Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce"ok idan dagaske kike kuma kinasona to kiyi bacci dasafe zancewa Daddynki yazo yad'aukeki " d'aga mata kai kawai tayi sannan takoma takwanta kusan seven minutes sannan sukaji saukar numfashinta alamun tayi bacci, Abba ne ya ce"anya kuwa zata iya yin kwana biyunnan?" Insha Allah Amma ta ce sannan suka tashi suka fito.......




Da sassafe tatashi tashiga kitchen dan d'ora abinda za'ayi breakfast dashi , kusan awa biyu sannan takammala tajera a dinning table tashiga danyin wanka , zaune tasameshi yana shafa mai kallonsa tayi ta ce"good morning my love" murmushi yayi ya ce"morning dear kintashi lafiya? cikin rangwad'a tak'araso kusadashi takarb'i man hannunshi sannan ta ce" lafiya lao let me help you " daga haka tacigaba da shafamasa man . Bayan tagama tabud'e wardrobe tadauko mishi kaya karb'a yayi ya ce"thank you" murmushi tayi ta ce" it's my pleasure " sannan tashiga wanka..



Bayan sungama breakfast ta kalleshi ta ce" dear dan Allah idan babu damuwa inaso zanaje gidan zeeta anjima" kallonta yayi ya ce"Allah yatsare" Ameen ta ce sannan tafara kwashe kayan dasukaci abincin shikuma yayi waje....




Kai tsaye apartment d'in Mama yanufa yana zuwa yayi sallama yashiga , amsa masa sukayi suna zaune suna tab'a hirarsu. Zama yayi yagaishesu suka amsa , Ma'a tayi murmushi ta ce"Ango ansha kamshi saboda amaryarce yasa jiya bakazoba?" Kwabe fuska yayi ya ce"kai Ma'a wani irin saboda Amarya wallahi fita nayi kuma bandawo da huriba shiyasa " murmushi tayi ta ce"ai nayi zaton saboda amarcinne kak'i zuwa" zaiyi magana wayarsa tafara ringing hakan yasa yayi shuru ya d'aga wayar , gaisawa sukai sannan ya ce "ohk ganinan Abba" daga haka yakashe wayar. Kallonsa Ma'a tayi ta ce" lafiya?" murmushi yayi ya ce" wallahi takwarar Mamace take rigima" sai alokacin Mama ta ce "ba'agurinka takwana ba?" tashi yayi sannan ya ce"Amma ce ta ce nabarta tayi two days a can kumawai yanzu sai kuka take " murmushi Mama tayi ta ce"idan kadaukota kazo da'ita zanbata wani Abu" murmushi yayi ya ce" to kawo akaimata" hade rai tayi ta ce"baza'a bayarba d'in " dariya yayi sannan yayi waje.....




Da sallama yashiga parlon ya tadda ita zaune kusada Abba tana game awaya sanye take da wata dogowar riga ta atampa tayi kyau sosai, tana ganinshi tahad'e rai ta d'auke kai, murmushi yayi ya zauna suka gaisa sannan ya ce"Abba gani" kallonta Abba yayi ya ce"besty ga daddy'n " juyarda kanta tayi batareda takalleshiba , murmushi sukayi dukkansu Amma tataso tazo tadafata ta ce"Nana daddy'n kifa yazo" fashewa tayi da kuka ta ce nibabu ruwana dashi nadaina kulashi" murmushi Amma tayi ta ce "daddy'n naki kika daina kulawa?" d'aga mata kai tayi ta ce" nibana kulashi kucemasa yatafi karya sake zuwa" tashi yayi ya ce" toh Amma natafi saboda idan anjima zantafi abuja gwara naje nashirya " yana gama fad'a yajuya zai fita, ganin d'aga tafiya zaiyi yasa tatashi tagudu taje ta cukyuikuyemasa riga tana kuka. Kallonta yayi ya ce" menene?" Fashewa tayi da kuka tana dukanshi akirji , d'agata yayi ya d'orata akan kafadarshi yace"shikenan ya'isa stop crying " a hankali tafara rage kukan nata har tayi shuru, kallonsu Abba yayi ya ce" bari muje saimundawo" ada lafiya sukace suna dariya.......




Suna fitowa yasaka amotar driver da guards sukazo ya d'aga musu hannu sannan ya karb'i mukulli yayi waje....



Zaune suke suna hira zeeta ta kalli Hafsa tace "wai dagaske kike bai ganeba dukda yakasance medical doctor?" murmushin mugunta tayi tace"zan miki karyane? ai daya gane natabba saiya yimun magana amma ko uffan bai ceba akafada miki nid'in tawasa ce?" Dariya suka sheka sannan zeeta ta ce"wallahi Hafsa bakida imani amma yanxu tunda kinyi aure saiki saurarako?" wani mugun kallo tayi mata ta ce"ai yanzuma nafara wallahi " dariya tayi suka tafa ta ce"shiyasa nake sonki over " daganan suka cigaba da hirarsu ta watsewa.......





Sai kusan magrib suka dawo sosai sukasha yawo dukdan hankalinta yakwanta , suna shigowa ya ce" muje namaida ke wajen Amma " hade rai tayi ta ce" Allah bazaniba kuma ko kakaini saina gudo" babu yanda baiyi da'ita ba amma k'ememe tak'i haka ya hak'ura suka nufi apartment d'insu da'ita....



Suna shiga Hafsa na zaune sai taunar cingom ake ansha wasu English wears masu kyau ko ina najikinta ad'ame yake , suna shiga ta tawo dagudu ta rungumeshi ta ce"welcome back " kallonta Nana take kamar idanunta zasu fad'o sai kuma takalli Daddynta ta ce"daddy metake anan kuma wayasa ta rungumeka?" kallonta yake amma ya gagara bata amsa ganin yayi shuru yasa ta fashe da kuka ta kalleta ta ce"kizo kifita agidanmu !! Kizo kifita" jawota yayi ya ce"Nana kitsaya kiji " tureshi tayi ta ce "wallahi saita fita bazata kwana agidannanba" babu yanda baimata ba amma tak'i hakan yasa ya daka mata tsawa ya ce" bazata fitaba d'in, idan baki saniba to itadin matata ce kekuma auntynki ce shashasha kawai " kallonsu sabililah


dayansu ta nunata dayatsa amma saidai kafin tayi magana tatafi luuu tafad'i ....


K'arasawa yayi kusada ita yana jijjigata yana cewa"Nana!! Nana!!kitashi please! kitashi zanyi Mike bayani" amma inaaa ko numfashi batayi, cikin tashin hankali ya d'auketa yayi waje da'ita, yana fitowa yahadu da Aliyu dazaizo wajensa ganin Nana a hannunsa yasa ya tambayeshi ya ce "Dude lafiya?" kallonsa yayi ya ce "






Comments, share pi sabililah


Story and written by:
*Nanameera*





Meera Love's yhu🥰🥰🥰🥰🥰[12/29/2023, 21:51] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B

🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️.......3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣




____________✍🏻Kallonsa ya yi ya ce " Dude please kiramib Doctor ka ce masa zan kawo Nana." "ok. ya ce sannan ya kira Doctor'n ya faɗa masa ...



Bayan an samata drip da allurai ta samu tayi bacci, zama ya yi agefen gadon Aliyu ya zo ya dafashi ya ce" Dude faɗamin me ne ne yafaru ?" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bashi labarin duk abinda ya faru, shuru ya yi sai kuma ya ce" toh yanzu me ne abunyi?" cikin sanyin murya ya ce" nima ban sani ba gaba ɗaya kaina ya kulle" zama ya yi sannan ya ce" dole a samo mafita." shuru sukai na wani lokaci sai kuma Aliyu ya ce

"yanzu abin da za kai idan ta tashi ka zaunar da ita ka bata haƙuri nasan zata haƙura tunda batasan ita matarka bace"

kallonsa yayi ya ce

"Waya faɗa maka? rannan agabana Ma'a ta faɗa mata kuma taje wajen mahaifiyarta ai kasan dolene ta faɗa mata"

Toh yanzu me nene mafita?"

Mafita ɗaya idan ta tashi nabata haƙuri sai kuma nasata a makaranta hakan zai rage mata raɗaɗi tunda tun safe sai yamma zata dawo kuma agajiye kaga da taci abinci sai bacci"

murmushi Aliyu ya yi ya ce

"Kuma kayi dabara Allah ya sa ta yarda "

Ameen ya ce .....




Bayan fitar sa da Nana ta keta zuba ido amma shuru kakeji har wajen sha biyu hakan yasa ta tafi ta kwanta rai ɓace ......





Sai wajen ƙarfe sha biyu sa rabi ta farka ta hau kalle-kalle , dai-dai lokacin ya fito daga wanka. Kallonsa ta yi sai kuma ta ɗauke kai murmushi ya yi ya ƙaraso wajen ta ya zauna gefen gadon, kallonsa ta yi ta ce

"Daddy dagaske ka auri aunty Hafsa?"

Jawota ya yi jikinshi ya ce

"Dagaskene Nana kiɗauka wannan itace ƙaddararmu, amma duk inda za'a kisani ki nanan amatsayinki na favourite ɗina "


Fashewa ta yi da kuka kamar ranta zai fita , ƙara janta ya yi jikinsa ya rungume sosai ya ji zafin zazzabi ajikinta cikin rauni ta ke ce wa


"Daddy baka sona wallahi baka sona meyesa daddy? meyesa kafaɗamin?" ta ƙareshe maganar tana sakin wani sabon kukan ƙara shigar da'ita jikinsa yayi jikinta nashafar fresh skin ɗinsa.


Cikin lallashi ya ce "Nana dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri kinji nasan zaki iya Nana kiyiwa daddynki wannan alƙawarin "

cikin shashsheƙar kuka ta ce"daddy wallahi banasan aunty Hafsa kaji?"


Shafa kanta ya yi ya ce" ki yi haƙuri kijure kodan saboda Ni please Nana "

Shuru tayi masa ahaka har bacci ya ɗauketa , sai bayan da tayi bacci ne ya sunkuya daidai fuskanta ya ce

"Ki yi hakuri Nana badasan raina haka ya faru kawai babu yanda na iya haka ya faru kiyi haƙuri babyn daddynta"


Cikin bacci ta ce

"Daddyna insonka karka tafi ka barni please"..


murmushi ya yi ya ce" muna nan tare har abada insha Allah"


Story and writeen by

*Nanameera*



Meera Love's yhu
[1/1, 15:03] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


🅿️......3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣





___________✍🏻 Washe gari sai kusan ƙarfe takwas ta tashi daga bacci bayan ta yi wanka ta na zaune ta na breakfast shi kuma ya na operating laptop ta ƙalleshi ta ce

"Daddy kai baza kayi breakfast bane??"

murmushi ya yi ya ce" zan yi amma ke ki gama sannan"

kwabe fuska ta yi ta ce
"A'a wallahi kazo muyi tare"

babu yanda ya iya haka ya taso ya zauna ta kalleshi ta na murmushi ta ce

" yawwa Daddy ɗan albarka"..


Suna cikin breakfast ɗin Hafsa ta yi sallama ta shigo , amsawa ya yi ta na murmushi ta ƙaraso lokaci ɗaya Nana ta ɗauke kai , zama ta yi sannan su ka gaisa , murmushi ɗauke a fuskarta ta ce

"Nana ya jikin naki??"


kallonta Nana ta yi amma babu amsa, Abdussamad ne ya kalleta ya ce " Nana bakiji aunty na miki magana ba??"


turo baki ta yi ta ce " toh ni ina ruwana da'ita da zata kulani"



Kallonta kawai ya ke tunda ta fara maganar cikin lallashi ya ce "Nana ba jiya mungama wannan maganar ba???"


Fashewa ta yi da kuka ta ce "toh ina ruwanta dani kuma banace na haƙura ba to ka ce mata ta yi tafiyarta"


murmushi Hafsa ta yi ta ce "Allah sarki Nana bakyaso nazo wajenki??"
ɗaga mata kai ta yi , miƙewa ta yi ta ce "ok babu matsala Allah ya ƙara sauki , dear bari naje gurin Mommy " ok ya ce sannan ta fita .....




Tunda ta shiga gidan bata ce da mommy komai ba sai huci ta ke , kallonta hajiya fadeela ta yi ta ce


"Wai ke dawa kike wannan hucin??"

kallon mommy ta yi ta ce " wallahi mommy na rantse saina raba shi da yarinyar nan " da mamaki mommy ta ce "wace yarinya kuma" Nana mana ta faɗa. Murmushi hajiya ta yi ta ce

"Hafsa bana faɗa miki ba saina na ce miki ki haƙura da aurensa amma kika ƙi , yanzu gashinan kina fuskantar wulaƙanci , saboda baya sonki amma baki jiniba kinbi zigar ƙawaye "

tashi ta yi ta ce "haba Mommy idan bazaki rarrasheni ba bai kamata ki faɗamin haka ba inasonshi kuma wallahi bazan rabu da shiba "

kallonta mommy ta yi "ni kuma babu ni aciki duk abinda kika jawa kan ki babu ruwana" tana gama faɗin hakan ta shige ɗaki ta barta. Murmushi ta yi ta ce " zakuwa aga abinda zanyi" sannan ta yi waje ..



Tana fita ta shiga mota ta yi waje.....


Bayan sallar isha'i suna zaune a asibitin suna hira Ayrah da Hamed suka shigo , zama sukai aka gaisa Hameed ya ce

"Nana ya jikin??"

murmushi ta yi ta ce " uncle naji sauƙi"

masha Allah ya ce sannan ya kalli Abdussamad ya ce " naje nayiwa Abdul magana ya ce "ko zuwa gobe ta fara zuwa "

murmushi ya yi ya ce "ok babu matsala bari sai anjima na aika asiyo kayan karatu" kallonsa Nana ta yi ta ce

"Daddyna yaushe zan fara zuwa makarantar ??"

hancinta ya ja ya ce " idan an sallameki yau to gobe "

Ihuu ta fasa ta rungumeshi ta na dariya suma duk sai dariya sukai mata.....


Next Day.....


Da hur-hur ta tashi daga bacci saboda zumuɗin zata fara zuwa makaranta bayan ta sakko ƙasa ta tadda Daddyn nata yana vidoe call da wasu business partner ɗinshi , zama ta yi har saida suka gama sannan ta kalleshi ta ce

"Daddy na gama shiryawa" murmushi ya yi ya ce "Nana bazakiyi breakfast ba??" kallonsa ta yi ta ce "Ni na ƙoshi kawai mutafi " noo sai kinyi breakfast sannan zamu tafi " kwabe fuska t yi ta ce " Dan Allah daddy mu tafi wallahi na ƙoshi" murmushi ya yi ya ce

"Ok mu tafi " dai-dai nan Hafsa ta fito rabonta da su tun jiya a asibiti , kallonsu ta yi ta yi murmushi ta ce " good morning" murmushin ya mayar mata ya ce " kintashi lafiya?" lafiya lao ta ce sannan ta ce " ina zakuje ?" kallonta ya yi ya ce "Nana zan kai makaranta" murmushi ta yi ta ce " masha Allah sai kun dawo Allah ya tsare" Ameen ya ce sannan ya yi waje.....

Kai tsaye apartment ɗin Mama ya huce sabon tun da ya tsaya da Hafsa Nana ta yi gaba , yana shiga ya tarar sai hira suke dasu Ma'a da Abba. Gaisawa sukai Ma'a ta ce

"Oh su Nana za'a shiga jami'a sai kidaina kukan banza ai" kwabe fuska ta yi ta ce " nidai ba kulaki zanyiba saboda yau makaranta zani yanzu na zama babba " dariya sukayi duka mama ta ce

"Amma meyasa baka nema mata admission a gidan nan ba??" kallonta ya yi ya ce

"Saboda ina so tasaba da mutane idan ta zauna agidannan bazata saba da kowa ba saboda basuda yawa amma idan tayi university awaje zata saba da mutane da yawa kafin mukoma saboda banjin zamu ƙara two months anan" cikeda gamsuwa Mama ta ce " kuma hakane to Allah ya bada sa'a " tashi Abba ya yi ya ce " wace makarantar ce?"

"Maryam Abacha " ya amsa masa , kallon Nana ya yi ya ce " toh Allah ya bada sa'a akula banda wasa sai kin dawo " dariya ta yi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce

"Toh Abba idan nadawo zan baka labari komai kaji " murmushi ya yi ya ce "toh sai kindawo sannan ya yi waje.....

At school...

Suna zuwa aka karɓesu hannu bibbiyu saboda sanin wayeshi , bayan angama komai aka kaita class shi kuma yadawo inda ya bar wasu guards dan tsaronta ......




Hafsa ce zaune a parlour'n sai ƙawayenta da suke sauraronta nusy ce ta ce

"Lallai ma wato har wannan yarinyar ce zata miki rashin kunya baki faffasa mata baki ba ??" leema ce ta tuntsire da dariya ta ce " wallahi kam ni idan ni ce ai wallahi saina cire mata haƙora tab ai Hafsa kinban mamaki " tsaki Hafsa ta yi ta ce


"Wai ku ni banga amfanin kiranku ba wallahi , muzauna musami solution amma sai wasu maganganu kuke " murmushi zeeta ta yi ta ce " come down besty ai kinsan bazamu barki ba " gyara zama nusy ta yi ta ce " ni aganina idan ya fita kikama ta kiyi mata duka kafin ya dawo " kallonta Hafsa ta yi ta ce " amma dai bakida hankali ko? yama za ayi na daketa so kike ya sakeni ?" tsaki zeeta ta yi ta ce " rabu da'ita banza kawai ana maganar mafita ta na kawo shirme " leema ce ta ce " nidai aganina hanya ɗaya ce shine ki mallakeshi , saboda idan baki mallakeshi ba to duk abinda zakiyi sai yaga laifinki , amma idan kin mallakeshi to cikin sauƙi zaki rabashi da yarinyar " shuru sukai dukkansu sai kuma Hafsa ta ce " leema nifa branson wannan tsaface-tsafacen wallahi inajin tsoro saboda yanada ruƙo da addini " dariya zeeta ta yi ta ce " nima da haka nake tunani " a babu yanda zatayi ta ƙarbi shawarar su suka tashi akan gobe za'a je gurin malamin.....




Sai kusan magrib ta dawo , driver na sauketa ta tafi apartment ɗin Amma , tana zuwa ta faɗa jikin Amma ta na dariya. Murmushi Amma ta yi ta ce

"ƴar makaranta , ya school ɗin ?". dariya ta yi ta ce " Amma nagaji bari nayi wanka saina baki labari kafin Daddy na ya dawo " ok Amma ta ce kana tashiga ɗaki .....


Har kusan takwas na dare tana apartment ɗin Amma tana bata labari , ganin dare ya fara ya sa Amma ta ce " Nana kizo kitafi gida kar dare ya yi " toh ta ce sannan ta tashi ta ɗebi kayanta tayi mata saida safe ta yi waje....

Tana fitowa ta haɗu da Daddynta ya fito daga mota da gudu ta tafi ta rungumeshi ta na dariya , shima dariyar ya ke ya ɗagata sama , sauketa ya yi ya ce " babyn daddy ya school ɗin ?" fari ta yi da ido ta ce " daddy muje ciki zan baka labari sosai " murmushi ya yi ya ce "Ok muje yau zansha labari " dariya ta yi sannan suka jera suka nufi gida .....



Bayan sunyi wanka suna zaune suna hira tana shan chocolate ya kallleta ya ce " toh bani labarin school ɗin taku" murmushi ta yi ta ce " ai kuwa makarantar ta yi kyau sosai, kasan me Daddy ?" ɗaga mata kai ya yi ya ce " A'a " murmushi ta yi ta ce " nayi ƙawaye gudu biyar " waro ido ya yi ya ce " duk ayau ɗin ?"" ɗaga mishi kai ta yi , kallonta ya yi ya ce " toh zanfaɗa miki bakinyi ƙawayeba banda wasa Nana , banda rashin karatu kinji" dariya ta yi ta ce " insha Allah" rungumeta ya yi ya ce " Allah ya yi albarka" Ameen ta ce suka cigaba da hira ........


Next Day .....


Tunda safe ta huce makaranta alokacin daddynta ya na bacci , bayan ya shirya suna zaune da Hafsa ta ce masa " yallaɓai inason zan fita" kasancewar bai iya hana mace fitaba ya ce " Ok Allah ya tsare nima yanzu zani Abuja " murmushi ta yi ta ce "ameen nagode ".....



Bayan sun fito daga lectures suna zaune da ƙawayenta suna hira Azrah ce ta ce " wai Nana yaushe zaku koma American?" kallonta ta yi ta ce" nima bansani ba amma naji daddy ya ce bazamu huce two months ba " tab ɗijan amma shine aka sakaki amakaranta ?" to kar asakani kike nufi ko kuwa yaya?" murmushi ta yi ta ce " bahaka nake nufiba, amma mr. president ne daddynki ? wallahi inasonsa " da mamaki Nana ta kalleta ta ce " wane kike so ɗin ?" murmushi ta yi ta ce " daddynki mana ko akwai matsala ? nafi shekara biyu inason na haɗu dashi saboda shi nacewa daddyna sai ya kaini America karatu amma ya ƙi, yanzu kuma gashi nasameshi ta dalilin ki Nana, dan Allah ki taimakeni"

Tunda ta fara magana suke kallonta, tana gama faɗa Nana ta ce


"Ashe kuwa zaki shekara ɗari ba kiyi aure ba idan har daddyna zaki aura" Hameeda ce ta ce " haba Nana menene abun faɗar haka ai idan niceke wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare tunda dama bakyason matarshi kinga idan ya auri ƙawarki sai ku haɗe mata kai " Aneeserh ce ta ce " wai ku mene haka ? yama za ayi ƙawarta ta auri babanta wannan ai abin kunya ne " tsaki Azrah ta yi ta ce "neeserh babu ruwanki dani saboda baƙin cikin kar nazama first lady to Allah ya fiki " a fusace Nana ta miƙe ta nunata da yatsa ta ce " toh bari kiji idan kina tunanin zaki aureshi to wallahi kima daina " ko saboda me ?" cikin faɗa ta ce "sabida mijina ne!! "




Comments, share nd like.




Story and written by:

*Nanameera*


Meera Love's yhu🥰🥰🥰🥰🥰[1/2, 23:41] Nanameera: https://chat.whatsapp.com/DlFBkx450nJA8CYpdTTx8B


🌹🌹 *NANAH*🌹🌹




Story and written by:


*Nanameera*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



🅿️....3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣



___________✍Kallonta suke da mamaki yayinda ta yi gaba ta barsu awajen, bayan ta koma gida kai tsaye apartment ɗin Mama ta tafi , ta na shiga ta huce ɗaki ta yi wanka , bayan ta fito ta tadda Ma'a zaune ta na kallo. Ƙarasowa ta yi ta zaune kusada ita , kallonta Ma'a ta yi ta ce

" ke kuma yaushe kika shigo??"

murmushi ta yi ta ce " ɗazu lokacin kina ɗaki , ina Mama?"


" Mama ta na ɗaki ta na bacci"


Shuru Nana ta yi ta na tunani ganin haka ya sa Ma'a ta ce " wai ke me akai miki " kallon Ma'a ta yi ta ce

"Ma'a wai Daddyna mijina ne da gaske ?"

murmushi Ma'a ta yi ta ce " meyasa kike tambaya Nana ?"

" kawai tambayarki nayi "

Da gaske mijinki ne amma kwata-kwata baki ɗaukeshi matsayin miji ba. Kallon Ma'a ta yi ta ce

"Toh ma'a mezan masa ?"

Kallonta Ma'a ta yi ta ce

" amma ke shashasha ce , banda haka da kinyi hankali "

Turo baki ta yi ta ce " ni kinsan wa ce bana so , wallahi aunty Hafsa na tsaneta "

murmushi ta yi ta ce " toh ai kishiyarki ce saboda haka idan kinga daddynki ya yi mata wani abu to kema ki ce dole sai an yi miki kuma......

kidaina gurɓata mata tunani , ba dai-dai bane sukaji Mama na faɗa


Kallonta Ma'a ta yi ta ce " A'a Mama wane irin gurɓata tunani , idan batasan ita wa ce agurinsa ba to wallahi sai Hafsa ta kusa rabasu , saboda ba tada hali ko kaɗan "

Zama mama ta yi ta ce

"Duk da haka idan yanzu ta riƙe duk abinda ki ka faɗa mata toh zata dunga tada fitina agidan saboda kinsan halinta "


Turo baki ta yi ta ce " ni dai inason mijina kuma saina faɗa masa Mama bata sona kwata-kwata , Ma'a na ta fi "


Murmushi Mama ta yi ta ce

"Toh ki faɗa masa sai ya zo ya kulleni ko ya rufeni da duka "

Kallonta ta yi kamar za ta yi magana sai kuma ta yi waje , bayan ta fita Mama ta ce " Allah ya shirye ki"...



Misalin ƙarfe tara na dare suna zaune su na kallo a tv Nana ta ce , " daddyna ai kai mijina ne ko?"

Kallonta ya yi ya ce " toh ke kuma a bakin wa kika ji?"

Kwabe fuska ta yi ta ce " daddy kawai ka ce eh"

Haɗe rai ya yi ya ce " baza'a faɗa ba "

Fashewa ta yi da kuka ta kwanta zata fara birgima ganin hakan ya sa ya ce " ya isa , kiyi shuru " cikin shagwaba ta ce " daddy ka ce Eh "

Murmushi ya yi sannan ya ce " Eh "

Kallonsa ta yi sai kuma ta kyalkyale da dariya , saida ta yi mai isarta sannan ta ce

"Kasanme daddy?"
girgiza mata kai ya yi ta ce

" yau wata classmate ɗina ce ta ce tana sonka , ni kuma na yi mata rashin mutunci kuma na daina kulata"

Tunda ta fara maganar ya ke kallonta har ta idar sannan ya ce " Allah ya kyauta " murmushi ta yi ta ce " ay ni kaɗai ka ke so ko daddy ?" gudun rigimarta ya sa ya ɗaga mata kai ta na dariya ta ce " yawwa ni ma ina sonka sosai daddyna....





Akwan atashi ba huya yau kusan two weeks da fara zuwanta makaranta , zaune suke ita da mate ɗinta suna cin abinci , bayan sungama sun fito suna tsaye suna hira Hameeda ta ce

" wai ke Nana bazaki kula wannan lecturer'n ba?"

Kallonta Nana ta yi ta ce " wai ke Hameeda bakida hankali?" rashin hankali kamar ya ya ?, nifa na gaya miki gaskiya ban yarda wai daddynki ne mijinki ba " hararta ta yi ta ce " kada ubangiji ya sa ki yarda " murmushi Aneeserh ta yi ta ce

"Nana dan Allah rabu da ita

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment