Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce,"Ni ma na shiga, ina ta sallama, na ji
shiru. Ya jikin na sa? Na gan shi a k'asa ne." Duk
suka zauna suka sanya shi tsakiya. Zarah na
fadin,"Ni ma na shigo, na gan shi zaune ana. Wai
ya gaji da kwanciya." Ai da gajiya, kwanciyar."
Koma yau da bango ya jingina, ya rufe ido. Ta
ce,"Sannu." Da kai ya amsa. Ta mike ta dauko
filo, ta tsugunna gabansa,"Dan daga in sa maka
filo, zai fi maka dadi." Yayi shiru kamar ba i ji
ba.Yayin da Nusaiba ke fadin,"Shi ke nan gara da
ka sa baki. Da su Antina za'ayi min wayau." Ya
kalle ta a dage ya ce,"Kyale ta kawai, tashi ki tafi
abin ki." Ta kuwa mike za ta wuce, Zarah ta
rikota,"Wai sai ki tafin kuwa? Ta ce,"Me zan jira
Antina? Ai na yi ma ku hira, yakamata in je in
barci." Karfe 9?" "Eh mana. A kwanta da wuri, a
tashi da wuri." Fuska yamute ya ce,"Don Allah ki
kyale ta, ta wuce mutun na jin barci a hana shi?
Tana can tana kallon Naseer, ya 6ata rai ba sauki,
Nusaiba ta zame hannunta,"Allah ya ba mu
alkhairi. Yayanmu Allah ya karo sauki." Amin." Ya
fada a fizge. Ita kuwa Zarah ta kasa ma motsi
tayi. Tana kallo Nusaiba ta bar dakin. Dariya ya
kamayi, ganin yadda Zarah tayi sukuiti duk jikinta
ya mace." Ta nuna shi da yatsa ta ce,"Ka daina
sa mana baki idan muna magana." Fuskar ta
kunshe da shagwa6a. Dariya ya ci gaba da yi
mata. Suka ci gaba da hira. Karfe 11 da kyar ya
bar ta ta koma dakin ta, ta yo shirin barci ta
kulle dakinta, ta dawo wajen sa.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Bayan kwana 2. Nusaiba
ta kar6i girki, a ranar kuwa gidan cike yake da
baki da 'yan dubiya har da iyayen su. Tare suka
hada suka yi girke-girken abincin su kuma tare
suka ji ta kula da bakin su.Kamar yadda suka
saba gwanin sha'awa. Zarah ta gaji tu6us! Don
haka tana yin ishha'i, tayi wanka ba ta jira komai
ba, ta bi lafiyar shimfidadden gadon ta, babu
6ata lokaci, barci ya sace ta. Nusaiba kuwa bayan
ta gama shirin ta, sashin Zarah ta soma zuwa,
kofar falon na garkame. Ta tsaya kame da
ha6a,"Ba dai hat Antina tayi barci ba? Lallai
Antina." Ta jinjina kai ta wuce wajen Mai-gidan.
Yana kwance, gaba daya dakin yayi masa
bakikirin. Babu abinda yake tunani illah Zarah,
abinda ke 6ata masa rai kuwa, yai ba ita zai gani
a dakin sa ba. Ko sallamar ta bai iya amsawa ba.
Ta zauna gefen gadon, tana fadin,"Ka san wani
abu? Wai Antina har tayi barci." Ya baki taso ta
ba? Ta kulle kofar falon ma Ya ce,"Yayi mata dai-
dai. Daga nan bai sake cewa komai ba, nan ya
bar ta zaune, a zaton ta ma barci ne ya sace shi.
Yana jin ta, ta rufe shi, sannan ya kwanta, sai da
tayi barci, ya jawo filon sa, yasa kasa ya dawo
nan ya kwanta. Karfe 2 dare, ta farka, don yin
sallar dare. Can ta hango shi bisa kafet Mamaki
ya kamata. Ta sakko ta tsaya kan sa tana kallo.
Kamar ta tashe shi, wata zuciya ta ce ma ta kila
ya fi son kwanciyar kasa ne. Don haka ta wuce
bayi, ta kama ruwa, ta yi alwala ta fito. Motsin ta
ya farkar da shi barci, amma san bai bari ta gane
ba. Ta daura zani, ta dora hijabi ta haye sallaya
ta fara sallah. Shi kan sa ta burge shi, da zai fadi
gaskiya. Ta jima bisa sallaya tana addu."a kafin
ta mike, ta nufo gunsa ta tsugunna. Yadda ya
kwanta a yaye babu lullubi, sai ta ga kamar sanyi
yake ji, don haka ta mika hannu ta janyo bargo
ta sake lullube shi. Ta koma gado tayi kwanciyar
ta. Naseer yayi shiru ya rasa me yake sakawa a
zuciyar sa. Har asuba bai koma barci ba, haka
kuma bai daina sake-saken iska ba cikin ransa
ba. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Tsawon wata 1, Naseer yana samun kulawa wajen
amaransa da wacce yake so da wacce bai damu
da kulawar ta ba. A son ra'ayin sa ko sannu baya
buk'ata daga gare ta, shi yasa kullum yake jin sa
kamar bisa k'aya cikin gidan nan. Kuma bai san
dalilin da yasa kodayaushe k'ara tsanar Nusaiba
yake yi ba, duk da bajintar da suke nuna masa
ita da iyayen ta. Wani lokaci har tsoron zuciyar sa
yake ji, ta yadda ko alama ta k'i amsar Nusaiba.
Hannun sa yayi sauki sosai, domin har ya kan fita
ya je wajen iyayen sa, ya gaishe su. Bai ta6a
shiga sabuwar kerarriyar Jeep din sa ba, wace
Alhj ya sake masa, sai da Zarah ta goranta masa.
Shagon dinkin Sageer ya iso yayi fakin ya fito duk
jama'ar wajen idanuwan su akn sa. Idan ka dube
shi sai ka rantse da Allah wani hanshakain dan
kasuwa ne. Gaisuwa jama'ar wurin ya rinka
amsawa, sannan yayi sallama shagon. "Allah ya
kiyaye min na Zarah, angon Nusaiba." Ya wuce
shi ya zauna a kujera. Sauran yaran shagon suka
gaishe shi da jiki, ya amsa. Sageer ya biyo shi,
shi ma ya zauna kujerar gefen sa ya ce,"Duk na
zura ido in ga wa zai fito daga wannan
shimfidediyar mota, ashe Alhaji na ne, ka gan ka
kuwa?Ai za'a ce ka ba wata biliyan dari baya
mutumina." Ya ce,"Ka bari kawai, ni kai na tsoron
gidan nan na ke yi da motar nan. Zarah ce ta
matsa min na kinkimota." Yayi dan murmushi ya
ce,"Arziki. Kashi Naseer, ka riga ka tako kuma
kowa yana da hanyar da Allah ya shiryo masa
inda zai sami abincinsa. Allah ya kara hada mu
da masoyan mu." Ya dan nisa kafin ya ce,"Yanzu
tsakanin ka da Allah ba ka min kallon auran jari
na yi? Kyar Sageer ke kallon sa,"Me yasa kai ka
cika tsarguwa ne? To idan ma auran jarin ka yi,
ina ruwan mutum? Ina cewa shi ma mu2m ya
sami damar yin hakan, sannan zai yi? Naseer, ba
auran jariba, ko auran damfara ka yi, babu
ruwan ka da mutane kowa ta shi ta fishshe shi.
Abinda Allah ke duba ita ce zuciya, shi yasa ake
so a kodayuashe ta kasance tsarkakkiya." Ya dan
yi hucin zafi ya ce,"Na fahimce ka, amma kar ka
manta ba kowa ke da irin tunanin ka ba. Ni kuma
na tsani zargi, ina fitowa motar nan kowa sai
kallo na yake yi, har da gaisuwar gulma, dole in
na shiga wannan, ayi magana ta. Ka san ban da
hakuru, idan na ji ba za'a kwashe ta dadi ba,
komai gemun mu2m." Ya dan bubbuga kafadar
sa, yana dan murmushi,"Allah ya ki yaye min
angon amare, hakan ma ba za ta kasance ba.
Insha-Allahu. Ai yanzu ka wuce da ajin fada, sai
dai ka yi rabon na 'ya'ya a cikin gida ko ba haka
ba? Wani dan bazawarin murmushi yayi ya
ce,"Aje wannan maganar, ka san ina son yara,
kar ka tada min kwadayin su." Ko?" Sageer ya
tambaya, ido waje. Ya ce, "Ah? To mece ce ribar
auran?, Ita Zarah ma ta ki fara laulayi, sai ja min
rai take yi." Sageer ya fashe da dariya suka tafa.
Sannan ya nuna shi,"Zarah kadai? Har da
amarya, lokaci guda za su zazzage ma tagwaye."
Take nan ya sauya wani shafin." Ka san wani
abu? Na kusan fara zuwa koyon dinki, jira na ke
hannu na ya gama warkewa." Baki sake yake
kallon sa."Ina son ka ranar yanko zance, babu
seti. Mutumin da hidiman karatu ke gaban sa, ga
fita wasanni, yaushe za ka sami lokacin zama
nan? Lallai za ka sha mamaki, kai ba ka na
karatun ba, ka rinka koyon dinkin? Ya ce,"Ai na
ma riga na sha mamakin. To wai me yasa ka ke
son koyon dinkin yanzu?" "Ra'ayi na ne ya sauya,
yanzu kuma dinkin na ke so." 'Yar dariya Sageer
yayi,"Allah ya nuna mana lokacin." Ya ce ,"Amin.
Ya dan jima nan suna ta hira, sannan ya je ya
gaida Umma. Abba ya riga ya fita kasuwa. Daga
can gida su Zarah ya nufa, suka sha hira da
Innar sa. Haka yayi ta yawon sa a gari, ba shi
nan, ba shi can. Saboda yasan Nusaiba ke da
girki, bai koma gida ba, sai gab da Sallar
magariba. Suna zaune a falo, kowacce ta tsala
don mamaki. Yayi sallama ya shigo, suka amsa
dauke da fara'a, sannan suka yi masa sannu da
zuwa. Idon sa akan Zarah yake amsawa. Kan sa
tsaye ya wuce kujerar da take, ya zauna bisa
hannun kujerar, yayin da take fadin. "Haba
yayanmu, kuma tun safe har magariba ba'a ko
waiwayen gida? Haka ake yi? Kawai yadda take
motsa bakinya, shi ya tsura wa ido,, yake kallo.
Nusaiba ta ce,"Ai ni ban ma san abinda zance ba
Antina." Ya dan lumshe ido kadan, ya bude su,
kafin ya ce, "Na yi laifi kenan? Ta ce,"Tambaya
ma ka ke? Kodayake babu ruwana, tsakanin ka
da amaryar ne. Aron bakin ta na yi, na ci mata
albasa. Bari na yi haramar sallah." Ta mike za ta
wuce, yayi wuf ya cafke hannunta. Adon ta kawai
ke kidima shi, tayi masifar kyau,(Material) din ya
amshi jikinta sosai." Ta waigo a firgece, ta rasa
ma me za ta ce?" Zo in ji warin albasar da ki ka
ara ki ka ci." Ta dubi Nusaiba da ke kallon su,
tana dariya ta ce,"Au dariya ma ki ke yi, ba za ki
kwace ni ba, ki na kallo zai kar ya ni." Ta gintse
dariyar ta ce,"Duk zan iya jinyar ku." Ya janyo ta,
ta fada da karfi ta dawo inda ta tashi ta sake
zama. Ya matso ta sosai, ya ce,"Haba Fati na,,
daga shigowa ta kuma sai ki tashi, don me? Ta
dan kalle shi a karkace ta ce,"Sallah zanyi,ga ta
can ana kira." Ba ta jira komai ba, ta shammace
shi, ta wuce." "Zarah! Ya kira ta, ta waigo. Yayi
dan jim yana kallon ta, kafin ya ce,"Kin yi kyau."
Ta dan kama kugu, ta sauke numfashi ta dubi
Nusaiba,"Kin ji abinda ya ce? To kar ki yarda ya
kallame ki, sai ya gaya miki inda ya je ya ki
dawowa ya ci abincin rana. Ni babu ruwa na." Ta
wuce, ta bar Nusaiba na murmushi. Shi kuwa ita
ya bi da kallo har ta shige sashin ta. Ya ja
gajeran tsaki, wani kullutu ya tsaya masa a wuya.
Ga wacce yake so ya sakata ya wala da ita, ance
ba haka ba. Mutane na ganin auran gata aka yi
masa. Ina gatan? Bayan rayuwar sa na cikin
kunci, bai da walwala ko alama. Can cikin tunanin
sa, ya ji kamar Nusaiba na kunkuni. Ya daga ido
har sun fara ja, saboda damuwa, ya ce,"Mene
ne? Ta ce,"Sannu da zuwa na ce." Ya dai amsa
ne kawai, amma bai ga dalilin sake yi masa
sannu da zuwa ba, bayan sun yi masa tun
shigowar sa. Ta ce,"Shiru ka ki dawowa, muna ta
tararrabi, duk da dai abincin ba cinsa ka ke sosai
ba, ai da dadi ka dan dawo mu gan ka ko saboda
yanayin jikin ka."Yayi shiru yana dubanta,
sanaben da take yi, shi ya sa shi 'yar dariya. Ya
gyada kai,"Yaro man kaza." Ya fada a ran sa. Ta
ce,"Dariya ma na sa ka? "Na dai sa kai na, ai kin
san ba za ki iya sa ni dariya ba. Ko za ki iya? Ta
kada kai,"Wace ni, amma kasan bai kamata ka
rinka dogon yawo ba ko? Ya ce, "Na daina
Hajiyar. Zan iya zuwa in yi sallah? Tayi dan
murmushi, ta ce,"Ruga da gudu, ka yi sallah, ina
nan zuwa da kayan abinci." Kya ci abinki." Ya
wuce yana fadi a ran sa. Ta bi shi da kallo, yanzu
kam ta yarda son Naseer ya fara shiga ranta, sai
bata san abinda ke damun sa ba, ba baya sakin
jiki da ita sosai ba. Ta sauke numfashi ita ma ta
tashi. Ya dade da yin barci tsakar daki bisa
lallausar kafet, lokacin daya ji ana kwankwasa
kofar dakin ya farka firgigi, ya dubi agogo karfe 4
saura kwata na asuba. Tuni Nusaiba ma ta tashi
zaune bisa gado, tana tambaya,"Waye? Bai amsa
ta ba, ya wuce kofa yana fadin ,"Zarah! Menene?
A lokaci guda yana bude kofar. Me zai gani? Wasu
Samudawa ne majiya karfi cikin shigar bakaken
kaya, tun daga bisa kan su har kafafuwa, ba ka
ganin komai, sai kwayar ido. Sun tado Zarah da
bakin bindiga. Ko kafin ya gama shan mamaki,
sun hada da Zarah da kofa tare da shu sun
bankado su tsakar dakin." Ganin haka yasa
Nusaiba ta aza hannu bisa kai, ta kwarara salati
mai karfin gaske! Bata karasa ba, wani daga cikin
su ya kwashe ta da mari. Ya daka mata
tsawa,"Shutu.! Ta rarrafa da gudu ta kwakumi
Zarah, suka dunkule waje daya, bakinta na ta
tsato jini. Naseer ya bi su da kallo ya ce,"Me ku
ke so? Wanda ya fi kowa rashin imani ya dubi
hannun Naseer da ke rataye a wuyansa, yasa
kwafcecen takalmin da ke kafar sa, ya togar
hannun, sannan ya aje kafar bisa hannun ya
murza son ran sa.Daga yadda Naseer ya ji
yanayin hannun, ya tabatar da babu makawa ya
sake karyewa. Amma saboda taurin ran sa, ko
kara bai yi ba, ya sake cira kai ya dubi wanda
yayi dakali da hannun sa, ya ce,"Menene abin
duka bawan Allah? Ina cewa abinda na ke da shi,
su zan ba ku? Magana ta gaskiya, kun yi rashin
sa'a ban da komai gaba daya cikin kudina cikin
gidana na dubu talatin ne, suna cikin jakar can,
ku je ku dauka." Ya maka masa kasan bindiga ya
ce,"karyaKi na yi segiya, ina kudi? "Abinda na ke
da shi na gaya maku." Baba tausayi ya shiga
tafka masa takalmi. Nusaiba tayi karfin hali, ta
durkusa hawaye na zuba murya na rawa ta
ce,"Don Allah ku yi hakuri, ku daina dukan sa,
muna da gwalagwalai masu yawa da tsada, akwai
wayoyi kuma a waje na. Akwai dubu hamsin, duk
zan hada ma ku. Don Allah ku kyale shi, ba shi
da lafiya. Zarah kuwa kamar ta mutu, ko
numfashin kirki bata iya yi. Take nan ogan ya
hada su da yara 2, kowacce aka rakata dakin ta,
ta hado duk abinda take da shi. A wajen Zarah
ma an sami dubu goma ragowar sadakin ta da
Malam Umar ya ce dole sai ta kar6a. Amma
gwalagwalan Nusaiba iyaka ne, domin a cikin su
akwai na dubu dari biyu da hamsin. Ganin su ne
ma yasa ogan 6arayi ya kyale Naseer, ba don
haka ba da sai ya kwashi kashin sa a hannu. A ce
gida kamar wannan, ya 6ata lokacin sa ya shigo
bai sami komai ba? Dole kuwa ya debo rabon sa
a jikin Mai-gidan. Amma duk da haka warwas
suka bar Naseer. Matansa suka tarairayo shi. Sai
a lokacin yaje jin kansa kamar ba a jkin sa yake,
shi yasa ma ya kasa tashi tsawon lokaci. In ban
da kuka babu abinda su Zarah ke yi, shi kuwa
fadi yake,"Hasbinallahu-wani-imal-wakil........
Wasa-wasa fa Naseer ya kasa motsi, abin ya kara
firgita matansa. Nusaiba ta bazama falo ta nufi
gefen da wayar gida take (Land-line) jikin ta na
rawa ido na tsiyaya, ta nemi lambobbin gidan su
a Kaduna. Hankali tashe Alhj Basheer ya dauka,
don ya tabbatar da babu lafiya, wannan waya
karfe 4 da rabi." "Hello." Muryar Nusaiba ya ji
cikin kuka yana fadin. "Abba na! B'arayi sun ku
san kashe Naseer, ga shi can kwance, ya ka sa
motsi! Gabansa ya yanke ya fadi, ya dauki salati,
bakin sa na rawa kafin ya ce,"Harbin sa suka yi?
Ta ce,"A'a tsabar duka ne Abba na. Don Allah ku
taimake mu, sun kwace komai, har wayoyin mu
balle in kira wasu anan. Ya ce,"Ku kwantar da
hankalin ku, kin ji? Zan kira Abban sa, ni ma ina
tafe Insha-Allahu. Ina Zarah take? Ita ma lafiya
ko? Ta amsa,"Eh tana can wajen sa." To shi
kenan, ki koma ku natsu, kin ji? Ta ce,"To." Ta aje
waya tana share hawaye, ta koma dakin ta gaya
wa Zarah ta kira Abbanta. Suna nan zaune, sun
ta sa yayan na su, sun rasa abinda za su yi
masa, kan sa na bisa cinyoyin Zarah. Ya bude ido
da kyau, ya ce,"Mai gadi ya shigo kuwa? Suka
girgiza kai a tare, suka amsa,"Bai shigo ba." "Ko
sun kashe shi ne? Ya kara firgita su. Nusaiba ta
mike,,"Bari in dubo shi." Ta mike Zarah ta riko
ta,"Yanzu ke sai ki fita? Yana daga kwance ya
zura mata ido ya ce,"Lallai ke ba ki da hankali, to
fita, su kashe ki ke ma. Ba ta ce komai ba, ta
dawo ta zauna. Amma a son ranta da sun kyale
ta fita za ta yi, ta dubo lafiyar Mai-gadin su.
Tunda ba su ga ya shigo ba, bayan fitar 6arayin,
tabbas akwai dalili. Wani sabon tausayin su ya
sake rufe ta. Nan da nan hawaye suka tsinke.
Nusaiba akwai tausayi, sam-sam bata son ta ga
mutum cikin wani yanayi na rashin jin dadi, gaba
daya hankalin ta tashi yake yi.
Tun daga Kaduna Alh.Basheer ya debo 'Yan
sanda mota 1, motar sa na gaba, suna bin sa a
baya. Hajiya Zulai tayi shiru tallafe da kuncu bata
tunanin komai, illa tausayin sirikin ta. Allah ya
sakko masa da jarabci kufi da kufi.
.Tayi ajiyar zuciya, ta ce,"Allah ka mayar masa da
alkhairi." Alh.Basheer ya ce,"Amin dai, wannan
Yaro ai sai an mike masa tsaye da addu'a. Domin
ina ji masa tsoron mahassada." Ta ce,"Kai dai
bari. Allah abin tsoro,mutum abin tsoro. Ubangiji
ya raba mu da kowanne irin sharri." Ya sake
fadin Amin. Cikin mintoci 45 suka iso Zariya.
Gidan su Abba suka fara wucewa, suka dauko su
kamar yadda Alh. ya ce su jira shi, yana tafe da
"'Yan sanda. Gari ya fara shaa! Zai waye, suna
iso wa (Hanwa Low-coast). Get din gidan na
bude, shigewa kawai suka yi. Tun daga nan 'Yan
sanda suka fara ganin shaida, domin kuwa Mai-
gadi na daddaure, an like bakinsa banda dan
banzan dukan da ya sha na fitar hankali. A bakin
kofar falo, suka ci karo da su Zarah, wani sabon
kuka suka fashe da shi. Gaba dayan su, su Ummi
suka rungume suna rarrashi, sannan suka
dunguma inda Naseer yake, yana kwance gefen
idon sa ya kumbura sumtum! Wajen da aka buga
masa kan bindiga. Sallallami kowa ke yi. Su Abba
suka tarairayo shi, ya na fadin," "Sun k'ara karya
ni Abba. Sai an sake min dori." Babu 6ata lokaci
suka sa shi a mota zuwa gidan dori, suka bar
'yan sanda na yi wa matansa tambayoyi. Shi kan
sa Mai-gadi tare da shi suka tafi, aka ja masa
targade 3 ajikinsa. Daga can suka kai su asibiti,
don samun magunguna. Karfe 10 na safiya suka
dawo. Gida ya cika. Inna ta dubi Naseer, duk ya
muzanta, ya sauya kamanni. Hawaye fal ya cika
idanuwan ta, ta ce,"Wannan Yaro ka na ganin
tashin hankali. Allah ka yaye mana masifa." Duk
saura suka ce Amin. Kowa ya ga Naseer yadda ya
galabaita, sai ya tausaya masa. Haka Sageer da
Yakubu suka yi shiru, suna masa duban tausayi.
Naseer B kuwa fadi yake cikin ransa,"Ba shi fafa
ba? Ya wani fito da mota mai nishi, yana kece
raini a gari. Ba dole 6arayi su biyo shi ba. Ai ga
irin ta nan. Allah sarki, ko alama Naseer B bai yi
wa takwaransa halacci ba. Da Naseer zai gane
daya tabbar da cewa lallai ba k'aramin sa'a yayi
ba a rayuwa, tunda har Allah yayi masa baiwar
da wani yake kallo, yana masa hassada." Bayan
sallar azahar iyayen su suka koma gidajen su.
Alh.Basheer kam ya kara jaddadawa Malam
Balarabe maganar nemar wa Naseer taimakon
addu'a. Malam Balarabe, ya san yana yi masa
cikin sallolin sa , farilla da nafila, amma duk da
haka, ya amsa wa Alh. Basheer da lallai za su
kara kaimi shi da Umman sa. Shi kuwa Naseer
bayan tafiyar kowa, yana zaune bisa Canis kafet.
Falo jingine da kujera. Su Zarah na kicin suna
wanke-wanke. Ya kwala mata kira ta zo. Ya dube
ta fuska daure, ya ce,"Ki je maza daki, duk
abinda ki ka san nawa ne, ki zuba min a jaka. Ke
ma ki hada da na ki kayan za mu koma Tudun
Wada? "Saboda me? "Saboda ra'ayina can ya
koma. Ta kada kai, "A'a yayana, 6arayi sun firgita
ka, kawai za ka ce. Amma ni ban ga dalilin
komawar mu Tudun Wada ba." Haushi ya kama
shi ya ce, "Eh haka ne, koma me za ki ce. Za ki je
ki hada min kayan, ko in tashi da kai na? Ta
kwala wa Nusaiba kira, ya 6allo mata harara ya
ce,"Ke na ce ki hado kaya, ina ruwan ki da ita?
Bata tanka masa ba har Nusaiba ta iso,"Menene
Antina? Ta ce,"Ki zo ta mu ta same mu. Yayanmu
ya ce mu hada kayan mu Tudun Wada za mu
koma." Saboda me? Kafin ta ba amsa. Naseer ya
yi kukan kura ya tashi ya bar falon. Suka bi juna
da kallo, kafin Nusaiba ta matso kusa da Zarah,
ta ce,"Me ya faru Antina? Fuska yamutse ta
amsa, "Ooho, amma zai wuce maganar 6arayin
nan ne? Ni ma shi na gani, zo dai mu je mu same
shi."Cikin daki Naseer ke ta hada kayansa da
hannun daya, cikin jaka. Gaban sa suka tsaya
Zarah ta fara cewa,"Yanzu yayanmu da gaske ka
ke yi? Ai da ka san haka ne, sai ka tada maganar
a gaban su Abba ka ji me za su ce? Ya ce,"Kuma
shi kenan ba ni da wani ra'ayi nawa, komai sai
an takura ni? Ba zai yuwu ba, kin gane ko? Ke ba
ki da wata hujjar ma da za ki ce ba za ki koma
Tudun Wada ba. Gara wannan ita nan gidan
Babanta ne, ko bata biyo mu ba, tana da hujja.
Idan kuma duk anan za ku zauna, ba matsala, na
gama magana, kar wace ta sake yi min wata." Ya
suri jaka yayi waje. Su kuwa sansarai suka tsaya
suna kallon ikon Allah, duk jikin su yayi sanyi, ba
ma kamar Nusaiba, domin kalaman Naseer ba su
yi mata dadi ba. Hawaye suka cika idon ta, ta
dubi Zarah ta ce,"Antuna, me yasa yayan mu ke
fadar wannan maganar ko gidan Baba na ne,
zaman wa na ke yi a cikinsa? Hasalima Abba na
bai ce ni ya ba gida ba." Zara ta kamo ta cike da
tausayi, ta ce,"Kar kiyi kuma amarya. Ba wani
dalili yasa yayan mu wannan abin ba, illa firgici
6acin rai." Ta ce,"Amma ai mu yakamata ace mun
shiga wannan halin ba shi ba." Koma dai
menene, ki manta kawai amarya, yanzu menene
abin yi? Ta ce,"Abin yi bai wuce mu bi shi ba,
duk abinda Abbansa ya ce, shi za'ayi ko? Shi
kenan, je ki hado 'yan kayan bukata, mu
tafi."Kowacce ta nufi dakin ta. Nusaiba kam
jikinta a salibe yake akan maganganun Naseer,
musamman da ta tuna da hudubar Abbanta
kafin a kawo ta gidan miji: "Nusaiba, babu
abinda za ki yi a rayuwar ki gaba daya a halin
yanzu, wanda ya fi biyayya ga mijin ki. Ki sani da
Ummanki da ni Alh.Basheer, ba mu da ikon
komai a kanki, saboda girman darajar aure. Sai
abinda mijinki ya hukunta akanki. Saboda haka
Nusaiba kar ki dauki aure da wasa, ki yi amfani
da ilimin ki, domin a yanzu ne yake da amfani a
gare ki. Magana ta gaba wacce na ke son gaya
miki, ita ce, koda wasa ban lamunce miki yin
wata magana akan abubuwan da na mallaka wa
Zarah da mijinku ba. Ina nufin gori, da babbar
murya na ke miki wannan maganar. Duk ranar da
ki ka gorantawa daya daga cikinsu, ban yafe miki
ba, domin kin watsar da mutuncin ki, kuma kin
rusa tarbiyar da muka baki. Ba kuma sai na gaya
miki ba, kin san matsayin matar da ta yi wa
mijinta gor.......... Ta share hawaye, ta zage zif
din jaka, tana fadi a ranta,"Har abada ba zan
baka kunya ba,"Abbana." Muryar Zarah ta jiyo
tana fadin,"Amarya kin gama? Ta amsa, Eh. Suka
kwaso kayan bukata, suka kulle ko'ina, suka fito.
A zaton su Naseer na waje, yana jiran su, tunda
ba su ji tashin mota ba. Ashe shi tunda ya fito,
ya tako ya tsare aca6a, ya haye yayi tafiyar sa.
Mai-gadi ke gaya ma su tuni ya fice. Kallun juna
suke yi baki sake. Dole Nusaiba ta koma ta dauko
makullan motar ta, ta ja suka bi shi. Ita Zarah ta
san rigimar Naseer, shi yasa, ma abin bai dame
ta ba. Nusaiba kuwa abin 2 ya hade mata,
damuwar da Naseer ya shiga, ga kuma
maganganunsa, ba su yi mata dadi ba. Sannu a
hankaki Zarah ke ta warware mata kullin zuciyar
ta, ta hanyar dibar ta da labaran wasu abubuwan
da Naseer din yayi na jarunta. Al'amarin kuma ya
koma daure mata kai. Ta saki waccan maganar,
ta koma tana tambayar kan ta, me yasa yau ya
tashi hankalinsa haka akan 6arayi? Zarah ma oho
ta ce, shi yasa har suka iso kan ta na daure. Suka
yi sallama cikin gidan dauke da jakunkunan su.
Umma ta fito ta tar6e su,"Ku shiga yana nan
falo. Ko kunya bai ji, wai ya taho ya baro ku can.
Naseer ai baya gajiya da abin fad'i. Yana zaune
gaban Abba suka zube suka yi gaisuwa. Malam
Balarabe ya dube shi, ya nuna su "Yanzu ba ka ji
kunya ba? Koma menene, ai sai ka hado matan
ka ku tahu tare, kai dai kullum bahagon mu2m
ka ke. ba ka sauyawa. Wai ma in tambaye ka,
me ka ke nufi da kun baro can? Rai 6ace ya
ce,"Ni fa gaskiya Abba ba zan zauna gidan nan
ba. B'arayi na ganin bangajejen gidan suna
shigowa ba sa mun komai, wata rana kashe ni za
su yi, kar fa ka mance Abba ni fa ba mai kudi
bane, rufin asiri ne kawai. Saboda haka nan
zamu zauna, idan ina son asirina ya kara
rufawa.Malam Balarabe yayi dan shiru, saboda
Naseer yana da dalilai masu karfi. Can ya dan
nisa ya ce,"To ka gaya wa Alhj ko? Ya kada
kai,"Ban gaya masa ba." Umma ta amsa,"Ka ji
matsalar ka, tunda ya zo yakamata ka yi maganar
nan a gabansa, amma ka ki, me zai ce? Malama,
ni ban goyi bayan zaman su anan ba. Su koma.
Ya kira Alhjn a waya, ya gaya masa tukuna." Ran
Naseer ya k'ara 6aci, ya zuba wa Ummansa ido,
tunanin sa kuwa, shi kenan kuma yanzu ba shi
da wani ra'ayi, sai abinda Alhj ya ce, ya runtse
ido, ya cije le6e,"Na shiga uku. Alhj ya mallake
min iyaye. Ya fada cikin ran sa. Ya bude ido, ya
dubi Umma,"Gaskiya Umma, sai dai ki yafe min,
na riga na

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment