Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma shi ko kadan be Jin sonta a zuciyar shi..
"Yazeed"
Firgiget ya dawo daga tinanin da ya lula,
ta qara cewa "Yazeed"


Yace "naam yusura yanxu Ina da mutane ke je zan Kira ki"


Tace "Aa Yazeed baza ka Kira Ni ba nasan halin ka"

Yace "bani nace zan Kira ki ba ki tapi mana"

Jakan ta ta dauka sannan tace "zan tafi Yazeed Amma zan dawo gobe har sai ka yarda ka soni Yazeed Ina sonka I love you Yazeed"


Da kallon kawai ya bita har ta fice sanye take da wani riga da wando sun matseta sosai kayan sai Dan qaramin gyale da ta sa, kadan kenan daga halayan yusura da baya so,


Tinda ta fita ya fada duniyar tunani Yana tina maganganun yusura, wata zuciyar tace Yazeed kawai ka aure ta tinda dai ba son Hameeda kake ba, wata kuma tace Aa Yazeed gida ma baza a yarda ka qara aure ba bayan ga Hameeda, da yaji bazai iya aikin ba tashi yayi kawai ya dau key din motar shi ya fita ya Kira safwan yace ya kula da sauran patient din





Yawan comment yawan typing 🤷‍♀







Aunty Baby ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺



💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻



®☄
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻








*Bismillahir rahmanir rahim*





*page* 2⃣6⃣to2⃣7⃣








Ko da yay Yazeed ya tafi gida part din su ya huce, mgn yusura ce kawai ke mai yawo a kwakwalwa, Yana shiga D'akin ya Sami Meme na waya da qarwata suna mgn ne akan bikin, zaunawa yayi a kusa da ita ya Dan kwantar da kanshi a cinyar ta sannan yace,

"Meme na" yayi mgn ne cikin shagwaba.

Meme tace "Naam my only son menene naga fuskan ka ta chaja kuma ai yanxu ma ba lkc dawowar ka aikin bane"

Yace "hmmmmm Meme hakan kurun naji bana son zaman asbiti shine na dawo gida na dan huta"

Meme tace "to my son dama akwai mgn da nake son inyi da Kai"


D'a guwa yayi Yana kallon ta yaji wace mgn ce,


Yace "to Meme Ina jinki"


Sai da ta shafa kan shi sannan, tace

"Ina cikin farin ciki Yazeed"

Mik'iwa yayi a jikin ta dan kafin yaji Meme ta Kira sunan shi da wuya Amma to wani irin farin ciki take haka....


Sannan ta cigaba da mgn, "Wallahi ba qaramin dadi nake ciba way Kai zaka aure Hameeda Ina son Hameeda kaman yanda nake sonka Yazeed Dan Allah ka daure ka faranta wa Hameeda na San Bata sonka Amma ka daure ka chusa Mata sonka"

Wani irin bugawa girjin shi yayi, daman mgn wannan banzar yariyar zatayi mai to shi gaskiya yanxu yake jin zai iya auran yusura shi ya gyara Mata halayanta dan ita tana son shi ba abinda baza ta iya ba sbd shi,

Taba shi Meme tayi dan taga ya tafi wata duniyar
tace "Yazeed baka ji abinda nace bane"?

Yace "naji Meme Amma nima Ina son in gaya miki wata mgn"


Tace "Ina jinka"




"Hmm daman hmmm"

Sai kuma ya kasa mgn dan yasan Meme da wuya ta yarda,

Meme ta qara cewa "ina jinka"

Yace "Meme akwai wata yariya da take Sona tun muna Landon kuma na Mata alkawarin zan aure ta shine" hmmmmmm
Sai kuma ya kasa qarasa wa


Meme tace "shine mai, badai so kake kace min zaka aure ta ba to Wallahi Yazeed karka kuskura in qara Jin wannan mgn" ta karashe zancen da fada, tace "Wallahi karka yarda ma Daddy ka yasan mgn nan, to ita Hameeda kayi Yaya da ita "?

Shi Yama kasa mgn sbd wani irin tsanar Hameeda yaji ya qara ji a zuciyar shi akan ta za'a Hana shi abinda yayi niyar yi to Wallahi sai dai ita ya fasa auranta,


Meme tace "wai ba mgn nake maka ba"

Yace "Meme ai itama zan aure ta Amma a fara yin na"...... Bata bari ya qarasa ba ta gwabe mai baki tace

"Shashasha Wanda basan abinda yake mai ciwo ba tin yaushe ake ma mgn aure kace Kai baka da budurwa sai yanxu da aka baka yar uwarka shine zaka fara ma mutane maganan banza tashi ka bani guri kuma Bari Daddyn naka ya dawo in fada mai shashanci da kake tinanin yi"


Tashi yayi ya fita rashin b'ace akan wannan yariyar Memen shi ta gwabe mai baki to Wallahi akan ta zai rama Allah ya kaimu ayi bikin, part din shi ya huce kwantawa kawai yayi Yana tinanin yusura ga wacce take son shi har kuka take sbd shi Amma za'a hada shi da wacce qaramar yariyar da ko 18yr bata rofa ba...


*************
Maman Nusaiba ce zaune abin duniya duk sun ishe ta Dan ita har yanxu bata ga aikin ya fara ci ba, wayan ta ta dauka da danna ma qawarta Haj zuwaira kira ringing biyu ta dauka, tace

"Sai yau aka tina dani ai Haj kin ban mamaki sai kace Ni ne miki laifin"

Maman Nusaiba tace " haj kenan ai kece kin ban haushi kin San fa Ina da aure na mai yasa zaki kaini gun wannan bokan, duk cin amanata ban taba zina ba shiyasa na damu sosai"


"Hhhhh Haj kenan ai Wallahi Ni zuwaira naci dubu sai ceto maiye a ciki Dan kayi zina abunda ba wani ne ya ganka ba ai ba wani Abu"


Maman Nusaiba tace "duk ba wannan ba nifa har yanxu ban fara jin fadan su ba, shine nace ko zamu koma ne Amma fa gaskiya bazan qara aikata kuskuran da na aka ta ba"

Haj zuwaira tace "Ni in qara rakake kizo kina Jin haushi na ba inda zani"


Maman Nusaiba tace "haba qawata ai ko wancen ma Dan ban saba bane Amma kiyi hakuri"

Haj zuwaira tace"to shikenan Allah ya kaimu gobe zan zo"


Maman Nusaiba "tace yauwa qawata na gode sai goben "

Wata dry ta sak'i hhhhh sai Ni Haj zuwaira tace "zaki ci ubanki ne ai gabaki daya kudin ki sai na cinye"




Hameeda ce zaune a parlour su suna kallon tarkon kauna a tashar arewa24, sai ga zarah nan ta shigo.


Tace "Kai Hameeda ke kina son wannan film din nikon banga abin kallo a ciki ba"

Hameeda tace "Zarah kenan in kika fara kallo baza ki Bari ba sbd Yana da kyau Ni Wallahi omar din nan haushi ya ke bani ace mutum bashi dry sai kace wani yay Yazeed"

Dry Zarah tayi sannan tace "au nagane abin da yasa kike kallon wannan film din Yasin sbd Omar na kama da yay Yazeed ne"


Hararan ta Hameeda tayi sannan tace "Wallahi zaki sa ma na daina kallon film din"


Fadila dake shigowa yanxu tace "yo ki daina kallo mana ai mundai San baza ki daina kallon mai kama da mijin ki ba"


Dry suka kwashe da ita duka Hameeda kon ta qara ciki ta fam..

Zarah tace "Yan Mata biki na ta k'aratowa mai kuke ganin zamu shirya ne dan bikin Yan Mata uka ba wasa ba"


Fadila tace "haka ne Amma ki bare mu kammala exam, sai a San abinyi"

Ita dai Hameeda Bata ce k'ala ba, sai ma wayan ta da ta fito tana game....




Lakaci na ta tafiya

Yanxu haka bikin su Hameeda sauran wata biyu, shirye shirye ake yi ba kama hannun yaro Dan kowa Yana so ya fito da d'iyar shi, ita dai auntyn amaryar maman Fadila kenan tare suke abin su da Momyn Hameeda, maman Nusaiba ba kon ita daya ke abinta Daman ba son yaron take fa kawai dai tana yi ne Dan ta yarta tafi kowa fice a gidan


Yanxu haka kuma exam din su Hameeda sauran paper uku su gama


Yau kuma iyayan uncle Hamed sukai Shirin zuwa, sun gama komai nasu papan Hamed da kanin shi sai kuma abokin shi, Hamed ne ke ta Kiran Hameeda wayan be shiga ba sai kawai kawun shi yace ba matsala bari su tafi tinda ita yariyar tana son shi ai ba matsala, hakan kon aka yi shi ya kaisu har bakin Gaten din gidan su Hameeda sannan sannan ya je neman musu iso gun getman din yaje ..


Yace "baba Dan Allah baban su Hameeda na Nan"?

Getman din yace "eh suna Nan duk mazan gidan"

Yace "to dan Allah kace musu suna da baki"


Getman din yace "to"

sannan ya tafi part din big Daddy ya nufa Yana xuwa kon ya Samu big Daddy ya fito zai fita yace sai da suka gaisa sannan yace mai suna da baki,


Big Daddy yace "baki kuma daga Ina"

Getman din yace "eh baki ne Amma bansan daga Ina suke ba"

Big Daddy yace "to kace musu su shigo ka Kai su D'akin baki"

Getman din yace "to alh sannan ya huce"

Yana zuwa yace ma Hamed ance su shiga sai Hamed ya je ya gawa papan shi sannan shi kuma ya shiga motan, fita sukai a motan suka shiga gidan D'akin bakin getman ya kaisu.


Big Daddy ne ya shigo da sallama sai da suka gaigaisa sannan..


Yace "ban waye ku ba"


Kawun Hamed ne yace "sannu alh sunana alh sagiru shi kuma wannan sunan shi alh mustapha papan Hamed kenan sai kuma wannan sunan shi alh Abbas" abokin papa kenan


Big Daddy yayi murmurshin yace "to sannun ku da zuwa"

Alh Abbas "yace wato alh dalilin zuwan mu gidan ka shine d'ana yaga yarku yace Yana so shine muka zo in Allah yasa ba ayi Mata miji ba"


Saudat ce ta shigo da babban faranti a hannun ta sannan ta gaishesu ta fita ruwa ne da kayan motsa baki....



Big Daddy yace "ga ruwa ku Sha alh"

Duk suka ce sun gode sannan alh Abbas ya cigaba da mgn


Big Daddy yace "to duk da dai bansan wacce kuke mgn ba Amma dai yaran uku Mata an musu mijin dan yanxu haka ma sauran wata biyu bikin su"


Kawun Hamed yace "to Ina ga dai wannan ba a Mata miji ba gaskiya"

Big Daddy yace "ko ya gaya muku sunan ta"


Kawun Hamed yace "eh sunan ta Hameeda"

Big Daddy yace "kash Hameeda bikin ta sauran wata biyu ko dai Saudat yake mgn"


Alh Abbas yace "Aa alh Hameeda ce"


Big Daddy yace "Ina mai baku hakuri Hameeda an riga da an Mata miji yayan ta zata aura"


Sai yanxu papan Hamed yayi mgn yace "to alh mun gode da karamcin da ka mana, ita kuma Allah ya basu zaman lfy"


Duk suka amsa da ameen sannan big Daddy yace


"Shima Allah ya bashi mace ta gari"


Nan ma suka ca ameen sannan suka mik'i zasu tafi,

big Daddy yace "baku ci komai ba"

Suka ce ba komai daga gida suke..

Hakanan suka fito gidan jiki a sanyaye, Hamed na ganin su ya fito daga mota ya tare su da murnar shi, yace
"Kawu sannan ku"

"Yauwa" kawai kawun Hamed yace

Motan suka shiga suka fara tafiya har suka kai gida ba Wanda yayi mgn, sai da suka fito a motan Hamed yayi haryar part din shi papan shi yace Aa ya biyo su, parlour suka shiga gabaki dayan su umman Hamed tana ganin su ta tare su da murnar ta, gabaki daya zauna wa suka Hamed Yana kan cerpat, papa ya gyara murya yace


"Hamed duk Dan adam an San shi da yarda da qaddara mai kyau ko Mara kyau..........




_In naga comment in cigaba in ban gani ba kuma Ina muku fatan alheri dan bazan dinga muku typing ba baku comment😊_


I love you 😘 all my fan's💃💃💃💃






*comment*
*share*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺



*💅BABU SHI A ZUCIYATA💅*




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻





*Bismillahir rahmanir rahim*






*page* 2⃣8⃣to2⃣9⃣








Hamed dai baice k'ala ba, dan tinda yaji ana mai wannan maganar yasan to ya rasa Hameeda har abada.


Papa ya cigaba da cewa, "Hameed an riga da an sawa Hameeda Ranar bikinta sauran wata biyu kayi haƙuri ka daure Allah ya baka wacce tafi Hameeda, sannan yanxu na yanke shawaran haɗaka da ƴar'uwarka Hanifa"


Umma kallon dan nata kawai take yi Dan tasan ba ƙaramin so yake wa Hameeda ba Amma ba rabon shi bace, Daman (hausawa sunce matar mutum ƙabarin sa)


Kawun Hameed yace,

"Masha Allah wannan haɗin yayi Allah ya kaimu lokacin"


Duk suka amsa da "ameen" shiko Hameed ma ai ya kasa magana, ɗakin shi ya tashi ya tafi.


Abokin Papa yace,

"Allah sarki Allah ya cire mishi sonta a zuciyar shi"


Papa yace, "in banda yaran zamani ma maiye dan kana son budurwa baka samu ba, ba sai ka koma kan wata ba"


Umma tace, "to Allah yasa dai ita Hanifa Bata da Wanda take so"


Papa yace, "wannan kuma ai ke ya kamata ki tambaye ta, Amma nasan dai ba Wanda take kulawa kin San Hanifa akwai nutsuwa"


Haka dai sukai ta tautaunawa............


*************

Big Daddy kon suna fita shima ya wuce part ɗin Haj Jadda, ya Kira Abbu da Abba yace su samai shi a part ɗin Haj Jadda, Nan da Nan kon suka haɗu.


Haj Jadda tace, "ince dai lfy?"


Big Daddy yace, "lfy lau fitan nan da nayi sai aka ce min nayi baki Ina zuwa na samai su, sun zo tambayan auren Hameeda"


Haj Jadda tace, "wace Hameeda kuma ita da aka mata miji ko basu San bikinta ya matso bane"


Big Daddy yace, "basu sani ba Amma na gaya musu"


Abba yace, "to ai gwara da ka gaya musu"


Haj Jadda tace, "halin ma ƴar banzan yariyar nan ta San da zuwan su dan ta kunyata mutane yasa ta turu su"


Big Daddy yace "haba Haj Jadda tasan an Mata miji Ina zata ce wasu su zo kuma"



tashi yayi ya kalla agogon hannun shi yace, "Bari in wuce daman baƙin nan ne suka tsayar Dani"


Sai yanxu Abbu yayi magana yace, "to Allah ya dawo da kai lafiya nima Ina ga yanzu zan fita"


Haj Jadda tace, "a dawo lafiya"


******
Hameed tinda ya shiga ɗaki ya dafe ƙirjin shi, wani irin nauyi yaji yana mai sannan kanshi na sarawa, wasu hawaye ne suka zubo mai masu zafi yace,


"Wallahi nasan mutuwa zanyi bazan iya rayuwa Babu ke ba Hameeda nasan kema dole akai miki, shikenan yanzu na ƙara rasaki Hameeda wayyo Allah Daman ɗaukan Raina akayi da ganin wannan ranar"



ji yayi an dafa shi ya d'ago yaga ko waye,
Umman shi ce ƙwalla ta cika Mata ido tace,

"Hameed ka zamo namiji mana kayi haƙuri da ƙaddaran da tazo ma Dan Allah karka sa kanka cikin damuwa kasan halin ciwan ka"


hannunta ya rik'e sannan yace,

" Umma Wallahi Ina son Hameeda bazan iya rayuwa Babu ita ba, kina gab da rasa Ni Wallahi Ina ma Hameeda son mutuwa ya zanyi da rayuwa...."



Tari ne ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa abinda zaice , tari yake kaman na ɗaukan rai idon shi ya firfito, ya saki hannunta ya rik'e ƙirjin shi.

Kuka Umma ta fashe da shi sannan tace,

"haba Hameed mai yasa zaka min haka dan Allah karka tafi ka barni"



shiko ko jinta baya yi, da taga abin bana ƙare bane ta fita ɗakin da gudu, parlour ta shiga tana,


"Alhj ka taimake ni Hameed, Hameed kar ya mutu ya barni"


Papa yace, "Hameed kuma mai yasa mai shi"?


Kawun Hameed yace, "ai ba tambaya zamu tsaya yi ba muje mu gani"


Fita sukaiyi dukan su, ɗakin Hameed ɗin suka nufa, yanda yake haka yake hannun shi dafe da ƙirjin shi.




cikin hanzari Alhji Abbas yace, "Alhji kama shi mu sashi a mota"


kama shi sukaiyi suka Kai shi mota sannan suka shiga, Umma hijab ɗinta kawai ta ɗauko a ɗaki sannan suka wuce hospital..........


****

Yana bacci yaji wayan shi na ringing, baƙuwar number ce shiyasa ya mayar da wayan ya ajiye, Kiran aka ƙara yi nan ma be ɗauka ba sai da akai Kira uku sannan ya ɗauka cikin Jin haushi yace, "waye"


Daga can tace, "haba Yazeed yanzu number nawa ma baka da ita ai Daman nasan ba Kira na zakayi ba shiyasa na Kira ka"


Sai yanzu ya gane ashe Yusura ce yace "oh sorry Yusura ya kike"



Tace, "hmmmm my Yazeed sonka ya hanani bacci ko da yaushe fuskanka ita ce farin ciki na pls my Yazeed ka yarda ka aure Ni daga baya ka soni"


ta ƙarashe magana cikin wani irin Kashe murya.


Ji yayi duk Yanayin shi ya sauya sannan yace, "uhhmmn to zanyi shawara"


Tace, "kaman yaushe zan ƙara Kiran ka inji"

Yace, "ki bari in nayi zan Kira ki"


Sai da ta ƙara Kashe murya sannan tace, "to my Yazeed sai ka Kira Ni din Ina nan Ina jiran ka I love you"



"Hmmmmmmmm" kawai yace Mata dan duk ta gama canja mai Yanayin shi.



yanzu dai ya gama yanke wa kanshi shawaran zai auri Yusura tunda ta riga ta nace mai.


hakan Nan zai aure ta, murmushi yayi yace, "hmmmmm daman Ina son macen da zan aura ta zamo babba saboda itace zata iya ɗaukan nauyi na ba ƙananan yara ba irin su Hameeda......"



Suna isa hospital ɗin aka amshe su da sauri, Daman Alhjj Abbas ɗan shi likita ne ya Kira shi yace suna hanya suna zuwa kuwa aka amshi shi da sauri aka Kai shi wani D'aki.



sosai suke bashi taimakon gaggawa sakamakon ciwan zuciyar shi dake niyar tashi, Allah ya taimaka an kawo shi da wuri da sai dai wani ba shi ba..


Umma ba abinda take sai kuka Dan shi kaɗe Allah ya Bata gashi yanzu tana niyyar rasa shi, papa yace haba,


"Hajiya addu'a zaki mai ba wannan kukan naki ba"


Hawaye ta share sannan tace, "haba Alhji ka banni nayi kuka na baka ganin halin da Hameed ke ciki ne"


Yace, "to addu'a ki ya ke buƙata ba kuka ba"


Dr ne ya fito, da sauri kawun Hamed ya tare shi yace ,


"Dr baku ce mana komai ba"

Yace "ku biyo ni office"

Office ɗin suka shiga, kujera ya nuna musu su zauna sannan yace,


"wato Alhji Allah ya taimaka kunyi gaggawan kawo shi sannan kuma ciwan shi Yana ne man tashi to yanxu dai Allah yasa munyi maganin abun sannan kuma a kiyaye ɓata mai rai dalilin wannan ciwan nasu nasan farin ciki da walwala da fatan za'a kiyaye"


Papa yace, "insha'Allah za'a kiyaye za'a iya ganin shi yanzu?"

Dr yace, "gaskiya ba yanzu ba, saboda ya Samu bacci yanzu sai zuwa anjima zaku ganshi"


Kawun Hameed yace, "to shikenan mun gode Dr Bari mu je waje kafin ya tashi"



Dr yace, "to Allah ya bashi lfy"


suka amsa da ameen sannan suka fito daga office ɗin......


****


Zaune take a kan kujeran parlour su abin duniya ya isheta, musamman in ta tuna auran nan sai taji gaban ta ya faɗi, tinanin irin zaman da zasuyi da Ya Yazeed kawai take, wasu hawayen baƙin ciki ne ya zubo mata, duk son da take ma Hameed ya tashi a banza kenan.



innalillahi ya zatayi da ranta, dafa ta taji anyi, dubawa tayi taga Momy ce zaune a kujeran ta dafa kafad'ar ta tace,

"Hameeda mai yasa baza ki ma kanki faɗa ba, kinsan dai auran nan dole ne to mai nasa kanki damuwa, to tun wuri kima kanki fad'a Dan Wallahi Ni ba irin iyayan nan bane musu goyawa y'ayan su bayan rashin gaskiya, dube ki yanda kika ramai kaman bake ba, baki cin abincin baki komai Wallahi zan Bata miki rai"


Kuka Hameeda ta ƙara fashewa da shi sannan tace, " haba Momy da wanne zanji da wannan auran ko da faɗan da kike min, Ni Wallahi ma gwara na mutu na huta"


ta ƙarashe zance cikin matsanacin kuka.

Dariya Momy tayi sannan tace, "to Hameeda ki mutu mana ai lokacin ki ne yayi in kin mutun"

Tace, "Wallahi Momy na mutu sai kinfi kowa kuka"

Momy tace, "Ni ba kukan da zanyi, tashi ki wuce kitchen kiyi abinda zaki ci jibi duk yanda kika ramai"


Hameeda tace "to" tare da Mik'ewa.......


***
Karfe 7:30 dai dai Hameed ya farka cikin wani matsanencin kuka Yana cewa, " Hameeda Allah yasa mafarki nakeyi ba da gaske rasa ki zanyi ba"


Umma dake zaune a kujeran ɗakin tayi saurin tashi ta matso inda yake tace
Hamed, "ka tashi"?

Yace, "Umma dan Allah kice min mafarki nakeyi na rasa Hameeda Wallahi nima zaki rasa Ni"


Umma ta share hawaye sannan tace,

"Hameed kayi haƙuri ka rasa Hameeda Allah ya cire maka soyayyar ta a zuciyar ka, kasa ma ranka haƙuri kasan ba lfy gare ka ba"


riƙe hannunta yayi sannan yace, "Umma baki San zafin da zuciyata take bane, Amma insha Allah zan cire ta a zuciyata nasan da wuya hakan Amma zan kok'arta"


Dr ne ya shigo D'aki sannan ya ƙara duba shi yace , "bawata matsala zuwa gobe ma zai iya sallamar shi"


tea Umma ta haɗa mai sannan ta zauna tana bashi har ya shanye, Hanifa ce ta shigo D'aki hannun ta rik'e da basket ɗin abinci fuskan ta ba walwala sosai...


Tace,"Sannu Umma ya mai jiki"?


Umma tace, "Hanifa kece sai da nace miki karki zo gobe zamu dawo Amma kika zo"



muryanta a sanyaye tace, " Umma abinci fa nayi muku kuma nasan bakici komai ba"

Umma tace,"to Allah ya miki albarka"


Hanifa tace, "Ya Hameed ya jiki"?


"da sauƙi" kawai yace ya juya da kanshi,
Tace, "Allah ya ƙara sauƙi"


haka sukai ta firan su da Umma shidai bece musu ƙala ba, har 10:00pm tayi Umma tace Hanifa ta tashi ta tafi gida gobe ma ba sai ta zo ba tinda goben zasu dawo, Hanifa tayi musu sallama sannan ta tafi.......


Washe gari Ya Yazeed ne cikin Shirin shi na asibiti ya fito part ɗin su Meme ya shiga dan yin breakfast, yana shiga Dining ya wuce anan ya Samu Big Daddy da Meme Suma suna break ɗin.



gaishe su yayi sannan ya zauna ita dai Meme ciki ciki ta amsa.


Big Daddy yace, "lfy dai ke da ɗan gidan naki"


Sai da ta ƙara haɗa rai sannan tace, "bar wannan shashashan yaron"


Big Daddy yace, "a dai mai haƙuri" Yana faɗa ne Yana dariya dan yasan bata fushi da ɗan nata.


Shidai Ya Yazeed break ɗinshi kawai yake dan sai da ya gama tukun yace,


"Meme na a min afuwa Ni zan huce"

Tace, "a dawo lfy"

Big Daddy ma yace, "sai ka dawo my son"


yace, " Allah yasa"

sannan ya fito cikin sauri Dan yayi Lette..


Yana zuwa asbitin office ɗin shi ya wuce Yana buɗe ƙofan kenan yaji an rungumo shi ta baya............












*comment*
*share*










*AUNTY* *BABY* *ce*✍ 🥰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺




💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼






*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻





_Wayyo dadi 💃💃💃💃💃💃 a gaskiya naji dadin comment din ku na kwana kin nan, comment din ku na qara zuga Ni Ina qara suburbud'a muku typing🥰🥰🥰🥰_






*Dedicated to my mother ❤️ Allah ya bar min ke uwata*😍😍😍




*Bismillahir rahmanir rahim*




*page* 3⃣0⃣to3⃣1⃣





Juyowa yayi a fusace yaga wacece tamai wannan rungumar, yusura ce sanye cikin wani riga da wando pink da blue tayi kyau sosai, sai murmushi take zuba mai


Finciketa jikin shi yayi sannan ya ture ta, "wai baki da hankali ne yusura mai zaki wani

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment