Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waiwayar gidaba koson sanin halinda dangintasuke ciki lokaci zuwa lokaci take wayadasu Umma gaba d'aya tacire k'aunar Adeel a *ZUCIYARTA* harmamakin kanta take watarana Wai itace kemantawa dashi amma duk Sanda tatinadashi tabbas *ZUCIYARTA* saita motsa domin tasoshi Sosai Saidai tad'auke d'amarar mantawa dashi tinda ba itakegabanshi ba Kuma batason namijin dazaikasance k'aunarta gareshi tafi yawa hakan yasa tazab'i cireshi aranta baki D'aya, Kuma Alhmdllh Ubangiji yana K'arb'ar Addu'ar ta domin tanasamun sauk'i akai Kullum zab'inta takan rok'a gurin Allah, wata d'aya yarage mata ta kammala karatunka na master's duka tadawo Nigeria..



Khairyce a kitchen tana had'amusu girki domin yau wurinta yake,

Shigowa Azma tayi tanawani yatsine fuska dataga Khairy tamkar taga kashi, fridge tabud'e tad'auko ruwa Marasa Sanyi harzata fita Kuma saita dawo tsayawa tayi tasha ruwan Had'id'a jifa da gorar suran ruwan suka fallatsa sukawaneke jikin Khairy domin saiti da ita tajefa gorar, juyawa tayi zatafita , cikin Jin zafin Abun Khairy tace"ke mlm bakiganin Abunda kikayi ne ko makauniyace ke,"?



Juyowa Azma tayi tadawo tanamata kallon k'ask'anci domin dagangan tayi sotake tatanka "ke lalle yarinyar nan wato harkinyi baki dakike iyamin magana nice makauniya ba,"?



"Eh Mana idan keba makauniya bace to mahaukaciyace kanwane dalili zaki watsamin ruwa,"



"Saboda kinyi gangancin shiga rayuwar da batakamaceki ba kamarni nagirme ajin ace Inada kishiya kodako wadda ta ansa sunanta balantana ke k'od'ad'd'iya y'ar matsiyata y'artalakawa, ma....,"


Tauuuuuuu taji Khairy tasauke mata Mari a fuska,

"Wllh bazan d'auke zagin Iyayena gawane k'aramin Mara kunyaba daga yau daga yanzu duk Wanda yasake Fad'ar kalmar banza ga Iyayena wllah saina bashi mamaki bazan sake saurarawa kowaba Wllh,"



"Lalle nikika mara,? Kina y'ar talakawa zakisa Hannu kimareni? Heee bakisan wacece Azma saina nuna miki tawa kalan haukar, kinmareni a fuska Amma wallahi a zuciyarki zanrama saikinga nawa kallan kishin yanzu mukafara nayi Miki Alk'awarin kuma wannan Marin bazai tafi Abanza ba kema saiya sauka kanfuskarki,"

Ficewa tayidaga kitchen d'in cikeda sak'e sak'en Abunda zatamata tajefa Bak'in ciki a yau, samo mafita tayi hakan yasa tasake shewa tafad'a kangadon tareda cigaba da Chart's d'inta da saurayinta Ameer.


Saikusan yamma Adeel yadawo d'akinsa yawuce gajiye canne k'a Ida kowacce tasameshi dan hakacan Khairy takaimasa Abinci sunaci suna fira yau cike yake da d'aukin kasancewa da ita, shi harma yamanta dawata Azma, Kwanciyar tayi kank'irjinsa suna fira Ahankali salon yasoma sauyawa sunatsaka da faranta ranjuna sukaji k'arar nwayarsa kamar zaishare Kuma Abun yayi yawa yasa yamik'e Cikin takaicin katsesa yaduba wayar daddy Saida gabansa yafad'i yadai daure yad'auka "Kayi daidai Adeel yanzu Shirin kashe y'armutane kake ace Batada lafiya sai gidane zasusani bakaiba yanzu indabandakatar da mahaifintaba kasan meye zaifaru Maza kaje kaduba y'armutane,"


Tsaki yaja cikin takaici yazura jallabiyarsa yafito yanufe d'akin Azma tagani zuwansa daman lab'e take tayi Saurin komawa ciki takwanta kangadon tana nishi Had'id'a murk'ususun K'arya, k'arasawa cikin d'akin yayi yanafad'in"Saboda me bazaka fad'amun Bakida lafiya ba harsaikin Kira Daddy na,"



Shuru kawai tanacigaba dajuyintane kangadon duk tahargitsa komai, ganin Lalle dagaskene yasa yahau gadon cikin tausayawa yace"waimeke damunkine,"?

Kuka tasake masa tanak'ara shigewa jikinsa, nanik'arsa kawai take, kunnashi tasoma Cikin k'arfin hali yace"fad'amun meke damunkine," Hannunsa tad'aura kan mararta tanawani k'ara narkemasa, shafamata yasoma duk atinaninsa dagaske batada lafiyar ne,


Cikin kukan shagwaba tace"yunwa nakeji"


"Kinganiba tayuma yunwarce kedamunki, bari nad'aukomiki,"


K'aralafewa tayi jikinsa"a'a nibanason kamatsa inajin zafine bagawarkaba kakira Khairy mana kasatakawomin,"



D'aukarwayarsa yayi daga Cikin Aljihunsa yakirata, zaune take bakin gado tarafka tagumi ganin kiransa yasatad'aga da sauri

"Kikawoma y'ar uwanki Abinci yanzu ashe batada lafiya ne kiyi sauri," yanagama maganar yakashe Kiran sai sannu yakemata, itakuwa ta lafe jikinsa aranta sai dariyar mugunta take, a fili kuwa saik'ara narkemasa take,


Hijabi tasaka tad'auko Abincin A kula tashigo da sallama ansawa yayi kanyace tashigo, yarda tagansu Saida zuciyarta tamotsa taji wani irin kishi shisam baima lura da Yanayintaba Amma Azma tagani murmushi tasake mata Had'id'a kashe mata Ido d'aya,


Ajewa tayi Cikin dakewa takecemata Sannu,

"Yawwa" kawai ta ansa


"To tashi kici Abincin"


"To kazubamin"

"Kinga Khairynaaaaaa zubamata a plate d'in, zubawa tayi tabasu yak'arba yasoma k'ok'arin d'agata yabata kaudakai Khairy tayi duk cikin jikinsa tazauna yabata abaki loma d'aya tayi tasoma kakarin amai tana k'ok'arin mik'ewa, kamata tayi sai Sannu yakemata duk yarud'e Ganin yake kamar sakacinsa ne yasa ciwon yakamata saida yaga tadaina kakarin Aman sannan yadaina shafabayanta "Sannu mekikeso yanzu,"?

"Kagatagaji wallahi kawaima kutafi kada nashiga hakkenku bari nakira momyna tazo muje gida,"


"Nooo darenefa kuma ai Anan kikasami ciwon kawai fad'amun idantagaji nizanyi Babu indazanje saikin samu sauk'i itama ai maibari nazauna dakece fad'amun mekikeso,"


Cikin shagwaba tace," tea"

"Khairy jeki had'a mata tea yanzu,"


Kallon Azma tayi Azma kuwa sai dariya da gwalo take mata Afakaice,


"Kaga wallahi nagaji bazan iyaba" tafad'a tana mik'ewa daniyar barin d'akin


"Khairynaaaaaa nizaki cewa bazaki iyaba,"

Batako kulashiba tafice ranta namata zugi,


"Kinga Bari nahad'a miki," kwantarda ita yayi yafice dakansa yahad'a Mata tasha yabata magani Atare sukayi bacci rungume da juna, Khairy kuwa kuka tasha hartayi bacci..................



_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_


WhatsApp number 07064904617
0r
07031012948


*ZUCIYAπŸ’”πŸ”πŸ’”*
```FREE BOOK```


_APRIL (4) 2024_



_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE πŸ’žSTORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😒 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY β˜ οΈπŸ’€πŸ‘ΉπŸ˜ˆ... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYAπŸ’”πŸ”πŸ’”...Free book.....
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *ZUCIYAπŸ’”πŸ”πŸ’”*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._



*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ HAUSA NOVELS πŸ“š MRS_MLM TAKUCEπŸ₯°πŸ₯°*



................................βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“


........................


*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ HAUSA NOVELS πŸ“š MRS_MLM)*




*Page 99 To 100*



```FINAL.......
FINAL....
FINAL...... PAGE IN SHA ALLAH 18/4/2024 APRIL THURSDAY```


*Allah kabani ladan inda nayi Daidai cikin labarinnan inda nayi kuskure kuma Allah kayafemin...... Anan wannan Littfin yana ganardamu cewa kada ka walak'anta mutum Domin bakasan inda zai Amfanekaba watarana, sannan inak'ara Jan Hankalin masu nasudaina tsanar talaka Domin Suma dasukeda Kud'in Bawai rawa sukayi Allah yabasuba Kuma badan sunfi cancanta bane kowa da inda rabonsa yake Kuma kanada baida saika taimakeshi wannan Shine Rayuwa Allah kabamu Ikon Kyautatawa kowa da kowa ma Kuma Allah kashirya masu Kud'inka dakeda irin Wannan rayuwar Allah yaganardasu, mukuma Allah kabamu Ikon nema Kuma kabamu namu karabamu da Rok'on abun kowa Ameen Ameen......*




Batsammani saiga daddy gidan, Khairy ce Kawai Gidan saishi Sannu dazuwa suka masa ko kallanta baiba balantana ya ansa Hakama Mom"


"Ina y'ata take,"? Cewar daddy


Adeel yagyara Zama k'asanda yake Zaune yace" Nima kodanadawo bangantaba Kuma Bansan indatajeba dama bazaman gidan takeba,"



"Kaga Banda sharri Adeel damacanfa basonta kakeba," cewar mom


"Hunm kiduba d'akin nata kigani ai"

Mik'ewa tayi taje taduba bakowa tafito tacewa daddy "Tabbas batanan"

"Dagaskene bakasan da fitartaba,"? Cewar daddy


"Wllahi Daddy bansaniba Abunda tagadama take Agidannan Kuma ban isanayi magana ba domin tanaganin tasami power gareka"


Shigowa tayi tana taunar cingom d'inta tamkar batagansuba haka tayiwucewarta zuwa d'akinta


Adeel yace"ke Baki iya Sallama bane ko gaida Manyane baki iyaba kobakigasu daddy bane,"?



Juyowatayi a walak'ance takallesu tayatsina fuska"idan nagansu mezan musu,"?



"Amma ai inda mutunci saikigaidasu ko badan surukiba ai mahaifinkine tinda Abokin Abbanki ne so shida mahaifinki ai bawani banbanci ba,"


"Ah dakata dakata dakata nace Adeel tawace hanya yakeda Had'id'a zaizama kamar Abbana? Ah nifa banason kalan danki mahaifinka dai Kai yahaifa nikam nawa uban yanagidan wannan ubankadai so Saidai akirashi da uban miji,"


Sake Baki galala daddy yayi yana kallonta, Mom kuwa kasa hak'uri tayi tace" Azma dama hakakike Bakida kunya balantana tarbiya Ashe,"


"Too Hahaha lalle yanzu ke harkinada bakin cewa Banda Kunya ko tarbiya? Ai duk Wanda yasan rariya yasan dole tazubda ruwa maganar Rashin Kunya ko tarbiya Atanbaye nagaba kuma, mtswww Mutane sai Bak'in sa'idan tsiya inbanda munafurci meye nawanke k'afa rana tsaka kuzowa mutane," cigaba tayi datafiya


Adeel yace"to daga Ina kike Ni yanzu inatanbayarki a matsayina namijinki inakike zuwa a kwanakin wani sa'in harki kwana Batareda izininaba,"?



"To Sannu su miji Manya da ka'auran anfad'amaka direni zakayi guri d'aya? Wannan ai Saidai Kawai y'artalakawa badai niba domin ni inada Y'anci fita kuma yanzu nafara bashegenda zaidakatardani wallahi,"

Dukansu sakebaki sukayi suna kallonta da mamaki musamman Daddy Khairy kuwa mik'ewa tayi tabar wurin Aranta tanafad'in Allah ya Kyauta,


K'ala Adeel baicemata

Cikin takaicinsa daddy yace" yanzu kanagani Agabanka yarinya tatsitsiya tacimin mutunci tafad'amin magana sonranta amma bakace komaiba,"


"Habadai daddy mezance? Nikaina basauraramin takeba kuma kagani, Kuma ai takaine shiyasa bakaji metaceba? tace Saidai nayiwa y'artalakawa kuma Alhmdllh kadaigani saboda itatasami tarbiya barin wurin tayi Bayan duk Abunda kakemata haryanzu bata tab'a Koda kallonbanza bane gareka bata tab'ajin haushinka ko rik'eka arantaba Kullum gaisuwa maikyau takemaka amma wadda kakeso kake yabawa kaga Abunda tamaka saboda tanaganin kaida ita bawani banbanci saboda Itama y'armasu Kud'i ce, hak'uri kawai Zakuyi,"



"Tashi mutafi gidansu dai zani naga Iyayenta nata insune sukabata lasisin yimana Rashin Kunya,"


Mik'ewa sukayi sukabar Gidan Rai b'ace sukanufe gidansu, Cikin sa'a Kuwa duka sunanan palourn


"Lafiya naganku haka wujiga wujiga cikin Ranarnan,"? Cewar abban Azma


"Yoba dole kaganmu hakanba yarinya sai rashin Kunya............,"
Duk Abunda tamusu dawanda takewa Adeel yafad'a Masa,


Aikuwa Sai Abba yasoma masifa "yo ai bak'arya tayiba tagirme taduk'amaka Mana, saboda duk Abunda kake tak'amadashi itakanta tanadashi balantana kuma ni, dan haka Alhaji mansur Inak'ara g'argad'inka dakubi y'ata a hanakali inbahakaba wllahi kotuce zatarabamu, Aure yazama na k'addara da jaraba haba tashi kubarmin gidana,"


Alhaji haruna"ni kake fad'awa magana harkake cewa nafitarmaka daga gidanka,? Auran d'ana shine jaraba da k'addara harzaka iya kallon kwayar idona k'afad'amun Wannan maganar,"?


"Eh nafad'a maka duk Abunda Zakayi kaje kayi, Kuma idanbakabar gidannan ba wallahi zansaka karnuka sumaka Rashin mutunci,"

Girgiza kansa yayi yabar gidan Ransa harwani suya takemasa yanzu yakejin dana sanin had'a Zuri'arsa da Alhaji mansur amma koyanzu da lokaci dolene awarware Auran damacan Adeel bason Auran yakeba, mom Kuwa saik'ara zugashi take,




"Amma dear Meyasa baka hanataba datana musu Rashin Kunya,"?


"Hunmm Khairy Kenan waike yanzu kinji zafin Abunda tamusune,"?


"Sosai naji zafin hakan wllahi dankawai Banda Abunda zanyine dana d'auki mataki kanta Kuma kaima kanada laifi meyasa zakazuba Ido indakakeda dama kabari ayiwa iyayenka rashin mutunci,"?


"Allah Sarki Khairynaaaaaa zuciyarki Maikyau ce Wllh Ina godewa Allah daya mallakaminke, kinga manta da zancen kawai kwanta kihuta Bari nafita K'arb'o sak'ona,"



.........


Cikin sati d'aya Abid yarame dukyawani susuce kallo d'aya zakamasa kasan yanada damuwa, Tanbayar duniya Ummeensa tamasa amma ansar d'ayace bakomai hakanyasa takai zancen gun kakansa Maimartaba, tsaresa yayi da tanbaya Harsaida yafad'a masa Naina yakeso Saidai kuma yalura kamar tanada Wanda takeso,


Dariya Maimartaba yayi"haba saikace ba Namiji ba ai matsoraci baya Zama gwani kuma zankirata dakaina zanyi mata magana"

Shima dariya yayi cikeda Jindad'i yace"nagode ranka yadad'e Allah yak'ara Girma"


"Amee kaje Zamuyi magana daga sama"


Yarda Maimartaba yace hakan Kuwa Akayi domin taraduka family d'in akayi dukansu hardasu Adeel da matansa kowa ya hallara itakawai akejira, can saigata tashigo da sallama sanye take Cikin less dark maroon Wanda yayi matik'ar ansar fatar jikinta, sai k'aramin gyaledata yana kanta dawowarta kenan daga gun Aiki, "kuyi hak'uri khakhus go slow ne yarik'eni Allah yasa lafiya irin Wannan taron hakan nagaggawa," naina tafad'a tana k'ok'arin zama k'asa kusada Khairy sunayiwa juna murmushi,

"Waidama kece akasani zaman jira haka? Toni inaruwana da Abunda yashafeku, dahar Za'a katsemin uzurina asakani jiran wata banza,"cewar Azma tana yamutsa fuska

Jinsautin muryar kamar daga mafalki yasaka Naina saurin zabura tawaiga kamar wadda wani Abun yaciza,

Rik'e hannunta Khairy tayi tanafad'in"lafiya sister,"?


Mik'ewa tsaye Naina tayi Had'id'a nuna Azma da yatsa jikinta har rawa yake Cikin rawar baki tace"ya Adeel kardai kacemin wannan Itace Amaryar taka,"


Mik'ewa itama Azma tayi ganin Naina sambatayi tsanmanin sakeganin Naina Cikin Rayuwarta ba Lalle ko anyanka tatashi,


Zubawa juna Ido Sukayi cikeda tsantsar tsanar juna Had'id'a tuhuma ko Wanne da Abunda kecikin ransa


"Waimeke faruwane kinsantane Naina," cewar Ummeenta



Wani mugun kallo sukebin junadashi, takawa Naina tayi taje gafda Azma cikin k'asada murya tace"Yau k'aryarki tak'are,"

Hannu Azma tad'aga daniyar wanke Naina damari Cikin sauri tarik'e hannunta "kinyi wannan kuskuren daga farko amma Yanzu bazaki Samu damar sake aikatasaba"


Gyaran murya Maimartaba yayi yace"jikata kizauna kifad'amana meke faruwa Kuma inakikasanta,"


Zama tayi kusadashi"nasanta a Istanbul ne kuma Lokacinda Muka fita nida Shareef Acan mukaganta hotel tareda saurayinta idan zaka zagada photon ta kaf makarantar mu bawanda baisantaba tantiriyace Mara kunya batada k'awa macce Saidai Namiji kuma bawanda baisan Rashin kamun kantaba nayi mamakin yarda ace waikaine Adeel zaka k'are da Auran wannan abar,"



"Kunga nifa bazan saurare cinmutuncinku ba danhaka duk Abunda Zakuyi Bismillah,"


"Abunda zamuyi ai afili yake Kai Adeel Yanzu basai Anjima Inason kafad'a Gaban kowa kasaketa kuma sakinda baida gyara,"


"Koda bakanemi nayi hakanba zanyi domin koyanzu Auran nawa baihanata shek'e ayarba nasan Komai, dan haka kije Azma ni Adeel nasakeki saki Uku,"


"And so what's, mtswww matsiyata Kawai," tafice tabar Gidan

Nasiha Maimartaba yayiwa Daddy Sosai domin shine silar samun wannan marar kunyar cikin Ahlinsu,

"Abunda yasa nataraku anan shine nayanke hukuncin had'a Auran Abid dakuma Naina,"


Zabura Naina tayi Cikin rawar murya tace"Aure kuma kaka nida ya Abid,"?


"K'warai kuwa Naina na Isa daku shiyasa nayanke wannan Hukuncin nanbada jimawaba Za'a d'aura Kuma bawanda zaijada Hukuncina,"

"Amma kaka inada Wanda,..."


"Wayekikeso samadani d'an uwanki Naina? Mezaibaki Wanda Ni zankasa baki, wllahi Inasonki Naina fiyedashi,"


"Ya Abid yaushe kafara sona? Nidai a'a Gaskiya a'a abari nayi zab'ina dakaina ni banason Auran zumunci ko Had'i Gaskiya Ni a'a," tamik'e tana gunguni


"Naina kiyarda dani tawa Soyayyar ba irinta Adeel bace bazan tab'a watsamiki k'asa a'idona harcikin *ZUCIYATA* nakesonki wllahi idanbansamekiba komai zai iya faruwa dani dama *ZUCIYA* ta Naina kisaurareni dan Allah,"


Wucewarta tayi yabibayanta saurayin Shiga Gabanta yayi yad'auka gabanta yace"tinda Aka haifeki nake k'aunarki nayi iya k'ok'arina wurin b'oye tawa Soyayyar ne saboda kince Adeel kikeso dukanku Ina k'aunarku shiyasa bazan iya Fad'ar sirrin *ZUCIYA* taba gamedake amma nashiga wahala maiwuyar fassara, idan zaki tina Wanda yake yawan miki text da b'oyayyar number bakowa bane faceni,"


Saurin kallonsa tayi"k'warai kuwa nine Naina kiyarda dani" fidda Wayarsa yayi yakira Aikuwa saiga number tabayyana


Murmushi tasaki Had'id'a Godiya ga Allah daya batamai k'aunar harhaka Kuma Cikin ahlinta,

"Katashifa da mutane a palourn tafad'a tana k'asa k'asa da murya"


"Saboda Samun k'aunarki bazanji kunyar duk'amikiba Koda akasuwane haryanzu baki ansaminba kinasona,"?


"Eh inasonka ya Abid"


"Dagaske,"?


"K'warai kuwa"


"Yakai Wanda kikama Adeel," yafad'a yana kwab'e fuska Alamar kishi

Dariya tasaki"oh ya Abid rigima nifa yanzu nafahimce bana wani k'aunar Adeel Kawai haukan KURUCIYA ne"


"Kintabbata"


"Sosai inadakai ai magana tak'are Kuma my soul mate"


"I like this name"


"Me too,"


"To sarakunan Rashin Kunya" Cewar Hajiya mama


Guduwa Naina tayi sukuwa suka saka dariya...




BAYAN SHEKARA D'AYA

Anyi Auren Naina da Abid soyayya sukebugawa sosai Yanzu haka tanada cikinsa, inda Khairy kuwa yaranta biyu,


Daddy nagani Cikin tashin hankali domin kuwa Kud'insa masu yawan gaske danashi Dana jama'a dayak'arb'o dominyin canji duka dollars d'in sukab'ata, Koda zai'a Saida komai nasa korabin biyan bashin mutane bazasuyi ba tashin hankali yasashi fad'uwa yasuma akawuce dashi Asibiti masu Kud'i kuwa suntabbatar sai Anbiyasu Kuma baida Hanyar Samun Kud'in hakan yasa ciwonsa tsananta,



Tafiya bawan Allan keyi ga yunwa ga Rana gazafi kwatsam saiya hangi jaka gefen hanya yajuya ko Ina bakowa zuwa inda jakar mutumin yayi yaduba ganin Manyan Kud'ine Saida yatsorata domin Arayuwarsa baitab'a ganin dollars ba d'auka yayi yanufe gidansa baifad'awa kowaba dama gidan shine Kawai matarsa batanan cikeda tsoro da zulmi yayi bacci zuwa safiya yashirya yatafi Gidan redi'o mafi kusa yace asaka cigiya idan ansamu maisu Afad'amasa nanma suke fad'amasa Ankawo sanarwar neman Kud'in nawani Alhaji ne, tare Suka rankaya zuwa Asibiti dankaisa yaga Alhajin ,


Kodasuka Isa Asibitin har afitoda daddy police sunsashi gaba domin Ansaka k'ararsa Kan Kud'in Sauran Ahlinsa kuka Kawai suke, Mom kuwa nangaban kowa tatakemasa gidan wuta kanbazata zauna dashiba tinda yanzu talaucine zaibisa haka yanaji yanagani yabata saki domin shak'e wuyansa tayi kandole saiya saketa,


Harza'a sashi mota mutumin yace"Adakata ga Kud'in natsinta Kuma nadawo makadasu,"


Sake baki Daddy yayi ganin shigar mutumin Koda ba'a fad'aba kaga talaka talakanma matsiyaci amma shine yadawo masa daduka Kud'in, dubawa Akayi Kuma duka Kud'in ne, Kama Hannunsa Daddy Yayi yasaki kuka yana Godiya Rana tafarko da daddy yayi nadamar aibata talaka, yanzu Kam yaga ranar talaka kuma yaji kunyar Abunda yafad'a gameda talaka Masu Kud'in dayake tink'aho dasu saigashi duka sungujesa Harda mom amma TALAKA shine yadawo masa dadukan farincikinsa,


Alkairai dayawa mutumin yasamu Kuma Daddy yamaidasa kamar d'an uwa, duniya juyin K'osai Wai yau Daddy ne da k'aunar talaka harda samun y'artalakawa ya Aura

Hunmmm lalle duniya tafi bagaruwa Jima maishirya d'an Adam Dan dole..


Mom Kuwa Abunda take tak'ama tatara tahad'u da yandafara Suka cinye,
Azma kuwa karayar Arziki tasami mahaifinta itakuwa tasami HIV garin yawonta Abu Yama Abba yawa kusan maikud'i Idan yarasa Kud'i daga K'arshedai Abba yahad'e *ZUCIYA* yamutu bajimawa itama matarsa tabisa Azma tashiga duniya..



D'ayan familyn kuwa rayuwa suke cikin farinciki da Jindad'i yanzu dai Daddy Yana k'aunar talaka Sadaka kuwa ba'a Magana saiya yazauna Cikin talakawa suyita fira ba kyama........


ALHAMDULILLAH

ANAN NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTFIN NAWA MAITAKEN *ZUCIYA* ALLAH YA K'ARA SHIRYAR DAMU, SAIMUN SAKE HAD'EWA A SABON LITTAFINA MAIZUWA NANBADA JIMAWA BA IN SHA ALLAH.......................

TAKU HARKULLUM MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 QUEEN OF WRITER πŸ“ HAUSA NOVELS πŸ“š (MRS_MLM)



_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_


WhatsApp number 07064904617
OR 07031012948


THURSDAY 18/4/2024 APRIL






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment