Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin likafanin
sa, suka sallace shi, aka wuce da shi makabarta.
Naseer bai iya zuwa ba, saboda ba zai iya
jurewa ba, yana kallo a cusa masa Ameer cikin
rami. Yana zaune kai cikin guiwa a falon Abba,
ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Ji yayi an
dafa kansa, ya dago a natse, yadda ya bi wanda
ya dafa shi. Alh.Basheer ne a gabansa, yayi
mamakin da bai ji sallamar su ba. Ya mike yana
masa sannu da zuwa, ya amsa, ya ci gaba da
fadin." "Zauna ka ji?" Suka zauna tare, ya gaishe
shi. Bayan yayi masa gaisuwa, ya ce, "Umman
ku ta ce an je kai shi ko? Ya ce,"Sun tafi tun
dazu." Ya ce,"Allah ya kara mana hakurin rashin
sa. Tare muke da Ummin Nusaiba, tana can
sasan wajen Umma." Ya ce,"Bari in je mu gaisa."
Ya mike ya fice. Alhj na masa kallon tausayi.
"Yan mintoci kadan ya dawo, ya sake zama. Bai
iya cewa k'ala ba, har zuwa wani lokaci, kafin
Alhj ya katse shirun,"Naseer! Ya dan dube shi ya
amsa. Ya ce,"Don Allah ka daina yawan tunani,
komai ya sami bawa da izinin Allah. Ba kai kadai
ba ne, Ubangiji na jarabtar bayin sa da masifu
iri daban-daban. Amma idan bawa yai hakuri,
ya jure komai wucewa yake yi, tamkar bai ta6a
faruwa ba. Abinda na ke son ka da shi shine. Ka
k'ara yawaita sadaka da addu'a, domin ita
sadaka tana yaye masifa da damuwa. Sai kuma
hamdala ga Allah. Ko wane yanayi ka tsinci kan
ka, to ka gode wa Allah. Ubangiji na wadata mai
yawan yi masa godiya. Ba wadatar kudi kawai
na ke nufi ba, har da wadatar zucci. Ka sani
idan zuciya ta wadatu da imani, duk abinda zai
zi wa bawa, zai kasance mai mika wuya ga
Allah. Kar ka damu, ka ji? Ya sauke numfashi ya
gyada kai, ya ce,"Na gode." Sun jima. Alhj
Basheer na yi masa nasihohi kafin su Malam
Balarabe da sauran jama'a suka dawo daga
makabarta. Nan ya bar su ya fita,Suka yi
sallama da jama'a, yayi masu godiya kowa ya
kama gaban sa. Aka bar su su 2 da Sageer.
A hakikanin gaskiya Alh.Basheer na son Naseer,
shi yasa duk ya damu da irin halin damuwar da
ya shiga, tunda yayi aure. Yau wannan, gobe
wancan. Shi kuma Naseer na masa kallon duk
matsatsin daya shiga. Alhj ne sila, don haka
babu wani dadin bakin da zai masa. Ya fadi,
kunni yaji, amma aiki da shi ba zai ta6a zama
dole ba. Naseer kenan.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Wata 2 da rashin Ameer. Bikin Sageer da Fa'iza
ya rage saura sati 2, ka na Kausar tsakanin su
sati 1. Watau na sati 3 ya rage. Angwaye da
amare na ta fafutikar shirye-shiryen biki, ita
kuwa Nusaiba wani abu ke daure mata kai, mai
kama da al'amara. Al'adar ta d'if, ta dauke
wata 2 kenan. Ana neman a shiga na uku. Ga
wani ciwon kan safe da take fama da shi, yawan
kasala da taruwar miyau a bakin ta. Bata gane
kan gadon ta ba, ko alama sai dai bata fidda
shakkun ciki take dauke da shi. Ta runtse idonta
tamau? Ta dauki salatin Manzo ta yi wa Allah
tasbihi mai yin yadda ya so." Watau rabon Da,
ya kawo ni cikin gidan nan kenan? Ta dan yi
murmushi, domin take nan ta tsinci soyayar
abinda ke cikin ta.Tana so ta nuna wa Antin ta
alamomin da za ta gane, amma tana jin tsorin
kar Naseer ya sani. Watakila ba zai so haihuwa
da ita ba, tunda baya sonta. Kar ya munafunce
ta da wani abin, ya zubar da cikin. Saboda haka
ta ci gaba da 6oye yanayin ta, babu wanda ya
fahimce ta, illa tsiyar k'iba da Antin na ta
kullum take yi mata. A haka suka sha bikin
Sageer. Amarya ta tare kusa da gidan su Sageer
din, ya kama hayar gida karami dakuna 2, kicin
da bayi. Sageer ya kama angwanci, babu kama
hannun Yaro. Sati da ya zagayo tun ranar
alhamis Nusaiba na Kaduna, ko dama duk ta
kosa ta sami 'yar damar da za ta gida, ta dan
kwana 2. Tana like jikin Umminta, dadi ya ishe
ta, ga madarar Holandia mai sanyi take ta
faman sha, tun isowar ta. Haka Ummi ke cikin
farin ciki ganin yadda Nusaiba tayi k'iba, ta
k'ara haske sosai. Tana ta kallon ta, tare da lura
da yanayin ta, ita kuwa Nusaiba ta k'i yarda
wani abu yanke a bakin ta, kar miyau ya taru,
kamar dai yadda take yi a gida Zariya. Bikin
Kausar yayi armashi kwarai da gaske, angonta
Injiniya Abdul-Malik yayi bajinta. Haifaffen
Unguwar Sarki, amma yana aiki da hukumar
gida da ke Lagos.Ta tare a makeken gidan sa da
ke (Abuja Road) kafin lokacin da za su d'aga
Lagos. Ranar asabar Zarah ta zo, kuma ta so
kwana. Kiri-kiri Naseer ya hana, ya kasa, ya
tsaye da yamma dole ta biyo shi, ya dawo da
ita. Nusaiba kuwa sai da ta kai litinin.
Alh.Basheer yayi ta ciwon baki, yana wa Ummi
fada yana ganin kamar da hadin bakin ta
Nusaiba ta kai Mondy. Karfe 4 kayanta an gama
kintsa su a mota. Direba zai maida ta. Tayi tsaye
tsakar falo tana kallon iyayen ta, kamar kar ta
tafi. Hawaye ya gangaro kafadarta,"Kuka za ki yi
shagwa6a66iya? Ta tsura masa ido, hawayen
suka zubo shar-shar! Yasa hannu ya goge su, ya
sake cewa,"Menene abin kuka? Kin ga kama
hanya ku tafi. Allah ya kiyaye hanya. Ki kula da
kanki da kyau. Kin ji? Ga katon 4 nan na
Holandia, na ce a sa miki a but." Umminki ta
ce,"Yanzu shan ta ki ke yi sosai ko? Ta dan
sadda kai kasa. Yayi murmushi, ya dago
ha6arta,"Haka Umminki ga gaya min, ga ta dai
a tsaye, ko ba ke ki ka gaya min ba? Ta wuce
shi da gudu ta koma gun Ummi, rungume ta. Ya
ce,"Ummita, sai mun yi waya." Kafin ta ce wani
abu, ta bar wajen da gudu, ta fita. Me za su yi,
ba dariya ba, kamar almara ta ga Naseer na
fakin a harabar aje motici. Ta ja tsaya, tana
kallon sa. Mamaki ya ishe ta. Daga bayan ta, ta
ji muryar Abbanta na fadin , "Ah , ga ma mijinta
nan ya zo." Ya zo ya wuce ta, ya nufi wajen
Naseer da ke fitowa daga mota. Da sauri ya
tsugunna. Alhj ya mika masa hannu tare da
sallama. Ya mika na sa yana amsawa. Sannan
suka gaisa, kafin Alhj ya ce,"Ashe za ka sami
zuwa? Ai tun jiya na tambaye ta, ta ce min ka
na da.(Exams), ba za ka zo ba." Kan sa tsaye ya
ce,"Mun fito da wuri, shi ne na ce bari in zo
kawai in dauke ta." "Yayi kyau. Dama fitowar na
ta kenan zu su tafi. Bari direba ya kwashe
kayan, ya mayar but din ka." Ya bude but din.
Direba na juye kaya, shi kuma ya shige cikin
gidan, don gaisawa da Ummi. Ko dama Nusaiba
tuni ta koma ciki, kan ta daure, tana tambayar
kan ta." Wai ashe maza ma sun iya kisisina?
Kurame sak! Suka zama cikin mota, yadda ya
like kunnensa da Ear piece haka ta manne na ta
da sauraren tafisr din Marigayi Sheik Jafar
Mahmud Adam Kano.
(Allah yajikan Mallam Ja'afar na Gadon kaya me
Ahlussuna, tare da iyayenmu baki daya


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment