Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in rakata in dawo ".


Hameeda tace " to sai kin dawo ki samai ni kitchen Wallahi yinwa nake ji ".


Fadila tace ok

Tana juyowa sukai ido hudu da yay Yazeed fuskan nan nashi kaman kullum d'aure. yau kam harda gyalass .😎

*nace to fa harda gyelashi bari inyi Nan* 🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀











*comment*
*vote*
*share*









Mr's Aliyu ce ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺


💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼






*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻







_*gaskiya Ina jin dadin comment din ku musanma mardiyyah Ina yinki irin over dinnan 🥰🥰🥰💃*_




*Bismillahir rahmanir rahim*





*page* 2⃣0⃣to2⃣1⃣





Tana juyowa sukai ido huɗu da shi .

Ya ƙara tamke fuska yace "ke! daga Ina kike dan wulakanci ma ba hijab?. ".

Wani kallon wulaƙanci tamai sannan tace " Ina ruwan ka in bansa hijab ɗin ba ?".


Yace " Hameeda rashin kunya taki har takai Ina miki mgn kina mayar min to Wallahi ki kiyaye Ni in ba haka ba wataran sai na karya ki idiot kawai ".


"Hmmmmm yay Yazeed kenan ai Wallahi baka ga ranin ba ma Sai ka yarda an daura auran nan dan Wallahi ka aura masifa da bala'i kuma Wallahi bana son ka bazan taɓa sonka ba mutum Yana da Wanda yake so Amma za'a haɗa shi da wani."
ta ƙarashe zance tana barin wajan


Shiko binta kawai yake da kallon , kaman ba Hameeda ba ita ce zata tsaya tana gaya mai wannan magana lallai yayi sake to shiko sai ya bari anyi auran yaga abin da ta isa ta mai .



komawa yayi part ɗin shi ya kwanta cike da tinanin mgn Hameeda wai Bata son shi to waya gaya Mata shi zai ma taɓa sonta a duniya ai Wllh never ya san wannan yariyar da ko budurwa Bata gama zama ba.. Yana wannan tinanin har bacci yayi nasaran daukan shi .




Hamed ne kwance a d'akin shi tinanin duniya ya isheshi Yana ta Kiran Hameeda take dauka daga karshe ma kashe wayan akayi to shi mai yasa maita da har Bata daukan wayan shi .


Wani tinanin ne ya zo mai kawai ya tashi ya fada toilet yana fitowa yayi Shirin shi cikin bakin yadi mai sharashara Wanda har faran singlet din shi ana gani yayi kyau sosai abin ka da farin mutum daukan key din motar shi yayi ya fito daga part din nashi part din Umma ya nufa dan yau kwata kwata be fito ba sai yanxu.. ba kowa a parlour bedroom din ta ya nufa ya samai ta tana ninke kayan ta.


yace "sannu Umma ".

d'a guwa tayi tana kallon shi dik ya fada gashi fuskan shi kaman da damuwa.



tace "baka da lfy ne naga dik ka fada kuma yau baka fito breakfast ba ".

Zaunawa yayi a gefanta sannan yace wllh umma banjin dadin jiki na ne kawai.

Tace to "mai yake damun ka bari Hanifa ta kawo ma break ɗinka in kaci sai kasha magani "

Yace no" Umma bana shaawar komai yanxu ma fita zanyi,"


tace" Kai da baka da lfy Ina kuma zaka? "

Yace" zanje gun abokina Fahad ne."

Tace "to a dawo lfy."


Fita yayi ya shiga motan shi be tsaya ko Ina ba sai gidan su abokin shi Fahad Yana zuwa ya Kira shi yace ga shinan a bakin Gat.


Fahad yace to ga shinan zuwa be daɗe ba kon ya fito Yana shima ya fito daga motan shi gaisawa sukai irin na aboka sannan Fahad yace Hamed mu shiga ciki ko

Hamed yace "no abokina ba dadewa xanyi ba kawai muyi mgn a mota "

Fahad ya kalle abokin nashi da fuskan shi da a laman damuwa sannan yace "haba Hamed wani irin baza ka shiga ba "

Hamed yace "ok muje bana son surutu da yawa "

Fahad yace "to muje "

D'akin Fahad din suka wace suna shiga ya Sami kujera ya zauna Yana sauke ajiyan xuciya. Fahad ya yace "wai Hamed maike damun ka ne kwatakwata ba walwala tare da Kai ?"


Hamed yace "Hameeda kullum Ina Kiran ta Bata daukan waya na gashi papa yau zai dawo Ina so suje gidan su kafin ya tapi Wallahi Ina cikin damuwa sbd ban San maike damunta ba ".


Fahad ya nisa kafi yace "ai wannan mai sauki ne kawai muje gidan su muji ko lfy."


Hamed yace "to shirya mu tafi"

Fahad yace "ok bani 30min kawai"

Hamed yace "ok "





Maman Nusaiba ce ita da qawarta Haj zuwaira suna Shirin fita. Haj zuwaira tace


"haba Haj kiyi sauri mana kin San dai boka Dan dunkulu baya san jira kuma nace mai da wuri zamu zo."


Maman Nusaiba tace "to Haj ko break banyi ba Amma tinda kin matsa mu tafi kawai "


Haj zuwaira tace" Ina wani zance break ai kawai In mun dawo mayi dan ko Ni banyi break din ba "


Maman Nusaiba tace to tashi mu tapi na gama. Haka suka fito maman Nusaiba ce mai jan motan suka kama hanyan wani kauye da ke can cikin Zaria tafiya suke har saka bar kwalta suka shiga D'aji tafiyan awa daya ce ta kaisu inda suke San zuwa.


Haj zuwaira tace "muyi fakin anan dan mota baza ta shiga gurin ba "

To kawai maman Nusaiba tace dan gabanta sai faɗuwa ya ke ta rasa dalili

Fitowa sukayi a motan Haj zuwaira ta rike hannun maman Nusaiba da jikin ta ke rawa wata buka Haj zuwaira ta nuna ma maman Nusaiba tace" yauwa Kinga bukan can mu qarasa ko "ta faɗa tana Jan hannun ta.



gurin bukan suka nufa suna zuwa Haj zuwaira ta saki hannun ta tace "bari in je in mai mgn "
To kawai maman Nusaiba ta iya cewa
Haj zuwaira kuwa bukan ta shiga wani katon mushiriki ne zaune kan wani jan buxu fuskan nan tashi ba ken gani ga rantamaiman Kai bashi da wani tsawu sosai. Washe jajayan hakurin shi yayi Wanda basu wuce goma ba Amma sun cikin bakin sabida girma.

Haj zuwaira tace" a lfy dai boka Dan dunkulu ifiritu ya baka lfy ya qarama sawan kwanan" kirari dai kala kala


Wata uwar ashar ya mulmulo yace" sarki Dan tsamake na miki barka da zuwa kice wa Wanda kuka zo ta shigo da kafar hagu "


Haj zuwaira tace "an gama Dan dunkulu" fita tayi tacema maman Nusaiba ta shiga Amma da kafar hagu haka kon maman Nusaiba tayi ta shiga tana zuwa ta xube gaban shi.

Tace "Ina gaisuwa Dan dunkulu ifiritu ya baka abin da kake so. "

Ya hadiye wani miyu mukun kake ji a zuciyar yace ai dole na huta da wannan. Sannan yace dik abinda ke tafe dake na sani yanxu mai kike son ayi musu


gaban maman Nusaiba ne ya fadi tace "kasan mai ke tafe da Ni? "
Wani ashar din ya qara sannan yace "qarya zan miki ne ?"

Bakin maman Nusaiba har rawa yake gurin cewa Aa

Sannan yace" to mai kike son ayi musu ?"


Haj zuwaira ta kalla sannan tayi mgn a hankali tace" mai za'a yi musu "

Haj zuwaira tace "ki faɗi abun da kike son ayi musu mana "




Sai sannan ta kalle shi tace" a lalata auran tinda dai yariya ta Bata aure shi ba to ita ma baza ta aure shi ba"

Wani ruwa ya dauko sannan yayi dan dube duben shi yace "wannan aure bazai taba lalatuwa ba dan naga kaman da yara a ciki "

Duban shi maman Nusaiba ta qara yi sannan tace" haba boka Dan dunkulu ya zaka ce bazai lalatu ba ?"

Yace "eh abinda na gani kenan Amma yanxu mai kike son ai musu a kashe su ko kuma ai musu kurciya ko kuma a sa musu kiyanyar juna ?"


Zuba ce ta rubata sharaf dan dik makircinta baza ta iya kisa ba.
Haj zuwaira ce ta tabota tace mai kike son ai musu?
Maman Nusaiba tace" kawai a sa musu kiyanyar juna da ko anyi auran baza suyi zaman lfy ba "

Yayi wata shegiyar dariya sannan yace "aikin gama ya gama sai dai da sharadin zaki bamu kanki dan ifiritu ya yaba "

Ras Ras gaban ta yace" tace na shiga uku da auran nawa ?"

Dafa ka fadar ta Haj zuwaira tayi sannan tace" haba Haj sai kace wani ya San abinda kikayi waye ana daga Ni fa sai ke haba karki bada Mata mana "


Wani gumi maman Nusaiba ta sharce sannan tace "Wallahi Ina Jin tsoro "
Haj zuwaira tace" dan Allah ki cire tsoro qawata badai bukata zata biya ba ai ba matsala "ta fada tana Mata murmushi

Maman Nusaiba ta qara kallon shi gaba dayan shi wari yake ga wani uban daud'a a jikin shi wani irin take ji a jikin ta

Kallon ta yayi yace" shikenan In baki yarda ba amma ki San da sani dik abinda ya samai ki ke kika ja "


Bakin ta na rawa tace "na yarda "

Washe jajayan hakurin shi yayi sannan yace" yauwa Yar gari "

Ya dube Haj zuwaira yace" sai ki bamu wuri ko"

Murmushi Haj zuwaira ta sakin mai kafin "tace a gama Dan dunkulu"

Ita kam maman Nusaiba ba abinda tayi sai kolla Amma in ta tina ai dik kan Nusaiba tayi sai taga ai ba komai bane in dai 'yarta zata dauwama cikin farin ciki

Ta sowa yayi ya matso gareta. Wani irin wari ya dushi hancinta Bata San sanda ta tofar da miyu ba
a zuciyar shi kuwa cewa yake zaki gane kuren ki tinda kin zo hannu. gyalanta ya fara cirewa sannan ya cire Mata komai nata shima ya cire ya haye kanta haba ya fara aiki........







Hamed ne da abokin shi Fahad cikin mota sun zo dai dai Gate din su Hameeda
Fahad yace" to yanxu waye zai Kira mana ita.?"


Hamed yace" bari in ma getman din su mgn" fitowa yayi daga cikin motar sannan ya fara noking din Gate din yayi
getman ne ya leko sannan yace waye

Hamed yace "dan Allah hameeda na Nan ?"
getman din yace" eh tanan nan "
Yace" Dan Allah dan yi min sallama da ita "
Yace "to wa za'a ce Mata
Hamed yace kace Mata Hamed ne "




getman din yace to sannan ya huce part din su Hameeda konkwasa kofan D'akin yake.
Saudat na zaune tana kallo ta ji anan noking tashi tayi taga ko waye tana bude kofan taga getman tace Aa baba Kaine
Yace eh "Saudat Hameeda na ciki ne ?"
Saudat tace" eh tana nan lfy ?'
Yace :eh wai Hamed ne ke kiranta "
To Saudat tace sannan yace bari in fada Mata
Yace to tare da barin gun


Kwance take kan bed dinta tana aikin nata wato tinani ta ramai sai dai ta kara fari Saudat ta shigo tace aunty Hameeda wai kizo in ji uncle Hamed
Mikewa tayi daga kan gadon tace wani Uncle Hamed din Dan bayi tinanin zuwan shi yanxu ba

Saudat tace uncle Hamed din ki mana

Hameeda tace to gani nan daman sanye take da daguwar riga atamfa sai kawai ta gyara fuskan ta ta yafa gyalan ta ta fito dan Momy Bata Nan ta tapi gaishe da mara lfy a asbiti shiyasa kawai fitowa tayi..

Jingine yake da jikin motar shi ta fito tinda ta fito yake binta da kallon har ta iso gare shi tayi mai kyau sosai sai dai kaman ta ramai ya fada Yana sakin Mata murmushin shi yace my Hameeda
Tace naam my Hamed Ina yini
Ya amsa sannan yace baki da lfy ne hameeda in na Kira wayanki baki dauka sannan kuma yau sai kika kashe wayan?

Ta shagwabe fuska tace haba to wani tambaya kake son In amsa
Yace dika mana
Tace to bani da lfy ne shiyasa Ni wayan ma kwana biyu ban dauke ta ba

Yace ayya my love shiyasa nima asha Banda lfy
Hey guys ka manta dani ko cewar Fahad da yake fitowa daga mota
Ina yini Hameeda ta fada tana sanya kanta kasa

Fahad yace lfy lau amaryan mu ya kk ya hutu

Tace alhmdllh
Yace to haka ake so

Soyayyar su suke sha Dan ita Hameeda har ta manta da wani aure da aka ce za'a Mata tinda taga sanyin ranta





Be sararamata ba sai da ya kwashi awa biyu sannan ya d'akata wani wahalan kuka ta saki ji take kaman ta mutu Dan azaba ko kallan ta beyi ba yace ta tashi ta bashi guri dan Yana da baki yace ta tapi zata ga aiki da cikawa sannan kudin aikin ta dubu hamsin hakan Nan tana kuka ta ciro kudin shi ta bashi sannan ta maida kayan ta ta fito a bukan
Haj zuwaira ta tare ta da Haj ya naga kin dade
Wani mugun kallo ta watsa Mata sannan ta shige mota jikin ta dik ciwo yake Haj zuwaira na ganin haka ita ma ta ciga Bata ce Mata komai ba har suka kawo gida ta fitowarta ba tare da ta kula ta ba
Haj zuwaira yace kajin min Mata waye ce kike da zaki dinga min fushi mtsww ta ja tsaki tana fitowa daga motar Bata bi bayan ta ba sai ma hucewar ta gidan ta da tayi cike da haushin fushin da maman Nusaiba keyi da ita......





Haka suka gama Shan hiran su ta soyayya sannan ya Mata sallama ya tafi ita ma ta koma gida sai sannan ma Hameeda ta tina da auren yay Yazeed din da za'a Mata wani haushi ne ya kamata tace Wallahi bazan taba auran ka ba yay Yazeed na tsane ka....

Washe gari.....











*comment*
*vote*
*share*











Aunty baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺



💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA* 💅🏻







®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼






*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻







*Bismillahir rahmanir rahim*







*page* 2⃣2⃣to2⃣3⃣






Washe gari.

Hameeda ta tashi da wani irin ciwon ciki da duk wata takeyi, kuka sosai takiyi dan dama bai Mata da wasa kuma duk wata takeyi.

Mamy ce ta shigo dakin hannun ta rike da kofi tace "Hameeda tashi ki Sha wannan maganin kafin yayan ki Yazeed ya fito sai ya miki allura".


Tashi Hameeda tayi tana matsa kwala tace, "Momy dan Allah karki Kira shi Wallahi bana son allora" .


"A dole kuwa a miki kin San da ita d'aya ce ke saukan miki da wannan ciwon,"

Maganin ta amsa tasha sannan ta koma ta kwanta ita kuma Momy ta fita Kiran yay Yazeed.




Maman Nusaiba kam tana shiga D'aki toilet ta wuce tayi kwanka sannan ta gargasa jikin ta dan ba karamin ciwo yake Mata ba.


a zuciyarta kuwa in banda tsine ma Haj zuwaira ba abinda takiyi dan Bata gaya Mata sai ya kwanta da mutu ba aiki keyi da baza ta ba sai dai ta nemi wani bokan. Haka dai take ta zancen zucinta har ta fito daga toilet din .

Nusaiba ta Tarar a kwance kan bed dinta tana chatting kallon ta tayi taga chatting dinta take hankalin ta kwance
tace Nusaiba" wai bakin San na dawo bane" ?

Kallon ta Nusaiba tayi sannan tace "au ashe fita kikayi ai ban sani ba , yauwa mama dan ban dubu goma wata kawata ce zatayi birthday shine zan siyan Mata gift".

Wani kallo maman Nusaiba ta zubama Y'ar tata sannan tace "da kin San inda naje da baki camin in baki kudi ba". ta fad'a ranta bace


Nusaiba tace "to mama Ni Ina ruwa na da inda kika je, Ke daman in dai mutum zaice ki bashi kudi sai kin mai masifa". ta fad'a tana k'ok'ari tashi a gurin .


Maman Nusaiba tace "haba Nusaiba Dan ke fa naje in da naje Amma kike k'ok'arin fata min rai".

Nusaiba dai fitan ta tayi bata tsaya taji mai take cema Mata ba.


Yaya Yazeed na kwance a D'aki shi yaji a na knocking,
yace "waye"?

Momy tace "nice Yazeed bude min"

Tashi yayi yaje ya bud'e k'ofan sannan yace "au Momy"

Momy tace "Yazeed Hameeda ce ciwan ta ya tashi kasan dai yanda take Shan wahala ga ta can sai kuka take". ta qarashe zance muryarta a sanyaye .

Yace "to Momy muje in duba ta" .


Tana kwance sai faman kuka take tana kiran Abbu zata mutu sai gashi ya shigo, kallon ta yayi a zuciyar shi yace "jibeta ciwan ciki take ma wannan kuka" .

Momy tace"Hameeda tashi ga yayan ki yazo duba ki".

"Hmmmm Ni Wallahi momy bana son allora kuma kin San ita zai min pls Momy ya tapi kawai" .




Dan k'aramin tsaki yaja sannan yace "kin tashi ko sai jikin ki ya gaya miki".


"Wayyo Abbu ka zo ga wannan mugun zaimin allora wayyo Meme wayyo Allah na," haka Hameeda ke ta fad'i sai kace taga alloran ma a hannun shi

Momy tace "Allah hameeda ranki zai baci".

Yay Yazeed yace "barta Momy ta tashi ta biyo Ni D'aki Dan ban fito da kayan da zan duba ta ba" .

Hameeda tana jin haka ta gane akwai muguntar da zai hada Mata, tace "Aa ka bani magani kawai" .

Ko kallon ta beyi ba yayi fitar shi, dole yasa ta tashi tana mai zubar da k'wallah...



Ko da suka je allura taka ya dauko Yana sanya maganin a cikin ta sannan
yace "ki matso dan Ina da abinyi in kuma baki so shikenan ya daga kafad'in🤷‍♂ sa".

hawaye ta share sannan ta matsa kusa da shi ta tsaya
tace "to gani".


Alluran ya saita sannan ya janye rigar ta ya fara Mata bako tausayin Dan in ya tina mgn da ta gaya mai sai yaji wani mugun haushin ta.


ita kuwa kankame jikin ta tayi hawaye wani na bin wani.....




Yana gama Mata ko mgn be Mata ba ya huce abin shi.


Tana bin bango har ta fita daka part din taje nasu Dan ciwan ya fara Mata sauki. Nan kuma jinin ya fara zuwa shiyasa take saurin ta koma D'akin ta gyara jikin ta........





Yaya Areef ne zaune a parlour su yana aiki a laptop dinshi, sai Fadila ta fad'u mai a rai yace ya gamata fa yayi mgn da yariya da tin randa akai mgn Nan be qara sata a ido ba. tashi yayi ya fito ya nufi part din su Fadila Yana zuwa dai dai kofan ya hadu da su Mubeen suna ball,
Yace "Mubeen zonan" .
Mubeen "yace to yaya"
Yay Areef yace "Fadila na nan"?.
Mubeen yace "eh tananan".
Yace "Kira min ita kace ta samaini a D'aki na".

Mubeen"yace to yaya".


D'akin Fadila Mubeen ya shiga Daman ta fito wanka kenan,
yace "Aunty wai yaya yace ki zo yanxu".

Fadila tace "wani yayan"?.

Yace "Yaya Areef, yace kuma ki samai shi a D'akin shi".

Fadila tace"to naji".

Shiryawa tayi cikin atamfa riga da siket sun Mata kyau sosai, ta fito ta nufi D'akin nashi .


Tana zuwa ta fara knocking.
yace "yes come in".

Shiga tayi da sallama a bakin ta,
ya amsa Yana Wani watsa Mata wani shu'umin murmurshi....

Ita sai taji duk ta tsargu, kallon ta yake kaman yau ya fara ganin ta
Tace "Ina yini".

Yay Areef yace "lfy lau, Fadila kin tashi lfy"?


Tace "alhmdllh" .kanta na k'asa "tace kace in zo" .


Yace "eh Fadila dama tambayanki nake San inyi" .



Tace "Allah yasa na sani".




Yace "Fadila kinji yanda big Daddy yace ko, to ke mai kika ce Ina Sona ko baki Sona ki bada min tsakanin ki da Allah" ya qarashe mgn Yana kallon fuskan ta.


Tace "yay Areef Ni........





To fa Fadila ko mai zatace 🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺



💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻







®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻



*Dedicated to babu shi a zuciyata fan's 2*


Wannan shafin nakune kuyi yanda kuke so dashi Ina Jin dadin comment din ku💃💃💃💃💃💃 Allah ya barmu tare🥰😍😍




*Bismillahir rahmanir rahim*






*page* 2⃣4⃣ to2⃣5⃣




Tace "yay Areef Ni na yarda da zaɓin da big Daddy ya min Allah yasa hakan ne Mafi Alkairi"


Wani irin sanyi yaji a zuciyar shi, Dan be taba tinanin Fadila zata amince da wuri ba...

Yace "gaskiya Fadila naji daɗin amincewar ki Allah ya miki albarka"

tace"ameen yay Areef Ni bari in tafi"

Tashi yayi yace "to muje in raka ki"

Tace "la, yay Areef da kayi zaman ka"

Yace "Aa ni dai muje"

Tafiya suke cikin farin ciki da annashuwa dan ba qaramin daɗi yake ji ba yau dinnan, suna zuwa kofan D'akin su.
Yace "Fadila Ni na huce sai na Kira ki"

Kanta a kasa tace "to yay Areef" sannan ta shiga dikin su....




Big Daddy ne zaune a D'akin Haj jadda suna magana akan yanda bikin zai kasance Dan yace Mata ya tsayar da rana wata hudu, lkc su Hameeda sun gama exam,


Haj jadda tace "to Allah ya kaimu lkc yasa kuma ayi da mu"


Big Daddy yace "ameen"



Hameeda da uncle Hamed kuwa suna Shan soyayyar su dan har yanxu baban Hamed be samu lkc zuwa gidan su Hameeda ba, ita kuma Hameeda Bata gayamai an Mata miji ba


Yanxu kowa na gidan yasan an tsayar da biki wata hudu, har yanxu kuma ba wata jituwa tsakanin yay Yazeed da Hameeda sai ma tsanar juna da sukayi duk abinda zai hada ta da shi bayi take ba shima haka, shiko yay Areef da Fadila kaman zasu had'iye juna Dan so


Fannin Nusaiba da Nabil ma dai sai a hankali dan be taba zuwa ba sai dai ya Kira ta a waya wayan ma ba wani firan arziƙi suke ba ita tayi shuru shima yayi shuru har ya gaji ya kashe dan shi baya daukan raini




Bayan sati uku



Yay Yazeed ne zaune a office ɗin shi Yana duba marasa lfy, sai ga wata yarinya ta shigo fara ce sosai Amma daga gani tana qarawa da mai,

Tace "Dr Yazeed Ahmad, ashe daman zan ƙara ganin ka Kai Amma yau sai na tasa a cikin tarihin rayuwata"

D'aguwa yayi ya ga kaman yasan mai muryan ai kon yana ganin ta,
yace "Yusura?"

Tace "naam Yazeed ai Wallahi ba haka alkawari yace ba tinda muka dawo shikenan baka k'ara nema na ba kuma dai kasan yanda nake sonka Yazeed Wallahi har yanxu sanka be fita a zuciyata ba I love you I love you so much my Yazeed"


Tinda ta fara mgn yake kallon ta yace "lallai Yusura har yanxu kina Nan da shirmanki ko"?


Tace "wai Yazeed yaushe zaka gane Ni masoyiyar ka ce ta asali kullum Ina kawo ma Kaina kana yar fa Ni Amma bazan gaji da nuna maka ina sonka ba"


Yace "duk ba wannan ba yanxu dai ga guri ki zauna"


Zaunawa tayi a gujeran da ya nuna Mata sannan, tace

"Yazeed da fatan dai bakai aure ba dan Wallahi duk mace da tayi kuskuran auran ka to wallahi....."

Bai bari ta k'arasa ba yace "haba yusura wani irin mgn kike haka Ni tin muna makaranta na gaya miki ki cire Ni a ranki Ni bana sonki kuma iyaye na baza su bari in aure ki ba pls ki cire ni a rayuwan ki kinji yusura pls" ya qarashe zance da alaman lallashi



Wani uban ashar tayi sannan tace "Wallahi Yazeed qarya kake dole ka soni Wallahi sai ka aure Ni Yazeed mai kake so inyi ma Wanda zaka aure Ni Allah Ina sonka Ina sonka Yazeed in ban aure ka ba zan iya mutuwa" tana magana ne tana kuka


Wani irin mugun tausayinta ne ya kama shi yasan yusura tana son shi Amma shi halayanta ne baya so kuma Yana tinanin ma da wuya iyayan shi su yarda ya aure ta, Dan yusura wayaryiyace ta karshe tun suna Landon take son shi tasha fada da mutane sabida shi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment