har kowa ya watse akabar ta itakad'ai sai wajen k'arfe sha d'aya sannan yashigo gidan kai tsaye d'akinsa yahuce yaje yayi wanka yagama shirin bacci sannan yashigo dakin datake , sallama yayi ta amsa sannan yashiga zaunawa yayi gefen gadon ya ce "yi hak'uri fa nabarki ke d'aya" murmushi tayi ta ce "wallahi Babu komai yaya yahuce" kallonta yayi sannan ya ce "Hafsa ina neman wata alfarma agurinki", shuru tayi ta ce" ina jinka yaya " cikin sanyi murya ya ce "Dan Allah Hafsa kizauna lafiya da Nana dukda yanzu batanan idan tadawo kirik'eta tamkar k'anwarki" murmushi tayi ta ce "karka damu da wannan ai kobakai Nana kanwatace insha Allah zan rik'eta matsayin kanwa kamar yanda kafada" murmushi yayi ya ce "nagode" daga nan kuma wasan yafara sauya salo hakan yasa nafito najawo kofar da kyau...



B'angaren Nana kuwa kasa bacci tayi haka tayi ta juye-juye har asuba tayi...



Dasafe tana had'a masu breakfast kallonta yake cikeda zargi saidai yayi alk'awarin babu wanda zaiji amma yayi mamaki sosai. Bayan sun gama breakfast ne yatashi zai fita ta ce "A'a yaya ina kuma zaka da safennan?" Kallonta yayi ya ce "zan fitane saboda zanje government house, amma karki damu zan tawo miki da kayan dad'i" murmushi tayi ta ce "toh Allah yadawomin dakai lafiya" ameen ya ce sannan yayi waje, yaso yaje yaga Nana saidai kuma yanaso yabi umarnin Mama hakan yasa yafita kawai...


Hafsa kuwa tana shiga daki takira kawarta zeeta ringing biyu tadauka ta ce"amarsu ta ango" dariya tasheke da ita sannan ta ce "fad'i ki k'ara fad'a" murmushi tayi ta ce "bani nasha" zamata gyara tace"kinsan bai ganeba daman nafad'a muku ya iya aiki Doctor farooq badaga nanba "murmushi zeeta tayi ta ce" ai yanzu nagani kam " daga haka suka cigaba da hirarsu..


Story and written by:

*Nanameera*



Meera Love's yhu[12/28/2023, 16:00] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️.....2️⃣7️⃣&2️⃣8️⃣



_______________✍🏻Sai wajan k'arfe sha d'aya tatashi kasancewar bata kwanta da huriba, fito warta kenan daga bedroom bayan tayi wanka. Amma ce zaune aparlon suna breakfasts da Abba , k'arasowa tayi ta zauna gefen Amma sannan tagaishesu , kallonta suke cikeda tausayawa saboda yanda tarame daga jiya zuwa Abba ne ya ce " besty bakida lafiyane?" kwabe fuska tayi ta ce "Abba kakaini gurin daddyna" murmushi yayi ya ce" ok karki damu zankaiki amma yanzu kifara cin abinci ko daga nan saiki rakani unguwa idan muka dawo saina kaiki wajen daddy'n " murmushi tayi ta ce"yawwa besty nagode sosai" dariya Amma tayi ta ce"wato besty'nki kika sani ko?ai shikenan " dariya tayi harsaida dunful d'in ta ya loma ta ce"haba ai kema ban manta dakeba kice second bestyna" dariya sukayi dukansu sannan suka cigaba da breakfast niko nace iyaye dad'i......






Wajejen k'arfe bakwai nayamma yadawo , sosai yake agajiye hakan yasa bai iya zuwa apartment d'in Mamaba kamar yanda yasaba kawai yahuce gida. Yana shiga yatadda Hafsa kan kujera ansha k'ananun kaya tana ganinshi tataso ta rungumeshi cikin kissa ta ce"welcome my Excellency ya gajiya nasan kagaji sosai muje kawatsa ruwa sannan kazo kaci abinci " murmushi yayi yana zareta daga jikinshi ya ce"nagode sosai amma nariga nacewa Amma zanzo naci abinci kinga baikamata naci ananba ko" sosai ranta ya b'aci amma ta danne ta ce"ok babu matsala " peck yabata agoshi sannan yashige bedroom dinsa ....






Zaune yake yanacin abinci a parlon'n Amma sunata hira kasancewar sunsaba da zama suyi hira, kallonsa Amma tayi ta ce"son!" d'ago kai yayi ya ce "na'am Amma" inason kayimin wata alfarma idan babu damuwa" murmushi yayi ya ce"Amma kenan fad'i insauraranki Allah kuma yasa zan iya" shuru tayi sai kuma tace "dan Allah Abdussamad dan Annabi kabar Nana ta zauna agurina saboda akwai abubuwa dayawa dazan koyamata idan yaso ko sati d'aya tayi saika dauketa" shuru yayi sai kuma ya ce" Amma saina ga kamar one week yayi yawa inama laifin kwana biyu haka yanzufa na kwana d'aya fa ikince tarame sosai " murmushi tayi ta ce"shikenan tayi kwana biyu". Suna cikin hirar suka shigo itada Abba tana ganinshi tatawo dagudu ta rungumeshi tana dariya, murmushi shima yayi yashafa bayanta cikin jin dad'in ganinsa ta ce"Daddyna meyasa katafi kabarni jiya? " murmushi yayi ya ce"I'm sorry dear bazan sakeba" turo baki tayi ta ce"next time idan kasake nadena kulaka" angama ya fad'a yana dariya. Abba ne ya ce" kigama murnarki bayau zaki bishiba" kallon Abba tayi sai kuma tafashe da kuka ,dariya suke mata sosai hakan yakara tunzurata tacigaba da kukan , Amma ce ta ce "rabu da Abba kinji daughter" tashi tayi takoma jikin Amma takwanta tana shashshek'ar kuka ahaka har tayi bacci. Abbane ya ce" yanzu yaza'ayi suzauna gida d'aya kana ganin zata yarda" murmushi yayi ya ce"toh nima bana ceba amma insha Allahu zata yarda " Allah yasa, shuru yayi sai kuma ya ce"yawwa dama inason nafad'a maka wata magana " hankalinshi yabada ya ce"inajinka" cikin nutsuwa ya ce"daman inason Nana takoma makaranta kafin mukoma saboda bansan zamanta haka babu karatun , to nayiwa shuguban makarantarnan magana ya ce toh shine nakeso natambayeka naji koka yarda" murmushi Abba yayi ya ce"kajika dawata magana kawai sainace bazata koma makarantaba Allah yasanya alkhairi, wayaga Nana a jami'a" dariya sukayi duka Amma ta ce"tasamu tayi hankali " daga haka yatashi ya ce" Abba zantafi saida safe allah yatsareku da rigima " Ameen sukace sannan yayi waje.....






Kwance suke akan gado Ayrah nakan kirjinshi ta ce"uncle " d'ago kansa Hameed yayi ya ce"na'am " nikam ina tausayin Nana saboda Hafsa batada hali ko kad'an nasan wahala zatasha dan ba lallai bane uncle A yaganeba saboda makirace" shuru yayi sai kuma ya ce"ni kuma gani nake haka shine mafita " kwabe fuska tayi ta ce "kajima uncle yaza'ayi kishiya tazama mafita?" murmushi yayi ya ce"saboda yanzu ne zatayi wayo takuma San kanta , ahakan dakike ganinta tanada zafin kishi bataso kowa yarab'eshi kinga kuwa dole zatayi fad'a da Hafsa kuma tunda yafison Nana hasalima bayanson Hafsa to duk abinda Nana takeso shi za'ayi" murmushi tayi ta ce"Allah yasa " Ameen ya ce sannan sukayi bacci abinsu.....



Misalin k'arfe biyu da rabi tafarka kasancewar fitila akashe take yasa ta ce " Daddyna!! Daddyna!! " shurun dazaji yasa tafasa k'ara wanda saida su Abba suka jiyota suka fito dan sund'auka wani abunne yasameta , suna shigowa dakin suka kunna fitala sukayi kanta saboda yanda take kuka kamar ance daddy yamutu, cikin tashin hankali suka hada baki suka lafiya meyasameki? Fashewa takumayi da kuka su duk sun rikice Abba yakara cewa"Nana lafiya " kallonsa tayi ta ce"Abba Daddyna Ku kiramin daddyna nibazan kwana ananba"



Comments, share pi sabililah.



Story and written by:

*Nanameera*



Meera Love's yhu
[12/28/2023, 19:25] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️......2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣




______________✍️Cikin lallashi Abba yace,"gurin daddy zaki?" d'aga mishi kai tayi ya ce" shikenan kiyi shuru kidaina kuka kibari dasafe nayimiki alkawarin zan kaiki daka ina" fashewa tak'arayi da kuka ta ce"noooooo ni yanzu nakeso" rasa yanda zasuyi da'ita sukayi , Amma takalleta ta ce"Nana bakince idan nace kiyi Abu zakiyiba?" d'aga mata kai tayi ta

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment