Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai dama ba dole akayi mata ta yarda ba " kama hannunta ta yi sukai gaba kasancewar su biyun sunfi shiri....



Zaune ta ke ta na karatu a bedroom ɗinta , chan kuma ta tafi tunanin yau kwata-kwata ba taga daddynta ba , miƙewa ta yi ta fito parlon dan nemanshi. Zaune ta sameshi kan kujera Hafsa kuma na gefenshi sai hira suke abin su, lokaci ɗaya ranta ya ɓaci madadin ta yi masa magana sai kawai ta yi juyawarta ta koma ɗakinta ta hau sana'ar kukanta .....



Tun ta na sarai da zuwansa har ta kwanta ta yi bacci ba tareda ta sa kashi a idonta ba .....


Shi kuwa kwata-kwata ya manta da wani batun Nana sai barcinsa ya ke abinsa........




Washe gari ma haka ce ta kasance dan har ta gama shirin makaranta ba taga ya fito , bayan ta fito ta tadda Hafsa ta na jera kayan breakfast akan dinning kallonta ta yi ta ce

"A'a ƴar gidan daddy makarantar za'a ta fi ?"


Kallonta kawai Nana ta yi amma bata bata amsa ba dai-dai nan ya ƙaraso parlour'n sai a sannan ta gane amfanin yi mata magana dan ta haɗa ta dashi. Bayan ya sakko ta sunkuya har ƙasa ta gaishesa ga mamakinta sai ta ga bai amsa ba saima tafiya da ya yi ya zauna , cikeda damuwa da kuma rashin sabo ta ƙarasa kusada shi ta ce


"Daddy na gaisheka baka amsa ba, kuma tun jiya baka zo wajena ba " ta ƙarashe maganar ta na zubda kwalla .



Kallonta ya yi ya ce " tashi akaina " maimakon ta tashi sai ta ƙara narkewa ajikinsa cikin shagwaba ta ce

"daddy me nai maka ?, wallahi ina karatu a school sosai bana wasa kuma...... Wata gigitacciyar tsawa daya daka mata ya sa ta yi saurin ta shi daga jikinsa jikinta na rawa .




Kallonta ya yi ya ce


" ok sa'ar wasanki ce itako?, har zata kulaki amma kiyi mata banza ko? , koma arziƙin gaisheta babu ko ?, amma kinzo kina yimin maganganun banza get out of my side!!! " .

Da gudu ta yi waje ta na kuka kamar ranta zai fita , kai tsaye apartment ɗin Amma ta shige.



Zaune ta ke ta na breakfast kasancewar Abba ya fita tun safe yasa sai ita kaɗai , tana shiga ta faɗa jikinta ta na cigaba da kukanta , kallonta Amma ta ke ba tareda ta ce mata komai ba saboda sanin halinta na ƙin rarraso, kusan ten minutes ta na kukan sannan ta fara sauke ajiyar zuciya. Saida ta ga ta yi shuru duka sannan ta ce


"Nana ke dawa?, me akai miki?" tashi ta yi ta goge idonta ta ce "babu komai " babu komai kike kuka? Amma ta sake tambayarta, shuru ta yi mata saboda ta yi alƙawarin bazata sake faɗar abinda daddynta ya yi mataba koda kuwa zai kasheta, ganin ta ƙi magana ya sa Amma ta ce

"Tunda baza kiyi maganaba zo kici ki ci abinci ki tafi " tashi ta yi ta ce

"Naƙoshi sannan ta yi waje " kallo Amma ta bita dashi har ta fita sannan ta ce" Allah ya shiryeki " .........




Tunda taje makaranta ba tada sukuni har aka tashi babu yanda ƙawayenta basuyi da ita ba akan me akai mata amma bata basu amsa ba......



Bayan ta dawo gida ta shiga bedroom ɗinta ta yi zamanta bata buɗeba , Hafsa ce tazo ƙofar bedroom ɗin ta kwankwasa , cikin nemam bala'i ta ke cewa " Nana ki fito mana daddynki fa ya kusa dawowa , sai kuma ta tuntsire da dariya ta ce " da an magana daddyna ! daddyna , to yau ina daddyn naki? abinda ya faru ɗazu dake kaɗan kika gani a cikin abubuwan dana tanadar miki, sai kin gwammace kiɗa da karatu " cikin sanyin murya ta ce


"Babu abinda kika isa ki yi min sai wanda Allah ya ƙaddaromin , saboda haka ga me fili ga mai doki , nasan baki isa ki yi ajalina ba sai idan Allah ne ya ɗoran min , banza mahaukaciya, jaka kawai " .


Fashewa ta yi da kuka ta ce " dear kaji ni Nana ke ce wa mahaukaciya, jaka saboda nazo na ce mata tazo ta ci abinci " ta ƙarashe maganar ta na sake rushewa da kuka , Abdussamad da shigowarsa kenan kuma baiji komai a maganar ba sai mahaukaciya, jakar da ta ce , afusace ya ƙaraso gaban kofar cikin kakkausar murya ya ce

"Nana buɗe kofarnan " jin muryarshi ya sa ta ji hankalinta ya kwanta hakan yasa ta buɗe kofar ta na kallonshi ta ce "dadd..... Bata ƙarasa faɗaba ya wanketa da mari jikike tass, tsabar kiɗimewa kasa kukan ta yi sai kallo da ido wannan shine karo na farko da ya taɓa dora hannu akanta da niyyar duka, ita kuwa Hafsa sai murmushin mugunta ta ke ta na ganin haƙarta ya cimma ruwa.


Tashi ta yi zata shiga ɗaki ya daka mata tsawa ya ce

" ɗazu kinyi ma rabu da ke shine yanzu ma kika sake ko ? saboda ke arayuwarki bakyajin magana , to zanyi maganin ki bata haƙuri "


Muryarta na rawa ta ce

" kiyi haƙuri bazan sakeba " murmushi Hafsa ta yi ta ce " babu komai ya huce Allah ya shirye ki " kallonta ya yi ya ce


"Ohya kiyi kneel down anan gurin , ki ɗaga hannu sama ki rufe ido , idan na fito na tarar bakiyi ba,to zakiga abinda zan yi miki " yana gama faɗin haka ya yi gaba Hafsa na biye dashi......



Tun tana sa ran zai fito ya ce ta tafi har ta daina , duk abun Nana amma tana matuƙar yi masa biyayya ko sau ɗaya ba tayi yunkurin tashi ba ahaka har lokacin sallar asuba ya yi ya fito dan tafiya masallaci ya ganta agurin har ya huce sai kuma ya dawo ya ce , " kee , anan gurin kika kwanta ?" shuru ta yi ba ta ce komai ba ya ce " tashi ki huce ki tafi ɗaki " sannan ya yi waje sai asannan ta miƙe don tafiya ɗaki , amma da kyar ta kai tana zuwa ta faɗa kan gado ta na kuka , ko amafarki ba ta taɓa tunanin akwai rananr da daddynta zai mata haka ba amma gashi yau tana gani da idanunta , tana wannan saƙe-saƙen har bacci ɓarawo ya saceta ......




Comments , like nd share.




Story and written by:

*Nanameera*


Meera Love's yhu🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[1/3, 22:22] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B

🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️.......3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣




____________✍🏻Sai kusan ƙarfe goma sannan ta farka , da ƙyar ta iya ta shi ta shiga banɗaki dan yin alwala , bayan ta yi sallah ta na zaune ta kasa shiryawa ta tafi makaranta, ta na ta zaune ta ji an shigo ɗakin , ɗaga ganta ta yi ta ganshi tsaye akan ta ya na kallonta, ƙarasowa ya yi ya zauna gefenta still ya na kallonta ya ce

"Nana zo nan "

tashi ta yi ta zo kusadashi ta zauna gefenshi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Jikinta ya taɓa don jin temperature jikinta ya ce


" Nana kinga rashin jin magana ko?, kwata-kwata bakyajin magana yanzu mene ne yake damunki?" cikin sanyin murya ta ce

" Daddy kayi haƙuri bazan sakeba dan Allah " ta ƙarashe maganar ta na hawaye.


Cikin kulawa ya ce " ok naji yanzu me zaki ci ?"

cikin kuka ta ce " Daddy dan Allah karka ƙara tafiya ka barni kaji "


Rungumeta ya yi ya ce " shikenan ya huce , kema ki dinga jin magana kinji Mamana " ɗaga mishi kai ta yi ta na kwanciya a jikinsa ...


Shiryawa ta yi ya na kallonta ya ce " zaki iya tafiyar Nana?"

Kwaɓe fuska ta yi ta ce " daddyna ƙafata ya na ciwo sosai " .

" sannu idan mun fita sai na siya maki magana kinji " ɗaga masa kai ta yi sannan ya kama hannunta suka fito..



Suna fitowa suka ga Hafsa ta na zaune ta hakimce ta na taunar cingom, kallansu ta ke da mamaki don bata taɓa tunanin hakan ba , murmushin yaƙe ta yi ta ce


" dear fita zakuyi ?"

"Eh fita zamuyi, zan kaita ta ci abinci sannan na karɓa mata magani "


" ohk sai kun dawo Allah ya tsare "

Ameen ya ce sannan su kai waje........




Suna fita ta kira nusy ta na ɗagawa ta ce " nusy nifa ban gane ba , kamar aiki ya yi amma kuma kinga kwana biyu ya wargatse " cikin ƙufula nusy ta ce " ke wallahi kin fiye abu , banda haka ai malamin ya faɗa miki ya nada addini saboda ko zaiyi amma zai iya wargatsewa wani lokacin , amma karki damu yanzu zanje wajensa nima zai mun wani aiki " ohk ta ce sannan sukai sallama sai a sannan taji sanyi aranta, ni kuwa na ce Allah ya shirya...........



Sai kusan magrib sannan suka dawo ya huce masallaci ita kuma ta yi gida , bayan sun idar, ta na ta jiransa amma shuru ka keji tun tana jiransa har bacci ya ɗauketa.........



Haka rayuwa ta cigaba da ta tafiya Nana ta zama kamar ba ita ba kwata-kwata ba tada sakewa banda makaranta babu inda ta ke zuwa ko gurin su Mama bata zuwa bare gurin Amma , sai ta kwana uku bata haɗu da Daddynta ba idan sun haɗu kuwa sai dai faɗa da zagi da kuma sakata ayyukan da suka fi ƙarfinta , ta yi baƙi kamar ba Nana ƴar gayun nan ba kuma babu wanda suka sani dan bata faɗawa kowa ba. Yau ma kamar kullum ta shirya dan tafiya makaranta , tana fitowa ta tarar da DAddynta zaune suna hira da Hafsa ta yi ƙiba abinta zuwa ta yi ta tsugunna ta ce


" Daddy zan tafi "

Baiko kalleta ba sai ma kallon Hafsa da ya yi ya ce " as i said.....


Haka ta tayi kallonsa har ta gaji ta tashi ta tafi....


kamar kullum suna zaune bayan sun fito daga lectures Hameeda ta ce

" Nana kenan ni wallahi idan ni ce saina san duk yanda nayi na rabasu wallahi , amma ke kin zauna "


Kallonta Nana ta yi ta ce


" toh me zanyi Hameeda?, so kike na yiwa daddy rashin kunya ?, bazan iyaba daddy yafi ƙarfin haka agurina wallahi ko kasheni zaiyi bazan taɓa faɗawa wani ba "


Murmushi Hameeda ta yi ta ce " amma ni inada wata shawara guda ɗaya idan zaki bi " inajinki , " shawarata itace , ina jawad ?"

Kallonta Nana ta yi ta ce " wane Jawad ɗin ?"


Wannan me son naki ɗan gidan minister " tsaki Nana ta yi ta ce "toh ni ina ruwana dashi ?" murmushi Hameeda ta yi ta ce

"Ke kuwa kike da ruwa dashi saboda shi ne kaɗai solution ɗinki " da mamaki Nana ta ce " solution kuma ?, ta yaya jawad zai zama solution Hameeda ?"


Dariya ta yi ta ce " ta hanyar kawoshi gidanku kuma ki tabbata Daddynki ya ganshi , ke ce masa shi kikeso ki aura " afusace ta ɗago kanta ta ce " what ?"



Comments, share nd like.




Story and written by :

*Nanameera*




Meera Loves yhu 🥰🥰🥰🥰🥰🥰

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment