Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanya kayan ado musamman duk wabi abu da zai dauki hankalin patient ta hanyar sound dinshi ko wani abu shiyasa ake sanya uniform and ko takalmi bada kowanne ake zuwa ba dole sai preferred wanda aka za6a..irinsu zobe su agogo da sauransu suma duk are prohibited sbd suna iya daukan hankalin mara lafia shiyasa ake fara training mutum ya saba tun a school kafin ya tafi clinic..so i hope u understand dan nasan wasu zasuce wnn ta cika tsanani da yawa ko kuma ace tana rubuta abunda ba haka bane bayan haka tsarin kudan duk wani health institution yake saidai wasu sufi wasu tsanantawa)...karasawa yayi cikin office din ya tsaye nan inda take zaune snn yace"a ka'idar wnn abun da kikayi suspension za'a baki kuma bazaki dawoba har sai ya baje amma yanxu tunda you are going for holiday punishment dinki shine bazaki rubuta exams dinki na yau ba"...a rikice ta dago tana kallonshi idonta har ya ciko da hawaye...kallon nata yakeyi shima aikam nan da nan tayi kasa da nata don bazata iya daukan wnn kallon nashi ba...Nur ya taso daga seat dinshi ya zagayo inda yake yace"Bob me kakeyi ne haka pls?..meyasa bakajin mgn?.."a fusace yace mishi"ita why bazaka tambayeta meyasa batajin mgn ba?..meyasa ta cika fitina duk wani abu da tasan zai ja mata matsala bazata hakura dashi ba"...shiru gaba daya sukayi suna kallonshi...shidai Nur har yanxu bai dena mamakin wnn behaviour din nashi ba...shi kuwa ganin kallon da yake mishi ya karasa ciki ya dauki wani file akan table dinshi snn ya juya ya fita daga office tunda dama abunda ya kawoshi knn...kaman jira takeyi ya fita ta saki wani kuka mai ciwo...Nur ya dawo kusada ita da sauri yana kallonta a hankali yace"Lamido stop crying plss...dont cry"..girgiza kai kawai take as tasan idan daddy yaji an hanata rubuta exam sbd lallen da tayi applying fada ne zata sashi kilan ma saiya hada da duka..sam ba mai daukan iskanci bane shiyasa take mugun tsoronshi...ganin yanda take kuka Nur ya sake kwantar da murya yace"dan Allah stop crying kinji...duk wnn abun da kikaga yanayi baikai zuciyanshi ba...yanxun kije can office din nashi ki bashi hakuri"...yana rufe baki ta dago a razane tana kallonshi...sai kuma ta hau girgiza kanta tace"Sir bazan iya zuwa ba...inajin tsoro"...yace"don't be..ba abunda zaiyi miki inshaAllah believe me...kawai idan kinje ki kwantar da muryanki kice yayi hakuri dan darajar Mummy da Daddy na tabbata idan kika fadi haka zai hakura"...shiru kawai tayi tana kallonshi kaman bataji me yace ba...saida ya sake mata mgn snn ta fita daga office kaman mara lafia...secretary dinshi na ganinta tace ta jira ta fara mishi mgn...landline dinshi ta kira ta fada mishi yanada bakuwa kai tsaye yace a barta ta shigo...saida ta gama goge tears dinta snn ta shiga office din kai a kasa kaman munafuka...kanshi na sunkuye yana signing wasu papers so bai ga wanda ya shigo ba...ta karasa gaban table dinshi ta tsaya gabanta sai aikin faduwa yake...batasan why take tsoron bawan Allahn nan ba dan duk yanda takai da son ta bude baki tayi mgn kasawa tayi...kawai imagining take ta koma gida daddy ya samu labarin an hanata exam sbd tayi lalle...duk wnn abun da take baisan tana tsaye kanshi ba saida ya gama signing papers din ya dago...mamaki ya kamashi sosai dan baisan itace bakuwar ba...idanunta rufe suna fitar da hawaye sai bakinta daketa motsi kaman tanaso tace wani abu...kallonta ya tsaya yayi da kyau irin kallon da bai ta6a yima wata mace a dunian nan ba...tun daga kan idonta da suke rufe har zuwa kan lips dinta dake shinning as a result of hawaye daya wankesu har yanxun kuma basu dena motsi ba...haka nan yaji wani irin sanyi na rufe mishi jikinshi...irin internal sanyi da mutum keji idan yana fever...ya dauke kanshi da sauri sai kuma yaji hadadden zafi yana maye gurbin sanyin daya faraji...ranshi ya 6aci sosai jin yanda temperature dinshi ke raina mishi hankali...yanxun nn yakejin sanyi after a minute kuma ya farajin zafi...ita kuma har yanxu taki bude ido tana tsaye tana karanta mishi Yaseen cikin zuciyarta wai ko Allah zai dorata a kanshi ya janye abunda ya fada...ganin bayan sauyin temperature har mood dinshi ma ya fara sauyawa gata kuma ta wani yi mishi tsaye a kai kaman wata soldier ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace mata"keh.."a hankali ta bude idonta ta dora kanshi sai kuma ta sauke da sauri tana kwa6e fuskanta irin yanda babies keyi idan zasuyi kuka ganin wnn kallon data tsana yakeyi mata...kirjinta har bugawa yakeyi dan tsoro ta rasa wane irin magic mutumin nn keyi dake sanya mata tsoronshi haka...shidai Bobby baki da hanci ya saki yana kallon ta6ara iya ta6ara...yanda tayi da face dinta dama kana gani zakasan sanrgatacciya ce ta ajin farko ma kuwa...ranshi yaji ya sake 6aci dan a dunia ya tsani shagwa6abbun yara wlh...ya tsani yaga an zubama yaro ido yana zuba iskanci son ranshi baza ayi mishi fada ba sunan wai ana sonshi...can kasan makoshi yace"spoiled brat"...a fili kuma komawa yayi yayi relaxing kan kujeranshi still yana kallonta yace"leave my office if u don't have anything to say"...da sauri ta shiga girgiza kai cikin stammering tace"Sir...am...sorry"...wani kallo yake binta dashi before yace"what did u said?.."ta dan turo baki tace"i said am sorry"...tana rufe baki yace"sorry for yourself..now leave"...shima yana rufe bakin ta hade hannayenta alaman roko tace"Sir dan Allah...dan annabi..dan darajar Mummy da Daddy kayi hakuri"...shiru yayi yana kallonta totally speechless as ta fadi biggest weakness dinshi...in his entire life bashida weakness daya wuce parent dinshi likewise his strength especially Mummy that is still alive...ko ba'a fada ba kuma yasan aikin Nur ne wnn and he will definitely have to deal with him...ganin yanda yayi shiru ya kurama spot daya ido ta sake karya muryanta tace"Sir Please!.."wnn kallon dai data tsana ya watsa mata kafin ya nunata da finger dinshi strictly "but this should be your last...i promise duk na sake ganinki dashi you'll face the consequences"... tun bai rufe baki ba tace" nagode Sir..thank you so much"...bai sake cewa komai ba sai kofa daya nuna mata...ta dan ta6e baki tana goge tears dinta snn ta juya ta fita cikin ranta tace"inyamurin banza".

Taci sa'a tana zuwa aka fara raba question papers ta karasa seat dinta da sauri ta zauna...Billy daketa baza ido taga shigowanta tun daxu ta saki ajiyar zuciya dan sam hankalinta bai jikinta ganin har za'a fara bata shigo ba.

11 daidai suka fito daga exam hall...already Hamma Najeeb na zaune cikin mota yana jiransu dan haka suna fitowa suka nufi inda suka hango motanshi...shima yana hangosu ya bude motan ya fito...suna karasowa ta wani kwa6e fuska kaman zatasa kuka snn ta kama hannunshi ta rike idonta na cikowa da hawaye...hankali a dan tashe yace"what happened again?.."ganin taki mgn ya juya yana duban Billy yace"me akai mata?.."Billy ta buda hannu alaman bata saniba...shi kuma ya kama hannunta suka kan wasu cement chairs dake gefe still hannunta cikin nashi yace"Maama plss talk mana..waya ta6amin Mamana?.."tana turo baki tace"Hamma i don't want to come back to this college kayi mgn da daddy plss"..yace"but Maama why?..did something happen again?.."tace"Proprietor ne...Hamma wlh ya tsaneni..kawai daxu yayita min wulakanci hadda cewa bazanyi exam ba sbd nayi lalle..nidai i don't want to come back plss"...kamo dayan hannunta yayi yana dubanta da kyau yace"Maama kinsan daddy bazai ta6a yadda ba tunda ke kika dage sai an kawoki nan...but i think i have to talk to Proprietor din naku ya bar takura maki kawai"...tana goge hawayenta tace"there is no need..idan kaje ma wulakanci zai maka na sani...Hamma inyamuri ne fa..ko cikakken hausa bai iyaba"...yace"to indai bakiso inje in sameshi ki bar kukan nan haka..yanxun ku debo kayanku mu wuce amarya nata kirana wai inyi sauri in kaiku da wuri"..da sauri ta karasa goge hawayen nan da nan kuma saiga murmushi a fuskanta tace"laaa Hamma kasan har na manta wlh...Billy taso mu tafi nasan yanxu ana can ana shirye shiryen kamu"...girgiza kai kawai Billy tayi tana mamakin halin Lamido da shegen son biki..yanxun nan fa take kuka sha6e sha6e amma daga jin mgnr biki ta wartsake...kayansu kawai suka dakko daga wani class don dama basu fito da shirin komawa hostel ba..suka zuba su cikin booth snn suma suka shiga motan Hamma yaja suka tafi...basu samu yin sallama da Sa'eed ba as har time din yana exam hall bai fito ba..dama ba lokaci daya suka shiga ba so sun rigashi fitowa.

Saida suka fara tsayawa Bauchi suka ajiye Billy snn suka wuce Gombe bayan tayima Lamido alqawarin zata zo gobe ayi bikin da ita yau dai tanaso ta huta gajiya...suna shiga cikin Gombe murnanta ya kasa 6oyuwa dan ba karamin missing gida tayi ba...kai tsaye GRA suka nufa inda a nan Estate dinsu yake...Estate ne babba inda ciki duk wani wanda ke amsa sunan Lamido yake.. a nan ciki gidansu yake tun daga kan 'ya'ya da jikokin Lamido maza baya bari suyi nesa dashi mata ne kadai suke fita shiyasa ake yima Estate din laqabi da LAMIDO'S PALACE...horn yayi jikin tangamemen gate din shiga Estate din wanda daga can samanshi aka rubuta THE LAMIDO'S in capital letters..masu gadi sukazo suka bude mishi yasa kan motar ciki...tsayawa fadan haduwan ciki ma bata baki ne kawai dai is one of the biggest and beautiful Estate i have ever seen...ya tsaru ne iya tsaruwa snn yana daukeda gidajen da ni kaina bazance ga adadinsu ba don sunada yawa sosai...layi na uku ya shiga by his right side snn yayi parking motan a daidai kofan gidan daya kasance shine na uku layin...tun kafin ya kashe motar ta bude kofa ta fita da gudunta ta fada cikin gidan...bata ga kowa a parlor ba dan haka ta wuce zuwa dakin Ammi...a gaban madubi ta isketa zaune tana daura dankwali ta karasa da saurinta tayo hugging nata ta baya tana fadin"Ammi nayi missing diki wlh"...a hankali ta juyo ta zame hannunta daga jikinta snn ta daure fuska tana kallonta tace"bakida hankali kou?..wnn shine sallaman?.."rungume hannu tayi tana turo baki tace"Ammi nayi kewarki nefa sosai shiyasa amma kiyi hakuri"...juyawa Ammi tayi tacigaba da daurinta tace"zakici ubaki ne"...sake turo baki tayi tace"yanxu Ammi ko gaisawa fa bamuyi ba"...Ammi data gama daura dankwali tana kokarin sa wayanta cikin hand bag dake hannunta tace"ni kike jira in gaisheki ai tunda ke kika haifeni"...kaman bata son mgn tace"Ammi ina yini..ya gida"...tace"lafia lau ki wuce kije kiyi wanka ana gama ma su Husna make up kema ayi miki ku taho..tun daxun ake tafiya sbd ke nace su jira ku wuce tare"...tace"to bari inje Ammi..amma Aunty Fiddausi bata zo bane?.."tace"bazata samu zuwa ba Mufid ne ba lafia wai...yanxun mu fara zuwa ku gaisa da daddy sai kije kiyi wankan"...tare suka fita daga dakin bayan Ammi ta yafa mayafinta...tayi kyau sosai cikin coffee lace daya amshi skin clour dinta sosai snn kallo daya zaka mata kaga tsananin kamar da Lamido takeyi da ita...a zahiri kuma bazaka ta6a cewa ta haifeta ba dan yanda suka jero sai sukayi kaman kawaye...a palor suka samu daddy zaune yana yin waya...suka karasa ciki Ammi ta zauna kusa dashi ita kuma malama A'ee ta zauna a kasa tana wani irn nutsuwa kaman mutumiyar kirki...bayan ya gama wayar ya dubi Ammi da tayi mishi kyau kwarai yace"har kin gama?.."tace"na gama daddy zuwa zanyi Najeeb ya ajiyeni a hall din kafin ya fita..su kuma idan sun kammala sai Idris ya kawosu"..gyada kai yayi yana fadin"ohk"..snn ya maida kallonshi ga Aysha da take zaune tsumu a kasa kaman ba ita ba..cikin sabuwar nutsuwar data aro ta yafawa kanta tace"daddy barka da yamma"..yace"yauwa Aysha an dawo?.."tace"mun dawo daddy"...yace"Maa sha Allah ya exams?.."tace"daddy Alhamdulillah"...yace"to Alhamdulillah ya ban ganku tareda Bilkisu ba?.."tace"sai gobe zatazo daddy"..ya gyada kai yace"Allah ya kaimu..sai kije ki fara shiryawa kar suzo suna jiranki"..a hankali ta amsa da"toh.."snn ta mike ta bar parlon...itama Ammi mikewa tayi da bag dinta a hannu tace"nima bari in wuce daddy lokaci na kara tafiya"..kama hannunta yayi ya zaunar da ita yace"ki bari in kaiki da kaina mana...irin kyau da kikayi ya kamata ace sai na gama gani zaki tafi"..murmushi ta saki tana girgiza kai tace"daddy bakada dama wlh...inaga sai kaga mun aurar da Aysha snn zaka gane girma ya fara zuwan mana"...yaja dogon hancinta yace"ke girma ya fara zuwan ma bani ba..kuma ko mun aurar da Aysha ni babu abinda zai canxaki cikin zuciyata"..daria ta saki tana jin kaunar mijinta ta ko ina a jikinta snn ta sake mikewa tace"to nidai ayimin uzuri in wuce ba don ni ba..nasan yanxu ana can ana menana wlh"...bai sake yunkurin hanata ba yace"sai kin dawo Allah ya kiyaye"..ta amsa da"Ameen"..with a smile snn ta fita daga parlon...a main parlor ta samu Najeeb na jiranta dan haka yana ganinta ya mike suka fita tare..dukda cewa hall din da suke bikin cikin Estate din yake yanada nisa sosai da baza'a iya zuwa a kafa ba.

Aysha kuwa tana shiga dakinsu ta iske Husna zaune ana mata make up din Yusra kuma na kwance kan gado...saida suka gama rungume rungumesu itada Yusra as usual Husna nata faman ta6e baki tana binsu da harara snn ta fada bathroom tayo wanka sharp sharp ta fito...lokacin am gamawa Husna an farama Yusra...ita kuma ta tayar da sallah bayan ta idar ta dauki kayanta da yake iri daya dasu Husna har dinki ta saka snn ta zauna zaman jira.

Karfe biyar da wani abu suka shigo cikin hall din...dukkaninsu suna sanye cikin atampan ankonsu dark blue da adon sky blue a jikinta...kaman yanda na fada dazu hatta dinkinsu iri daya ne haka daurin dankwali da akai musu shima iri daya ne..takalmi da jakansu ne ya bambamta amma duk color daya ne...hall din ya cika makil da mutane banda sautin waka ba abunda ke tashi a ciki...amarya na zaune high table tareda angonta...Aysha na hangota ta fara zuwa inda take kawai suka rungume juna cikin rada tace"adda ruky kinga kyan da kikayi kuwa?.."amarya data kasance cousin dinta domin diyar yayan daddy ce tace"duk kyauna ban kaiki ba Lamido"..ta matsa daga jikinta tana dan turo baki tace"kema Lamidon zakice?.."itama amarya komawa tayi ta zauna snn tace"yes koba sunanki bane?.."tace"sunana ne kaman yanda kema yake sunanki..so daga yanxu duk kika kirani da Lamido kema da Lamidon zan kiraki"..murmushi kawai tayi mata ita kuma ta juya ta tafi..can inda ta hango da yawa daga cousins dinta ta nufa wanda duk yawancinsu age mates dinta ne suma duk suna sanye da anko...nan suka hau rungume rungume suna farin cikin ganinta.



Daga wnn page na kawo karshen Free pages dina sbd haka inayina kowa fatan alkhairi...wayanda sukayi patronizing a big thank u to all Allah ya saka da khairan🙏🏻

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment