Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ


๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป




๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“šโœ๏ธ._*
[โ„Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]




*_STORY & WRITTEN_*
*By*

*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ



*_Da sunan Allah mai rahama nake fara wan'nan book din Allah yasa abin da zan fada a wan'nan littafin ya f'adakar da kuma nisha'dan'tarwa sai fa kunyi hkr dan sabon shiga ce_.*๐Ÿ˜„



*Dedicated to Sady baby*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ


*Wannan page din na kine my friend ๐Ÿ˜™๐Ÿ˜™ kiyi yanda kike so da shi.*



*_DONT 4GT TO VOTE,COMMENT AND ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @ AboriginalWrtersAsso._*




```Bismillahir rahmanir rahim```



2019 publishe.
*Page* 1โƒฃ



"Hameeda dan Allah ki tashi mu tapi kin san yaya Yazeed baya san jira ko, "

"Kai keko fadila kin cika naci mutum be gama shi'ryawa bane zai fita shima Yaya Yazeed din da kike mgn ai sai da ya shirya san'nan ya fito to Allah sai na."


"Gama hmmmm lallai hameeda kin raina yay Yazeed ."

"way kuko baza ku fito ba kowa ya shirya amma ku kuna Nan kuna wan'nan kwalliyar banza."

" Yauwa momy gwara da kika zo ni na shirya hameeda ce bata gama ba ."

"Kai hameeda maza tashi ku tapi momy."

" Sauran kadan fa".

" Allah ranki zai baci."

"to momy nagama."


" To sai kun dawo."

Mikewa tayi ta dau gyalan ta ta yafa suka fita .

suna fita sukaga duk Yan matan gidan nasu kowa yaci kwalliyya kaman Wanda za'aje kasan sarauniyar kyau.

Yaya Yazeed ne yace.

" ku sai yanxu kuka ga daman fitowa?"

Fadila tace " yaya dan Allah kayi hakuri".

yace .

"kowa ya huce ya hau mota".

Hameeda kon ko kallo ma be isheta ba.

Yaya Yazeed yace.

" Ke"

kowa ya juyo ita ko tapiya ma tacigaba dayi .

saida ya qara cewa

"Ke".

Sai Saudat tace .

"Aunty Hameeda da kefa Yaya Yazeed yake".

Cikin fusata Hameeda tace .


"To ni ke ne sunana ko hameeda".


Cikin b'acin rai yaya Yazeed yace .


"Wato kin San ma dake nake ko ,to wacce motan zaki hau ba wan'nan ba."


Tace " Lallai motan ma Sai an gaya min wace zan hau, naga dai mutum bashi ya siya ba."

Ta fada tana mur guda baki.

Yaya Yazeed yace .

"Ni kike fadawa haka to baki isa ki hau ko wace mota ba sai wan'nan sai dai in ki fasa zuwa."

Cikin masifa tace .

" Akwai wallahi bazan hau motan ka ba."

Kowa ya huce ya shiga mota ban da Hameeda.


Fadila tace " Hameeda dan Allah kije ki hau motan".

"Fadila wallahi bazan hau motan shi ba".

Fadila tace .

" hmmm ke dadi na dake saurin fushi indai Yaya Yazeed ne ai kon saba ta fada tana dry,

mtswww Allah ya kyauta muku."


" Nusaiba kenan ke kuma wayasa bakin ki ban sani ba hmmm wallahi yanzun zan basa ma yariya baki"

inji Nusaiba

"haba dan Allah ke kulum in ba'ayi rigima ba baki Jin dadi Ina ruwanki da mgn mu."

"Da ruwa na fadila barta wallahi ta min ne yanxu zata gayama jikin ta dan ta sanni sarai".

" wai me kuke jira ne?"

cewar Aunty talatu

Bakomi Aunty yanxu zamu wuce".

"To a dawo lfy ".

Kowa ya shiga mota Amma Hameeda take shiga ta Kai wajan motar su Yaya Areef, taji yay Yazeed na cewa

" Allah hameeda kika shiga sai kin sani waye."


Hameeda tace .

" Ina ruwan mutum na ne da ni."

ta fada a zuciyar ta

" kizo ki huce to ".

Yaya Yazeed ya fada.

"naji".

hakan nan dai ta hau suka dau hanya daman motan daga ita sai Nusaiba to ba shiri suke ba shiyasa ba Wanda yayi mgn har suka kai wani hall din party.

daman bikin abokin Yaya Yazeed din ake to shine yace dik Y'an matan gidan da samari su shirya su tapi.

suna zuwa kuwa kowa ya fito aka fara shiga Amma yay Yazeed ko Alamar fitowa baiyi ba, kuma bai bude musu ba.

Nusaiba tace "Yaya Yazeed kowa ya tapi fa".

yace

"To rike ke nayi ne".

Tace " A'a naga baka bude bane ".

Tsaki kawai yayi ya bude mata ita kon Hameeda ko kala Bata ce mai ba ta fita .

Suna fita fadila tazo suka wuce tare.

Suna shiga gurin kallo ya koma kansu barin ma Hameeda.

Ai kam Nusaiba ta hada rai kamar bata taba dariya ba.










*in kuna so a cigaba ba to zanga comment*.





*Comment*
*Share*
*vote*





*Aunty Baby ce*โœ๐Ÿผ

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ



๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป




๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(ฦณAN ASALI)๐Ÿ“šโœ๏ธ._*
[โ„Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]




*STORY & WRITTEN*
*BY*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ



*Dedicated to my family*๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜


*_DONT 4GT TO VOTECOMMENT AND ALSO FOLLOW US ON OUR WATTAPD @AboriginalWrtersAsso._*





```Bismillahir rahmanir rahim```


2019
*Page* 2โƒฃ


Nusaiba ta hada rai.
Ita kuwa Hameeda ma Bata San tanayi ba.

Hameeda tace , " Fadila nifa ban San kallo wallahi , jiba sai kace sunga wani abu."


Fadila dai murmurshi kawai tayi har suka qarasa wajan ango da amarya.

Angon yace,


" ai nayi fushi sai yanxu zaku zo."


Fadila tace, "Kai Yaya Safwan ai munzo da wuri ma".

Yace "Ina shi my friend din"?

Fadila tace, "gashin zuwa".


Hameeda tace, " Amarya ya kike?."

Sadiya amarya tace,

"lfy lau sai yanxu zaku zo ko".

Hameeda tace, " hmmm da kika samu ma muka zo, bari muje mu zauna".

samun wani gurin da ba maza suka zauna.

Fadila ta fito da wayan ta tace,

"sis bari in mana pic".

Suna cikin pic kawai sai ga wani guy ya zauna gujeran dake kallon Hameeda.

ita kuwa Bata ma san da zaman shi ba hoton su kawai suke.

sai can Saurayin yace,

" haba 'yan mata ba mgn ya kuke"?

Fadila ce kawai tace,

"lfy"

Yace, "wai baki mgn ne"?

ya nuna Hameeda.


duk da haka ko kallo shi din batayi ba .

Yaya Yazeed ne sai da yagama cin maganin shi sai gashi ya shigo.


y'an Mata gurin kon suka rude kowa sai gyara fuska da gyale ake shiko ya qara hada fuska har ya qara sa gun angon.

Angon yace " yeah my friend nayi fushi ace biki na San yanxu zaka zo?"

Yaya Yazeeda yace .

"oh sorry abokina".


Angon yace " hmmm to ya".

Mc ne ya fara sanarwa ga babban abokin ango nan nafa aka fara sakin kida yan'mata da samari aka fara chashewa ana zuba liqi.

Mc yace Amarya da Ango su fito, Nanfa aka fara liqi .

Yaya Yazeed ma ya fito ya fara liqi har Ango da Amarya suka koma aka sa wakar Wizkid ta fever .

Daman Hameeda nasan wakar, nan kowa ta fito tana rawa.

kamar ance Yazeed dago ya ganta ana ta zuba Mata kudi, ita kuwa sai rawa take.

Daman Hameeda da rawa hmmmm ba'a mgn.

Baisan lkc da yaje ya figeta ba tana kwa'cewa ya dalla Mata mari.

Aikuwa taji Marin nan.


Cikin b'acin rai ya yace .

" Wato ke iskanci da kike yi ne yau zaki mana ko, wacce yariya kikaga tana rawa a gidan mu? banza Yar iska".

Cikin tsiwa Hameeda tace .


" Ni wallahi ba yar iska bace, kuma sai na qara yin rawan dan baka isa ka hanani abun da nayi niya ba".

Wani marin ya qara mata .

yaya Areef da yaga fitowan su yace.

" Haba Yaya Yazeed yau daya dan tayi rawa ai ba wani abun bane...."

Wani kallo da yayi masa ya Hana sa qarasawa .

Wuce ki shiga mota .

"Ba inda zani tunda dai ba kafan ka bane, ka takura min ka tsaneni mai na tare ma."

tana fada tana kuka๐Ÿ˜ญ

janta yayi da karfi Wanda har sai da ta yarda jakarta, yasa ta a mota .

shiko Yaya Areef kallon ikon Allah kawai yake .

ya figi motan da gudu be tsaya ku Ina ba sai bakin gate din gidan.

horn yayi mai gate man din yayi saurin budewa ana bude mai ya huce ko gaisawan da suke da get man din bai tsaya ba.

ya bude ya fito yace.

" fitar min a mota".

Hameeda kuwa tana fitowa tace.

" motar banza motar wofi ai daman Kai ka sani ba Ni na shiga ba mtswwww ".

tayi hucewar ta.

galala Yaya Yazeed ke kallonta yace .

"Lailai yarinyar nan ta manta koni waye".

Hameeda tana barin wajan part din su ta wuce, tana shiga parlour momy tace.

" Hameeda har kun dawo ne'?

" Eh momy".

kawai tace ta huce dakinta.


Magana take tana fadin.

" Wai Ni Hameeda Yaya Yazeed zai yiwa haka, hmmmm wallahi sai yayi daya sani kuma rawa yanxu na fara tana cire kaya tana fada.

(niko nace mai yasa bakiyi a gaban shi ba ๐Ÿคฃ)

tana gamawa ta fito parlour momy tace.

" Hameeda yanxu yayan ku Yazeed ya zo wai kije ki kaimai abincin shi ."


Hameeda tace "Kai momy daga dawowar mu , shifa wannan yaya Yazeed din ya cika sa mutum aiki ."

"Hameeda yanxu Kai abincin ne aiki"?

cewar momy

" Wallahi ke da shi ba ruwana"

"To momy yanxu fa muka dawo ko hutawa ba muyi ba ."


Momy tace " Hameeda baza ki wuce ba".

" To momy ".

kitchen ta huce ta fara hadamai tana masifa.

" wai shi mutum saikace ni daya ce a gidan yabi ya takura min .

tana cikin hadawa ne taji Fadila na mgn da momy saiga ma .

Fadila tace " hehehe ๐Ÿ˜ˆ qanwar Yaya Yazeed ya aka riga mu dawowa tana fada tana dryn shaqiyanci".


Hameeda tace " oho ban sani ba banza kawai Ni ki daina hadani da wannan mutumin."

fadila tace " wai wa kike hadama abincin ne?"

Hameeda tace "wannan yayan naku mana".

Fadila tace " wanne kenan kinsan suna da yawa "?


Hameeda tace "Yaya Yazeed mana wai in hadamai abincin kinji gulma fa."

Fadila tace" hmmm kije ki kaimai kafin ya fara masifar shi".

Hameeda daukan tire din tayi ta nufi part din Yaya Yazeed din .

tana zuwa ko salama ta shigewar ta d'akin.

Yana zaune akan kujera ya daura kafan shi zaman tebir din dakin laptop dinshi yake dannawa.

Abincin kawai ta ajiye zata fita yace

"Ke"

tsayawa kawai tayi Bata juyo ba.

yace "baki iya sallama bane".
Cikin rainin hankali tace .

"oh namanta".

Cikin fusata yace .


"dan ubanki sallama ce kika manta yau zaki gane bana wasa dake".



Cikin b'acin rai ya Mike ya nufi inda take.









To komai Yaya Yazeed zaima Hameeda ๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”





*Mu hadu a next page*๐Ÿค




*Aunty baby*โœ๐Ÿผ

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ


๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป




๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*๐Ÿ“šโœ๐Ÿผ.

[โ„ Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]


_*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT AND FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersaAsso._*




*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ


*Dedicated to SAUDALA fan's group*๐Ÿ˜Š

*gaskiya naji dad'in comment din ku Allah yabar kauna ina yinku irin over din na*. ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

*Bismillahir rahmanir rahim*


2019 Published.
*page* 3โƒฃ





Cikin 'bacin rai ya Mi'ke ya nufi inda take Yace ,


"Ke Hameeda dan kan uwarki Ni sa'an ki ne? dik gidan nan wa kika ga Ina wasa da shi"?


Hameeda tace, " oho tambaya ta kake ko mai, nifa gaskiya ka takura min haka kawai.... "


Yaya Yazeed kallonta kawai yake, shi besan mai yasa yanxu baya ma Hameeda hukunci ba ko yayi niyar zaneta sai yaji ya kasa Amma in be Zane yariyar nan ba baza ta saitu ba.


juyawa yayi bayan shi kawai yaga wata wayan canji, d'auka yayi ya nufo ta.


Hameeda kuwa tana gani ya d'au abin duka ta fara zare ido dan tasan bashi da wasa wajan duka .


tace, " Yaya Yazeed dan Allah kayi hakuri wallahi bazan qara ba".

Yaya Yazeed yace,

"lallai kin Raina min wayo ai yau sai kinji a jikin ki ."


yayo kanta kuwa ta fasa ihu tana fad'in,

"wayyo Allah jama'a Yaya Yazeed zai kashe ni"


"Ke dalla ki rufe min baki ubanki na miki".

Aunty Talatu dake wajan window d'akin taji ihun Hameeda tace,


" Hameeda! Hameeda! Lpy? "

Hameeda taji kaman ana magana hakan yasa tako q'ara ihun.


Aunty Talatu ta sake cewa, "wai lfy kuwa kina tama mutane ihu Hameeda"?


Tace, "ba Yaya Yazeed bane zai dakeni"


Aunty Talatu tace, "Haba Yazeed mai tamaka kai kuwa"?


ko kallo Aunty Talatu baiyi ba ya wuce bedroom Yana 'kwafa.


Hameeda kuwa da tasamu bai ta'ba lafiyan jikin ta ba ta fito d'akin tana Allah ya isa.


Aunty Talatu tace, "wai mai kike mai ne, kinsan Yazeed ba ha'kuri gare shi ba."


" ba fa komai na masa ba"


Hameeda tace ta wuce, tana zuwa d'aki
Momy tace mata,

"ke kuma daga Kai abinci saiki nemi wuri ki zauna?"


" Momy sani yayi na gyara masa d'aki"

"OK"

kawai momy tace da ita.


Nusaiba ce ta shigo d'akin tana wani bata rai .

Tace ,

"ke Hameeda Haj Jadda na Kiran ki"


Hameeda tace, "naji"


"Momy bari inje wai Jadda na kira na"


"to Hameeda in zaki dawo kije gun Auntyn ku Amarya kice ta baki kayan dan jiya na siyan muka less ke da Fadila da Nusaiba"


"yeeeee Momyna kenan Allah ya amfana, Amma Momy mai yasa kika siya da Nusaiba kinsan dai Mamanta ba so take ba ko"


"Haba Hameeda ke har yanxu baki hankali ba, yanxu kawai sai in siyan miki abu inki siyan ma Yan uwanki"


" to Momy mai yasa baki siyan ma Saudat ba naga dai ita ce ma 'yarki, Amma ki ba mutum abu ba godi bare nagode.. "


"to Hameeda maiye rayuwan in shi be gode ma ba ai Allah nagani ko "?

"hmmmmmm Momyna kenan Allah ya barmun ke " ,

"maza kije K'iran da ake miki kinsan halin Jadda dai"

" to Momy "

fita tayi a d'akin taje Kiran Jadda, daman ba nisa gare su ba.


part biyu ne tsakanin su daga na Aunty Amarya sai na Maman su Nusaiba.

tana shiga Jadda tace,


"sai yanxu kikaga daman zuwa gimbiya.."


Hameeda batace Mata komai ba kawai tace,

" Ina wuni"

"lfy" kawai Jadda ta amsa.


" daman na kiraki ne in fad'a miki gobe ubanku zai dawo sai ki fad'awa uwarki dan asiri ya karye sai abi wani bokan."


sororo Kawai Hameeda tayi tana jinta _asiri_ ta 'ฦ™ara maimaitawa _lallai ma Jadda nan.._


"hmmm Jadda kenan ai asirin ma matsayi ne wata dik abinta Bata isa tayi asirin ba kuma yaci....... "


"Laaa Haj Jadda kike fad'awa magana, lallai Hameeda kin riฦ™a"


cewar Maman Nusaiba da zuwan ta kenan tayi maganar .



To fa wan'nan gida nasu Hameeda ya yake ne?๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”

*Sai mun had'u a page nagaba muji yadda wan'nan cakwakiyar zata kasance*.








*comment*
*vote*
*share*





Aunty Babyโœ๐Ÿผ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ

๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป



ยฎ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*๐Ÿ“šโœ๐Ÿผ

[โ„Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]



_*DON'T 4GET TO VOTE, & COMMENT FOLLOW US ON WATTPAD @*_
_*AboriginalWrtersAsso.*_




*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ



*Dedicated to BABU SHI A ZUCIYATA FANS GRP*.๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ




*Bismillahir rahmanir rahim*



2019 published.
*page* 4โƒฃ




"Barta-barta Hajara ai tasha a nono"

cewar Haj Jadda.


Ita kuwa Hameeda tana tsaye ko motsi takasa dan halin Haj Jadda inda sabo tasa ba dashi kaman ba ita ta haifi ubanta ba.


kwata-kwata Bata sonta sabda kawai da aka haifi Hameeda ba'a sa mata sunan taba shine ta ษ—au Karan tsana ta d'aura mata.


duk abinda Hameeda zatayi bata birgeta shiyasa itama bata wani shiga harkarta.abinda ke gabanta uwarta, bata son rashin mutuncin da take mata sam duk kuwa da irin abinda Mommy ke mata bata gani.


"Au tsayawa kike akan mutane shegiya mai halin dagin uwa,toko dukanmu zaki ne"


"Ai wallahi gwara da halin dagin uwata nayi banyi naki ba"


Hameeda na fad'ar haka tayi tapiyar ta .



"Haj wallahi yariyar nan Bata da kunya yanxu harke zata dinga gayawa mgn"


cewar Naman Nusaiba.


"Ai barta Yusuf d'in ya dawo, zata san dawa tayi ".


Hameeda kuwa tana fita part d'insu ta wuce ,kota kayan da Momy tace ta amso banta biba.



*WACECE HAMEEDA ?*


Hameeda dai 'yace ga Alh Yusuf, Alh Yusuf su uku ne a d'akin su, Alh Ahmad shine babba sai Alh Yusuf sai kuma autan su Alh Abubakar dika Haj Jadda ce ta haife su.



Mahaifinsu ya daษ—e da rasuwa tin Abubakar Yana shekara 5, daga nan Haj Jadda ta d'au nauyin karatun su har suka gama Allah yasa suka samu wani abu a duniya dan Alh Ahmad babban d'an kasuwa ne shiko Alh Yusuf ma'akacin Gomnati ne .



Alh Abubakar ma dai d'an kasuwa ne,Alh Ahmad ne ya fara yin aure ya auri yariyar mai gidan shi bayan shekara 5 Allah be basu haihuwa ba Nan fa Haj Jadda ta fara masifa saidai yayi aure ba'afi wata ba da zance Allah ya bata ciki nan fa ake ta murna har Allah ya sauke ta lfy ta samu namiji mai suna Yazeed tin daga Nan Bata qara haihuwa ba har Alh Yusuf yayi aure ya Sami mata mai suna Hajara.



Hajara na shekara ta haihu itama namiji ta samu aka samai Areef tin daga nan Haj Jadda ta 'Kulla da Hajara Bata da abokin shawara sai ita daga Areef sai shamsiya sai kuma Nafisat shima Alh Abubakar Allah ya had'a shi da wata Ameena.



Aunty amarya a shekaran kuma Alh Yusuf yace zai ฦ™ara aure lokacin Hajara tana da cikin Nusaiba haba Nan fa Hajara tace Bata San zance ba shikuma yace sai yayi da da farko Haj jadda ta Hana sai daga baya kuma tace yayi ba komai ai kon rana d'aya aka d'aura musu aure shi da Abubakar amare sun tare lfy .


Shekaran su d'aya suka haihu Ameena ta haifi ฦดarta Fadila, ita kuma Zainab Momy ta haifi ฦดarta Hameeda.



Haj Jadda taso asa sunan ta ne sai kuma aka sa sunan yayan Momyn data rasu hakan yasa Haj Jadda ta tsani Momy kenan.



*Cigaban labari.*




Pls in nayi kuskure ku min afuwa kunsan Ni din sabon shiga ce kuma Dan adam 9 yake bai cika goma ba barin mu sabon shiga . Allah ya barmun tare ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜





*Comment*
*vote*
*share*






Aunty Babyโœ๐Ÿผ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ


๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป



๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION_*๐Ÿ“šโœ๐Ÿผ

[โ„Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersAsso._*





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ





_A gaskiya zan daina rubutun litafin nan sbd ba'a comment ko litafin ne be muku dadi to ban sani ba in be muku dadi ne gwara tin wuri in sani in daina Bata lkc Ina yi kunsan dai yanda typing yake kuma muna da abinyi pls in baku so to in sani in daina bata lkc na_ ๐Ÿ™‚๐Ÿคจ



*Bismillahir rahmanir rahim*



*page* 5โƒฃ



Hameeda ce sanye da uniform din makaranta riga da wando sai karamin hijab kayan son Mata kyau sosai dan Hameeda fara ce tana da dan tsawo kadan Bata da Kiba sosai .


"Momy Ni na tafi kin San yau zamu fara test".
cewar Hameeda kenan

Momy tace "to Hameeda Allah ya taimaka, san'nan ki fara zuwa part din Haj jadda ki gaisheta sannan sai ki huce kin San yau daddyn ku zai dawo ".

Hameeda tace "Kai Momy kin San fa nayi lati kuma su fadila na jirana Kar in Bata musu lkc ki bari in na dawo pls Momy ".


"To shikenan A dawo lfy ".

"To Ameen Momyn na ".



Tana fita kuwa taci karo da Fadila ta biyo Mata su wuce .


"A Fadila da yanxu zanje part dinku ashe kin taho ".

Fadila tace "Eh wallahi Hameeda kin San yau zamu fara test Kar ya hanamu shiga Sir haidar ".



Hameeda tace" hhhhh wallahi bai isa ya Hana mu shiga ba tinda dai my uncle Hamed na nan ".

Suna fitowa bakin Gate din gidan sai ga Yaya Areef Nan yace to su shiga ya Kai ku.

Hameeda tace " Yaya Areef Kai da zaka tapi office kawai ka bari mu tapi karmu saka lati ".


Yay Areef " yace ku wuce ku shiga kun tsaya min surutun ku ".


To kawai suka ce suka shiga


Minti 10 ne ya kaisu dan basu da wani nisa da school din
Yana sauke su suka wuce .


Hameeda sai zabga murmushi take .


Fadila ce ta zungureta tana f'adin,

" ke Hameeda Allah ya shirye ki yanxu zaki je ki hadu da uncle Hamed ko kuma kin San test zamu shiga Allah yasa ma bai zo ba".

ta fada tana dariya

Hameeda tace " aniyarki ta biki kin san da in banga uncle Hamed ba Allah bazan iya rubuta komai ba.......".

Muryar da tajine ya hanata qarasawa . k'yakyawan saurayine ajin farkon dan gayu fari tas da shi .

" sarauniyata ".

ya qara fada a qaro na biyu

Wani murmushi Hameeda ta sakin mai tana cewa ,

"my uncle Hamed ".

Yace "Na'am sarauniyar kyawawa kin tashi lfy? da fatan dai kina cikin koshin lfy dan wallahi jiya kadai da banganki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment