Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba Ina cikin tashin hankali, Hameeda kece farin cikin Hamed Allah ya rasaki zai iya rasa ransa gabaki daya Yana fada hannun shi dafe da zuciyar shi ".


Habawa Hameeda ai sai taji ta kaman a sama gajemare

"My Hamed Ni da Kai mutu ka raba takalmin kaza wallahi duk randa aka rabani da Kai an rabani da Raina ina sonka kaman Raina......





"Hameeda! Hameeda!! kizo mu shiga class fa ko so kike a hanamu yin test din ku da soyayya Bata isar ku"

Fadila ce mai mgn .



Uncle Hamed yace "oh sister mu kiyi hkr yanxu zata zo ".

Hameeda tace "my Hamed na tapi sai mun fito daga test ".

Uncle Hamed yace "to my sarauniya sai na shigo dan yanxu zan shigo class din ku in muku English da fatan dai kinyi karatu sosai duk da dai nasan my Hameeda akwai kwakwalwa".

Hameeda tace "hmmmm my Hamed kenan ".

Har bakin class din su ya rakata sannan ya huce office dinsa yana tinanin shi fa wallahi gwara ya je gidan su Hameeda yayi mgn tun wuri Kar ya tsaya kallon ruwa kwado ya mai kafa dan in ya biyewa Hameeda sai wani ma ya riga shi dan kullum sai in yayi Mata mgn sai tace wai sai ta gama secondary to Allah shi ya gaji haka dai yayi ta surutun shi shi kadai .

******

Yay Yazeed ne yayi Shirin shi na zuwa aiki suit ne fari ajikin shi gashi nan nashi kaman na larabawa yasha gyara yay Yazeed dai fari ne sosai, Yana da tsawon Kashi, Yana da dan fadi daga saman, in ba kaji Yana hausa ba sai kace ba bahaushe bane fuska nan tashi murtik dan kafin kaga Yana dry da aiki sai in yna tare da iyayan shi maza Amma in ba hka ba ka dade baka ga dryn shi ba fitowa yayi daga part din shi hannun shi dauke da jakan aikin shi ,dayan kuma rike da faran riga ta likitoci kenan motan shi ya nufa an wanke mai ita sannan yasa kayan aikin shi a ciki ya nufi part din Haj jadda .


Salama yayi Haj jadda tace ,

zaune a daya daga cikin kujeran parlour ta zubama tv ido Kai kace tana jin abinda ake fada ,

"A'a gaka miskili daga Ina kuma ".


Yay Yazeed yace haba matas sallama nayi Amma baki amsa ba kin fara wani waye miskili... ?"

Haj jadda tace " yo ni Ina ruwana da sallaman ".


Yay Yazeed yace " au haka zakice to in kuma in da na fito ".



"To ka koma mana ".



"Hmmmm haba matas wai waya tabokine?"

" Ni tashi ka ban guri ace yanxu duk iyayan ka ba mai ma f'ada ".

"F'ada kuma Haj jadda mai nayi ".

cewan yay Yazeed yana dan murmushi .



Haj jadda tace " kayi aure kaki yin aure kafi so har sai kanin ka Erif yake ko an anreef yayi ya barka ".


"Hhh Haj jadda ke har yanxu baki iya Areef ba "?


Haj jadda tace "hmmmm to suna ne kaman na aljanu baza a sama yara sunan mu nada ba sai wa'in Nan sunan banzan ".








*Gaskiya yau na muku typing da yawa qila ma har da na gobe*๐Ÿ˜„










*Comment*
*vote*
*share*






Aunty Baby ce โœ๐Ÿผ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ

๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป



๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
*_ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*๐Ÿ“šโœ๐Ÿผ

[โ„Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]


*_DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @_*
_*AboriginalWrtersAsso.*_





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ




*Dedicated to my only son Areef*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ



*Bismillahir rahmanir rahim*


*page* 6โƒฃto7โƒฃ


Ko da su Hameeda suka tashi a school sai suka fito Gate din mkrt su uku da Fadila da Hameeda sai kuma wata class mate din su zarah suna tafiya suna fira .


Sai ga motan uncle Hamed nan yayi parking kusa da su ya fito Yana kallon Hameeda Yana Mata wani shu'umin murmurshi yace,

" Hameeda shine ko ki jirani ko".....



"Hmmmmmm my Hamed kasan ba Ni daya bace shiyasa ".




Yace " to naji yanxu dai kuzo in qarasa da ku gida".




"A'a wallahi Karmu baka wahala ".

cewar Fadila tana kallon Hameeda taga ta yarda ko Bata yarda ba sai taga Hameeda ko a jinkin ta ma .



Yace "my sarauniya dan Allah Kar kice min Aa nasan haka zaki ce ".


Hameeda tayi murmurshi kawai Bata ce komai ba.


Ya bude Mata gaba yayi Mata alama da hannun shi ta shiga su kuma su Fadila suka shiga baya .

Motan tayi tsit ba mai mgn sai can yace "my sister ya test"?


Fadila tace "alhmdllh".


yace " yayi sauki ko"?

Fadila tace "ummmmm ba wani sauki ka zuba mana questions dik naka ma yafi zafi ".

uncle Hamed yace "haba dai my sister ".


Hameeda dai tana jinsu Bata ce komai ba har suka qaraso gidan su dan gidan su zarah na bayan gidan su ne
Su Fadila suka bude suka fita suna mai godiya .

yace "ba komai".

Hameeda zata fita yace yana son mgn da ita tace to tana gyara jakan ta na mkrt a jikin ta.



Yaya Hamed yace "Hameeda".


Yanda ya Kira sunan sai da tsigan jikin ta ta tashi .


Hameeda tace " Na'am ".



Yace "wai ya kike so inyi ne kullum na miki mgn akan in Toro iyayan na ayi mgn auran na a huce gun Hameeda wallahi ban San in rasa ki Dan in na rasaki kaman na rasa Raina ne kuma jiki na na bani za'a kwace min ke pls rabin Raina ki taimakawa masoyin ki".

ya qarasa zancan muryan shi na rawa




Tinda ya fara mgn Hameeda take kallon shi har ya gama sannan tace ,

"my Hamed Ina sonka Amma bana son inyi aure ban gama secondary School ba kuma in Sha Allah ni matar kace ba mai rabamu har mutuwa sai dai ta dauke mu tare....... "

Yace "to Allah yasa ".


Hameeda tace " my Hamed bari in huce Kar momy ta jini shuru su Fadila har sun shiga gida ".

Yace " to sai munyi waya ki kula min da kanki kinji".

kai kawai ta daga mai.

yace "bye my dear I love you Hameeda".

Tace "love you too my Hamed ".

Ta bude murfin motan ta fito .


Fitowan da tayi yayi dai dai da zuwan yay Yazeed wajan.


Yaya Yazeed na cikin mota ya hango Hameeda tana fitowa a mota kuma har ta tsaya ta gilas din mota tana daga mai hannun haba ai be San lkc da ya fito a motan ba.

yace"Ke"



Hameeda dake tsaye bayan ta gama dagawa uncle Hamed hannun taji ance "Ke" ai sai da hantar cikin ta ta kada .


Yac"e daga gidan uban wa kike sannan wani shegine ya sauke ki a mota ".


Dik wannan tambayan da yake Mata ta kasa amsa ko daya

Yace "ba mgn nake miki ba "?


Bakin ta na rawa tace "daga mkrt ".

"Mkrt shine ke daya ko Daman ke daya ce ke zuwa mkrt ?"

Hameeda tace " A'a ai tare muka dawo ".



"Zaki ci ubanki ne in baki gayamin gaskiya ba , wuce muje gida."

jikin ta na rawa suka fara tafiya ai da sauri sauri take tafiyan Dan ta wuce part din su suna shiga Gate din gidan yace ,


"part dina zaki huce ba naku ba ".

ai gaban Hameeda ya rasss


Yace "way ba mgn nake miki ba shigiya mai fuskan aljanu wato maza kike bi ko ".


"Maza cewan Hameeda".


Yace "in ba maza ba mai bazaki tahu tare da Yan uwanki ba sai ke daya to yau Allah ya tona asirin ki Daman wannan rawan ka naki ai ba'a banza ba ".




Hameeda tace " wallahi sai Allah ya min sakaiya kuma ka tambaya Fadila in ba tare muka dawo ba......."

Yaya Yazeed yace " zaki rufe min baki ko sai nayi kwallo da ke banza yar isaka ".



"Kuma yau sai kin gane kuran ki dan har big Daddy Alh Ahmad sai yaji tinda aure kike so ba gwara su miki ba kuma ki huce muje kafin jikin ki yayi tsami".

Hameeda na hawaye ๐Ÿ˜ญ ta huce part din Yaya Yazeed a zuciyar ta kuma tana tsine mai suna shiga ya rufe kwanfan harda sa key ya zauna a gujera ya daura kafa da kan daya yace,

" zo ki zauna a nan".

ya nuna Mata kasa zaunawa tayi ,

sannan yace "uban mai ya shigar dake motan wani namiji da ba dan gidan nan ba".


Hameeda tace " wallahi Yaya Yazeed uncle din mune na mkrt kuma ba Ni daya bace harda Zarah da Fadila ".




"Wallahi in baki fada min gaskiya ba sai na Zane ki ".


Hameeda ta qara fashewa da kuka tace "wallahi kuwa gaskiya na fada ma kuma ka Kira Fadila ma....... "



Marin da taji ne ya hana ta qarasawa.

" dan ubanki baza ki bada min gaskiya ba sai na balla ki.....

.Kiran wayan da akayi ne yasa shi tsayawa daga Marin da zai Kara Mata wayan ya ciro a aljihun wandon shi Yana dubawa yaga abbu Daddyn su Hameeda ya dauka cikin ladabi yace ,

"abbu barka da rana"

" eh abbu to ok Allah ya dawo da kai lfy shikenan to a huta lfy ".





Yace " wallahi Hameeda in baki fada min maye tsakaninki da Wanda ya ajeki a mota ba yau sai na balla ki ".



Muryarta ta dashi sabida kuka tace,

" wallahi uncle dinmu ne kawai ".


Yaya Yazeed yace "Allah ya kaimu gobe zanje mkrt inji wani dalili malami zai dauki daliban a motan shi har ya kaita gida".

Hameeda tace "Allah ya kaimu ".


Yace " tashi ki ban guri kafin in basa miki Kai ".



Tashi tayi tana Allah ya saka Mata kuma wallahi gobe ko ya zo mkrt zata nuna Bata San shi ba .



Har takai bakin kofa yace "ke" juyowa tayi batare da ta amsa ba .

Yace " zo ki gyara min d'aki sannan ki wanke min bedroom wallahi in d'akin Nan be gyaru yanda nake so ba hmmmmmmmm Allah kadai yasa dukan da zan miki".




Hameeda tace "yay Yazeed banci abincin ba kuma Wallahi yenwa nake ji dan Allah ka bari zan gyara ma daka baya ".




"Dalla malama ki huce ki fara abinda na saki ".


Hucewa tayi tana yi tana kuka har ta gama tace mai ta gama. Hannun kawai ya daga Mata alaman ta tafi ta bashi guri .






Momy kon taji Hameeda shuru sai ta Kira Fadila tace ko Hameeda na part din sune dan Bata shugo ba kuma taga kowa ya dawo daga makaranta Fadila tace Bata Nan kuma tare suka shigo gida Bata fadawa Momy a motan uncle Hamed ta barta ba ok tace shikenan qila tana part din Haj jadda dan dama tace Mata ta je ta gaisheta






Fadila na fitowa daga part din su Hameeda Gate din gidan ta nufa ta bude ko zataga Hameeda Amma shuru sai ta dawo tana tinanin Ina to Hameeda taje.............












*Wallahi naso muku mai yawa Amma waya ta sai hawan chaji ya kamata sai Allah ya kaimu gobe I love you all my fan's*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹







*comment*
*vote*
*share*






Aunty babyโœ๐Ÿผ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ


๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป



๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
_*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_๐Ÿ“šโœ๐Ÿผ

[โ„Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]


_*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersAsso._*





*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿผ





*Dedicated to Ummu Irfaan, maman khady, and ummu Sadeeq.*๐Ÿ˜

*wannan page naku ne kuyi yanda kuke so da shi naji dadin comment din ku na jiya Allah ya bar kauna*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ



_Musu min mgn ta private Ina godiya Allah ya bar zumunci kuma Ina mai basu hkr da jiya ban samu Daman amsa su ba_.




*Bismillahir rahmanir rahim*




*page* 8โƒฃto9โƒฃ





Fadila tace Ina to Hameeda taje.............





Hameeda kuwa tana fitowa daga part d'in Yaya Yazeed part d'in su ta wuce.




Sallama tayi Momy da ke fitowa daga bedroom d'in ta ta amsa sallama tana kallon Hameeda da jikin ta asanyaye .


Momy tace "Hameeda daga Ina tinda kuka dawo daga makaranta baki shugo ba?".




Hameeda tace.

"Ba Yaya Yazeed bane ya sani wai in gyara mai D'aki Wallahi kuma yunwa nake ji ".



Momy tace " To ga abincin can kan daning".


" To".

kawai hameeda tace ta wuce .



Maman Nusaiba ce zaune a parlour ta tana waya da qawarta Haj zuwaira .


tace.

"Wallahi haj nima haka nake son ayi dan yaron yanxu kudi na shigo mai sosai".

Haj zuwaira tace.

" To ita Nusaiba na so"?.

"Yo Haj Ni Ina ruwa na da wata so mu dai kawai ta yarda ta aure shi mu zamu kudi."

Haj Zuwaira tace ." Ai in ma Bata yarda ba gurin bokan nan zamu je shi zai sa ta yarda ".

maman Nusaiba tace "Allah Yar gari "?

Haj zuwaira tace " Allah kuwa ".


maman Nusaiba " Tace haka za'a yi zan Kira ki dik yanda mukayi da ita".


Haj zuwaira tace " To shikenan ".




Big Daddy ne da abbu suka dawo D'aki Haj jadda zuka huce .



Tana zaune a parlour kaman kullum tana basgar goron ta su Daddy suka shigo.


Haj jadda tace " A'a kaga mutanan Abuja".

abbu ne ya zauna gujeran da Haj jadda take yace,

" Haj kina lfy ya muka samai ku ".

Haj jadda tace " lafiya lau Yusuf ya aikin".

abbu yace . "Alhamdulillah".

Haj jadda tace " Madalla ".


Daddy yace " Haj Ina huni ".

tace "Lafiya lau"....




Haj jadda ta gyara zama ta fara mgn.


" Daman akan yaron nan Yazeed ne ".

Abbu yace "Badai laifi yayi ba ko Haj "?

Haj jadda tace. "A lallai mai d'a baza ka tsaya in fada ma abinda ake ciki ba zaka fara wani ba laifi yayi ba to ku dai kuka sani aure nake son yayi yaro ya zaman mana gardi a gida to Wallahi ko mai aure"......


Ba Abbu ba har Daddy sai da yayi dry way ya zaman musu gardi a gida Kai Haj jadda da rigima take.


Abbu yace "Karki damu Haj in Sha Allah za'a mai".

Haj jadda tace "Da dai yafin muku sauran kuma yaran Nan su Nusaiba su ma dik ku musu auran aca gida dik yara ba aure Kai Allah ya shirye ku".

ta fada tana tashi a guri Ni bari inje in kwanta. Daddy da abbu suka Mata sallama Suma kowa ya huce part din shi .



Abbu ya shiga part din maman Nusaiba tana zaune ko alaman tashi batayi ba sai da ya shigo parlour sannan tace ,


"Alhaji sannu da hanya".

yauwa kawai yace yana zama kan kujeran parlour.



Abbu yace " Ina yaran Nan ne banji su ba "?


Maman Nusaiba tace Duk suna D'aki su".

yace "Kira min su".

tashi tayi tana cewa ai ka dawo kenan kuma mutum bashi da hutu mtswwww tayi tsaki .


In baku manta ba Daman nace muku yaran Hajara hudu ne Shamsiya da Nafisat sunyi aure sai kuma Areef da Nusaiba .




D'akin Nusaiba ta nufa ta fara kwankwasawa Nusaiba na waya da wani class mate din ta Imran taji ana buga Mata kofa tace waye?


Maman Nusaiba tace "Uwarki ce Nusaiba".

tace "Kai mama menene kuma"?

" Ki bude mana wai".

cewar maman Nusaiba tashi tayi tana wai ko mai tazo yi min D'aki oho Mata budu D'akin tayi maman Nusaiba tace ,

"Abbun ku ke Kiran ki kinsan shi da naci in baki zo yanxu ba ya dinga Kiran ki kenan."

Nusaiba tace "Kai shi abbun na daga dawowar shi har zai fara ta kurawa mutane".

(gaskiya iyaye Mata muna da sakaci wajan nuna ma yaran mu matsayin uba a gare su yin zancen uba Mara kyau a gaban yaro nasa yara su Raina mahaifin su Dan Allah mu kiyaye )



D'akin Areef ta nufa Amma be dawo ba


Nusaiba na zuwa ba ladabi balle biyeya tace "Abba gani ".


Abbu yace "Yaushe ne zaku fara zana jarabawar ku Nusaiba"?

tace "Ni dai ban sani ba amma dazu mukayi test. "

Abbu yace " Allah ya taimaka ".

tace ameen tana tashi a gurin .


Abbu ya kalla agogon hannun shi yace Hajara Ni na tafi in kwanta ko kala Bata ce mai ba ya qara cewa way ba mgn nake miki bane ?


Hajara tace "To mai zance "?

Alh yace "Wai Hajara yaushe zakiyi hankali ke kwata kwata baki girma to Allah ya shirye ki".

Yana gama fadan haka ya huce abinshi Daman a D'akin Momy ya ke .




10:30 Yaya Yazeed ne ya fito daga motan shi daga gani daga gun aiki yake part din memen shi ya tafi Yana shiga ya tarai da Daddy ma Yana Nan suna zaune a kasan dadduma Daddy na cin abincin sallama yayi gabaki daya suka dago suna kallon tilon d'an nasu Wanda suke so da kauna cikin ladabi ya karason in da Daddy ke zaune shima ya zauna kusa da kafan shi yace,


" My daddy Ina huni ya kasuwan da fatan kana cikin kushin lfy"?

Daddy yayi murmurshin su na manya yace "My son lfy lau alhmdllh ya naka gun aikin".

yace.

"Alhamdulillah Daddy ".


Meme tace" Wato Kun matan da Niko lallai my son ta Daddyn ka kawai kake ".


Yaya Yazeed yace "Haba memena ya zan manta da ke ya matso in da meme take ya Dan kwantar da kan shi jikin ta ya memena na gaji da yawa Wallahi".


Daddy yace" My son wai yaushe zakai aure ne haba my son."...

Yaya Yazeed yace "Daddy kwata kwata shekarata nawa kuke min zancan aure 28 fa ne haba my Daddy".



Daddy yace.
"Hmmmmmm my son kenan zo muci abincin nan nasan baka ci komai ba".


Yaya Yazeed yace" To".


tare suka gama ci Yaya Yazeed ya musu sai da safe sannan ya tafi Yana tinanin mgn Daddyn shi wai aure haba sai kace wani babban mutum.........


Ko da abbu tafi part din su Momy ta gama hada mai komai na abincin Yana shiga ta tashi ta tare shi cikin murna da farin cikin shima haka.



Momy tace "Sannu da hanya abbun Hameeda da fatan ka dawo lfy".


abbu yace " Lafiya lau alhmdllh".


tace " To haka ake so ga abincin ka can Yana jiran ka ".

abbu yace. " Allah ya miki albarka Zainab".

Momy tace ameen


Hameeda tana D'akin ta taji kaman muryan abbun ai da sauri ta fito tana murna abbu da da hanya yace,


" yauwa my daughter kina lfy"?


tace " Lafiya lau abbu".

yace " To ya makarantar na tambaya Nusaiba tace kun fara test ko"?

Hameeda tace " Eh abbu ".


yace " To Allah ya bada sa'a".

tace "Ameen".


Saudat ma ta fito da gudun ta ta hau kan cinyar shi tana mai shagwaban da ta saba Hameeda ke Saudat baki girma Wallahi jiki fa a kan cinya sai kace wata qaraman yariya Abbu yace ai auta ce ki barmin auta ta ta huta Momy tace Saudat sauka Abbun ki yaci abincin ko Saudat tace to Momy Hameeda tace Abbu Momy good night Abbu yace night my darling daughter Momy ma tace sai da safe...


Washe gari


love you all my fan's ๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ๐Ÿ’‹







*comment*
*vote*
*share*







Aunty babyโœ๐Ÿผ

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ


๐Ÿ’…๐Ÿป *BABU SHI A ZUCIYATA*๐Ÿ’…๐Ÿป




๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌยฎ
_*ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION (YAN ASALI)*_๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

[โ„Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON'T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD*_
_*@AboriginalWrtersAsso.*_









*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*โœ๐Ÿป


_posting day:_
_Monday & Tuesday only๐Ÿ‘Œ_




Bismillahir rahmanir rahim





*page* 1โƒฃ0โƒฃ to 1โƒฃ1โƒฃ





Washe gari.


Yay Yazeed ne yayi Shirin shi na zuwa asbitin yayi kyau sosai.

wayan shi ne yayi ringing dubawa yayi ya ga sunan abbu, yace to abbu kuma da safen nan.

dauka yayi da sallama yace,

" Abbu Ina kwana."

Abbu yace " lfy lau my son ka tashi lfy".

yay Yazeed yace "lfy Abbu, "

Abbu yace "kafin ka fita asbiti ina son ganin ka."

yay Yazeed yace " to Abbu insha Allah ".

yana gama Shirin shi ya dau mukullin motan shi ya fito....


Part din su Hameeda ya shiga dan ansa kiran Abbu

yana shiga ya Sami Saudat a parlour.

yace "Saudat"


Saudat dake zaune tana home work tace,


" Na'am yay Yazeed Good morning".

yace "Morning ya kk Ina momy.. ?"

Saudat tace " tana kitchen tana hada breakfast."

yace " ok Abbu be tashi ba?

Saudat tace *eh be tashi ba."

yace ok... Gujera ya Samu ya zauna Yana duba waya...


Hameeda tace "Momy bari in fara shirya breakfast din tinda an gama hadawa..."


Momy tace " to shikenan daga Nan ki huce ki shirya Kar kiyi Letty."

Tace "to Momy.. "


dining ta nufa ta hada komai sannan ta fito parlour tana kiran Saudat.


Saudat ! Saudat !! way mutum yayi ta Kiran ki kina ji.


Saudat tace " haba Aunty Hameeda home work fa nakeyi.. "

tace "to dan kina home work shine baza ki amsa ba , to kije ki shirya dan ba jiranki zanyi ba."

Saudat tace " to Aunty.. "

yay Yazeed na zaune yana jin su ko kallo bata isheshi ba.


Abbu ya fito daga bedroom din shi yace,

" A'a Hameeda baku shirya makaranta ba?"


tace "Good morning Abbu , yanzu zamu shirya na taya Momy hada breakfast ne."


Abbu yace "to shikenan".



Yay Yazeed yace "Ina kwana Abbu. "

Abbu dake zama a doguwar kujera yace,

" lfy lau my son har anyi Shirin aikin? "


Yay Yazeed yace "eh Abbu.. "




Momy dake fitowa a kitchen tace,

" A'a Yazeed Kaine ?"


Yay Yazeed yace "nine my Momy kin tashi lfy".



Momy ta fadada murmushin ta tace,

" to ku taso muyi break dan nasan baka ci komai ba ".



Yace "to my Momy kaman kinsan kon banyi break ba..."

Hameeda dake tsaye haushi ya kamata wai da wannan dan rainin wayo za suyi break mtswww .

Momy tace "ke kuma lfy ki kike ma mutane tsaki.... "

Hameeda tace "wani Abu na tina Wallahi.. "

Momy tace "zo kiyi serving din mu mana ,"


Hameeda tace to.


Ta fara serving din su tana zuwa na yay Yazeed tace,

" mai zan zuba maka".

a daqile tayi mgn shima sai yayi kaman bai ji ta ba .

ta qara cewa mai zan hadama. Sannan yace kisa min tea kawai...


Abbu yace " haba my son Ina tea zai isheka."

Yay Yazeed yace "Abbu bansan abu mai nauyi ne da safe. "

Abbu yace " ok Amma kana dinga cin abincin."

To kawai yay Yazeed yace.....


Suna gamawa su Hameeda suka tashi dan shiryawa makaranta Momy ma ta mike dan kwashe abun da suka bata .



Abbu ya gyara zama Yana fuskantar yay Yazeed sannan ya fara mgn kaman haka.


"Yazeed" yaya Yazeed Na'am Abbu

Abbu yace "Ina so ka fito da matar aure nan da 3week sbd Haj jadda ta fara mgn dan haka Nan da sati uku Ina so ka fitar da Mata Suma sauran Yan uwanka Mata zan musu mgn Amma sai Allah yasa sun gama jarabawar su Dan daga Nusaiba har Fadila da Hameeda aure dasu zanyi... "



Ji yayi abin duniya yayi mai yawa har yaushe ya Samu matar aure nan da sati uku shi da ko budurwa bashi da ita kai wannan tsohuwa da rigima take ko Ina ruwanta da shi kwatakwata shekaran shi nawa da zata damu yayi aure.......


Yana cikin wannan tinanin ne yaji Abbu yana cewa,


" zaka iya tafiya Amma ka tabbatar sati uku na baka in ba haka ba dik Wanda muka zaba ma to Kai kaja. "


Yace " to shikenan Abbu Ni na tafi ".


Abbu yace Allah ya bada sa'a..


Yana fitowa daga part din su Hameeda part dinsu ya huce tinani fal. ranshi ya rasa yanda zaiyi gashi wai in be fito da Mata ba za'a bashi dik Wanda ake so Kai shi yaga ta kanshi...



Ya shiga da sallama Daddy Yana kan 3str Yana kallon labaran safe Meme kuma na hada mai shaye suka amsa sallaman suna kallon shi fuskan shi ba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment