Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace"Billy kin tabbata ta samu sauki kuwa?..duba fa yanda take kuka?.."harara me kyau Billy ta watsa mishi tace"kajika da wani magana sai kace bakasan halin bestyn naka ba...allura fa akayi mata shine take wnn abun kamar an yankata"...bata rufe baki ba wadda akama alluran ta dago tana dubanta fuska shabe shabe da hawaye tace"ni wlh gara a yankani akan dai ayimin allura...sbd tsabar mugunta inata ce miki kizo mu gudu amma kika ki har saida wnn azzalumin yazo"..rai a bace Billy ta mike tana kokarin barin wurin tace"ba laifinki bane Lamido laifina ne da nake damun kaina a kanki...next time dama kina fara rashin lafiyarki saidai bestyn naki yazo ya kawoki Clinic amma bani Bilkisu ba...kuma wlh saina kira Ammi na bata labarin duk iskancin da kikayi"...tana gama fadin haka tayi wucewarta ta barsu a wurin...Lamido ta sake fashewa da matsanancin kuka shi kuma bestyn nata ya danyi kasa da murya yace"besty dont mind Billy kinji..yanxu ki daure ki tashi in maidaki hostel sai ki samu ki huta sosai"...yana rufe baki ta hau girgiza tana hawaye tace"i dont think i can walk besty..gaba daya leges dina sun sake rikewa"..ya sake fadin"daurewa zakiyi besty just try it zaki iya"...ba musu ta dafa kujeran da take zaune tareda mikewa da kyar...shima mikewan yayi ya nufi inda motarshi yake ya bude snn ya dawo ya taimaka mata suka karasa wurin..tana shiga shima ya zaga ya shiga snn tayar da ita suka nufi gate din hostel.






Alhamdulillah Allah ya sake dawo dani habibties with another unique and interesting love story💞💞saidai this time around tafiyan nada bambanci dana baya domin kuwa Dr.BOBBY na kudi ne...masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank sai a tura evidence of payment through 07063800556.

Ina mika dumbin godia ga all of you out there Allah ya biyama kowa bukatunshi na alkhairi💞









Rano✨









🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22


02


A bangaren Bobby yana komawa office yayi sanitizing hands dinshi with a hand sanitizer snn ya fada kan sofa ya zauna yana jin haushin abunda ya faru...gaba daya bacin ranshi sai ya karu fiyeda wanda yake ciki already...tunda yake bai ta6a ganin sangartacciyar yarinya kamn wnn yarinyar ba...allura kawai takema wnn abun...kawai yau ta sashi yin abunda ya manta yaushe rabonshi dayi koda a gidane kuwa..ya manta when last yayima wani injection ko yan gidansu akwai Nurse dake musu injection shi Mummy kadai yake yiwa amma yau wnn spoiled brat din saida ta tilastashi yayi mata...yana zaune lokacin da sukazo wucewa yaji wani gursheken kuka da takeyi kamar wadda akama operation...haka nan
yaji kaman ya dauki bindiga ya harbeta har saita dena wnn kukan...For Gods sake injection kadai take yima wnn ta6aran?..wnn wace irin lalatacciyar yarinya ce?..wai meyasa wasu iyayen if sunga sunada kudi sai suyita spoiling yaransu haka?..meyasa yaran masu kudi yawancinsu sangartattu ne?...koda yake ba duka masu kudi suka taru suka zama daya ba dan shidai yasan a gidansu ko Miemie ce tayi wnn iskancin ba abunda zai hanashi lakada mata dan iskan duka...sai faman sakin tsaki yake feeling extraordinary hot inside...yana cikin shan coffee Mr.Obi ya shigo da abinci daga gida...ya karaso ya ajiye kan table snn ya mishi sallama ya fita...shi kuma Bobby ya maida kanshi ya lafe jikin kujera tareda lumshe ido...kaman daga sama yaji voice din Nur akanshi...bai bude idon ba sai cewa yayi"waya baka izinin shigowa office dina?.."Nur ya dauki basket din abinci ya nufi dinning dashi kafin yace"har saina wani jira an bani izini?..ko dazu ma kawai nace bari in dana ne?.."bai sake cewa komai ba saida ya mike ya isa dinning din ya zauna snn yace"why are you doing this?..meyasa zaka tura mutumin nan wajen Mummy?.."a nuste Nur yace"because you are not willing to listen to me...kai kanka kasan da kayi abunda nakeso tun farko bazai kaimu ga hakaba...kuma mutumin nan yanada kirki Bobby kaddarane kawai ya fada mishi snn yanada iyali kuma duk ta karkashinka suke samun abinci yanxu kanaso kayi musu cutting hanyar samun abincinsu sbd small mistake daya aikata?.."a hankali Bobby ya sauke ajiyar zuciya before yace"amma daga small mistakes ake zuwa har manyan mistakes ka sani...kan wane dalili zaka turashi wurin Mummy"Nur yace"nayi maka alkawari inshaAllah bazai sake ba...to be honest banajin dadin yanda kake kasa hakuri da workers dinka...sbd suna aiki a karkashinka ba yana nufin su slaves dinka bane...suma mutane ne kamar kowa and suna bukatan a ringa yi musu uzuri akan wasu abubuwan...banajin dadin wasu maganganun da suke fada a kanka shiyasa nakeso ka gyara"...tunda ya fara mgn Bobby yayi shiru yana sauraronshi yasan gaskia yake fada mishi yana kuma jin dadin yanda abokin nashi ke zaune dashi tsakani da Allah shiyasa komai dacin gaskia yake fada mishi ita...ganin yayi shiru yana tunani Nur dake kokarin kai loma baki yace"so yau azumi kakeyi knn?.."baice mishi komai ba yayi serving abincin shima ya shigaci a hankali...suna cikin cin abincin yace mishi"kasan me na gani a clinic yau?.."a hankali Nur ya girgiza kai alaman aah...saida ya sake sakin wani tsaki cikeda takaici yace"a spoiled brat..wata yarinya ce mai shegen shagwa6an tsiya...can u imagine yarinyan dake high institution ta tsaya tana kukan injection?.. wlh if u see how she was crying zakayi tunanin surgery akai mata..she was crying out loud kaman mara hankali..gaba daya ta karasa spoiling mood dina for the rest of the day..i feel like strangling her"...saida ya gama Nur ya shiga murmushi gamida girgiza kanshi yace"i think it was Lamido"..da sauri Bobby ya kalleshi yace"how do you know that?..besides mace kaji nace maka ba namiji ba.."Nur ya saki wani murmushi yana sake kai loma bakinshi yace"ai bama ni ba kaf FCNM bana tunanin akwai wanda baisan who is Lamido ba...jikar Lamidon Gombe ce...and duk college din nan Ita kadai na san tanama allura wnn kukan...she is allergic to injections"...Bobby na tabe bakinshi yace"ba wani allergy tsabar iskanci ne kawai da kuma sangarta"..Nur na girgiza kai yace"bazaka gane bane Bob...tunda nake ban taba ganin mace kaman yarinyar nan ba...she is so different from other girls...komai nata special komai nata unique...kaga na farko she is beautiful kai she is more than beauty itself... Snn she is intelligent...wlh ban taba ganin yarinya mai brain dinta ba..she is a genius tunda ta shigo makarantan nan take overalling kaf department dinsu...gata very young snn gata da goog heart...gata kum..."bai kai ga karaswa ba Bobby ya katseshi da fadin"malam hold it plss...this one you are saying as if you are taking about your girlfriend"..da sauri Nur yace"she really is an angel Bob you will never understand"..still bai bari ya karasa ba yace"naji enough talking about her now and ka sake cemin Bob you'll see the other side of me"...sake kai loma Nur yayi yana murmushi yace"wnn other side of you din ai koda yaushe cikin ganinshi nake..har devil side of you ma duk na gani so am not afraid"tsaki kawai Bobby ya saki baice mishi komai ba duk ya sake spoiling mood dinshi...suna gama cin abincin ya kira Mr.Obi yazo ya tafi da ragowar...sai a lokacin Bobby ya samu damar ce mishi ya kira Dr.Bukar yace mishi ya dawo bakin aikinshi..Nur yasaki kyakyawan smile kafin yace"i've already done that ai..tunda mgn yaje wurin Mummy nasan dole zai dawo ai"...harara Bobby ya maka mashi yace"wato u did it on purpose koh?.."Ugo ya daga shoulder dinshi tareda fadin"yes".

Karfe 4 ya fara shirin barin College bayan ya dawo daga masjid...kafin ya fita office wayanshi ya fara ringing yana dubawa yaga Sister akan screen...baiyi wasting time ba ya dauka yana cewa"Aunty Sumy how far"...daga daya bangaren sis dinshi tace"Bobby kanajina?...wata qawata ce ta kirani wai yarinyanta ba lafia sun kaita hospital dinka shine tace i should please ask u kaje ka duba musu ita plss"...saida ya gama sauraran abunda ta fada snn yace"but Aunty Sumy akwai many doctors a hospital din fa?..kinsan ni yau ba ranan shiga hospital bane yanxu haka ina cikin college"...Aunty Sumy ta sake yin kasa da murya tace"haba dan qanina...kirana fa tayi sbd tasan na isa insaka kaje...yanxu kawai sai in kirata incemata kace bakaza samu daman zuwa ba...kana ganin ya dace hakan?..kanaso ka nuna mata ban isa da qanina ba knn?.."dan daure face yayi yana turo baki yace"Aunty Sumy are you emotionally blackmailing me now?..this is not fair"..da sauri Aunty Sumy tace"ba wani emotional blackmail am just telling you the fact..dan Allah ka taimaka kaje ka duba musu ita Please otherwise zasuyi tunanin ban isa da qanina ba"...yayi shiru kamar bazaice komai ba sai can yace"i will go"...Aunty Sumy ta washe hakora tana fadin"yauwa my Lil bro Allah ya maka albarka kaji...Allah baka mace ta gari"...yana tabe baki ya kashe wayarshi yana kunkuni...cikin ranshi yace"tunda kin gama dani ai dole kice haka"...bai sake wasting time ba ya fita daga office...kafin ya karaso Mr.Obi ya bude mishi mota dan haka yana zuwa ya shiga ciki shima driver ya shiga suka fita daga makarantan...kai tsaye yacema Mr.Obi"Hospital zaka kaini".


FCNM Female Hostel,Apartment C Room 2a.


Zaune take tsakiyar gado ta zuba tagumi da duk hannayenta...gaba daya hankalinta naga Macbook dinta dake ajiye gabanta suna video call da yan gidansu...kana ganin yanda ta daure fuska take faman turo baki zaka fahimci fada akeyi mata...fara ce sosai kamar ka tabata jini ya fito kuma kallo daya zakayi mata ka gane Fulani blood ke running a cikin veins dinta dan she is full blood Fulani of Gombe state...face dinta daukeda siririn pointed nose da cute red lips masu masifar kyau sai kuma sexy idanunta da suke nan farare tas dasu kaman na larabawa...gashin kanta nada tsawo sosai tayi parking dinshi a tsakiya ta saki jelan nata yawo a gadon bayanta...red jessy ne a jikinta mai daukeda tambarin Manchester United a kirji sai black trouser dinta three quarter...daidai da bedsheets da pillow case dake shimfide kan bed dinta Red ne mai daukeda tambarin Manchester United ko ta ina...wnn alama ne na she is a die heart fan of MUFC...babu dankwali ko hula a kanta hakan kuma ya bayyanar da silky black hair dinta da yake nan a barbaje...ganin yanda ta bada hankalinta kacokam ga vidoe call datake yasa nima na karasa dan inga da wanda take magana...wata mace ce da kallo daya zakayi mata ka gane mahaifiyarta ce sbd tsananin kama da sukeyi da ita...hatta dimples dinsu da yake lostawa duk sukayi motsi da cheeks dinsu iri daya ne...dukda ba a zahiri nake ganinta ba dimples din are so visible da kana dora idanu a kanta zaka gansu...cikin fushi takeyi mata fada snn ta karkare da fadin"kuma wlh duk na sake jin ance kinyi irin wnn rashin hankalin sai ranki yayi mummunan baci tunda ke har yanxu bazakiyi hankali ba...kece babba amma kullum rashin hankalinki karuwa yake...na tabbata ko Yusra da take karama bazatayi wnn iskancin da kikeyi ba kawai sbd zaayi maki allura sai kiyita zubama mutane ihu kina musu kuka sai kace karamar yarinya?..dont worry daddynku yana dawowa dama zan fada masa ga abunda kikeyi a makaranta"...tunda Mom dinta ta fara fada batace wani abu ba sai yanxu...hankali a tashe murya tamkar zata fashe da kuka tace"Ammi dan girman Allah karki fadama daddy kinji wlh bazan karaba...Ammi kinsan yanda allura yakemin shiyasa nayi kuka wlh amma i promise bazan kara ba pls pls plssss"..ta karasa mgnr hawaye na wanke mata fuska...tasan muddin mgnr nan yaje kunnen daddy ta gama yawo...ta sanshi sarai mutum ne shi mai zafi shiyasa baya daukan nonsense kuma ta tabbata idan yaji mgnr nan yana iya zuwa har Kano yayi maganinta tunda tun tasowarta ake wnn rikicin da ita akan allura...tun tana yarinya dama duk zaayi mata allura saidai ya tsaya a gabanta rikeda bulala snn zata yadda...har zuwa yanxun kuma ta kasa sabawa dashi...tana rufe baki Ammi tace"to wlh na sakejin mgn makamancin haka sai kinci ubanki kuma itama Bilkisun zan fada mata duk kika fara period sai su barki da abunki tunda ke har yanxu bakisan annabi ya faku ba"...da sauri ta sake cewa"am sorry ban karawa"..Ammi bata sake cewa komai ba sai tsaki data saki tareda mikama sisters dinta dake zaune tun dazu suna jira suyi mgn da ita Macbook din hannunta kafin ta fita daga parlorn...da sauri ta goge hawayenta dan bataso su gani...immediate sister dinta mai suna Husna ta shiga duban screen din fuskanta da wani murmushi tace"hajia Adda mai kukan allura"..da sauri ta dago idanunta tana watsa mata harara tace"so na zama abokiyar wasanki ko Husna?..raini ya fara shiga tsakanina dake ba?"...Husna ta shiga girgiza kai tace"kai Adda dan Allah nidai bance haka ba...kawai dan nace mai kukan allurr"..bata karasa ba ta daka mata wani hadadden tsawa tace"Husna kina hauka?..ni kike fadama mgn haka koh?.."Husna tayi shiru tana duban yar uwar tata baki a tsuke tace"Allah ya baki hakuri..laifina ne ma dana dage sai nayi mgn dake..sai anjima"..daga haka ta mike da sauri ta ajiye Macbook din ta tafi dakinsu abunta...Yusra ta matso da fara'arta sosai tace"Adda don't mind her kinji?..she is not a good girl"..lokaci daya murmushi ya maye gurbin face dinta tace"of course she is not habibty..how are you?.."Yusra tace"ina lafia Adda..ya karatu"...saida ta dan bata rai snn tace"karatu ba dadi habibty kuma ina missing dinku sosai"..tace"muma muna missing dinki Adda amma Hammanmu yace duk zai sake zuwa wurinki damu zaizo"...tace"to shikenan habibty i can't wait to see you...yanxu ki bama Hamma Macbook muyi mgn dashi"..ba musu ta mike zuwa inda Hamman nasu ke zaune yana sararonsu ta mika mashi MacBook din...yana amsa yaja cheeks dinta tareda mikewa ya fada dakinsa...saida ya zauna akan bed snn ya daidaita screen din yana dubanta da kyau yace"so you are done"...tana wani tale baki tace"Hamma Ammi kaman zata cinyeni sbd fada...hadda cewa saita fadama daddy nidai dan Allah kace mata kada ta hadani dashi kaji"...murmushi ya saki yana cigaba da kallonta yace"ai ke dince Maama bakya jin mgn...na rasa gane wane irin tsoro kikema injection da duk akazo yi miki sai kin tarama kanki jama'a sai kace ba health personnel ba"...tana sake turo bakinta tace"Hamma dan ina health personnel dole sai naso allura ne?.."yace"ya kamata kiso ta mana tunda kina yiwa mutane"..ta rungume hannunta a kirji tana girgiza kai tace"nidai aah wlh..dan inayi bashi yake nufin dole nima sai anyi min ba...yanxun yaushe zakazo ka ganni kaga fa yau almost 6 weeks knn baka zo ka ganni ba"..yana murmushi yace"i will come inshaAllah nima ba karamin missing dinki nakeba...aiyuka ne kawai sukamin yawa suka hanani zuwa ganin qanwata"...nan da nan ta saki smile daya bayyanar da dimples dinta tace"to yaushe zakazo Hamma?.."yace"zanzo Maama amma ba yanxu ba...kinga wnn week din daddy zai dawo amma inshaAllah yana tafiya zamuzo har su Husna"..tace"to shikenan Hammana thank you"..shima yace"thank you cutie pie amma yanxu qafan ya warke koh?.."tana gyada mishi kai tace"ya warke wlh...kuma ko injection din ma bayamin ciwo kaman yanda yakeyi da...kilan proprietor dinmu bashida zafin hannu"...murmushi kawai Hamman nata yayi kafin yace"ohk ki samu ki kara hutawa yanxu and kice ina gaishe da Billy da kyau"..da sauri tace"zataji inshaAllh...besty fa?.."saida ya danyi jim snn yace"shima ina gaisheshi"...ta sake amsawa da zaiji snn sukayi sallama...ta ajiye Macbook dinta a gefe tana sauke ajiyar zuciya tace"Finally"...tana kokarin kwanciya Billy ta fito daga kitchen hannunta rikeda bowl data dama custard a ciki...tana karasowa ta janyo table ta dora mata akai snn tace"ga custard din nan idan zakisha"...Aysha ta dan daga ido ta kalleta sai taga fuskanta daure tace"haba mana Billy...haba my besty..fushin bai kare bane har yanxu?.."harara Billy watsa mata tace"kije ki nemi inda bestynki yake dai amma ba a nan ba...kawai dazu kikasa mutumin nan yayita watsa mana wadan nan shegun idanun nashi masu kama da na aljanu...saura kadan na saki fitsari wlh sbd tsabar tsoro"...Aysha na kokarin fashewa da daria tace"haba Billy fitsari kuma sai kace wanda taga mala'ika"...Billy tace"ba gara mala'ika ba Lamido shi yanada imani snn aikin Allah yakeyi...amma Proprietor fa kullum fuskanshi a haka yake sai kace namijin saniya"...wnn karon daria Aysha ta saki sosai sai kace ba itane me kukan allura ba dazu...saida tayi me isarta tace"wlh ni kaina bansan sanda na shiga hankalina ba...gaskia idanun mutumin nan basuyi ba a rayuwa...kawai kuna hada ido da mutum kiji kmr yayi miki asiri"...Billy ta sauke ajiyar zuciya tace"shiyasa ni ko hanya bana son hadawa dashi ballantana mu hada ido hantar cikina tazo tana kadawa"...kafin Aysha tayi mgn wayanta ya dauki ringing...ta dan tsayar da dariyanta snn tayi picking tareda fadin"my bsty"..a daya bangaren yace"besty ya jikin naki?.."tace"na samu sauki sosai besty"...yace"to Alhamdulillah wajen injection dinfa?.."saida ta kalli Billy taga yanda take ta wani tabe baki snn tace"shima da sauki sosai...Billy tace wai ita bazaka tambayi yanda take ba"...da sauri Billy tace"Allah ya kiyaye yaushe na fada miki haka?..me ma akai akayi wani Sa'eed da har zan damu dan bai tambayeni ba...ya dade baiki tambayata ba wnn matsalarku ce ba nawa ba"...Aysha najin Billy ta fara mgn tayi putting nata on speaker tace"besty kanajin mutumiyar taka koh"...yace"inaji rabu da ita besty duk wnn maganganun da take fada basu kai zuci ba...i know she is boiling inside sbd mai girma Sa'eed bai tambayi ya Bilkisu take ba"...tun kafin ya rufe baki Billy ta sake fadin"nikam Allah yayi min tsari da ganin wnn rana...kudai kuje can kuyita abunku amma bada Bilkisu ba"..Aysha dai na zaune gefe tana sauraronsu tanata yi musu daria...ta kasa gane wnn 'yar tsama dake tsakanin Billy da Sa'eed tun tale tale...tun farkon haduwarsu basa jituwa sam suna haduwa zasu fara tsokanar juna sai kace mage da bera...Friendship dinsu kuma ba karamin sake karfi yakeyi ba...dukda kasancewar kowa state dinshi daban karatu ne kawai ya hadasu a kano ba karamin shakuwa sukayi da junansu ba...shi Sa'eed dan kaduna ne sunanshi Sa'eed Mukhtar Makarfi...shekarunshi 25 yana karantar basic Nursing a FCNM dukda cewa saida ya kammala Bsc dinshi kawai sbd sha'awan Nursing profession yayi joining FCNM kuma sai Allah ya hadashi dasu...yanxu haka yana final year...Billy kuma asalinta jihar Bauchi...Bilkisu Ibrahim Muqaddas shine cikakken sunanta...she is a 2nd year student of Basic Midiwifery...class dinsu daya da Lamido likewise hostel dinsu..ita kuma Aysha Ahmad Lamido shine complete sunanta...suna kiranta Lamido kasancewar almost kowa a school abunda yake kiranta dashi knn...mahaifinta bafulatani ne Alhaji Ahmad Adnan Lamido shine present deputy controller general na Nigerian Custom Service snn shine 'da na biyar cikin jerin 'ya'yan Lamidon Gombe Alhaji Muhammad Adnan Lamido...mahaifiyarta kuma Maimunatu itama asalin bafulatanar Gombe ce...yara uku garesu Aysha itace babba sai Asma'u da suke kira Husna sai kuma Yusra data kasance 'yar auta...shi Kuma Hamma Najeeb cousin brother dinsu ne da mahaifinsu ya rike tun kafin a haifi Aysha shiyasa suka saba dashi sosai dan idan ba fada akayi ba bazaka taba tunanin Cousin dinsu bane.
Wnn knn...

Bobby bai samu dawowa gida ba sai after magrib...haka kuwa ya shigo gidan rai a hade sbd tsabar gajia da yayi...driver na shigowa ya samu wuri yayi parking snn ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya zagaya ya bude mishi kofa mai gadi yazo ya bude yanata faman mishi kirari sai kace wani sarki...Bobby bai iya ce mishi komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi entrance...tun daga compound din gidan zaka gane mamallakinshi ba karamin mai kudi bane duba da girma da kuma tsagwaron kyau da kuma tsaruwar gidan...katoton Mansion ne daya amsa sunan Mansion saidai abu daya daya bani mamaki is yanda naga gidan shi kadai ne kaf girman layin nasu..ko makota basu dashi dan sai kayi tafiya mai nisa daga nan kafin ka fara hango gidajen mutane...cikin raina nace kilan mutanen gidan basu son zama cikin mutane...ga uban motoci zube cikin compound din bila adadin sai kace ba kudi ake sawa ake siya ba...hatta plate number dake jikin motocin nashi duk sunanshi ne a jiki tunda daga Dr.Bobby 1,2,3 har zuwa ba adadi dan ban samu damar irga adadin yawan motocin ba...ajiyar zuciya na sauke ina jinjina baiwar kudi da Allah yayi masa at such young age snn nabi bayanshi zuwa cikin gidan...bai samu kowa a central parlour ba sai tv dake aiki sai kuma sanyin ac da qamshin freshener da suka hadu suka bada wani sassanyan qamshi a dakin...shi kanshi palorn abun kallo ne...bai tsaya wasting time ba naga ya nufi wani corridor suit dinshi rataye a shoulder dinshi...another parlour naga ya shiga wnn karon dai da akwai mutane a ciki...ya karasa ya zauna kusada wadda kallo daya nayi mata na gane Mom dinshi ce...if you see yanda yayi da face dinshi zai baka daria sosai...ya lumshe eyes dinshi tareda dora kanshi shoulder dinta voice dinshi can kasa cikin igbo yace"Mummy am home"...Mummy na shafa kanshi fuskanta daukeda wide smile itama da igbo din tace"welcome back son..akwai gajiyan aiki koh"...ya danyi pouting lips dinshi before saying"gajia sosae Mummy...kawai Aunty Sumy tace lallai sai naje na duba yarinyan friend dinta a hospital"..Mummy na cigaba da shafa kanshi ta maida dubanta kan Aunty Sumy dake zaune gefe tana aiki cikin system dinta tace"gaskia Sumayya baki kyauta min ba..haka nan kin wahalar min da yaro"..aunty sumy daria tasa sosai kafin tace"Mummy dan yaga kina biye mishi nefa yake wnn abun...ko Sabeer da yake dan auta baya wnn shagwaban da yakeyi..you better grow up wlh wnn shagwa6an babu inda zai kaika"...ta karasa mgn referring to him.






Littafin Dr.BOBBY na kudi ne...masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank... sai a tura evidence of payment through 07063800556.










Rano✨







🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22



03



Sake pouting lips dinshi yayi yace"Mummy blackmailing dina fa tayi wai idan banjeba friend dinta will think bata isa dani ba"...Mummy na kokarin bude baki tayi mgn wata yarinya da batafi 16 years ba ta shigo parlorn da wani mugun gudu kaman wadda kura ko zaki ya biyota...ta tsallaka ta boye bayan Mummy ba tareda ta lura da Bobby da har yanxun ke rungume jikinta ba cikin sauke numfashi tace"Mummy talk to uncle Sab plss...haka nan ya sameni a dakina wai na shiga mishi daki na taba Macbook kuma nidai Allah ban taba mishi komai ba..ko hanyan dakinshi ma banjeba"...tana rufe baki sai ga Sabeer din ya shigo parlorn shima a sukwane yanata kalle kallen inda zai hangota ya fara cewa"Mummy kinga Miemie kawai na ajiye abuna taje ta tabamin koh?..Mummy Allah kiyi mata mgn idan ba haka ba i will..."Bobby bai barshi ya karasa ba ya daka mashi wani tsawan da hatta Miemie dake boye bayan Mummy batasan time da ta fito tana rarraba idanu ba...ya shiga binsu da wani mugun kallo gaba dayansu aikuwa ba shiri duk sukayi kasa da idanunsu domin babu mai karfin zuciyar da zai iya jure wnn kallon da idanun Bobby ke binsu dashi...lokaci daya duk suka shiga taitayinsu dan ba karamin tsoronshi sukeji ba..haka zalika idanunshi ba karamin ladabtar dasu sukeyi ba musamman Miemie da duk ya zuba mata su sai taji kaman ta saki fitsari a wando sbd tsoro shiyasa duk gidan ba wanda suke tsoro kamanshi dan ko kadan baya saurara musu sbd yanda kullum cikin rikici suke yanda kasan tom and jerry...kullum cikin one rigima or the other suke duk kuwa da tazaran shekarun dake tsakaninsu aikinsu knn...saida ya gama binsu da matsiyacin kallo snn ya sauke idanun kan Miemie yana sake tamke fuska yace"meya kaiki dakinshi?..ban ma hanaki zuwa dakinshi ba?.."jiki na rawa Miemie tace"ka hana Uncle Bobby amma wlh nidai banje dakinshi ba...ina cikin zamana fa kawai yazo yace wai na shiga mishi dakinshi"...saida ya bari ta gama tsaf snn ya maida dubanshi ga Sab still fuska daure yace"kai ya akai kasan ta shiga maka daki?.."da sauri yace"Uncle Bobby na gama aiki cikin Macbook dina ko saving banyi ba na tafi masjid shine ina dawowa kawai naga tayi deleting"..yana rufe baki Miemie tace"Uncle Bobby i swear he's lying ni ban taba mishi komai b..."bata samu sararin karasawa ba sakamakon wani kallo da Bobby ya shiga binta dashi...yana pointing Sabeer yace"mate dinki ne shi da zakice yana karya?.."da sauri ta girgiza mishi kai alaman aah...Bobby yacigaba da fadin"menene sunanshi?.."hawaye na cikowa idonta tace"Uncle Sabeer"...ya sake fadin"who is he to you?.."hawayen da suka cika idanunta na zuba kan fuskanta tace"he's my Uncle"..wani kallon Bobby yacigaba da binta dashi ba shiri ta sake cewa"he's my mother's brother"..Bobby yace"good..ko don sbd wnn matsayin baiyi deserving respect dinki ba?.."wnn karon da kyar ta iya bude baki sbd kukan dake cin karfinta tace"he deserve"..yace"then why are you not respecting

Please Login or Register in order to submit comment