Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna masa hanya suje ya rakata,tafiya suke amma ba wanda yace komai acikinsu ita tana tunanin mai zata fuskanta a wajen aryana yayinda shikuma ke tunanin menene lababrinta,dahahka har suka iso bakin layin dazai sadata da gidansu,inda taja ta tsaya tare da shaida masa sun iso kusa da gidansu,karba icen tayi ta nufi gida bayan tace masa ta gode ,inda shikuma batare da yace mata komaiba kawai ya bita da kallo har ta kule ma ganinsa.
A cikin gida kuwa ba irin tozarcin da huda bata ganiba awajen aryanan sanadiyyar rashin dawowar fahriya daga inda ta aiketa da wuri.Fahriyance tashigo gidan cikin sanda dauke da icen da saheel ya bada tana muzurai,abinda ta ayyana a ranta shine yafaru domin kuwa aryanan rufeta tayi da duka matsananci,tana dukantane tanan fadin"har nice zan aikeki ki yimin abinda ranki yakeso,ko kin manta matsayinki ne, to uwarki ta fadamiki ke bakomaibace face baiwa wadda bata da ikon kanta kuma tunda kin ga ke kina da taurinkai to kijira nan da wani wata mai zuwa zan sayar dake ga fataken dasuke zuwa duk bayan shekara ,inkuma kinga akwai wanda zai sanja min abinda nayi niyyah to ki kawoshi.Duk da dukan yataba uwar da yar amma kalmominta na karshe sun fi komai tayar musu da hankali a cikin zancennata domin ba karamin girgizasu yayiba,cikin halin ko inkula da abinda ta fada ta juya izuwa dakinta tan cigaba da fadar duk abinda yazo bakinta.Bayan gama wannnan cakwakiyarne huda taja yar ta daki domin bata irin abinda ta boye don irin wannan ranar wato guntun abinci,domin tasan koda wa take takama yau daga ita har yar ta bazasu samu guntun kanzon da take basuba na kasan tukunya idan angama abinci,koda isarsu dakin sai huda ta zaunar da fahriya akan guntun buzun dayanke dakin wanda ko kare aka sakamasa dakyar ya kwanta akai,ba abinda fahriya take sai aikin kuka da jan zuciya,shiru uwar tayi tana kallon yar domin bata dama tagama cire abinda ke cikin ta kafin suyi magana,saida ta dau lokaci tayi shiru kana huda ta fara gyaran murya tare cewar"duk kwanakin baya dana ce miki cewa nina jawomiki wannan rayuwar kin amincewa da magan ta kikayi fahriya amma ko kinaso koba ki so nasan nice na zawo miki wannan rayuwar dakika tsinci kanki aciki,wanda gashi har tana nema tafi tawa rayuwar tsanani,kaicona dasan zuciya daban tuno yanayin da zan saka rayuwarki ba,saidai duk da haka bazan gaji dacewaa kizama mai jajircewa a rayuwarki,sannan ki tsare mutuncinki dakuma yarda da duk wata ,kaddara data zo miki a rayuwa wannan shine iya abinda zan miki,kuka take amma hakan bai hanata maida martanin maganar da mahaifiyarta ta kemata ba "ahaha ummi kidaina fadin haka da sannu komai zaizo da sauki kuma zan kasance mai tuna maganarki a koda yaushe,namiki alkawarin hakan.Dahaka suka cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin da suka kwanta.
Duk da kuncin da bayin allan ke ciki bai hanasu fawwalawa allah dukkan rayuwarsu ba,a bangaren fahriyah kuwa yazamana yanzu kullum itake debo ruwa sannan kuma da itaa ce,duk da hakan na bata wahahla amma hakan baisata damuwaba sanadiyyar haduwa da foneee da take a jejin dakuma wani sa'in saheel wanda take ganin a matsayin shima wani mai muhimmanci a rayuwar ta , yauma a zaune take a bakin rafin domin ta debi ruwa,yayinda kuma saheel na gefenta shida fonee suna ta nishadi,saboda yawan haduwa dasuke har yakai ga sun san lokacin da ta ke zuwa diabn ruwa da kuma itacen kuma da lokacin da idan takai a tare da su zata iya fuskantar kalubalen aryana,basu jima a zaune ba fahriyah ta fara yunkurin tashidomin lokacin tafiyar ta yayi,saidai kafin ta kai ga tashi saheel yamamta magana ta hanyar cewa ta koma ta zauna yanason yin magana da ita,fuskanta ne yai kicinkicin alamar idan ta dade zata karbi hukuncin a gida,lurada hakan da yayine yasa yace mata,"kin yarda dani ?"shiru tayi da jin tambayarsa kafin tace"ehhh" "to shikenan idan kin yarda dani,to kicire damuwar dadewar dazakiyi anan wajen acikin ranki,sannan idan kin yarda dani inason ki bani dukkanan tarihin rayuwarki,dakuma yanayin hakin kuncin dananga kina fuskanta a kananan shekarunki ,"a ynanayin da yake mata maganan da alamar rashin wasa kamar kullum ya tabbatar mata dacewa da gaske yake yi ba alamar wasa a lamamrinsa,hakanne yasa ta bude baki,tafara bashi lababrinta tundaga farkon abinda tasani har karshe,saidaid kuma ta tsinci kanta da kasa bashi lababrin abinda yafru a gida bayan haduwarsu ta farko,daga bayane da ta tuno yanda ta amince dacewa ta yarda dashi da farko,yasata kawai bashi labarin kmai batare da boye ko kadan ba....................."ina da mafita idan zaki amince"abinda yafito daga bakin saheel kenan bayan jin labarinta.

written by SADI-SAKHNA(the legendary novelist)


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

*BY SADI-SAKHNA*


(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

written by sadi-sakhna

(04)
Koda tazo kan fadamasa hukuncin da aryana ta yanke akanta sai yazamana muryarta yai rauni alamar abin ya taba zuciyarta sosai,hummm yaja ajiyar zuciya kafin yace"a yanayin da kika bani lbrin ina ganin akwai mafitar da za;a samu akan lamarin"kallonsa tayi da alamar mamaki kafin batare da tace komai ba, ciigaba yayi da magana ta hanyar cewa"ina ganin inada wata mafita amma inaso kije kiyi tunani akai idan kinga hakan yayimiki"shiru yayi domin jiran amsar abinda zatace,kallonsa kawai tayi kana tace cikin muryar tausayi,daga ni har ummina bamu da wata mafita a halin yanzu sannan,saidai abu daya nasani shine banason abinda zai rabani da ummina nabarta a wanna halin itakadai,duk da cewar yanayin kangin bautar dazan shiga agaba idan har kudurin baaba aryanan ya tabbata akaina sai ya ninka wanda na ke kai yanzu"tausayinta ne ya darsu azuciyarsa kafin yace cikin muryar rarrashi"hakane abinda kikace saidai ita umminnaki itama irin tunanain ki takeyi wato batason ki shiga yanayi marar kyau,sannan mafitar wannan lamarin shine dolene ki cire burinki na farko wato kinisanta da umminki ta hanyar barin wannan gidan na tsawon lokaci kafin ki cikawa umminnaki burinta"abinda yafada ya bata mamaki matuka nacewa dole tayi nesa da mahaifiyarta idan tanason ta cika mata burinta na kaucewar yar ta daga kangin bauta,kafin takai ga maganr dake bakinta sai ya katseta ta hanyar cewa"karki bani amsar da baki gama tantancewaba,sannan kiyi tunani akan abu kafin ki zartar,kuma tun da farko nafada miki cewar nabaki lokacin dazaki zartar da abinda yake daidai na rayuwarki,domin kullum ki fuskanci girma kafin ya fuskanceki.Zaki iya tashi naraka ki kaman yanda nsaba a kullum"haka suka gama magananr batare daya sake bata damar yin wata maganrba,mamakin mutuminne yasake kamata dakuma yanayin maganarsa,har suka iso wajen da zasu rabu kana ya juya ya kalleta"idan makullin hannunki yakas bude kofar da kike hange,to kijaraba wata kofar harki samo kofar makullin,karkiji shakkar shiga duk kofar da makullin yabude koda kuwa abinda take cikin kofar bai mikiba,hakika rayuwarki abin tausayine amma kisani watarana sai labari"koda ya kawo nan da zancensa sai yamata kyakykyawan murmushinsa kafin ya zuya domin komawa da baya,duk da acikin kalamansa ba wanda tasamu mafitarsa amma hakan bai hana ta basu ma'ajiyi arayuwartaba hartakai ga ba kalma daya da da ta bace a cikin kwakwalwarta ba.Juyawa tayi ta nufi kofar gidan,sai a sannan kirjinta ya buga a ta tuno irin dadewar datayi a rafin,shiga tayi sandarta kanta tsaye tanufi inda randar aryanan take,sai bayan tajutene tajuyo ta kullah da aryanan akan wata kujerarta,jikinta ne yafara karkarwa domin amsar hukuncinta,saidai ga mamakinta babu kalma daya daya fito daga bakin aryanan,saidai harara data ke aika mata kaman idont zai fito,ganin bata kulata bane yasata shigewa dakinsu da sauri,abinda yafaru da wasu lokuta kadan dasuka wuce tsakaninta da saheel ne yadawo mata cikin kanta,tambaya tayima kanta wanda bata da amsarta wato"shin yaaa saheel yanada hannu a rashin fadan baaba aryana?ta ya ya?"ohoooooo
************ ****************
A daular SARAHAM karkashin jagorancin sarki HURUDDEEN dan SHAMAM.Shekaru biyu da suka wuce a yankin.
Daular saraham,daulace data wuce hankalin duk wani mai tunani afuskar kyau da kayatuwa,a bangaren tsari dakuma dumbin mulki.Sannan duk wata masarauta da take wanzuwa a wannan zamanin tana karkashin ikon ta,wannan daukaka ba iya shikadai daular sharaham take dashiba harma da karfin dakaru wanda suke a jinsi daban,sannan kuma anmusu horo na musamman wajen watsa duk wani taaro daya aikata ba daidai ba,duk da daukakar da wannan babbar masarauta take dashi hakan baisakata aikata badaidai ba ga mabiyanta,tayi suna wajen adalci dakuma kaunar duk wani wanda yake karkashinta hakan ya taimaka wa wannan masauranta wajen daukar duk wani abu daya fito daga cikanta da muhimmanci sosai.
Wannan daula ta saraham tanada girman kasa kana dakuma mutane masuji da a fada a sassan duniya ,yawancin duk wanda mutum yagani a wannan nahiya to yakasance mai yawan matsayi idan har an gwadashi da halittun sauran nahiyoyi ,yanayin halittar su mai daukar haske daga idon ma'abocin kallo musamman wanda suka kasance jinin sarautar wannan nahiya ,shiya basu kashi mai tsoka wajen dagun kai ga sauran al'ummar dabasu kasance daya daga cikinsuba.
sarki HURUDDEEN dan SHAMAM shike rike da ragamar mulkin wannan masarauta yanada ya'ya'guda biyu SHAMAM wanda ake kiransa da yarima AMAM ,da ga sarauniya SAFEENAH wanda itace karama kuma amarya a wajen sarki huruddeen ,sai macen wanda itace gimbiya MEELAH,kuma babbar ya' a wajen sarki huruddeen kuma ya' ga gimbiya ZULAIKAH wanda itace uwar gida a masarautar saraham.
Duk da kwanciyar hankalin dayake wanzuwa a cikin masarautar ,hakan ya kebantane ga iya al'ummar dake nahiyar ,amma masifar da'ake shukawa a cikin masarautar dakuma irin muguntar ta take wanzuwa mutun zai sha mamaki idan yagani.
******** ******** *********
WAIWAYE ZUWA GA GIDAN SARAUTAR SARAHAM.
next chapter please 😊😊😊🙌.



(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

whatpad username:SAKHNA03

phone number:09035784150

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

*BY SADI-SAKHNA*


(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐


written by sadi-sakhna

(05)

Lokacin da sarki shamam girma yazo masa saiyazamana yafara tunanin sauka daga kan mulki dan bawa dansa huruddeen shima damar baje tasa fasahar a fagen mulki.
Koda ya sanar da dannasa gudurin sa sai yanuna bai amince da hakan ba ,wanda saida ya fahimtar dashi kana yakarbi kudurin mahaifinnasa.
Al'amarine yakankama na bikin nadin sarautar sabon sarki a kasara saraham wanda take daya tamkar da dubu a dukkan fadin duniya.
A bangare daya kuwa babu wanda yakai gimbiya zulaikah farin ciki domin a ganinta tasamu duk wata nasara da take da burin samu a rayuwarta,saboda lokacin tana da karamin ciki wanda sai mutum ya kula sannan yasan da zamansa.A dukkan hidima da ake da kuma shirye shirye babu wanda yakai gimbiya zulaikah narka dukiya dakuma tanadin ranar nadin mijinta akan karagar mulki,a ganinta dole ne tafikowa a cikin taron duk dama allah yayita da san mulki dakuma mallakar kowa a karkashinta.
Gimbiya zulaikah ya' ce ga wazirin masarautar saraham wanda yashiga yafita har saida yayi nasarar hada yarsa da yarima huruddeen domin wani nasa kudurin da ba wanda yake da masaniya akai ,a fada lokacin da sarki shamam yayi niyyar murabus wazirin sa UWAISU yafi kowa bada baki akan kar hakan ta faru saidai lokacin da ya koma gida yasanar da matarsa SARAAHAH wato mahaifiyar gimbiya zulaikah sai yazamana sun fi kowa farin ciki da hakan,waziri uwaisu ne yakalli matartasa kana yace.
"a yau ina farin ciki sosai ,lokacin damuka dauka na burinmu yacika yazo,matakin nasara yana tare da mu ,da sannu ragamar wannan masarauta zata dawo jinina watarana"
"hakane kam domin a halin yanzu yar mu zulaikah na dauke da yaron ciki kaga idan ta haifi da namiji sarauta ta dawo jinin mu gabaki daya,dasannu zamu mamaye wannan masarsuta da kadan kadan "
kallon matar tasa yayi data gama goya masa baya da bayanin dayayi kana yayi murmushi gefen baki mai dauke da mugunta.
Ranar da takama ranar nadin sarki huruddeen sai yazamana maimakon wanda za,a nada yayi farinciki sai murnar takoma ga iya matarsa da danginta ,wanda a zahiri kuma kowa zai dauka tamkar basa farinciki da hakan.
Bayan angama nadine a fada ,sarki shamam mai sauka daga kan mulki yafara bayani kamar haka:
"hakika yau ta kasance ranar farinciki a gareni da allah yabani ikon mika wannan mulki ga dana wato huruddeen,ina yiwa daukacin dukkan al'ummata farinciki dasamun sabon sarkinsu wanda zai shigaba da mulkarsu har zuwa yanda allah zaiyi,kai kuma inajan hankalinka daka dora akan adalcin da wannan masarauta tasaba yi harma dakuma kara kokarinka akan yanda kasameta,saidai kafin na rufe jawabina ina mai sanar dakai cewar nayimaka zabin iyali ta biyu wato gimbiya SAFEENAH wanda take ya ga daya daga amintaccen sarkinmu wato sarki URWATU,wanda za'a daura a yanzu ,domin bai kamata sarki kaman na nahiyar SARAHAM yakasance da mata daya ba ,dan haka ina mai tayaka farinciki dasamun wannan dama na auran gimbiya SAFEENAH "
Koda yagama bayaninsa sai a take waje yadauki sautin muryar mutane na taya sabon sarkinsu wato huruddeen samun wannan nasarori a rana daya.
A bangaren waziri uwaisu kuwa har akagama hidimar daurin auren sarki huruddeen da gimbiya safeenah baiyi koda tari ba ,domin abin yazomasa a bazata yanda bai taba tsammani ba.
A cikin gida kuwa gimbiya zulaikah wanda yanzu takoma sarauniya zulaikah kuma mata daya tak awajen sarkinnata zaune take akan kujera tana wani shan kamshi agaban mutanen data gayyata domin su tayata murnar wannan rana ,a inda gefe daya kuma bayinta suke yabonta da kalmomi masu sawa duk wanda aka amdata masa su cewar yafi kowa a fadin duniya.
suna cikin murnar ne wata baiwa tashigo da hanzarin ta ,takai bakinta ga kunnen sarauniya zulaikah tana me rada mata wani abu da mu bamu ji mai aka fada ba,wani irin zabura tayi ta mike daga kan kujerar datake tana wani kumbura kamar maciji, fuskarta kuwa dauke take da wata irin razana kaman an aiko mata da sakon mutuwa,magana tafara cikin daga murya wanda har saida muka razana mu masu rahoto(ummu najma uwar tsoro canna ganta ta buya a bayana tana leko kai kaman kace fittt ta tsere da gudu)...
"hakan bazai taba yiyuwa ba domin nice ta farko kuma ta karshe a wajen sarki huruddeen ,bazan taba yadda wata tashigo gonata ba,idan kuwa har tayi garajen hakan to hakika sai ramin maciji yafi mata kwanciyar hankalin zama fiye da cikin gidana ,kin tafka babban kuskuren shiga gonata ko ke wacece ,inaaaa bazai yiyu ba dole a katse wannan auren dan ban amince dashi ba,bazai yiyu baaaaa"
wani irin numfarfashi take wanda har saida yasa mutanen dake wajen bajewa batare da sun shiryaba ,inda ita kuma uwar gayyar tai cikin turakar ta a fusace....nina ce madallah ,ni gani nasan waje ,harda gayyatar mamar faruqu rakiya ita da ummu najma ,amma ko yar kazar basu yaga musu ba ,tsabar rowa 😊😊😊.
koda ta nufi dakinta,daukar alkyabbarta tayi tai hanyar bata zame ko ina ba sai hanyar wajen inda bayinta da dakaru ke biye da ita a baya ,harara ta tsaya ta daga musu ,wanda har saida tasa hantar cikinsu kadawa dan tsoro ,ja sukayi suka tsaya daga bin bayanta ,yayinda tayi wucewarta zuwa gidansu .
shigarta gidannasu ne ta tarar da mamar ta tsaye ,bude bakinta tayi zatayi magana sai takatse yar tata tahanyar nuna mata daki ,wato ta shiga ciki,shigewa tayi inda tasamu babanta a zaune yayi shiru kaman yadaina motsi ,zama tayi a gabansa fuskarta a jike da hawaye ,tana ayyanawa a ranta kenan abinda aka fadamata gaskiyane,batasan maganar ta ya fito filiba saida taji mahaifinnata yana fadin ,
"tabbas abinda kikaji da gaskene babu karya a ciki ,dan a gabana hakan tafaru ,ban taba tsammanin ko wani ne yace da shamam ya aurawa dansa wata matar zai aminceba bare kuma shida kansa ,hakan yaban mamaki ,nayi tunanin yadauki ya' ta kaman yarsa ashe bahaka bane ,wai to yaushe suka hada baki da wancan sarkin ne bansaniba ?hmmmm ,saidai ki kwantar da hankalinki hakika shamam yasaya wa gidan sa tashin hankali da kansa ,domin kuwa bazan taba bari abinda suke tunani yakasance ba,inaso kibude kunnuwanki ki saurari mai zamu fada nida mahaifiyarki a halin yanzu"............
kuka sance dani a chapter ta gaba 😊😊😊😊


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

whatpad username:SAKHNA03

phone number:09035784150

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

*BY SADI-SAKHNA*


(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐


written by sadi-sakhna

(06)

"Da farko banason kinuna kiyayyarki a fili a wannan auran,inaso ki nuna tamkar baki damu ba ,sai kowa yasake dake akan haka kafin zamu dana tarkonmu akansu wanda basu da ikon fita daga cikinsa"
"shikenan abba zanyi yanda kace ,amma nida burina shine a wargaza aurennan tun yanzu dan har yanzu zuciyata takasa aminta da zancen kishiya,hakan yana kona min rai sosai"
"wai ke bakya jin abinda mahaifinki yacene ?ki kwantar da hankalinki da sannu zamu cimma duk wani burinmu ba karbar ragamar masarautar saraham ,ko baki gani yanzuma cikine dake ? idan kika haifi namiji ai saidai ta biyo a baya kuma bazamu taba barta ma ta haihu a cikin gidanba "
"shikenan mungama magana kitashi ki koma kar wani yazargi wani abu sannan ki tarbeta,cikin kwanciyar hankali ,,kuma ki kula da cikin dake jinki domin a halin yanzu shikadaine damar mu ta gaba"
shine abinda mahaifiyarta tagama fadamata bayan hudubar da waziri uwaisu yagama fada mata,tashi tayi ta fara shirin komawa gidannata tare da damarar aikata duk wani abu daya fito daga bakin iyayennata.
A bangaren amarya kuwa koda akasanar da ita daurin aurenta da sabon sarki huruddeen ,hakan bai wani dameta duk da batada masaniya akan shirin aurennata,saboda al'adar masarautar tasuce aurar da gimbiyo ga duk wanda yadace batare da zabinsu ba.
Zaune take akan dardumar dake dakinta bayinta na zaune a gefenta sai ga kira daga turakar mahaifinta akan yana nemanta,tashi tayi batare da tace wani abu ba tabi bayan jakadan cikin sanyin jiki wanda yakasance tamkar halinta.
Koda ta isa turakar iyayenta ,shiru tayi kaman lbrin daya ke zagayawa a cikin fadar bai iso gareta ba ,hakan yasa sarki uwartu fara magana.
"safeenah nasan bazakice komai ba ,kaman sauran yan uwanki akan abinda yake faruwa wanda nasan cewar labarin ya isa kunnenki ,to ki dauka cewar haka abin yake ,sarki shamam dakansa ya zo izuwa gareni neman iri,saboda kyawawan halaaye irinnaki yasa ni amincewa da zaboki acikin yan uwanki ,duba da dattako dakuma halin kawarai na masarautar saraham ,dan haka in fatan zakiyi biyayya akan hakan"
"inshaallah zan kasance mai yin biyayya akan hakan duk wani zabi daya kasance ya fito daga gareku matukar bai kasance sabon allah bane"
"nagodee da wannan magana taki ,da yardar rayuwarki zatayi albarka saboda wannan biyayya taki ,shikenan ki tashi ki tafi zaku fara bukukuwa na al'ada a sashen mahaifiyarku kafin suzo tafiya dake ,allah ya miki albarka tareda zuri'arki gabaki daya "
Tashi tayi wanda tana fita wani kiran yazo daga sashen mahaifiyarta ,wucewa tayi zuwa ga kiran mahaifiyar tata,tana shiga idan ta ya sauka kan manyan matan da suke zaune akan kujerun turakar mamar tata ,karisawa tayi ta gaishesu da daddaya kafin ta zauna a wajen mahaifiyar tata ,kallon gimbiya safeenah tayi kafin tace.
"nasan mai martaba yamiki bayanin komai akan abinda yake faruwa dan haka inso kidora akan yanda nasanki na halayenki ,duk da bikin yazomana a lokaci kadan saida munne mi alfarmar zuwa daukar amarya nan da kwana uku ,dan haka,akwai wanda aka dauka masu gyara dakuma kwalliya wanda zasu fara yimiki daga yau har zuwa nan da ranar daukar amarya,tashi muje dakin dazaki fara zama domin yin gyaran ko ?"
Tana gama bayanin ta mike suka fara tafiya zuwa wani sashe daban inda za'a fara gyaran jikin gimbiya safeenah ,wanda har suka isa tana yimata karin haske akan sha'anin auren daya hau kanta.

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

(07)

Share hawayen daya fito daga idonta tayi ,,kana ta gyara zamanta domin fuskantar sabuwar tafiyar dazasu tsinci kansu a ciki ,duk da dauriyar da zuciyarta ta kudurci niyyar yi ,amma duk da haka hankalinta a tashe yake domin bata san mai zata riska a wannan sabuwar rayuwar ba ,da haka suka yi ta keta garuruwa da kuma hanyoyi har ta kaisu ga isa ,nahiyar saraham,tun daga yanayin kananan garuruwan da suke farko farkon nahiyar ,hakan ya tabbatar musu da cewa tabbas sun shigo babbar nahiyar ,da babu kamarta.
Wasu irin dakarune masu yanayin halittar karfi ,suka fara zuya karafan dake jikin kofar shiga masarautar domin bawa gimbiya safeenah damar shigewa ita da tawagarta ,yanayin yanda kofar take budewa shiya zamo abin kallo ga tawagar ,saboda girma dakuma tsari na masarautar.
koda suka isa masarautar basu zame ko ina ba ,sai sashen da aka tanada a al'adarsu na saukar duk wata amaryar data shigo gidan sarautar.
Tun daga bakin sashen da aka sauke su suka tabbatar wajen ya hadu matuka ,inda aka saukar da amarya daban haka sashen da bayinta yake daban ,shkma maza daban mata daban ,sannan inda masu tsaronta suke shima daban.
Baiwa daya ce a wajenta itace sameerah ,wanda dama tun tasowarta ko yaushe tare suke ,gimbiya safeenah ce ta yaye mayafin dake kanta kafin tace ,"sameerah shin ke wani irin yanayi gameda wannan masarautar ,gaskiya har yanzu zuciyata a raunane take da wannan sabon waje dana tsinci kaina a ciki"
"ya shugabata hakika dole zuciya zata ji rauni kasancewar ta a wajen da bata mafarkin kasancewa ,sai dai duk wanda yadogara da allah to lallai allah yana tare da shi ,sannan dun rintsi mu ma zamu kasance tare dake ,a wannan waje batare da mun juya baya ba inshaallah "
"nasan zakuyi hakan sameerah sai dai ..............." bata kai ga karisa maganar ta ba ,suka jiyo maganar wasu mata daga bakin kofar suna neman izinin shigowa ,sameerah ce ta kalli gimbiya safeenah ,kafin ita kuma tayi mata alamar tace su shigo,ai kuwa kamar jira take ,ta daga murya tare da fadin,
"izini ya karbu daga wajen gimbiya sannan kuma sarauniya a wannan masarauta mai dumbin daraja"
koda jin furucin sameerah dasukayi ,sai suka fara shigowa ,daya bayan daya suna jeruwa a gaban gimbiya safeenah bayan sun gama shigowa ne suka rusuna gabadaya a gabanta su goma shabiyu ,yan mata ne masu kyawun halitta ,gabadaya fatar jikinsu kyalkyali take duba da yanayin halittarsu ,sannan kuma kayan jikinsu dukka iri dayane ,hakika wannan yan mata sun hadu sosai ,daya daga cikinsu ce tafara magana ,kuma da alama itace shugabarsu saboda yanayin shigarta ya fi nasu kayatuwa,
"laleh mar haba ya shugaba ta dazuwa wannan masarauta ta saraham ,kuma sarauniya kana kuma amarya ga mai girma sarki huruddeen,hakika idan za'a bamu dama ,zamu gabatar da kanmu a matsayin wani rukuni na bayin wannan masarauta wanda suke da alhakin kula da duk wani nau'in kwalliya na jinin sarautar saraham ,a yanzu ma idan sarauniya bazata damuba ,mun zone mushiryata cikin kayan ado na al'adar wannan masarauta domin fita da ita zuwa ga sauran bangaren wannan masarauta"
kara sunkuyar dakai sukayi lokacin da shugabarsu tagama jawabinta ga gimbiya safeenah ,uhmmm tunda suka fara bayanin sameerah ta tsiresu da ido ,yayinda gimbiya safeenah kuwa idonta yake kasa tun kallonsu da tayi na farko,sameerah ce ta yi gyaran murya kafin tace,
"shin sarauniyar saraham ta amince da bukatar wannan bayi na kwalliya ?"
sai a sannan ta dago kai ,kafin tace" ba matsala zasu iya fara aikinsu "cikin sanyin muryar ta.
Bayan sun ji abinda tafadane suka fara fitar da wasu abubuwa kala kala ,take yan matan

Please Login or Register in order to submit comment