Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baro Hanwa, ba zan koma ba, Idan
kuma ba kya son rayuwa ta, shi kenan, zan kai
kaina a kashe." Nusaiba tayi wuf ta ce,"Umma,
ku kyale mu mu zauna anan din. Ni na san Abba,
ba zai ce komai ba. Kuma kula da kaya, ai ya fi
ban cigiya. Tunda yana ganin nan zai fi mana
sirri, sai mu zauna, ko Antina? Ta ce,"Gaskiya
ne,Umma ku kyale shi kawai."Umma ta nisa
kafin ta ce,"Ka ji Malam, yanzu wa zai kira Alhjn
yayi masa bayani?" Ya ce ,"Shi mana. Ba shi ke
da uzirin ba? Je ki dauko masa makullin sasan su,
su gyara."Umma ta mike, ta wuce dakin barci.
Malam Balarabe ya ci gaba da fadin,"Ka dauki
waya yanzu-yanzu ka kira shi, ka gaya masa." Ya
dauko wayar sa ya mika mai,"Ungo yi anmfa da
tawa." Yasa hannun hagu ya amsa yana neman
layin. Umma ta kawo makullan, ta mika wa
Zarah. Ta kar6a suka fito tare da Umma. Tsarin
ginin yayi matukar burge su, musamman
Nusaiba. Ita kan ta, ta tabbata babu laifi Naseer
ya kashe wa gidan kudi. Umma ta kawo tsintsiya
da abin goge-goge, ruwa cikin bokiti da Omo.
Nan da nan suka gyara wuri ko wacce ta za6i
dakinta. Alh. Basheer kuwa abin dariya ma ya ba
shi. Nan take ya yanke hukuncin ya ce duk su
zauna har zuwa lokacin da hankalin su zai
kwanta. Babbar mota yasa Sageer ya samo, su
Zarah suka je suka kwaso iya kayayyakin da zasu
iya debowa. Suna ta aikin gyaran Waje. Umma na
taya su. Shi kuwa dan gogan yana kwance
karkashin inuwa inda aka zuba masa shimfidar
karamar (ChaniS Carfet) suna hira da Sageer. "Ai
ni ban san cewa kai matsoraci bane, sai yau.
Ashe gaba da gabanta. Aljani ya taka wuta. A
taurin rai irn na ka, ban ta6a zaton akwai abinda
zai hana ka sukuni ba." Yayi wata 'yar dariya, shi
kadai ya san ma'anar ta, kafin ya ce,"Kowa ma
hakan yake fadi, dazun nan Inna ta zo ta gama
min tsiya. Amma ka san wani abu? Ina sane da
abinda na ke yi. Kawai yarinyar nan na ke so na
kure, a zato na za ta ce ba za ta biyo ni ba, ko
iyayen ta. Ka ga na sami wata kafar taso da
rigima. Sai kuma ta ba ni kunya mayyar." Wani
zabgegen tagumi Sageer yayi, yana kallonsa, wani
haushi ya kama shi, ya jima kafin ya ce,"Ni kai
na da ni na aikata ba na ji kunyar. Yanzu kuma
sai yaya? Ya ce,"Haushi ka ji? Idan ba na yi, ina
nuna ni ma na isa ai raina ni za'a dama ta samu
kuwa, dole in yi amfani da ita tun kafin yarinyar
nan ta yi min gori waya rana. Ka san mata. Ni
ban damu da shirgin ta ba, ta nemi ta raina min
wayau." Sageer ya kada kai, ya ce,"Duk rashin
soyayyan ta ya kawo wannan matsalar. Saboda
haka magana ma 6ata baki, sai dai a kullum ba
zan daina gaya ma ka, ka bi a hankali ba. Ni zan
koma. Allah ya k'ara lafiya, ya kuma tsare na
gaba." Ya ce,"Amin." Je ka, kai dama ai ba abokin
kuka bane." Na ji, a nemi abokin kuka a gaya
masa, ranar da ta dariya ta zo, kar ace an san
mu." Ya mike ya wuce, yayi sallama da Umma da
su Zarah. Suka yi masa godiya, ya fice, ya bar
gidan, ba tare da sun sake cewa juna affan ba,
shi da Naseer.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
BAYAN WATA BIYAR
a hankali Nusaiba ta fara fahimtar irin zaman da
su ke yi da Naseer, tamkar zaman doya da manja
ne. Haka ya bata daman gane banbancin karara
yake nunuwa tsakanin ta da Zarah. Al'amarin ya
soma damunta, saboda ta ka sa gano dalilin da
yasa hakan ke faruwa? Su kuwa iyayenta a
kodayaushe kokarinsu ta zauna gidan mijinta
tana mai ladabi da biyayya. Watannin 5r kenan
da barin su Hanwa, kuma tuni hannun Naseer ya
warke, amma Alh. Basheer ko Umminta babu
wanda ya sake ta da zancan su koma can. A
tunanin su babu komai, tunda suna jin dadin
zaman su anan Tudun Wada, kusan duk
abubuwan da aka sace masu, sun maida masu
sabbi. A yanzu ba abinda Alh.Basheer ya fi maida
hankali a kai, shine ya g a Naseer ya koma
makaranta sosai,hankalinsa ya karkata ga
karatun sa, akan ya dawo wasa gadan-gadan. Shi
kuwa Naseer kallon hadarin kaji yake wa kowa.
Komai aka ce yayi, sai ya nishadantu sannan yayi
shi. Shi a dole da kan sa yake so ya ja akalar sa.
Safiyar wata juma'a Zarah ta tashi da wani
azababben zazza6i mai dafa jiki. Hankalin
Nusaiba ya tashi lokacin da ta shigo dakin, don
ganin yaya Antinta ta kwana? Nusaiba ke da girki,
kuma wannan al'adarsu ce kullum safiyar su
binciki yadda dayansu ya kwana. Wannan
halastacciyar dabi'a mai kyau ce, kuma hakan shi
ya wajabta ga kowanne musulmi a hakkin zaman
tare. Da gudu ta koma dakin Naseer, barci mai
dadi ne ya dauke shi. Bata san lokacin da ta dasa
hannunya a jikin sa ba, ta hau bubbuga shi,
"Yayanmu! Yana ji, ya kyale, haushi da takaici
duk suka yi masa bargo. Idanuwanta suka kawo
kwalla, muryar ta, ta soma rawa,"Yayanmu, don
Allah ka tashi,"Antina ba lafiya......... Bata gama
fada ba, ta ga yayi wufe ya mike, ita da ke duke
gefen gado har ya riga ta ficewa. Ta biyo
bayansa, cikin sauri ta iske shi a dakin. Bisa
gadon ya haye, ya yaye bargon yana kira. "Zarah!
Menene? Jikinta yayi zafi sosai, tana rawar sanyi,
ta kasa magana. Ya rumgumo ta jikinsa." Zarah!
Bude ido ki dube ni, ina ke miki ciwo? Da kyar ta
iya fada,"Zazza6i.""Tun yaushe? Ta ce"Da shi na
kwana. Ku kai ni asibiti." Idanuwan sa suka kada
nan da nan. "Haba Zarah, ya za ki kwana da ciwo
ba ki yi Magana ba? Ai haka babu kyau. Zarah
menene amafani na a gidan nan? Hawaye suka
tsunke wa Nusaiba, ta juya da gudu, tayi waje ta
nufi sasan su Umma. Shi kuwa Naseer tuni ya
kule, iya wuya. Duk yadda yake ji da matarsa, ace
ta kwanta cikin wani hali babu taimakon kowa,
alhali yana cikin gidan nan da ransa. Me ya jawo
wannan, in banda zaman Nusaiba cikin gidan
nan. Ba don haka ba, me zai nisanta shi da abar
son sa na tsawon awa daya balle a kai ga kwana?
Har ta kwana yashe ita kadai cikin mawuyacin
hali, abin tausayi. Ya runtse ido, tamau, kamar ya
kwarma ihu. Tabbas an rusa masa shirin tsarin
rayuwar da ya ci burin yi da Zararsa. Ya kuwa
zama dole ya tsani duk wanda ya zama sila ko
shi waye. Muryar su Umma ya ji suna fad'in, "Ka
zauna ka rike ta a daki? Asibiti ya kamata ayi
maza-maza a kai ta." Umma ta amso ta daga
hannun sa, suka shirya ta tare da Nusaiba. Suna
tafe a mota, yana k'ara wa kan sa zafi da
tunanin abinda ba shine ba, a iska yake sawa
ransa kunci, har ya soma sambatu cikin zuciya.
"Gaskiya ina son na sake da mata ta. Wannan ai
cutarwa ce." Ya daki sitari tare da ajiyar zuciya.
Umma ta ce,"Je ka a hankali Naseer, za ta sami
sauki da yardar Allah." Sun ga Likita, ta sha
bincike da gwajegwaje, sakamako ya fito k'arara
Zarah na dauke da ciki wata 2 cif. Ba karamin
girgiza Nusaiba tayi ba, kuma take nan ta
warware wa zuciyarta sark'ak'in da ta shiga na
me yasa Naseer yake nuna bambanci a tsakanin
su? Amsar kawai baya son ta ne. To me ya sa ya
aure ta? Tambayar da bata gano amsar ta ke nan
ba, har suka dawo gida. (Tofa me Nusaiba take
nufi


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100


Ajininsa yake 2-03
Posted by ANaM Dorayi on 11:45 PM, 11-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______.
.
. Cikin Zarah wata 3 kenan har yanzu ba wata
lafiyar kirki ta cika ba. Duk ta rame ta dushe.
Gaba daya ayyukan gidan Nusaiba ta dauke
mata, ga shi kuma tana kula ita sosai, a lokutan
da Naseer baya gida. Sai dai tsakanin ta da shi
ido ne kawai. Ba wai abubuwan da yake yi ba sa
damun ta ba ne. A'a kokari take yi tana hadiye
wa, saboda farin cikin Abbanta. Shi kuma Naseer
matsalarsa ke nan, rashin nuna damuwar ta, so
yake ya cusa mata, ta ji haushi ta nuna 6acin
ranta a fili. Amma ko alama ta ki. Yau yana
Kaduna don amsa kiran Alh. Basheer. A offi ce ya
same shi. Yayi gaisuwa kamar yadda ya saba.
Alhj ke fad'in,"Saura kwana hudu mu tafi Katsina,
ban ga ka na zuwa atisaye ba, kamar yadda ka
saba? Ya shafa keya, ya sunkuyar da
kai,"Kodayake ku manya ne, ba ha bukatar
atisaye." Ya kada kai,"Ba haka bane Alhj. Ka san
jibi za'a fara rubuta (External WAEC), ina zuwa
wasu 'yan (Lesson) ne shi yasa, "O.K." na ji. Yana
da kyau haka. Za ka sami zuwa Katsina kuwa? Ya
ce,"Watakila in sami zuwa, sai dai na duba (Time
table) tukuna." To Allah ya bada sa'a." Amin." Ya
amsa. Yayi shiru, kamar wanda ruwa ya ci. Da ka
kalle shi, ka san a susuce yake. Alhj kan sa ya
gane hakan, shi yasa yake ta kallo sa. Jim kadan
ya dago, ya dube shi, suka hada ido, ya ce,"Zan
karasa wajen su Yakubu.Ya ce,"To shi kenan.
Daga can za ka wuce gida ne? Ya mike yana
fad'in, "Eh!" A gashe su don Allah." "Za su ji." Ya
wuce. Alhj ya raka shi da kallo. Kai bai yarda ba,
akwai abinda ke damun Naseer, don haka har ya
kai kofa, ya kira shi, ya dawo ya ce da shi,"Zauna
Naseer." Ya ja kujera ya zauna. Alhj Basheer ya
dube shi da kyau ya ce,"Naseer ni na gaba daya
ka sauya min. Ba ka da kuzari kamar yadda na
san ka. Me ke damun ka? Gaya min." Yayi dan
yake ya ce,"Babu komai Alhj." Ya ce,"A'a ban
yarda ba. Look Naseer, ni Babanka ne na dauke
ta tamkar dan na haifa a ciki na. Kar ka 6oye min
komai, idan akwai abinda ke damun ka, ka gaya
min, muddin bai fi karfi na ba, zan maka
maganin sa." Ya sake girgiza kai ya ce,"Allah, Alhj
babu komai." Yayi jim, yana kallon sa kafin ya
numfasa ya ce,"Shi kenan, ina sauraron ka, idan
dai ka ga da matsala tafiyar nan, mu na iya dage
wasan har zuwa lokacin da za ku gama (Exams)
din, ko me ka ce? Ya ce,"To zan duba in gani." Ya
mike,"Zan tafi." Ka gaida Abban ka da kyau." Ya
wuce yana amsawa, Alh. Basheee yayi shiru,
yana tunanin, amma sam ya kasa gane kan
al'amari, ga shi a zahiri ya san Naseer ya canza,
ba haka yake ba, musamman idan suna da wasa,
ya fi kowa kosawa a tafi. To ko har sha'awar
wasan ma aka cire masa a rai? Ya tambayi kan
sa. Wani sabon tausayi ya lullube shi, ya
ce,"Allah ka shiga tsakanin mu da makiyan mu."
Shi kuwa dan gogan tafe yake, yana mamakiin
yadda aka yi ya koyi shara karya. Shi da ko biyan
kudin jarabawar bai yi ba, amma yayi ruwa yayi
tsaki akan zai rubuta jarabawa. Yayi dan
murmushi, ya ce,"Allah ka shirye ni." Ya jima
wajen su Yakubu, suna ta hirarrarkin duniya,
sannan ya baro Kaduna, ya dawo Zariya. Kai
tsaye shagon dinkinsa ya wuce, ya iske Sageer na
zaman jiransa."Dariyar me ka ke ta faman yi ne
haka? Ya jawo wata dirowa, ya dauko ambluan ya
mika masa,"Ta mece ce? Ya ce,"Kai dai bude. Ka
gani." Ya bude, ya duba sannan ya dube shi baki
sake." "Teaching ka samu a (Barewa College)."
Yaushe Appointment din ya fito? "Dazu aka kira
ni, aka ba ni. Ban dade da dawowa ba. Ina
samun (Part-time) kuma zan wuce in ci gaba da
Digree dina. Yayi murmushi ya ce,"Ka haye Yaro."
Allah ya sanya albarka." Amin." To kai ya bayanin
karatun? Yayi dan tsaki,"Zan yi mana." Kullum
haka ka ke cewa har an gama biyan kudin
(External) ka na kallo, ka ki biya. Me yasa saboda
Allah? Yakamata ace rashin son karatunka tun na
yarinta ya wuce." Ya ce,"Ni na gaya ma ban son
karatun ne? Kawai haushi aka ban, na fasa." Ya
6alla masa harara,"To wa kai ma wa? Ya ce,"Kai
nai mana." Bata yuwuwa haka Naseer, abinda zai
amfane ka, har wani zai ba ka haushi ka fasa?Ya
ce,"Zancan ka ke so. Ai ni ma na san abinda na
ke yi., Wai don ranin wayau, sai da zai ban 'yar
sa yake tambaya ta, ya maganar karatu? Diploma
gare ka ko Degree? Ya fadi yana kwaikwayon
salon maganar Alhajin. Sageer ya tsura masa,
ido,"Ba ka da kunya Wallahi, sirikinka? Ya ce
,"Kyale ni, lokacina na ke ci. Duk lokacin da na
nishadantu, na koma makaranatar! Kai me ma
sunan ka? Kullum mancewa na ke." Ya tambayi
cikin yaran shago. Ya ce,"Abbas." Yawwa Abbas,
kwaso min kayan koyon dinkin nan, ka ji? Ya tashi
yana fadin,"To." Ya dubi Sageer ya ce,"Yanzu fa
sai ka ji haushi na ko? Wai me yasa ba ka goyon
baya na ne? Yayi dan tsaki mai dauke da takaici,
ya mike ya koma bisa keken aiki, ya ci gaba da yi
wa kayan gaban sa aiki." Yayin da Abbas ya kawo
wa Naseer kayan koyon dinkin sa. Maida su
kawai, maida su." Yaro ya juya da su. Shi kuma
ya mike, ya fice daga shagon yayi gida."
**********************
Zarah na jingine da gado. Nusaiba na bisa
Kujera, suna ta faman hira. Sallamar yayansu
suka amsa. Sannan suka hada baki yi masa
sannu da zuwa. Wajen Zarah ya nufa, ya zauna
bakin gadon ya sumbaci kuncinta, ya ce,"Zarah ta
kenan. Maman Bebi ya kike? Ta dan kirne fuska
rumgume da hannayenta a kirji, ta zura masa
fararen idanuwanta da su ka kara tabbatar yana
yin da take ciki. Shi yasa take kara masa kyau.
Yayi murmushi sosai, ya sake fadin,"Bebina ya
kara miki kyau, ba ki ga yadda ki ka dawo ba.
Balarabiya sak! Yana sa aya. Nusaiba ta mike ta
bar dakin." Ya bita da kallo har ta fice, sannan ya
maido da fuskar sa ga Zarah, ya ja dogon hancin
ta, ya ce,"Me ki ke marmari, in je in nemo shi?
Ta ce,"Abinda ka ke yi ba shi da kyau, kuma baya
min dadi, kullum ina gaya maka zancan nan. Ga
shi nan tun bata jin haushi, yau ka kure ta. Ya ja
ha6arta, ya ce,"Shine ki ke 6alla min harara? Ba
zan yi wasa da mata ta ba? A wane nafsin aka
haramta min hakan? Ta ce,"Ba'a haramta maka
ba, amma an umurce ka da dalci, kuma an
wajabta maka shi. Gaskiya ba na son abinda ka
ke yi." Ya dan mari kuncinta, ya ce,"Ni ina so, ba
ki ji dadin da na ji ba yau, ba na bata haushi."
Ta dan lumshe ido, ta kauda fuska." Nusaiba ta yi
sallama. Zarah ta amsa. Ta shigo dauke da tire
karami. Ruwan sanyi ne da Jus na kwali da
kofuna 2, ta aje gaban sa. Yadda ya zura ido,
yana kallon ta, tana zuba masa ruwa. Shi ya ba
Zarah dariya. Ta gode Allah da Nusaiba ba
haushi ta ji ba, hasali ma ruwan sanyi ta je kawo
masa ya sha, ya ji dadin rashin adalci." Ta sa
hannu ta, ta mintsile shi, ya dan zubara, ya dube
ta. Ta daga gira, tana masa murmushi mugunta.
Ya juya kan Nusaiba, ya ce,"Daina zuba ruwan
nan, ba sha zan yi ba. Ta aje, ta mike ta
ce,"Antina bari in je in dan kwanta, tunda ga
yaya na nan ko? Ta ce,"Ayi barci lafiya amarya."
Bata saurari komai ba, ta koma dakin ta, ta
kwanta tana ta sake-sake har barci ya sace ta.
*****************
Yana zaune a shagon dinkinsa, baya aikin
komai, alhalin suna da wasa A Kaduna, amma
ya ce wa Alhj ana neman su a makarantar da ya
ce ya samu. Sageer na ta dinkin wata atamfa.
Naseer ya katse shi da tambaya. "Ban gane
bane, kodayaushe yarinyar nan ta kawo dinki,
sai ka aje na kowa, ka kama na ta. Ta fi sauri
biyan kudi ne?" Yayi 'yar dariya, ya ce,"Sa'ido
kuma ka koma?" Fa'iza ai kostoma ta ce, dole in
yi mata dinki." Ya kalle shi a dage,"Amma kai ba
karamin dan rainin hankali bane,"Don tana
kostomar ka, sai ka aje dinkunan da suka yi sati
4, ka kama wanda aka kawo jiya? Jiyan ma da
yamma." Fada ka ke min, kome? Ya ce,"Ban
sani ba. Bari kuma ta zo, sai kun gaya min
abinda ke tsakanin ku, kafin a bata dinkin nan.
Ina nan ina jiranta." Sageer yayi wata bazawarar
dariya,"Ashe za ka kwana anan. Kai idan ma ka
ban haushi, sai in kai mata gida, in ce ta bar
kudin." Ya nuna su Abbas,"Ka ga 'yan yaran
nan? Su za ka yi wa barazana, ba ni ba. Za to
zo ta same ni, ka san halina, ban kyalewa." Ya
dan kura masa ido, sannan ya baro inda yake,
ya zo wajen sa ya kamo shi,"Zo ka ji wata
magana." Ya fizge hannun sa,"Babu abinda zan
ji Malam." Ya jawo shi da karfi."Taso mana, wani
sirri za mu yi.". Ya taso suka fita waje. Me yaran
2 za su yi, ba dariya ba, suna wa juna
rad'a,"Yau an k'ure oga Sageer." Suna fita.
Naseer ya ce,"Yi sauri ka fadi abinda za ka fada,
in koma." Ya ce,"Don Allah kar ka yi min fallasa
gun yariyar nan." To menene na aje dinkin wasu
ka yi na ta? Ya ce,"Gaskiya sonta na ke yi, ta
kuma jima tana kawo min dinkunan ta da na
'yan gidan su, amma ni ban yi karanbanin gaya
mata ba." "Saboda me?" Ina tunanin wasu
abubuwa ne. Ka ga bai kamata in fara neman
yarinya ba. Tunda ba aure na shirya yi ba.
Amma yanzu zan taya, in gani idan tana so, shi
kenan." Ya kai masa duka a kafada, yana 'yar
dariya." Shine za ka dame mu da cuwa-cuwa a
shago, ai gara a gaya mata, mu san cewa ta mu
ce. Ka ga ko ni, sai in dinka, bari, mu je ka
gama dinkin, a sa a leda mu kai mata gida. Ka
san gidan na su? 'Yar layin Rimi ce." Ba matsala.
Allah yasa kar ka sha kaye." Daina fadi, kar ka
sani hawan jini." Suka dawo ciki, suna dariya
tare da tafawa. Karfe 6, dai-dai, suna dawowa
daga layin Rimi. Cike da farin ciki Sageer yake,
domin Fa'izah bata ba shi kunya ba. Da hannun
bibiyu ta kar6i tayin sa. Kusan ita ma ta dade
da kaunar Telanta Sageer cikin ranta. Kofar
shago suka yi fakin, lokacin da wayar Naseer ta
dau kuka, ya zaro ta, gaban aljihu ya duba.Tsaki
yai, ya mika wa Sageer, ya ce,"Don Allah gaya
mata na bar wayar caji ne a shago." Ya amsa,
yana dubawa, sai ya ga sunan Nusaiba. Ya dube
shi a yamutse ya ce,"Ban gane ba? Ka san
abinda ke faruwa a gidan? Kuskure ne wannan.
Naseer ka daina." Wayar ta katse. Yana can
yana tunani. Gaskiya ne kuma, haka banza
Nusaiba bata kiran sa a waya. Shi yasa tana
kara daukar ruri, ya figi wayar a hannun Sageer,
ya danna O.K. Ya sawa kunnan sa, "Menene?
Murya na rawa, ya ji tana fadin,"Jikin Antina ya
rikice, ka zo a kai ta asbiti." Ido waje ya aje
waya, yayi wa mota key, ya ja ta a guje."
Menene? Sageer ya tambaya. "Wai jikin Zarah
ya rikice. Ka ji ba...........?" " Yi shiru haka, don
Allah." Ba zan yi ba, kai gaskiya ce ba ka so, ba
kuma zan daina gaya ma ba." Yayi banza da shi,
yana ta surutun sa. Baya ma jin abinda Sageer
ke fadi, don ba shine damuwar sa ba. Yana
fakin kofar gida, ya fito cikin sassarfa, ya fada
gida. Sageer ya biyo bayansa. Suna tare da
Umma a dakin Zarar, sai murkususu take, ciwon
ciki da mara, nan da nan suka dunguma asibiti,
ko kafin su isa, jini ya tsinke mata, shi yasa
suna zuwa dakin 'yan 6ari suka wuce da ita.
Hankalin kowa ya tashi, ba kamar Naseer da
yake jin zuciyar sa na kokarin tsago kirjin sa.
Saboda tsabar firgicewa. Haka idanuwan
Nusaiba ya raina fata, tana zaune ta cusa kai
cikin guiwa. Addu'a kawai take yi, kama-kama
har bayan isha'i, sannan cikin dan wata 4 ya
fita.Idanuwan Naseer suka yi ja, amma jin Zarah
na nan lafiya, sai yayi wa Allah godiya. Anyi
mata wankin ciki, ta dan hutu zuwa tara da
rabi, na dare, suka dawo gida. Washegari
Nusaiba, ta hado kayan karin safe, ta shigo
masu da shi dakin Zarah. Tana zaune gefen
gado, ta dubeta, ta ce,"Mun yi waya da Kausar
dazu, ta ce, in gaishe ki, su Ummi ma ta ce za
su zo anjima." Ta ce,"Ina amsawa. Kausar ta ba
mu kewa, tunda muka dawo nan, ko ta leko
mu." Ta ce,"Kausar ai ba mutunci, da anyi
magana, ta ce karatu." Tana da gaskiya." Ba
wata gaskiya Antina, ke dai sakko mu karya." Ta
jefa filon kujera bisa kafet, suka fara karyawa.
Naseer ya shigo ya dau wanka, kananan kaya ya
sanya. Ya zauna gefen gado. Zarah ta hada
masa Tea ta mika masa. Ya kar6a yana sha,
suna 'yan hirarraki tare da Zarah. Wani lokacin
Nusaiba kan tsoma baki, musamman idan ta
fahimci Naseer ya ya6o mata magana. Bai tashi
a dakin ba, sai da Inna ta zo duba jikin Zarah.
Kwarai ta ji dadin yadda ta same su. Ba ta jima
da zuwa ba,"Direba ya kawo Ummi. Sun dade
suna hira a dakin Zarah, kafin Ummi ta koma
dakin Nusaiba, suka gana tsakanin da da
Mahaifi..
*********************
Shekara guda da rabi kenan da auran su, sau 2
Zarah na samun ciki, yana zubewa duk da
dabarar da ake mata a asibiti na daure
mahaifarta, saboda sun gano ita ce bata da
karfi.Da zarar cikin ta ya kai wata 4, sai a daure,
amma kash! Yana kai wa wata 5r, dole a bude
ta, don samun lafiyar ta. Zuban jini kamar
famfo, har sai cikin ya fita. Wannan shine ciki na
3n, kuma an daure mahaifar har bata hutu a
asibitin watau (Bed rest). Wata 2, ta samu, bata
aikin kome, illa ta ci, ta sha, tayi wanka ta
kwanta. Kusan Naseer a asibitin nan ya tare a
'yan tsakanin nan, musamman da ya ga cikin ya
tsaya har ya kai wata 6 da shiga na 7. Zaran
kuwa zaman asibitinya ishe ta, ta damu kwarai,
tana son su sallame ta, ta koma gida. Yau
Naseer na Kaduna. Suna da wasa. Dole ce ta sa
shi tafiya wasan, domin yau lahadi ce babu
wata karyar da zai wa Alhaji. Ta karatu. Nusaiba
ke tare da Zarah a asibiti tun safe. Abincin da
soye-soye kala-kala tayo mata, irin wanda take
sha'awar ci. Musamman (Cole-slow), tana
bala'in son cin sa fiye da komai, ga shi Nusaiba
ta iya yin sa, yadda ya kamata. Shi take ci.
Bayan sallar azahar, hira tayi hira har suka fada
zancan zaman ta asibitin. Ita ta fara
fadin,"Asibitin nan ya ishe ni amarya, amma
kowa ya ki bada goyon baya, in koma gida ko na
dan sakata, in wala." Wata 'yar harara ta sakar
mata,"Lallai Antina, da wa ki ka so ya goya miki
baya?Ki na ganin an fara samun nasara, muna
ta murna, shine za ki ce gida za ki." Ta
ce,"Koma ke ki ke zuga yayanmu, kullum yana
like da Doctor suna kus-kus? Ta ce,"Allah ko
daya. Amma Ubangiji yayi wa mai zuga shi
albarka. Me za ki zo ki yi a gidan? Ta nuno ta da
cokali." Ki na son in kwashe hakoran ki kenan,
kin san na koya wajen yayanmu." Tana 'yar
dariya ta ce,"Allah Antina a daina maganar
wasa, zaman ki anan yana da muhimmanci, su
Doctors din ai sun san abinda suke ji." Tayi dan
tsaki,"Don dai ba ke ki ke zaune wajen nan ba,
shi yasa. Wai ma to ko a gidan na ke, aikin me
zan yi? Taimakon da ki ke min, ai iyakar sa
kenan, ko Inna hakan za ta yi min. Ga mai
wanke-wanke Ummi ta turo mana. Dama can
wanki yi mana ake yi, menene kuma ya rage,
saboda Allah. Gaba daya babbar ka'idar ba'a
son miji ya matsa min, yayanmu kuwa ba shi da
matsala, matansa 2 ne. To ki gaya min menene
bambancin zaman nan da gida? Ta sauke
numfashi ta ce,"Ni dai ina shawartar ki Antina,
ki yi zaman ki anan ba. Ta aje filet ta ce,"Sai ki
ban hujja. Idan kuwa babu, kin san Allah ba zan
sake kai wani sati anan ba. Sai na na san yadda
na yi na tsere." Ta tsura mata ido,babu alamar
wasa a zancan ta. Ina sauraron ki." Ta dan yi
jim, kafun ta ce,"Hujja ta daya ce, akan babbar
k'a'idar nan da ki ka fadi, gara a kiyaye, kin fa
san yau da gobe sai Allah. Ta harare ta,"Ban son
iskanci, ke zaman me ki ke yi,?" "Aure mana.
Amma ina gaya miki ki yi zaman ki anan, shine
rufin asirin mu, don Allah ki bar mu mu sami
Bebin goyo." "Lallai kin maida abin wasa, za ki
sha mamaki na." Ta ce,"To Anti ba sai ana son
mutum ake kula shi ba? Ke ba za ki gane ba
Anti, amma ina gaya miki, ki yi hakuri, saura
'yan watannin kadan ne." Gaba daya zuciyarta
ta girgiza, domin nan take ta gane abinda
Nusaiba ke nufi, sai dai a fuska bata nuna mata
ba, kara maka mata harara tayi,"Ba ki da hujja
amarya, so ku ke kawai ku azabtar da ni da
zama waje daya kamar 'yar gidan yari ." Ta
kamo hannun ta, tana 'yar dariya,"Antina
kenan, Allah ya bar min ke. Ai shikenan, an
wuce wurin ko? Ta ce,"Ya zan yi?" Tunda haka
ku ka fi so. Ta mike ta dawo gefen gadon, ta
dan rungumota,"Da me da me zan kawo miki
gobe?" Ta ce,"Za6in ki, za6i na ne amarya. Ki
kawo komai, zan ci. Yanzu za ki tafi? Ta duba
agogo, sai zuwa 3 da rabi. Ta ce,"To kin ga idan
za ki tafi ko ki rage kayan wajen nan sunyi yawa,
ki bar min kwandon wanka da na burosh
kawai.Wadannan zannuwan duk ki koma da su,
gobe a kawo min wasu." Ta ce,"An gama
Antina." Suka ci gaba da hira har zuwa 3 da
rabi. Nusaiba ta kwashe kaya, kamar yadda
Zarah ta ce. Tun da Nusaiba ta tafi. Zarah ke
zaune bisa sallaya, 6acin rai cunkushe cikin
zuciyar ta, bata san lokacin da hawaye ke satata
ba, Sabida tsabar tausayi da takaici. Tana ganin
wayar Naseer na ta kururuwa. Amma ta ki
dauka, yayi kira ya fi sau 5, sannan ya aiko
sako, shi ma bata bude ba, balle ta san me ke
ciki.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Karfe 8 bayan sallar isha'i, Zara ta had'a 'yan
abubuwan da suka rage, cikin jakar hannun ta,
ta faki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment