Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tareda kama hannunshi yace"zo mu tafi dan Allah what's done is done saidai a kiyaye gaba kuma"..baiyi masa musu ba ya bishi suka fita daga dakin matron ta bi bayansu...suna fita ya daddage ya fizge hannunshi dake cikin na Nuru snn ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga...shima Nur karasawa yayi ya shiga snn ya dauko wayanshi ya kira mai gyara musu wuta yace azo a gyara a yau din nan...bayan ya kammala ya juya yana kallon Bobby daketa faman cika yana batsewa yace" Bobby are sure you are alright?.. wnn 6acin ran duk na meye?.."ko kallon inda yake baiyi ba balle yasa ran samun amsa...shima baiyi expecting amsan nashi dan haka yaci gaba da mgnrshi"you shouldn't have acted like that sai kace secondary school?..besides kudi fa suka biya"..tun kafin ya rufe baki ya juyo yana kallonshi da wani irin karaji yace"seriously bayansu kake bi?..yanxu da sun konamin building zaka iya biyana ne?..kuma da suka biya kudi ai ba kudin building dina suka biya ba kudin zama cikin Hostel suka biya so dole inyi mgn idan naga zaayi min 6arna"...shiru kawai Nuru yayi yana kallonshi deep down yasan da akwai abunda ke damunshi...ya tabbata wnn fushin ba iya na an kusa kona masa building bane dole da akwai wani abun a kasa...har suka koma cikin makaranta ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu...kafin su fita Nuru yace zai sauka dan bai gama aiyukan da yakeyi ba..babu wasting of time driver yayi parking shi kuma ya bude motar ya sauka snn suka cigaba da tafiya...bayan fitarshi Bobby ya sauke wani numfashi da yake rike dashi tun dazu tareda jingina jin seat din da yake hadi da lumshe idanu...baisan wane irin bala'i bane ya hau kanshi yau din nan...shi kanshi haushin kanshi yaji yanaji bai kuma san dalili ba...har ga Allah maganan da Nuru ya fada yasan its not that far from the truth..bai kamata yayi acting kaman yanda yayi ba amma ko Allah ya san shi kanshi baisan abun da ya hau kanshi ba a lokacin..bai kuma san daga ina duk wnn masifan yayita tahowa gareshi ba...kawai shidai ya tsinci kanshi cikin tsananin 6acin rai which he couldn't control..ya lunshe ido yana sake budewa har yanxun idanunshi basu dena hasko mishi ita sanye da kayan 'yan ball ba...ya saki wani tsaki kuma wai sbd tsabar iskanci shine ta juya musu baya wato tunda sun gama ganin gaba su kalli bayan ma knn...yau ya sake tabbatar da cewa ita din sangartacciya ce..idan ba haka ba why yarinya mace kamarta zaa barata tana supporting wani football club kuma har a gidansu a biye mata ana wani siya mata jessy da gajeren wando tana sawa..wai har bedsheet na Manchester sai kace wata namiji...runste idon yayi yana wani girgiza kai duk a kokarinshi na ya dena ganin pictures din nata saidai to no avail...gaba daya yaji yayi dana sanin zuwa Hostel din ma at the first place..daya sani da Nur ya kirashi kawai yace mishi bazai samu daman zuwa ba da shknn babu shi babu ganin wnn masifa...wnn yarinyar ya rasa wace iri ce ita da take kokarin yi masa kutse cikin rayuwarshi...ya tabbata masifan daya rufeta dashi hadda tsanar da yayi ma 'yan garinsu yasa shi haka...kilan da bai san 'yar Gombe bace bai zama lallai ya aikata abunda yayi ba...jingina ya sakeyi yana kara sakin wani tsakin duk ranshi yabi ya jagule...a daya 6angaren kuma ga wancan mara kunyan da yake kokarin sake kustowa cikin rayuwar 'yar uwarshi again..baisan me yake takama dashi ba har da zai dauki waya ya kirata sbd bashida kunya...sai kuma wnn kaddararren lecture da Mummy tace sai yaje yayima yaran can..shi sam wnn abun bi gamsheshi ba...baima san taya zai fara shiga class ya rike marker yace zaiyi musu lectures ba..baisan ta ina zai fara ba...a takaice har suka kai gida bai dena wadan nan tunane tunanen ba..gaba daya kanshi ya dauki wani zafi kaman wanda ke amfani da wutar lantarki.

Tunda suka fita Lamido ta zube nan kasan dakin tana sakin wani marayan kuka...Bilkisu ma batasan lokacinda ta durkusa nan kusa da ita ba suka taru suka hada kai sunata kokawa abunsu...if you see yanda suke kuka zakayi tunanin mutuwa akayi musu...saida sukayi na sama da one hour Billy ta dakatar da nata snn ta shiga rarrashin 'yar uwarta amma a banza...ta kwashi wasu 30 mins tana rarrashi ganin ba denawa zatayi ba ta mike tareda rage kayan jikinta ta fada bathroom...wanka tayo tareda alwala snn ta fito ta gabatar da sallahn azahar da akayi tun dazu basu tashi sunyi ba suna aikin kuka...har ta idar da sallahn Lamido bata dena kuka ba...ta karasa wardrobe dinta ta dauko dan dogon riga mara nauyi tasa snn ta sake komawa gun Aysha data koma kan gadonta ta kwanta tareda lullubewa da blanket...kawai ayyanawa take da ace daddynta irin easy going mutane ne da babu abinda zaisa ta sake kwana a FCNM saidai kawai su ganta a gida...to sanin da tayi kota fada mishi ma ba goyuwa da bayanta zaiyi ba kilan ma saidai ta janyo ma kanta fada yasa ba yanda ta iya haka nan zata hakura tacigaba da zama ko bataso...tun dazun wayanta ke vibration amma ta kasa tashi ta dauka...Billy da ta gaji da jin vibration din ta dauka tareda picking call din ta kara a kunne...a daya 6angaren Hamma Najeeb yace"Maama are you mad anata kiran wayanki bakya dauka?.."cikin voice dinta da bai gama warewa ba Billy tace"Hamma ba ita bace"..da sauri yace"Subhanallah Bilkisu what happened?.. you sound somehow..ina Maaman take? "..a hankali ta juya tana duban Aysha da har yanxun ke kudundune kan gado tace" Hamma gata...kuka takeyi tun daxu"..a dan rikice ya sake fadin"Ya Ilahi meya sameta?..bata wayan muyi mgn"..ba musu ta karasa ta yaye blanket data lullu6e dashi ta saka wayan a speaker snn ta ajiye kusada face dinta tace"Hamma gashi nan na bata"...da sauri yace"Maama can you hear me?..what happened?.. why are you crying?.."da sauri ta mike zaune tareda daukan wayan ta rike a hannunta har yanxun bata dena hawaye ba tace"Hamma bana son makarantan nan please..inaso in dawo gida dan Allah"..hankalinshi duk ya tashi yace"Aysha me yake faruwa ne wai?..me akayi maki?.."tana kuka tayi mish bayanin duk yanda sukai da proprietor daxun...yayi shiru har saida ta gama snn yace"to ki kwantar da hankalinki ina nan zuwa gobe kinji..first thing in the morning zan taho inshaAllah amma ki dena maganan dawowa gida kinsan daddy bazai yadda ba"...ta kai hannu tana goge hawayenta tace"Hamma to nidai kazo dan Allah...i really want to see you"..yace"ba damuwa zanzo inshaAllah..stop crying kinji"...gyada mishi kai tayi kaman yana kallonta...saida ya tabbata ta dena kukan yace"to bari in kaima Ammi zakuyi mgn dama itane tace in kiraki and karki nuna mata wani abu ya faru okay?.."a hankali tace"toh"...bai sake mgn ba ya fita zuwa parlor inda gaba daya suke zaune snn ya mikama Ammi wayan yace"yauwa Ammi gata"..Ammi ta amsa wayan tana fadin"kun gama sirrin naku knn?.."baice komai ba yayi daria ita kuma ta kai wayan kunnenta hade da sallama..a hankali tace"wa'alaiki salaam Ammi ina yini"..tace"lafia lau ya jikin naki?.."tace"naji sauki Ammi..ina Yusra"..Ammi tace"Yusra gata nan..kina jina?.."da sauri tace"inaji Ammi"..."wani mgn kika kira fiddausi kika fada mata?."..lokaci daya Aysha ta wani zaro ido hadda su rufe baki tace"aunty fiddausi wai?..Ammi me zan fada mata ni toh?.."bata rufe baki ba Ammi tace"zakici ubanki wlh..kin kirata kin hadata da 'yar uwarki shine yanxu kike tambayana me kika fada mata?.."ta marairaice tace"wlh Ammi kome Husna ta fada karya take..ya zaayi ma ki yadda na da mgnrta ni da nake babba baki yadda da nawa ba?."dan tabe baki Ammi tayi tace"da kike babba ai ba hankali gareki ba har yanxun..kuma kome kika fada mata maza maza ki kirata yanxu kice mata karya kike dan ba cikakken hankali gareta ba itama fiddausin"..batasan lokacin da murmushi ya dan subuce mata ba tace"kai Ammi maman tawa?.."Ammi tace"Maman taki fa shiyasa duk wani rashin mutuncinta ai kikayi gado..lokacin da muna gida Fiddausi ai ba karamar fitinanniya bace"..batace komai ba sai daria da tayi...Ammi tace"iceko kina kiran daddy ki gaisheshi?.."tace"ina kira Ammi..ko jiya saida na kira ban sameshi ba"..tace"to ki sake gwadawa yau ko gobe..ya danyi tafiya ne amma nasan a yau ko goben zai dawo"..tace"InshaAllah zan kira Ammi..ki bawa habibty mu gaisa plss"..ba musu Ammi ta mikama Yusra wayan snn ta bar parlon...Yusra ta amsa da murnanta saidai kafin tayi mgn Husna ta kwace wayan tareda kaiwa kunnenta tace"to Adda ni da baki nemana sai me?..duk tsiya dai ni kika fara sani kafin Yusran"...wani murmushin Aysha ta saki tanajin yanda lokaci daya duk wnn damuwan data shiga na tafiya tace"kuma dana fara saninki ai ba cewa akayi dole sai nafi sonki ba"...Husna ta wani murguda baki kaman tana ganinta tace"kuma ko Hamma zaizo na fasa biyoshi wlh"..tana gama fadin haka ta ajiye wayan tayi gaba abunta...Yusra ta dauka tana murmushi suka fara mgn...duk abunda suke Hamm na zaune yana kallonsu...lokaci daya Aysha ta mance da wani 6acin ran proprietor sukaita hira da qanwarta...basu suka gama ba saida ya kar6e wayan da kanshi...sai a lokacin ta samu ta shiga toilet tayo wanka snn tazo ta shirya ta sake hayewa kan gadon ta kwanta sbd Billy bata dakin...tana kwanciya sai abubuwa da suka faru suka shiga dawo mata...ta tuna yanda ya daure fuska ya kuma tsareta da wnn shegun idanun nashi mai kama dana aljanu ta bakin na Billy...batasan wane irin magic ke gare idanun nashi ba da yana dora mata su taji kaman an tattaro duk wani rashin nustuwa da tashin hankali na duniyar nan an dora mata su akai...anya kuwa mutumin nan ba wani abu yakema idanunshi ba?..tana cikin tunanin Billy ta shigo dakin ta mika mata wayanta dake hannunta tace"kar6i ki ce masa ya dena kirana dan Allah..haba! tun daxun yaketa faman kira ko yanaso ya shanyemun caji ne?.."ba musu Aysha ta mike zaune tareda amsan wayan daga hannunta taga Lamido's bestie ke kira...dariya ta saki sosai dan har gobe bata dena dariyan wnn sunan da tayi saving number besty dashi..wai Lamido's bestie sai kace wani yace bestienta ne ita...har kiran ya katse wani ya sake shigowa bata dauka ba...Billy data kulu tace"malama idan bazaki dauka ba bani wayata dan Allah"..bata bata wayan ba tayi kokari ta tsayar da dariyan snn tayi picking tareda karawa a kunne...yanajin an dauka yace"Haba my Billy"..Aysha ta wani zaro ido jin abunda ya fada hadda toshe baki tace"besty ba ruwana wlh"..dan dariya shima yayi kafin yace"inata kiran wayanki bakya dauka itama kuma wnn 'yar rainin hankalin sai wani jamin class takeyi taki daukan wayan sai kace saurayinta"..yana rufe baki Billy da taji kaf abinda ya fada ta daga murya tace"Allah ya kiyaye na rasa dawa zanyi soyayya sai kai...kuma a kashe a bani wayana sai ka kira wayarta ku cigaba da shirmenku"..dariya yasa sosai Lamido na tayashi...saida sukayi me isarsu snn yace"besty wai an fasa zuwa saloon din ne?..kin ganni fa tun dazu a bakin gate dinku ina jiranku"..tana dan girgiza kai tace"anya zuwa saloon din nan zai yiwu kuwa besty?..i don't feel like going out"..tana rufe baki yace"kuma shine baki kira kin fadamin ba saida na baro gida nazo?..fadamin me yake damunki da zakice you don't feel like going out?..na sanki da son yawo fa besty"...tayi shiru tanajin yanda 6acin ran dazu ke son dawo mata sabo fil...shi kuma jin tayi shiru sai yace"alright ki fito waje sai muyi mgn..ina bakin gate"..bata ce komai ba ta kashe wayan snn ta mike ta zura hijab tace ma Billy"taso muje"..tayi mata wani kallo tace"je ina?.."tace"wajen besty mana bakiji yace yana bakin gate ba?.."tsaki ta saki tana kokarin hawa kan gadonta tace"sai kin daw.."bata gama mgnr ba ta shiga janta suka fita daga dakin tunda already da akwai hijab a jikinta...har suka fito waje bata dena jan hannunta ba itama kuma bata dena kokarin kwatan hannun nata ba har suka karasa inda yake...ya bude mota ya fito yana kallonsu one by one kafin ya danyi murmushi yace"to a bani labari menene ya faru?.."Bilkisu ta daure fuska tana kawar da kai Lamido kuma tace su fara samun wuri su zauna first... duk basuyi gardama ba suka karasa wani dan wuri da aka zagayeshi da flowers tsakiya kuma cement chairs ne suma aka zagaye wurin dasu suka zauna...suka danyi shiru na wani lokaci kafin Aysha ta bashi labarin duk yanda sukayi da proprietor daxun...shi kanshi baiji dadi ba kuma suma yaga yanda duk Mood dinsu ya sauya dan haka yace ko baza'a je saloon ba shi yanaso ya kaisu wani wuri...Bilkisu ce ta fara cewa bazataje ba kunsan mutumiyar taku😂sai da kyar suka samu suka lalla6ata ta amince ta bisu..daga nan basu koma ciki ba suka shiga motanshi suka wuce..kai tsaye Ten to Ten ya fara kaisu yayi musu ordern abinci mai kyau yace suci dan yasan yau da kyar idan sunyi lunch gaba dayansu...ba suyi musu ba kuwa sukaci dan da gaske ba abinda sukaci tun breakfast... suna barin nan ya kaisu park nan kuwa duk suka ware suna enjoying kansu...bayan sun bar park din suka shiga Ado Bayero Mall sukayi shopping snn sukai branching a gidan grandmother dinshi dake Tarauni...tana zaune parlor tanashan nono da fura suka shigo...ta dago tayi musu kallo daya tareda ta6e baki snn ta cigaba da shan furanta...saida suka karasa ciki suka zauna Sa'eed yace"Hajjaju baki ganni da mutanen naki bane?.."sake ta6e baki tayi ta kur6i furanta kafin tace"ai ni ba ruwana da mutanen nan yanxu...tsakani da Allah suna cikin garin nan yaushe rabon da naga kafafunsu cikin gidana?.."dan murmushi Billy tayi tace"Haba Hajiya kinaso Sa'eed yaji kanmu knn?.."tace"yo jin kai na nawa kuma Bilki?..ai saidai kar a kuma"...Aysha daketa murmushi itama tace"to munji mun dauki laifinmu Hajiya kuma mun bada hakuri inshaAllah baza'a sake ba..daga yanxu duk weekend sai bestie ya kawomu mun gaisheki"...harara mai kyau ta watsa mata tace"sarauniyar 'yan dadin baki..to na hakura dai ba dan halinku ba..ya kuke ya karatun?.."sukace"karatu Alhamdulillah Hajiya..ya gida"..tace"lafia lau..ya wajen iyayen naku?.."Sa'eed dai na zaune yana kallonsu..lokaci guda i hira ya 6arke a tsakaninsu dama hajiya ba daga nan ba akwai labari su din ma kuma ba baya bane...a takaice sai da sukai sallahn magrib suka bar gidan...kai tsaye ya maidasu Hostel kowacce rikeda kayan kwadayin da suka siyo a shoprite..duk wnn kunci da 6acin rai da suka shiga daxun yayi disappearing..besty kam yayi kokari.

Wahsegari sunday karfe 7 daidai Bobby ya dannawa Nuru kira...bai dauka ba sai a karo na biyu ya daga cikin magagin bacci...Bobby ya dan ta6e baki jin bacci ma yake yace"kana jina?..ka fadama students din naka zan shigo 8 muyi lectures din..and tell them duk wanda ta wuce 8 batazo ba batada C.A"...yana gama fadin haka bai tsaya jin me zai fada ba ya kashe wayanshi...da mamaki sosai Nur yabi wayan da kallo kafin ya sake danna masa kira...saida ya kusa katsewa snn ya dauka..da sauri Nur yace"Bobby me kake nufi ne wai?..i don't understand"..babu gardama ya sake repeating abunda ya fada daxun..Nur ya wani marairaice yace"amma Bobby ka duba time kuwa ka gani?..this is past 7 yanxu har yaushe aka kira aka sanar dasu su fito gashi yau weekend"..a takaice Bobby yace"that's non of my business.. ba kai kakeso inyi musu lectures ba?..to gashi nan zanyi and wallahi duk yarinyan da ta sake na rigata shiga class din nan tayi loosing c.a so kindly call and ask them to start coming tun kafin 8 din yayi"...still yana gama mgn ya kashe wayanshi...Nur ya girgiza ya shiga neman number Lamido ya samu ya kirata...yasan duk meyasa Bobby ke wnn abun sbd yayi amfani da Mummy ya tilastashi yin abunda baiso ba shine shima yakeso ya rama ta wnn hanyan...yana zuwa kan numberta yayi dialing amma har ya katse bata dauka ba..shi kuma bai hajura ba ya sake kira..yana dab da katsewa ta dauja cikin muryan bacci tace"good morning sir"...yace"Morning Lamido inaso ki sanar da duk 'yan class dinku su shigo college zuwa 8 an samu wanda zaiyi taking over reproductive health dinku"..da sauri ta kalli wall clock dake manne cikin dakin nasu kafin tace"but sir this is 7:15"..yace"i know just try your best..tell them duk wadda batayi attending ba tayi loosing c.a and i want yiu to be fast about it please"..a hankali tace mishi"ohk"..snn ya kashe wayan...Billy dake bacci ta fara tashi tayi mata bayani snn ta dauki wayanta ta kunna data tayi musu bayani ta voice note ta tura a group snn kuma ta dhiga kiran duk wanda tasan zai iya sanar da wasu tana sake fada musu...Billy kuma fita tayi tayi announcing wa 'yan class dinsu dake cikin hostel din...saida ta tabbata ta fadama kowa snn ta koma daki..itama Aysha daidai lokacin ta gama kiran duk wanda zata sanar ma...tana duba agogo tana 7:35 dan haka ta mike da sauri ta fada bathroom tayi wanka sharp sharp tana fitowa itama Billy ta shiga...karfe takwas saura mintina goma suka gama shiryawa..ita tana sanye cikin abaya sky blue tayi rolling mayafin rigan..Billy kuma dogon riga ta saka na atampa ta daura dankwali sai veil dinta a kafada...koda suka fita compound drivern school bus har ya fito dan haka suna gama fitowa suka shiga motan zuwa cikin makaranta...motan na gama parking duk suka fito suka nufi class dinsu makarantan yayi tsit sai few students dake shigowa karatu...mutum 8 kadai suka samu a class din sunzo idan aka hada dasu da suke cijin hostel su 15 sun zama 23 knn out of 38...hankakinta duk yabi ya tashi ta dauki waya tana kokarin sake kiran wasu kiran provost ya shigo wayan...tayi picking da sauri tace"Sir wlh har yanxu da yawa basu karaso ba..mu 23 ne kadai a class din"..yace"no problem ki fada musu suyi sauri suzo before 9 ni zanyi kokari in rike maku shi har zuwa 9 din"...tace"thank you sir"..snn ta katse wayan...group dinsu ta sake shiga tayi announcing cewa an kara musu 30 minutes dan haka kowa yayi sauri ya karaso.
Cikin ikon Allah kafin 9 din gaba daya sun hallara...shi kuwa Bobby yana office din Nur time to time yana duba agogo...9 din nayi daidai ya mike duka fito daga office din tareda Nurun...suna haurawa sama ta window ya hangosu zazzaune cikin class din kowa da kalar kayansa sai ya dan dakata da tafiyan yana duban Nur yace"and why are they not in uniform?.."Nur yace"dama lectures din weekend bada uniform suke zuwa ba gaskia..kuma kaima bakace ace musu su sa uniform ba ai"..bai sake cewa komai ba suka karasa class din hannayensu zube cikin aljihu.






Masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank..sai a tura evidence of payment ta 07063800556.









Rano✨






🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22


08


Suna shiga gaba daya class suka hada baki suna gaishesu..Nur ne kadai ya amsa musu da "morning class ya weekend?.." suka amsa da lafia yace"well as a result of maternity leave da malaman Reproductive Health dinku ta tafi nasan you people do miss alot a karatunku ga kuma exams dake approaching...Class Rep dinku tazo ta sameni da maganan and our Generous Proprietor here says he will assist you guys har kuyi covering syllabus dinku"..ya karasa mgn da wani killer smile a fuskanshi tareda dan juyawa ya kalli Bobby dake tsaye rungume da hannaye yana sauraronshi...lokaci daya Class din ya dauki tafi jin Proprietor da kanshi yace zaiyi assisting nasu nan kuwa basu san saida aka kai ruwa rana before ya amince ba...Lamido da Bilkisu kuwa kallo daya sukayi masa gaba daya sukayi kasa da idanunsu..Billy dai addu'a take kada Allah ya kawo dalilinda zaisa wnn shegun idanuwan nashi su sauka a kanta..ita kuma Aysha hararan gefen ido take binshi dashi cikin ranta tace"inyamurin banza inyamurin wofi"..daidai nan kuma Nuru ya dubi Bobby yace"to Dr.Bobby bismillah"..daga haka ya koma can karshen class din ya samu wani empty seat yayi zamanshi a wurin...shi kuma Bobby ya dan kalli class din har yanxun yana rungume da hannu thinking from where to start...saida yayi shirun amost 3 mins kafin yace"where do you guys stop?.."daya daga cikin 'yan class din ta fada mishi last topic da sukayi...yana dan gyada kai ya tambayi course outline nan ma suka bashi...saida ya gama studying course outline din snn ya ajiyeshi kan table dake gabanshi yace"well according to the course outline kunada remaining 5 topics to cover before the exams..now zamuyi kokari muyi covering 2 topics the ramaining ones kuma zakuyi dividing kanku into 3 groups..each group su dauki one topic suje suyi studying dinshi sosai zuwa ranan Thursday zakuyi presentation..do u get me?.."gaba daya suka amsa da sun gane...shi kuma ya juya ga board dinsu yaga akwai rubutu a jiki sai ya sake juyawa garesu yace"who's ur class rep?.."gaba daya suka nuna Lamido...shi kuma ya wani daure fuska ganin itace dan lokaci daya incident din jiya ya fado masa a rai...itama daure nata fuskan tayi snn ta mike kanta a kasa..dukda ba kallonshi take ba tanajin wnn shegun idanun nashi a kanta..."come and wipe the board"..ya fada still looking at her...batayi musu ba ta fito tayi wiping board din ta juya zata koma ya sake fadin"da fingers dina kikeso inyi maku rubutun?.."bata juyo ba ta karasa seat dinta ta bude locker dinta ta dakko wani pink marker ta kai mishi snn ta sake dawowa ta zauna...duk wnn abun dake faruwa Dr.Nuru na bayan class din yana kallonsu...murmushi kawai yake yana girgiza kai cikin ranshi yace"zamuga yanda za'ayi wnn lecture"...sunan topic din Bobby ya rubuta jikin white board snn ya juyo yana facing dinsu yace yanaso daya daga cikinsu ta danyi briefing dinsu about the topic before he starts...wajen mutum biyar ne suka daga hannu shi kuma ya shiga binsu da kallo daya bayan daya yanaso yayi choosing mutum daya a cikinsu karaf idonshi suka fada kan Lamido...ya dage gira yana kallonta da kyau hadda sakin wani dan iskan smile cikin ranshi yana ayyana ita zaiyi selecting dukda ba daga hannu tayi ba kawai dai yanaso yana brain dinta da kullum Nur ke cewa she's genius she's this she's that..yau yanaso ya kure brain din nata...daga nan inda yake tsaye yayi pointing dinta da finger dinshi yace"You.."da sauri ta dago idanunta saidai suna sauka cikin nashi ta sake mai dasu kasa...still yana duban inda take yace"fito kiyi briefing namu akan topic din ba kece class rep ba?.."ya karasa mgn still da wani killer smile a face dinshi...ita kuwa qala batace ba ta mike daga seat dinta ta fito...ta juya taga sunan topic daya rubuta snn ta sake juyawa tana facing class din making sure bata kalli inda yakeba don kada ma ya zuba mata wadan nan idanun nashi yasa ta kasa ta6uka komai...bayani ta shiga yi musu dalla dalla kaman ba briefing dinsu yace tayi ba...tunda ta fara dama ya jingina da wall ya wani lumshe ido yana sauraronta sam baiyi tunanin zata iya ba...a yanda take explaining ma sai yakega kaman koshi da yake certified gynaecologist bai zama lallai ya iya yanda tayi ba..sam baiji dadin hakan ba kuma dan so yayi ya kunyatata a gaban Nur da kullum yake kiranta genius...yanxu kam ko da bai yadda she's genius ba tabbas yasan she's brilliant tunda har ta iya explaining abunda ba'a koya mata ba haka..daga yanayin yanda take magana kuma ya fahimci kaman she's used to it dan babu wani alaman tsoro ko rashin sabo a tattare da ita...duk sai yaji ranshi ya fara 6aci all of a sudden...hada ido sukayi da Nur aikuwa ya dage gira irin ya kaga?..shi kuma ya dauke kanshi ba tareda ya kalleta ba yace ya isa haka ta koma ta zauna...6oyayyen ajiyan zuciya ta saki cikin ranta tace"Finally"..sa zahiri kuma batace qala ba ta wuce ta koma seat dinta..shi kuma ya dora daga inda ta tsaya...bayani yake musu sosai shima irin bayanin da bai ma ta6a zaton zaiyi musu ba..suma kuma class din suna participating sosai...nan take yaji ashe yin lectures dinma is not as bored as he thinks...a da kawai gani yake irin boring lectures zasuyi sai kuma yaga ba haka ba baisan ko sbd class din suna participating bane...yana karasa topic din data fara ya shiga yi musu dayan shima kuma suna understanding sosai...a takaice saida suka dauki almost 3 hours kafin su gama...bayan ya gama amsa tambayoyinsu ya sake jaddada musu mgnr

Please Login or Register in order to submit comment