Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan kayan marmari ,da kuma magani ,da haka har jikinta yayi sauki ta koma kaman ko yaushe.
A tsaye take a kitchen tana dafa musu abinci da rana ,dan yanzu itake musu duk aikin gidan ,duk da yana hanata wani amma haka ta dauke ko wane aiki yazamana ita takeyi saboda yanayin kadaici da take tsintar kanta a ciki ,koyaushe ita kadai ce a gidan, ko fonee baya dawowa yanzu sai yayi kwana uku bayanan ,rabonta da taga saheel ya zauna a kusa da ita tun lokacin da rayi jinya ,tana warkewa magana ta daina shiga tsakaninsu kwata kwata ,zuciyarta cike da tunani ta gama abincin da takeyi ,saboda halin da take ciki ko abincin bata samu ikon cinsa dayawa ba ta ajiye shi tareda komawa daki bayam ta zuba masa nasa a kwanon da taga yana sawa a ciki .
Har yamma tayi lokacin daya saba dawowa gida yayi amma bai shigo ba ,hakalin ta ne yatashi sosai ganin lokaci yana kara wucewa ,rana ta fadi gari yayi duhu amma shiru ,ganin bataga alamar shigowarsa ne ba yasa ta komawa cikin dakin domin yin ibada.
Tana gamawa ko addu'a bata samu yiba ta kara fitowa tana lekawa ko zataga dawowarsa ,saida bacci yafara yadaukarta akan kujerar da take zaune, kafin ta ji alamar shigowar mutum ,zabura tayi ta tashi tana kallonsa ,magana ta fara yi masa ,
"yah saheel lafiya ? wani abunne yafaru "
amma ba tambayarta daya daya amsa ,saima wuceta da yayi ya wuce cikin dakin ,binsa tayi a baya cikin sanyin jiki ,fuskarta dauke da damuwa ,tsayawa tayi a bayan sa ,saboda yajuya mata baya yana kokarin rage kayan jikinsa.
Zubewa tayi akan gwiwoyinta tareda sakin kuka mai tsima zuciya ,juyowa yayi da sauri domin ganin mai yasameta ,saikuma abin yabashi mamaki ganinta akan gwiwoyinta ,tambayarta yafara yi,
"ke menene yasameki ?
dago jajayen idanunta tayi wanda daga ganinsu dama sun tara abu dayawa ,
"yah saheel inaso kayafewa ummah gameda hukuncinta akanka ,na aura maka ni batare da tunanin zaka takura ba ,sannan nima kayafemin saboda kasancewa ta acikin wanda suka shigo rayuwarka ,lokacin da nazo wajennan nayi tunanin zan samu farin ciki ..........
saidai bahaka bane ,domin bazai yiyu ka ka takurawa wani ba kai kasamu farinciki ........
nayi kokarin guduwa na koma wajen ummah ta ,saidai kuma natuna abinda ummah ta ,ta taba fadamin watarana cewar;
"fahreeyah bazai yiyu nabar wajennan ba ,domin kaman yanda haramunne matar aure ta fita daga gidan mijinta batare da izinin sa ba ,haka ma baiwa ko bawa haramunne ya gudu daga wajen uban gidansa "
narike wannan maganar a cikin raina ,wanda nasan a yanzu ina matsayin matar aurenne ,wannan maganar ce ta yimin katanga ga barin gidannan ,sannan ni shaidace akan cewa ba abinda ka rageni dashi tunsanda na kasance a karkashinka ,saidai abu daya da har yau tun tasowa ta a rayuwata na rasa shi ,shine farinciki ,ina kara baka hakuri akan shafa maka wannan mummunar kadarartawa a rayuwarka ,saboda nasan kaima karasa wani abu tunda na shigo gidannan wanda a da ba haka kke ba ,....😩😩😩......kayi hakuri yaya saheel "
numfashinta har sama sama yake saboda tsabar kukan datayi ,wanda yaci karfinta sosai ,rikota yayi tareda mannata a kirjinsa yana babbuga bayanta da hannunsa ,domin ko bakinsa ya gaza budewa bare ya rarrasheta ,ko kuma ya fahimtar da ita abinda yake zuciyarsa.
Jin ya riketa gam a jikinsa kuma ya yi shirune yasa ta dagowa kanta tana kallonsa ,shima kallonnata yake ,kafin yakai fuskarsa kusa da fuskarta ,jin harshensa tayi yana lashe hawayen dake zuba daga idonta kana ya sauka har wajen bakinta ,...........bakinsu ya hade waje daya tareda zura mata harshensa.....。。。。
gabobin jikinta da kuma tunaninta ne suka bijiremata a wannan lokacin ,ta hanyar amincewa da bakon yanayin dayake shigo musu ba tareda izinin ta ba ,duk abinda yake mata tana jinsa har takai ga ya zarce inda yakamata ya tsaya ,amma kuma zuciyarta taki bata daman tsayar dashi ................
jinta tayi a wata duniyar da bata taba jin labariba ,ko tsintar kanta a ciki ba ,saidai gashi yanzun yayannata yana aikata batareda saninta ba .............tunaninta ne ya tsaya cakkkk sanadiyyar wani irin bakon al'amari da ya ziyarci cikin jikinta ,wani irin kara ta saka ,kafin wani duhu ya rufe ganinta gabaki daya ................
A bangaren saheel kuwa,duk yanda yayi kokarin nisanta daga inda take saida hakan ya faru,lokacin dayaji dumin jikinta a nasa sai hankalinsa yatashi matuka ,har takai ga yakasa hana gangar jikinsa daga abinda take muradi ,cikin salo na musamman yake sarrafa dukkan gabban jikinta,lokacin da yakaiga shiga mashigar rayuwarta sai ya kasance yana yaki da zuciyarsa akan hana ta abinda take shirin aikata ,ganin bazai samu damar tsayar da ita ba ,saikuma kwakwalwarsa ta fara tsammanin rashin amincewa daga wajen fahreeyah ,amma babu wani tirjiya da kin amincewa daya fuskanta daga wajenta ,saima sakar masa jiki da tayi tareda bashi dukkan ragamar rayuwar ta ,lokacin da isa ga cikin rayuwartane yaji wata kara da ta keta cikin kansa ,saidai a halin dayake ciki bashida ikon karbar duk wani uzuri dazai iso gareshi ,barekuma har yayi tasiri a gareshi ..........
Bayan dawowarsa daga tafiyar dayayine ya kula da jikin fahreeyah da babu alamar motsi a taredashi ,zabura yayi ya mike tareda juyo da fuskarta izuwa gareshi ,
" wayyo me na aikata haka?"

SADI-SAKHNAce

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

chp(16)

Jijjigata yafara yi amma shiru babu alamar zata farka daga suman da tayi ,tashi yayi ya nufi bandaki ya hada ruwan wanka mai dan zafi kafin yadawo ya dauke ta kana ya kaita bandaki .
Cikin nutsuwa yake tafiyar da duk wata gaba ta jikinta saboda tsoron sake ji mata ciwo a karo na biyu,wani irin ajiyar zuciya ta saki sakamakon ruwan daya ziyarci fatar jikin ta ,shehsekar kuka tafara a hankali ,wanda hakan ya tabbatar da cewa ta tuna abinda ya faru da ita sannan yanayin jikinta ya tabbatar da cewa ta jin jiki.
Dago idonta tayi suka hada ido da saheel wanda shima dama kallonta yake ,da fuskarsa yayi mata alamar bada hakuri sakamakon har sannan bakinsa yagaza cewa komai ,mayar da idonta tayi ta rufe ,har yagama yimata wankan bata sake kallonsa har ya daukota suka dawo daki ,wata doguwar riga marar nauyi yasaka mata mai shara shara ,kafin yagyara mata kwanciya akan gadonnasu .
kallonsa tayi da mamaki jin yanda yake bata hakuri akan abinda yafaru ,domin batayi tsammanin zai yi magana ba ,
"FARYAH kiyi hakuri da abinda yafaru ,hankalina ya gushe a lokacin ina .......mai ....baki hakuri "
tsayawa yayi da hakurin dayake bata ganin murmushi akan fuskar ta 😊,
"wannan shine1dalilin dayasa kake kauracemin ? saboda kar ka rasa nutsuwarka a kusa dani ? "
"eh.....hh faryah ina tsoron aikata miki abinda nariga na aikata shiyasa bana zama kusa dake .........saidai aikin gama ya gama a halin yanzu wanda nariga na aikata ............."
katseshi tayi da cigaba da yake fada kafin tace ,
"yah saheel ka daina bani hakuri dan ka dau abinda yakasance mallakinka ,yanzu ina cikin farinciki daya kasance ba fushi kke dani ba ,kayine da wani dalili ,tun lokacin dana gane haka da baka cutu har zuwa yanzuba "
mamaki yaji dajin furucinta ,"kenan ta san wani abu akan wannan lamarin "yafada a cikin ransa ,
kaman tasan mai yake sakawa acikin ransa kuwa ,
"nasan kayi mamakin furucina koh ?😊😊,duk da nakasance wacce bata tashin cikin kawaye ba amma mahaifiyata tabani matsayi biyu a wajenta ,na uwa,dakuma na abokiya ,tasanar dani duk wani kalubale dazan fuskanta haske akansa ,hakan yasa lokacin da naji abinda kake aikata min banyi kokarin hanaka ba ,sai kawai na kudura a raina ajiyarka zaka karba a wajenna sai kawai na shirya taryar abinda zai biyo baya a zafin dazan ji ,domin ummah ta sanar dani wata magana lokacin da za'a daura aurenmu da daddare ,
"""fahreeyah inaso ki budemin kunnenki kiji mai zan fada;karki sabawa mijinki matsawar ba sabon ubangiji ya umarceki dayi ba ,sannan karki hana shi jikinki indan yabukaci hakan ,sannan kiyi hakuri da halin dazaki shiga a lokacin ,komai zai wuce watarana """
"hakanne yasa nasaka shi a cikin jerin abubuwan dazasu kasance abin tunawa a rayuwata "
rugumota yayi a jikinsa tare da saka kansa a gefen wuyanta yana shakar iskar data fito daga cikin gashinta ,
"faryah ke ta musamman ce ,hakika duk wanda yasameki a matsayin abokiyar rayuwa ya taki sa'a babba ,nagodee da fahimtar ki a gareni ,KE TAWACE HAR ABADA ,kuma nayi alkawarin baki kariya dakuma kulawa har karshen rayuwata ,zan zauna dake a kowane hali matsawar muna numfashi faryah nayimiki wannan alkawarin "
kara kankameta yayi a jikinsa har saida tayi yar kara ,dagowa ya da sauri tareda tambayarta menene ? Murmushi tayi masa tareda cewa cikin muryar shagwaba ,
"yunwa nakeji ,kuma nakasa motsawa "
"ohh shine dama yasaki yin kara ?
"uhm "
"ni nayi tsammanin ko matseki nayine ai ,bakida matsala idan abincine bari naje na kawo miki ,kar ki tashi kinji ?"
"tohh "
"yawwa sarauniyata "
"sarauniya kuma ? nidin ?"
"eh mana ,karki damu dayawan magana ,baki da lafiya ,bari na dawo yanzu ".
Yinin ranar fahreeyah batayi komai ba domin duk wani abu da take bukata daga fada yake kokarin yimata shi ,idan ta tashi to wani laluririn zatayi shima sai ya taimaka mata ,koda kuwa bata bukatar hakan .
Bayan sati daya da faruwar sabon al'amari tsakanin wannan ma'urata sai yazamana shakuwa da shiga tsakaninsu sosai ,koyaushe suna tareda juna ,yanzunma saheel ne a zaune kan kujera fahreeyah kuma na kitchen tana hada abinci ,batayi tsammani sai jinsa tayi a bayanta ,
"ahhhh yah saheel abincin zai kone fah "
"idan bake kika koneba banida matsala da hakan "
"uhm to kabari na gama tukun "
"idan kuma bazan iya jiraba fah ,kincemin ba yunwa kike ji ba ai ,to idanni kike dafawa ai kinsan ba wannan yunwar nakeji ba ........."
"uhm kayi shiru haka naji toh ",
ajiye abincin sukayi tareda lulawa inda suka ga yafimusu abincin.
Fahreeyah ce ita kadai a cikin gidan kasancewar rana ta fara zamanne ya isheta sai tashi tana zaga bayan gidannasu domin samun abinda zai debe mata kewa ,wani lambu gefe da gidannasu taje ta zauna ita kadai tana tunanin yanda rayuwarta ta sanja daga bakin ciki zuwa farinciki ,murmushi ita kadai take fitarwa daga fuskarta ,wanda duk wanda yaganta yasan tana farinciki ,wata k'ara da tajine yasa tashi da sauri tana waige waige kozata gano daga inane ,kuma da alama muryar macene mai karancin shekaru wanda take cikin tsaka mai wuya ,bin karar take har tazo ga wani waje ta labe tana ganin mai yake faruwa da yarinyar,wasu mazane masu jikin karfi suka daddaureta wani kuma na dukanta akan sai ta tashi .
Azabar da taga ana ganawa yarinyarne yasata rufe bakinta domin kar muryarta ta tona mata asiri ,jikinta ne yafara rawa har takai ga tazame daga inda take tsaye ,karar faduwarta ne yajawo hankalin mazan daga inda suke ,itama kuma a lokacinne ta dago da niyyar tashi daga wajen ,idanuwansune yahadu da nata ,inda tayi sauri juyawa da gudu ,amma kashh domin kafin takai ga barin wajen har suncimmata cikin zafin nama irin na yan maza.
Tsayawa tayi tana karemusu kallo cikin tsoro ,ganin yanda suke zagayata kamar sun samu nama ,ja da baya take yi suna kara binta suma ,fuskarsu babu alamar tausayi bare tasaka ran zasuji rokonta idan tayi niyyar yi ,bata gama tunanin mafitar datake kokarin samu ba taji wani abu yadaki tsakiyar kanta ,take wani duhu ya lullube ganinta ta fadi kasa sumammiya ............

SADI-SAKHNAce

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

chp(17)

Saheel ne a zaune a bakin gidansu gefensa kuma fonee ne a zaune shima.Dukkansu damuwace kwance akan fuskarsu ,da alama sun rasa wani abu mai muhimmanci a garesu ,saheel ne yayi ajiyar zuciya kafin yace .
"ina kika shiga faryah ? ina kika shiga sarauniya ta ?,hakika kin kasance wani bangare na jikina a halin yanzu ,rayuwa babu ke zaimin wuya a rayuwata ,kaman yanda na fada a baya ke tawace ,kuma da sannu zamu hadu duk daran dadewa sannan ............"
bai gama surutun dayake ba yaji motsin mutane a bayansa ,yana juyawa yayi arba da dogarai a bayansa ,dauke kansa yayi daga kallonsu kafin yace cikin muryar fushi ,"meyake tafe daku ? waya aikoku wajena iyeee ?😠"
sukuyawa sukayi alamar ladabi a gareshi kafin sukace ,"takawarka lafiya sarki dan sarakai ka gaji sarauta gaba da baya da girman daukakar ka yariman da babu kamar sa ..................tohh yadai ?? 😊😊,me kukace reader ,show me your perceive😊😊.
。。。。。。。。。。
Farfadowar fahreeyah ne daga doguwar suman da tayi ta tsinci kanta a cikin wani keji na itace tare da wasu sauran yan mata guda biyu da kuma wasu samari suma guda uku ,kallonsu take tana rarraba ido yayinda suma ita suke kallo alamar wuya a tattare dasu .
Babu abinda yake tashi acikin kejin sai numfashin su dayake tashi mai cike da wuya acikinsa ,bayan anyi tafiya mai nisane sukaji antsaya,wani mutumine yabude su tareda mika musu wani ruwa acikin gora mai masifar datti ,wawar karbar ruwan akeyi har ana ture wasu gefe ,kallonsu ta tsaya tanayi wanda tashinta kenan daga suman datayi bata gama gane mai yake faruwa ba ,saidai lokacin da taga ana kokuwar ruwane tagane cewar ashe fah itama kishirwa taci jikinta sosai ,saida suka gama kokuwar kafin suka dan diga mata a makogaranta itama ta shaida dan ruwan.
Bayan sun gama hutawane kuma aka sake cigaba da tafiyar da bawanda a cikinsu yasan lokacib tsaywarsu.
Darene yafara kama waje yayinda hasken rana yafara hada nasa yanasa domin ya tattare yabawa dare shima yaci tasa kasuwar ,a dadai lokacinne kuma zazzabi yayi dirar mikiya a gaba daya ilahirin jikin fahreeyah ,wani irin jijjiga takeyi sakamakon karfin zazzabin daya fi karfin tunaninta ,wata yarinyace bazata wuce sa'arta ba ta matso kusa da ita tareda tambayarta ,
"baiwar allah mai yake damunki haka ?"
"b....bansaniba n...nnn...nima ,amma jiki..........jikina zai...kkk...kama ....da wuta "
"ahah mai yayi zafi haka ? ko zazzabi ne yake damunki ?
"ehhh "
tafada hawaye yana zubowa daga cikin idonta ,saboda azabar ta ke ji a cikin ta ,matar ce ta dauki ta dauki wani dan tsummanta ta kara yafawa fahreeyah akanta saboda ganin karkarwar datake yi ,
"nagodee baiwar allah da taimakonki saidai bansan sunanki ba ?"
"ahh sunana LEEMAH ni y'ar cikin garin barduguce ,nice wacce kikaga suna dukana har suka kamaki "
"ayyah to me suke nufi damu dazasu kamamu ?"
"nima bansaniba ,amma daga gani ba nufine mai kyau ba saidai muyi ta addu'a "
"shikenan na gode da kulawarki "
"nima nagodee ki kula da kanki allah ya sawwake "
"ameen "
Haka suka ci gaba da tafiyahar sujayi kwana biyu a hanya ,wani gari daban suka fara hangowa tun daga nesa mai girman gaske,gofar garin aka bude musu domin basu damar wucewa ,kalle kalle suka farayi ganin abubuwa iri iri acikin garin har akazo wani waje mai tarin mutane ,korosu aka farayi daga cikin kejin ana jerasu kaman kaji ,saida aka gama jerasune wasu mutane sukazo suna kallonsu da alama zana zasuyi daga ciki ,wani babban cikinsune ya fara magana da cewar ,
"umarnine daga masarauta kaman yanda yake ,zaku bada bayi biyu ga masarauta a kowane kawowa kafin ku wuce inda zaku je "
"ehh mun sani zamu fitar da haraji kaman koyaushe,saidai kuyi mana uzuri ,domin zamu baku wanda suka gaji sosai saboda bazasu iya tafiya daganan zuwa masarautar saraham ba "
"shikenan ku nuna mana su ,babu komai idan suka huta za'a basu aiki "
mai bayinne ya jawo wani dan saurayi mai laushin jiki dakuma fahreeyah ya turasu gaban mutanen da suka zo ,
"wannan sune lagar tattu a ciki ,wanda bazasu iya doguwar tafiyarmu ba ,"
kallonsu suke kafin suka bawa wasu bakaken bayi dasuke tare dasu damar sakasu a wani kejin ,amma shi na karfene yana da zanen sarauta a jiki
tafiya akeyi saidai basa ganin hanya saboda yanayin tsarin karfen kejin ,kofar masarautar aka bude suka shiga har zuwa harabar wajen masarautar ,fito dasu akayi zuwa gaban UWAR BAYIN masarautar aka durkusar dasu ,kallonsu take cikin kaskanci kafin tace,
" menene sunanku ? "
"ni sunana fahreeyah "
"ni kuma sunana KHAMEEL "
"to ita wannan macen (tafada tana nuna fahreeyah )ku kaita sashen DANDALIN BAYI ,shikuma ku kaishi wajen YAN BARGA ,kutashi ku bisu maza ,gakunan kaman a karya ku ".
Tisa keyarsu akayi kowa zuwa inda aka bashi yayi aiki.
Tafiya sukeyi fahreeyah na binsu abaya ,tana tunanin tashi daya rayuwarta tasake juyawa a karo na biyu ""an gudu ba'a tsiraba kenan "",ta fada acikin ranta ,wani doguwar hanya suka bi tana biye dasu a baya har zuwa wani katafaren muhalli mai dauke da dakuna a cikinsa da yawa.
Wata mata ce tafito daga cikin wajen ta zuba wani uban adoo mai daukar ido ,maraba tayi musu cikin rangwada da kalmasa harshe ,
"maraban ku da zuwa wannan dandali mai dauke da abubuwan shakatawa dakuma dauke kewa ,mai yake tafe daku ?"
"sakone daga uwar bayi ,tace a kawo miki wata sabuwar baiwa zata fara aiki anan wajen ,"
"shikenan zata iya shigowa domin baje tata basirar a wannan fagen "
"tohh maza ki shiga ta amsheki ".
Matarce ta jata zuwa cikin harabar muhallinnasu ,tsayawa tayi ta tareda zuyowa tana kallonta,
"yan mata baki bani sunanki ba ?"
"sunana fahreeyah "
"ohhh suna mai dadi tun daga sunanki ke mai kyau ce sosai ,gaskiya zaki haska idan kika goge nan gaba kadan "
"uhmm addah bangane abinda kike nufi ba fah "
"😊😊,baki ganeba ,ki bari nan gaba kadan zaki gane mai na ke nufi ,kedai ki biyoni kawai yar sheela 😊😊"
"uhmm amma addah ..........."
"daina kirana da wata addah ,kice kawai ZILZILIYYAH ,haka sunan yake "

SADI -SAKHNA ce

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

chp(18)

Shiru tayi a tsaye bata da niyyar shiga cikin dakin saida zalziliyyah ta ne takula da cewa ita kadai take tafiyanta wanda takee bayan ta bata ma biyota ba ,juyowa tayi takalleta tareda cewa ,
"Menene kuma yatsaida ke haka? Kibiyoni na nuna Miki inda zaki zauna ko a wajen zaki kwana iye?"
"Ahah dama naji kince wai zamu dunga shakatar da wasu .......nikuma ina da aure fah gashi....."
" Ya'isa haka yan mata , me kike tunani,kina da zavi? to kicire hakan a zuciyarki ke baiwa ce yanzu Wanda zata bada jikinta don bakin masarautar nan suji dadi,Dan kimanta da cewar kintaba rayuwa a baya bare kuma aure ,idan kuma bahakaba zaki fuskanci hukuncin da bakya tsammani"
Jikin fahreeyah ne yayi sanyi game da jin furucin shugabar tasu, Wanda har aka kaita wajen dazai kasance muhallinta kukane yake zuba daga idonta saboda rashin mijijnta datayi Wanda tasan a yanzu yayi mata nisan da bata tsammanin zata iya cimmasa .
Wani daki zalziliyyah takaita mai girma ,saidai daga gani akwai mutane masu Dan dama dasuke rayuwa a ciki, saboda abubuwan kwanciya da kuma shirgi na masu dakin da idonta yayi arba da shi ta ko'ina,muryar zalziliyyah ce ta saka ta dawo da hankalinta daga barin kallon dakin zuwa kallon shugabar tasu,
"Toh wannan shine rukunin dakin dazaki dunga zama ,shi wannan wajen shine muhallin Wanda zasu dunga taryar bakin dasuke tsaka tsaki,wato ba masu matsayi sosai ba, yanzu bari naje ina da abinyi,zamu kiraku training idan kinyi s'a zaki iya shiga rukunin bayi masu tarar manyan baki,"
Duk magananr da takeyi har tayi ta gama fahreeyah bata tanka mata ba, saboda zabar jimamin halinda ta tsinci kanta a ciki.
Dudduba dakin tafarayi kozata samu wajen da ba kayan wata a gurin ta zauna,wani waje tagani mai a gefen kayan wata ta wajen barin dama a dakin, saida ta fara dan gyara wajen kafin ta zauna,jin kamar jikin ta yayi tsamine saboda tafiyar dasuka yi a hanya ya sata dan kishingida ko zata samu dan hutu kafin jiran mai rayuwar zata zo mata dashi kuma in an jima.
Can cikin baccine taji ana zungurar ta kafa,hakanne yasata tashi a razane domin ganin mai ya,wata mace tagani a tsaye a kanta tana mata wani irin kallo na rashin mutunci,yayin da matan dasuke bayanta kuma suka fara magana cikin dariya,
"Yau zaki san taka wajen KIRISAH,duk abinda ya faru dake kinyiwa kanki"
Ita wacce suka kira da Kirisah dinne tafara hura hanci cikin fushi tareda cewa
"Ba magana nake Miki ba?ko keh kurmiyace ba zaki ban amsa ba iyee?"
"Uhm ban.......san .wajenji bane,dazu zalziliyyah ta kawoni, kuma na ga,bakowa a wajen ne shiyasa na zauna"
"Kutt harni kike cewa dan kinga ba kowa a wajenne kika zauna?t to barikiji nafada miki,cewa nan duk wajena ne, domin ni waje daya yayimin kadan, kuma duk abinda bayanke a dakinnan akeyi,tashi kibani waje,kinyi sa'a ke bakuwa ce dakin fuskanci hukunci daga wajena"
Tashi fahreeyah tayi tareda matsawa can gefe a dungun dakin ta zauna tana mai da numfashi sakamakon wani zazzabin daya fara ziyartar jikinta a karo na biyu,zawo rigarta take tana sake rufe dukkan jikinta saboda sanyin da take ji yana ratsata,a dunkule a wajen da take baccin wahala yadauke ta.
Washa gari da wuri ta tashi saboda baccin kasan datayi saidai bataji zazzabin a jikinta ba kaman yanda ta kwana da shi jiya da daddare,yunkurawa tayi ta tashi saboda jikinta ba karfi,mata tayi arba dasu sun cika dakin masu irin kayan ta sak, saidai kaman wanda ita suke jira da gansu,haka taga sun fara tashi a tare kowa tana nufar hanyar waje,itama binsu tayi dan dama tanason ta rage marar ta saboda fitsarin daya ci karfinta sosai,wani wajen ta kula dashi suna shiga dakayansu wasu kuma na fitowa jikinsu a jike, jikinta ne yabata cewar bandaki ne dan haka kawai sai ta nufi wajen,ta saka kai zata wuce kuma sai taji maganar wata a bayanta tana fadin
"Baiwar Allah naga kina shirin shiga wajen wanka amma ba kayan dazaki sanja,ko ba'a baki kaya kala biyu bane?"
"Ahah an bani yanzu fitsari zanyi ne"
Murmushi tayi mata kafin ta ce
"Kuma fitsari a wajen nan, Hala ko ke bakuwa ce?"
"Ehh ni bakuwa ce"
"Ayyah to zo muje Nara kaki wajen fitsarin toh"
"To nagode"
Bin take a bayanta har suka je wani wajen amma ginin wajen sa masu matsakaicin girma ne, tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli fahreeyah,
"To nan shi ne wajen bahaya da fitsari,wancan kuma da kika gani wajen wanka ne"
"Nagode baiwar Allah"
"Kikirani da Sareenah"
"Toh"
Saida tashiga tagama abinda zatayi kafin ta koma inda aka kaita da sunan shine dakin ta, sake zama tayi wajen da ta kwana,saikuma ta ji ana shelar zuwa cin abinci, itama binsu tayi a baya domin ganin wace hanya zasubi.
Wajenne Shima kaman tsarin dakunansu,wato filine kowa yasamu wajen da zai zauna kawai.
Bayan sun gama zama ne aka fara binsu da abinci a kwano ana raba musu,duk wanda yagama sai ya kai kwano zuwa wani waje daban kafin ya fita,ita dai duk abinda suka yi binsu take tana aikatawa kawai, wajen wanki ne kawai bata bisu ba saboda kayan ta sabine babu datti a jikinsu tukunna.
A haka dai suka gama al'amarinsu na ranar har zuwa lokacin da wani daren yasake shiga inda shima zazzabin ta yasake lallabowa daya ga dare yafarayi,haka ta gama sheshekar zazzabin ta har bacci ya dauketa.
Washa gari bayan sun tashi, fahreeyah bata sha wahala ba wajen gano dukkan al'amuran da suke gudanarwa a kullum.
Saidai yau shugaba zalziliyyah ta kirasu zuwa training lokacin dasuka gama cin abinci,da koyarwar gyaran jiki aka fara nuna musu,sai kuma kwalliya da kuma karairaya domin birge duk wani da na miji,sabin bayin da'aka kawone aka fara yiwa kwalliya don ganin nasu zubin,tun ana fara kwalliya zalziliyyah ta kalle ta tareda cewa
"Fahreeyah na maida ke rukunin masu tarar manyan baki"

SADI-SAKHNA ce

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 .....

Please Login or Register in order to submit comment