Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idon kowa, ta fiyo a hankali ta bar
asibitin. Aca6a, ta haye ya aje ta gida. Bata yi
sallama ba, har ta shigo cikin gida. Umma na
can ciki tana sallah. Abba kuwa bai dawo daga
masallaci ba. Don haka ta wuce da sauri sasan
su, ta tura falon ta shiga. Shirin na ta gwanain
sa'a, domin Nusaiba na can bayainta tana
wanka. Saboda haka ta wuce dakin ta. A rufe
yake, amma ba da makulli ba, tayi hamdala ta
shige, ta mayar a hankali ta rufe. Ta aje jaka ta
koma gado ya kwanta don hutawa, don bin
dokar likita. Naseer bai shigo Zaria ba, sai tara
saura kwata, kai tsaye asibiti ya wuce don ganin
Zarah tare da neman sanin dalilin rashin daukar
wayar sa.Kowa na bisa gado, amma gadon
Zarah babu kowa. Ya tambaya. Suka ce su ma
ba su ganta ba, babu ma wanda ya san lokaci
da ta bar asibitin. Hankalin Naseer in yayi dubu,
ya tashi, ya bude wa Nosis wuta masifa yake
kamar ransa zai fita. Da kyar suka samu ya
sassauto ya saurare su. A inda suka shawarce
shi da ya je gida ya duba, tunda ga shi babu
kayanta ko daya sai 'yar karamar kular abinci
kan dirowa. A fusace ya fice asibitin baya ko
ganin titi sosai, saboda tsabar fushi. Lokacin
daya shigo gida karfe goma saura 'yan mintoci
ne, su Umma har sun rufe sasan su, wucewa
kawai yayi ya fado falon. Nusaiba ma ta jima da
rufe dakin ta. Sai dai ba barci take yi ba
tunanin duniya ya ishe ta, tare da juyayin irin
yanayin da ta tsinci kanta, wanda a kodayaushe
take aje shi a matsayin kaddara daga Allah.
Kofar dakin Zarah ya wangame, cikin zafi da
fushi. Kwance ya ganta ba kuma barci take yi
ba, domin idanunwanta ya fara arba da su. Bai
rufe kofar ba, ya wuce da sauri yana fadin."
Zarah kin kuwa san abinda ki ke yi? Don me za
ki baro asibiti, ba tare da izinin kowa ba? Ta
dauke kan ta, tayi banza da shi har zai ga zama
bakin gadon." Ba za ki yo magana ba?" Shi yasa
na ke ta kiran wayar ki, ki ka ki dauka? To kar ki
ji da wai, yanzun nan za ki koma asibitin, tashi-
tashi! Kar ki 6ata min lokaci." Ta dube shi, ido
fal da hawaye ta ce,"Ba zan koma ba yayana."
Ta yunkura ta tashi zaune, yayin da ya saki baki
yana al'ajabinta, "Ba za ki koma ba? Ta
ce,"Kwarai ba zan koma ba Ai ban san rashin
adalcin ka har ya kai haka ba yayana. Don me?
Saboda me? Ka na cutar da 'yar mutane ka na
so ka ci wutar Allah ne? Hawaye suka soma
zuba. Ya ce,"Nusaiba ba matar ka ba ce? Don
me za ka aje ta shekara daya da rabi, ka na
cutar da ita? Kuma tana kallo na, tana sane da
abinda ke Faruwa. Wannan zalunci ne. Allah ba
zai bar ka ba yayana, gara ka san halin da ka ke
ciki, ka gaggauta yin gyara........... Ya daka mata
tsawa wacce ta kara jawo hankalin Nusaiba da
tuntuni take jin 'yan surutan da bata gane daha
inda suka fitowa ba, don haka ta taso a hankali
ta fito. "Ya isa Zarah! Ya isa! Dama saboda
wannan maganan ki ka baro asibitin ba izini? To
ina son ki sani, babu ruwanki a ciki wannan
maganar, ban kuma ce ki sa kanki a ciki ba,
zamanta daban, zaman ki daban, kar ki sake
yimin wannan maganar." Tayi zuciya sosai,
idanuwan ta suka kara yo waje, ta ce,"Kwarai
akwai ruwa na a ciki domin ni ban dauki
Nusaiba a matsayin kishiya ba, 'yar uwa ta ce,
kuma ina kaunar ta tsakani da Allah. In don
akan wannan cikin yasa ka ke kumfar bakin,
don me na baro asibti, bari ka ga yadda za'ayi
da shi, tunda shi kadai ka ke so, ba ka tsoron
Allah." Tana fada ya ga ta mike bisa gado ta
hau buga tsalle sama tana direwa da karfin
tsiya, hawaye na zuba bakinta na fadin,"Ban son
shi, sai ya zube wallahi! Nusaiba ta kara
mannewa da bango, ta fasa kuka sosai, ciwon
zuciyar ta ya karu, har sai da ta sulale kasa. Da
kyar ta rarrafa ta koma dakinta. Nan bisa kafet
ta kife, tana rusar kuka, wanda ita kanta ba za
ta iya tantance dalilin yin sa ba,Illa iyaka ta san
ita abar tausayi ce, sai dai kuma ai bata
ratayawa ranta son Naseer ba, tana dai zaune
ne kawai, don farin cikin Abbanta kamar yadda
ta fahimta shi ma Naseer ya amshi auranta ne
saboda girman Abban na ta a idonsa. Amma da
ciwo, ka na zaman mu2m bai damu da shirgin
ka ba. Sai da yayi ta maza sosai, sannan ya
cukuikuyo Zarah yayi iya kokarinsa kafin ya
samu ya manna ta ajikin sa,"Kin yi hauka ne
Zarah?? Za ki kashe kan ki ne? Ta rushe da kuka
sosai, bai ta6a ganin tashin hankalin Zarah irin
na yau ba. Gaba daya jikin sa yayi sanyi,"Ki yi
shiru Zarah, na ce na ji, na yi laifi, zan gyara."
Ta sulale a hankali ta zauna, saboda yadda take
jin jikin ta ko'ina ya daddure. Ya biyo ta da
sauri, ya dago fuskarta,"Za ki takaita ni ne
Zarah? Don me za ki min haka? Murya na rawa
ta ce,"Dole in yi maka yayana. Domin rayuwar
ka na cikin hatsari, kai har da ni ma, tunda ta
gaya min na sani, hakki na ne in gaya ma ka
gaskiya. Zalunci babu kyau yayana, kar shaidan
ya kai ka ya baro, shi gaba daya mece ce
rayuwar? Ya tallafi kuncinta, ya goge
hawayenta." Duk na ji, na ce zan gyara. Amma
ita ma bai dace ta gaya miki ba, wannan rashin
kunya ne." Ta ce,"Tayi rashin kunyar. Ai ba
kanta tsaye ta gaya min ba. Magana mu ke akan
zamana asibitin, na ce ya ishe ni, zan dawo
gida, tunda tana nan za ta dauke min komai. Ka
ji abinda ya kawo maganar. A hakikanin gaskiya
ka cutar da........ Ya toshe bakinta,"Yi shiru, ya
isa haka. Na dauki kuskure na, shi kenan? Saura
gyara." "Ai zan gyara. Yanzu da ki ka baro asibiti
me su Umma suka ce? Ta ce,"Ni ba wanda ya
san na shigo gidan nan, har ita amarya." Ya
ce,"To ki taso bakin ki alaikum in maida ki."
"Muryar Umma ya jiyo tana kwala ,"Naseer!
Naseer!! Ya runtse ido, "Shi ke nan ga Umma
can ta fito." Ya mike yana amsawa ya fito. Tana
tsaye kofar falo. "Hayaniya na ke ji, wai me ke
faruwa? Ya rasa me zai ce, sai kawi ya
ce,"Umma Zarah ce ta gudo daga asibiti."
Zarah? Ta fada cikin al'ajabi. "Ina take? Ga ta
nan cikin daki, na yi na yi ta zo mu koma ta
ki."Jin muryar Ummar yasa Nusaiba ta buda
kofa ta fito. Tare suka cusa kai dakin, tana
zaune tana faman share kwalla. Nusaiba ta ruga
ta rungume ta,"Antina, me yasa? Ganin Zarah
na kuka, ita ma na ta ya dawo. Umma ta
ce,"Amma dai Zarah ba ki da hankali, ki na
wasa da lafiyar ki ko? Maza mike ku koma, kafin
in kira Abbanku, ba na son jin wata magana."
Nusaiba ta sake ta, ta kamo hannayenta,"Tashi
Antina mu je a maida ke." Ta mike Umma na
fadin"Nemo mata hijabi." Kafin Nusaiba ta
dauko hijabin, jini ya malalo har bisa diddigen
ta. A hankali ta yaye zane ta duba, ido waje ta
kalli Umma. Wasu hawayen suka tsirgo. "Umma
duba ki gani." Ta hau salati da tafa hannu.
Naseer ya rude,"Kin ga irin ta ko? Kafin su yi
haka ya sunkuce ta yayi waje. Nusaiba ta biyo
su da gudu hijabi a hannu. Umma ta kwala wa
Abba kira ya fito a rude. A rudan take gaya
masa, ta fice da gudu. Kafin ya fito waje. Naseer
ya ja mota sun wuce, nan ya tsaya yana ta
sababi shi kadai. Da ka gan su ka san a rikice
suke gaba dayan su, babu mai takalmi balle
mayafi. Zarah ta sha fada wajen Likita da Nosis.
Suka yi mata allura maimakon jini ya tsaya, sai
ciwon mara kamar za ta wuce barzahu.Dole a
kwance mahaifa. Haka Likita ya gaya wa su
Naseer. Zufa ta keto masa, babu abinda zai iya
yi, tunda hakan shi ne samun lafiyar ta. In anyi
sa'a a sami dan.Komai na Allah ne, haka nan
suka fauwala wa Allah. Ana kwala kiran sallah ta
haiho dan ta namiji. Sai dai yayi k'ank'anta.
sosai. Naseer yayi kamar zai rasu, don murna,
haka Nusaiba ke sauke numfashi tana kokarin
dai-daita shi. Ba su ga Yaron ba, saboda an
hanzarta sa shi a kwalba. Bayan an kintsa
Zarah, an fito da ita dakin hutu, can suka kutsa
kai suna rige-rigen gaishe ta. Minti 15 bayan
fiddo ta. Naseer ya koma da Umma gida, don
kwaso kaya da dukkan abinda ya dace. Nan
suka bar su tare da Nusaiba, duk doki ya ishe
ta, ta kosa ta ga Baby. Tare suka dawo da Inna.
Daga bisani ne su Abba da Malam Umar suka zo
asibitin, suka duba Zarah! Zarah kam ta sha
fada wajen iyayenta akan baro asibiti da tayi. Ta
amsa laifin ta, ta kuma bada hak'uri saboda
bata son kowa yasan dalilin barinta assibiti.
Babu wanda ya ga Baby, domin likita ya hana,
ya ce sai karfe 6 yamma za'a fito da shi, idan ya
sha nono a maida shi.Ai kuwa Umma sai da ta
jira lokacin yayi. Wata Nos ta fito da shi don
koridon dakin aje jarirai wanda shi ma a rufe
yake ruf. Kai! Wannan Yaro Allah ya zuba halitta
mai kyau a wurin nan. Tamkar Naseer yayi kaki,
kamanin su daya, amma ya zarce Naseer kyau,
nesa ba kusa ba. Tun da yayi arba da Baben
nan, jikinsa ya dauki rawa, ya ji gaba daya
duniya, babu abinda yake so fiye da Bebin. Da
haka Nusaiba ta tsinci kaunar Bebin nan cikin
ranta, kamar ta gudu da shi. Amma ina. , Minti
30 aka ba su, su gan shi, lokacin na cika, da
kyar Nos ta kar6e shi hannun Naseer, ta koma
da shi. A ranar Abba ya rada wa Yari sunan sa
watau Iliyas!.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Satinsu 3 a asibiti sai dai Zara ta zo gida tayi
wanka ta koma. Babu wanda bai zo ganin su a
asibitin ba, hatta Fa'iza. Sageer ya kawo ta, ta
gaida Zarah. Haka Kausar bata yi kasa a guiwa
ba ta zo, ta kuma ce za ta dawowa ranar da aka
tsaida shagalin suna. Cikin wayoyin Naseer
hotunan Iliyar (Ameer) ne birjik iri-iri. Babu
yadda za'ayi ya wuce awa, bai bude ya gan shi
ba, kwarai ya kwallafa Yaron nan cikin ran sa,
kamar shi kadai ya fara yin Da.Sun shafe sati 3n
nan cif! Sannan aka sallami Bebi. Nusaiba na
son ta rike shi a mota, amma ubansa yayi kane-
kane. Sageer na tuki, yana masa tsiya, ganin
yadda yake ta kara rurrufe shi da shawaul, don
Likita ya ce kullum ya kasance a lullu6e. Ranar
da ta zagayo, aka shirya gagarumin shahalin
suna. Nusaiba ta kashe kudi, abubuwa kala-kala
tayi na ci da na rabo, balle uban gayya. Ko
lokacin bikinsa bai saki jiki da aljihu irin na
wannan yaron ba. Mai-jego kuwa ta kwashi kaya
akwatuna 2 manya. Nusaina ta shirya kayan
Bebi da zannuwan Mai-jego. Banda wasu
tarkace cikin (Ghana most go). Bayan kowa ya
watse. Nusaiba da Naseer na zaune suna kallon
yadda Umma ke wanke Bebi da ruwan zafi,
yayin da Zarah ke bayinta tana na ta wankan.
Nusaiba ta dube ta, ta ce,"Ni kuwa Umma in ki
na wankan nan, sai in ta mamaki." Mamakin
me? Ta ce,"Ni gani na ke kamar zai sumbule, ke
kuwa ki na tayi masa, ba kya jin komai." "Dariya
Umma tayi. "Nusabai oho! Ka ji Naseer, ashe in
ta haifi na ta, ba za ta iya wanke shi ba." Tare
suka kalli juna da Naseer, yayi yaken dole, ita
kuwa kunya ce ta rufe ta, ta mike za ta wuce,
ya ce,"Ina za ki kuma? Ba ke ki ka dauko zancan
ba?Tsoma bakin sa yasa ta k'ara azama ta bar
dakin. Umma na dariya. Naseer na murmushi,
yana fad'a a ran sa, "Yarinya sai salon
tsiya."Umma ta nade Yaro a tawul mai laushin
gaske, tana fadin,"Ita ma Allah ya kawo masu
albarka." Ya shafa k'eya ya ce,"Umma hanzarta
ki sa masa kaya akwai iska. Ta zubo masa ido ta
ce,"Na k'i, ka fi ni son shi ne? Ya kada kai yana
murmushi,"Tuba na ke UmmaTa." Yana rufe
baki. Abba yayi kiran sa, ya tashi ya fice. Abban
na falon sa a zaune bisa kafet, shi yasa yana
zuwa ya tamkwashe kafa gaban sa, ya ce,"Ga ni
Abba.." Ya dube shi da kyau ya ce,"Na yi maka
zuru in ga irin hankalin ka, sai na lura lallai ba
ka da hankalin." Gabansa ya fad'i, ya k'ara
matsowa ya ce, "Me na yi Abba? Ya ce,"Maganar
komawa Hanwa, na ji ko tada zancan ba ka yi,
me ka ke nufi? Ya dan sunkuar da kai, ya sauke
numfashi,"Yaya mu2m zai ba ka gida, amma ka
ki zama? Saboda 6arayi sun shiga ma sau 1?
Anji ba ka da lafiya wancan karon, har yanzu ba
ka warken bane? Yayi dan shiru kafin ya
ce,"Abba ba haka ba ne. Ni kai na ina son
komawa can, amma da zarar na tuna da irin
dukan da na sha wajen 6arayin nan, ni kan ji
tsoro ya kama ni. Kar ka damu Abba za mu
koma."Ya ce,"To ka hanzarta sa ranar, ku koma.
Na san Alhj na da kawaici, ba zai ce komai ba.
Amma babu dadi mu2m yayi ma ka kyauta, ya
ga ka na yi wa abin rikon sakainar kashi, ko kai
ne ranka ba zai maka dadi ba." Ya ce,"Haka ne,
insha-Allahu zan san yadda za'a yi." Yauwa sai
ka yi wa Allah godiya kawai kan matanka a hade
yake, asirinka ya rufu dari bisa dari, domin
zaman lafiyar iyali a cikin gida, shine kwanciyar
hankalin Mai-gida." Ga su dai yara k'anana,
amma Allah yayi masu kaifin hankali, shi yasa a
kodayaushe na ke k'ara jawo hankalinka a kan
kamanta adalci tsakaninsu. Ba cuta ba
cutarwa,Naseer wannan shine tsoron Allah, ka
sani zai tsaida ku ranar da ni da Umman ka ba
za mu iya cetonka ba. Ina fatan ka ji ni da
kyau? Ya numfasa sosai, ya ce,"Na ji Abba, na
gode." Ya ce,"Ita kenan maganar, je ka wajen
iyalinka." Ya mike jiki babu kwari, ya fito kai
tsaye dakin sa ya wuce, bisa gado ya kwanta
rigingine. Tunani ya addabe shi, ya rasa ta inda
zai 6ullowa al'amarin. Sati 4 kenan da suka yi
sa'insa da Zarah akan Nusaiba, sam ya rasa ta
yadda zai fuskance ta, domin shi mu2m ne mai
tsananin son ra'ayin sa. A JININSA YAKE!." Idan
ya so abu, ya so shi har abada, inda ya kyama
ce shi baya waiwayar sa balle ya daga masa
hankalli Sai dai a yau Abbansa yayi maganar da
za ta sa dole ya waiwayi abinda ba shi cikin
tsarin sa, wanda a da yake ganin sai dai rai yai
halin sa ko in ta gaji, ta nema wa kan ta mafita.
Ya tashi zaune yayi wawan ajiyar zuciya, ya dubi
agogon hannun sa karfe 9 na dare. Ya diro daha
gado, ya fice ya dauki mota iya bar gidan.
Kwana 2 tsakani. Ya kama ranar juma'a.
Wannan rana za ta iya zama daya daga cikin
ranakun tarihin rayuwar Nusaiba. Shigowar ta
daki kenan, sun gama shan hirar su da Antinta,
misalin karfe 10:30 na dare. Ta yi shirin barci ta
haye gado, ta jawo littafin turanci (Novel), ta
fara karantawa, don kauda tunani, kafin zuwan
barci. Bata wani jima ba, ta ji an dan
kwankwasa kofar ta, ta aje littafin ta taso ta sa
makulli ta bude. Sai da gaban ta ya fadi, saboda
wanda ta gani tsaye a kofar dakin ta. Ido waje
take kallon sa, shi kuwa bai saurari komai ba, ya
wuce ciki, hannun sa dauke da lemun
gwangwanin. (Coke). Tsakar daki ta iske shi, ta
nemi gefen gado ta zauna tana mai tsananin
mamaki. Lemun hannun sa ya miko mata. Ya
ce,"Ki sha yanzu." Ta kar6a ta duba, bakin
gwangwanin a bude yake, ta sake kallon sa,
bata iya cewa komai ba. Ya zura hannaye aljihu
ya ce,"Ko ba za ki sha ba? Ta gyada kai, ta
ce,"Zan sha mana." Ya ce,"To ki shanye, kin ji?
Ta amsa da kai. Ya juya yayi waje. Ta bi shi da
kallo, sannan ta juya bisa lemu, ta tsura masa
ido,"Menene dalilin bani lemu in sha da tsohon
dare? Kashe ni kuma yau zai yi? Gara ya kashe
ni ma kowa ya huta, shi kenan an raba
gardama." Kwalla suka tsatso mata, ta goge su.
Kan ta tsaye ta kafa gwangwanin lemu ta yi sha,
har ya kare. Tayi zuru gefen gado tana jiran
abinda zai biyo baya. "Yan mintoci kadan ta fara
hamma, idanuwanya su ka yi nauyi. Kafin ayi
haka, ta rasa duniyar da take, nan ta wuce
lauuuuu........bisa shimfida warwas! Minto 10
tsakani ya dawo dakin, ya zura mata ido. Sai
kuma ya ji tausayinta ya kama shi. "Tabbas
kwayoyin nan sun fi karfin jininta ga shi yayi
mata (Over dose)." Ya gyara mata kwanciya, ya
dafa goshin ta yayi addu'a. K'arfe shida na
safiya, ya shigo dakin Zarah rike da carbin sa,
yana ja. Ko gaisawa ba su yi ba, ta ce,"Ban ga
amarya ba, bari in duba ta." Ya ce,"Barci take
yi, tunda ta tashi tayi sallah, ta zube kamar
matacciya." Wayyo, gajiya ce, bari in kyale ta, ta
huta baiwar Allah. Tun da ka yi haihuwar nan
bata yi sukuni ba? Ya zauna kusa da ita ya
ce,"Ke ba kya gajiya da wasa amarya."Ta watso
masa harara ta ce,"Me ye na ka a ciki? Ya
langwabe kan sa a kafadar ta ya ce,"Babu komai
Antin amarya. Ni matsala ta na yi missing din ki
da yawa, yaya bayanin yake ne? Ta janye
kafadar ta, ta ce,"Koma dakin ka yanzun Umma
za ta kwaso ruwan wanka." Turo mata fuskar sa
yake yi kamar zai cinye ta, kawai muryar Umma
suka ji daf da kofar daki tana fadin,"Jama'a, wai
yau ina Nusaiba ne? Yayi zumbur ya suro Ameer
yana girgiza shi," Kai sarkin kuka ne ko? Ka
hana mutane barci da sassafe kuma ka tashi.
Dariya ta kullewa Zarah ciki, da kyar ta kirne ta
ba Umma amsa,"Barci take yi Umma." Ta
ce,"Allah sarki, gajiya ce, komai sa ta ce ita ce
za ta yi." Ta dire bahon wanka Zarah ta miko
mata kujera da kayan sabulu. Naseer ya miko
Bebi, sannan ya tsugunna ya gaishe ta, ya samu
ya sulale ya koma dakin sa. Agogo ya fara duba
wa kafe 7 sau kwata. Yayi kasake yana
tunani,"Kai 'yar mutane fa shiru? Ya tambayi
kan sa. Ya zubara ya fito. Kofar ya murda a
hankalu ya bude. Kwance ya hango ta yadda ya
bar ta, tun kiran sallar farko. Ya shigo ya maida
murfin a natse ya rufe. Ya matso ya shiga
bubbuga ta, "Ke! Tashi! Ba ki san gari ya waye
bane? shiru ka ke ji. Malam ya ci shirwa.Tsoro
ya fara kama shi, bai san lokcin daya haye
gadon ya tarairayi ta ba, ya dan bubbuga kuncin
ta,"Ke Nusaiba! Ke! Can cikin sambatu take ta
surutan da bai san abinda ta ke cewa ba. Tayi
lauuu.....ta fada bisa filo. Idon Naseer fa ya
raina fata. Bayi ya shige ya debo ruwa ya
tarairayo ta, yana shafe fuskarta, yana kira tare
da bubbuga kuncinta. Da kyar ya samu ta dan
budr ido jajur! Ta dube shi,"Ki tashi aka ce, gari
ya waye, kowa sai tambayarki yake yi." Ahaf,
ashe duk surutun banza yake yi, zurun da tayi
ma sa a cikin barci ne. A hankali ya ga idon ya
karasa rufewa. Ya dafe goshi, ya runtse ido, ya
ce,"Na shiga uku.!" Da ya rasa na yi, sai ya
gyara mata kwanciya, ya rufe ta ya bar dakin.
Mota ya dauka ya nufi gidan Yakubu ya dauki
doki ya bazama filin sukuwa yayi ta zagaye, ba
ji, ba gani, saboda damuwa. Ba shi yasan halin
da yake ciki ba, sai da ya ji shi cikin ciyayi yana
birgima. Yayi lamo kamar ya mutu. Wasu
mutane 2 suka dago shi suna tambaya,"Ba ka ji
ciwo ba? Ya mike ya na fadin,"Ban ji, ba na
gode." Ya kar6i akalar dokinsa a hannun su, ya
taka ya haye, nufi Tudun Jukun. Karfe 10 saura
kwata, yake fakin, ya shigo gidan yana fargabar
me zai shiga ya ji? Yana yin sallama kuwa.
Umma ta kwala masa kira. Ya nufi gunta
ajikinsa a sanyaye,"Ga ni Umma."Ta ce,"Nusaiba
barci har tara da rabi, da kyar muka tashe ta ni
da Zarah. Wane irin barci ne haka, yarinya bata
ko iya tsayuwa? Ya zaro ido, ya ce,"Ina take
yanzu? Ta ce,"Tana daki, ta ce kanta ma ciwo
yake yi, shine na ce ko asibiti za ka kai ta? Ya
wuce da sauri, yana shiga falo yayi karo da
Zarah ta fito kicin,"Yayanmu, barcin amarya yau
ya ba mu tsoro, kamar wacce ta sha wani abu?
Tana nan kai na faman ciwo." Tana daki ne?
Tana nan akwance." Ya wuce dakin, ya bude ya
shiga. Tana kwance Idanuwan ta rufe, ya tsaya
kan ta yayi kira,"Ke! Ki tashi aka ce a kai ki
asibiti." Ta bude ido jazur, ta dube shi, wani
sabon takaici ya lullube ta, hawaye suka cika
idanuwanta fal, ta ce,"Na sha magani, ya
daina." Umma ta ce,"A kai ki asibiti, ta so mu
tafi mana." Tayi shiru tunani ya rufe ta, bata
ta6a zaton Naseeer yana kin ta haka ba, sai
yanzu ta tabbatar da bata da makiyi kamar sa.
Shi yasa tunda ta wartsake, ta tantace halin da
take ciki, ita ma ta fara tsanar sa, irin wanda
bata ta6a ji ba. Tayi kuka cikin bayi, ta kuma
roki Allah yayi mata sakayya, idan har akwai
cutarwa a cikin abinda Naseer ya yai mata. Yayi
sauri ya kauda kai, jikinsa ya k'ara la'asar. Ya
kama hanya da sauri zai bar dakin. Zarah ta
kawo kai." Asibitin za ku? Ya ce," Ta ce bata
zuwa." Saboda me? Ta wuce gun ta, "Amarya!
Me yasa? Ta goge kwalla ta ce,"Na sha Panadol
Antina." Ta ce,"Ai yanayin barcin da ki ka yi ba'a
gane masa ba, shi yasa Umma ta ce ki zo a kai
ki."Tayi shiru bata da niyyar tashi. Can ta jiyo
muryar Umma,"Ina Nusaibar? Nan da nan ta
sakko daga gado, ko kafin Umma ta karaso cikin
dakin, ta dauko hijabi. Ya ce,"Kin ce ba za ki
ba?" Za ni Umma, hijabi zan sa." To ki je yana
jiran ki a mota." Suka fito Zara ta rako ta bakin
kofar gida. Ta shiga mota. Suka tafi, babu mai yi
wa wani magana. Sun iso cikin asibitin. Nusaiba
fa ta kafe ta ki fitowa daga mota. Yadda bai ce
mata fito ba, haka ita ma bata motsa ba daga
inda ta ke zaune ba. Haushi ya kume shi, yana
ganin kamar tana son ya rarrashe ta ne." "Lallai
yarinyar nan ta raina ni." Hannu yasa ya zaro
wayarsa, ya danna (Ear piece) yana jin gindan
Rediyon (Queen FM). Ga hotunan Ameer yana
kallo hankalin sa kwance. Kusan minti 30 suna
zaune, ita ji take kamar ta fice daga motar tayi
tsuntsuwa ta ganta gidan iyayen ta. Da ya ga
abin na ta da gaske ne, sai ta buga tsaki. Shi
take 6ata wa lokac, sai ya buga tsaki yayi wa
mota key, ya figeta a guje. Yana yin fakin kofar
gida, ta bude ta fito ta shige cikin gida. Ya bi ta
da kallo, kafin ya ce aran sa,"Duk su Zarah su ja
siyo min raini." Yayi tsaki ya fito ya shiga ciki.
Suna tare da su Umma suna tambayar ta yadda
aka yi? Yana isowa, tana fadin,"Babu komai
Umma, dama maganin barci na sha, don un
sami barci, ashe ya fi k'arfin jini na, amma
Likita ya ce ba komai zai sake ni." Umma ta
ce,"Ai shi ke nan, sai ku kiyaye shan
maganunguna haka kawai. Don Allah kar ki
sake, kin ji? Ta ce,"To Umma." Yinin nan guda,
bata iya cin abincin kirki ba. Saboda tsabar
tunanin kaddarar da Allah ya sauko mata.
Washegari ta tambaye shi zuwa Kaduna.." A
dawo lafiya." Ya ce da ita. Da kan ta ta tuka
motar ta tafi.."Can ta wuni tare da Umman ta,
suna hira ta ji dan sanyi a ranta. Kamar kar ta
dawo ta rink'a ji, shi yasa ta rink'a nuk'u-nuk'u.
Yamma tayi sosai. Abban ta kuwa ya ce ba za ta
kwanan ba. Direba yasa, ya ja mata motar ya
dawo da ita. Shi ya koma a ta haya.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sannu a
hankali Zarah tayi arba in. Kodayaushe Ameer
na wajen Nusaiba, ita ke masa komai, ta shaku
da shi sosai, kuma tana son Yaron, duk da irin
cin kashin da Baban sa yake mata. Wanda har
yanzu abinda yai mata, yana cikin ranta. Ta sa
ido ta ga ko zai sake kwantawa, amma baiyi
gigin k'arawa ba, saboda shima al'amarin ya
dan sanya shi nadama, bata dai isa ya nuna
mata ba, balle ya bada hakuri. Saboda haka
suka ci gaba da zaman da suka saba tuntuni.
Kwanan Ameer 50 dai-dai, yayi wayo ya kumua
shiga ran kowa. Da asuba Zarah ta farka tana
mamakin irin barcin da tayi. Lallai Ameer ya sha
kuka, bata ji ba. Domin tayi tunanin tun lokacin
da ta bashi nono take barci. Tausayin shi ya
kamata, ta tashi ta dauki shi. Kara bude ido tayi
sosai, don sai taga kamar. Gaba daya jikin sa ya
sandare Tsoro ya kamata, jikinta ya dauki rawa
ta dan girgiza shi, ina rai ya riga yayi halinsa, da
sauri ta diro daga gado tare da shi ta nufi kofar
dakin Naseer ta bubbuga, ya fito ya bude mata.
"Duba Yaron nan ka gani ko motsi ba yayi.
"Inna-lillahi"wa-Inna-ilaihir-raji'un! Haka yake ta
faman fadi yana girgiza shi. Tuni Nusaiba ta ji,
sai ga ta a gigice. Naseer yayi waje da shi, suka
biyo bayan sa, suka dunguma sasan su Umma.


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100


Ajininsa yake 2-04
Posted by ANaM Dorayi on 08:19 PM, 20-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
Abba ya kar6e shi, ya rungume a jikin sa ya
ce,"Ku yi hakuri. Allah ya kar6i abin sa."
Nusaiba ta sulale nan hawaye suka tsinke mata.
Zarah kuwa dakin ta ta koma ta zauna bakin
gado tana sallallami. Shi kuwa Naseer kafewa
yayi kai da fata aje asibiti a duba masa Yaro,
k'ila suma yayi. Ya dube shi ya ce,"Hakuri fa za
ku yi Naseer, wannan yaron ya riga ya rasu,
babu abinda za'a iya yi masa. Kujera ya zauna
dabbas! Idanuwansa suka bushe kamas! Kirjinsa
na bugawa.
Abba ne ya iya gayawa duk wanda ya kamata
ya sani. Nan da nan jama'a suka taru. Umma
tayi masa wanka, aka shirya shi,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment