Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabo aka fitarma waziri da rabonshi kaman yanda yake a addinance...a ranan da aka gama a ranan ya tattara su gaba daya suka bar garin ba tareda ko waziri sunje sun duba ba...duk yanda Mummy tayi dashi kan suje suga jikinshi snn suyi mish sallama kin yadda yayi dan shi gani yakeyi ma kaman da wazirin aka hada baki aka kashe musu mahaifi tunda kira akai aka ce shine bashida lafia amma da sukazo sai sukaga akasin haka.

Abuja suka koma direct sukayi parking abunda zasuyi parking...ya sai musu sabon gida a kano kuma bai yadda wani cikin 'yan uwan Daddy sun saniba snn ya sake daukosu suka dawo...gaba daya saida yabi ya canxa musu sim card dukda dama ba wani communicating sukeyi da yan uwan daddyn ba amma still saida ya canxa musu dan kwata kwata baison sake ganin kowa a cikinsu...su barsu suji da ciwon kashe musu mahaifi ma da sukayi...ko Sab da ba wani contact dinsu yakeda ba saida Bobby ya amsa layinshi ya bashi new one...Mummy dai bada son ranta yake abubuwan nan ba amma ko yaya tayi mgn sai taga ranshi ya 6aci fiyeda tunani...da farko ma cewa yayi sai yayi bincike if ya samu da akwai sa hannun one of them a accident din Daddy then bazai ta6a hakura ba saiya mgnr court...da kyar da sidin goshi Mummy ta samu ta taushe shi ya hakura da zancen...itadai har zuciyarta bata zargin akwai sa hannun wani a cikinsu...kawai tanaga ai duk kiyayyan da suke mishi bazasu iya aikata wnn danyen aiki especially akan dan uwansu...a lokacin abokan mahaifinshi da yawa suna kokarin taimaka mishi ya samu aiki amma yace shi sam bazaiyi aikin force ba infact bazai ma iya aiki under government ba...da taimakon wani uncle din Mummy wanda ya kasance likita ya bude katon Hospital dinshi mai suna Freedom Specialist Hospital...ya dauki ma'aikata sosai kuma most of them yare ne as gaba daya yanxu ya tsani hausa fulani because yana ganin kaman duk halinsu daya da 'yan uwan daddy...snn kuma ya tsani Gombe ya tsani duk wani abu daya fito daga garin...bayan shekara daya Allah yasa mishi albarka sosai dan ya kusan ninka abunda ya kashe a iya wnn shekaran...daga nan sai yayi tunanin ya bude Nursing and Midwifery College snn ya bude primary da secondary school duk a nan cikin kano...da yake kudi ne suke aikin in no time ya samu fili ya siya aka fara mishi aiki...a shekara na biyu ya bude Freedom College of Nursing and Midwifery Kano da kuma Freedom Science Academy Kano...nan ma yayi employing staff sosai suma kuma daga igbo sai yoruba sai kuma sauran tribes amma bai dauki bahaushe ko daya ba...a lokacin ya damqa Freedom Science Academy a hannun Aunty Sumy cox 6angaren data karanta knn shi kuma College din ya damqashi hannun abokinshi Dr.Nur...da shawarwarin Mummy dana sauran mutane abubuwa suke tafiya yanda ya kamata...cikin shekaru kalilan ya samu kudi fiyeda tunanin mai karatu...ya cire Miemie da ilham daga school da suke zuwa ya maidasu freedom shi kuma Sab ya nema mishi admission a Nigerian Police Academy Wudil as yana matukar son ya zama Police sbd it was his Dad's ambition.

In summary cikin shekara biyar Bobby ya zama hamshakin mai kudi a kano state...tuni ya gina musu very big mansion a can airport road inda babu mutane sosai...gaba daya rayuwarshi yanxub bai cika son mu'amala da mutane ba especially hausawa cox yana ga kaman suma zasuyi treating nasu some how sbd kasancewar Mummy inyamura...gidane mai kyau da girman gaske inda babu wanda zai takurama wani a cikinsu...a takaice dai yana kulawa dasu sosai sosai kaman yanda yayima Daddy alkawari...cikin shekarun nan kuma ya sake bude another College of Nursing and midwifery a Lagos sai kuma Freedom College of Health Sciences and Technology shima a Lagos...da yake a can ya girma har yayi primary da secondary school so yanada mutane a can sosai da suke handling mishi Colleges din as bai cika samun time yana zuwa sosai ba saidai yana providing musu duk wani abu da suke bukata...bayan nan kuma ya bude Freedom Medical College Gwagwalada Abuja...itama ba karamin kawo mishi kudi takeyi ba and a wata baifi yaje sau daya ba wani lokaci ma sai yayi two months baije ba sbd aiyuka da suke mishi yawa...haka rayuwansu yacigaba da tafiya har zuwa yanxub da Mummy ke son dawo mishi da duk pain da agony da suka fuskanta a baya.







Inaga gobe zaku jini shiru sbd zan danyi tafia...sai zuwa jibi in Allah ya kaimu💞🌸


Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidencs of payment ta 07063800556.











Rano✨





🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22


11


Bayan sati hudu...


Yau tuesday Aysha na zaune cikin dakinsu kan study table ta dora macbook dinta akan table din tana kallon wasan Manchester United da Liverpool live...sai ihu takeyi tana nishadi duk ta cika dakin nasu da ihu sbd best player dinta Pogba gana performing well...yana ta6a ball zata hau ihu yanxu ma daddagewa tayi ta kwalla wani uban kara tana fadin"Goaal..yes yes..go on senior Man..go ahead"...Billy data fita karatu tun daxun sbd exams da suka fara jiya ta shigo dakin rungumeda katon text book dinta a kirji...ta karasa ta ajiye text book din kan shelve snn ta shiga rage kayan jikinta tana hararan Aysha tace"duk kinbi kin cikama mutane daki da ihu sai kace a kanki aka fara kallon ball"...Aysha da gaba daya hankalinta ke ga abinda take kallo ta saki wani smile tace"bazaki gane bane Billy wani hadadden ci Ronaldo yayi yanxun nan...and kinsan waye yayi assist?.."sake ta6e baki Billy tayi tana daura towel a jikinta tace"ya wuce Martial ko Rashford...ko kuma wnn gantalallen Lingard din"...tace"to duk basu bane Pogba ne..kuma gaskia kika sake cewa Lingard dinmu gantalalle za'aji kanmu dake a hostel din nan"...sake ta6e baki Billy tayi tareda shiga bathroom...har ta fito daga wanka hajia indo na nan inda take tana kallon ball dinta...ihu kuma ba fasa yinshi tayi ba saidai Pogba bai ta6a ball amma sai tayishi...Billy tayi banza da ita ta gama shiryawa abunta snn ta shiga kitchen ta hado corn flakes ta fito...tana zaune tana sha wayanta yayi kara...ta dauka ganin one of colleagues dinsu dake cikin hostel ne...tambayanta yarinyan keyi yaushe zasu fita karatu dan duk aka fara exams suna haduwa suyi karatu gaba saya su 'yan class dinsu dake cikin hostel din su 15...Billy ta amsa da bata sani ba su tambayo Lamido...tana tsaka da kallonta mutum biyu suka shigo dakin...daya daga cikinsu tace"Lamido ya mgnr karatun mu na yau ne?..kowa yana Common Room fa ku biyu kawai ake jira"...san juyowa tayi tayi musu kallo daya duk hankalinta naga kallon da take sam bataso a wuceta tace"safiyya dan Allah kuje ku fara da Billy ana gama wasan nan zan zo"..tana rufe baki Billy tace"babu wani farawan da zamuyi kawai idan bazaki koyawa mutane ba ki fada musu ba sai kima hanya hanya ba"...ta fada tana wani basarwa tasan tunda ta fadi bazata iya cigaba da kallon ba dan a dunia ta tsani mutum yace tayi mishi wulakanchi taki koya mishi wani abu...harara sosai ta sakarwa Billy kafin ta juya tana dubansu tace"ku bani 5 minutes plss ana tafiya half time zanzo"...Billy ta juyar da kai tana kunshe daria dama tasan maganinta knn...kaman yanda ta fada ana tafiya half time din ta mike ta fita hajia Bilkisu tabi bayanta...gaba daya sauran sun taru a Common Room din su biyu kadai ake jira...dakin yanada girma sosai snn da akwai expensive set of kujeru masu kyau a ciki hadda su tv da fridge da standard ac inshort dai babu abunda babu ciki har su curtains da center table like normal parlor dai sosai...each apartment sunada Common Room dinsu da bama wani zama ciki sukeyi ba sai idan abu ya kama irin haka...bayan sun zauna Billy tace"to yanxu da wanne ya kamata mu fara"...da sauri wata tace"mu fara complicated midwifery dan Allah...daxun dana daukoshi zan fara karatu har wani hazo hazo naga ina gani sbd tsabar bana fahimta"...gaba daya sunyi na'am da haka dan haka suka fara da shi din...course outline dinsu suke dauka sunabi one by one suna explaining snn duk wanda yakeda tambaya ya fada a amsa mashi...suna gamawa dashi sukayi other course din da shima zasuyi exam dinshi gobe snn suka watse.

Washegari bayan sun fito daga exam Aysha ta shiga kiran Sa'eed da tun safe bata ganshi ba...yana dauka tace"bestie where are you?.."yace"ina downstairs...kun fito daga exams?.."tace"eh..bari muzo downstairs din"...tana kashe wayan ta dubi Billy tace"muje yana kasa"...Billy ta wani hade rai tace"wai me zaiyi miki ne da kiketa nemanshi tun daxu?.."Aysha bata ce mata komai ba taja hannunta suka sauka kasa...can wajen wasu flowers masu kyau suka hangoshi yana zaune da wata class mate dinshi da alama yana koya mata abu ne...karasawa wurin sukayi suka zauna shi kuma ya sallami yarinyan da suke tare snn ya shiga kallonsu with a smile yace"so how was the exams?..Aysha tace"exam Alhamdulillah besty ya naka?.."yace"it was fine"...kallon Billy dake duba littafin hannunta yayi yace"so Bilkisu ya exams?.."tace"lafia lau"...ya kalli Aysha suka hada ido snn ya sske cewa"sai wani hade rai kikeyi sbd kin ganni...ki kwantar da hankalinki munayin counsil bazaki sake ganina ba"...ya karasa mgnr kaman wani abun tausayi...lokaci daya sai Billy ta dago tana kallonshi...idan akwai abunda ta tsana bai wuce yayi mentioning counsil exam ba duk sai taji jikinta yayi wani sanyi...ganin yanda ta kura mashi ido suka sake hada ido da bestyn shi sukasa daria...bayan sun gama yace" my Mom will be coming tomorrow.. hope zakuje ku gaisheta?.."da sauri Aysha tace"of course zamuje mana bestie..Allah ya kawota lafia...and yauwa bestie zaka kaimu lalle ranan Thursday idan mun fito daga exams...kasan cikin week din nan zaa fara bikin Adda Ruky"...yace"na sani besty amma baki ganin zaku samu matsala idan aka ganku da lalle?..nasan kinsan cikin ethics dinmu hadda kin applying wadan nan abubuwan"...tace"i know besty amma bansan ya zanyi bane...tun Thursday fa zaa fara bikin kuma ni bazan samu zuwa ba sai friday kaga banida time din yin lalle da sai na bari idan mun koma muyi...besides nafi son lallen kanawa yanxu..yafi namu kyau"...bai sake cewa komai ba kawai ya girgiza kai dan yasan tunda tasama ranta sai tayi lallen nan duk abunda zai fada ma ba changing mind dinta zatayi ba.

The following day kaman yanda suka tsara bayan sun fito daga exams suka koma hostel sukayi changing kaya snn ya kwashesu zuwa Tarauni gidan kakarshi...suka samu Mom dinshi zaune a parlor da Hajia sai dan autansu Mahmud...suka karasa ciki suka zauna snn suka gaisheta...ta amsa musu da fara'a tana tambayan su ya karatu...suka amsa da fine...tace"ga bestie ga Bilkisu koh?.."Sa'eed dake sauraronsu yace"Mom ashe baki manta ba"..tace"ya za'ayi na manta tunda kullum cikin zancensu kake"...Hajia tace"nima nan haka yake damuna da zancensu..magana daya biyu zaice besty tayi kaza ko kuma Billy tace kaza"...daria sukayi gaba daya jin yanda Hajia ke immitating mgnrshi...yana dan hararanta ta gefen ido yace"yanxu Hajia haka nake mgn?.."tace"oho kai ka sani"...sister dinshi ce ta fito daga daki waya kare a kunneta...tana ganinsu tayi hanging call din ta wani karasa cikin parlon da gudu ta fada jikinsu...Sa'eed yac"Lubna meye haka?..karya min su kikeso kiyi ne?.."ta daga jikin nasu tace"sorry yaya..nayi farin cikin ganin kawayena ne...kawayena da basu damu dani ba"..ta karasa mgn kaman zatai kuka...Mom tace"to sai ku shiga daki ku karasa mgn dan naga kaman they are not comfortable here"..Lubna ta mike tsaye rikeda hannayensu tace"yanxu kuwa Mommy"..daga haka
ta jasu zuwa dakinda ta fito Sa'eed ya bisu da kallo har suka shige...Hajia dake ankare dashi tun dazu tace"mutum dai yayita yaudaran kanshi da sunan kawance..watarana kana zaune wani zaizo ya dauke ya barka da cizon yatsa"...juyawa yayi yana kallonta yace" me kike nufi?.."tace"me kuwa nake nufi daya wuce kana son mace kana yaudaran kanka wani wai kuna kawance..idan bakayi da gaske ba kana zaune zata auri wani ta barka wlh"...yace"to ke waya fada miki inason wata a cikinsu?..we are just friends "..tace" shine nace kacigaba da yaudaran kanka Sa'eedu"...bai sake mgn ba ya juya yana kallon Mom dinshi sai yaga daria take musu..zaiyi mgn tace"babu ruwana tsakaninku ne wnn"..

Suna shiga daki suka zauna suna sake gaisawa...Lubna tace"da gaske mutanen nan baku damu dani ba..ko nemana fa ba wanda yakeyi a cikinku"...Billy tace"wlh abubuwan ne sai a hankali Lubna amma inshaAllah daga yanxu zumunchi sai kince ya isheki koba hakaba Lamido?.."da sauri tace"sosai ma kuwa..daga yanxu mun kulla knn har sai mun isheki"..tace"nikam ba wani dadin baki da zakuyi min dan bazan taba yadda ba sai naga kunzo har kd bikina snn zan yadda daku"..Billy tace"u mean an kusa bikinki?.."tace"in the next three months inshaAllah"..Aysha tace"Allah ya kaimu ya sanya alkhairi...amma besty bai ta6a fada mana ba wlh"..Billy tace"shine nima nake mamaki ai..koda yake kadan knn daga aikin Sa'eed"...nan kuma hiran nasu gaba daya ya koma kan bikin Lubna da irin shirye shiryen da zasuyi...if u see yanda suka sake da juna suna labari zakayi zaton tasowa sukai tare tun kuruciya nan kuwa basu dade da sani juna ba shima ta dalilin Sa'eed wani lokaci da tazo ta dade a kano ya kaita hostel dinsu shknn suka kulla kawance...basu fito daga dakin ba saida yazo da kanshi yace su fito ya maidasu snn suka fito...sukayi sallama da Mom da Hajia da har yanxu suke parlor...Mom ta basu dambun nama da tayoma Sa'eed da Hajiyarta cikeda wani flask aikam sukaita godia snn suka tafi har Lubna data dage zatayi musu rakiya...kaman yanda ya saba duk ya fita dasu sai ya siya musu kayan kwalama yake maidasu yauma haka ya tsaya a grand square ya sai musu su chocolates da sweets snn yayi dropping nasu a hostel su kuma suka koma tareda Lubna.

Washegari Thursday suna zaune a premesis kafin time din shiga exam dinsu yayi motan Proprietor ya shigo makarantan...Ayshata wani hade rai dan tana gani ta gane motanshi ne...ko gama parking motan baiyi ba securities da some of staff da sukaga shigowanshi sukayi inda motan yake kaman yanda suka saba...tana daga zaune tana ganin yanda suka bude mishi kofa ya fito sunata wani washe mashi baki hadda masu risinawa suna gaisheshi kaman wani ubansu...Billy ce ta fara lurada ita sai tace"are you okay?.."ta saki wani tsaki tana fadin"mutanen can ne suke bani haushi wlh...dubi yanda sukema inyamurin mutumin can kaman zasuyi mishi sujada...kawai dan mutum nada kudi sai kuyita kaskantar da kanku a wurinshi da yawa daga cikinsu mafa sun girmeshi"..girgiza kai Billy tayi tace"to ke ina ruwanki...kuma an fada maki ba inyamuri bane har yanxu kin ki yadda koh?.."ta maka mata wani harara tace"wai wnn mutumin zaki kalla kice ba inyamuri bane haba Billy.."Sa'eed daketa sauraronsu yace"da gaske ba igbo bane shi besty..ance dai Mom dinshi igbo ce amma babanshi bafulatani ne fa"...da sauri Billy tace"tell her...bafulatanin ma kuma dan garinku"...da sauri ta daga kai tana kallonta tace"what do u mean?."Billy tace"ina nufin dan Gombe ne shi mana"...tun kafin ta rufe vaki tayi spitting tana binta da wani disgusting look tace"God forbid...how could such a heartless person come from Gombe?..gaskia i doubt that kilan dai bakuji daidai ba...and wether u accept it or not mutumin can inyamuri ne kuma na tabbata yana daga cikin masu assasa yakin Biafra sbd tsabar mugun halinshi"...daria suka sa mata gaba dayansu aikuwa ta cika tayi fam har ta mike zata bar wurin Billy ta janyota da sauri tace"to shikenan Sa'ees tell her mun yadda inyamuri ne shi"..da sauri yace"eh mana kuma a cikin inyamuran ma yana daya daga cikin masu assasa yakin Biafra so are we good now?.."murguda musu baki tayi tana hararansu...ganin time din exam ya gabato duk suka mike zuwa classes dinsu.

Karfe biyu da wani abu ya daukesu suka tafi lalle kaman yanda suka tsara...Lubna ce tace tasan wani gidan lalle a Na'ibawa sun iya lalle sosai dan haka kai tsaye can ya nufa dasu.

Basu suka baro gidan lallen ba sai after six kowacce da rangadeden lallenta mai kyau har Lubna da tace bazatayi zuwan banza ba dan haka dole akayi mata itama...tun da suka fito yake yabon lallen nasu amma wai na bestynshi yafi kyau...Lubna tace"Yaya wnn dai son zuciyarka ka fada gaskia"..Billy tace"ai kadan ma kika gani daga aikin Sa'eed"...Lamido dai dariya take sai kuma ta dan rausaya kai tana dubanshi tace"yanxu besty hostel zamu koma knn?.."yace"eh mana you guys have exams tomorrow "..tace" mun riga mun gama karatu wlh besty dan Allah ka kaimu yawo kaji"...ya dan harareta yace"wani wai kun gama karatu sai kace yin karatun kike"...tace"nidai dan Allah muje yawo pllss ko Billy "..dagowa tayi ta watsa mata harara yace" then we are definitely going back to hostel tunda hajia Bilkisu bata yadda ba"...da sauri Lubna tace"Billy kice kin yadda plss"...kmr bazata ce komai ba sai can tace"shikenan amma we won't stay long"..Aysha tace"hakanma mune da godia hajia bilkisu"...daria kawai Sa'eed yayi yace"to ina zamuje yanxu?.."da sauri Aysha tace"mu fara zuwa mudassir da akwai veils da nakeson siya"..yace"besty da shopping"...tace"ba haka bane besty kaga ko ban siya a nan dole ina sauka Gombe inje in siya kasan fa gobe ne kamun adda ruky"..jinjina kai kawai yayi sarai yasan halin kayarshi da shegen son biki...suna isa mudassir din gaba daya suka fita zuwa ciki...ta kwashi veils wajen guda four snn ta dauki shoe da bag...Billy ma ta dauki nata sai Lubna da suka tilasta mata ta dauki mayafi itama...sunzo wajen biyan kudi Aysha ta mika card dinta..Sa'eed ya watsa mata wani kallo yace"and what's that?.."tace"besty kullum fa kai kake biya yau daya dai ka bari na biya plss"..bai sake ce mata komai ba ya amsa card dinta daga hannun mutumin snn ya bashi nashi...ana gama cire kudin suka fita daga wurin rikeda ledojin kayan da suka siya...daga nan Chicken Republic suka wuce suka samu table suka zauna snn aka kawo musu menu kowa yayi ordern abinda yakeso...suna nan zaune kafin a kawo abincin sukaji sallama kusa dasu gaba daya suka juya inda sukaji sallaman...wani mutumi ne da akalla zaikai iri 50 to above yana nuna empty seat dake wurin yace"may i?.."Sa'eed ne yace mishi"Bismillah"...a hankali yaja kujeran ya zauna snn ya mikama Sa'eed hannu suka gaisa yace"sorry i interrupt you guys...wlh tun daga kabuga na biyoku har nan wajen"...mamaki sosai ya bayyana a fuskokinsu jin tun daga kabuga yake binsu...ganin kallon da suke mishi sai ya saki murmushi ya nuna Aysha da finger dinshi yace"because of her"...wani mamakim ya sake kamasu jin abunda ya fada...shi kuma ya saki murmushi yana duban Sa'eed da yayi tunanin ko yayansu ne yace"can i please talk to her in private?.."shiru Sa'eed yayi ya juya yana kallonta sai yaga tana wani blushing kanta a kasa cikin ranshi yace"dama nasan za'ayi haka wlh..besty da shegen son sugar daddies"...jin har yanxu baiyi mgn ba mutumin ya sake fadin"only 5 minutes plsss"..yaja plss din da har saida ta dago ta kalleshi...a hankali Sa'eed yace"Sure u can"..mutumin yace"thank u so much..you are a life saver"...daga haka ya mike tsaye yana mata wani kallon kasa kasa yace"Ma'am"...batayi mgn ba ta mike tabi bayanshi zuwa wani table a can gefe...da kanshi yaja mata kujera ta zauna snn shima yaja ya zauna yana facing dinta yace"Allah yasa dai banyi laifi ba"...ta danyi murmushi hadi da girgiza mishi kai...shi kuma yayi mata kuri da ido kamab ya samu tv...saida suka hada ido ya sauke wani numfashi tareda cewa"u are very beautiful...shiyasa ina kallonki naji komai nawa ya tsaya..naji bazan iya hakuri ba har saida na biyoki...Allah yasa ban kawo kaina inda za'a wahalar dani ba"...still murmushi ta kara saki tana girgiza kai...yace"my name is professor Ahmad Abdu Kurawa and i think i have fallen for you"...shiru kawai tayi tana kallonshi sai taji ya burgeta sosai...this is exactly why she loves sugar daddies cox they are straight forward ba wani kwana kwana a tsarinsu...snn ga iya handling mace da nuna mata so da kauna...shiyasa duj ta shirya yin aure batada burin da ya wuce ta samu sugar daddynta ta aura yanda zata yita zabga shagwa6a son ranta ana lallashinta...jin batace komai ba ya wani rausaya voice dinshi yace"dan Allah say something plss..wlh i love you..i love you so so so much"...murmushi ta kara saki tana rufe fuska da hannayenta sai ya saki murmushin shima kafin yace"ohk i guess i have to give u some time to think right?.."da sauri ta gyada mishi kai..yace"alright then you take your time...amma plss kiyi min mgn inji sai in tabbatar da banyi zuwan banza ba"...still smiling tace"sunana Aysha Ahmad Lamido"...yana gyada kai yace"your name suits you...dama ina ganinki naji a jikina wnn beautiful soul din must be Aysha..thank you so much Aysha for giving me your time...yanxun zan wuce sbd na bar yaro a mota kema kuma naga 'yan uwanki suna jiranki"..batace komai ba sai murmushi shi kuma ya zaro card dinshi ya ajiye mata yana cewa"ga card dina nan saiki kirani or better still bani number dinki cox i can't the risk of loosing you"...batayi musu ba ta amsa wayanshi tasa number dinta...saida yayi dialing yaga ya shigo snn ya katse tareda mikewa tsaye yana kallonta yace"to ni zan wuce beautiful Aysha..zan kiraki inshaAllah and Allah yasan baza'a bani negative news ba"...tace"inshaAllah"...yace"alright bye"...itama tace mishi"bye"snn ya juya ya fita itama ta mike ta dauki card dinshi daya ajiye ta koma inda suke..Lubna tace"so har kun daidai knn?.."itadai tayi murmushi tareda fara cin abincinta...Billy tace"ai bama saikin tambaya ba Lubna wlh nasan da kyar idan batayi accepting dinshi ba..Lamido da shegen son sugar daddies"...shidai besty yana jinsu baice musu komai ba...suna gamawa suka bar wurin time din dare ya farayi sosai yayi dropping nasu a hostel su kuma suka wuce Tarauni.







Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.












Rano✨






🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

I dedicated this whole page to my darling small mom🥰❤️Hajia Fiddausi Musa Kibia aka Mrs MD aka Maman Mufeed da Mufeedah🥰❤️Ina roqon Allah ya biya maki dukkanin buqatunki na alkhairi Aisha Indo loves u so much🥰❤️


12


Washegari Friday zasuyi final paper na first semester level two knn..zasuyi hutun two weeks snn su tafi clinical posting...tun wajen 7 suka baro hostel zuwa cikin makaranta..daga ita har Billy murna suke zasuje gida dan ko weekend sun kwana biyu basu je ba...kafin time din exam yayi provost ya kira wayanta yace tazo yanason ganinta...babu wasting of time kuwa taje office dinshi yace list din yan class dinsu yakeso ta bashi yanxun nan...ta juya zata fita ya dawo da ita ya mika mata pen da paper yace ta zauna nan ta rubutasu yasan zata iya tunda ba wani yawa garesu ba...ba musu ta amsa ta zauna ta fara rubutawa shi kuma Nur yacigaba da aiki a Laptop dinshi...a hankali Bobby ya turo office din ya shigo...idanuwanshi basu sauka ko inaba sai hannun Lamido da lallenta yayi wani moroon yanata shinning abunka da farar fata...ranshi yaji ya 6aci sosai like how dare this girl apply henna a hannunta bayan tasan baya cikin ethics... har ya karaso cikin parlon basu sani ba sai kawai sukaji yace"keh.."a gigice ta dago tana kallonshi..fuskan na sarari yace"bakuyi professional ethics bane?.."voice dinta na dan cracking tace"mun...yi"yace"then why did you apply this rubbish a hannunki?.."tayi shiru kanta kasa tana 6oye hannunta...Nur dake kallon abokin nashi da mamaki yace"C'mon Bobby ni banga wani abu anan ba..maybe kafin su tafi clinical posting ya baje so relax "...a fusace ya juya yana kallonshi yace" amma kai kanka kasan duk wayan nan abubuwan is prohibited a profession dinta koba a clinical area bane"...shiru kawai Nur yayi yana kallonshi..baisan why he easily gets angry when it comes to her ba..he remember yanda yayi acting ranan da sukaje hostel...ita kuwa Aysha daure fuskanta tayi tana dan turo baki har yanxun kanta kasa dan ko a mafarki batason sake hada idanu dashi...(note:nasan wayansunku will be like ya zaayi a hanata yin lalle sai kace a secondary school..well duk wanda yayi health institution yasan banbancinsu da secondary school dan kadan ne coz sunada strict dokoki snn kuma akwai ethics so ba yanda zaayi mutum yazo yana yin anyhow a irin wnn makarantun sbd suna dealing da lives of many people..da akwai rules da dole mutum sai yabi while in school ko kuma clinical area..na farko dai applying lalle is prohibited especially during clinical posting..snn ba'a

Please Login or Register in order to submit comment