Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka sauke su, amma ya ce
babu komai, kawai jikin sa ne bai masa dadi.
Sannan yana jin kamar baya sha'awar yin wasan.
Yakubu yayi ta kwantar masa da hankali, yana
kara koda shi tare da nuna masa nan fa garin
bayinsu suka zo.
***hhh wai bayinku,hada rai,dan karamin
tsaki,,mttssswww.. Maji magani****
Ya zama dole ya zage damtse ya ba mara da
kunya, su nuna masu sun zo garin su, sun fi su
rawa.Ya ji ya amince da shawarwarin Yakubu,
amma ba su cire masa damuwar sa ba. Karfe 2
saura 'yan mintoci, gasa ta kankama. Naseer dai
ya hau doki ne. Alh. Basheer na ta yi masa
addu'ar samun Nasara. Yakubu ya bubbugi
kafadar sa ya ce,"Ja mu je, dan gidan Alhj, ba
wani bayan kai! Ya zaburi doki, ya fada sahu.
Duk dawakai sun jeru izini. Kawai suke jira su
tashi jimawa kadan aka ba su izinin tafiya. In ba
ka yi, ba ni wuri. Naseer fa ya cilla, sai dai tafe
yake yana tunanin zuci. Babu abinda ya fi masa
yawo a rai, sai zancan Zarah muryar ta yake ji
tana fad'in **"Ni kuwa yayana gani na ke duk
zance ka ke yi. A hankali za ka so ta!** Yana
tafe, yana girgiza kai da karfi, don bai son jin
muryar. Kamar ma karuwa ta rika yi. Shine akan
gaba,"Jama'a na ta hargowa, muryoyin su suka
yamute masa tare da ta Zarah. Kiris ya rage ya
iso karshe, bai san lkcn daya saki linzami ba, ya
kame kan sa, yana layi tare da kiran "Inna-
lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un! Duk su Alhj suka
kame kaf, suna hangen sarautar Allah. Ko kafin
su gama mamakin meke shirin faruwa? Naseer
suka hango yana mulmulowa kasa. Alh. Basheer
ya keto fili a guje, dukkan yaran sa suka rufo
masa baya, yayin da tuni 'yan taimakon
gaggawa suka kai wa Naseer dauki. Ya ji ciwo
sosai, in ban da jini, babu abinda ke fita ta
hanci ta baki. Kowa ya rude musamman Alh.
Basheer da Yakubu. Nan take motar asibitin ta
dauke shi zuwa asibitin Murtala, inda ya sami
taimakon Likita. Bayan an gama bincikarsa babu
karaya, inda ya ji raunuka, an daure su da
magani, sai Alhj ya dauko shi zuwa gida. Ba su
tsaya Zariya ba, kai tsaye Kaduna ya wuce da
shi asibitin Likitansa, yasa aka ware masa daki
na musamman shi kadai. Daga bisani ne suka
sanarwa duk wad'anda suka dace su sani,
musamman su Abba. Kan ka ce kwa6o? Asibitin
ya cika da iyaye da masoyan Naseer, duk da
dare ya fara yi. Anan Zaran da Nusaiba suka
fara haduwa ko da ganin junan su, babu
gabatarwa, take nan suka shaida junan su.
Nusaiba ta rike hannunta, ta nuna ta ga su
Alhaji. Ta gaida su cikin ladabi da girmamawa,
su ma suka amsa cikin fara'a, tare da nuna
kauna gare ta. Shi kuwa Naseer barci kawai yake
yu, bai ma san wad'anda suka zo ba. A daran
nan suka sake biyo hanya, suka dawo Zariya,
aka bar Abba tare da shi. Zarah da Nusaiba kan
ba su runtsa ba, saboda tunanin yanayin da
suka baro Naseer. Duk da cewa Likita ya ce da
saukin jikin amma abin akwai tausayi. Abu
kamar hadarin mota, ko ina ciwo. Haka hankalin
Alh.Basheer ke tashe, domin bai bar asibitin ba,
sai 12 dare, suna tare da Malam Balarabe. A
lokacin ne suke shawarar dole a rink'a yiwa
Naseer addu'a, saboda yanayin bakin mutane.
Don Yakubu ya gaya wa Alhjn labarin da Naseer
din yake fadi, kafina fara wasar. Washegari haka
su Umma suka dawo mota guda (Bus). Naseer
na kwance baya ko iya tashi, saboda tsamin jiki.
Komai da ake bukata, sun iske direba ya kawo
daga gidan Alhj. Bayan kamar awa daya, motar
ta juya da su Inna. Aka bar Umma da Zarah
tare da Sageer. Su Biyun ma kadai ke tare da
shi lkcn da Direba ya sake dawowa da Nusaiba
da Umminta. Ummi na gama gaishe shi, suka
sake fita tare suka bar Nusaiba tare da su.
Kowacce na zaune, sun tasa shi gaba. Sageer ya
dube su, yayi dan murmushi ya kada kai.
Naseer ya dago ido, ya ce,"Lafiya? Ya ce,"Lau.
Me aka yi? Ya amsa,"Gatan yayi maka yawa.
Kamata yayi ka mike kawai, ka ce ka warke. Ko
me ku ka ce tagwayen Jah-Jah? Lumshe ido
yayi, ya kauda kai, yayin da Zarah ke
fadin,"Gaskiya ne, amma don ragwanci ko motsi
bai iya yi." Nusaiba ta ce,"Ina fatan ma dai ya ci
abinci? Don na lura, baya son cin abinci." Ya
bude ido, ya kwada mata harara, in ban da
salo, yaushe ta san ban son cin abinci? Ya maida
idon ya runtse, yana wani gajeran tsaki. Zarah
ta cafe,"Babu 'yar tsaki anan yayana, ina jin
Abba na gaya wa Umma ko dan Tea kadan ka
sha. Ba tare daya bude idanuwan sa ba, yake
fadin,"Ai sai ku yi min dure."Ta ce,"Yanzu kuwa,
amarya hado min Tin ya gani, idan gatse yake
yi." Ta kuwa mike ta hado shi. Yana kallon su.
Sageer na ta dariya. Sageer dago mana shi." Inji
Zarah. Ya dubi Sageer din, ya kara daure
fuska,"Ta6a ni, ka ga yadda zan fasa ma baki."
Ya ce,"A hakan? A hakan kuwa." Nusaiba ta
ce,"A janye 'yar wasa, yakamata ka sha Tin nan.
Daurewa za ka yu." Ya rufe ido,"Na koshi." Da
anyi magana kuwa, sai ka rufe ido, zama da
yunwa ai wani ciwon zai sa maka." In ji Zarah.
Wani irin kallo yai mata, bai ce komai ba, ya
maida idon ya sake rufe shi. Shiru bai kara
tankawa kowa ba, har suka gaji da rarrashin sa
ya sha Tea. Alhaji na shigowa Nusaiba ta labarta
masa. Bakin gadon ya zauna ya ce Sageer ya
kama shi ya tashi zaune. Da kyar ya iya zama,
saboda ciwo ga takaici. Alh. Basheer yasa aka
miko masa kofin Tin. Ya debo a cokali ya
ce,"Ungo ka sha Naseer ciwo da yunwa
mazaunin su daya, gaba daya suke mukurkushe
mu2m." Malam Balarabe da Umma suna ta
murmushi. 'Yar kunya ta kama shi, ya sunkuyar
da kai." Kar6i mana, menene abin kunya, ni ba
Abbanka bane? Ya miko hannu ya kar6i kofin."
Zan sha Alhaji, kawo." Ya mika masa yana 'yar
dariya. Kur6a yake a hankali. Alhj na rarrashin
sa har ya shanye, a je kofin.
~~~~~~~~~~~~~~~
Sati 2 yayi a asibitin, shi kan sa idan zai fadi
tsakani da Allah, ya san shi dan gata ne, kuma
Alh.Basheer ba karamin so yake masa ba.Hatta
Hajiyar su Yakubu, miyar kajin turawa tayo masa
dakwale cikin kwano, ta kawo masa. A 'yan
tsakanin nan shakuwa tsakanin Zarah da Nusiba
tayi karfi sosai, sun fahimci juna kwarai da
gaske. Kausar kanta, ta yaba da Zarah kuma
tana mata kallon wacce za'a zauna lafiya da ita.
Shi kuwa uban gayyar tamkar ya dauke kan sa
ya maida gida yake ji, saboda ginsa da yayi da
zaman Kaduna. Abu mafi ban haushi a gun sa,
wanda yake k'ara sanya shi damuwa, shine
gaba daya aka hade masa kai. A ganinsa kenan
babu wanda zai kai wa kukansa, illah mutum
daya, watau Naseer B. Shi yasa daya zo asibitin,
ba shi da abokin hira, sai shi. Yayi ta yi ma sa
famfo, yana k'ara cusa masa kiyayyar Nusaiba a
rai. Koda aka sallame shi, haka a kodayaushe
Alhj ke tafe masa da abubuwan alkhairi., sai da
ya tabbatar da Naseer ga gyagije sosai.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Watannin 4 suka shude a
cikin wannan hali, babu abinda ya sauya a
zuciyar Naseer a game da auran Nusaiba. Yana
zuwa wajen ta, don bin umurin kawai, haka ya
kan kira waya, ya ce mata ya take? Sai dai idan
ta turo masa (Text) da ingatattun kalamai, shi
sai ya tura na shi babu komai ciki (Blank) Ga
musun tsiya, idan za ta shekara gardama, ba zai
ta6a sakar mata, dole ne ta yarda, ya turo sako,
wayar ta ce mai matsala. Saboda haka ne ta
daina ba ma kanta wahalar aika sako. Sai dai
abin yana bata mamaki yana kuma sanya ta a
tunani. Me yasa sauran sakwannin ke shigowa
dai-dai, amma ban da na shi?Musamman
sakwanin gaisuwar Ibrahim da take yawan
samu. Kodayaushe baya gajiya wajen aiko mata
da (Text) din gaisuwa da addu'o'i, wani lokacin
har da kalaman so da kauna masu neman
dagula lissafin ta. Haka nan take dauke kai, ta
fuskanci zabin Abban ta, koda sau daya, za ta
ga murmushi sa a sati. Wannan ta aje shi a kila
haka halittar sa take, miskilanci. Kuma haka
kawai, ta ji miskilancin yayi mata dai-dai, domin
ita kanta bata cika son namiji mai yawan dariyar
tsiya ba.
Karshen watan nan su Zarah suka kammala
jarrabawrsu ta karshe. Ko dama ita kadai ake
jira. Nan da nan shirye-shiryen biki ya kankama
musamman a Kaduna gidan Alh. Basheer. Ba
k'aramin gagarumin biki aka shirya ba. Gidan
daya ba su, tuni aka gama gyare-gyaran cikinsa,
aka fent shi ciki da waje. Sannan yasa aka zuba
tsaddadun abubuwan bukata na gani na fada
har sashin Zarah. Duk da haka Naseer ya kashe
wa Zarah makudan kudade wajen siya mata
kayan daki, musamman kayan kicin, kuma
kullum gaya mata yake yi ta rage shishshigewa
Nusaiba, don kar ta raina mata ajinta. Ko alama
Zarah bata son irun wadannan kalamai na sa, a
kodayaushe, tana nuna masa ita da zuciya daya
take kaunar Nusaiba.
Biki saura kwana 7, Alh. Basheer ya kira Naseer,
abinda ya gani ya daure masa kai, wasu kaya
setin akwatuna ne guda 2, gaba daya shakare
da kaya. Ummi ta bubbude masa daya bayan
daya,kafin Alhj ya ce. Wad'annan akwatuna seti
daya Zarah ne, daya kuma na Nusaiba ne.
Kamar yadda yake a al'ada, kowace amarya ana
kai mata. Wannan tsakani na da kai ne ko
Umminku na gargade ta, ban ce ta gaya wa
kowa ni ne na yi su ba, kai ne ka kawo wa
Nusaiba. Wancan setin kuma ka kai wa Zarah.
Shiru Naseer yayi, ya rasa ta cewa, domin
zuciyarsa cunkushe take fa mmkn Alhj. Watau
ya dai dage sai ya siye shi da karfin Naira. Kudi
shegu ne. Ya karkada kai,"To ni me zance
yanzu? Idanuwansa suka cika fal da hawaye. Irin
wannan hidima ko kallon banza na yi wa
Nusaiba, idan Abba ya sani, ai na kade, sai
ganye na." Bai san kwalla ya zubo masa ba, sai
da ya ji Alhaji ya dafa shi, yana fadin. "Haba
Naseer, menene haka? Kai ba Da na bane?
Kullum ina gaya maka hakan, amma kamar har
yanzu ba ka yarda da ni ba. Look! Ka na ji na?
Nusaiba kawai gare ni, sai Allah ya k'ara min da
kai, na kuma gode masa. To kai ma ka gode
masa domin kyautar daga gare shi take. Share
hawayen nan don Allah."Ya kai hannu ya goge
kuncin sa, yayin da Ummi ke fadin,"Namiji ai
jarumi aka san shi, kar ka ba matan ka kunya
mana." Ya kara sunkuyar da kai Alhj na dariya.,
Mai-gadi ya loda masa akwatunan a bout, shi
kuwa yana zaune, yana zuba godiyar karfin hal.
Nusaiba bata nan? Sun shiga gari da Kausar
shirye-shiryen biki." Saboda haka ba 6ata lokaci,
ya damko hanya, ya dawo cike da aljabi tare da
wasi-wasi wai kauna ce ta sa Alhj ke masa
hidima? Shi kam bai yarda ba, saboda 'yar sa
da yake son lik'a masa ne kawai.
****Kai jama'a nifa Naseer dinnan yafara bani
haushi****
Ga Abba tare da Umma, sun baje akwatuna ba
sa aikin komai, face sa albarka. Umma har
kwallanta sharaf-sharaf. Bayan sun natsa.
Naseer ya ce dole a kaiwa Zarah gaba daya
kayan, watau da nasa setin akwatunan da yai
ma ta., Abba ya ce hakan bai zama adalci ba,
zai fi kyau ya aje su, bayan sun tare gidansa, ya
raba masu kowacce ta kwashe kason ta. Umma
ma ta goya wa Abba baya. Akan dole Naseer ya
karbi wannan shawarar. A yammacin ranar.
"Yan-uwa da abokan arziki suka kai kaya gidan
su Zarah. Hakika iyaye da 'yan uwan Zarah sun
ga abin mamaki, domin sun ga kaya iya ganin
su. Su kuwa Abba da Umma a kodayaushe a
cikin dogiya da shi wa Alh. Basheer albarka suke
har zuwa ranar daurin aure, yayin da hidimomi
da dama na shagalin biki akai tayi a Kaduna da
Zariya. Nusaiba tana zuwa na Zarah. Ita ma
Zarar ta halarci walima da (Mother's day) a
Kaduna. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Ranar asabar
da safe karfe 11, aka daura auran Naseer da
Zarah. Karfe 2 dai-dai ita ma Nusaiba ta
tabbata mata Naseer, tun daga lokacin duk wani
farin ciki da ke zuciyar ango ya rufe kofar sa.
Wani irin yanayi daya rinka yi a wajen, shi ya
tabbatar wa Sageer lallai abokin sa na cikin wani
yanayi na daban, don haka ya ja shi gefe, ya
kare masa kallo, gaba daya idanuwansa jajur!
Suke. Ya sanyaya murya ya ce,"Ka ga yadda ka
dawo kuwa Naseer? Bai kamata ka rikide haka
ba a wajen nan, don ba haka aka san ango ba."
Ya sauke numfashi, a yamute ya ce,"Ban son
yarinyar nan Sageer, ka na zaton wasa na ke yi?
Mts! Yayi dan gajeran tsaki, ya kauda kai,
"Rayuwa ta vata damu kowa ba, sai shahalinku
ku ke yi, ni kadai na san abinda ke damu na. Ka
je ku ci gaba da hidimomin ku. Ka kyale ni
kawai." Jikin Sageer yayi sanyi, tausayi ya kama
shi, ya kamo hannu Naseer ya ce, "A hankali za
ka so ta mutumi na. Please ka jure, ka zama
namiji, kar ka mance kuma har da Zarah yau ta
ka ce, halas-malak. Yakamata ka gode Allah,
domin yayi maka kyautar da ba kowa ke samu
ba. Mata 2 a lokaci guda ko a zamanin da, sai
dan gata. Illar kawai da ba ka son Nusaiba.
Amma ina gaya ma za ka so ta, saboda yarinyar
bata da wata mishkila." Ya dauke numfashi."
Sageer ba zai gane ba, menene amfanin
maimaita magana 1? Ya fada a ran sa. Ya daga
ido zai ce wani abu. Kausar ya hango tana
dube-dube, da gani, su take nema, don haka ya
ce,"Ha sarkin kaudin can zuwa, da alama mu
take nema." Sageer ya juya, ko kafin su fito fili
ma, ta hango su. Wajen ta nufo,"Haba ango
kuma sai ka 6oye, ina ta billayin nema? Ya
ce,"Magana muke." Ta ce,"Ummi ce ta ce in
tambayi motoci nawa ku ka zo da su? Sageer ya
bata amsa." Akwai kanana 10, ga kuma wata
Bus can, sun isa ko a karo? Ta ce,"Bari na
tambayo. Ta sake duban Naseer." Ango! Ango!!
Ya dan murmusa, ya kauda kai, ta ce, "Har yau
din ma murmushi kawai zan samu? Bakin ango
ai baya rufuwa, balle kai mai Double. Zan so in
ga Competition din. Ni zan ba ka abinci a baki,
ni zan kai ka ka sha madara! Dole ta sanya shi
dariya. Sageer kam har da kyalkyawa. Ta wuce
da sauri, tana fadin " Ku jira ni, na tambayo,
Naseer ya gintse dariyar, ya ce,"Wannan 'ya da
tsanannan surutu take." Ya ce,"Ba ga shi ta sa
ka dariya ba? Mts! Ni yanzu ma zan sa6e." Ka je
ina? Ya ce, "Zariya zan koma." Wajen Zarah ko?
Me za ta yi min? Ban da ta k'ara 6ata min rai?
Ai duk bakin ku daya. Makullin Naseer B zan
kar6a, in je dakin sa, in huta awa 2, kafin ku
iso."Sageer yayi dariya, ya ce,"ANGO kenan, kai
wane hutu ka ke nema a wannan yamutsin? To
Allah ya kiyaye hanya, amma ka san duk taron
nan, saboda kai aka yi shi ko? Hakkin ka ne ka
ba kowa kulawar da ta dace." Ya ce,"Menene
amfanin ka? "Ba wasa na ke yi ba, tafiya zan yi
idan na ci gaba da zama wajen nan, jini na zai
hau. In wannan kwakwazon ta dawo, ka san
yadda za ka yi da ita. Sai kun taho. Kamar
wasa, haka Sageer ya saki baki yana kallon
Naseer ya amshi makullan Naseer B, ya wuce ya
fada mota. Jama'a da maroka na bin sa, yana
fadin yanzu zan dawo. Yana nan tsaye. Mamaki
ya kusan kashe shi. Kausar ta dawo ta shaida
masa moticin sun isa, idan ma da k'ari. Ummi
ta ce ba matsala. Abba ya ware wasu
masamman, don dibar jama'a. Naseer bai san
lokacin da barcin takaici ya sa ce shi ba, bisa
katifar Naseer B. Can a mafarki yake jin wayarsa
na bugawa. Ya bude ido da kyau, duk jikin sa
yayi tubus! Saboda tsabar gajiya, da gaske
wayar ta sa ce ke bugawa. Ya lalubo ta, ya duba
Sageer ne akan layi. Cikin muryar barci ya
ce,"Ya aka yi? Ya ce,"Me kuwa aka yi? Dan rainin
wayau. To mun iso muna fly-over yanzu. Idan
ka ga dama, mu hadu a can ,"Yanzu da gaske
kun dauko yarinyan nan." Haushi ya kama
Sageer, ya rasa me zai ce? Sai yayi tsaki ya
kashe wayar sa, ya ci gaba da tuki. Naseer ya
dubi agogo karfe shida da kusan kwata. Ya mike
da kyar, yayi mika, kansa kawai ya ji ya dauki
ciwo, ba kadan ba. A haka ya fito ya kulle dakin
ya shiga mota, ya nufi (Hanwa Low-cost). A
hanya ya kira wayar Umma, ya shaida mata
bakin sun iso. Nan da nan aka shirya kayayyakin
abinci kala-kala. Bus guda tare da 'yan tar6ar
baki suka tafi. Naseer na isowa. Jeep din Antin
Jordan na fakin. Ta fito da yaranta, wajen ta ya
nufa, ya dan rankwafa, yana mata sannu da
zuwa. Bakinta har kunne, ta bubuga kafadar sa.
"Angon Nusaiba. Angon Zarah. Ina ka shige, na
yi neman duniya, ban gan ka ba? Ya shafi k'eya,
ya ce,"Kira na aka yi nan Zariya, dole na dawo."
Anti ta ce,"Haka wannan abokin na ka ya ce,
"Dama an daura aure, ban ga ango ba, ko sau
daya, shi yasa na tambaya. To Allah yasa
albarka." Ya ce, "Amin." Ta wuce ciki, shi kuwa
ya wuce wajen su Sageer. Yana wa Allah godiya
da karyar sa ta zo dai-dai da wacce Sageer yayi.
Karfe 9 saura kwata aka kawo Zarah, a lokacin
bakin Kaduna duk sun juya, wadanda suka rage,
ba su fi mu2m 10 ba. Antin Jordan da kan ta, ta
jagorance su zuwa sashin Zarah. Bayan yan
kawo amarya sun gama ba ido su abinci, motoci
suka koma da su gida. Aka bar mu2m 3, suka
taya ta kwana. Haka ma Zarah ba karamin
mamaki ta sha ba da ganin dakin auranta. Ko a
mafarki bata ta6a tunanin irn sa ba, saboda
haka ta kwana yi wa Allah godiya tare da rokon
sa zaman lafiya dauwamanme. Washegari
safiyar lahadi, karfe 9 za'a gudanar da hawan
Yakubu. Sukuwa ta musamman wacce Yakubu
ya shirya. Filin sukuwa ya ci ka fal da Zaratan
'yan wasan tseren Polo daga ko'ina 'yan kallo
kuwa babu masaka tsinke maza da mata.
Alh.Basheer da tawagar sa ma suna wajen.
Tsofaffin 'yan wasa irin su Yakubu da shi kan sa
Yakibu su suka fara sharar fage, inda dokin
Yakubu yayi wa saura fintinkau. Daga nan
sukuwa ta ci gaba. Kowa na nuna bajintr sa,
abin gwanin sha'awa, sai wanda ya gani. Karfe
11 dai-dai, rana ta soma zafi, wasa ya zo
karshe, kamar yadda Yakubun ya shirya. Ango
shine zai rufe fili, don nuna farin cikin sa ga
dimbin masoyan sa da suka taru. Saboda haka
Yakubu ya mike ya dau lasifika yayi wa ango
kirari, ya kwarzanta shi, sannan yayi kiran sa,
"NASEER, ta so ka ja mu je! Yana mike wa, duk
wuri ya yamutse da hargowa da tafi, shi kuwa
kansa ne ya ji yana sara ma sa. Domin duk
lokacin da aka kira shi angon Nusaiba, ya kan ji
jinin sa ya k'ara hauhawa. Ya tsaya gaban dokin
da ya saba hawa, ya cire kuben da ke kan sa.
Yakubu ya dora masa ta kwano. Ya taka ya haye
doki. Ji ka ke tafi, ta ko'ina. Yayi karfin hali, ya
daga hannayen sa sama, yayi gaisuwa ga kowa,
sannan ya tsala wa doki bulala, yayi haniniya ya
zura a guje. Naseer fa bai san abinda yake yi
ba, gudun kawai yake yi kura na tashi., Rayuwar
sa gaba daya cikin kunci take har ya kan kai ga
lokuta da dama yana mancewa da tunaninsa.
Abinda ya faru da shi kenan a halin yanzun. Ya
sakarwa dokin sa linzami, ba san irin gudun da
yaje yi ba. Ai kuwa ba a jima ba, kafafuwan
dokin suka sarke, yayi haniniya, yayi sama, me
jama'a za su gani? Ango ya watso k'asa
warwars! Wuri yayi tsit!Na 'Yan dakikai, sannan
gaba daya jama'a suka dauki salati, yayin da
tuni jama'a da ke kusa da wajen, suka yanyame
shi. A sume suka wace da shi asibiti. Ba 6ata
lokaci aka kai shi (Emengency). Kowa ka duba,
hankalinsa tashe yake, musamman da Likita ya
ce yana da karaya 2, a hannun sa na dama.
Alh.Basheer zufa kawai ke keto masa, fadi ya
ce, "Inna-lillahi"Wa-Inna-ilaihir-raji'un! Ana cikin
halin haka, su Malam Balarabe suka iso, ba'a
jima ba Jeep din Antin Jordan ta aje su tare da
amare. Kowacce ido warwaje, ta sha kuka. Ba su
ma yi kuka ba, sai da suka ga angon su
magashiyyan a kwance, bai san halin da yake
ciki ba. Antin Jordan kuwa tunda ta iso ta tsinke
da fada, kamar ta ari baki, wai me yasa za'a
bar ango yayi sukuwa? Duk laifin na su Alhaji
ne, haka take ta fad'a. Sam ta mance haka
Allah ya kaddaro. Bai farfado ba, sai la'asar, ya
sha mamakin ganin sa a gadon asibitin. Wani
sabon bakin ciki ya sake turnike shi. Wannan
wace irin masifa ce?


Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100



Ajininsa yake 2-02
Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 11-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
.Gaba daya an gur6ata masa rayuwarsa? Take
nan ya kara tsanar Nusaiba, ba wai a zuci ba ya
kadai ba, har cikin jinin jikinsa yake jin bai
sha'awar zama tare da ita...Lallai iska na wahalar
da mai kayan kara, domin Alhj ba karamin
hidima ya sha ba a asibitin nan da kudin mai
dorin gargajiya. Angwanci dai ya dawo asibiti.
Anan abokansa da suka zo daga nesa suka yi
bankwana, suka koma zukatan su cike da
tausayin Naseer. Baya magana da kowa, illah
iyaka eh, ko a'a, ko kuma ayi masa sannu ya
amsa. Hatta ita kan ta Zarah kallon ta kawai yake
da ido, domin haka ya fiye masa kwanciyar
hankali, kar a gane da ita kadai yake magana.
Kwanansa 3 a Shika. Likita ya gama tabbatar wa
Alh.Basheer babu wani rauni a jikin sa, sannan
aka sallame shi. Aka dawo da shi gida. Haka suka
wuni kar6ar baki, a cikin su harda su Lubabatu,
Hauwa'u da Maryam, watau mutanen Zarah na
makaranta. A daren wannan rana Zarah ta feso
wanka, ta sa wani dan karamin dinkin atamfa riga
da siket, ta fito ta leka sashin Nusaiba, ita ma
wankan ta shiga, saboda haka ta wuce sashin
Naseer. Bisa kafet ta same shi zaune, ya jingina
da bango, idanuwansa rufe suke, sallamar da ta
yi. Shi yasa ya bude idon, yana kallon ta har ta
zo kusa da shi, ta zauna. "Yayana tashi ka yi? Ya
ce,"Na gaji da kwanciya, jiki na duk yayi tsami."Ta
dan dube shi, ta ce,"Sannu yanzu me za ka ci? Ya
dan kada kai,"Ban jin yunwa." Suka yi dan shiru
'yan dakikai, ta dago ido ta dube shi. Ita shi ma
yake kallo, don haka tayi dan murmushi, ta sauke
na ta idon. Hannun sa ta ji ya riko na ta, jikin ta
yai sanyi, ta kasa motsi." "Zarah!" Ya kira ta a
wata siga mai taushi. Kunya kawai ta ji ya lullube
ta, ta kasa duban sa. Ya kara kwantar da muryar
ya ce,"Ki dube ni, na ce, ni ba angon ki bane? Ko
don kin ganni a karye? Hannun ta daya, ta dan
kare baki, tana murmushi. Ya kara runtse
yatsunta ya ce,"Kin ga irin ta, ba don kun jawo
min ba, ai da tuni na kauda wannan kunyar." Ya
kara bata kunya, kamar ta tsere. Ya jawo ta, ta
matso shi sosai, ya rungumo kafadarta ya ce,
"Zarah kullm ina yiwa Allah godiya daya ba ni ke,
saboda ke kadai na ke so a rayuwata. Sai dai
yanayin da na ke ciki, ya zame min wani jarabci,
wanda na ke ganin sai kin taya ni addu'a. Allah
ya kawo min iyakar sa. Allah yana gani, kuma ya
ga abinda ke zuciya ta, tamkar kan k'aya na ke
cikin gidan nan. Saboda haka na ke neman hadin
kan ki, ki taimaka min kullum ki kasance tare da
ni, domin ke kadai ke yaye min bakin cikin da ke
rai na."Ta sauke numfashi, cike da tausayi, ta
dan dube shi ta ce,"Kullum ina tare da kai
yayana, na sha gaya maka, ka daina damuwa. Ka
kuma daina daukan wannan aure a wani matsayi
na daban, face hadin Allah. Ba ka san abinda
Ubangiji ya 6oye a cikin sa ba. Ba wai ba na
kishin ka ba ne, ko alama ba haka bane. Ban ki
in kasance ni da kai a gidanka ba, amma na yi
imani da cewa, duk wanda zai yi jayayya da
shinrin Ubangiji. Tabbas yana tare da wahala, ga
kuma tarin zunubi. Domin daga nan ne mutum
yake fadawa muguwar hanya, saboda bakin kishi.
Na san ka na so na yayana, amma ka sa ni.
Nusaiba ma amanar ka ce." Shi fa ba ya ma ko
son ya ji an ambaci wannan sunan, sai ya ji
kamar ya kurma ihu. Yayi ta maza saboda Zarah
da ke kusa da shi. Ha6arta ya dago ta dube shi,
yayi murmushi sosai, ya ce,"Na ji maganar ki,
kuma zan yi iya kokari na. Abinda ba na so kawai
a rink'a saurin kama ni da laifi.." Ta ce,"Kamar
yaya? Ya kada kai, ya ce,"Wannan sirri na ne, ba
zan fada ba, na samu ana kallo na, kunya ta sa a
daina. Kinga na yi wa kai na." Ta sa hannu ta
dan buge hannun sa da ke ha6ar ta, ta kauda
fuska, tana 'yar dariya. Shi ma dariyar yake yi, ya
sake juyo fuskar ta, ya jingina gashin sa jikin na
ta, ya ce,"Kin min alkawari kullum ki na tare da
ni, me yasa za ki kauda min fuska? Ta kwantar
da ido k'asa, bata tanka ba." Kin sa tayi 'yan
sumbatar kuncinta,"Da ke na ke magana." Ta
ce,"Bari in kira amarya mu shirya yadda za mu
rink'a girki." Ta yunk'ura za ta mik'e, ba tare da
ta ji ta bakin sa ba. Hannun ta gam!Ya rike shi.
Ta juyo dauke da murmushi ta ce, "Don Allaj bari
in kira ta." Ya lumshe ido, yana girgiza kai,"Ban
ce ba." Ta dade tana kokarin kwacewa, amma ta
kasa. Motsin bude kofa suka ji. Tare da sallama,
ta dage da karfi ta fizge hannun a lokaci guda,
shi ma ya sake ta yayin da Nusaiba ta kawo kai.
"Bata fahimci komai ba, domin Zarah a tsaye
take. Shi kuwa dan gogan tuni ya dauke kai cike
da haushin Nusaiba, ta katse masa hanzari." Ke
za ni kira amarya, na lek'o dazu ki na wanka."
"Ta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment