Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

walwalla.


Daddy yace "my son ya naganka haka ko baka da lfy ne? "


yaya Yazeed yace " A'a Daddy lfy na kalau Ina kwana. "


Daddy ya amsa ya gaisher da meme ma.



tace "ga abincin shi can kan dining."



yay Yazeed yace " shi ya koshi Dan Sai da ya fara zuwa part din Abbu tukun na".


Meme tace " to badamuwa."


Dan ta San Momy nasan yay Yazeed sosai tin yana yaron shi...



Yace "Ni zan huce asbiti dan Ina da patient da yawa."


Duk suka mai Allah ya tsare ya kare..


Ya tashi ya tafi.













*comment*
*vote*
*share*






*Aunty baby ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_




*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻



*Dedicated to my besty Maryam Ahmad😍😍😍 qawar amana*





*page* 1⃣2⃣to1⃣3⃣



*Bismillahir rahmair rahim*






Ya tashi ya tafi



Yana zuwa asbiti, office ɗin shi ya wuce dan yau kanshi a kulle ya ke, Ina zai samo matar aure nan da sati uku?

Wayan shi ne yayi ringing banza yayi da ita sai da aka yi 3miss call sannan ya ɗauka ko duba wake Kira beyi ba yace.


"hello,"


Safwan yace , "haba abokina kwana biyu shuru tindaka biki fa Ina ka shige ne."



Yaya Yazeed yace , "lfy lau na barka ne ka gama cin amarci sai yau ma zaka tina da ni".




Safwan yace, " haba abokina Wallahi ba haka bane, Wai ya naji muryanka kaman kana cikin damuwa lfy dai ko ?".

Yaya Yazeed ya nisa sannan yace,

" Wallahi Safwan Ina cikin tashin hankali Abbu yace in fito da matar aure nan da sati uku sanin kai ka ne ko budurwa Banda ita, Wallahi Kaina ya kulle bansan yanda zanyi ba."

Safwan yace , "tab abokina matar aure nan da sati uku lallai kana cikin tsaka mai wuya. Amma ga shawara."


Yaya Yazeed yace, " Ina jinka ".



Safwan yace , " Ina Ameera class mate dinmu daman tana sanka kawai kaje ku sa santa dan Wallahi Ameera ba karamin so take maka ba ".


"Lallai Safwan baka da hankali wannan yariyar zan aura tab to ai gwara in jira su aura min duk wacce tai musu da dai in aura Ameera."



Safwan yace, " to ga Yasmeen wace kullum sai tamin mgn ka tana sanka sosai Wallahi har biki na fa ta zo dan ku hadu Amma bata ganka ba, "


Yaya Yazeed yace, " to ai gwara in aura Ameera da Yasmeen, kai baka da anfani Wallahi Ni fa yariya mai hankali nake so bawai irin Yan matan da kake mgn ba."



Safwan yace, " to shikenan ka zauna kawai su Abbu su zaɓa ma Mata dan Ni na gaji duk wacce na faɗama kace Bata maka ba sai ka jira a baka ƴar qauye dan naga hakan kake so." Yana gama fadan haka ya kashe wayan shi



Yaya Yazeed yace, " oho ma ni ina son mace mai Adini kana faɗa min wa'inda sallah ma bata damai su ba "

ya daura kanshi a gujeran office ɗin ya cigaba da tinanin shi...


Maman Nusaiba ce zaune a kan bed ɗin ta tana tinanin yanda za'a yi ta jawo hankalin Nusaiba ta so yay Yazeed dan Wallahi baza ta ga samu taga rashi ba ai dole ma Nusaiba ta yarda ta aura Yazeed tana cikin wannan tinanin ne Abbu ya shigo.


"Wai tinanin mai kike ne ina ta sallama hankalin ki na wani waje?".

cewan Abbu kenan yana zama bakin gadon da take .


Maman Nusaiba tace,

" Ah, Alh yaushe ka shigo banji sallaman ka ba? ".

Abbu yace , "Ina zaki ji sallama na kuwa kina can kina tinani ".


Maman Nusaiba tace,

" hmmmm Alh daman Wallahi Ina son mgn da Kai... "

Abbu yace Ina jinki


Maman Nusaiba tace,

" hmmmm ban San dai yanda zaka duba mgn ba Amma dai nasan kowa zaiji dadin wannan hadin daman Nusaiba ce da Yazeed naga ya dace a hada su aure ."


tana fada tana satar kallon shi taga yanda fuskan shi ko ya canja ko kuma Amma taga be canja ba sai kawai ta cigaba da mgn ,

"Alh ya naji kayi shuru......."





_Allah ba dan halin ku ba yasa nake muka typing shiyasa nima yanxu ba kullum zaku dinga jina ba_










*comment*
*vote*
*share*







Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺


💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai ɓata,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_






*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻





*Dedicated to my family ❤️❤️❤️ and my brother hamoudi🥰*




*page* 1⃣4⃣to1⃣5⃣




*Bismillahir rahmair rahim*





Tace Alh ya naji kayi shuru.


Abbu yace, '" Ina jinki. Lallai Hajara baki da tinani yanxu Yazeed ne zaki ce zai aura Nusaiba ko to ban yarda ba ke daman kin iya San kan ki",


Yana cikin mgn ne yaji wayan shi na ƙara ɗauka yayi yace "hello."

Abba ne baban su Fadila yace "Yaya Haj Jadda ce take neman mu ga big Daddy shima ya zo shine nace ai baka fita ba ko.?"

Abbu yace "eh ban fita ba gani Nan zuwa."


Abbu ya kalli Maman Nusaiba wacce ta hada rai ta cika fam kaman zata fashe yace,

" Wallahi daga yau na ƙara Jin mgn Nan a bakin ki sai kin sani tinda ke baki da tinani ... "


Yana gama fadar haka yayi huce war shi.


Maman Nusaiba tace" Wallahi ko ta boka 👹 sai Yazeed ya aura Nusaiba dayake ba Sona yake ba shiyasa baya san ƙaruwar mu to aure ne kaman anyi shi",


tana ta fadan ta dai ita ɗaya...


Abbu kon Yana zuwa part ɗin Haj Jadda ya samai su duk a zaune ya gaisher da Haj Jadda sannan ya zauna shima yace "Abubakar Ina batan dai lfy. ?"



Abba yace , "lfy lau daman kan mgn yaran nan ne shine big Daddy ya yanke hukunci ."


Abbu yace , "to Allah yasa alkairi ina ji ".


Big Daddy yace, " na yanke hukunci Areef zai aure Fadila sannan kuma Yazeed zai aure Hameeda sai Nusaiba kuma yaron abokina Nabil,Ba Wanda ya isa ya fasa wannan abu da nasa ".


Haj Jadda tace, " A lallai ka nuna min Kai ka haifa yaran nan shiyasa bakayi shawara Dani ba to alkur'an ban yarda ba sai dai in Nusaiba ta auri Yazeed ka haɗa aure da irin tsiya to Wallahi ban yarda ba ko kuma a fasa auran gaba ɗaya.. "



Big Daddy yace, " haba Haj mai yasa kike haka ne yaran nan gaba daya jikokin ki ne yanxu zaki hada faɗa tsakanin su kina nuna kinfi San wannan da wannan. "

Abbu ya katse shi da ai Yazeed ma Yana da matar da yake so dan ɗazo da safe nayi mai mgn ya nemo matar da yake so Nan da sati uku to ai sai a bari ya kawo tukun na ko Dan ba a mai shigan hanci ba .


Abba yace , "Aa Ni Ina ganin abin da big Daddy ya fada shine dai dai ai basu suka haife muba mu muka haife su dan haka dole su bi abin da muke so...."



Haj Jadda tace, " oho muku dai tinda Kun nuna min ba Ni na haifa yaran ku ba ai shikenan Allah ya sanya alkairi/"

Big Daddy yayi murmurshin su na manya yace , "Haj Jadda kenan Ameen ai daman haka muke San kice yanxu sai a fara shirye shiryan biki ko dan auran yara shida ba wasa ba. "


Abbu yace , "saurin mai kake ai sai a bari my son ya zo dan shine babba aji ta bakin shi ko ".

Abba yace, " ai kawai a hada family meeting tinda jibi Saturday ".


Big Daddy yace, " eh haka za'a yi sai a faɗawa Shamsiya da Nafisat dan su tambaya mazajan su. "

Haj Jadda tace , "wannan kuma ai iyayan su Mata zaka gawa. "

Abbu yace , "to shikenan Allah ya kaimu Saturday ɗin Ina San zuwa Abuja yau amma gobe zan dawo insh Allah ".

Big Daddy yace, " Allah ya kiyaye hanya. "

Abba ma yace Allah ya kaishi lfy...

Haj Jadda tace "Kai Amma Yusuf baka jin tafiya Abuja ka maida shi kaman Zaria da kaduna".

Abbu yace, " ai dole ne Haj ku dai kuyi tamana addu'a ".

Tace "to Allah ya Kai ka lfy ya kuma dawo mana dakai lfy ".

Abbu yace ameen



Hameeda ce zaune a class yau kwatakwata Bata jin daɗi tama kasa fita break bare su hadu da uncle Hameed ɗin nata. Sallaman shi kawai taji sanye yake da farar shedda am Mata dinkin hannu yayi kyau sosai kallon shi kawai take ta kasa ɗauke ido a kanshi.

Yace "kallon fa
Sai kace baki taba gani na ba" Yana faɗa yana zama saman tabir din da take.

Tace "Wallahi kamin kyau ne sosai Ni baka taba min kyau bama kaman na yau Wallahi dik haushi ya kamani yanxu haka ka shiga class Mata na ta kalle min kai? "


Yace "haba my only kin san dai ba wacce takai matsayin da zan sota kin mamaye ko Ina Allah son da nake miki daga ummi sai papa pls ki yarda gobe su papa su je gidan ku Wallahi kullum jikina na bani in banyi sauri ba to gaf nake da rasa ki pls kinji my Hameeda".



Hameeda tace "hmmmm my Hamed kenan ai in gayama Hameeda ta kace ba Wanda ya isa ya mallake Ni sai Kai inshallah Ni matar kace kuma na yarda su papa suje gidan mu".


Hamed yace "Hameeda kin yarda su papa su je gidan ku..?"

" Hameeda dan Allah da gaske kike kai Allah na gode ma hameeda ke tawa ce inshallah Allah na gode ma da ka bani Mata kaman ki Hameeda mai kike so in miki Hameeda sbd wannan kyautar da kika min .


Hameeda kawai tsayawa tayi tana kallon shi wannan murna haka sai kace an daura auran gabaki daya.






Tofa ana wata ga wata 🤔








*comment*
*vote*
*share*









Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺


💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_




*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻




*Dedicated to my talala family ❤️ Allah ya qara hada kanmu yan uwa rabin jiki*😘😘😘




*Bismillahir rahmair rahim*




*page* 1⃣6⃣to1⃣7⃣



Hameeda tace "Haba my Hamed sai kace an daura auran gaba daya?"


Yace. "Hmmmmmm Hameeda kenan baki san irin son da nake miki ba ko,Wallahi Hameeda dik ranar da na rasa ki zan rasa Raina, Ina mai rokon Allah yasa ki zama mallakina matata uwar yarana.."


Tace "Ameen my Hamed ai ka kwantar da hankalin ka Ni ta kace har abada".


Yayi murmurshi yace " To Ni bari in koma office Kinga an kusa komawa break".


Tace "To my Hamed bye sai an tashi kuma".

Yace "Shikenan ki kula min da kanki kinje ".

Tace "To" 😘😘😘

Yace "Kai Hameeda zaki sa in kasa aiki fa Wallahi wannan 😘 haka ".

Tace "Ba wani nan in ban maka ba waye zai ma ".

Yace "Babu fa my only".


Ko da aka tashi sai da suka Sha soyayyar su sannan Fadila ta zo suka tafi gida.

A gida kuwa su big Daddy ba Wanda suka gayawa a Mata sunce sai ranar Saturday tukun na kowa yaji shiyasa ko da Hameeda ta dawo gida hankalin ta kwance sai ma murna da takiya iyayan uncle hameed zasu zo Amma Bata gayawa kowa ba dan nunawa zatayi ba ita tace ya turo ba sai dai kawai in an tambayeta tana son shi tace eh.

(Ni kon nace Hameeda ai an bar shiri tin rana bakin san an bawa yay Yazeed ke ba)😂



Uncle Hamed kuwa cikin farin cikin ya shiga gida ko gate man sai da yasa Yana cikin farin cikin a parlour ya samu Umma na zaune Hanifa ta daura kanta a kafan Umman suna fira.


Sallama yayi Umma da Hanifa suka amsa.

yace "Ke Hanifa Wallahi baki girma ni daga min uwa karki karya min ita".


Ya fad'a yana murmurshi.


Hanifa " Tace haba yay Hamed har wani girma nayi ,wai yau ya naganka sai farin cikin kake Allah yasa alkairi."

Umma tace " Wallahi kuwa abun da zance kenan keka riga ni".

Yace "Hmmmmmm Ummana abunda kike so inshallah an kusa dan Hameeda tace in tura gidan su".

Yana fada yana wani shafa Kai alaman ya ji kunya. 😏

Umma tace "Alhamdulillah inshallah yau zan gayawa papa ku sai su tsada ranan zuwa ko?".


Uncle Hamed yace "Yarda kika ce umma ".

Ita kuwa Hanifa tinda Hamed ya fara mgn gabanta ke faduwa dan ba qaramin so take mai ba wasu hawaye ne suka fara zubo Mata dan Wallahi tana bala'in son shi.


"Hanifa tashi ki kawo ma yayanki abincin".

cewar Umma dake duban Hanifa
Saurin tashi tayi dan Kar su gane yanayin da take ciki kitchen ta shiga tana hada mai abincin tana aikin kuka wai Allah na ya zanyi da rayuwata ya Allah ka cire min son Hamed a zuciyata Allah ka zaba min Mafi alkari sai da ta wanke fuskarta sannan ta hada mai komai ta huce part din shi dan yace can zata Kai mai .


*Wanene Hamed*


Hamed d'a ne gun Alh Mustapha Wanda yake cewa papa sai Mahaifiyar sa Murjanatu Umma ya taso cikin gata da so irin na iyaye shi kade Allah ya basu shiyasa soke son shi kaman rainsu.
Hanifa yar qanwar Umma ce tin tana Yarinya Umma ta dauke ta har ta girma Allah yasa Mata soyayyar Hamed Amma .

Cigaban labari.

Yau ta kama Saturday daman big Daddy ya gayawa kowa yau akwai meeting karfe 11:00 shi yasa kowa na gida har su Shamsiya sun zo


Kwance take kan bed din ta tana waya da Hamed, tace. " My Hamed bari in je in shirya yau muna da family meeting kuma har damu aka ce ban San maiyasa ba ".

Hamed yace " To shikenan my dear anjima su papa za su zo ".


Tace ' To Allah ya kawo su lfy".

Sai da suka dan taba hira sannan suka sallama

10:00 dai dai kowa ya halarci babban parlour gidan Haj jadda na zaune kan babban kujeran parlour meme da momy suna kujera daya maman Nusaiba tana zaune kan 1st haka ma ummi maman Fadila su big Daddy ma suna tasu da ban.

Yaran kuwa dik suna kasan kafet kama daga kan Yaya Yazeed, yay Areef, shamsiya, da yaran ta biyu suna ta wasan su Nafisat kuwa yaronta daya Bata ma yaye shi ba

Hameeda da Fadila suna gu daya Nusaiba tana kusa da uwarta haka dai dik kowa yayi shuru yana jiran a fara mgn .

big Daddy ne ya fara mgn yace ayi Addu'a kowa yayi sannan ya fara mgn kaman haka ,


"Ba komai yasa na hada wannan meeting ba sai dan ku Yazeed, Areef , da kuma su Fadila , da Hameeda, da Nusaiba. Sannan Ina so dik abinda na fada ya zama zaima kowa dad'i a Nan gun nasan zakuyi alfahari da wannan hadin da nayi ko ba yau ba."


Babu abunda kirjin yay Yazeed ke yi sai bugawa.

Big Daddy ya cigaba da cewa "Nasan ku yara ne masu biyaya Allah ya muku albarka "


Dik aka amsa da Ameen dan kowa burin shi big Daddy ya fada abin da yake san fada .


Yazeed big Daddy yace Yana duban shi.
Yaya Yazeed ya amsa da Na'am Daddy ,


Big Daddy yace.


Inshallah Kaine mijin Hameeda ".

Ai ba yay Yazeed ba kowa a parlour sai da ya kirjin shi ya buga Hameeda kowa sai da numfashin ta ya dauke na hucen gadi .


Big Daddy yace " Kai kuma Areef Fadila, sai kuma Nusaiba Nabil, Allah yasa alkairi a cikin wannan abu da na hada sannan kuma ko bayan Raina Kar Wanda ya sauya wannan hadi. "


Big Daddy yace "Haj jadda baki ce komai ba. "


Haj jadda tace "To Ni mai zance Allah dai ya bada zaman lfy yasa alkairi".


Kowa yace ameen .


Ita kam Hameeda ma Bata san mai ake cewa ba dan gaba daya Bata fahimtar komai .

Maman Nusaiba ce ta fara mgn "Haba dan Allah dan ba'a sona shi yasa Yar tawa ma ba'a so ya zaayi a hada ta da wani wai Nabil to Wallahi ban yarda ba sai da....."

Bata qara saba Abbu yace " Hajara mai kike Shirin yi yayan nawa yace Abu ke kece ba haka ba to Wallahi baki isa ba kika qara mgn a bakin auran ki dan Wallahi bazan dauka rainin ki ba yanxu ".

Haj jadda tace " Haba Hajara ai hakuri zakiyi tinda aikin gama ya gama ki taya su da Addu'a kawai ".

Abbu yace "Kowa ya tashi ya basu guri dan Abbu yana da fushi sosai yafi su big Daddy fushi shiyasa kowa ya tashi ya tafi".

Hameeda kuwa sai Fadila ce ta taimaka Mata ta tashi dan kwatakwata bata Jin abinda ake cewa

Yay Areef sai washe baki yake dan shi Yana son zabin iyayan nashi fatan shi Allah yasa ita Fadilan ta so shi.....😁





*To Ina team din Yaya Yazeed sai kuYace o muyi tawaye😎 dan gaskiya baza mu yarda ba*😂











*comment*
*vote*
*Share*






Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺


💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻





_*Dedicated to my only Mr Aliyu rabin Raina🥰🥰🥰😍 Allah ya barmu tare soldier na*_❤ 👨🏼‍✈





_Wato baka gane masoyan ka sai wani Abu ya samai ka gaskiya Ina godiya my fan's Allah ya bar kauna ina tare da ku Yan babu shi a zuciyata fan's_💃💃💃💃💃💃💃💃💃🥰🥰🥰



*Bismillahir rahmanir rahim*



*page* 1⃣8⃣to1⃣9⃣






Kuka Hameeda take sosai Fadila har ta gaji da lallashi ta qara fasa ihun da har momy sai da ta shigo d'akin.


" wayyo Ni Hameeda na shiga uku ya zanyi da Raina Wallahi bana son shi, *BABU SHI A ZUCIYATA* .

Momy tace " Hameeda bazaki ma kanki fada ba kiyi shuru ke daya aka bawa Wanda bake so yanxu wa kika ji yayi wani mgn sai ke ko Hameeda shikenan kija min zagi ".

Tace "Momy Wallahi in kuka aura min yay Yazeed mutuwa zanyi Wallahi Momy baya Sona nima bana son shi kuma nayiwa Hamed alkawari pls Momy ke uwa ce ta gari baza ki so in shiga wani hali ba dan Allah Momy ki taimaka min". tana mgn tana kuka

Momy ta tausawa Y'ar tata Amma baza iya Hana wannan abu ba tunda big Daddy ne yasa.

Zaunawa tayi a bakin gadon da Hameeda take ta maso da kanta kan cinyarta tace ,

" Hameeda kiyi hakuri da kaddaran da ta samai ki nasan abin son Yazeed Amma kiyiwa iyayan ki biyaya inshallah zaki ci rabar abun gaba."

Hameeda ta qara fashewa da kuka tace "Momy ya zanyi da Raina Momy na shiga uku Momy yay Yazeed baya Sona Wallahi kashe Ni zaiyi ".

Momy tace "A'a Hameeda Yazeed bazai kashe kiba ke Y'ar uwarsa ce Ni dai ki cire damuwa a ranki kinji Hameeda".

Kai kawai Hameeda ta daga .
Momy tace "bari inje D'akin na." Fadila ce kawai ta amsa da cewa to Momy .

Fadila " haba Hameeda mai yasa haka dik kin dagawa Momy hankali kiyi hakuri mana ai ba ke daya aka zabawa miji ba harda Ni Amma mai kika ga nayi pls Hameeda dan Allah ki daina wannan kukan".

Tace" Fadila qila ke kina son yay Areef ne shiyasa baki damu ba Amma Ni Wallahi bana son yay Yazeed *BABU SHI A ZUCIYATA* kuma Wallahi ya yarda aka daura auran na Wallahi ya shiga uku da Ni dan bazan taba zaman aure da wannan mutumin ba ."

Dry sosai Fadila keyi tace "A lallai Hameeda yay Yazeed din to Allah ya kaimu muka ana Shan love❤"

Duka Hameeda ta d'aka mata tace " dawo za'a Sha love din sai dai my Hamed kuwa."

haka dai suke ta firan su rabi dik fada ne dan Fadila akwai ta da tsokana.



Shi kuwa yay Yazeed Yana D'aki ya rufe kanshi yama rasa mai ke mai dadi a duniya shi dai da a hada shi da Hameeda gwara an hada shi da mai aikin gidan su dan Wallahi baya son ko ganin tane balle kuma wai aure .Kai da sake gaskiya hakadai yake ta mgn shi daya .


Maman Nusaiba sai faman safa da marwa take dan Wallahi baza ta taba barin ayi auran Nan ba yanda yarta Bata aure shi ba haka ita ma Hameeda baza ta aure shi ba dan an Raina Mata wayo shine za'a hada yarta da wani Nabil wayar tace tayi Kara tana dauka tace, "Haj zuwaira dan Allah kizo gidana yanxu akwai mgn da zamuyi ".


Haj zuwaira tace "lfy ko Haj "?
Maman Nusaiba tace "lfy ba lfy ba dan yau wan can yayan nasu ya yanke auran yaran nan shine dan rashin mutunci ya ba Nusaiba Nabil yaron abokin shi."


Haj zuwaira tace " iyeeee lallai ne mu da muke son ta aura Yazeed."
Maman Nusaiba tace 'to ai ba wannan ba Hameeda yasa ".


Haj zuwaira tace " tab Wallahi sunyi karya dan Wallahi Yazeed mijin Nusaiba ne kota boka kota malam sai Nusaiba ta aure shi ."

Naman Nusaiba tace " Ni dai kizo sai musan abinyi ".


Haj zuwaira tace to gani nan.


Hameeda sosai ta shiga cikin damuwa bata ci Bata Sha wuni daya kawai ta ramai sai kace mai ciwo Bata da aiki sai kuka da anyi mgn tace babu shi a zuciyatar har Momy ta fara fusata da ita ta daina ko kallon ta dan haushi take bata sai kace an hada ta da mutuwar ta .


ko Hamed ya Kira ta ma Bata dauka Dan Bata San mai zata ce mai ba .

Tana kwance a kan gadon ta tana aikin nata kuka. Zarah ta shigo
Zarah tace " Hameeda mai yasa mai ke baki da lfy ne".
Hameeda tace "A'a zarah mai kika gani "?

Zarah tace "Hameeda dik kin rame".


Tace "lfy na kalau kawai dai ".


Zarah tace "kawai mai ?"


Hameeda tace "Zarah auran dole za'a min dan Wallahi bana son shi *babu shi a zuciyata*".


Zarah ta maimaita auran dole Hameeda ki fada min kin sani a duhu

Hameeda ta fashe da kuka tace "yay Yazeed wai za'a aura min ".

Zarah tace " yay Yazeed Hameeda yay Yazeed fa lallai dole kiyi kuka, Amma kiyi hakuri kiyi biyaya."


Hameeda ta qara goge hawaye tace " shikenan "
Zarah tace " tashi ki rakani zan tafi daman na Kira kine naji wayan a kashe shine nace bari in zo ko lfy ".

Tashi tayi tana gyara Dan kwalin tace mu tafi .


Fitowa sukayi zarah tace "mu fara shiga part din su Fadila".

Hameeda tace " to".

a parlour suka hadu da Fadilan ma zata fito .


Hameeda tace "shikenan ma kin hutashe mu daman D'aki ki zamu ".


Fadila tace "nima kam gunki Zane kinsan yau zamuje amsa dinkin na".

Hameeda ta dafa Kai tace Kinga na manta Wallahi .


Fadila tace "ai nasan haka zaki ce ".


Zarah tace "Ni ku rakani Kun tsaya surutun ku".

Fadila tace "hmmmm yariya mun kosa zama manya ko Hameeda ta fada da tsokana ".


Hameeda tace "au daman yara ne mu "?"


Fadila tace " yara ne mana 18yrs fa Kinga lkc da zaki haifan ma yay Yazeed d'a kina 19yr".


wani wawan tseki mtswww Hameeda ta ja Allah ya rabani haihuwa da wannan .

Dry Zarah tayi tace "Wallahi Ni zan tafi ai ke daman Fadila in bakiyi tsokana ba baki Jin dadi.'


Fadila tace "naji mu tafi dai ".

suna tafiya suna hira har suka kawo Gate.

Hameeda tace "Ni dai anan zan tsaya Kinga bani da hijab ".


Zarah tace " to shikenan sai munyi waya ".


Fadila tace "Ni bari

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment